Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai su da kara da karamci da tsantsar ha'din kai
sun ta ya ni murna sosai da abin alheri suka ce a baki."
Dariya na yi na ce." Aikuwa na gode sosai amma dai su yi hakuri ba zan ba su ba."
Yana dariyar shima ya furta." Kai tsaye abinda na gaya musu kenan, sun ce wai ke y'ar baiwa ce ta mussaman kina haihuwar yara masu daraja da albarka."
Murmushi kawai na yi
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa akwai kud'i da na bawa Nabila za ta had'o musu kaya akwati hud'u Hasan biyu Usaini biyu idan kin duba abinda bai yi ba ko ake buk'ata sai ki yi magana ko?"
Na dube shi sosai ina fadin." Akan me za ka bata kudi kace ta had'o mini kaya, me yasa ba ka yi shawara da ni ba ko ni ban san abinda ya dace da su ba?"
Ya ce." Hajiya sassauta mana ita ta nema ba ni naga dacewar bata kudi ta sayowa yarana kaya ba business d'in ta ne da take yi kenan da aje waje a sayo sai a saya a wajenta ko?''
Shiru na yi ban ce komai ba. Ba zan yarda da wannan shishshigi ba duk abinda yake tsakaninsu ba ni buk'atar ji, jiki magayi ne duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka. Ba ha'ka mai ya kawo rami, idan ta yi wari sai mu ji ai!
Ya cigaba da cewa." 'Kiyasin kud'in nan da mutanan nan suka ba ki a matsayin alheri na haihuwar yaran nan sun haura miliyan saba'in. Ni kuma na ba ki tukwucin 'karamin kamfanina na soap (sarrafa sabulun wanka) wanda yake mariri."
Da wani irin mamaki na dago ina kallonsa miliyan saba'in!
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kad'an kenan daga irin alherinsu ba wani abu ba ne, kin cancanci fiye da haka Allah Ya yi miki albarka."
Na ce." Me yasa za ka ba ni kamfani guda?''
Kai tsaye ya furta." Saboda ina shirye-shiryen bud'e wani zuwan da suka yi kenan!''
Na girgiza kaina a hankali na ce." A a ba zan kar'ba ba gaskiya ka haihu fa, nan gaba da ni da kai ba mu san iya adadin yaran da za ka sake haifa ba duk neman da za ka yi a yanzu saboda su za ka yi don haka ka bar shi na gode sosai da kulawa da addu'a abinda ka yi wa yarana wad'anda ba kai ka
haife su ba wallahi ya ishe ni."
Ya furta." Wanne yara ne ban haifa?'' Ya tsira mini ido da jin haushin maganata.
Na cire idona daga cikin nasa a hankali na kwantar da yaron ina fad'in." Ni dai ba ni neman fitina don Allah idan alheri ka yi niyyar yi mini ka yi daidai gwargwado wannan ya yi yawa.''
Ya ce." Abinda na yi niyyar bayarwa kenan Amina."
Na yi shiru ban ce komai ba amma zuciyata cike take da mamaki bayan zunzurutun kudi har miliyan saba'in da kamfani guda abin kamar ya yi yawa fa.
Koda su anti Yagana suka zo na gaya musu Ya Falmata ta dinga fad'in bake ki ka ro'ka ba baki ya yi akan me za ki ce masa ba kya so. Kowace haihuwa da alherinta tunda har ya iya mallaka miki kamfani to dukiyarsa takai ta kawo wata'kila shima bai san adadinta ba, idan kin lura bayarwa yake yi tana sake ru'banya. Allah Ya kawo wasu abokan nasa su sake baki arzikinki ya ninka na da mu abinda muke so kenan.
Ita dai anti Yagana shiru ta yi da alama yadda abin ya girgiza ni haka ya girgizata. Ta kasa cewa komai sai kallo.
Zuwansu anti Yagana ya 'karawa gidan walwala domin dama can akwai jituwa tsakanin Hajja da ita gefe guda kuma ga Ya Falmata sarkin barkwanci da bada dariya ta zauna tana ta ba su labarin matan da suke zaman shahada a makka da yadda suke shan tiriri da wahala guje-guje itama abinda ya koro ta kenan.
A daran ranar duka muna falon an gama cin abinci sai ga Hauwa ta yi sallama ta shigo Khalil na biye da ita a baya.......
'
*GARKUWAR BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*161*
Ni tausayi ma ta ba ni ganin gabad'ayanta kamar a ki'dime take da wannan yanayin na rashin gaskiya da kame-kame duk a k'okarinta na kare a kanta suka gaisa da Hajja tana ta nanata musu cewa ba ta da lafiya a kwance take har yanzu jikinta babu dadi har da 'yar 'kwallarta wai an gaya mata kwanansu biyu da zuwa amma ba su je gidanta ba.
Hajja dai shiru ta yi mata kawai ta zuba mata ido Hajiya Saratu ce ta tanka mata itama ba wata magana mai tsayi da muhimmaci ba. Yadda dai ta girba 'karya tare da d'orawa kanta ciwo duk mai hankali yasan da cewa k'arya ce tsagwaronta babu wani mashahurin ciwo a tattare da ita balle ya hana ta zuwa duba jininin d'an uwanta. Ko ba ta zo domin ni ba tunda kishiyarta ce ta zo domin mijinta kuma d'an uwanta balle ma ni ban ga abinda na yi mata mai muni ba da zata sanyawa ranta k'iyayyata mai zafi. Haka kowa ya bi ta da abinda take fad'i ana ta yi mata sannu da jiki
tana rantsewa da Allah wai bata da lafiya itama. Ni kuwa na tabbatar da cewa k'arya take yi tunda halinta ne d'orawa kai ciwo haka take yi ko kunya ba ta ji. Da haka muka gaisa da ita suka gaisa da su anti Yagana babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska Ya Falmata ma sai tsokanarta take wai ko itama ta ci wake ne. Ganin haka ya sanya ta saki jikinta saboda yadda aka goya mata baya cewar bata da lafiya har su Hajjan gabad'aya. Khalil ya dinga jin dadi yaron ya d'auki yaran d'aya bayan d'aya ya kai mata tana duba su tana dariya wadda nasan ba ta jin dadi ba ce fadi take kamarsu daya da Babansu yadda ake ta fad'a haka take cewa har tana kallona mun fi ki karfin jini Amina.
Ban iya ce mata komai ba sai kallo kawai domin koyaushe sabon darasi nake d'auka daga gareta. Ana haka maigidan ya sakko ya kuwa ji dad'i ganinmu tare da ita gabad'aya ana wasa da dariya shima ya zauna duk da akwai rashin sakewa tsakaninsa da su anti Yagana mussaman Ya Falmata kunyarta yake ji tunda yasan 'kanwar Mamana ce, bai dai za'ke sosai ba ana hira da shi jefi-jefi hankalinsa ma yafi karkarata kan yaransa da zamansa a wajan ya sanya suka kewayeshi. Ita kuwa Ya Falmata bata suruktaka da shi ta cigaba da sakin bakinta daidai misali a yi dariya idan ta kama a kuma jajanta a cikin abinda aka tattauna.
Tare suka tafi tunda dama kwanaki d'aya kenan da kar'barta girki gobe ne zai dawo gidana ya kwana.

Washe gari da wuri yarinyar nan Lad'ifa ta zo ta zauna zaman yi mana 'kunshi ta fara yi mini jaa kimanin awa biyu aka cire ta zana mini fulawa ba'ki a kafafu da hannu. Ya Falmatace za ta yi mini kitso idan sun cire lallan da aka yi musu domin ita da anti Yagana sun ce suma ba za a bar su a baya ba.
Wajan biyar na yamma sai ga tawagar gidanmu Gwaggo ce kawai babu domin bata jin dadin shine dalilin da ya sanya ba ta samu zuwa ba tabbas da nasan tare za su taho da su Hajja.
Mamaki ya kama ni sosai mota suka biyo ta haya hakan kuwa bai yi mini dadi ba tunda da sun kira ni sun gaya mini nasan idan na gaya masa zai iya sanya direba ma daga can ya d'aukosu duk yawansa.
Sahura da Yusura da yaronta da ba su jima da yin arba'in ba. Ummansu Hadiza da Ummansu Saminu Fati da Hassana da Usainar gidanmu sai matar Hamusu itama amma ba ta zo da yaran ba suna can wurin Gwaggo Yusi shine jagora. Da kuma Ummatu babarsu Sunusi uwargidan Baba Sule kuma k'anwar Ummansu Hadiza ce ubansu d'aya. Sai Fiddausi yarinyar da ta zauna a hannuna lokacin bud'e gidana na kuntau ita da Yusura a lokacin da na ta fi umara ta farko kaddarar aure ta ratsa tsakani muka rabu ta koma gidansu. Duk ga su yau dalili ya kawo mini su.
Ita kuma amarya Hajara matar Usaini ana can babu lafiya yadda Fati take gaya mini suna zargin ciki ne da ita ciwo take yi sosai har da su k'arin ruwa. Ikon Allah kenan
Wannan zugar da suka yi ta tabbatar mini da cewa dama sun shirya sun kuma tsara yadda tafiya za ta kasance amma rashin gaya mini shine abinda ya b'ata mini rai.
Sashenmu na ba'ki dake gidan na sanya aka gyara musu 'yan gidanmu kenan suka yada zango a can su Baba Tabawa na ta hidima da abinda za su ci. Sahura da Yusura kuma muna tare da su. Ita kadai ce na san da zuwanta a yau din saboda kayana da za ta kawo mini tunda mun yi waya da Hamusu ya ce mini ya kai mata tun kwana biyu da suka wuce amma shima bai gaya mini matarsa na tafe ba.
Sun yi mini bazata kuma na ji dad'i masu k'orafin ba su ta'ba zuwa ba dalili ya kawo su. Amma har yanzu ni dashi ba mu tsayar da ranar walimar ba. Kwana shida da haihuwa a yau din kenan gobe yara za su sake amsa sunansu amma ba ni tsammanin a ranar za mu yi taron walima kamar yadda ya saba duk haihuwar da za a yi masa alamu sun nuna akwai shirye shiryen da yake yi.
A daran da ya shigo na bi shi saman duk da ba girkina ba ne na Hauwa ne amma wasu lukutan yakan shigo ya yi sabgoginsa kafin ya fita kamar yadda idan ya je can yake yi, kuma ban ta'ba kalubantarsa ba ganin yadda shima yake takatsantsan da gujewa abinda zai kawo masa rikici yana wanka na zauna ya fito da ya gan ni a zaune sai ya d'auke kansa ya tafi ya tsaya gaban mudubi kad'an ya shafa basiline a jikinsa ya fesa turare ya sanya kayan shan iska fuskarsa ta nuna mini akwai abinda yake ji wa haushi.
Gaishe shi na yi ya amsa tare da zama gefena na d'an tsura masa ido ina kallonsa shima yana kallona kafin na ji ya furta." Zan ga ranar da zan yi miki abu ki yaba mini Amina har yanzu ban iya ba a wurinki na gode k'warai kin kyauta."
Na ce." Wani abu ne ya faru kuma?" Da wani irin yanayi ya ce." Saboda na baki wani abu da bai kai ya kawo ba shine ki ke bin 'yan uwanki kina gaya musu menene abin magana akan abinda na yi anan a gaya mini hujjar da ta rahamta mini yin kyauta da abinda nake so da dukiyata. Ke na ce na bawa wannan wuri ba 'ya'yan da muka haifa tare ba. Ko na ta'ba yi miki wata babbar kyauta duk tsayin zamana dake bayan wannan?"
A d'an sanyaye na ce." Wa na gayawa ka ba ni kyauta?"
Don har ga Allah ban yi tunanin su anti Yagana za su yi masa wata magana ba tunda ni su kadai na gayawa Babanmu bai sani ba haka zalika ban sanar da Baban Saude ba.
Ya gyad'a kansa yana fad'in." D'azu da safe kafin na fita 'yar uwarki ta same ni a haraba tana yi mini wasu maganganu shin me kuka d'auke ni ne? jahili wanda ba shi da ilimin addini ko me? kyauta ke na bawa ba yara ba. Ko kuwa idan na yi Hauwa ko a ahalinta alheri sai kowa ya sani. Za ku nuna mini yadda zan yi da abina ne Amina. Duk abinda nake yi ina sane babu wani yaro da zan haifa walau ke ki ka haifa ko ba ke ki ka haifa ba na fifita shi akan d'an uwansa. Ko an ce dole idan na kwanta dake a daren girkinki itama sai na kwanta da ita. An tilasta mini cewa idan na yi jima'i da Hauwa yau gobe sai na yi da Amina?."
Shiru kawai na yi ina kallonsa da mamaki. Lallai anti Yagana ashe shiyasa ta yi shiru bata tanka mana ba ashe da akwai abinda ta kud'irta a ranta yadda dai ransa ya 'baci hakan ya tabbatar mini da cewa ta fad'i maganar da ta tunzura shi kamar yadda yake nanata cewa dukiyarsa ce kuma duk abinda yake yi yana sane shi ba jahili ba ne.
Ya cigaba da cewa."
Babu d'ayanku da nake da ta'kidin takewa ha'kki ko na fifita yaranta duka ni na haifa kuma babu wanda bana so a cikinsu ina kuma addu'a Allah kada ya kama ni da hak'kinku, hakan kuma baya na nufin na sarayar da iko da mutuncinta ba duk wadda ta yi mini ba daidai ba a cikinku zan yi mata hukunci daidai gwargwadon abinda ta aikata mini. Idan har ba ki son abinda na baki shikkenan kada ki kuskura ki kara wata magana da wani zai tsaya gabana ya kalubalence ni. Na duba dacewa da cancanta a kanki ne Mutum nawa ne suke 'kasan ki? kuma mutum nawa suke ci da sha a karkashinki? mutum nawa ki ka tallafa suka tashi? ko kuma kin d'auka haka nake zaune dake kara zube ba ni bin abubuwan da ki ke gudanarwa
arziki na Allah ne amma menene makomar yaranki da koyaushe ki ke nanata mini cewa ba ni ne ubansu ba. Idan yau na fa'di na mutu a shari'a ba su da gadona. Idan na d'auki abu na baki sai ya zama lefi da tiri-tiri da magana kamfanin majizai na baki ne Amina?"


Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Har yanzu bakina a mace yake na kasa cewa komai saboda mutuwar jiki da mamaki duk yadda yake ganin k'ima da mutuncin anti Yagana yau ta kai shi bango tunda gashi yana ba ni sa'ko zuwa wajenta. Na rasa abin cewa kawai sai na yi shiru da bakina domin ba ni so kuma lamarin ya girmama shi da ita anti Yaganar babu wanda zan za'ba tana da hujja shima yana da tasa hujjar kamfani kuma muddin ana so na kar'ba akashe shi ya daina aiki koma gabad'aya a sayar mini da shi a bani kudin na had'a da wanda suke hannuna alherin da abokansa suka yi mini na nemi plaza cikin kasuwa na saya ko Kuma na sanya k'wararru su gina mini na sake fad'ada harkokina wannan shine magana.
Adamu ne ya kira shi a waya ina ji suka gama magana yana gaya masa gasu nan shi da Yusi za su kawo sa'ko in ji anti Nabila ita ba ta kira shi ba saboda tasan yana gida sai ta sanya yaran.
ya ajiye wayarsa to a nan ne na magantu cikin had'e rai na ce." Ka ajiye wannan kaya domin kuwa yarana ba za su sanyasu ba Allah shine d'aya ko kuma kawai ku yi tanadi kai da ita idan kun yi aure kun haihu shikkenan kun huta. Ko sun kawo kayan nan a banza, idan lallai sai Nabila ce za ta sayowa yaran nan kayan sanyawa a bar shi kawai zan saya musu a matsayina na uwarsu."
Bai juyo ya dube ni ba ya ce." To shikkenan ai tunda kin ce haka ta riga ta sayo sai a ce mata me? ki a ajiye kada Allah Ya sa ki yi musu amfani da shi din."
Na ce." Ba kuwa zan yi ba, ai ga shawara nan na baka za su yi maka amfani idan kun haihu."
Ya dube ni yana fad'in." Kina da hankali kuwa
Giwa da wa zan haihu?"
Na tare shi da sauri ina ce wa." Da ita mana ko ka d'auka shashashai ne mu, ka ji kunya wallahi."
Ya 'bata ransa yana fad'in." Yanzu ke tsakani da Allah ba ki ji kunyar yi mini wannan maganar ba, duk kalolin matan da suke duniyar nan Amina na rasa wadda zan aura sai wannan matar me zan yi da ita?"
Na ce" Me yasa zan ji kunya tunda kai ba ka ji ba. Haba Malam babu wata magana da za ka fad'i wallahi tallahi na yarda da kai, ina ruwanka da ita da business dinta ka sayi kaya a wajanta saboda kana tausayata mata ko akwai shagunan sayar da kayan baby's cikin garin nan da yawa me yasa ba za ka je da kan ka ka sayo ba, ka bi dare da rana ka samar da cikinsu sayo musu kayan da za su sanya ne zai gagareka."
Ya girgiza kansa yana ce wa." Ba zan shiga shago sayan kaya ba. Ni ma wanda nake sanyawa telana ne yake kawo mini su a dinke ya san irin yaduka da shaddodin da na fi so ko tafiya na yi kin ta'ba ganin na sayo muku abu, idan kina ganin za ki iya zuwa ki sayo musu abar maganar don Allah don Annabi zan baki kudi wannan din kuma sai a ajiye idan Allah Ya sanya na samu wasu biyun daga wajan Hauwa shikkenan na huta.
Ta'be baki na yi tare da d'auke kaina ban ce komai ba.
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Kafin na shigo na ga alamar muna da ba'ki tun daga haraba hakene?"
" 'Yan gidanmu ne!" Na fad'a a takaice. Ya saki fuska yana fad'in." Sun zo taya mu murna kenan, na ji dad'i sosai kuma idan na ci abinci zan sakko 'kasa mu gaisa sai a yi musu magana."
"To." Kawai na ce na tashi tsaye. Ya rike hannuna na koma na zauna kusa da shi. B'akin lallen da ya zanu a saman fatar hannayena ya shiga dubawa. Ya bud'e tafikan hannayen yana kallo yatsun ya yi marron sosai zanan fulawar ya fito. Ya dinga sauke ajiyar zuciya yana fad'in." Ya yi kyau sosai mu ga na 'kafafun." Gim na yi kawai ta yaya zan iya nuna masa k'afafuna na cikin safa. Ya sunkuya kuwa ya cire safar yana ta dubawa na zubawa 'keyarsa ido takaici da haushinsa ya ishe ni. Maganar Nabila idan har ta yi nisa akwai wani gagarimin lamari da zai faru tunda shi bashi da tunanin yin nesa da mu'amula mai tsayi da ita bayan gaisuwa. Ai tsakanin mace da namiji idan sha'kuwa da tausayi suka shigo ciki akwai alamun kauna. Ya nuna son cigabanta da tausaya mata tunda idan an yi magana sai ya ce business d'inta ne a saya a wurinta kada a je waje a saya.
Ya d'ago da wani irin yanayi na yi saurin d'auke kaina ya tsira mini ido har yanzu hannunasa yana cikin nawa ya ce." Za ki ba n      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  i abinci ko na tafi na kwanta a haka?"
Na furta." Duk yadda ka ga ni, amma ai ba ni ce mai baka abincin ba."

Ya ce." Kwana biyu itama tana ta ciwo kullum a kwance take ciki ne da ita ba kuma sosai take sarrafuwa ba ke kuma kin ga kina da masu aiki." Na katse shi da gaggawa ina fad'in.'' Na hana ka d'aukar mata aiki ne? tana da lafiya bata da lafiya ba abinda ya shafe ni ba ne. Cikin dai masu aikin gidan nan Wallahi babu wadda za a d'auka.''
Ya ce." Ba a ce dama za a d'auki ko daya ba, za a kawo mata nata masu aiki itama."
Na d'auke kaina ban ce komai ba. Ya ce."
A kawo mini abincin dai ko ba shi da yawa kada abin ya yi mini yawa kuma." Na tashi kawai na tsinci hannunsa saman tudun mazaunaina. Na juyo da sauri ina kallonsa. Ya cire hannun shima yana kallona. Wato da bai samu sararin d'ora hannunsa a kirjina ba kamar yadda ya saba sai Allah Ya bashi sa'a ya d'ora a na baya.
Ya furta." Menene fuskata za ki buge na tare."
Na janye idona daga kansa kawai na wuce cike da mamaki wai tambayata yake yi menene saboda na kalleshi wato shi bai d'auki abinda ya yi a matsayin wani abu ba."
Ina saukowa na tarar da ita ta zo ana ta hira da ita. Usaini ma yana hannunta. Hasan din na goye bayan Taburni yana bacci.
Ta miko mini shi tana fad'in." Tun d'azu yake neman nono."
Ban ce komai ba na kar'be shi na zauna gefan Hajja wadda suka ta hirar duniya da Ya Falmata tana ta basu labarin rikici da masifar tashin hankalin da aka shiga a maiduguri lokacin farkon boko haram.
Khalil na sanya ya d'auko mini wayata a d'aki na kira Fati na ce su zo gabad'aya za su gaisa da maigidan. Ta ce mini abinci suke ci da sun kammala za su zo.....
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*162*
Ganinta a zaune ya sanya na share kawai ban kai masa abincin ba idan ya koma gidanta sai ta bashi abinda taci su kwanta duk rashin moruwarta da yake fad'i ai ba zata kwana da yunwa ba.
Na ji tana magana da Hajja kan zuwa inna Uwani gobe wai sun yi waya Hajjan ta bata amsa da cewar itama ta sanar da ita.
Ya sauko cikin mutunci da kulawa ya zauna a falon bayan shigowarsu Fati gabad'aya ya gaisa da su har yana jan su Hassanar gidanmu da tsokana haka dai suka dinga sinne kai irin na rashin sabo yadda ya zauna ya kula su shine abinda ya d'an sassauta mini zuciyata domin kuwa ko babu komai bai 'kyamace su ba ya nuna suma cikakkun mutane ne masu kima da karamci zuwansu ya sanya shi farinciki har yana mik'a godiyarsa wannan yana daya daga cikin kyawawan halayensa karrama mutum duk rauni da rashinsa baya ta'ba nunawa na 'kasa da shi cewa shi ba komai ba ne, fuskarsa a sake zai mu'amulanci mutanan da ya tabbatar da cewa ya fi suttura da rufin asiri.
Mun d'an jima tare da shi a falon da su ma gabad'aya kafin ya yi wa Hajja sallama ya fita. Jim kad'an itama ta tashi ta bi bayansa bayan ta yi mana sallama kamar dai gaske ta saki jikinta tana walwala tamkar babu komai a zuciyata Hauwa kenan .
Yusi kuwa kam ganina da shi biyu tunda suka zo yana can tare da Adamu sai da gari ya waye tukkuna suka shigo su biyu da akwatina hud'u jiyan ba su samu damar kawo kayan ba.
Muna d'aki gabad'aya anti Yagana Ya Falmata da Sahura. Yusra tana bacci saman kujera bata tashi ba.
Na bi su da ido har suka gama shigo da akwatinan kayan suka ajiyesu a gefe ban ce komai ba.
Muka gaisa da su suka zauna cikin nishadi da jin dad'in had'uwa da juna wannan so da k'aunar da suke yi wa junansu har mamaki yake ba ni.
Hassan na hannun Adam Usaini shi kuma yana hannun Yusi na ji shi Adam din yana fad'in." Mama Baba ne ya ce mu kawo miki kayan nan akwai wasu kayan ma da za mu d'auko da yamma anti Nabila ta ba ni lambar wayar direban idan suka iso zai kira ni."
A takaice na ce." To shikkenan."
Ya mi'kawa anti Yagana yaron da yake hannunsa ya riga Yusi fita shi yana zaune kamar akwai magana a bakinsa na dube shi ina fad'in." Kai ma ka zama munafiki ko?"
Ya dube ni da sauri yana fad'in." Munafiki Mama?" Na gyad'a kaina ban ce komai saboda takaici to bayan wad'annan

Please Login or Register in order to submit comment