Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban tsammaci da Hauwa yake waya ba sai da na ji yana fad'in." Kin fi kowa sanin matsalar hakan tunda ma'aikaciyar lafiya ce ke to me zai sanya kuma ki aikata, idan kika zubar da cikin ai mun huta gabad'aya tunda ke ba za ki yi aiki da abinda ki ka sani ba."
Ban ji abinda take ce masa ba. Ya ce." Ina cikin jama'a ne sosai muna kar'bar gaisuwa abokin nan nawa Alhaji Amadu ne ya rasu nasan zuwa yanzu kin samu labari ko ta kafafan sadarwa ne dalilin da ya sanya kenan ban samu damar amsa kiranki ba gashi yanzu da na nutsu na kira ki da kaina."
Shiru ya yi yana sauraranta har ta gama yi masa magana cikin kuka wanda nake jin sautinsa kad'an kad'an. Ya ce." To shikkenan a d'aure mahaifar idan hakan shine solution ai kin fi kowa sanin hakan tunda ajikinki take gobe ki je asibiti da wuri ayi miki aikin Allah Ya sawwa'ke."
Ya kashe wayar da damuwa a tare dashi. Ni ma sai na ji hankalina ya tashi wato dai muddin kana raye a duniyar nan ba zaka huta ba.
Bai gaya mini ba amma na fahimci kadan daga cikin abinda suka tattauna cikinta ne yake barazanar zubewa. Na gaza ha'kuri na tambaye shi ya ce." Wai fita suka yi suka yi tare da Sadiya tafiyar kasa mai tsayi saboda rashin hankali tasan tana da karamin ciki bayan sun dawo gida shine take ganin jini kad'an kad'an wai tana tunanin cikin zai iya zubewa dole sai an yi d'aurin mahaifa."
Da damuwa a tare da ni na ce." Aikuwa dai yana da kyau ta yi gaggawa zuwa asibiti gobe wata'kila tana da matsalar mahaifa bata da k'wari shine dalili amma kuma itama ta yi ganganci yin doguwar tafiya a k'afa tana da karamin ciki kamar ba ma'aikaciyar lafiya ba.
Ya ce." Abinda take zargi kenan idan cikin ya zube ai ta huta."
Ya k'arasa maganar cikin takaici da jin haushin lamarin.
Haka kawai na ji na damu da hakan domin har ga Allah bana so wani abu ya samu cikin Hauwa ba don komai ba sai don ganin tabbatuwar farinciki da walwala a fuskarsa. A yanzu dai zuria itace karshen abinda yake nema a wannan duniyar bayan Allah Ya wadatashi da komai a duk lokacin dana kalleshi na tuna har yanzu bai ajiye magaji ba hankalina yana tashi sosai kuma nakan zubar da hawaye masu yawa domin jarabawar da ta same mu ni dashi na riga nasan ko na saki zuciyata da gangar jikina na haihu za mu sanya rai ne akan abinda muka samu bayan kuma ba mai d'orewa ba ne. Astagfirullahi wannan shine babban dalilin da ya sanya nake ji a cikin raina ko cikin na samu zan iya zubar dashi ba tare da ya sani ba don gudun shiga damuwa matsananciya bayan na bari na haihu muna ji muna gani mu rasa abinda muka samu kamar yadda muka rasa babynmu ta farko.
Abin mamaki da daure kai a wannan daran ma na jigatu kwarai da aniya a hannunsa don ban ta'ba tsammanin ma zai neme ni ba ganin irin jimawar da muka yi jiya muna abu daya. Abu na biyu kuma a tunanina gagarimin rashin da ya yi zai dakusar dashi kewar komai na jin dad'in duniya ashe ba haka abin yake ba fahimtata ma kamar idan yana cikin damuwa ya fi kulafucin lamarin washe gari na tashi da ciwon jiki matsananci domin irin sarrafuwar da na yi a hannunsa a daran jiya Ina ganin ko ko kwa'babbiyar fulawar borodi ba ta kaini buguwa ba.
Ina kwance gado bayan na yi wanka na kasa tafiya gidan rasuwar Yusi ya shigo yana gaya mini wai anti Nabila kanwar Hajiya Maryam tana kira na zo ko zan iya rarrashin antin nasu ta karya kumallo. Na ce masa ya je ganin zuwa yanzu. Da kyar na rarrafa na tashi na sanya hijabi saukata kasa ta yi daidai da shigowarsa hannunsa da ri'ke da carbi da alama daga wurin kar'bar ta'aziyya ya taso ya ce mini na je maza wurin Hajiya Maryam na zauna tare da ita yanzu Adam yake sanar dashi an yi an yi da ita ta ci abinci taki ci.
Na ce yanzu Yusi ya zo ya sanar da ni. Na fahimci tunda aka yi rasuwar yake bawa abinda ya danganci matar muhimmanci don jiya ma shine ya k'arfafa mini gwiwar zama a kusa da ita a cewarsa zan deba mata kewa bayan 'yan uwanta. Ban ta'ba kawo komai ba a cikin raina abinda dai na ajiye shine bai ajiye lamarin Alhaji Amadu a nesa ba domin kuwa Allah ne kadai yasan irin taimakekeniyar da suka yi wa juna ba a lokacin da suke neman rufin asiri na duniya.
Hajja suka sauka kamar yadda ya fad'a Hajiya Saratu da kannan mahafinsa su biyu Maza a ciki akwai mahafin matashi ta biyu wato Aysha wadda ta rasu sakamakon zazzabin typhoid kafin ta tare a gidanshi.
Ba sosai na sansu ba duk da kasancewar suna da yawa kad'an na sani daga cikinsu, hakan yana da ala'ka da rashin zamanmu a gari tun bayan aure dangin Hajja ma in banda rasuwar da aka yi ta kanin mahaifin Hauwa babu wanda nasani daga cikinsu.
Wannan karon mun sake sosai da Hajja da alama sihirin da aka yi mata ya warware babu wani kallo na baibai a tsakanina da ita sai mutunci da girmama juna.
Haka aka yi zaman makoki na kwanaki bakwai mutumin nan bai daga kafa ba. Kullum da safe zai fita cikin jama'a ya kar'bi gaisuwa da daddare kuma sai ya rikid'e ya koma jarababbe na bugawa a jarida.
Wannan dalilin ya sanya na yanke shawarar guduwa ba zan iya ba don ban san abinda ya zama ba kuma idan zai jima anan din bai koma legos din ba Hauwa sai ta zo ta kar'bi lamarinsa domin dai sha'aninsa ya fara ba ni tsoro da mamaki.
Ban sanar dashi maganar data assasa mini zuwa ba sai bayan an share makoki kwanaki tara da rasuwar tukkuna na gaya masa amma ta sigar da ba zai zarge ni ba ai taimako ne kuma duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi sosai na gaya masa yadda alhaji Muntari ya dinga fad'i tashin akan lamarin yarana kuma ya rike mini su ba tare da ya bambamtasu da wanda ya haifa ba, na kara jadadda masa cewa abinda ya asassa mutuwar aurena dashi akansa ne saboda rubutun da na yi a fece book akan abinda ya faru wanda ya danganci Kamalu dashi.
Bayanin da na yi masa cikin nutsuwa ya sanya ya fahimce ni ya kuma tausaya mutuka da gaske koda yake dama shi mai tausayi dalilin da ya sanya mini fargabar gaya masa saboda tsohon mijina ne ban san fassarar da zai yi mini ba. A take a lokacin ya ce na yi waya da Baba Sule duk abinda muka tattauna sai na sanar dashi zai taimaka in sha Allahu.
Ban yi kasa a gwiwa ba kuwa na kira Baba Sule a waya ya gaya mini har yanzu dai ba kai ga kar'bar kudin gidan ba domin duk wanda zai zo tayin wulakanci yake yi. Na ce masa to abar batun sayar da gidan za a biya masu hakki hakkinsu insha Allah rabbi duk wanda yasan yana bin Alhaji Muntari kudi ya yi mini list din sunansu a takarda tare da asusun ajiyarsu idan na dawo sai ya kawo mini ni kuma zan tura masa sunayensu ta whasap sai a biya su hakkinsu.
Na sanar dashi yadda muka yi da ya ce hakan ya yi amma fa na ajiye maganar tafiya don su Hajja ne kadai za su tafi bi ba yanzu sai nan da kwana talatin lokacin Alhaji Amadu ya yi arba'in da rasuwa shi ma kuma a daidai lokacin zai koma bakin aiki can Legos.......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*58*
Zaune na tashi ina goge hawayen idonta na dube shi sosai kafin na ce." Ba ni da ajandar komawa gidan Alhaji Muntari domin kuwa da da niyyar hakan a cikin raina wallahi tallahi da kaddarar aure ba ta ratsa tsakanina da kai ba."
Na numfasa Ina kallonsa yayin da shi kuma ya sake hade fuska tare da zubo mini ido da yanayi na neman rikici a tare da shi.
"Abu daya zuwa biyu ya sanya ni kokawa da rasuwar bawan Allan nan ko ka yarda ko kada ka yarda bai dame ni ba na farko shine hallacin da ya yi mini a lokacin da nake buk'atar agaji ya yi mini da kudi da karfinsa daidai gwargwado. Na biyu yadda gidansa ya tarwatse tun yana raye yaranshi suke walagigi ina ga kuma bayan rasu. Maganar nan da muke yi da kai a yanzu hankalina nakan babban yaronshi Turmuzi wanda tun asali nasan da cewa fitinanne ne an ce mini yanzu lamarinsa ya sake ta'barbarewa, ba zan manta ba mahaifinsa ba ya sha kokawa akan sha'aninsa. Wad'annan abubuwa biyu dana lissafa maka sune suka fi tsaye mini a rai domin kuwa na riga nasan sha'anin zumunci a yanzu ya zama abinda ya zama tunda can ma danginsu ba masu zumunci ba ne balle yanzu da baya raye kuma dama shi kadai ne mai dan rufin asiri a cikinsu. Ni uwa ce kuma na yi gwagwarmayar rayuwa da yarana nasan zafin da ake ji idan aka rasa wani 'bangare dalilin da ya sanya kenan nake tausayawa Anti Maimuna uwargidanshi domin ita amaryar ta gudu ta watsar da yaran yanzu gabad'aya suna hannunta kusan su tara ka gaya mini ya za ta yi dasu wane hali za ta shiga domin ciyar dasu da basu tarbiya.
Shiru ya yi bayan na kammala maganata ya gyada kansa a d'an kausashe ya furta." Wannan shagube ne kawai Amina, ni kike so ki yi wa guri a matsayinki na uwa ko?"
Na yi kasa'ke ina kallonsa tare da auna maganarsa domin na gaza fahimtar inda ya dosa.
Ya d'ora da cewa." Af ai ni na uba ba ne, tunda ban haihu ba ban san zafinta ke da ki ka haihu ke ce ki ka san ciwon haihuwa."
Jikina ya d'an yi sanyi jin yana nema ya canza magana nasan hakan baya rasa nasaba da masifar kishin da yake kasa sarrafa shi shine dalilin da ya sanya yake jujjuya maganar dole sai ya fusata ni.
Sai kawai na share shi ban sake cewa masa komai ba na koma na kwanta hawayen na sake bin gefan fuskata. Ni har ga Allah mutuwar Alhaji Muntari ta dake ni sosai na kuma kara tabbatar da cewa duniyar nan aikin banza ce. Wannan ya sanya ni rushewa da kuka da karfin gaske ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ya kuwa zabura! da ganin yadda nake kuka haikan! Sai jikinsa ya yi tubis ya matso kusa da ni sosai yana d'an jijjiga kafafuna da hannunsa. Na sake tsananta kukan da nake yi had'e da jan hanci.
Ya nisa sosai kafin ya furta Yi shiru, yanzu dai Allah Ya jikansa abinda zan ce kenan, sai abu na gaba ina so ki gaya mini yadda kike so ayi tunda ai ni na zama rumfa sha shirgi muddin wannan hawayen zai tsaya ki fad'i yadda ki ke so a yi miki zan yi in sha Allahu."
A hankali na dube shi ina nazartarsa akwai sasaauci a fuskarsa da kuma alamun tausayi da nadama kuma tunda ya ce zai yi to babu shakka kuwa zai yi din."

Na tashi zaune. Ya sanya tafin hannunsa na dama yana taya ni goge fuskata. Na ja hanci a karon da ba zai lissafi ba. Na ce." Ni abinda nake so kawai wannan yaron nasa Turmizi a d'auke shi a kai makarantarsu Kamalu bayan haka kuma ka shirya mana zuwa gaisuwa ni kuma zan zauna da anti Maimuna mu tattauna idan ya kama sai a bata jarin da zata kama sana'a ko?"
Idonsa a kaina ya ce." Hakan ya yi miki?" Kaina na daga. Sai ya ce." Ai ni mai aiwatarsa ne tunda haka ki ka tsara shikkenan za mu je amma sai bayan an yi addu'ar arba'in din Alhaji Amadu idan na yi musu ta'aziyya daga nan sai na wuce Legos abinda na manta ban gaya miki ba kuwa hajiya Maryam ta bukaci akan na bar mata Yusi dalilin sha'kuwar da take tsakaninsa da yaranta akaran kaina ban so hakan ba sai dai ba yadda zan yi ne a yanzu tana buk'atar rarrashi da kuma biye mata akan dukkanin abinda take so domin dakushe mata kewar maigidanta, na san macace mai kokari sosai za ta kula da yaron kamar nata sannan ta yi alkawarin mayar dashi makarantar da Adam yake zuwa sai ya cigaba da dora karatunsa ina fatan babu matsala ta b'angaranki ko?"
Haka kawai na ji ban ji dadin saurin yanke hukuncin da ya yi ba. To amma ba yadda zan yi koda kuwa raina bai so ba haka zan kar'bi hukuncin da ya yanke na tabbatar da matar tana da wata matsala mai muni ba zai bar mata yaron ba.
Washe garin ranar da aka yi addu'ar cikar kwanakin arba'in na rasuwar abokinsa kamar dai yadda ya fad'a muka nufi kano bayan ya jima a gidan abokin nashi wanda na tabbatar da cewa ya shiga ne domin yi masu sallama da kuma kara tausarta yadda yake nuna kulawa da iyalin marigayin nake ji kamar kafin rasuwar tasa ya bar masa wasiyayyar hakan ne
Gidan Hajja muka sauke ta ce itama sai a yi tafiyar da ita don haka muna idar da sallar la'asar muka nufi gidan Alhaji Muntarin dake kawo jirga inda na zauna yau kwanaki hud'u kenan da rasuwar an tashi daga zaman makokin sai kad'an daga cikin 'yan uwanshi sai kuma Babanmu tare da Baba Sule da suke zaman jiran isowar isowarmu tunda mun yi waya dama.
Kai tsaye cikin gidan muka nufa ni da Hajja Yallabai din ya tsaya daga waje tare da Babanmu da jama'ar da suka ankara dashi.
Kasa juriya na yi ganin yadda anti Maimuna ta zabge ta zama kamar mashiriciya ba komai ne ya janyo hakan ba kuwa sai jinyya da fargaba da zullumi na rayuwa. Tana tare da kakarta wadda itace ke zaune tare da ita don ta d'eba mata kewar takaba sai kuma yaran gasunan sun kara girma Salimat ta zama cikakkiyar budurwa sai dai dukaninsu babu wata sutturar arziki. Sun gane ni gabad'ayansu suka dinga gaisheni na yi musu ta'aziyya na tambayi anti Maimuna Turmuzi ta ce mini tun washe garin ranar rasuwar uban ba su kara ganinshi ba.
Nan ta shiga warware mini halin da suke ciki da yadda wasu daga cikin ma'kotan da akayi zaman arziki suke dan taimaka musu ta ce mini ai tun kafin rashin lafiyar maigidan nasu ta yi tsanani Jamila ta gudu ta ce ba zata iya ba kuma duka yaranta ta bari ko bata fadi mini ba na gansu da idona. Muka ci kukanmu muka ko shi ni da ita don kasa ha'kuri na yi a lokacin da take ba ni labarin tana kuka ina yi ina kallon Hajja ma tana share hawaye domin kuwa kowanene dole ya tausaya rayuwar kuncin da suke ciki. Shigowarsu ita ta sanya muka yi shiru Yallabai din tare da Babanmu Baba Sule da 'yan uwan Alhaji Muntarin suka yi musu jagora.
Sosai ya yi wa anti Maimuna ta'aziyya ya kuma jajanta mata kwarai tare da yi mata nasiha mai ratsa zuciya da kawo misalai mabambamta daga karshe kuma ya kare maganarsa da jadadda mata cewa zai taimaka mata iyakacin bakin kokarinsa.
Godiya kakarta ta dinga yi har da kuka Hajja ta dinga bata baki akan ta daina kuka hakan ba komai ba ne face taimakon kai da kai idan har bai yi hakan da dukiyar da Allah Ya hore masa ba sai ta zame masa masifa.
Mun tattauna sosai da anti Maimuna inda muka tsaya a matsaya guda daya cewa bayan ta fita daga takaba zata fara gudanar da kasuwancinta a cikin gida za ta duba abinda ya fi saurin tafiya a unguwar sai ta kafa kowa rabonsa zai samu.
Muka nufi gidan Hajiya Dogara domin yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya. Matar da kyar take iya kallona saboda nauyi da kunyar abinda ta yi mini akan Kamalu ta dinga godiya kamar ta yi kuka domin alherin da Yallabai din ya yi musu na saukewa mamacin tarin bashin da ake binsa tun kafin ya yi bankwana da duniyar.
A ranar da daddare ya aiki Sukairaju da kayan abinci da masarufi masu yawa gidan Alhaji Muntari.
A gidana muka sauka gabad'aya har Hajja domin ya fi kusa da Dambatta ga dare ya yi Hajja ta ce da safe ta tafi ba ta son tafiyar dare.
Baba Tabawa da Yusura sunan lafiyar Allah kamar ina tare dasu domin abinci da kayan masarufin dake store dina ina tsammanin za su iya hauraa shekara basu kare ba. Bayan haka kuma akwai masu tsaro a gidan kuma mun yi waya da Sahura sati daya da tafiyata na ce ta dinga zuwa gidan tana duba su duk sa'i da lokaci.
Baba Tabawa kuwa aka ci sa'a ta yi favorite dinsa towon dawa amma miyar ku'bewa bushashshiya sai dai ta wadatu da daddawa da nama sai k'amshi take yi. Aikuwa ya ci sosai har yana tsokanarta wai ta fi ni iya abinci dama idan na yi towo ha'kuri kawai yake yi yana ci. Hajja itama ta yaba mata sosai ta ce mini a ajiye mata d'umame da safe kafin ta tafi sai a d'umama mata shi. Baba Tabawa tace ai kamar ta sani ta yi shi da yawa.


Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biyani hakkina ba

Had'uwarmu ta daran yau sai ta zama ta daban domin kuwa lamarin da ya bijiro dashi bai samu kar'buwa ba a wajena yayin da shi kuma ya kafe kai da fata sai ka ce wanda aka yi wa wahayi lallai ta haka yake so ya biya bukatarsa to sai bijirewata ta wanzar mana musayar yawu domin kuwa ni dai ban ta'ba jin inda aka yi wata kwanciyar aure a tsaye ba. A ganina ma ta wannan sigar ta yaya mutum zai fahimci wani abu ya za a yi lamarin ya yi armashin da kowa zai gamsu. Ya dage shi fa ga ta yadda zai yi domin sai ya fi gamsuwa a cewarsa ko ya koma zai jima sha'awarsa ba ta motsa ba ni kuma na ce ba zan iya jurar tsayuwa ba na amince a yi akwance duk yadda yake so zan yi amma a tsaye ba zan fahimta ba. Ai lamarin na mutum biyu ne ba na mutum d'aya ba. Sai ya fara fad'in ai Ubangiji ya ce ku shiga gonakinku ta kowace siga amma ban da ta waje daya don haka shi yau zai gwada yi a tsaye. Tun abun yana ba ni dariya da mamaki har ya dawo ba ni haushi da ganin kamar yana so ya sauka daga koyarwa addinin musulunci ya bi turbar nasara domin kuwa sune shaidanu masu kirkiro abun da zai cutar da mutane.
Ya ce idan ba zan amince ya yi ta haka ba kuwa sai da na yi sucking dinshi har ya biya bukatarsa. To dama dama wannan da sauki tunda wani sa'in ina yi masa amma ba sosai ba don baya ganewa muddin ba wajan nan ya shiga ba. Ya za a yi sucking ya iya gamsar dashi a yadda yake sai mu kwana ba mu rintsa ba. Amma dai na fi aminta da yin hakan akan ya yi a tsaye k'afafuna ma ba zasu iya jurewa ba.
Sarewa na yi da sha'aninsa domin kuwa duk tsayin lokacin da na d'auka ina yi masa abinda ya buk'ata din ko gezau bai yi ba wai da sunan samun satisfying yana dai nishad'antuwa k'warai da gaske tabbacin yadda nake yi masa yana jin armashi ammafa babu wani shau'ki na kawowa.
Gajiya na yi kawai na matsa gefe daya domin kuwa kafad'una sun k'age dalilin sunkuyo jikina ma gabad'aya ya yi tubis bacci ne yake mamayata. Ganin haka ya sanya ya janyo ni a ki'dime ya fara sarrafa ni akwancen dai ya biya bukatarsa amma ta siga daban daban. Ni kam duk wanda ya bashi shawarar yin amfani da maganin k'arfin maza ya cutar dashi domin kuwa abin nasa yana nema ya yi yawa. Da sassafe ya shirya yana ta zoyalata zai tafi amma zai dinga zuwa ta mafarki. Na.dinga zumbura baki ina fad'in duk wanda ya baka shawarar yin amfani da maganin karfin maza ya d'ora ka a hanya mara b'ullewa ai ba a ce kada a yi jima'i ba amma daidai misali yanzu baba don Allah wane hali zaka shiga a can babu mace a kusa......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*59*
To sai a lokacin ya ke gaya mini shi babu wani maganin karfin maza da yasha hana karya dai ya yi amfani da maganin sanyi watanni uku da suka wuce lokacin da Falalu mai yi masa abinci ya je garinsu mahafiyarshi ta bashi ya kawo masa a matsayin tsaraba. Falalun ne ma da kanshi ya dafa masa maganin da yake sassa'ke ne da saiwowi ya had'a da citta kaninfari tafarnuwa ya dafa shi sosai ya zuba masa a babbar gora ya yi amfani dashi.....08089965176 Wallahi maganin sanyi ne sadidan har basir ma yana lalata tasirinsa a jikin dan adam. Kaikayin gaba zafin fitsari fitar iska rashin ni'ima zubar fitsari karancin sha'awa ciwon mara ciwon kafafu rashin haihuwa. Ciwon ga'bo'bi rashin gamsuwa maganin kuma maza da mata ne duk wani dattin da yake mara za a fitsarar dashi, ga masu buk'ata a yi mana magana kai tsaye ta lambarmu da muka d'ora za a yi wa Allah godiya  kuma za a yi mana godiya.

Na yi mamaki sosai da na ji ya fadi haka. Dama ai duk lalacewar namiji wajan saurin kawowa ko rashin dogon zango ko kuma daukewar sha'awar da kankancewar gaba gabad'aya sai dai idan bai yi katari da sahihin magani ba. Haka zalika ma duk lalacewar mace wurin rashin ni'ima bushewa da fitar iska, d'aukewar sha'awa da matsalar rashin gamsuwa daga maigidanta sai dai idan ba a yi katari da ingantaccen magani ba. Haka zalika ma 'yan mata da zawarawan da suke da niyyar shiga d'akin mazajensu yana da kyau su ma su magance sanyin da yake tattare dasu domin gujewa matsala...08089965176 a tuntub'e mu kai tsaye muna tura kayanmu kowane gari.

Bayan kwanaki uku da tafiyarsa yanayin jikina ya fara canzawa lamarin ba sabon abu ba ne a wajena amma ban tabbatar ba dai tukkuna har sai da lokacin yin la'adata ya yi ya wuce ban yi ba yayin da ciwo-ciwon da nake ji yake 'kara tsananta. Kakarin amai da safe taruwar yawu kasala saurin bacci da k'yankyami. Ciki ne da ni ba shakka lamarin bai yi mini wani armashi ba domin kuwa ban shirya d'aukarsa ba kuma ba na tsammanin zan gaya masa har sai na yanke shawarar da nake ganin itace mafita ga rayuwata.
Ko anti Yagana ba zan gayawa ba balle ta dakusar da ni domin kuwa yana da kyau komai mutum zai yi ya kiyaye faruwar abinda zai sanya shi shiga rud'ani a gaba.
A takarda na rubutawa Yusura abin gwaji ta fita bakin titi akwai chamis ta je ta sayo mini da sassafe na yi sakamako mai kyau ya fito positive. Shiru na yi da bakina kuma na dinga kokarin ganin na karfafi jikina don kada Baba Tabawa ta fahimci halin da nake ciki. Ba Allah zan yi wa butulci

Please Login or Register in order to submit comment