Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba na kyale shi kawai. Gabad'aya na rasa yadda zan yi da sha'aninsa jikinsa ya nuna alama yana buk'atar ganin likita. Ya d'auki wayarsa Ina zaune ya kira Sukairaju wallahi na zaci ya d'auki shawarata ne ashe ba haka ba ne, koda Sukairaju ya shigo sai ya rufe shi da fad'a irin wanda ban ta'ba ganin ya yi masa irinsa ba domin kuwa a cikin yaransa na tabbatar da cewa yana sonsa kuma tasu ta zo daya. Fadi yake yi da kai za a had'a ba ki a kashe ni ko Sukairaju me ya sa na d'auki amana ragamar kula da rayuwata shige da fice na da duk wani motsina amma za ka bada goyan bayan cutar da ni, ban aminta da kai ba a wannan ga'bar jiya na yi maka shiru ne domin ban gama nazari akan faruwar wannan lamarin ba, yanzu zuciyata ta amince mini da hadin bakinka wajan ganin kun kai ni kasa in banda kai babu wanda ya san na shigo garin nan ya aka yi har k'ososhin jikin sabuwar motata za su zube baka sani ba, ina kake ina ka ajiye motar ? Kai ne ka cire k'ososhin ko kuwa wani ka biya ya cire domin biyan buk'atarku wannan amsar nake so ka ba ni tun muna biyu ni dakai ka fito ka gaya mini asalin abinda ya faru.
Ya zube a gabansa cikin tsananin damuwa da tashin hankali yana cewa." Wallahi Yallabai ban san yadda aka yi ba, kuma zargin da kake yi mini ba haka ba ne, ba ni da niyyar cutar dakai Yallabai shekara nawa muna tare menene ban samu ba ta dalilinka, babu abinda ba ka yi mini ba na rayuwa idan ma na cutar da kai nasan Allah ba zai barni ba, a ko'ina ne zan iya sadaukar da rayuwata akan taka rayuwar ni dai nasan lokacin da muka koma unguwar domin d'aukar kaya daka bar ni a bakin mota ka shiga gidan na dan zaga baya domin yin fitsari da na yi sai na fito sai na tsaya sayan lemon fata anan bakin titin dai shikkenan abinda na sani, ina kuma tunanin wannan damar aka samu har ka cire k'ososhin motar ni kaina ranka ya dad'e na fara zargin akwai hannun Alhaji Sammani a ciki dalili nasan tunda ka rubuta masa takardar sallama ba zai ta'ba ha'kura ba mutum ne ma'ketaci wata'kila yana bibiye da kai har ya gano kaine ake d'auka a motar dukda boyewar da ka yi, kuma ranka ya dad'e jama'a da yawa sun san kana garin nan tunda shekaran jiya mun shiga asibitin Malam Aminu cikin motocinka wanda kowa ya sanka dasu, to ka ga bibiyarka ba zai yi wa wanda yake burin cutar dakai wahala ba.

Jin ya yi shiru kansa a kasa shi ya tabbatar mini da cewa maganganun Sukairaju sun kar'bu a wurinsa. Na ce." Kada ka yanke hukunci cikin fushi, ka yi bincike dukda abin akwai rikitarwa amma ba na tsammanin za a had'a ba ki da Sukairaju a cuce ka."
Ya dube ni kafin ya ce." Za a had'a ba ki da Hamusu kenan?"
Da tsananin faduwar gaba na ce." Hamusu kuma?"
"Kwarai kuwa bayan shi wanene makusancinki?wanene ya kawo ni gidanki ta yaya za a kwance wasu daga cikin k'ososhin dake jikin tayar motata babu sanin Hamusu."
Na gyad'a kai da zullumi mai yawa a tare da ni na furta." Ba na tsammanin haka ranka ya dad'e, dukda dai ba a shedar mutan amma Hamusu ba zai aikata hakan ba."

"Me yasa kai tsaye ki ka fad'i haka umm?" Ya fad'a idonsa a tsaye akaina cike da zallar tuhuma da mugun zarginsa da ya motsa.
Shiru na yi domin kuwa ba na so mu jayayya agaban Sukairaju.
Ganin haka ya dube shi tare da ba shi umarnin fita.
Ya tashi yana fad'in." Na gode Yallabai, amma ya kafar taka Ina fatan bata yi maka ciwo ko?"
A takaice ya ce." Ta warke Sukairaju na gode, kada ka yi nisa zan iya nemanka a kowane lokaci."
Ya d'an risina yana godiya kafin ya kama hanyar fita.
D'akin ya yi shiru ni fargaba da damuwa sun ishe ni, zuciyata nata tsalle da k'in rashin amincewa Hamusu zai aikata mini haka. Wata zuciyar tana ce mini Amina makashinka fa yana gindinka, ba ki san menene a zuciyarsa ba zahirinsa kawai ki ka sani.
Hawaye masu zafi suka fara kasa tsere a kumatuna idan kuwa hakan ya tabbata lallai Hamusu ya cutar da ni ya zalinci kansa ya zalince ni, ya 'bata mini nasabar yarana."
Ya nisa kafin ya ce." Har yanzu ba ki yarda da maganata ba ko?"
Girgiza kaina na yi a raunane na ce." Ba wai ban yarda ba ne, abun ne kawai yake ba ni mamaki da al'ajabi."
Sai ya girgiza kansa yana fad'in." Ni ma zargi na ce Ina yi ba wai na ce shi din ba ne, amma dai kin san shine mafi kusa dake da ni, kuma shine ya yi mini jagora gidanki, kafin Sukairaju ya san inda nake wanene zai je ya kwance 'kososhin mota?"
Ina kuka na ce." Yanzu ka gama fad'a zargi kawai kake yi baka tabbatar ba, to me zai sanya ka tsaye ba tare da ka tsananta bincike ba ka nuna shine, kenan zargin da kace ka na yi bashi da amfani kawai ka fito fili ka ce Hamusu ne yake yun'kurin raba ka da duniya shikkenan sai zambu da gugar zana su 'kare."

Ganin yadda hankalina ya tashi da maganar da ya yi akan Hamusu ya sanya bai sake tashin maganar ba, amma nasan ba wai ya ha'kura ba ne ya yi shiru ne saboda bashi da tabbas akan abinda yake zargi. Ni kaina ba wai na ce Hamusu ba zai iya aikata hakan ba ne, ai da adam ne wanda yake tattare da ajizanci amma amincewa kai tsaye bashi ne adalci ba. Muna nan dai zaune ni dashi cikin rashin sukuni ya kira personal doctor dinshi a waya ya yi masa bayanin yadda yake ji a jikinsa gabad'aya ko'ina ciwo yake yi masa ga rashin test a bakinsa da zazzabi kad'an. Doctor din ya ce zai yi masa text na magunguñan da zai sa a sayo masa domin yanayin bayanin da ya yi masa yana tunanin zazzabin maleria ne ke so ya kama shi.
Ban yi mamaki ba da farko kukan ciwon jikin da yake yi na d'auka tsautsayin da suka samu ne ya ce shi babu wani waje da ya bugu a jikinsa bayan 'kasan giwarsa da targad'an da ya yi. Tabbas zazza'bin kuwa zai iya kama shi sakamakon sauron da ya cije shi a gidana. Ya kira Sukairaju domin ya zuwa wajan sayar da magani ya sayo masa. Kafin shigowarsa na ce." Ni da za ka d'auki shawarata da ka je asibiti ba fa a wasa da lafiya."
"Ba ina da za ni fa ." Amsar da ya ba ni kenan babu walwala a fuskarsa. Sai na yi shiru kawai na zuba masa ido yana da wani irin hali muddin bai so yin abu ba to babu wanda ya isa ya tursashi, ni kuma a tunani na zuwa asibitin kamar zai fi muhimmanci ko da yake wannan din ma ga dukkanin alamu babban likita ne tunda ba zai d'auki likitan da bai san aikinsa ba domin duba lafiyarsa ba....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*


*51*
Na dawo na same shi yana cigaba da aikinsa ammafa fuskarsa ta dan canza kad'an.
Hankalinsa na kan abinda yake yi ya ce." Kina jin mu da Hajja ko?'
Na nuna ban fahimci komai ba.
Ya furta." Wai itama Hauwa ta dawo nan tunda tana da juna biyu, Hajja tunda ta samu labarin cikin nan ta hana kanta sukuni, na ce mata a a dai ai ba zama zan yi ba wata'kila ma jibi zan koma."
Na ce." Me yasa kace mata a a, ta dawo nan din don Allah idan tare take so mu zauna ai da d'akuna idan kuma gidanta daban take so ai kana da iko, itama Hajja tana da dalili ai lokacin da nake rainon baby ta zauna mini."
Ya ce." Idan har Hauwa za ta dawo nan to ke za ki koma domin ba zai yiwu a ce ku nan ni ina can ba, idan bukata ta motsa mini matan banza kuke so na bi."
Shiru na yi kawai ban ce komai ba, ba na tsammanin zan sake komawa legos koda kuwa Hajjan ce ta bada umarnin haka.
Na ce.'' Yanayin yadda Hajja take magana ya nuna kamar a cikin bacin rai take shiyasa tun farko naso na je na gaisheta ta san da zuwana domin sai ta ga kamar ana 'boye mata wani abu ne. Na tare a sabon gida baka gaya mata ba sai 'boye-boye kake yi baka so a san kana garin nan ban gane dalilin yin hakan ba har yanzu."
"Dalilina na yin haka suna da yawa Amina, amma yanzu tunda mun sasanta ba kya jin haushina zan gaya miki na farko duk wanda ya ga jerin motocina na gidanki zai zargi wani abu rabuwar auranmu da nake ta b'oyewa duniya zata sheda hakan har ita hajjan ta ji labari gani can ina zawarcinki ke kuma kin koma zaman kanki irin na baya wanda mutane suka shede ki da haka. Za a yi ta yawo damu a duniya kowa na tofa albarkacinsa bakinsa. Na gayawa Hajja cewa kin je can maiduguri biki ni kuma na ce mata zan zo nan domin duba Gwaggo wadda ta haifi mahaifin Yusi, ko da na sauka garin nan hakan na sake gaya mata.
Amma wannan ba abin da za a tsaya ana ta magana ba ne, zan yi magana da Inna Uwani a samu wata dattijiwar sai a tura mana ita can su zauna tare har Allah ya sauketa lafiya."
Na ce." Idan dai hakan zai janyo matsala don Allah Hauwa ta dawo nan itama ba na son abinda zai sa Hajja ta ga rashin kyautawata"
Babu damuwa ya ce." Idan kin aminta hauwa ta dawo ai abu ne mai sau'ki sai ta dawo din ke kuma sai mu koma tare "
Girgiza kai na yi na ce "A a ni kam ai na dawo kenan in sha Allahu."
Ya ce." To sai ki ja bakinki ki yi shiru tunda ke kin yi nasara amma ba zai yiwu a ce duk ku tattara anan waje daya ba.
Ya fita sallar azhar bai dawo ba ya bar wayoyinsa a d'akina ana ta kira na shiga d'akin a daidai lokacin da wani kiran ya sake shigowa na d'auki wayar na duba sunan Hadiza ne yake yawo cike da mamaki nake bin sunan da kallo. To kai tsaye dai ba zan yanke hukunci cewa Hadizar gidanmu ba ce tunda mutam ne na mutane akwai ma'aikata mata da suke yi masa aiki mabambamta har da k'warori. Ba yadda za a yi na daga wayar tunda akwai tsaro (security) sai na ajiye har ta katse wani kiran ya sake shigowa a k'alla akan idona sai da aka kira sau kusan shida kafin a hakura. Ya shigo a gurguje yana fad'in.'' Ban san me mutane suka zama ba a wannan duniyar ba ni da lokacin da zan 'bata akan yin jawabi dangane da Sammani abinda suka samu na shaci fad'i ya ishesu babu wata gidan jaridar da zan tsaya bata lokacina a kansa.
Na ce." Wani abun ne ya faru kuma?"
Ya zauna gaban abincin dana shirya masa yana cewa." Sun ankara da ni ne duk da na rufe fuskata da takunkumi yanzu bakin gate din gidan nan mutane ne cike manema labarai da mabukata."
Gabana na dan bugawa na ce." Akan me suke neman labari kuma?
"Dangane da abinda ya faru mana tsakanina da Alhaji Sammani suke neman jin ta bakina."
Na ce." Ka ja bakinka kawai ka yi shiru don Allah kada ka ce komai bayanin da ka yi da farko ya wadatar wata'kila wasu sun samu labarin ko ya yi yun'kurin kashe ka ta hanyar sanyawa a kwance maka k'ososhin mota."
Ya ce." Ba na tsammanin haka, lamarin dai da suka samu shine na salwantar mini da gidan gonata dake tiga da kuma sabon kamfanin da na fara ginawa a mariri wanda shi kadai ya san da ajandar hakan to akan hakan dai suke so su ji abinda zan ce."
Na ce." Ai ka ce ka yafe masa ba shikkenan ba. Mutane ne ba su san zaman lafiya shi kansa nasan yanzu yana can cikin jin kunya da damuwa ga kuma fargabar irin kallon da mutane za su dinga yi masa.
Ya ce." Ai idan har suna ganina ba za su daina bibiyata ba Amina, ba ki san dan jarida da na ci ba ko."
Shiru na yi ina kallonsa ya janyo wayarsa dake saman gado yana fad'in." Zuba mini abinci ina so na fita zuwa gidan hajja ina fargaba wallahi."
Na fara had'a masa abincin a tsanake na ce.' An kira ka a waya ka ga ni ko?"
Ya na duba wayar ya ce." Hadiza ce yayarki."
Na dube shi cikin nutsuwa." Hadiza kuma?"
Ya d'aga kansa a hankali ya sanya wayar a kunnansa kiranta ya yi.
Kaina ya kulle da mamakin lamarin dama tana kiransa ashe shiru na yi kawai domin na ji wannan karon kuma dame take tafe.
Gaisuwa suka yi ita dashi cikin girmawa har tana tambayata da Yusi shi ma ya bata amsa da kulawa tunda na fahimci duk abinda ya shafe ni yana bashi girma.
Magana take yi masa cikin rauni har da rawar murya amma sakamakon yadda muryarta ta yi kasa ban ji komai ba.
Na ji yana fad'in." Allah Ya rufa asiri in sha Allahu za a duba yiwuwar yin hakan, Allah Ya shirye shi da sauran masu hali irin nasa.
Ya kashe wayar yana dubana kafin ya ce." Kuna da wani d'an uwa wanda Allah Ya jarabta da rashin ji ?" Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Ba mu dashi gaskiya anti Yagana ce babba a gidanmu a maza kuma Usani ne Hassan dinsa ya rasu.
Ya gyad'a kansa tare da cewa." Tana gaya mini dan'uwanku hukuma ta kama da zargin damfarar wani mutum miliyan hud'u da rabi."
Na ce." Shine me kuma? Ba zai wuce d'an'uwanta da na sani ba mamarta sai da ta yi aure a wani wurin har ta haihu sannan Babanmu ya aureta shine kawai abinda na sani.
"Tunda har Mamanta tana auran mahaifinku ai idan da kara shi ma d'an uwanku ne ko ba haka ba ne."
Na ce" Don girman Allah ka daina biyewa Hadiza bata da gaskiya fa, ba zan boye maka ba ko kwanaki nan karyar rashin lafiya suka shirya da Ummansu ita Fatin ma bata sani ba ka d'auki kudi ka basu har miliyan shida sannan kuma na ji labarin an ce ka bata jari har tana zuwa Dubai sarin kaya. kai baka gaya mini ba itama bata gaya mini ba, ko da yake ai ta san bata da gaskiya ba zata gaya mini ba, wannan ma ban yarda ba karya take yi wallahi."
Jim ya yi yana nazari kafin ya ce." Ta bukaci na taimaka mata kasancewar bata da aure dana tambayi matakin karatunta ta ce mini ko sakandire bata gama ba a gidanku ke kadai ce ki ka danyi karatu to kin ji dalilin da ya sanya na d'auki kudi na bata da niyyar ta yi jari domin ta tsaya da kafafunta a matsayinta na bazawara rashin sanar dake ba shi da ala'ka da wani abu tunda ni ban iya alheri na fito ina shela ba."
Da takaicinsa na ce." Don ka gaya mini sai ya zama wani abu to ta dalilin wa kasan Hadizan Ina ce 'yar'uwata ce."
Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Ni ba 'yar uwata ba ce kenan?"
Shiru na yi ina kallonsa. Ya girgiza kai bai sake cewa komai ba ya fara cin abincin dana hada masa.
Bakincikin abinda Hadiza take yi mini ya hana ni sukuni sai da na bari ya fita zuwa gidan Hajja tukkuna na kira anti Yagana muka gaisa na gaya mata maganar tariyata a sabon gida sannan na sanar da ita irin rashin mutumcin da Hadiza take yi.
Ta ce ai d'aurin gindin babarsu ta samu auran suke su gurgud'e miki Amina amma idan ba haka ba wannan ai zubarwa da kai mutunci ne tun mutumin nan yana yi musu kara da kawaici har sai sun kure ha'kurinsa ta zubar mana da mutunci wallahi "
Na ce." Anti Yagana Ina ganin kawai zan je gidan ne mu yi duk wacce za mu yi da ita gaskiya na gaji da abinda take yi mini wallahi ba zan jura ba.
Ta ce." Kada ki je yin hakan zai iya b'ata masa rai ai mai hankali ne shi ya san komai kawai yana biye mata na tabbata idan ya gaji ko sauraranta ba zai kara yi ba.
Ki zuba mata Ido kawai saboda idan ki ka yi magana za a d'auka kece ki ke hana mijinki alheri shima kuma tunda bai gaji ba ai kudinsa ne ba na ki ba."


Gudun aure littafin kudi ne, kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Mafarin samun matsalata da Hajja kin amincewa da komawa legos kamar yadda ya zo yana gaya mini sun yanke shawara ita dashi akan ni na koma can din domin kula da Hauwa a matsayina na wadda ta yi haihuwa uku. A cewar Hajja duk da Hauwan nurse ce ai b'ata ta'ba haihuwa ba balle ta ce ga yadda take kuma koda ta zo haihuwar yana da kyau a ce da akwai wani a kusa da ita. Lokacin da ya zo yana gaya mini kawai jinsa nake yi da kunne domin na tabbatar da cewa zamana ne ba a buk'ata anan din saboda ya kafe kai da fata ba zamu tattaro mu dawo nan gabad'aya ba dole wata ta koma can tare dashi.
Na farko dai Hauwa ba yarinya ba ce a lissafin ma shekaru ma ta d'ara ni da kusan shekaru hud'u sannan kuma wace irin haihuwa ce ba ta gani ba, idan ba a shigo da son zuciya ba ina ganin ita kanta ma za ta iya kar'bar haihuwarta idan ta kakare ai akwai asibiti sai su je can, zamana babu wani abinda zai amfana tunda ba wani shiri muke yi ba to kamar dai yadda ya nemi alfarma wurin inna Uwani Ina ganin shine maslaha kawai a kai mata dattijuwa daga cikin danginsu.
Da har Hajja ta amince da da shawarar da ya yanke kafin ya bar gidan ta kira inna Uwani suka yi magana ita ta rusa shirin ta ce ita dai hankalinta sai ya fi kwanciya Hauwa ta dawo kusa har da yin kuka tana gayawa Hajja ai ýÿÿÿ‚
ƒ




ˆ

Š

Œ

Ž









˜

š

œ

ž
Ÿ
 
¡
¢
£
¤
¥
¦
§
¨
©
ª
«
¬
­
®
¯
°
±
²
³
´
µ

·
¸
¹
º
»
¼
½
¾
¿
À
Á
Â
Ã
Ä
Å
Æ
Ç
È
É
Ê
Ë
Ì
Í
Î
Ï
Ð
Ñ
Ò
Ó
Ô
Õ
Ö
×
Ø
Ù
Ú
Û
Ü
Ý
Þ
ß
à
á
â
ã
ä
å
æ
ç
è
é
ê
ë
ì
í
î
ï
ð
ñ
ò
ó
ô
õ
ö
÷
ø
ù
ú
û
ü
ý
þ
ÿ
 ta je ta taya ni rainon ciki har sai da na haihu tukkuna..

Assalamualaikum. Ina kwanaku ya gida ya yara. Ina fatan duk Kuna lafiya. Mun kammala book 3 Kuma typing din da na yi ya kare don haka za ku d'an yi mini ha'kuri na d'an wani lokaci sati daya ko 'kasa da Hakan in sha Allahu rabbi idan na tara wani da yawa sai mu cigaba. Na gode sosai da sosai Ina kuma fatan labarin Yana yi muku dadi fiye da yadda nake tsammani Amina ta ce tana miko gaisuwarta....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*


*52*
Wannan dalilin ya sanya Hajja ta ce ya gaya mini na shirya idan zai koma sai mu tafi a tare. Kuka sosai na dinga yi ina fad'in ba a yi mini adalci ba domin sai da na shekara daya a can kafin Hauwa ta tare me zai sanya kuma yanzu a ce mini na koma saboda wani dalilin da bai shafe ni ba, iyakacin gaskiyata na gaya masa ba wai ina b'akinciki da haihuwar da za su yi ba, ina ganin kamar akwai son zuciya a wannan hukuncin dukda Hajja ta wuce ta nemi wata alfarma a wurina na turje mata to amma na riga na gama tabbatarwa da kaina cewa wannan hukuncin itama ta yanke shine domin son rai da kuma farantawa 'yar'uwarta ai ya gaya mini tunda aka samu cikin ta rasa sukuni idan zai yiwu ita din sai ta sake komawa ta zauna mata kamar yadda ta zauna mini ai ba hujja ba ce a ce dole sai ni zan je na zauna tare da ita tunda suna da yadda za su yi.
Rarrashin duniya babu irin wanda bai yi mini ba na ce ba fa zan bi shi ba domin da muna abun arziki da ita ne ma da sauki to kowa ta ciki na ciki me zai sanya na je na bautata mata daga baya wani sharrin ya b'ullo.
Ya nuna ai saboda shi zan yi, idan ma bai isa ba to na bi umarnin Hajja kamar yadda ta buk'ata kada na bijire, na ce ai ba ra'ayinta ba ne itama ta yanke hakan ne domin ta farantawa 'yar'uwarta rai.
Kwana da yini muna ta abu daya domin duk ta inda ya biyo nasan hanyar da zan zame kaina na nuna masa ba da hurumina ne ba, ni ma lokacin da na haihu 'yar uwata Hadiza ce ta zauna mini. Na kuma gaya masa ko da wasa kada ya sanar da mahaifina domin yin hakan zai janyo mana matsala mai girma saboda na riga na san halinsa sarai.
Itama anti Yagana ban gaya mata ba duk da mun yi waya da ita a ranar muna tattauna matsalar da ta shafe mu amma har muka yi sallama ban fad'a mata maganar ba.
Da yamma sai ga Hajiya Saratu na karbeta hannu biyu sosai muka gaisa dama can muna girmama junanmu akwai kuma kunya da kawaici sannan Ina ganin darajarta sakamakon tana da sunan Mamana.
shiyasa ko da ta fara yi mini maganar ban iya jayayya da ita ba kawai na yi shiru saboda ina jin nauyin na ce mata ba zan koma ba yanayin dana shiga ya nuna mata cewa ban yi na'am da abinda suke so ba. Jiki ba kuzari muka yi sallama ta tafi..
Sai da ya shigo gidan yake tambayata Hajiya Saratu ta zo na ce masa eh daga haka ban sake wata magana ba. Ya dinga bibiyata yana so ya ji abinda muka tattauna da ita bance masa komai sai da daddare tukkuna ya kira ta a waya a gabana suka yi Ina jin sautin maganarta tana cewa dashi idan zai yiwu kawai ya ha'kura tunda abu ne na lokaci Hauwan ta dawo tunda haka suke so saboda itama tana ganin kamar idan aka ce dole sai na koma an shiga shakkina idan ta haihun anan an yi taron suna sai ya tsara yadda zaman zai kasance idan ma za mu dinga zuwa can muna yi masa wata shida shida mu dawo hakan zai yi alheri.
Na fahimci azancin Hajiya Saratu kuma kamar ta zo da sasanci anan a wannan ga'bar zai iya ha'kuri tunda ta b'angaransu sun dage ya ha'kura ta dawo nan din har ta haihuwa abu ne na lokaci kad'an bayan ta haihu sai mu raba na je na yi wata shida idan na dawo sai itama ta je ta yi nata wattanin.
Ya kar'bi shawarar ne saboda gajiya da ja'ina daka kowane bangare amma na fahimci dan ba yadda zai yi ne ya amince ya fara shirin komawa amma cike yake da jin haushina acewarsa ni ce ya kamata na dubi halin da zai shiga amma kishi da son rai ya hana ni yin abinda ya dace. Shiru kawai na yi masa ban tanka ba har ya kammala shirinsa babu cikakkiyar jituwa a tsakaninmu na yi ta so mu rabu cikin girma da mutunci yana bijirewa haka na zuba masa ido har ya kammala shirinsa ya tafi babu

Please Login or Register in order to submit comment