Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai sanya ni raba su dake saboda suna sonki itama ta yarda da hakan."
Yana gama fad'in haka ya d'ora mini yaron saman cinyata ya kama hanyar samansa yana magana." Idan Hakan bai yi miki ba ni ma sai ki raba ni biyu ki d'auki b'angaran da kike so a jikina sai ki bata rabin tunda duk a kaina kuke wannan 'kiyayyar junan idan na mutu kowa zai huta ai."
Na dinga kallonsa har sai da ya gama hawa steps na daina hangensa na dawo da kallona kan yaron da yake ta zura hannunsa cikin rigata nono yake nema. Babu kuwa halin ba shi domin tunda suka fara wayo nake had'a musu kamu irin wanda Sultan ya sha yana kan matakinsu balle yanzu da ake yin azimi ba ni yarda su tsotse ni da tsotsan jaraba.
Bai sauko ba sai daf da za a sha ruwa mun gama aiki Hadiza na gyara kicin din muka dinga jin kuka a falon na fito da saurin gaske. wanda ya yi daidai da saukowarsa Minal ke kuka tare da Sultan Hauwa ta turo mai aikinta Ladidi wai su tafi tare. Sauran sun yi cirko-cirko. Kuka fa sosai Minal ta ri'ke hannunsa tana fad'in." Baba ba kaine ka ce mu zauna a can ba sai Mama ta dawo, to ina za mu je ai nan ne gidanmu Ladidi za ta d'auke mu."
Sultan da tafiyarsa ta yi k'wari sosai ya taho da d'an gudu ya rige gefan rigar uban yana kuka ya sunkuya ya d'auke shi yana kallon Khalil ya ce." Je ka dauro alwala lokacin sallah ya yi." Yaron ya juya da sauri ya bar wajan.
Sai ya dubi Ladidin yana fad'in." Je ki abin ki idan an jima zan shigo da yaran."
Ta risina da sauri kafin ta juya ta kama hanyar fita.
Khalil ya fito da alwala sai ya dire Sultan din a kasa ya ce." Ri'ke hannunsa muje massalacin tare."
Ya yi gaba da sauri su kuma suka bi bayansa..
Na dube su Usaina ta ri'ke hannun Minal din tana zaune dirshen 'kasan ties amma kukan ya tsagaita. Na ce." Ya isa haka ta shi kuje ku yi alwala a yi sallah sai a ci abinci ko?'
Ta daga mini kai tana sakin ajiyar zuciya ta tashi 'yan uwan suka tasa 'keyarta zuwa dakinsu.
Daga ni har ita Hadizan cikin damuwa muke amma ni na yi kokarin ganin na kawar da tawa damuwar domin samar mata da kwanciyar hankali. Ba wani abu ba ne yake nukurkusarta face maganganun da Inna Uwani ta gaya mata d'azu. Bud'e baki ma da 'kyar ta iya saboda damuwa. Babu komai ai rayuwace duk wanda ya yi wa kaddarar wani dariya watarana Ubangiji shima zai jarrabe shi da abinda zai zama abin nuni da zind'e a idanun jama'a. A fakaice na d'an dinga jan hankalinta da wayo da rarrashi ta ci abinci tana ta nuku-nuku da hawayen dake ma'kale a kwarmin idonta.
Tunda yau ma din a gidanta zai kwana ban tsammaci sake dawowarsa ba mussaman tunda ga irin rabuwar da muka yi wajan goma da ashirin muna falo muna kallo gabad'aya har da yaran ba su kwanta ba. Ya shigo ri'ke da hannun Sultan yana ta sauke ajiyar zuciya yaro idonsa ya yi jawur da kumburi almar ya ci kuka ya k'oshi. Khalil dake biye a bayansu Fadi." Yake yi ga ta can Usai din je ka."
Ya kuwa tafi wajenta da sauri yana sauke numfashi. Na dubi Khalil din ina fad'in." Me ya same shi?"
'yar dariya ya yi kafin ya ce." Wai ba zai kwana a can ba shine yake ta ihu yana kiran Usaina."
Abin ya ba ni dariya da tausayi. Na d'an janyo hannunsa ya taso ya tsaya kusa da ni tare da dora hannunsa saman cinyata na ce." Anan kai ma zaka kwana ko Sultan?"
Ya d'aga kansa. Na furta." Ashe kwanciyar dole kuke yi a can din ko Khalil?''
Shiru ya yi bai ce komai ba sai ma ya yi k'asa da kansa.
Hadiza ta mike tana fad'in." Bari a gyara musu shimfid'a." Ta nufi d'akin nasu da sauri.
Na ce su tashi su bita su canza kaya sannan duk su yi alwala kafin su kwanta.
Duk abinda ake yi yana tsaye yana kallonmu bakinsa ya mutu da alama ya rasa abinda zai ce. Bayan shigowarsu na dubi Khalil Ina fad'in" D'auko Usaini ka biyo ni dashi d'aki." Dama Hasan yana ri'ke a hannuna na tashi da shi a kafa'data kai tsaye bedroom dina na nufa ba tare da na sake kallon wajan da yake tsaye ba, a haka yara za su yi hutu a wajanta na kwanaki suna yi kamar za su mutu saboda kuka ashe da babu kowa a gidan ha'kuri kawai suka yi suka zauna tunda yanzu na dawo kuma sun nuna mata basu san wata ba bayan ni. Da nata da nawan gabad'aya don ni sai nake ganin twins ma sai su zauna a hannunta ba tare da koke-koke ba nata ba su zauna ba Minal dai da Sultan sun tsaneta wallahi abin har mamaki yake ba ni. Ita Minal yadda take bala'in sona shine abinda yake sanya mini sanyin jiki shi kansa Uban na lura da yadda jikinsa ya mutu abin ya fi karfinsa Hauwa ta haifar mini yara Allah mai iko......
'þ
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*169*
To ban san abinda ya kasance a tsakaninsu ba washe gari dai da misalin sha d'aya da wani abun Ladidi mai aikinta ta kawo musu kayansu kaf na can wanda suka yi amfani da shi bayan tafiyata kano da kayan sallar tasu da suke a hannunta pants takalmansu da kayan kitso abin wuya da hannu kowanne da na shi da alama duk ta had'a ta yi order din wurin Sadiyar gabad'aya girkina ne a ranar bai shigo ba sai bayan magriba tukkuna ya buk'aci abin bud'e baki na hada masa babu wata sakewa don sai nake ganin kamar akwai abinda ya boye mini. Kunun tsamiya muka yi da k'osai yadda ya kusa shanye dogon jug hakan ya tabbatar mini da cewa kunun ya yi masa dad'i k'osan ma ya ci fiye da biyar saboda sakin manya muka yi. Ya sha zo'bon dana had'a daidai gwargwado ya kammala yana godiya ga Allah kafin ya dawo da hankalinsa gare ni
Na yi shiru ina sauraransa." Akan maganar da muka yi dake kwanakin baya kin ce kina buk'atar a musanya miki wannan kamfanin ko?"
Na gyad'a kaina a nutse na furta." E, idan zai yiwu ba wai na raina kyautar ba ne kawai dai na fi gane business din da nake yi ina ganin idan na sake samun wani reshen anan za a samu alheri."
Ya ce." Shine dalilin da ya sanya ai na sake tambayarki tuntuni nake ta shawara a kan hakan kyautar za ta koma kan Hauwa tunda ni ba ni so a tashi kamfanin ko babu komai kadara ce mai girma da ta kafu tunda a 'kalla da kafa kamfanin zuwa yanzu ya haura shekara goma sha shida duk yanzu muna kan aikin fad'ad'a waninsa ammana akwai buk'atar shi d'in a cigaba da aiki da shi. Na mallakawa Hauwa shi ke kuma akwai tallan wasu tsoffin shaguna da aka yi mini cikin kasuwar wuse din idan mun kammala da masu shi zan sanya ma'aikata su rushe tare da sabunta shi zuwa plaza din kamar yadda ki ka buk'ata a k'alla dai za a iya samun shaguna sha biyu 'kasa shida sama shida a hankali idan Ubangiji Allah Ya sanyawa abin albarka sai ki yi wadda ta fi wannan din ko?''
Na ce." Hakane na gode sosai Allah Ya saka da alhari ya kara arziki ya kuma jikan iyaye."
Ya dinga amsa cike da jin dadi yana jifana da wani irin kallo wanda na gama fahimtar ko na menene.
A daran kam na kar'be shi sosai kuma na yi kokarin ganin na yi masa bajinta wajan ganin na bashi farinciki yanayin yadda na tallafe shi ya k'ara dilmayar dashi cikin yanayi na shau'ki da sambatu irin wanda ba a tonawa wannan lamarin ai ba zai fasu ba idan da rai da lafiya a jikin gangar jiki.
Kwanaki biyu bayan wannan su Baba Tabawa suka dawo murna a wurin yara ba a cewa komai tsalle mussaman Sultan ya rirriketa tana dariya itama ta rungumeshi bakinta kamar gonar audiga gabad'aya sun canza da wata iriyar nutsuwa alamu ibadar da suka gudanar ta samu karb'uwa a wurin Ubangiji domin fes suka dawo da wani annuri na mussaman a tattare da su.
Dawowarsu ta sake bud'e wani sabon babi na farinciki a gidan ya kasance koyaushe cikin wasa da dariya da juna mussaman da bikin sallar ya gabato Mairo ta tsefewa yara kitso an wanke tas Taburni itace makitsiya Lad'ifa mai lalle saura kwana uku sallah ta zo ta yini tana yi wa yara washe gari ta dawo ta yi mini tare da Hadiza aikuwa tasha kudi wurin maigidan mussaman da ya ga na yaran ja da ba'ki ya fito sosai ya dinga duba kafafun nasu yana murmushi ta had'a kayanta ta tafi cike da farinciki dubu dari biyu kudin lalle kawai duk da Hajiya Maryam ta saba yi mata kyauta amma wannan ta yi mata bazata domin duk zuwan da take yi mini lallen ni nake sallamarta yau sai ga shi rabonta a ya rantse, ta samu kudi da turaruka da sabulai na hada mata da gyale mai kyau.
A daran mai dinkinsu ya aiko da shi kowanne k'alla gudu leces biyu a tamfa daya sai shadda daya wadda ta ci uban aiki abin mamaki har da na masu aiki set biyu Hadiza kuma aka yi mata uku manyan atamfofi. Sai na 'kara mata da lece daga cikin kayana dake d'inke wanda ban sanya ba. Takalmi na bata set biyu masu tsayin dunduniya duk sabbi da abin wuya da hannu.
gaskiya babu lefi ya yi kara ya kuma nuna halin dattako domin duk wanda yake karkashina yana sane da shi yana kuma ko'karin fitar da hakki ban ta'ba tunanin zai yi wa Hadiza d'inkin sallah ba duba da ganin yadda abubuwa suka yi masa yawa ashe yana sane da ita a gidan ya kuma fitar mata da hakkinta.
Wannan shine abinda ya gudana bayan ramadan mun yi bikin sallah cike da annashuwa da farinciki tun daga kan masu aikin gidan maza dake waje da na cikin gidan su Baba Tabawa kowa ya kasance cikin nishadi da jin dad'i. Washe garin sallah yaran gabad'ayansu gidan Nusaiba suka yini bisa jagoranci Adam sai magriba suka dawo ta had'o su da snacks da yawa da kud'i Babansu ya dinga fad'a wai me yasa za ku kar'bo mata kudi ina lefin hidimar da ta yi musu. Na ce sallah ce ai don ta ba su kudi ba lefi ba ne.
Sun je gidan Hauwa amma ba wasu wani jima ba suka dawo itama ta had'o su da tarin chocolates masu yawa har da sa'kon gaisuwa zuwa gare ni. Cikin raina na ce tunda kin fara dafe wasu kadarori ai fitina ta kusa zama tarihi kyautar kamfanin da ya yi mata ya taka muhimmiyar rawa wurin dakushe mata damuwa tun bayan abinda ya faru ba ta sake fito da wani salon ba ga yaranta har yanzu suna hannuna.
Salim ya zo hutun sallah tunda yana can legos yana aiki a sabon kamfanin da suka bud'e shi ya dinga fita da yaran wuraran wassani ashe lokacin da Mamansu na raye haka yake yin jigila da su duk shekara ya ce ma saboda su ya dawo domin yin bikin sallah.
Sati daya ga sallah Inna Uwani ta shigo har gida wai sallama ta zo yi mini zata tafi. Na bata turaman atamfofi uku da kudi dubu ashirin na ce ta kara guziri. Babu jin kunya ta dinga yi mini godiya daga lokacin na sake tabbatar da cewa muguwar kwad'ayayyice mai son abinda duniya Allah ne ka'dai yasan abinda Hauwa ta had'a mata domin tafiya dashi wanda kuma nake da tabbacin cewa shi kansa maigidan ya yi mata sallama mai kyau Allah Ya kyauta ya rufa asiri yanzu zamani ya lalace tundaga lokacin dana ganta a shekarun baya tana yi masa yarfen magani a kafar bane na tabbatar da cewa bata da hali kuma bata tsoron Allah kuma za ta iya aikata komai a kan biyan buk'atarsu tunda ai ba zata za'be shi ba ta ajiye 'yarta ba duk wannan jidali da koke-koken da take yi akan abin duniya ne tana taya 'yarta kishi tana kuma yi wa 'yar uwarta ciki daya zagon 'kasa a yanzu idan ya fadi ya mutu

Na kudi ne littafin kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

damuwarta kad'an ce tunda ba ita ta haife shi ba mahaifiyarsa da yaransa sune suka yi rashi. Bala'in damuwar da suka shiga a lokacin da cikin nan ya zube ba zai misaltu ba domin an same shi ne da k'yar ni ma na gazgata maganarta bai fiye kwanciyar aure da ita ba domin da yana yi da ita ka'in da na'in zan samu sasaauci ta wannan fanni amma Allah ne da kullum duk ranar girkina sai ya neme ni idan har ba mu yi sunna ba to akwai dalili mai karfi wanda ya assasa rashin faruwar hakan koyaushe cikin doki da sambatuna yake ya sha fad'in shi kullum tamkar sabuwar budurwa nake a wurinsa abin ya yi ta ba ni mamaki haihuwa biyar ciki har da biyu sau biyu tun ina d'aukar maganarsa da dad'i ne na shau'ki har na gazgata domin da dukkanin gaskiyarsa yake fad'in hakan. To wannan shine dalilin da ya sanya su shiga tashin hankali a lokacin da cikin ya lalace har suna neman rabuwa saboda ganin kada a yi biyu babu yanzu kuwa na tabbatar da cewa ko da bata samu kula ta fannin auratayya daga wajansa ba to za ta cigaba da hakuri tunda ta fara samun abinda take buk'ata.
Hadiza wata uku a gidana ta murmure haskenta ya dawo ta yi ki'ba jikinta ya fara cikewa domin dawowar masu aikin gidan na hana ta yin wata wahala mai yawa sai dai duk da haka takan yi mini d'awainiya da yaran amma ba sosai take shiga kicin ba. Hakan ya yi mini dadi sosai domin ta fara sakewa na saya mata sabuwar waya domin ta kara d'eba mata kewa da mantar da ita irin wahalar da tasha a baya wajan zamanta a gidan kurkuku idan tana ba ni labari irin wahalar da ake sha ni kuka ita kuka daga karshe ma na ce ta daina gaya mini domin yadda ta ba ni labarin wani ma'aikaci da ya dinga farautarta a lokacin da bai samu hadin kanta ba kullum sai ya sanyatawa kwashe busashen kashin band'akunan gidan da hannu kuma ba zai bata sabulu ta wanke hannunta ba haka idan an kawo musu abinci za ta ci bayan ta wanke da ruwa kacal tana gaya mini hannunta har sai da ya kame da d'oyin kashi. A d'akinsu kuwa mutum biyar sai da suka mutu saboda wahala tasha kwana da gawa a d'aki daya. Tun daga lokacin na ce ba ni son labarin saboda shiga tashin hankali nake yi na ce ta dage da addu'a tare da neman afuwar Ubangiji tsautsayi da mugun ji da gani asara tare da danasani Ubangiji Allah Ya kare mu.
Ranar wata lahadi ya kasance girkina ne maigidan bai tashi a bacci da wuri ba sai bayan sha biyu na rana yana tashi kuwa ya ce mini towo zan yi masa kuma da hannuna miyar zogale.
Aka duba kicin kaf babu zogale dole sai an shiga kasuwa Masa'udu ya je gida ganin iyalinsa tun sallah bai dawo ba shi kad'ai ne ya yi wannan nisan zaman domin ko su Taburni da Mairo satinsu hud'u suka dawo bakin aiki bayan sun je sun gaisa da iyalinsu tare da yi musu alheri daga cikin alherin wanda yake ri'ke da su.
Mairo da Hadiza sune suka shirya shiga kasuwa sayo zogale dalili Taburni da Baba Tabawa na aikin abincin rana. Suka shirya suka tafi Sukairaju ya kai su na hada musu da sautin tsamiya domin ya dingi shan kunun tsamiya ko bayan wucewar Ramadan sai ya ce a dama masa kuma ba dare ba rana duk lokacin da buk'atar son shan kunun ya bijiro masa wadda muke da ita tana daf da k'arewa da zo'bo tunda ana yi masa baya shan lemo mai gas.
Ba su yi awa d'aya ba kuwa suka dawo da komai da komai har da daddawa duk da ban buk'ace ta ba dalili ina da ita da yawa kuma mai mugun kyau wadda Hajja ta sanya aka yi mini ita mussaman lokacin haihuwar su Hassan da Magaji ya zo ya kawo mini kwalli da garafuni ya had'o mini da ita manya mai dadi a miya. Na ce ita din ma da suka sayo ba za ta'ki ba za ta yi amfani.
Tsaf na shirya masa towon shinkafa da miyar zogalen kamar yadda ya buk'ata na yi amfani da zallar tsoka na k'aramar dabba wurin had'a miyar da ta ji gyad'a da manja ta yi kyau sosai tana ta tashin k'amshi.
Cikin santi ya ci towon nan wurin malmala biyu kad'an ne bai cinye ba ina ta yi masa dariya ganin yadda yake sud'e hannu ina fad'in idan baka koshi ba sai a sa wani bai ce mini komai ba ya sud'e yatsun hannunsa tas ya shiga toilet domin yin burush

Bayan kwana biyu ya je gidan Hauwa ya yi kwanakinsa ya dawo yake gaya mini wata magana. Jikina ya yi sanyi sosai na zuba masa ido a hankali na ce." Hadiza fa ka ce, bai duba shekarunta ba kwanaki biyar kawai ta ba ni shekara arba'in da biyar muke ni da ita ba budurwa ba ce.''
A nutse ya furta." Akwai haramci ne cikin abinda Annabi Muhammadu S.a.w ya yi. Kada ki yi mana sa'bo hajiya shima Sukairajun ai ba saurayi ba ne ya ta'ba aure."
Na zuba masa ido sosai da mamakin jin maganarsa. Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ya ta'ba aure shekarun baya a can mahaifarsa mutumin Zamfara ne kin ta'ba neman labarinsa a wajena?"
Na girgiza kaina a hankali ina cigaba da kallonsa sai ya cigaba da ce wa.'' Ya zo nan kano cirani muka hadu da shi a titin Yahya gusau watarana tun kafin na yi shura a duniya yana sayar da fetur da kanikanci ya gyara mini mota a lokacin da lalace daga lokacin ya zama wanda nake bawa gyaran mota a duk lokacin da ta samu matsala muka yi sabo sosai har dai ya zama direbana kafin Ade da D'ahuru Sukairaju yaro ne mai Amana da nutsuwa da kuma girmama mutane ya gaya mini ya yi aure amma matar ta rasu wurin Haihuwa sasha zuwa garinsu wurin mahaifiyarsa kafin ta rasu. A duk lokacin da ki ka gan ni tare da Ade to Sukairaju ya je ganin gida tunda duk 'yan uwansa suna can garin. Kuma ba na tsammanin Hadiza za ta girma shi sai dai su yi daidai a shekaru to menene aibu shine ya gaya mini da zata amince sai ya aureta shi yana sonta duk da na gaya masa abubuwan da suka faru a baya ya amince da hakan, don haka ina nema masa auranta a wajenki tunda kece uwar dakinta idan kin ce a yi za a yi."
Na yi kasa'ke ina kallonsa kafin na ce." Allah sarki wallahi ni kam ba ni da jayayya ko na kawo tasgaro muddin Hadiza ta amince zan fi son haka tunda har ka yabi kyawawan halayensa kuma ni ma na sheda hakan idan tana sonsa sai mu sha biki."
Ya yi dariya yana kallona kafin ya ce." To ta wace hanyar ki ke ganin za a sanar da ita halin da ake ciki, kin ga ni yayata ce da kunya na tunkareta ko."
Na d'an harare shi ina fad'in." Yayarka fa ka ce." Ya gyad'a kansa yana fad'in." K'warai kuwa ko da yini guda ta girme ki ai sunanta Yaya Hadiza a wajena."
Na yi kasa da kaina ina murmushi na ce." Shikkenan to ni zan gaya mata in sha Allahu rabbi za ta amince."
Ya furta." Da na fi kowa farinciki kuwa, ni kuma na yi alkawari zan yi iyakacin bakin kokarina.'"
Na gyada kaina ina fad'in." Ubangiji Allah Ya tabbatar da alheri." Ya kama hannuna yana cewa." Amin Ya Allah."

Ai a daran na same ta da maganar ta dinga dibi-dibi da 'kyar ta bud'e baki jikinta a mace babu wani karsashi da sukuni a tattare da ita ta kalle ni sai na hangi k'walla mai yawa cikin kwarmin idonta ta ce.............

In sha Allahu da ni daku mu sanya rai saura 8 chapter littafin nan ya kammala Allah Ya taimake ni ya kuma yi riko da hannuna dan isar Annabi. Ina miko godiya kwarai da fatan kowa ya sha ruwa lafiya. Ubangiji Allah Ya kar'bi ibadarmu ya 'yantar damu.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*


[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*170*
Shiru na yi ina sauraranta a yayin da take gaya mini abinda yake damunta har tana zubar da hawaye na damuwa da kunci tare kuma da fargaba. Jikina ya yi sanyi sosai domin dai na riga na gama fahimtar manufarta ba wai auran ne abin gudu a wajenta ba abinda zai haifar bayan yin sa shine take ji wa tsoro da zullumi. To ai babu wata cuta da Ubangiji bai yi maganinta ba duk da infection wani irin ciwo ne da yake saurin dakusar da mu'amula da auratayyar da aka gina cikin tsananin so da sha'kuwa. Bayan rashin ha'kuri daga b'angaran ma'aurata abu na biyu da yake saurin kassara aure da lalatashi shine infection mussaman idan an yi katari da cewa macace taje da shi ta shafawa namiji abin sai ya yi muni da tsanani aure ya gurgu'de ba tare da yaje ko'ina ba. Hadiza na ga wautarta kwarai domin yanzu a k'alla da fitowarta daga gidan gyaran hali za a samu wata hudu to tun a lokacin ya kamata a ce ta sanar mini da abinda yake damunta domin neman magani ka'in da na'in. Zubar ruwa da kumburin gaba abu ne mai tsanani watarana zata iya wayar gari da susa tunda shi infection din idan ba a yi sauri an tare shi ba girmama yake yi har wasu su d'auka ta dalilin da rashin kula. Dama tun zuwanmu daki daban na ware mata a falon nan take kwana hakan ya sake yi mini amfani kywarai domin kuwa ina ganin da an yi had'akar toilet to wani zai iya d'auka wannan lamarin ba abin yin shiru ba ne kenan da wannan mas'alar ba ta zo ba haka za ta cigaba da zama da ciwo yana cin ta har sai ya zama babba irin wanda ake gudu. Tabbas babu maganar aure a wannan yanayin da ake ciki tukkuna sai an magance matsalar idan ya so ko ma menene sai ya biyo baya babu amfanin gaggawa cikin kowane lamari kuma aure ba abin wasa ba ne idan har an yi shi to kowace mace tana bukatar zama a dakinta rayuwa ta din-din din ai abinda ya fi infection ma za a iya d'auko shi a wannan gida domin da ta biyewa mazan dake bibiyarta wata'kila da da cutar 'kanjamau za ta dawo tunda yanzu maza da yawa sun lalace da neman matan banza ba wai ma'aikatan gidan ba manyan mutane ma da suke yawo cikin manyan riguna da motoci na alfarma tare da wata suttura ta Allah amma sai ka same su a hotels tare da karuwai suna amfani da su kuma suna da iyali a gida har da yaransu.
Haka dai na kwana cikin tunani da nazari da safe ashe yana hankalce da ni yana ta shirin fita ya ce na fito masa da takalminsa sahu ciki dake ma'ajiyarsa na fito masa da shi din kamar yadda ya buk'ata ya fesa turare ko'ina na jikinsa ya zo ya zauna gefena a nutse ya fara sanyawa k'afafunsa safa sai da ya kammala tukkuna ya dube ni amma bai ce komai ya gyara zaman gilas dinsa ya furta." Akwai abinda yake damunki Giwa ashe mun kai matsayin da yanzu za

Please Login or Register in order to submit comment