Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ka hadu har aka kulla auratayya matsala na faruwa iri-iri tunda dama kafatanin auran ha'kuri ne jin dad'insa kad'an ne. Amma dai da sauki akan ace abu biyu ne suka hadu waje daya dangantaka ta jini zumunta mai karfi kuma da dangantaka ta aure sai abin ya zama wani iri iyaye su shiga idan an kai magaryar tu'kewa lamarin ya yi tsamari a tsakanin jini d'aya a !!!!!!! !
! ! !
!!!!!!!!!!!!!!!!!!! !!!"!#!$!%!&!'!(!)!*!+!,!-!.!/!0!1!2!3!4!5!6!7!8!9!:!;!!?!@!A!B!C!D!E!F!G!H!I!J!K!L!M!N!O!P!Q!R!S!T!U!V!W!X!Y!Z![!\!]!^!_!`!a!b!c!d!e!f!g!h!i!j!k!l!m!n!o!p!q!r!s!t!u!v!w!x!y!z!{!|!}!~!!!samu rabuwar kai da zargin juna daga kowane b'angare duk domin kiwatar kai bisa zargin zalintar juna.
Abinda ya faru kenan da shigarmu gidan Hauwa ni Hajja gaisuwa kawai ta ratsa a tsakani Inna Uwani ta dinga kuka tamkar wadda ta yi rashin jinji nan abu tana fad'in idan abin nan bai zai yiwu ba a rabu tunda akwai maslaha a sha'anin aure Ubangiji da ya umarci a yi shi ya hallata rabuwa (saki) domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tana kuka tuk'uru tare da jadadda Hajja Hauwa ce kadai ta rage mata a duniya a yanzu tana ji tana gani kuwa ba za ta bari ta yi asararta ba saboda bak'incin da kishiya take gumamata miji ma ya guma mata nasa.
Hajja dai shiru kawai ta yi jikinta a mace tana kallonta ita na kuka Hauwan ma na kuka irin mai ciwon nan.. ganin haka ya sanya na yun'kura na tashi jikina a sab'ule gwiwata duk ta sage saboda ganin wannan lamari bai yi mini dadi ko kad'an ba amma Allah ne shahidi idan har ina cutar Hauwa a zamantakewa to ina ro'kon Allah Ya saka mata.
Na ji maganarta tana fad'in." Dole ki tafi ki tafi Amina ke ma kin san abubuwan da kuke yi wa yarinyar nan ba ku kyautawa idan har tana da hakki a kan ki da shi mijin naku ta bar ku da Allah."
Tana kuka ita Hauwan ta ce." Ban ce miki Amina ta yi mini wani abu ba inna, ni kawai na gaji da zama da mutumin da bai san raunina ba bai kuma yarda ya haihu da ni ba sannan bai san ya rarrasheni ya tausaya mini idan ina cikin b'akinciki ba. Wallahi da gaske nake Hajja na gaji yara Allah Ya raya su tunda dama ai ba hannuna suke ba."
Hajja ta dube ni a sanyaye ta ce." Zauna yadda muka zo tare haka za mu tafi tare ai ke ma ba bare ba ce."
Na koma na zauna din
Kamar yadda ta umarta.
Ta dube yar uwarta cikin nutsuwa ta furta." Tunda kun yanke shawara kan cewa rabuwar kuke buk'ata abu ne mai sau'ki ai Uwani dalili ni kaina lamarin nan ya ishe ni wallahi ba zan tantance wanene mai gaskiya ba a tsakaninsu Tajo ne ko ita Hauwa. Amina kuwa ku daina sanyata a ciki babu abinda ya shafeta ban fad'i haka don ina goyon bayanta ba. Ita da Hauwa duk daya suke bambanci kawai ita tana bin umarnina tana kuma yi mini biyayya bisa duk abinda na umarceta tana son abinda nake so wata'kila ba ku san da cewa asalin auranta da mijinta umarni ne daga gare ni ba gani daya rana d'aya da ni da ita mun roki Allah kuma ya amsa mana bata san ni ba, na nemi alfarma ta yi mini a lokacin da mata da yawa suka guji auransa saboda ceton ransu ita tace ta ji ta gani duk da tana da labarin abinda ya faru da shi a baya. Wannan shine abinda ya dasa mini kaunarta cikin zuciyata kuma ban fifita ta a kan ki ba Hauwa na dai gaya miki bambancinku amma tunda kun yanke shawara a tsakaninku zan same shi domin gaya masa uzurinku sannan kuma ina so nasan abinda yake yi miki na take hakki ai dole ne shima a nuna masa kuskuransa tunda ni uwarsa ce kuma har yanzu yaro ne a wurina dole ya bi abinda nake so."


Littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Cikin jan hancin da kame-kame ta fara magana." Abubuwan da yake mini ba za su lissafu ba Hajja dole a cikin aure nasan ana cin karo da matsaltsalu da yawa kuma dole a yi hakuri, amma ni tunda na faru a tare dashi ban ji dad'i irin yadda nake so ba duk wanda ya ba'kunce mu yasan zaman ha'kuri nake yi ya gaya mini ya kuma nuna a zahiri zama yake yi dani saboda yaran da muka haifa da kuma zumuci, duk haihuwar data ratsa tsakaninmu tsananin rabo ne yakan jima bai kwanta da ni a shimfida daya ba, ni zan ta bin sa domin neman hakkina wallahi bai ta'ba yi don dad'in ransa ba. Ya karkata b'angare d'aya ya fifitata fiye da ni ya k'aunaci yaranta Y
yana biya mata dukkanin buk'atunta Hajja ya zan yi da rayuwata na samu ciki ya zube ya nuna bai damu ba alhalin da kyar na same shi tunda ba kwanciya muke a gado daya ba ya cigaba da abinda yake gabansa ba shi da damuwa tunda ya nuna ga da wadda ya fi buk'atar haihuwa da ita." Ta ja hanci hawaye na silalowa a saman kuncinta ta cigaba da cewa." Ni na gaya muku ba ta yi mini komai lefi nasa ne tunda ya kasa daidaita tsakani na da ita ya fifitata ni kuma yana nuna mini kamar akan dole yake zaune da ni."
Hajja ta tsira mata ido kawai tana kallonta. Ni kuwa na shiga nazarin maganganunta. Abinda ya kara tashin hankalinta zubewar cikinta tunda kowa ya san yadda ta jarbatu da haihuwa idan har gaskiya ne abinda ta fad'i a kansa to
bai kyauta ba wata'kila ita tana d'aya daga cikin jerin mata masu buk'ata shi kuma ba a jarrabe shi da ita ba. Ga ciki ta samu tana murna tunda ta fad'i dama ba ta so na fita yawan yara a gidan to sai kuma ya zube shi mai cikin bai nuna damuwarsa ba, ga ni kuma ina haihuwar bibbiyu shine babban tashin hankalinta abubuwa da yawa suka taru a zuciyarta."
Na ji Hajja tana fad'in. " Haihuwa ta Allah ce Hauwa itama Amina bibbiyun da take haifa ba ita ta bawa kanta ba rabo ne, kuma akwai gadonta a jininta. Amma kuma idan har da gaske ne abinda ki ka fada lallai akwai buk'atar zama a tsakani domin ai ke ba baiwa ba ce mutum ce me zai sanya shi ya dinga take hakkinki a shimfida wannan cutarwa ne ki yi hakuri ki barwa Allah ikonsa kin ji ko, wad'annan da ki ka haifa uku ki yi ta yi musu addu'a Allah Ya raya miki su sai ki ga sun tara miki garke guda. Wani ma yana can Allah bai ta'ba bashi haihuwar ba kuma haka zai koma ga mahallicinsa. Lallai zan yi masa magana idan har ba zai gyara ba to sai ya baki takarda ba dalili ba ne wannan Allah cewa ya yi idan har ba za a yi adalci a tsakanin mata biyu uku hud'u ba to kada a yi domin gujewa sa'bawa Ubangiji."
Inna Uwani ta goge fuskarta tana fad'in.'' Ni kaina abin nan ya ishe ni wallahi na gaji da bata ha'kuri da danneta akan ta zauna. Yanzu ga shi ta hadu da hawan jini saboda tarin damuwa."
Hajja ta ce.'' Uwani na ce miki abin zai zo da sauki ai, shi wanda yake da alhakin sakin a yau zan zauna da shi domin mu samu matsaya kada wannan ya dame ki."
Ta yi sakato da baki tana karyar da kai gwanin ban tausayi.
Ta yun'kura ta tashi a hankali tana gyara yafan mayafinta ta dube ni tana fad'in." Tashi mu tafi." Na tashi da sauri domin dama kamar akan 'kaya nake a zaune a wurin.
Ta dubi inna Uwani tana Fadin." Idan an yi Isha'i sai ki shigo domin jin ina aka kwana."
Da sauri ta ce." To shikkenan." Ta sake duban Hauwa a karon da ba zai lissafu ba ta ce." Ke Kuma ki kara hakuri kin san dai illar yawan tunani da damuwa ko tunda ga abinda ya haifar miki don haka ki cire duk wani zullumi da tunani da ba'kin kishi a ranki Hakan shi zai sanya ki samu zaman lafiya."
Daga haka sai ta kama hanyar fita na bi bayanta cikin rashin karsashi.
Muka isa gidana babu wanda ya yi magana. ban ta'ba ganin tsananin bacin rai a fuskarta ba sai yau damuwa gabad'aya duk ta dabaibayeta ga tarin shekaru don ma da kula sosai amma matsalar nan kadai ka iya tayar mata da ciwonta. Na rasa da wane kalami zan rarrasheta domin kwantar mata da hankali saboda gabad'aya yanayinta ya canza da bakincikin abinda ya faru.
Na gyara mata fillo a masaukinta ta kwanta tare da mike kafarta na fita daga d'akin cikin mutuwar jiki da tunanin mugun kishin Hauwa a kaina shi zai halaka mata rayuwa kamar yadda hajjan ta fad'a domin kuwa duk mai hankali yasan tsananin kishi ne yake damunta da ganin k'yashi.

Ban san yadda ta kaya a tsakaninsu ba domin tunda na shiga d'akina ban fito falo ba ya dai kira ni a waya da ya dawo to nasan dole za su zauna zaman tattaunawa yara ma sai Mairo ce ta kawo mini su tunda wurin baba Tabawa na bar su.
Sai can wajan goma da arba'in na dare ya kira ni a waya lokacin nasan sun tashi.
Na leka domin dubata tana saman dadduma a zaune da cazbaha a hannunta ganin haka ya sanya na ja mata kofar kai tsaye saman nasa na nufa zuciyata na dokawa haka kawai rashin hakurinsu na nema ya d'agawa tsohuwa hankali.
Ya fito daga wanka yana sanya kaya a jikinsa kafin na zauna ya ce na kawo masa abinci ban ce komai ba na sake sauka kasan da zummar bin umarinsa.

Abinci ya ci ya koshi sosai ina kallonsa babu wata damuwa mai gigitarwa a tattare da shi ya kammala ya goge bakinsa da tissue ya ja gefe na sauka da tiran abincin kasa na dawo na same shi jingine jikin gado yana duba wayarsa. Zamana bai sanya ya dube ni ba. Abin nema yake yi ya shafe ni kenan tunda magana ma ta gagare shi. Ban nemi lallai sai na ji halin da ake ciki ba tunda bai shafe ni ba idan shi ya gaya mini zan saurare shi ba ni da wata shawara da zan ba shi akai duk abinda ya yanke a tsakaninsu daidai ne.
Na daure zuciyata na kalle shi a nutse na ce." Ina tsammani tare za mu tafi da Hajja zuwa Kano Gwaggo fa jikinta babu dad'i tun lokacin haihuwar yaran nan take ta fama wallahi ya kamata na je dubata."
Ya yi shiru bai ce komai ba. Sai da na sake maimaita maganar tukkuna ya dube ni yana fadin." Don Allah kada ki k'ara mini wani b'acin ran Amina a bar ni cikin wanda nake a yanzu."
Na ce." A a ban gane kada na bata maka rai ba, zuwa duba jikin Gwaggo shine abin b'acin rai kuma?"
Ya shiru bai tanka mini ba."
Na ce." Ka dai duba don Allah babu rashin dacewa fa kuma ciwo ake dubawa."
Ya ce." To zan duba idan zai yiwu ."
Na ji wani takaici ya yun'kuro mini amma sai na danne na yi masa uzuri saboda yanayin da yake ciki na damuwa.
Haka muka wayi gari zuciyoyi babu dad'i da safe kafin na sauka kasa ta kira shi a waya aikuwa ya fashe tunda dama ya kumbura sumtum! jira yake yi a zungure shi ita in banda abinta tasan abinda ta yi kuma ai sai ta ja gefe ta yi zaman saurare. Fadi yake yi "Ban yi niyyar sakinki ba Hauwa ku kaini 'kara kotu mara mutunci masu mance alheri. Ni za ki yi wa wannan iskancin duk abinda nake yi miki ba ki ga ni ba sai kin had'a ni da uwata tuntuni na gaya muku ba ni son abinda zai d'agawa mahaifiyata hankali da girmana ku dinga yi mini terere babu wadda za ta rufa mini asiri ba ni da sirri a gidana. Kin cire kunya kin gaya mata karya da gaskiya ba ni baki hakkinki ni za ki yi wa sharri Hauwa wato duk ko'karin da nake yi miki ba ki gani ko? Ga ni ki ke yi yawan kwanciyar aure shi yake kawo haihuwa kina ganin daga 'bangarena ne haihuwar biyu da Amina take yi ba baiwa ba ce da rabo daga wurin Allah. Shikkenan kin buk'aci rabuwa ni kuma ba zan yi rabuwar a lokacin da kuka buk'ata ba.
Na ji cikin rawar murya tana fad'in." Ni wallahi ban ce mu rabu ba, cewa na yi ka gyara kuskuranka ni ma na gyara kuskurena mu zauna lafiya ai kowa ya sani ka fi buk'atar haihuwa da Amina kuma soyayyar da kake yi wa yaranta ya fi wanda kake yi mini da abinda na haifa."
Na cika da mamaki kwarai jin yadda take fad'in ita ba tace su rabu ba kenan k'aryata Hajja za ta yi bayan su suka fad'i haka.
Ya ce." Kina nufin Hajja ta fad'i hakan ne kawai domin ta ji dadin bakinta kenan, so ki ke na lalace a gadonki na dingi jima'i dake saboda ki tara yara kin d'auka sakarai ne ni da ban san abinda nake yi ba, ko kin yi zaton ban fahimci gasar haihuwa ki ke yi da Amina ba. Duk abubuwan da kuke gudanarwa a gidan nan daga ke har ita ina sane kuma ina bibiya shiru kawai nake yi muku. Ba zan sake ki ba, kuma ba zan sake yin cikin da za ki haihun ba sai mu ga yadda za ki yi."
Ya kashe wayarsa yana huci! Na dinga kallonsa gabana na fad'uwa. Oh! ikon Allah wata ta kunno bala'i yana nema ya shafe ni Ubangiji Allah Ya sawwa'ke musu wannan masifa.
Na tashi na sauka bai ce mini komai ba ni ma ban yi masa sallama ba.
Bayan kwana biyu da kansa ya ce na shirya da safe sai mu tafi tare gabad'ayanmu zuwa kanon shima zai duba jikin Gwaggon.
Na yi godiya a takaice babu wani sakin fuska domin haushinsa nake ji ganin yadda yake nema ya jingina ni a jikin badakalarsu.
Tare muka nufi kano a washe gari wanda ya yi daidai da saura kwana biyu a d'auki azimi a ranar da daddare ni da shi muka je har gida duba Gwaggo da sauki za a ce amma dai da kyar ta gane ni. Hamusu kuwa ya sha fad'a a wajensa ganin haka ya sanya ban yi masa nawa fad'an ba tunda an had'a gabad'aya an yi masa menene amfanin abinda ya yi wai kada a d'orawa mutane nauyi wannan maganar ta yi bala'in bata mini rai.
Da sassafe a ka d'auketa a kai kaita asibitin Malam tunda dama tana file Dr Iliyas da abokanan aikinsa suka shiga bata taimakon gaggawa.
Kwana daya ya yi ya juya ya ce yana da uzuri amma da shara'din na biyo bayansa da kwana biyu na ce masa to kawai ba ni kuma tsammanin bin sa sai na yi sati gidan Hajja na zauna bangaranmu na gidan. Ban zo da mai aiki ko daya ba tunda tafiyarsu a cikin satin nan ne azimi da kwana uku ko hudu yaran kuma sun dan yi wayo ni da iyami mai aikin Hajja muke kula da su.
Da daddare ma da zan sake zuwa duba jikin Gwaggon a gida na bar su wajanta Magaji ya d'auke ni a mota zuwa asibitin Malam din.
Wani ikon Allah wai ana tunanin samun sau'ki da rangwami a wajan da aka kaita domin kula da lafiyarta sai abin ya kara rikicewa jikin ya'ki dad'i yadda ake buk'ata Gwaggo ta kai ta kawo sai da aka sanya mata abin numfashi a hanci saboda bata iya yi da kanta.
Kuka na dinga yi a fakaice saboda tashin hankalin ganin yanayinta wani siririn hawaye na zuba ta gefan idanunta tana daga kwance a gado(tun muna yara Iya kakarmu ta wajan Uba da zata rasu ta dinga yin wannan hawayen na gefan ido aka ce mana wai na sallama da duniya ne) Gwaggo na
mike a gado ana ta cuku-cuku a kanta duka rai ake yi wa wannan fafutukar amma zahiri ciwo ya ci karfinta sosai Gwaggo lokaci take jira domin tun ganin da na yi mata a gida na sare.
Babu wani kuzari muka fito daga d'akin ni da Hamusu ba mu jima muna magana ba muka yi sallama saboda dare ya yi na shiga mota Magaji ya ja muka fita daga asibitin.
Bacci mai cike da mafarkai marasa kyau na yi da asuba na tashi jiki a mace Ina zaune saman dadduma Yusi ya shigo da tsananin tashin hankali. Ganinsa a hargitse sai gabana ya fadi ya furta. Mama Allah Ya yi wa Gwaggo rasuwa. Baba Hamusu ne ya kira ni a waya yana gaya mini wai yana ta kiran wayarki a kashe d'azu da asuba ta rasu.......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*167*
Mutuwa dai itace karshe mai yanke nisha'di da walwala mai jefa zuk'ata cikin firgici a lokacin da aka yi tabbas mutane na shiga cikin hankalinsu tare da tuna yaushe tasu zata riske su kuma a wace rana ne. Mutuwa ko ta kafiri ce takan sanya tsoro da nadamar duniya to balle mutuwar mumunai daga cikin salihan bayin Allah. Ha'kika mu da muke ahalinta mun yi rashi kuma mun koka 'kwarai da gaske bisa rashin ta da muka yi amma wani abin mamaki da ikon Allah yadda ma'kota ke kuka wiwi har da yara k'ananu bisa rashinta shine abinda yake bawa kowa mamaki. Lallai Gwaggo tana d'aya daga cikin wad'anda Ubangiji Allah Ya fadi cewa tundaga mutuwarsu ake gane cewa 'yan aljanna ne. Sosai ta samu jama'a kwarai da gaske haka zalika duk wanda zai zauna ya tashi sai ya fadi alherin da ta yi masa da jikinta ko kuma da aljihunta. Gwaggo ta samu sheda daga wurin ma'kotanta da sauran abokanan arziki duk tsayin zamanta a garin kano a kuma cikin unguwar da take aure babu abokin fad'anta tsakaninta da kowa lafiya ta rabu.
Gari yana yin haske kad'an muka tafi ni da Hajja da Yusi lokacin tuni an kawo gawar daga asibiti ma'kota mata sun cika gidanta mazansu a waje da sauran danginsu abbansu Yusi tunda dama ba wani yawa ne da su ba layin cike yake da jama'a yara da manya cikin alhini da tashin hankali.
Sai yamma tukkuna mutanan maiduguri suka iso cikinsu har da Dada kakarmu na dinga mamakin ko'karinta tunda itama bata da wani 'koshin lafiya. Ta ci kuka kuwa sosai tana fad'in ta so ta zo ta samu gawar aminiyarta ta yi mata addu'a. Anti Yagana Ya Falmata da kuma iyalin baban Saude dana Babanmu Babagana mahaifinsu babandi tare muka yini da su da magriba Hajja ta ce na kira mata Magaji suka yi waya ta ce ya d'auko babbar motar da za ta d'auke mu gabad'aya mu tafi can gidan nata mu kwana gabad'aya har da su tunda gidan Gwaggo bashi da girman da zai d'auke mu duka. Haka kuwa aka yi bayan isha'i magaji ya zo a lokacin ne muka yi sallama da Ummansu Hadiza da Fati suka tafi tunda suma tare duk muka yini Babanmu kuwa da shi aka yi jana'izar Gwaggo shine akan gaba. Ita kuma Ummansu Saminu tana kwance bata jin dadi dalilin da ya hana ta zuwa kenan. Shi ma Usaini ya yi wa Hamusu kara sosai domin yinin ranar rufe shago aka yi duk suka zauna wajan kar'bar gaisuwa har ya kawo matarsa Hajara muka yini tare da su gabad'aya tana ta fama da d'an cikinta da ya huda zani ya fito kurcici sosai na ji dad'i bisa wannan karar da suka yi mana.
Hajja ta sanya aka gyara musu d'aki a cikin falonta tunda da akwai dakuna hud'u duk kuma a shirye suke gyaran da Iyami ta yi kad'an ne tace su shiga su huta kafin a kawo abinci.
Muna tare da su gabad'aya don sai a lokacin ma iyalin baban Saude ke yi mini barka tunda ba su samu ikon zuwa taron sunan da muka yi ba kamar yadda ya yi mini alkawari saboda rasuwar mahaifin Mamansu Abahuraira amaryarsa kenan. Na ce da su babu damuwa komai nufin Allah ne. Sun yi godiya sosai wai ba su zo ba amma sakon turaman atamfofi ya iske su har gida.
Ranar Kamalu muka yi bidiyo call da Kamalu ya yi wa kowa ta'aziyya tare da jajantawa cikin alhini to ya za a yi abinda kowa yake fad'i kenan lokacinta ne ya cika amma abin farincikin rahamar Allah da ake yi mata zato.
Ban yi tunanin zuwansa a ranar ba tunda duka bai fi kwanaki uku da komawarsa ba
Allah sarki sai gashi wajejan k'arfe goma sha biyu na dare har da mintina akai ya shigo gidan Hajja wata'kila tafiyar mota ce kuma bai fito da wuri ba. Ya d'an ba ni tausayi ganin yadda rayuwarsa take gudana a tafe daga nan sai can babu wani hutu idan har an kwanta to dare shima a cikinsa sai an yi wata ibadar ta jijjiga jiki. Lokacin da ya samu kwanciya da wadataccen hutu na dole da rashin sukuni
shine lokacin da Hajiya Maryam ta shimfid'ar dashi shine ya yi kwanciya mai kamar mutuwa hutun dole ba don dad'i ba.
Muka kwana tare da shi a b'angaransa na gidan inda na sauka da zuwana. Sosai ya yi mini ta'aziya ya jajanta rasuwarsa ya kuma bayyana alherinta tare da jadadda mini ri'ke amanar da ta bashi kafin rasuwarta.
Da gari ya waye ya riga mu yin gaba domin ko cikin gidan bai shiga ba wurin su Hajja basu san ya zo ba. Ya ce duk idan sun had'u gidan rasuwar sai su gaisa.
Haka kuwa aka yi a can gabad'aya suka gaisa da su Dada ya zauna cikin jama'a ana ta kar'bar gaisuwa da shi Babanmu a gefensa da Baba Sule sai Idiris dana hange shi a gefe a zauna kusa da Baba Sule duka muka gaisa kafin mu shiga ciki nan ma ma'kotanta suna ta hidima da wasu daga cikin danginta da suka sauka jiya da daddare.
Ranar sadakar uku daga gidan Hajja aka yi abin sadaka abinci mai kyau ciki har da wainar shinkafa fanke da wainar gero da sauransu haka Magaji ya d'auki kololin abincin ya tafi ya kai gidan da sassafe.
Kafin ya dawo ya dauke mu gabad'aya zuwa gidan.
A ranar ne Sahura da Yusura suka zo mini gaisuwa da yamma kuma sai ga anti Maimuna uwargidan Alhaji Muntari tare da Salima babbar yarinyarsu goye da d'anta a baya. Na ji dadin ganinsu kuwa abubuwa da yawa suka hana ni neman inda suke a duk lokacin da na zo garin amma ina samun labarin Turmuzi a wurin Hamusu tunda ragamar kula da shi tana hannunsa har yanzu shine ma yake zuwa duba shi makaranta kamar dai yadda ya dinga d'awainiya da Kamalu.
Muka gaisa sosai cikin karamci da kulawa ta ce mini itama labarin rasuwar ta ji ta ce bari su zo tun kafin a watse tasan ina nan ban tafi ba sai su yi mini gaisuwa. Na dinga godiya kuwa ina tambayarta yara ta ce mini duk suna nan lafiya lau. salimat ta kwanto mini yaronta daga bayanta tana sinne kai Sahura na tsokanarta to abin ai ba wahala tunda dama 'kawar Yusura ce kusan sa'annin juna ne itama gata nan da d'anta daga zarar an yi auran ne sai haihuwa yanzu shiyasa wasu samarin a cikin irin abinda suke saye na angwanci suke hadawa da pampas da set din kayan sanyi domin jiran ko ta kwana.
Anti maimuna ta ce mini tana nan tana sana'arta sai abinda ma ya yi gaba domin har ta kama shago gaba da su kad'an ana sauke mata motar itace da buhuhunan gawayi tana gaya mini ita Jamila tana can harkar film take yi. Kuma sau biyu ta zo ta duba yaranta tun bayan rasuwar Babansu ta tayar da masifa a sayar da gidan a bata gadon yaranta sai da aka yi mata rubdugu jama'ar unguwa suka yi mata tara-tara kamar za su daketa sannan ta kama borin kunya yaran unguwar marasa kunya masu jini a jikina suka ce duk ranar da ta sake shigowa unguwar sai sun zane mata jiki. To tun daga lokacin ne

Please Login or Register in order to submit comment