Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an tashi lafiya wata matsala dai ba ta faru ba ni na gaji ma da zaman nan wallahi Ya Falmata tunda mun had'a kaya an jima muna yin wanka mu kama hanya."
Na ce." Sai dai gobe tunda ya fita kuma har yanzu bai shigo ba ai ba za ku tafi ba tare da kun yi masa sallama ba."
Ta ce." Bashi muke bin sa da sai mun jira ya dawo Amina."
Na ce." Duk da haka dai anti Yagana a bari ya dawo din ya fi mutunci."
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba. Itama Ya Falmata din ba ta tanka ba maganar dai da take ta jaddada mini shine kada na yarda ya auri Nabila domin babu haske a cikin al'amarin. Yadda ta zafafa sosai abin har mamaki yake ba ni, kishi take taya ni sosai Hauwa ma don dai tana ciki ne muna tare da yaranta babu yadda za a yi da ita.
Ba su tafin ba kuwa sai da gari ya waye tara na safe sun fito lokacin Masa'udu ya kwashe kayansu tsaf ya kai mota su Hajja na d'aki ba su fito ba muka shiga tare muka same su ashe inna Uwani a gidan ta kwana duka muka gaisa cikin mutunci da raha. Ya Falmata tana fad'in." Bako zai yi halinsa Hajja mun yi shirin tafiya, mun gode sosai Allah Ya kara girma yara kuma Allah Ya raya su."
Ta dinga amsa da "Amin mune da godiya Allah Ya saka da alheri."
Tare da ni su gabad'aya muka yi musu rakiya bakin mota suka shiga Ya Falmata da anti Yagana ita Sahura sai gobe yadda muka yi da ita za su tafi.

****
To sati uku da haihuwa gidan na mu ya daidaita kamar ba a yi wata dabdala ba kowa ya watse an bar ni da yara da masu aiki kamar yadda muke a da. Hassan da Usaini basa zuwa hannuna sai idan yunwa ta kawo su suna can wurin Baba Tabawa da taburni da daddare ne kawai nake kwana tare da su, shima maigidan muddin ranar girkina ne sai dai ya sakko kasa ya same ni a d'akina.
A tsukin suka tafi saudiya umara shi da Khalil kamar yadda ya fadi ranar dana haihu. Sati biyu suka dawo a cikin satin kuma ya sabunta mini komai na gidan tun daga kasa har zuwa sama komai sabo da sabbin kayan kicin abin dai kamar wata sabuwar amarya. Hatta da kayan da yara suke sanyawa sai da aka fitar da su aka yi musu sabbi Taburni da Mairo sune masu iyali a kauye Kuma sune masu wahala da yarab na ce su kwashe suka kuwa cika manyan bacco suka ajiye da jiran lokacin ziyara tunda sun ce sai sallah za su ganin gida yanzu muna daf da shiga wataran Ramadan kuma a watan dai za su tafi umara in sha Allahu rabbi.
Tun bayan watsewar kowa Hauwa ma ta d'auke kafarta tun ma dai washe garin ranar da muka yi walima ba ta sake shigowa ba, hakan bai wani dame ni ba dalili nasan dama abin ba d'orarre ba ne. Na ma yi mamaki sosai da ta iya jurewa a yadda na santa da tayar da fitina har aka gama wannan kacaniyar ba ta ce ga abinda aka yi mata ba.
Shi kuma daga nasa bangaran babu yabo babu fallasa ya ce muna damunsa da maganar Nabila zai fita daga harkar kowacce domin da akwai abubuwan da suke gabansa ba mu isa mu raba masa hankali ba. Da gasken ne sabgogi sun yi masa yawa domin tunda suka dawo daga umara shi da Khalil bai fiye zama a gida ba. Ya je Kano kusan sau uku a kasa da sati hud'u. Ba ma shi da lokaci sosai idan ya dawo da daddare ya ci abinci ya dinga lissafi kenan yaran ba kasafai yake zama da su sosai ba, na yi wankan tsarki tuntuni amma bai lura ba saboda abubuwan da suka sha kansa a tunaninsa har yanzu ina cikin jinin 'biki bai ta'ba nema na ba sai dai 'yan ta'be-ta'be kafin a kwanta.
Order na yi daga kano wurin GARKUWAR MATA 08089965176 package irin na masu jego na ce ta had'a mini na aminta kuma na gazgata sahihancin maganinta shiyasa ba ni shakka da shakku a ko'ina zan yi mata TALLAH da k'umaji da karsashi. Ta kuwa yi mini delivery har garin Abuja na sanya Masa'udu ya je ya kar'bo komai cikin girma da arziki nannad'e da salatif. Na durfafi gyara jikina domin bahaushe ya ce wai idan kana da kyau ka kara da wanka.
Yau da yake girkina ne baya gari ya tafi kano Amma ya ce lallai a gida zai kwana. Na yi tatul ta ko'ina kuma buk'ata na ke ji. Sosai yau kwana hamsin da shida da haihuwa na dawo Amina sosai
Ado da kwalliya na yi mai kayatarwa don an sake yi mini wani sabon lallen ma baya wanda aka yi mini na bikin suna ba. Sai yanzu na sake gazgata alfanun raba gida hankalina a kwance yake sosai a yanzu Hauwa na can gidanta ni ma ina nawa duk ta ta zame mini jiki amma wallahi watarana har mancewa nake yi da ita mussaman yanzu da muka sake yaiwata a gidan ko ta ina babu kad'aici akwai kuma fahimta mai kyau da masu aikina muna girmama juna

Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

mutuntawa tabbas da maza da yawa za su gane jin dadin da kwanciyar hankalin da yake tattare da rabawa iyali mazauni da dayawa ba a sa samu rikici da rabuwar kai ba. Khalil ne yakan d'an je gidan jefi-jefi wataran kuma idan babu makaranta ya ja 'yan uwan su je su d'an zauna mata babu kuma wata matsala da ta ta'ba faruwa dalilin zuwansu nasu domin yadda na fahimta so take itama ta ja su a jiki ta samu irin soyayyar da suke mini har sultan yanzu ya daina tsoronta da shi suke zuwa idan za su tafi hakan yana yi mini dadi sosai yaro ne Khalil amma mara mantuwa shiyasa ake cewa idan za ka yi sharri ko wani abu na rashin kyautawa kada ka yi a gaban yaro dalili baya mance abu. Yanzu da ya fara girma ya gane cewa mamansa itace matsalar gidansu gashi a aikace cikin hikima yana ta ko'karin ganin ta gyara ta dawo mutuniyar kirki tunda ba zai mance abubuwan da suka dinga faruwa ba.
A bakin yaran nake jin Ladidi suna yawan kiran sunanta sai da na tambayi yaron wacece ita yake gaya mini mai aiki ce da ta zo daga bauchi sunanta Ladidi take wasa da su tare da yi musu tatsuniya ashe kenan an kawo mata mai aiki wata'kila ma ta jima domin lokacin da ta jibgi danyen naman nan na yi ta mamakin yadda za ta yi dashi Ashe tana da mai yi mata hidima ko tare suka zo da inna Uwani Allah ne ya sani.
Sai dare ya dawo bayan ya yi wanka ya ci abinci ya bukaci ganin yara har saman suka same shi ya kuwa kasance da su na tsayin mintina talatin ana ta gaisuwa masu hawa jikinsa na yi masu tsokanarsa na yi Usaina ce me jan gemunsa tana fad'in ya yi fari furfurar ce bata iya fadi ba har tana nuna masa sabon kitson hannu da Taburni ta yi musu tana cewa." Ka ga nawa ba'ki naka kuwa fari baba ka goge ya dawo irin nawa." Tana ta jan gemun yana dariya kallonsu kawai nake yi har suka gama ya ce su sauka k'asa zai huta da suka fita d'akin ya rage mu biyu ya ce." Na ga lokacin da zan huta Amina, wallahi jikina ciwo yake mini ga shekaru ga wahalhalun rayuwa."
A takaice na ce." Sai sai shekarun amma kai yanzu har wata wahala kake Sha?"
Ya d'an harareni yana fad'in." A a ba na sha a kwance nake samun kudin tunda mafia nake yi."
Dariya maganarsa ta ba ni na yi a takaice ban ce komai ba sai kallonsa da nake yi masa
Ya yi kwafa yana cewa." Yarinyar nan Nabila nema take yi ta matsanta mini fa wai zuwa ta yi can wajan Hajiya Ayya mahaifiyar Alhaji Ahmadu akan na aureta."
Ban ce komai ba sai Ido mu je dai zuwa.
Jin ban yi magana ba ya sanya ya ja goron numfashi kafin ya furta." Ni yanzu karfina duk ya 'kare kun karar mini da shi bana ji jin zan iya ajiye mata uku a yanzu kuma kowacce tana jira na kwanta da ita ni na fara gajiya wallahi."
Duk yadda na kai ga dannewa sai dariya ta subce mini na ce." Haba kaine fa na ji kana fad'in babu abinda ya fi wannan sabga dadi a duniya kuma sai kace ka gaji."
Ya furta." Da gaske na gaji Amina duk da sunna ce mai kyau ai duk fafutukar da na dinga yi a baya wallahi ina son haihuwa ne, Ubangiji Allah Ya ba ni sai godiya yanzu ma ban ce ba ni so ba ina neman kari ina nufin abinda aka yi a baya yanzu ba za a yi ba."
Na girgiza kaina ina kallonsa kafin na ce." To sai ka ce mata me?"
"Na ce sai na yi shawara tukkuna."
Na yi 'kasa da kaina ban sake cewa masa komai ba saboda takaici wace shawara kuma ya fito fili ya gaya musu gaskiya daga ita Nabilan har wadda ta yi kamun k'afa da ita tunda babu buk'atar aurenta a ransa babu amfanin yi mata yawo da hankali.
A daran dai wani lamari ne ya kasance a tsakani na dashi mai armashi da wahalar mantawa. Soyayya bata tsufa muddin za mu had'u muka zama tamkar sabbin ma'aurata ah to me za a fasa tunda da rai da lafiyar da kuma sauran kuruciyar shima duk fadi yake yi ai yana shiga hannu ya fara makyarkyata tamkar wa !ni d'an magyaru! GARKUWAR MATA ta gama gigita lissafin attajiri sai ya dawo ustaz a daran yabo da kalaman soyayya a cikin harshen labarci ya dinga zuba a yayin da jikinsa yake tsananin neman abinda duniyar ta ginu a kai. Allah Ya sa mu dace Amin.

***
Kwana biyu haka muka dinga gwangwajewa Muna shan soyayya a kuma wannan lokacin ne dana samu dama na gaya masa bukatata kan kyautar da ya yi mini da farko ya ce a a bai ba ni don na sayar ba yanzu haka ana ko'karin sabunta takardun wajan da sunana don haka babu niyyar sayar da shi a tsarinsa.
Na yi ta ko'karin ganin na ganar da shi nufina ya ki ya ce idan ba ni so kawai na gaya masa ba zai yi mini kyauta ba kuma na canza masa tsari ba ana cigaba da gudanar da abinda ake yi a kamfanin duk abinda ya kama na shiga da fita mallakina ne.
Ganin bai amince ba sai na kyale shi. Da yaje ya yi kwana biyu a gidan Hauwa ya dawo na ce masa ina so ya ba ni rancen kudi tunda dama wanda na samu na wurin larabawan nan suna hannunsa bai sa mini cikin acct dina ba. Babu wata fargaba ya tambaye ni abinda zan yi da kudi kuma nawa nake buk'ata. Na ce miliyan hamsin.
Ya jima yana kallona kafin ya furta." Me za ki yi da su?" Da mamaki sosai a tare da shi ya yi mini tambayar."
Na ce." Kasuwancina zan kawo nan garin zan kama shaguna cikin wuse market na zuba kaya tunda yanzu raba 'kafa ake yi."
Ya ce." Yaushe za ki biya ni?"
Na ce." Mu yi a rubuce shekara uku ko hud'u, in sha Allahu rabbi zan biya ka kudinka."
Ya gyad'a kansa yana kallona kafin ya furta." Ki ce kawai na baki kudi Hajiya kai tsaye amma ai kin san babu rance a tsakaninmu ko?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Da akwai mana idan da yarda da amana ko kana ganin ba zan iya biyanka ba?"
Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Za ki iya tunda me nema ce ke amma ki bari zan yi shawara akan hakan. Zan kuma sanya miki kudinki da suke hannuna."
Na 'bata rai tare da cewa." Tunda sai ka yi shawara za ka ba ni me yasa ba za ka amince da shawarata ta farko ba abin nan ni ka ce ka bawa to me yasa ba za ka bari na yi iko da shi ba ashe kyautar ba har zuciyarka ka yi mini ba tunda ka hana ni na yi iko da shi."
Ya furta.'' Ai ni ban baki don ki sayar ba, kin ga kuwa babu wani dalili da zai sanya ki ce mini na ba ki umarnin sayarwa, amma dai yanzu tunda na ji hanzarinki ki bari na yi tunani tukkun ko an gaya mini haka ake tafiya kai tsaye komai yana buk'atar nazari da tunani."
Shiru na yi ban sake yi masa wata magana ba, muka cigaba da tafiya a haka shima bai sake tashin maganar ba ya kuma sanya mini kudina da suke hannunsa kamar yadda ya fad'a.
Ranar wata lahadi da sassafe na hau saman na same shi da yake a d'akina nake kwana wataran ya biyo ni mu kwana tare ranar da yake da ayyuka kuma ko ya biyo ni yana fita idan muka kammala uzurinmu.
Na same shi suna bidiyo call da Kamalu shigowata d'akin na ji yana fad'in." To ga tanan ma ta shigo Amina zo ga Ustaz sunan da yake kiransa da shi kenan tun lokacin da ya dawo daga makarantar horon da muka kai shi ni da Hamusu.
Na zauna cike da wani irin farinciki. Tunda ya tafi ba mu gaisa ba kusan wata uku da wani abu bana jin ma sun yi magana da Hajja don da sun yi din za ta gaya mini......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*164*
Mama ya kuke ina fatan duk kuna nan lafiya."Na kasa 'boye murnar ganinsa cikin suttura da nutsuwa tare da wata iriyar kamala ta mussaman na amsa idona a kansa. Lallai Ubangiji shine isashshe idan har mumini ya yarda da kaddara da jarabta ya kuma kar'bi abinda Allah ya wanzar a rayuwarsa tabbas hakuri da tawakallin da ya yi zai haifar masa da wani irin farinciki da murmushi na mussaman daga wajan Ubangiji.
Yana zaune yana kallonmu shima fuskarsa a sake da alama ya ji dadin ganin yanayinmu ni da yaron ya dinga murmushi bai dai tofa ma komai ba a cikin maganar da muke yi har muka kammala ya juyo kansa suka yi magana kad'an kafin mu yi sallama gabad'aya ya kashe wayar yana kallona har yanzu da murmushin a fuskarsa idonsa a kaina ya furta." Na jima ban gan ki cikin nishadi irin wannan ba Giwa, ke ko kunya ba ki ji irin ta iyaye da yaransu na fari."
Ni ma da murmushi a fuskarta nake kallonsa haka kawai sai na ji wani bala'in sonsa ya kara ninkuwa a cikin raina. Tabbas da sanya hannunsa da kuma kokarinsa tare da tasirin addu'ar da muke yi Kamalu ya kai matakin da yake a yanzu. Na hangi abubuwa da yawa a tattare da yaron kuma ni ma na yarda bayan wahala sai dad'i kamar yadda da yawa mutane ke fad'in akwai haske cikin lamarinsa ina ji a jikina yaron zai zama abin alfahari gare mu bakid'aya..
Na ce." To ai ni ba mutuniyar da ba ce, addu'a kawai fa na yi masa akwai abinda na yi na rashin kunya bayan wannan?''
Ya girgiza kansa yana kallona bai ce komai. Na kama hannuwansa a hankali na sanya idona a cikin nasa na ce." Ba ni da wata kalma da zan yi amfani da ita wajan nuna godiyata a wurinka. Ka cancanci duk wani abu a wajena na gode Allah Ya saka da alheri yadda ka tsaya mini akan yaran nan ka ke yi musu wahala da jiki da dukiyarka Ubangiji Allah saka da alheri. Yaranka Allah Ya kula da su."
Ya matse hannuna dake cikin nasa a nutse ya ce." Babu buk'atar godiya a tsakanina dake Amina ni ma ai kin yi mini alheri, kin cancanta kuma abinda ki ka haifa da wani namijin na sha gaya miki ki sa a ranki kamar da ni ki ka haifa, ni ne ubansu har yanzu kuma abinda nake ban yi domin a yi mini godiya ba ina neman aljannata ne."
Na ji idona ya ciko da ruwan hawaye kuma duk yadda na kai ga ganin na hana su zuba sai da suka kwaranyo ina so na yi magana na kasa kawai sai na fashe da kuka.
Ya kuwa ki'dime jikinsa har yana rawa ya d'an rungume ni a jikinsa yana fad'in." Menene kuma abin kuka abinda zai b'ata mini rai kenan me aka yi da za ki yi kuka Amina?"
Na kasa cewa komai saboda maganar ma da yake yi ta sake raunatar mini da zuciya na dinga yi cikin k'aramin sauti ya matse ni tsam a jikinsa yana dago fuskata tafin hannunsa yasa ya dinga goge mini fuska.
Na daure da yar rawar murya na ce." Na dai gode kuma ba zan fasa godiya ba Allah Ya saka da alheri."
Ya yi shiru bai ce komai ba sai shafa fatar hannuna yake yi ya kama hannun ya sumbuta a tsanake ya furta." Godiya za ki yi ga Allah ki kuma ajiye a ranki cewa yaranki ba za su yi maraici ba muddin ina raye.
***
To wannan ya wuce da sati uku muna zaune kalau zuwa yanzu hankalina ya d'an fara kwanciya dangane da lamarinsa da Nabila domin kuwa bayan rantsuwar da ya yi mini tun farko kan cewa ba zai aureta ba ya sake yin wata tare da jaddada mini cewa ko da Allah ya sake k'addara masa aure to ba ya tunanin zai auri mace kamar Nabila saboda a cewarsa ya hangi tarin matsaltsalu mabambamta daga wajenta.
Ranar dana kar'bi girki ya shigo da yamma anan gidana ya yi wanka ya shirya ya ce mini akwai ba'kin da ya yi yanzu zai fita zuwa guesthouse din shi..
Yana tsaka da kimtsa jikinsa Hajja ta kira ya daga suka gaisa da yake handsfree ne duk Ina ji tana tambayarmu da yara ya ce mata kowa lafiya sai na ji tana fad'in. "Ashe neman aure ka ke yi ban sani ba?"
Ya kuwa diririce ya juyo ya dube ni da sauri dalili yana da tabbacin na ji abinda ta ce tunda murya ya bud'e..
Ya nemi gefan gado ya zauna da wayar a kunnansa yana sauraranta ni ma duk Ina jin abinda take gaya masa wato Hajiya Ayya ta je har gida ta same ta maganar Nabila domin a yadda ta yi mata bayani ma tana gaya mata sun daidaita junansu amma shi ya ce mata ta d'an saurare shi sai bayan sallah sai a d'aura auran tunda daf muke da mu shiga wataran azimi.
Ya cika da mamaki ainun gabad'aya yanayinsa ya canza da b'acin rai ya shiga rantse mata da Allah kan cewa bai san da maganar ba Nabila dai tana sonsa tuntuni ya gane amma bai yi mata alkawarin aure ba, duk abinda ta je ta gayawa Hajiya Ayya karya take yi.
Hajja ta ce." To ni dai abinda ta zo ta gaya mini kenan sai nace ban sani ba don baka gaya mini ba amma zan tambayaka na ji shin da gaske ne?"
Ya girgiza kansa kamar yana gabanta ya ce." Karya take yi wallahi ban ce zan aurta ba." Ta ce." Ba ka ce zaka aureta ba amma ka san tana sonka tunda gashi ka fadi da bakinka me yasa ka biye mata har aka yi magana da kai kace za ka yi shawara idan da ni za ka yi shawara to babu yawuna ga mata nan da yawa a gari idan lallai auran zaka 'kara ba zan hana ka ba, domin na fahimci tunda aka samu akasin auranka da yarinyar nan Hajara ka ke ta kame-kame babu yawuna wajan auran Nabila kanwar Maryam domin idan ka manta ni uwarka ban manta ba. Abinda ya faru a baya ba ni fatan ya sake faruwa ba. Idan za ka yi aure ka duba nagarta da cancanta kada kyale-kyale ya rudeka ka jefa rayuwarka a masifa ka jefa jama'ar da suke kewaye da kai. Tunda zuciyar taku a haka ta ginu kuma kana ji kana da kudi za ka iya to sai ka zo nan d'ambatta a duba maka wadda ta dace wadda kuma zata zauna lafiya da iyalinka."
Ya furta.'' Babu ma buk'atar karin aure a yanzu Hajja, kuma in sha Allah yadda ki ka ce hakan za a yi dama ba ni da ra'ayin auranta a cikin raina."
Ta ce." Abinda na gayawa Hajiya Ayya kenan zan tambayeka na ji ta bakinka wata'kila duk bada'kalar da ta faru ba ta da labari shiyasa har ta iya zuwa ta same ni domin na hada jini da dangantaka da zuriar Maryam Allah Ya yi mini tsari da su."
Haka suka yi sallama ta yi masa tas! Ya kashe wayar yana kallona a hargitse ya ce." Wato duk kara da kawaicin da nake yi wa yarinyar nan ba ta duba ba take bin iyayena har tana fad'in mun tsayar da magana bayan sallah d'aurin aure ni mahaukaci ne Amina?"
Na d'aga kaina alam e amma ban ce komai.
Ya nuna kirjinsa da yatsa yana fad'in." Mahaukaci ne ni ko?"
Shiru ban ce masa komai ba dai ya d'auki wayarsa da sauri yana fad'in." Kin ga ni da idonki na goge lambar wayarta tunda bata da hankali ni me zan ci da yar banza."
Bai goge ba ya sake kallona yana cewa." Kafin na goge yana da kyau na yi mata gargadi ba ni son sakarci da shirme?"
Na ce."Tambayata kake yi?"
Ta gyad'a kansa na furta." Lokacin da ku ka yi serving lambar juna ai baka nemi shawarata ba. Me zan ce maka yanzu duk abinda za ka gaya mata domin ta kiyayeka ka sani ba sai ka nemi shawarar wani ba.
Ya ja tsaki yana fad'in." Dogon rubutun ne ba ni so ai kar'bi ki shiga Whasap din ta ki rubuta mata cewa ba na sonta babu kuma maganar aure a tsakaninmu ta nemi miji daidai da ita ta aura.
Na sanya hannu na kar'bi wayar kamar zan bi umarinsa. Whasap number dinta na shiga ya yi serving da sunanta Nabila. Nan na dinga cin karo da stickas na soyayya da gaisuwar Juma'a iri iri tare da wasu irin wasik'u da kalaman soyayya masu motsa sha'awa irin dai yadda matan bariki ke janye hankalin mazan mutane. Gasu nan birjik kuma idan ta turo yana bud'ewa ya gani amma bai mayar mata da martani ba. Maganarsu da ta d'an yi tsayi akan tallan kayanta da ta yi masa shine ya kula ta har ya yi mata rubutu a takaice ya ce da ita yana so zai saya.
Kunya da takaice suka hana ni cewa komai na yi kasa da kaina tsabar b'akinciki wasu matan dai rako wasu suka yi duniya. Babban abin b'akinciki da takaici shine ka turawa mutum sako ka tabbatar ya gani kuma yana hawa online bai baka amsa ba gobe ma ka sake tura masa saboda rashin zuciya
messages kuma irin na soyayya da nuna kulawa har da fatan alheri amma mutum ya share abin da ciwo sosai amma ita kamar kidahuma mara sanin ciwon kai ko wannan ma kora da hali ne an nuna ba a yin ki a fakaice amma kin nace su kansu wasikun da suke d'auke da zantukan soyayya masu tattare da batsa babban dalili ne da zai sanya ya k'yamaci auranta bayan

Please Login or Register in order to submit comment