Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina tambayarsa abinda aka samu namiji ne kuma gabad'aya suna cikin koshin lafiya.
Fatan alheri na yi musu gabad'aya tare da addu'ar Allah ya raya abinda aka samu. Ya kuma bada lafiyar shayarwa. Ya ji dad'i kuwa ya dinga amsawa cikin jin nishadi.
A ranar ya shirya tafiya bauchi da nufin zuwa ya je ya dawo duk a ranar tunda tafiyar jirgice. Ban damu ba tunda ba kwanana ba ne, na yi masa addu'a da fatan alheri ya tashi ya fita domin zuwa ya kintsa.

Don Allah kada ki karanta mini littafi sai kin biya ni hakkina

Sai bayan ya tafi tukkuna na shiga tunanin da na sani na kar'bi lambar wayarta a wurinsa sai na kira ta na yi mata barka tunda rantsuwar nan da na yi tana nan ba zan sake taka k'afata garin ba sai dai duk abinda za a ce an jima ba a fad'a ba, wannan duniyar idan har mutum ya ce sai ya farantawa wani rai yana tare da wahala domin kuwa wasu lukutan ma wanda kake kokarin ganin ka bashi farinciki shine na gaba gaba wajan ganin ya jefaka a masifa. Baban Saude ba irin nasihar da bai yi mini ba akan zama lafiya da abokanan zamana, na kuma d'auki nasiha da shawararsa duk wadda ta shirya zaman lafiya da ni, to ni ma a shirye nake dana zauna lafiya da ita, amma wadda take ganin ta fi karfin ta ba ni girmana na babba a cikinsu sai ta yi rayuwarta ni ma na yi tawa.
Wannan shawarar na yanke a zuciyata wani sashe yana gaya mini cewa da duniya zata zageni hakan zai sake tabbatarwa da masu zargina cewa ina hassada da ciki da haihuwar. Tunda ai tun farkon samuwar cikin an sha rigima da ni akan wani dalili.
Ni ba zuwan ne matsala ba a wajena ba, Ina gudun kallon banza da habaici shine kawai abinda nake tunani, ba na so a yi mini abinda zai hasalani na kasa jurewa na aikata abinda bai da ce ba.

To daga cewa zai je ya dawo a yini sai gashi sai da ya share kwanaki uku tukkuna kafin ya dawo sauran kwana dayan Hajiya Maryam da kwana biyuna ya yi su ne a tare da Hauwa.
Ban damu ba saboda nasan hakan da ya yi shine daidai yana da kyau itama ya zauna da ita sosai domin su tattauna abinda ya shafe su.
Da daddare ya dawo wajan goma da rabi har na kwanta ya shigo yanayin dana gan shi ya nuna mini cewa ya d'an jima da dawowa domin jallabiya ce a jikinsa. A can gidanta ya sauka zai cike mata cikon kwana dayanta.
Ya zauna gefena ni kuma na tashi zaune Ina laluben hulata data fadi na mayar kaina a nutse na gaishe shi ya amsa yana yi mini wani irin kallo. Hakan ba sabon abu ba ne a wajena domin ni kaina na kan rasa me yake kallo a jikina babu dai abinda bai sani ba, babu kuma sabon abu.
Saukar hannunsa na ji saman kirjina. Da sauri na ture ina dan hararsa. Ya sake matsowa jikina na matsa da baya
Sai ya tsaya yana kallona kafin ya gyad'a kansa kamar wadda ta yi masa mugun lefi.
Na daure tare da ce wa." Ina Hauwa da jariri suna nan lafiya?"
"Lafiyarsu." Ya fad'a yana duba wayarsa kafin ya miko mini wayar yana fad'in." Kin ga hoton jaririn."
Na kar'ba da sauri ina dubawa. Kamarsu daya wallahi, ina dariya na ce." Kamarku daya fa Baba, wannan yaron hotonka ne."
Da d'an murmushi a fuskarsa ya ce." Haka mutane suke ta fad'i Hajja tana gaisheki yaushe za ki je ne?"
Shiru na yi ban bashi amsa ba, ina ta duba hotonan yaron da yake cikin wayarsa.
Sai ya sake maimaita tambayarsa.
Ba tare da na dago kai ba na ce." Gaskiya ba zan rufe maka ba babu inda zan je."
Ya dube ni da wani irin yanayi kafin ya furta ." Akan wane dalili, mai aka yi miki?"
"Ba a yi mini komai ba." Na fad'a cikin mamakin yadda aka yi ya manta irin wulakancin da suka hadu suka yi mini har da shi. Hauwa na je garinsu cikin gidansu amma bola ta fi ni daraja suka mayar da ni abar nunawa da yi wa dariya ita da 'yar uwarta.

"Idan kuwa hakane babu wani dalilin da zai sanya ki ce ba za ki je ba Amina muddin zan bada umarni ki bi shi."
Hawaye ya ciko idona na ce ." Don Allah kada ka takura mini, ka kyaleni na ji da abinda ya dame ni, ba zan je fa domin kuwa ina da dalilina, idan kai ka manta ni ban manta ba."
Ya gyara zama yana kallona tare da cewa." Ni ban manta komai ba Amina, ki fito fili ki gaya mini abinda yake damunki ba ki zauna kina barin shi a cikin ranki ba, na lura kwana biyu nan tun kafin Haihuwar nan ba ki da walwala ina alkawarin da muka k'ulla dake?"

Hawayen dake cikin kwarmin idona ya d'igo. Na sanya hannu na goge tare da ce wa." Ai ni ban k'ulla alkawari da kai ba saboda na san ba iya cikawa za ka yi ba, kawai mu yi ta zama a haka cikin munafurtar juna."

Sai kawai ya yi sakare da baki yana kallona. Ni kuma ina ta kuka kamar wadda aka yi wa rasuwa. Gadon ya hayo sosai ya riko hannuna kafin ya ce." Munafurci na yi miki?"
Shiru na yi ban tanka masa ba. Ya ce." Ki tona mini asiri kawai ba wai ki dinga b'oyewa ba, ki gaya mini hak'kinki dana take tun zuwanmu nan, ashe duk takatsantsan din da nake akan kada wadda ta zarge ni a cikinku wato hakan bai yi miki ba, kina yi mini wani irin kallo."
Hanci na ja, na cire hannunsa da yake cikin nawa na ce." Idan zaman gaskiya da amana muke yi menene na 'boye mini matarka tana da juna biyu, ai na gane nufinka kada ka gaya mini, na ji haushi ko na yi mata hassada ko?"
Da wani irin yanayi ya furta." Wace matar tawa ce take da ciki?"
Kallonsa na yi, muka had'a ido, sai na d'auke kaina ban ce masa komai ba
Yasa hannu ya dago kaina ido cikin ido ya ce." Ki gaya mini wacece take da ciki."
Na ce."Amaryarka?"
"Ita ta gaya miki tana da juna biyu?"
Shiru na yi domin ba ni da amsar da zan bashi sai na ce masa alamar hakan na gani. Sai a lokacin ma na fara jin kunya da nauyin abinda nake yi wanda hakan zai sanya shi saurin gano cewa kawai zafin kishi ne yake damuna...
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*74*
Ya jima yana kallona jin ban bashi amsar da ya tambayeni ba sai ya gyad'a kansa a nutse ya ce." Ni ne dai mijinta Ina ganin kafin ta gayawa kowa tana da juna biyu ni za ta fara gayawa, amma tunda maganar ta fito daga bakinki tabbas nasan ba 'karya ba ne, zan je na tambayata na ji dalilin da ya sanya ta 'boye mini abina."
Ri'ke hannunsa na yi a sanyaye na ce." Kada ka tambayeta don Allah."
"Akan wane dalili?" Ya fad'a cikin wani irin yanayi. Shiru na yi ban iya ce masa komai ba. Sai ya sake maimaita tambayar da ya yi mini a karo na biyu.
Na daure cikin daburcewa na ce." Ni ma fa ba gaya mini ta yi ba kawai ina hasashene."
Ya zuba mini idonsa 'kuri yana kallo. Nauyi da kunya ya sanya na yi kasa da nawa idon. Sai ya yi murmushi.
mai sauti kafin ya ce." Momi ba ta da ciki Amina, domin kuwa da tana da shi nasan ba zata rufe mini ba zata gaya mini tunda tasan abinda nake nema ne ido rufe, daga yau ki daina yanke hukunci akan abinda ba ki da tabbas akai."
Na yi shiru ban tanka masa ba, domin kuwa ni kaina nasan ba ni da abin fad'a kuma ya fi ni gaskiya to idan ma cikin ne da ita menene abinda ya dame ni.
Kamar yasan tunanin da nake yi kenan ya matso kusa da ni sosai yana cewa." Ni zan fi so ma ki fara samun cikin Amina."
Kallonsa na yi. Sai ya daga mini kai da wani yanayi ya cigaba da cewa." Momi ta kwana biyu shakararta arba'in da uku fa, ina tsammanin idan ba tsananin rabo ba a wannan matakin za ta iya wuce haihuwa don dai tana da karamin jiki ne."
"Humm." Kawai na ce masa ina nazartarsa sanin halin maza akwai wahala, sun iya dadin baki da yaudara amma in ba haka ba yaushe zai zo ya zauna yana tsara mini magana. Shekara arba'in da uku shine ta wuce haihuwa muddin tana yin jinin al'ada bai d'auke ba za ta iya d'aukar ciki.
Fuskata ya dago da hannunsa muka kalli juna sai ya matso da bakinsa daf da nawa yana so ya sumbuta gabad'aya yanayinsa ya canza da sha'awa. Ban yarda na bashi damar da hakan ba, ya gama lalube mini jiki da hannusa ya tashi ya tafi da sanyi jiki domin ga dukkanin alamu yana cikin wani yanayi na buk'ata. Bai fito ya gaya mini ba amma ina zargin ba wata cikakkiyar gamsuwa yake samu daga wajenta ba, koda kuwa ita tana gamsuwa da shi, to ta bangaransa dai sai a hankali. Ina kuma
gane hakan ne a duk lokacin da kwana ya dawo hannuna. Yakan nuna d'oki da murnarsa.

Washe gari da safe ina nad'e a gado ya shigo mini. Yanayin yadda ya shigo a hargitse ya sanya na gane akwai matsala. Na tashi zaune da sauri ina gaishe shi. Ya amsa a gajarce kafin ya ce." Ki shirya zuwa bauchi gobe in Allah Ya kaimu."
Kallonsa na yi naga babu nishadi a tare da shi. Sai na daidaita yanayin fuskata ni ma a nutse na furta." Na gaya maka fa ba na tsammanin zan je gaskiya saboda Ina gudun wulakanci, tunda a wancan karon ni na je, to mai zai hana wannan kuma ita ta je."
"Ba na son jayayya da taurin kai fa, kada ki 'bata mini rai, baki da wata hujja anan Amina"
D'auke kaina na yi ban ce masa komai ba. Ya girgiza kansa yana fad'in." Bari na kira Baban Saude na sheda masa tunda ba za ki yi yadda nake so ba."
Cikin dauriya na ce." Na fa gaya maka irin wulakancin da ta yi mini a wancan lokacin Hajiya Saratu ce kawai ta goyi da bayana, ya za a yi ka tursasani zuwa wurin da za a tozarta ni a wulakantani"
Ya zauna kusa ni a hankali." Zuciyata ba dad'i Amina, ke ma kada ki 'bata mini rai, ki yi abinda na ce dake kin ji ko, kada ki duba kowa ki duba ni Amina."
Yadda yake magana da yanayi na damuwa shine abinda ya sanya mini kasala. Na goge ragowar hawayen da yake idona na ce." Ba na gudun zargi da zagin mutane Baba, amma ina kishin kaina, kuma wasu lukutan ba ni da juriya idan aka nemi a ci zarafina sai inda karfina ya kare ba na so na je garin mutane a yi rigima da ni."
"Na fahimceki tuntuni Amina, amma ina so ki sani wannan zai zama abin zargi da gutsiri tsoma, ba na so na ji ana zaginki, ko a fadi mummunar magana akanki, duk abinda za ki yi ki yi shi domin ni kin ji matata."
Tausayi ya ba ni sosai gabad'aya a hargitse yake ga dukkanin alamu akwai abinda yake dannewa bai fito ya fad'a ba. Ni ma kuma ba zan so na ji ba tunda tsakaninsa ne da iyalinsa.
Zan je dominsa kamar yadda ya nemi alfarma, amma ba na tunanin zan kwana don ban ga dalilin yin hakan ba.
A wannan matsayar muka tsaya na ce masa ba zan kwana ba kuma sai dai mu je tare ya ce ya amince da hakan.
To na d'auka shikkenan magana ta 'kare har ya juya zai fita sai kuma ya dawo ya sake zama a kusa da ni kawai ya zuba mini ido.
Ni ma sai na zuba masa nawa mun jima muna kallonsa juna kafin a kasalance ya furta." Ba ki gane ina da matsala ba Amina?"
Na ce." Ban gane ba, ai na d'auka matsalar muka warware yanzu."

"Ke ce matsalata."
Ya fadi haka yana bin sassan jikina da wani irin kallo. Cikin zuciyata na ce ka gama zagaye-zagayen kenan, wata'kila ma ko karyawa bai yi ba ya tashi da fitina.
A nutse na ce." Ai ba girki na ba ne?"
"Na dawo hannuki tunda yau na gama yi mata kwana biyunta, kuma haka na wanzu cikin buk'ata domin ita ba ta cika lafiya sosai ba."

A hankali na ce." Lallai to ai a haka za ta saba, ni ba zan yarda mu fara 'yar haka ba gaskiya ya kamata ta zama mai juriya, tunda ni ma da haka na horu."

"Duk da haka dai ai hallitarku ba d'aya ba ce, Amina ni fa kina saurin tayar mini da hankali motsinki kadai yakan jefa ni a wani hali balle kuma na kasance a kusa dake giwar matana, kuma zinariyar gidan Tajudeeni"

Mamaki ya kama ni jin yau wanda ake yi banbad'anci shine shi ma yau wani dalili ya sanya ya shi yana yi. Na yarda namiji a gaban mace yakan zama sahorami koda kuwa mai mulki ne mai dukiya ne ko gawurtaccen malami akwai wajan da izza da jin kai basa tasiri.
Ya sa hannu ya janyo ni ya matse a jikinsa yana kyarma yake fad'in." Jiya na dauka mutuwa zan yi Amina, da tsananin bukata na kwana ki tallafe ni masoyata."
Na ce." Ni fa ka daina gaya mini sirrinka Baba, dan gaskiya ni ma ba zan ji dad'i ba idan na ji kana gayawa wata abinda yake tsakaninmu."
Hannunsa a cikin rigata ya furta." Babu ma wanda zan gayawa, to me ki ka yi mini, ni kullum cikin sanya miki albarka nake saboda Ina tsananin gamsuwa dake gimbiyata, Allah Ya ja zamaninki."
Murmushi na yi amma ba mai sauti ba na tashi daga jikinsa. Ya bi yo ni da kallo idonsa a kankance. Na ce.'" Na ji amma gaskiya ka bari sai zuwa dare a lokacin ne ka fita daga hannunta, amma har yanzu maganar nan da muke yi da kai a cikin hakkinta ne."
Sai ya tur'bune fuska yana fad'in." Wallahi ba ki isa ba, ba zai yiwu na zauna cikin lalura saboda wani lissafi na banza ba, ita ban samu gamsuwa ba da ita ba, ke kuma kawai sai na zuba miki Ido saboda Ina jin tsoronki ko."
Shiru na yi masa. Ganin haka sai ya cire jallabiyar dake jikinsa ya ajiye da sauri zan sauka daga gadon ya riko hannuna har yana murd'ewa.
Cikin zafi na ce." Zaka targada mini hannu Baba."

Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba

Bai ce komai ba ya kwantar da ni ta karfin tsiya ya danne tare da bankare mini hannu ya rirrike da hannuwansa yana fad'in." Ku ba yara k'ananu ba ayi ta fama da ku, ki 'kwace idan kin isa, ko kin d'auka na yi tsufan da ba zan iya yi mini irin wannan danniyar ba.
Ina dariya na ce." To duk mai ya kawo haka, ka sassauta mini don Allah ka cika mini hannu ka kwalmade mini su.
Sassautawa ya yi amma bai cika ni ba, ya ce." Yadda nake ji na garau ko saurayi matashi ba abinda zai nuna mini, ke kullum idan za a neme ki, ko kina so sai kin yi jayayya haka da'biarki take Amina.
Cikin jin ciwo domin hannuna ya k'age wajan hammatata na ce." Na ji don Allah ka sakar mini hannu wannan a zabtar da ni kake yi da gangan wallahi."
Ya sake ni ya zauna gefan gadon yana kallona." Cire kayanki." Yafad'a cike da bada umarni.
Baki na zum'bura tare da juyar da kaina. Bai sake cewa komai ba sai ya sanya hannu a jikina da kansa ya tube riga da siket din material din dake jikina ya cire rigar maman ya jefar a ki'dime ya had'a ni da jikinsa ya matse yana sakin wani irin numfashi ya dinga bin ilahirin jikina da sumbata kamar zai cinyeni.

****
To kamar yadda muka tsara tafiyar abinda ya faru kenan. Mun je bauci kuma cikin ikon Allah muka dawo a ranar da muka je din. Na kuma yi mamaki kwarai da gaske da naga canji mai yawa wurin Inna Uwani da ita kanta maijegon da 'yan uwanta, sun tar'be ni sosai cikin sakin fuska da kulawa ba kamar yadda na yi tsammani ba. Inna Uwani duk ta watsar da wannan kiyayyar da take yi mini yau har tana yi mana fad'a da nasiha ni da Hauwa akan mu zauna lafiya da juna, haka zalika kuma kada mu yi zaman gaba, mu had'e kai mu zama tsintsinya madaurinki d'aya irin abubuwan da aka yi a baya kada su sake faruwa. Sosai na yi mamakin hakan. Cikin zuciyata na ce dama ai karya fure take yi bata 'ya'ya kuma duk mai gaskiya zahiri shine a sama. Abinda nake ta gudu bai faru ba, wata'kila dana biyewa zuciyata dangane da abinda ta tsara mini na shiga bakin duniya kenan na kuma zama abar kallo da tofin alatsine. Yaro tubarkalla ma sha Allahu wanda tun ranar da aka haife shi babansa ya yi masa huduba da Ibrahim Khalil sunan kakansa kenan sai uban ya ce a dinga kiransa da suna Khalil. Ya sha gata kwarai da gaske daga wajan Babanshi da abokansa kuma ni ban ji haushin duk irin hidimar da zai yi akan haihuwarsa ba, komai yana da lokaci kuma amfanin dukiyar kenan.

Ba su shirya wani gagarimin taron suna ba don maijegon tana d'an fama da ciwon kafafu da yake sun yi kumburi irin na ciki, amma suna sacewa a hankalina. Ma'aikaciyar lafiya ce ita dalilin da ya sanya ma kenan ta ce babu wani gagarimin taro da zata yi iya family dinsu ma kadai sun isa tunda suna da yawa. Hakan ma don ba yadda za ta yi ne domin wani ko ka ce masa babu suna to sai ya zo shiyasa inna Uwani ta ce dangi ba za a hana su zuwa ba, ita kuma yanayin jiki da lafiyarta baya buk'atar hayaniya saboda jininta ya d'an hau kad'an bayan haihuwar amma dai ya daidaita yadda ake bukata yanzu.
Hidima sosai ya yi musu don gaskiya ya 'batar da kudi ko ga yanayin irin mahaukatan kayan da sayawa yaron ita kanta maijegon ya saya mata sutturu sannan ya bata kud'i. Haihuwar fari ce a wajensa itama haka babu lefi a cikin dukkanin abinda ya yi..........
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*75*
Da gaske dai maleji yake yi da amaryarsa domin tun yana 'boyewa yanzu a fili yake nunawa. Ita dai macace wadda ta kware wajan iya kalamai romance amma fa a shimfida sunanta sorry raguwa ce. Wata'kila hakan kuma yana da ala'ka da rashin sabo domin kuwa kowane namiji da irin hallitarsa zata iya kasancewa tsohon mijinta ba shi da karfin sha'awa da fitina irin nasa. Shekara da shekaru ta riga ta ginu a haka, ga shekaru sun tura tana sake yin rauni gefe guda kuma ga hidindimu na yau da gobe harkokinta na kasuwanci wannan kadai ya isa ya cire mata na ci da k'ulafucin d'a namiji. Shiyasa aka ce mata suna suka tara kowace mace akwai ta inda tafi kauri akwai kuma ta inda ta gaza, wasu matan kuma duka sai ka ga Allah Ya had'a musu mazajensu suna amfanuwa dasu ta kowane sashe. Tabbas ba yabon kai ba. Ni kaina na 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ tabbatar da cewa Ubangiji ya yi mini baiwa da ba kowace mace yake yi wa irinta ba. Bai fito ya gaya mini ba a fili ba amma na tabbatar da cewa ni ce giwa kuma zinariyar zuciyarsa da kuma cikin gidansa.

***
Kwanan Hauwa arba'in da shida da Haihuwa ya zo yana gaya mini za ta dawo amma ya nake gani domin ya bari ne ta gama wanka sai ya koma legos bayan mun yanke shawara. Na ce kawai ya bari ta zo nan 'din sai mu yanke shawara a tare domin ni har yanzu ban gama aminta da tsarin da ya yi ba, tabbas idan za mu raba wata shida shida ni da Hauwa to kuwa ban ga amfanin auransa da Hajiya Maryam ba domin kuwa idan ya ce zai biye mata akan abinda take so saboda wani dalili to kuwa babu shakka akwai gyara a cikin auransu. Ba zai yiwu a ce saboda mu kad'ai ne za mu dinga d'aukar lalurarsa ba. Itama ai matarsa ce tsakani da Allah kenan ni na yarda zan d'auki wata shida idan ya so su kuma su raba wata uku uku a tsakaninsu.

Da kansa ya je bauchi domin ya d'auko Hauwa da yaronta. Tabbas idan a da can babu soyayyarta a zuciyarsa to yanzu kuwa ba za a rasa ba, ba don komai ba sai dalilin abinda ya ratsa tsakaninmu wato yaron da suke haifa a tare. Ban ji haushinsa ba dangane da duk rawar kan da yake nunawa akanta da yaronta domin kuwa na riga na tabbatar da cewa hakan sai ta faru to damuwa da bakincikin hakan zai iya haddasa mini ciwo ne don babu wani abu da zan iya hanawa, matarsa ce kuma uwar yaronsa. Babu dalili mai k'arfi zan ce masa abinda yake yi ba daidai ba ne. A wasu lukutan ma ni da kaina nake taya shi mu had'u gabad'aya mu yi ta kallon hoton yaron wanda kamaninsa ke k'ara fitowa sak kamar ya yi kaki ya tofar.
Ranar da ta dawo tare da ita ya kasance domin gidane mai yalwa wadataccen zaman mace hud'u kuma cikin sakewa babu takura balle wata ta ce an matseta.
Washe garin ranar da ta dawo da yamma muna tare falon Khalil yana hannuna muna hira da ita cikin kulawa kamar babu wata matsala da ta taba faruwa a tsakaninmu yadda na lura ma ba ta fiye so mu had'a ido ba ko magana take yi kanta a 'kasa ko tana kallon wani waje daban a haka muke yin hirar. Cikin zuciyata na godewa Allah da bai sa na cuceta a zamantakewarmu ba abinda suka yi a can baya shine yake damunta
Towol din goyansa ta d'auko mini na goya shi a bayana, cikin kankanin lokaci bacci ya d'auke shi. Ina daga tsaye ina dan jijjigashi tana gaya mini irin rigimar da ya dinga yi kafin su yi arba'in har yanzu bashin baccin da ta tara bai sake ta ba.
Maigidan ya shigo amaryarsa a bayansa ta nade jikinta da wata lafiyayyar lifaya irin ta manya. Duk shigar da za ta yi da gayu ba abin mamaki ba ne domin ko bata auran mai dukiya ita kanta hajiyar kanta ce ga uwar dukiyar da aka mutu aka bar mata da yaranta.
Fuskarta a sake ta zauna kan kujera tana dariya yayin da take kallon Hauwa tana ce wa." Maijego ina fatan ba ki yi fushi da ni ba ko?"
Hauwa ta dan yi murmushi irin wanda babu nisha'di a takaice ta furta." Ban yi ba Hajiya ai maigidan ya ce ba ki ji dad'i ba ya jikin naki?"
Ta ce." Wallahi kam a lokacin na yi ta fama da zazzabi da mura har da ciwon kai, dalilin da ya sanya kenan ban samu zuwa ba."
Ta ce." Allah Ya sawwa'ke abinda ake ta fama dashi kenan."

Na kwanto yaron fuska a sake na mik'a mata shi ta kar'ba da walwala a fuskarta. Ko ba a fad'a ba ita din macace mai masifar son yara ko ba na bata ne wallahi irin rikon da take yi

Please Login or Register in order to submit comment