Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*17*
Ya dinga kallona kafin daga bisa ni ya ce." Na rasa wace irin macece Allah ya had'a ni da zama da ita. Ana ga gabas kina ga yamma An gaya miki kishi hauka ne, mahaifinki fa mata biyu gare shi, to ni me yasa zaki ce ba zan yi ba, ko kina yi mini bakinciki na samu abinda na rasa a baya ne."
Na ce.'" Na gaya maka duk abinda za mu yi kada ka sako mahaifina a ciki, shi ka raina ko? Kwanaki ka zage shi yanzu kuma kana so ka gaya masa magana. Akan wane dalili? Na rantse da zatin Allah ba zan jure hakan ba zan d'auki mataki."
Maganata sai ta bashi dariya ya dinga yi yana kallona daga bisani ya girgiza kansa yana fad'in." Ki d'auki duk matakin da za ki d'auka, ina jiranki, a dake dai ba zan daku ba, kuma ni sharri ki ka yi mini ba ta inda na ambaci sunan mahaifinki na zage shi, yarinyar nan har yanzu ba ki san wanene Tajo ba, amma Humm!"

Kada ki karanta littafin nan ba tare da kin biya ni hakkina ba yar uwata.

Tashi na yi na fita daga d'akin domin Ina ganin zamana ba zai haifar da d'a mai Ido ba. Da daddare misalin sha daya da wani abu ya kira ni a waya don har na kwanta ma muna hira da Hadiza kad'an kad'an bacci Yana fizgata yace na same shi a samansa. Ba na so Hadiza ta gane muna fad'a dashi na tashi nasa hijabina na fita.
Yana tsaya a bakin kofa ina shiga ya murza mukulli. Na dube shi babu fara'a." Gani.'' Sai ya kamo hannuna ya ja ni muka nufi gado.
Tunda na ga taketakensa na fara janyewa domin ba na jin dad'in komai rayuwata a takure nake yin ta. Ga kuma takaicin da yake k'unsa mini.
Duk daburunsa suka kare jikinsa ya dinga kyarma, domin ya kai makura wajan bukatuwa kuma ya kasa samun hadin kaina. Duk inda ya ta'ba a jikina zan ce wayyo, ko na d'auki hannun na cillar dashi. Ya kasa sarrafa ni domin na cure wuri d'aya tamkar alkaki. Sai ga kwalla mai yawa a cikin kwarmin idonsa saura kiris ta zubo.
"Ki bari na yi ko kad'an ne a hankali zan yi na gaya miki, ba ni da wata iyalin sai ke, ki daure kada ki jefa ni a cikin matsala, Amina ke kanki kin san na yi juriya sati biyu ban nemeki ba ba na so na gwada miki karfi." Wad'annan maganganun yake furtawa jikinsa yana rawa yayin da gumi keta keto masa. Ya kai hannusa ya dora a kirjina yana shafawa. Na cire da sauri na juya masa baya. Sai yake matso ni yana shashsheka." Kashe ni kike so ki yi ko? Me na yi miki ki ke shiga hakkina, kin san bala'in da nake ciki kuwa amina."
Shiru na yi masa don har yanzu bai fara ba ni tausayi ba.
"Okey ki gaya mini nawa zan saya tunda ba zaki ba ni nayi don Allah ba, na ce ki gaya mini nawa zan siya."
A hankali na ce." Ba na siyarwa ba ne.'"
Ya riko kafadata tare da dora fuskarsa a tawa Yana cewa.'' To na ji, ki bari ko ban shiga wannan wurin ba na yi wasa da wannan kin ji ko." Ya kara kai hannunsa kirjina. Na ture shi na tashi zaune tare da matsawa can karshen gado.
Ya tashi zaune shima na kalleshi gabad'aya duk ya firgice girmansa ya fito sosai. A ki'dime ya ce." Wallahi tallahi zan gwada miki rashin Imani yanzu. Ke wace irin muguwa ce ne? me na yi miki, ko ke yarinya ce karama?"
Shiru na yi masa ban tanka ba. Sai yanzu zuciyata ta fara 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ sanyi domin ganin yadda na samu damar rama abinda ya yi mini."
Ya danna kafadata da k'arfi zai kwantar da ni. Na kuwa bude baki da k'arfi na tsala ihu! Ina fad'in." Wayyo cikina."
Ya cika ni da saurin gaske yana gyara mini cinyata data lan'kwashe. Na d'ora hannuna kan cikin ina hawaye. Shi ma ya kai hannunsa kan cikin daidai lokacin da yake ta motsi. Kusan minti biyar ya cire hannunsa. Ya lalubi gajeran wandonsa ya sanya. Ina kallonsa ya sauka daga gadon kamar mara laka a jiki ya nufi bandaki, tsaki na ja na tashi zaune.

Tunda haka ta faru a tsakaninmu bai sake nema na a shimfida, bai kuma 'kullace ni ba. Ni din ce ma na tsiri gaba dashi duk da na san ta wani gefan ya fi ni gaskiya amma ban yarda na nuna masa ba, domin zahirin gaskiya na ji ciwon zagin da ya yi mini.
Ban sake hawa samansa ba run ranar da abin ya faru sai na bari ya sauko tukkuna muke gaisawa, itama babu cikakkiyar sakewa a tsakaninmu Ita da kanta Hajjan ta fahimci akwai rashin jituwa a tsakaninmu. Wataran ta same ni a d'aki don kwana na yi ciwon mara ban kuma gayawa kowa ba ko ita Hadiza gajiya ta yi da tambayata ta rabu da ni.
Tana shigowa na yun'kura na tashi zaune Ina dan yamutsa fuskata. Ta zauna kusa da ni muna kallon juna na sake gaisheta duk da cewa da safe mun gaisa. Hadiza dake gyara kayanta a kwati itama ta sake gaisheta. Sai ta ce." Yau na ji ku shiru baku fito ba har ke Hadiza tun bayan da muka gaisa da safe na ce yau ba kwa jin hirar ne."
Hadiza ta ce." Wallahi ni na tsaya gyaran kayana ne Hajja ni ma yanzu nan nake zancen a zuciyata.
Sai ta dube ni a nutse ta furta." Ai na d'auka ko wani abin aka yi muku."

Yar dariya na yi gyara zama na ce." Hajja waye zai yi mana abu kuma, na d'an tashi da ciwon jiki ne wallahi shiyasa ban fito ba."
Cikin nazari irin na manya ta ce." Ai wannan ya zama dole tunda kina kan ga'ba, amma dai na fahimci akwai damuwa a tare dake tsakaninki da mijinki akwai matsala ko Amina?"
Girgiza kaina na yi da sauri na ce.'' Babu wata matsala Hajja me ki ka gani?"
Ta ce." Na ga abubuwa da yawa a cikin satin nan to na yi miki uzuri ne dalilin lalurar dake tare dake ni kaina ba na son abinda zai daga miki hankali."

Shiru na yi ban ce komai ba, amma maganarta kamar ta famo mini abinda yake damuna. Kwalla mai zafi ta zubo mini."
Ta dubi ni tana girgiza kanta ta ce." Maganar Hauwa tana damunki Amina, me zai sanya ki tashi hankalinki akan abinda ba ki ga an yi ba."

Na yi shiru ban ce mata komai ba, don gaskiya ina jin nauyinta sosai. To ya zan yi ne na yi kokarin ganin na danne abin a raina smma ya faskara ni kaina ban san ina da zafin kishi ba sai akan d'anta.
Ta riko hannunawana a nutse ta furta." Kada lamarin Hauwa ya daga miki hankali Amina, ni ina son tarayyarki da Tajo, kuma muddin ina raye ba zan bari ki wulakanta ba, kada ki ga Hauwa 'yar uwasa ce ki sanya a ranki cewa ko ya aureta zaki wula'kanta ko d'aya. Dake da ita duk daya kuke a wurina. Tajo ko bai auri Hauwa ba ai ba mu isa mu hana shi auran wata ba tunda Allah ne ya halasta masa, kada ki bari ya fahimci gazawarki ta wannan gefan kin ji ko."

Hawaye masu rad'adi suka fara ambaliya a fuskata kuka nake sosai domin yanzu na sake gazgata lamarin tunda gashi mahaifiyarsa tana gaya mini akwai fa auran ko mu dade ko mu jima, to ya zanyi da tsananin tashin hankalin da yake yun'kuro mini a zuciyata. dama wai haka ake kishin, ni fa tsakani da Allah ban ji kishi ko kad'an ba a lokacin da nake tare da Alhaji Muntari. Ban san yadda aka yi nake masifar tsanar na ji ana danganta shi da Hauwa ba sai duk hankalina ya tashi.
Rarrashina sosai ta yi da kalamai tausasa don ba ta fita daga d'akin ba sai da ta tabbatar na sake na daina kuka sannan ta fita da zummar yin sallar la'asar.

Hadiza ta dube ni tana tabe bakinta ta ce." Aure ko shekara ba a yi ba zai miki kishiya to ke yanzu haka za ki zauna babu wani taimako da za a yi mini. Ni fa wallahi ban yarda da Inna Uwani nan ba, gani nake kamar da sanya hannunta wurin sanya miki tsana da kiyayyar mijinki har ma da zafin zuciyar da kike ciki.

Kallonta na yi ina auna maganarta. Idan na fahimci inda ta dosa tana so na bi malamai da zummar a taimaka mini kada mijina ya yi aure ko kada na yi boranci a gidan
Ban iya ba tun farko kuma ba zan yi ba a yanzu, dama ita da Ummansu ne suke yi babu wanda bai sani ba dan shi kansa Babanmu ha'kura ya yi, ya kyale su amma ana yawan kawo masa tsegumi anga Ummansu tana binne laya a gidan tururuwa.

Na ce." Hadiza zan nemi taimakon Allah kawai, amma kada ki kara yi mini maganar na nemi taimako a wurin wani asararre me zai yi mini banda ya kara dagula mini lissafi. Kin ga a yanzu wallahi ji nake yi ina ma mutumin nan ya sake ni na huta don mugun haushinsa nake ji."
Ta ce." Kin ji ko, ai na gaya mini farrak'u ake so a yi muku shiyasa ma aka dasa miki kiyayyarsa, in banda haka menene abin kyama, ai idan ni ce nake cikin wannan daular wallahi ba zan wani damu ba don zai yi aure zan bi ta karkashin kasa ne na ruguza shirin.

Tsaki na yi, na yun'kura na tashi domin daura alwala ganin lokaci yana kurewa. Har na fito daga bandaki ba ta daina mita ba, wai mamaki take yi na ce ina so na bar gidan.
Cikin zuciyata na ce dama ke ai duniya ki ka sanya a gaba.

Ko kusa ko alama ban ta'ba kawowa cewa Inna Uwani za ta shiga tsakanina da mijina ta hanyar asiri ba. Na dai fi tunanin shi din ta yi masa asirin da zai auri 'yarta tunda na lura hakan shine burinta.

Nasiha da jan hankalin da Hajja ta yi mini sun dan taimaka wurin sassautowa ta, amma dai duk sanda zan kalleshi sai na ji zafinsa a zuciyata.
A ranar kuma don na nuna mata cewa na d'auki maganarta a gabanta na bi shi saman bayan ya shigo gidan. Hakan kuwa ya yi mata dadi sosai don a jikina na ji ta bi ni da kallo a lokacin da nake da niyyar tafiya d'akin nasa.

Tabbas da na san kunnuwa za su ji mini abinda zai daga mini hankali da ban bi shi ba. Ban ta'ba tabbatarwa da kaina namiji karin maganar nan gaskiya ne sai yau inda hausawa suke cewa namiji kanin ajali ne. Yau na gazgata domin ina shiga d'akin kunnuwa suka ji maganar da yake yi a waya mai tayar da hankali.
Yana tsaye a tsakiyar d'akin ya juya baya tunda dama kofar a bud'e ya barta dalilin ma da ya sanya kenan bai ji shigowata ba. Wayarsa yake hankalina kwance yana ta dariya kamar bashi da damuwa cikin annashuwa yake fad'in." Waye ya gaya miki ni mijin tace ne? umm! Ai ba haifi macan da zata juya ni ba Hauwa, idan kin ga na bar abu ni na so, ita kanta matata tana da alfarma ne a wurina shiyasa kuke ganin kamar ina tsoranta, ta aure ni a lokacin da kowa yake gudana, sannan ta daraja mahaifiyata a lokacin da ta nemi alfarma a wurinta. wannan abu biyun sune suke ri'ke da ita a gidana. Ina kuma jin zan iya cigaba da zama da ita dalilinsu, amma ke kanki kin san irin ra'ayina, ba kasafai na fiye son mace mai jiki ba. Ina ganin yanayinki da Samira ya kara jan hankalina gare ki Hauwa....
'
TAB! NAMIJI KENAN.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*18*
Ban ji mai ta gaya masa ba tunda ba hands free ya sanya ba. Na dai ji yana fad'in." Ok, ok babu damuwa, nawa ne kudin gyaran jikin?"
Ya yi jim kafin ya ce." Idan na yi wanka zuwa an jima zan saka miki, amma kada ki tsammaci d'aurin auranmu nan kusa kamar yadda na gaya miki, mu bari ta haihu tukkuna sai a yi komai a tsanake."
Ya sake yin jim kafin ya ce." Ok my love I miss you."
Ina tsaye har ya kammala yana juyowa muka had'a ido. ya dan razana da ganina tunda ya san na fi sati uku rabon dana tako kafata dakinsa. Cikin kankanin lokaci ya daidaita yanayinsa bai ce mini komai ba ya nufi bandaki. Na tare shi da hanzari muka tsirawa juna Ido.
Cikin zafin kishi dan har wani garara-garara nake gani a idona ce." Don girman Allah da Annabin rahama daga yau na daina cin arzikin da nake ci a gidanka sai me don ka kwance mini zani a kasuwa, ka gayawa wadda zaka aura ga yadda aka yi auranmu. Ai sun sani ita da babarta ba sai ka jadadda mata ba, baka tona mini asiri ba wallahi kanka ka tozarta ba ni ba, a yau ina gaya maka na yi nadamar wannan cikin na jikina, domin dama da dole aka yi mini."
Bai ce mini komai ba ya ratse ni zai wuce. Na ri'ko rigarsa ta baya da karfin da ni ban san ma ina dashi ba."
"Ai ba zaka burge ni ba sai ka auro kaf siraran duniya sannan za ka burge ni, kuma daga yau na daina cin arziki wata idan ka isa ka haifu ka sake ni na ce maka."

Fuzge rigarsa ya yi yana nuna ni da yatsansa." Na gaya miki ki shiga taitayinki fa, an fad'a din kina cin alfarma, ki yi abinda za ki yi."
Wasu hawaye suke keto kumatuna suka fara kasa tsare......'Abinda zaka ce kenan ko? to Allah Ya isa ban yafe ba maka."
Ya rike 'kugu kamar mace yana dubana ya furta." Da na yi me? ai idan Allah ya isa ne, ni zan yi miki, haka kawai kina nema ki jefa ni cikin matsala, idan auran ne ma ai kece ki ka asassa mini yinsa, kuma na gaji da abinda ki ke yi mini zan kira mahaifinki na gaya masa ko na kira antinki Yagana ba zan iya da bakin hali irin naki ba Amina na gaji da rarrashinki domin ni ba bawanki ba ne, haba duk ga mata nan birjik a gari ko kina ganin ba zan iya rabuwa dake ba ne?" Kasa magana na yi domin jin wani irin jiri na kokarin zubar da ni a wurin. Ya shige bandaki ya bar ni a tsaye duk dauriyar da nake yi sai da hawaye ya zuba.

Ina nan tsaye kamar dasashen itace ya fito ya same ni a inda ya barni, ya dube ni da mamaki a fuskarsa amma bai ce mini komai ba ya nufi wurin kayan shafarsa. Yana shafa mai a jikinsa amma gabad'aya hankalinsa yana kaina, ina kallon duk wani motsinsa ta gefan idona. Yanda ya nuna a shirye yake da tarar duk abinda nake ji dashi.

Ban ce masa komai ba na kad'a kaina na kama hanyar fita daga d'akin ina goge hawayen da yake zuba amma ya'ki tsayuwa idan na tuna abinda ya gayawa Hauwa akaina sai zuciyata ta d'auki zafi mai tsananin gaske. Ashe soyayyar karya yake yi mini domin ya amfana da jikina ne, babu irin kalamin soyayyar da baya yi mini idan muna kwance a bargo guda. Wai ashe akwai ranar da zata zo ya ci mini fuska a wurin matar da yake shirin aurowa.
Cikin damuwa mai yawa na sauka kasa, kuma duk yadda na so da ganin na daidaita kaina abin ya gagara domin zuciyata ta gama karyewa da mutumin nan munafiki ne na karshen, gashi ya riga ya gama da ni tunda ya d'irka mini ciki ya san dole wasu kudirorin nawa na janye su.

Hajja hankalinta ya tashi ganin yadda na sakko a hargitse ta kama ni ta zaunar kusa da ita. Lokacin zuciyata ta sake tsinkewa hawayen ya tsananta zuba a kumatuna.
Cikin damuwa ta fara tambayata abinda ya faru, gabad'aya yanayinta ya canza, sai na ji tsoron tashin ciwonta domin jikinta sai karkarwa yake yi. Ta dinga fad'a tana fad'in na gaya mata abinda ya yi mini.
Na yi kokarin tsayar da kukan da nake yi a raunane na ce. " Hajja ni ba zan hana shi aure ba, amma don Allah ki yi masa magana ya daina kwance mini zani a wurin wadda zai aura da kunnena na ji yana gaya mata cewa ina zaune a gidansa ne a matsayin alfarma, amma bana daga cikin irin kalar matan da yake da burin aura.
Hajja kin fi karfin komai a wurina a yanzu dai ko kara ki ka ajiye ki ka ce kada na tsallaka zan kiyaye saboda irin kulawa da soyayyar da kike mini, amma kalamansa suna nufin haddasa husuma tsakanina da Hauwa idan Allah ya kaddara shigowarta gidan nan, kin ga dama ya gaya mata ga yadda akayi ya aureni ai ba zata mutuntani ba tunda alfarma ya yi mini. Sannan tunda maganar auran nan ta b'ullo yake gaya mini duk maganar da yaga dama harda zagin iyaye Hajja ba zan iya jurewa ba domin iyaye sun wuce raini."

Ta dinga girgiza kanta tana fad'in." Alfarma ai ke ce ki ka yi masa Amina, kuma dole ace da mijin iya baba. Duk inda za a je kece Amina dai da ki ka aure shi a lokacin da kowacce mace ke gudun rab'ar inda yake ba don komai ba sai dan saboda matsalar da take tattare dashi.
Ke alheri ce a wurinsa shine bai sani ba da har yake fad'in wad'annan maganganun kuma wallahi muddin ya ce zai biyo ta irin wannan sigar zan rusa maganar auran gabad'aya."
Tana rufe bakinta ya sauko cikin jallabiya da wayoyinsa hannu. Ya zauna yana kallonmu wani irin yanayi a tare da shi.
Aikuwa ta rufe shi da fad'a ta inda take shiga ba ta nan take fita. " Wallahi Tajo ka kiyayi 'batawa matarka rai, kai baka da tausayi ne, baka duban abinda take d'auke shi kullum cikin daga mata hankali kake kana sanyata koke-koke. wai har kana cewa zaman alfarma take yi a gidanka. To idan har Amina zaman alfarma take yi, ni ma alfarma kake yi mini, yanzu ba ka ji kunyar yi wa yarinyar nan haka ba, kada fa ka manta tilasta mata na yi rana daya ban ta'ba ganintaba, itama bata taba ganina ba, amma saboda mai biyayya ce ta amince har ta aureka bayan duk ta san abinda yake faruwa da rayuwarka. Me yasa a lokacin da muka nemi Hauwan ta maye gurbin 'yar'uwarta taki amincewa saboda tana tsoron mutuwa, amma ita Amina ta sadaukar da rayuwarta ko ta mutu ko ta yi rai bayan tana da tarin k'udurori a rayuwarta. Tajo ba kai ka yi wa Amina alfarma ba, itace tayi maka alfarma ka ajiye hakan a cikin ranka, kuma muddin kana son mu zauna lafiya da kai ka kiyayi 'bata mata rai."

Sai da ya bari ta gama fad'an tukkuna ya sassauta murya a nutse ya ce." Hajja ku yi hakuri don Allah, amma yana da kyau ki saurari uzurina a wannan ga'bar ina da abubuwan da suke damuna game da yarinyar nan. Dalilin da ya sanya ban zo na gaya miki ba saboda naga ita din mafi soyuwa ce a wurinki, amma ai ni ma tana kwarata kwarai da gaske gashi bata da kunya wallahi, bata ganin girma da shekaruna kamar sa'anta haka take sa'insa da ni. Sannan bata ba ni kulawa ta kowane bangare, ta hana ni hakkina tsayin satika, kuma ina cikin sha'awa, duk lokacin da ki ka ga ta hau sama wajena wallahi masifa ta je nema ba kwanciyar hankali ba, ni duk yadda na so mu zauna lafiya ta'ki, yau ta ce wannan gobe ta ce wannan, ta'ki ta bari mu fahimci juna."

"Ayyo, shiyasa kenan kake sanar da Hauwa ta shigo a shirye itace matar so ko? gata 'yar uwarka, ga shi kuma kana sonta saboda tana kama da Samira, sannan siririya ce ita Amina kuma 'yar lukutan, sannan ni ce nace ka aureta, ni da ita muna cikin alfarma."

Murmushi ya d'anyi ya saci kallona. Ina ta goge hawaye don na ji dadin titsiyar da Hajjan ta yi masa, na cigaba da jan majina Ina shassheka da sake nuna raunina don kada ta yarda da abinda ya gaya mata a kaina.

Ya ce." Ni wallahi ina sonta Hajja ban ma san irin kalar son da nake mata ba, itama damar da ta samu kenan take yi mini iyashege yadda ranta yake so, ki daina fad'in tana cin alfarmar nan Hajja.".

Ta ce."To ai ba zata yi maka karya ba tunda dai da kunanta ta ji kana gayawa kishiyarta baka sonta ni na aura maka ita.
Da sauri ya ce." 'Karya take yi wallahi ni yaushe rabona ma da na yi waya da Hauwa, ni fa auranta bai wani kwanta mini a rai ba Hajja saboda k'arfafa zumuncinku da inna Uwani ya sanya har nake bibiyar maganar."

Da sauri na dube shi jin yadda yake rantsuwa da wallahi bai yi magana da Hauwa ba.
Hajjan ta ce." Oho toni dai na gaya

Please Login or Register in order to submit comment