Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abu sannan ta sake had'a kayanta a karo na biyu. Baba Tabawa da kanta ta d'auko mini takalmin da da nake amfani da shi a d'akina ta kawo mini na sanya na tashi ina fad'in.'' Ladifa alwala ai ta zama dole da fatan babu matsala ko." Tana murmushi ta ce." Babu matsala anti."
Kai tsaye d'aki na wuce na had'o mata Turaruka da sabulai.
Fitowa ta yi daidai da lokacin da ya shigo yana daga bakin kofa suna magana da yarinyar kamar sun d'an saba da juna ko da yake shi din ba ma'abocin shariya ba ne idan yau kuka hadu to zai mu'amulanceka kamar kun yi shekara da sanin juna, mutum mai sau'ki hali da nuna shi ba wani ba ne a rayuwa.
Wannan dabi'un nasa na zahiri sune suka danne ba badi'ini wanda mu da muka dangance shi kuma mafi kusa dashi yake yi mana. Amma kaf jama'a da ma'aikatansa yana mu'amulantarsu ciki sau'ki babu wata izza da nuna ni wani ne. Abinda anti Yagana take fad'a kullum kenan domin ita kanta ladabi yake yi mata ko magana suke yi baya iya had'a ido da ita wai ai yayata ce wasu lokacin har anti Yagana yake ce mata kamar yadda nake kiranta abin ya yi ta bani takaici da b'akinciki. Makirci sai kace babbakakken dan duniyar da ya gaji da yawon bariki kaf ya saye mini dangi har da Baban Saude domin sai da ya san yadda ya yi ya 'kulla abota da shi mai karfi. Amma nasan Baban Saude mutum ne mai tsinkaye da hangen nesa kuma ba zai ta'ba take gaskiya ya d'auki karya ba idan duk duk duniyar nan za a ba shi yana da taurin kai da ra'ayin rikau!

Ledar hannuna na mik'a mata ina cewa "Ki gaishe da mutan gidan, tunda kin ki kar'bar kudi ga wannan sai ki yi amfani da su, na gode kwarai."
Ta kar'ba tana godiya sosai kafin ta kama hanya ta fita cike da nutsuwa. Baba Tabawa ta wuce dakinta itama. Sai mu biyu a falon na daure na ce." Barka da shigowa."

Don girman Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

A takaice ya amsa kafin ya nemi hanyar matattakalar samansa. Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayansa. Ya shiga bandaki nasan alwala zai yi ya fito yana gyara hannun rigarsa dake tattare. Kallo daya ya yi mini ya kama hanya zai fita na ce." Idan babu damuwa Ina son magana da kai."
Bai juyo ya dube ni ba ya furta." To, bari na dawo daga massalaci." Ya fice a gaggauce.
Na samu gefan gado na zauna babu wani karsashi a tattare da ni, nasan da ban yi masa magana ba, bai zama lallai idan ya fita ya dawo ba, shigowar nan ma nasan ya yi ta ne akan dole domin sanin halin da muke ciki. Idan yana irin wannan nuk'ufurcin da d'aukewar kai wani irin damuwa nake shiga mara dad'i don ni kuma gaba damuna take yi idan na fara ma bana iyawa gwara kawai a yi fito na fito a shirya amma ba ni son kisan mummu'ke da ba'kin rai.
To ban yi tsammanin amsa min din da ya yi ta bogi ba ce sai da naga har an yi Isha'i ta shige bai dawo gidan ba ya barni zaune a inda ya bar ni ina dakon shigowarsa. Bakwai saura ya fita yanzu gashi takwas har da minti ashirin na samu kimanin awa d'aya da wani abu zaune zuru a d'akinsa.
Na tashi na sauka kasa raina a dagule haka kawai nake kasa jimirin jure shariyarsa akaina duk dauriyata gazawa nake yi, kuma da na ce ina son magana da shi zahiri ko ya dawo din wallahi ban san abinda zan ce masa ba.
Waya na d'auka na kira shi, bai yi jinkiri ba kuwa ya daga yana tambayata menene. Daburcewa na yi kafin daga bisani na daure na ce." Ka zo."
Ya ce." Akan wane dalili."
Shiru na yi ina d'an tunani sannan na ce." A lissafin da kake yi yau kwanan wanene a cikinmu?"
Kai tsaye ya ce." Kwana kamar yaya."
Na ce." Kwanan girki mana, wacece take da kai?"
Ya ce." Momi ce take da ni ma, saboda itace nagartacciya matar da take gudun fushina ita nake ganin zan iya kwanan aure da ita, domin zahiri da bad'ininta babu mugunta ko zagon kasa balle zalinci a tare da ita."
Shiru na yi maganarsa na dukan kaina. Na daure na furta." To mai kake nufi?"
"Ba na nufin komai, kawai dai ya kamata a ce na yi nesa daku dalili ban san menene a zuk'atanku ba ke da ita Hauwan mai aikawa a sayo miki maganin wankin mahaifa."
Maganar ta yi mini nauyi sosai, dama nasan abinda yake ta sa'barsa kenan. Na ce." Ai ba haka kawai ta aika a ka sayo mini maganin wankin mahaifa ba sai da dalili, idan ma kana ganin da hannunta a wannan case din to ka d'auki hakkinta wallahi."

"Ita din mutuniyar arziki ce kenan?" Ya fad'a da izgili." Na yi shiru ban bashi amsa ba domin yadda ya fadi maganar ya nuna mini cewar a fusace yake.
Jan tsakinsa na ji kafin ya datse kiran. Na cire wayar daga kunnena raina a kuntacce na tashi na shiga bandaki domin gyara jikina.
Da kyar na iya cin abinci duk kuwa da dokin sakawarar da na yi amma takaici bai barni na ci da yawa ba. Hauwa kam ko dand'ane ba ta ce ba a daran sai da Baba Tabawa ta yi mata fatan wake da manja da kifi ga uban attaruwun da ta ce a zabga mata saboda yanayin bakinta.
Sai bayan goma na dare tukkuna muka yi sallama kowa ya shiga domin ya kwanta.
Lokacin kiran Hajja ya shigo wayata can saman dirowa romat na d'auka na rage murya domin koda na shiga d'akin kallo na kunna domin idanuwana gabad'aya a soye suke da zallan b'acin rai da damuwa
Na shiga zullumi da nazari sosai a lokacin da na ga kiran Hajja domin sai nake tunanin ko ya sanar mata da wata magana ne. Yanayin yadda muka gaisa da wasa da dariya ya sanya na dan ji sanyi a raina sosai ta yi mini tambayoyi masu cike da hikima irin ta manya ni na na bata amsa cikin hikima ban yarda na sanar da ita akwai matsala ba tunda bai gaya mata ba, to fadarta daga bangarena takan iya janyo mini matsala babba......
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=L
*96*
Ta ce." Ga Yusi dai muna tare dashi anan falo duk ba mu kwanta ba, Kamulu kuma ya ce mini zai shiga cikin gari can gaba da gidanku rijiyar zaki ya ce mini idan ban manta ba an gayyace shi bude wata sabuwar makarantar islamiyya ya ce mini zai kwana a gidan Gwaggo da safe sai ya wuce can din."
Murmushi na yi a tsanake na ce." To shikkenan Hajja, Allah dai Ya saka da alheri na gode sosai, Allah Ya kara lafiya da nisan kwana."
Ta amsa da Amin Ya Allah. Kafin ta bawa yaron wayar na ji maganarsa yana fad'in." Mama barkanmu da dare.
Na ce." Barkanmu dai Yusi ya kuke?" Ya amsa da "Alhamdulillahi Mama." Shiru ya biyo bayan maganarsa. Gabad'aya tunda abin nan ya faru yaron baya sakewa da ni. Kamalu ne ma ya kira ni a waya shi ma sau daya sai ka ce wad'anda aka yi wa wata hud'uba akaina. Kai na girgiza a hankali na ce." To tunda ba ka da abin cewa sai an jima ko.".
Yana 'yar dariya ya ce." Mama kenan, na yi shiru ne ai ina sauraranki ko da abinda za ki ce mini."
Na ce." Da yake ni ce sarkin k'orafi ko?"
Shiru ya yi bai ce komai ba, amma ina jin sautin murmushinsa. Na ce." Malam kashe waya ka bawa mai ita."
Da sauri ya amsa da "To Mama." Amma ban ji ya kashe din ba, nasan jira yake yi ni na fara kashe tawa.
Murmushi kawai na yi na ajiye wayar a gefena tare da sauke ajiyar zuciya.

Washe gari kiran wayar Baban Saude ne ya tashe ni da yake jiya na jima ban yi bacci ba idona ya soye da tsabar tunani tare da neman mafita. Wannan shine dalilin da ya sanya da baccin ya kwashe ni bai ajiye ni a kusa ba domin ni kaina tunda nasan ba ni da tsarki sakin jikina na yi sosai motsin kirki ba na so na yi.
Hannu na kyarma na d'aga wayar lokaci guda idona ya yi tarmazai wani irin yanayi na shiga na fargaba kiran wayar Baban Saude a irin wannan lokacin yana da ala'ka da abubuwa da yawa. Walau mutuwa ko wata mas'alar domin kuwa nasan a cikinta muke
Muryarsa radau ya amshi gaisuwata ya dora da fad'in gani nan kan hanya domin kuwa daf nake da shigowa garin abuja.
Na ce." Baban Saude ziyara za ka kawo mana kenan, ka gaya mini abinda ka ke so ka ci yanzu da kaina ma zan shiga kicin din na yi maka.
Ya ce." Ai ba abincin gidanki na zo ci ba Amina, ni ko da me ki ka sauke ni a wajena daidai ne."
A hankali na ce." To shikkenan Baban Saude Allah Ya sauke ka lafiya."
Ya amsa da Amin a takaice kafin ya kashe waya.
Na jima cikin nazari da tunanin dalilin zuwan Baban Saude a wannan safiya haka sai kace wanda ya kwana a hanya. Ashe ni da mutumin nan ba mu isa mu kashe matsala mu binne ta ba har sai ya dangatata da iyayena.
Gaza ha'kuri na yi na daga waya na kira shi. Matarsa ce ta daga har tana kiran sunana. Da sauri na daidaita yanayina muka gaisa a tsanake kafin ta ce." Yallabai din bacci yake yi ko a tashe shi ne?"
Na ce. "A'a kada ki tashe bari idan ya tashi sai ki gaya masa na kira."
Na ji tana fad'in." Yawwa gashi nan ma ya tashi can sama sama na ji maganarsa ban fahimci mai yake cewa ba na ji tana ce wa dashi Maman Yusuf ce." Na ji shi sosai yana fad'in.'' Amina." Ta ba shi amsa da e, ita ce ya ce ta bashi wayar.
Na ji dad'i da bai nuna mata a cikin rikici muke ba. Maganarsa na ji ta daki kunnena."
"Ya aka yi?"
Zuciyata ta yi wani zullo kamar za ta faso kirjina ta fito. Kalmar ''Ya aka ayi din nan tana yi mini ciwo kwarai da aniya, bayan yasan a cikin yin muke ni da shi.
Na daure na furta." Yanzu don girman Allah Baba menene amfanin kiran Baban Saude da ka yi ashe ni da kai ba mu isa mu warware matsalarmu ba, mai ya sa har yanzu ka kasa yarda da ni."
"Ya za a yi na yarda dake Amina? ba ki d'auki hanyar ba domin kuwa duk yadda na so ganin cewa da ni dake mun zama abu daya kin ki ba ni goyon baya, 'kiri-'kiri ki ke nuna mini gadara da ikon akan yaran da ki ka haifa da namijin da ki ka fi so a duniyar nan. Na ha'kura na kyaleki duk da cewar nasan har yanzu zuciyarki na kewar wannan mutumin da ya riga ya gushe a doran duniya bayan da igiyoyin aurena a wuyanki. Tunda kin fad'a tun farkon fari soyayya ta gaskiya daya ce shi kuma ki ka bawa shiyasa ki ka fifita 'ya'yansa a kan nawa, zahirin kiyayya da rashin k'auna da kulawa kika nuna mini Amina
gashi ko kunya ba kya ji kina gwada fifiko da soyayya akan yaransa. Ni na yi ha'kilo na raba dare wataran ma da rana idan abin ya ciyo ni, na yi ta ko'karin ganin na samar da k'wayayyaina a mahaifarki kina zubarwa saboda ni din kare na bai kai tsaiko ba. Mai yasa zan yarda dake kuwa Amina. Na tabbatar da cewa Hassana da Usaina ma Ubangiji Allah ne ya nuna miki ikonsa a kansu ke kam ai tunda suka diro duniya ba ki isa ki shafe babinsu ba. Za su rayu ko da babu soyayyarki."
Kaina ne ya dinga juyawa maganganunsa na ta amsa mini kunnuwana. Na rasa wadda zan d'auka a ciki na yi nazari. Wane irin zargi ne wannan da mugun bala'in kishi. Yaya Aminu ma da ba kowan kowa ba a duniyar nan musaki mai lalura har shi za a dinga yi wa wannan mugun kishi na bala'i. Zuciyata ta ce da ni wannan shi ake kira da "Kishin kushewa."
Ban ankara ba kawai na ji kittt! ya kashe wayarsa. Na ajiye tawa a saman cinyata kana na tallafe ha'bata tare da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Da gaske shi din ya kira Baban Saude saboda yana zargin na sake zubar masa da ciki. Hawaye ne ya silalo saman kuncina, ni kam mutumin nan Ina ganin ni kadai ya tsana a cikinmu, gabad'aya ya ki bari na na huta a rayuwata.

Na kai minti goma ina nazari a cikin raina ba wai na fifita su Kamalu akan su twins ba ne. A a gane inda ya dosa a kan yaran ya sanyi ni kama kaina domin shi kusan duk rigimarsa akan su ne, idan na ce zan biye masa kamar yadda Hauwa take yin fad'a dashi akan abinda yake mana zuciyata zan sanya kunci shiyasa nake nuna masa tamkar yaran basa gabana. Amma Allah daya ne wallahi da tunaninsu nake kwana nake tashi a cikin raina, a duk lokacin kuwa da za su shigo mana nakan kasance cikin farinciki na yi ta kallonsu ina jin dadin ganinsu cikin kulawa har yanzu duk hasashe da zinden da Hauwa take akan matar ban hango wata tawaya ta cutuwa a tattare da yaranmu ba. Na farko a nutse suke shigo mana cikin tsabta. Su gaishe mu har da risinawa babu kiriniya irin ta 'kuruciya mussaman Khalil a nutse yake sosai, twins ne ma suke fad'a a tsakaninsu sai Minal da na ji uban wataran yana fad'in taurin kai ne da ita.

Cikin kasala na yi wanka ina ta nazarin hanyar da zan 'bullo da ita domin ko'karin ganin na kare kaina tunda ban san irin maganganun da ya tsarawa Baban Sauden ba, kuma ban san shi din da me yake tafe ba.
Ban yi wata kwalliyar kirki ba saboda babu nutsuwar yin hakan a tare da ni. Na gama shafa mai ina duba lallen jiya ya sake fitowa sosai ya bi fatar 'kafafu da hannuna ya kwanta abin ban sha'awa.
Zuciyata babu sukuni na fita falo muka gaisa da Baba Tabawa lokacin tara da minti takwas na safe ta kammala shirya abin kari tsaf har ta yi wanka. Na tambayeta Hauwa ta ce mini ba ta fito ba tukkuna.
D'akinta na nufa sai na sameta nad'e a cikin bargo tana bacci. Ban yi yun'kurin tashinta ba saboda nasan illar hakan na janyo kofar a hankali. Na dawo falon na zauna ina kallon Baba Tabawa daka can wurin daning tana gyarawa na ce." Baba mai aka yi ne yau."
Sai da ta d'ago ta dube ni kafin a tsanake ta ce." Kunun gyada ne sai kosai da fanke, sai na yi wa Hajiya Hauwa Indomee kuma kamar yadda ta buk'ata."
Na ce " To kawai tsiyayo mini kunun da k'osan amma ba mai yawa ba.
Ta amsa da kulawa. Na janye idona daga wurin da take zuciyata na can tunani na tsinkayi maganarta ina d'aga kaina na ganta a tsaye ta miko mini madaidaicin kofin da ta tsiyayo mini kunun kosai kuma ta ajiye mini shi a saman hannun kujerar da nake zaune .
Ban ce komai ba na sanya hannu na kar'ba sai ta zauna gefana jikinta a sanyaye.
"Na gama alamar akwai abinda yake damunki hajiya tun fitowarki na lura da hakan, ina yi muku addu'a tare da fatan Allah Ya iyakance muku wannan rikicin."
Haka kawai sai maganarta ta karya mini zuciya na ji hawaye sun cika idanuwana. Tunda nake shiga matsaltsalu na rayuwa da rikicin duniya ban ta'ba jin kewar mahaifiyata ba sai wannan karon da nake ganin karfi da dabarata sun yi rauni. Komai ya cakude mini na rasa yadda zan yi da rayuwata. A irin wannan yanayin ne ya kamata a ce na je kafadarta na d'ora kaina a kai, na yi kuka ta share mini hawaye ta kuma fahimce ni ba tare da ta kyare ni ba..
Hawaye suka tsinke mini dalili na kasa jimirin jure hana su gudana. Ina ganin kamar kukan ma zai sanya ni na ji sasaauci a cikin zuciyata. Duk da ban rayu da uwata na tsayin lokaci mai yawa ban shaku da ita ba, amma ina shiga tsananin tashin hankali da kewa a duk lokacin da na tuna cewa ba ta raye na tuna irin wahala da gwagwarmayar rayuwar da na fuskata gani a cikinta sau'ki sai daga Allahu rabbi..

Kada ki karanta littafin nan ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Anti Yagana uwa ce a makwafin Mamanmu amma bai zama tilas ta fahimce ni ba kamar yadda uwa take mayar da damuwa da kukan d'anta nata. Uwa ta kan kar'bi wahala da fad'i tashi akan dai duk rayuwar abinda ta haifa. Idan tawa tana raye a 'kalla ni ma zan ji sasaauci ta wani gefen zan je na gaya mata damuwata ta fahimci ni kuma ta ba ni shawarwari.
Cikin nashihun da Baba Tabawa take yi mini babu wadda na fahimta gabad'aya rauni ya yi mini 'kawanya na ma gagara tsayar da hawayen dake karakaina a dakalin fuskata. Daga karshe ta shi na yi ma na nufi daki rigif haka na fadi saman gado na fashe da kuka mai gunji ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Baba Tabawa hankalinta ya tashi ainun! domin biyo bayana ta yi da abin karin tana cigaba da rarrashina. Ganin halin da nake ciki ya sanya ta ajiye duk abinda yake hannunta ta tararrayoni jikina itama murya na rawa take fad'in." Amina komai ya yi tsanani maganinsa Allah don Allah kada ki karya mini zuciya da wannan kukan na ki, kowane bawa yana tattare da jarabawa, sai dai ta wannan ta fi wannan haka lamarin yake, amma ni a ganina matsalarku karama ce wadda za ku hadu ku maganceta ba tare da kowa ya ji ba, ban san ba ko bayan wadda na sani akwai wata matsalar da take damunki, don Allah ki yi shiru ki yi mini bayani ko Ina da shawarar da zan iya ba ki."
Rungumeta na yi sosai ina kuka na ce." Baba Tabawa na sare zuciyata ta yi rauni ta yi sanyin da ba za ta iya jimirin jure matsaltsalun da ta jure a can baya ba. Ni marainiya yarana ma marayu Baba Tabawa ga damuwa iri daban-daban wanda nake tare da shi shine mussababbi Baba Tabawa mutumin nan ya tsane ni, wallahi ya hana zuciyata ta huta, bala'in yau daban dana gobe, na gaji! na gaji da auransa ya zame mini karfen kafa a rayuwata."
Ta dinga girgiza kanta tana jimantawa kafin na ji saukar hannunta a kumatuna tana share mini hawaye take ce wa." Ki daina ce wa kin ga ji da ibadar Allah Amina, ba ki sani ba ko wannan itace hanyar shiga aljannarki. Ni kam sai nake ganin kamar kukan dad'i kuke yi, domin kuwa a kaso dari Ubangiji ya yi ba ku kashi tamanin, idan har an samu wani tasgaro da kalubale a cikin kashi darin nan a shawarce godiyar Allah ce za ta biyo baya. Kuna rayuwa ne anan a lullube amma Amina duniyar nan a rikice take wallahi talauci da k'akanakayi ya yi wa al'umma yawa. Matan aure zina zawarawa zina 'yan mata k'ananun yaranmu zina duk domin su ci abinci. A yanzu duk wata mata da Allah ya rufa mata asiri ta samu miji mai kula da iyali da d'aukar nauyin ci da sha da kula da lafiya, to wallahi tallahi ta yi hakuri ta zauna domin idan ta fito rayuwar da za ta fuskanta bayan auran gagarima ce. Amina mace yanzu ko tana da kudi tana kasuwanci muddin ba ta da miji abin zargi ce a wurin mutane koda kuwa tsarkakkiya ce, yanzu nan za ki ji wasu daga cikin marasa fahimta marasa hankali suna kiranta da sunan karuwa. Wannan rayuwar kin yi ta a baya Amina a lokacin duniya ta dan kwance gari bai lalace irin haka ba. Ki yi hakuri ki jure kalubalen gidan auranki in sha Allahu watarana sai labari......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan. Normal What'sapp group kuma #700 telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=L
*97*
Sosai maganganun Baba Tabawa suka sanyayyar mini da jiki. Duk abinda ta fad'a babu k'arya. Tabbas na yi gwagwarmayar rayuwa na san komai. Amma ni a irin fargabar da nake ci a yanzu sai nake ganin gwara mini zaman babu laluran miji hankalina zai fi kwanciya shin mai ake nema a cikin aure ne haihuwa to na samu. Ina da dukiyar da zan iya ri'ke kaina da yarana marayu. Allah da kansa ya ce a rabu idan abin ya ci tura, ai gabad'aya lamarin aure da maslaha ya zo domin kuwa abu ne na mutum biyu tare da yarjejeniya kafin tabbatuwarsa.
Fuskata na goge a lokacin na ji idanuwana sun tasa sosai, ba komai ne dalili ba sai irin kukan da na yi wanda na shafe tsayin shekaru rabona da yin irinsa.
Wayata dake saman madubi ta fara kara alamun shigowar kira. Da kanta da sauri ta tafi ta je ta d'auko mini ta ba ni na kar'ba ina dubawa A kunnena kawai na sa wayar kafin na bud'e baki da kyar cikin alamun cushewar murya da dashewa na ce." Na'am.''
Muryarsa babu amo ya furta." Baban Saude ya sauka tun d'azu yanzu haka muna tare da shi sashena da nake saukar ba ki."
Shiru na yi ban ce masa komai ba. Na ji yana fad'in." Ko ba kya ji ne?"
A takaice na ce." Ina ji ya za a yi yanzu to?"
"Ke muke jira?"
Ban bashi amsa ba na kashe wayata jin yadda zuciyata take wani irin harbawa, ina ganin sai mutumin nan ya kaini kasa tukkuna hankalinsa zai kwanta.
Baba Tabawa ta kwashe kayan karin kummalon tana fad'in." Sai dai a had'o miki wani don wannan ya yi sanyi.
Cike da sarkewar murya da numfashi na ce." Ki bari na dawo tukkuna na yi ba'ko daga Maiduguri d'an uwan Mamana ne ya

Please Login or Register in order to submit comment