Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna a kusa nake wata'kila kiris nake jira na fashe. Kuma haka din ne don abinda nake ji a can kasan zuciyata ni kaina ya shallake tunanina.
Ya kashe wayar tare da ajiyeta a saman cinyarsa kamar dai yadda na ajiye tawa. Sai ya d'auki gefan babban rigarsa ya d'ora a cinyata yana d'an murmushi amma bai ce komai ba.
Zumbura baki na yi tare da kawar da kaina nasa hannu na cire rigar daga jikina.
Sai ya sake mayarwa yana sake matsowa jikina. A hankali murya can kasa ya furta." 'kyan'kyamina ki ke yi Amina."
Shiru na yi ban tanka masa ba, kuma ban kalleshi shi ba. Sai ya d'auki hannuna da yake ajiye a saman cinyata ya had'e yatsunmu waje daya ya rintse can kasa da karamin sautin da ni kadai zan iya ji ya furta." Mu 'kulla alkawari." Hucin numfashin maganarsa ya sauka a gefan fuskata. Ya sake matse yatsun da k'arfi yana sauke ajiyar a zuciya ya furta." Kin ji Hajiyata."
Cikin wani irin yanayi na dube shi. Duk da idanuwansa rufe suke da gilashi hakan bai hana ni fahimtar halin da yake ciki ba.
Ban iya ce masa komai ba na janye idona daga kallonsa zuciyata na d'an yi mini zafi kad'an domin sai nake ganin kamar akwai raini a lamarinsa ai ya kamata a ce yanzu ba shi da lokacin kowa sai nawa tunda mun jima ba ma tare a ganina bai kamata ya tsaya wata mace ta kira shi koda matarsa ce din ya biye mata da zantukan soyayya ba.

Ya sake furta." Mun yi al'kawari ko Amina."
Da 'kyar na ce." Ai mun yi tun a gaban Baban Saude."
"Wani nake so mu sake yi ni dake kawai, kin ji rabin rayuwata." Na dube shi da sauri jin abinda ya furta wai rabin rayuwarsa. Lallai ban yarda ba idan har ni din rabin rayuwarsa ce ai ba zai dinga yin nesa da ni ba duk tsaurin lefin da na yi masa.
Ganin na'ki biye masa ne ya sanya ya rabu da ni, a haka muka isa kasaitaccen hotel din da sai wane da wane, yana ta tsokanata ya d'auki gefan rigarsa yasa a jikina ni kuma bana gajiya da cirewa
Na ce da Sukajiru ya shigo mini da akwatinana dole akwai abinda zan buk'ata kafin na kwanta sai na yi burush da kuma kayan baccina a ciki. Idan ya so gobe idan za mu tafi din ya kuma kai su motar tunda na tabbatar da cewar tafiyar jirgi za mu yi sai dai har yanzu ban gama tabbatar da cewa ina zai kai ni ya ajiye ba legos din ne ko Abuja.
Tunda na yi wanka na fito yake ta bina da kallo don da kyar ma ya iya tashi ya je ya yi nasa wankan ya fito babu riga a jikinsa sai dogon wandon kayan da ya cire ya zauna kusa da ni a gefan gado lokacin muna magana da Sahura ta Whasap ina gaya mata sai ta kwantar da hankalinta auran bai mutu ba ga ni ma yanzu a tare da shi a d'akin hotel.
Ganin ya zauna kusa da ni ya sanya na kashe data tare da ajiye wayar a gefe, Ina kallonsa ya d'ebi nasa wayoyin duka ukun ya kashe su, ban ce masa komai ba a hankali dai nake nazarinsa yanayinsa kadai ya gama fahimtar da ni halin da yake ciki. Ai na d'auka har yanzu da dokin amarcin a tattare dashi to mutumin da yake da amarya irin haka, ni kuwa zan d'an jarraba shi na ga ni saboda nasan babu wani dalili da zai hana shi 'kin kwanciya da ni a irin wannan yanayin da yake ciki.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*68*
Wajan ya yi tsit kowa ya yi shiru yana sauraransa. Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Tun kafin ta zo nan ta gaya mini halin da take ciki a waya da kuma ta zo ta sake jadadda mini duk abinda ya shiga tsakaninta dashi da abinda ta aikata masa da matakin da ya d'auka akanta. Dan Kuskure ta yi kuskure kuma ban goyi da bayan ta sake aikata hakan ba ko bayan raina na gargad'eta domin hakan fasadi ne mai girma. Ta kar'bi lefinta ta yi nadama ta tuba ga Allah kuma ta nemi gafara to me zai sanya ba za a yafe mata ba. Wannan sune kadai matsaltsalun Amina, kuma na ja kunanta kwarai da gaske akan ta gyara ta kiyaye a gaba. Ba wai ina goyon bayanta ba ne a yanzu ta ce ba ta da ra'ayin zama dashi cikinmu babu wanda ya isa ya yi mata dole domin kuwa ita ba yarinya ba ce ta san abinda yake mata ciwo sannan kuma tana da hujja ko a gaban alkali za ta fad'a masa dalilinta na son rabuwa da auransu saboda matsalar rashin daidaituwar jini da za a samar da yara masu ingantaciyar lafiya. Abu ne ya zo a zamanance ba mu ce za mu yi wa Allah wayo ba, amma zahiri lalurar nan akwaita dalilin da ya sanya ma kenan aka fara d'aukar matakin kare kai daga riskar abinda zai faru bayan an yi aure. Amma fa wannan bayanin nawa baya na nufin cewa ina goyuwa da bayan yahudawa ba ne a a ko daya domin kuwa ni kaina a lokacin da na auri iyalina babu gwaji na jini kuma ga yara na nan duka mun haifa lafiyarsu lau babu wani mai lalura daga ciki. Saboda haka Dada ki fahimce ni anan wannan ga'bar kada a tilastawa yarinyar nan a ce dole sai ta cigaba da zama da bawan Allan nan alhalin bai san girma da mutuncin ba."
Dada jikinta ya yi sanyi sosai duk karsashin da ta shigo dashi gidan babu shi a tare da ita a sanyaye ta ce." To yanzu na ji abinda kace Haruna, amma ya za ka yi ka hadu da mijin nata kasan dai shi ba yaro ba ne idan ma ka girme shi ba yawa kuma sannan ba irin mazajen yaranka ba ne da kasa ba yi musu tsawa da gindaya musu sharad'ai."
Dariya ya yi irin ta manya a tsanake ya furta." Ai na girme shi Dada, kuma yana auran 'yata duk kudi da wani abinda yake ji dashi ya zame masa dole ya ajiye a gefe guda kafin ya tunkaro inda nake muddin yana so mu daidaita. Ni wani kudinsa ba zai rud'a ni ba, ke kan ki kin san da wannan Dada."
Wani irin sanyi na ji ya sauka a zuciyata ta yi fes lallai Baban Saude ya shirya kare mini mutuncina.
Ya dubi anti Yagana babu fara'a ya ce." An ce yana kiranki a waya to na gargad'eki duk lokacin da ya sake kiranki akan lamarin ki ce masa ya nemi inda nake kuma ki sanar dashi daf nake da komawa wurin neman abincina domin ina sa ran a satin nan da za mu shiga asabar ko lahadi zan tafi muddin kuwa ya bari na tafi bai neme ni ba to sai na dawo kuma"

Cike da damuwa da kar'bar umarni ta ce." To shikkenan in sha Allahu don d'azu ma mun yi waya da shi har yana sake jadadda mini cewa shi bai saketa ba bayan wanda ya yi mata a baya shi kad'ai ne ya san wànda ya yi har yanzu akwai sauran igiyoyin auransa biyu a kanta."
Gyada kansa ya yi yana gyara zamansa ya ce." wannan kuma abinda ya shafe shi ne, ki yi dai yi kokarin bin umarina idan ya tuntubeki akan matsalarsa ki ce masa ya nemi inda nake domin kuwa matarsa tana hannuna."
Ta ce." To in sha Allahu rabbi."
Kwanan farinciki na yi a ranar saboda irin tsayuwar da Baban Saude ya yi akaina na ji dad'i kwarai da aniya kuma na yi masa addu'ar samun lada a wurin Allah.

***
To kwana uku a tsakani zuwansu Anti Yagana da safe ina bacci Sayyada ta shigo tana tashina wai Baban Saude yana kirana. Da zullumi na tashi na fita na wanke bakina sannan na nufi d'akinsa da yake can gefe da tsakargidan na yi sallama a nutse na shiga yana zaune da tukunyar shayi da mangal a gabansa ya gama dafa shayin yana tsiyayawa a kofi. Na sake gaisheshi duk da cewar d'azu kafin na kwanta mun gaisa. Ya amsa yana d'an motsa shayin da cokali kafin ya dube ni a tsanake ya ce." Jiya Yagana ta kira ni a waya ta gaya mini mijinki ya bu'kaci da a bashi lambata shine take neman izini na ce ta bashi babu komai to shine yanzu nan ya kira ni a waya yake gaya mini cewa yana nan tafe gobe juma'a komai dare zai shigo akan maganarku shin ya kike gani. Ni ba zan yi miki dole ba fa Amina domin kuwa ba kowane yake zaune da mutumin nan ba sai ke, idan har kin ga da 'kwara da cutarwa a ciki to ni don na ce masa ya sawwa'ke miki ba abu ne mai wahala ba a wajena. Idan kuma kin ga kina so ki cigaba da zama dashi sai a ja masa kunne tare da gargadin wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe idan har bai daina ba a gaba sai a d'auki matakin rabuwa ko yana so ko baya so tunda akwai al'kalai, shari'a kuma tana kan kowa da mai kud'i da kuma mai mulki.
Shiru na yi ina nazarin maganarsa. Babu shakka Baban Saude ya cika jarumin namiji domin kuwa abinda ya yi a yanzu ba kowanne zai iya yi ba dalili shi wanda za a titsiye din mutum ne wanda Allah Ya wadatashi da farcen susa ya kuma rataya masa taguwar arziki.

Na ce." Baban Saude idan har na rabu da auran mutumin nan duniya za ta zage ni. Sannan anti Yagana za ta 'kullece ni tunda har yanzu ta kasa fahimta. Ga 'kawata aminiyata Sahura mun samu matsala da ita duk ta dalilin haka. Zan cigaba da hakurin zama dashi muddin an nuna masa cewa abinda ya ke yi mini ba daidai ba ne, idan har ya gyara kuskuransa ni kuma na yi maka al'kawarin in sha Allahu rabbi zan yi kokari wurin ganin mun zauna lafiya, kuma zan kiyaye abinda zai sake kawo sa'bani a tsakaninmu kamar yadda ka yi mini nasiha."

Gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Ya jima yana kallona kafin ya gyada kansa a nutse ya furta." To Allah Ya yi miki albarka, ya kuma kare faruwar hakan anan gaba, sannan kuma ki yi amfani da duk shawarwarin dana d'ora ki akai, kina kallon yadda iyalina suka karanci halina tsaf to sai mu jima wata matsala bata gifta mana ba suna bina a yadda nake so, ni kuma ba na zalintarsu daidai gwargwado ina sauke hakkin kowacce. Ina so ki yi koyi dasu a dan zaman da ki ka yi tare dasu, ki d'auki darasi na zamantakewa tunda kina da abokanan zama to sai ku zama 'yan uwan juna, ku taimaka juna, ku ha'de kan yaranku waje daya, kada ku yarda wata 'baraka ta raba zumuncin yaranku a gaba za ku yi alfahari da haka. Sannan kuma kada ki kara samun ciki ki zubar wannan maganar na nanata miki ki ri'keta da kyau domin ba ke ki ke rayawa ba, haka zalika ba ke kike kashewa ba, tunda har kin yarda za ki cigaba da zama dashi a hakan to Ina yi muku fatan alheri Ubangiji Allah Ya sa har karshen rayuwarku wata matsala ba zata sake faruwa ba."
Hawaye na ji sun ciko idona saboda tsananin mutuwar jiki. Wato ana zaton wuta a ma'kera ashe Baban Saude mutumin kirki ne na gaske ban sani ba, lallai anti Yagana da mutanan da suke masa wani irin kallo sun d'auki alhakinsa domin kuwa mutum ne nagartacce mai mayar da d'an wani nasa, irin wad'annan mutanan masu tsage gaskiya da gudun abin duniya sun yi 'karanci a wannan duniyar.

Ina komawa d'aki anti Yagana ta kira ni a waya na daga tare da jin d'an faduwar gaba domin kuwa ban san dame take tafe ba. Sama sama ta amshi gaisuwa kafin ta fara gaya mini dalilin da ya sanya ta kira ni a waya. Na ce mata ai yanzu ma Baban Saude yake sanar da ni komai. Sai ta ja tsaki da alama har yanzu ciki take da ni don dai na yi mata nisa ne babu yadda za a yi ta zo inda nake ta huce fushinta saboda sanin halin maigidan , shiyasa haushina da take ji ya sake ninkuwa. Shiru na yi Ina sauraran duk maganganun da take yi uffan ban ce mata ba domin Ina iya yin magana ta ce na yi mata rashin kunya domin mu rabu lafiya duk abinda ta ce mini sai na ce to, ta kashe wayarta bayan ta gama gaggaya mini maganganun da ranta yake so da sunan jan kunne da gargadi akan zuwan da zai yi har tana cewa tasan ba ni da mutunci za a iya had'a baki da ni a wulakantashi da tozarci saboda yin hakan a wurin Baban Saude abu ne mai sau'ki dalilin da ya sanya ta kira ni kenan ta gaya mini sun yi waya dashi tun jiya kuma ya tabbatar mata da cewa da zummar sulhu zai zo.

Ajiyewar wayar na yi raina fes cikin zuciyata na ce da ke dashi dukkaninku ba kwa son gaskiya, ko yanzu ai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, na d'auka ai girman kai ba zai bar shi ya tako kafarsa ya zo ba, ai na ji dad'i mutuka da gaske da yadda Baban Saude yake da kafiya da dagiya akan ra'ayinsa. Duk da kwarjini da haibar da yake da ita ina da tabbacin hakan ba zai firgita Baban Saude ba dalili shi ma mutum ne mai ra'ayin rik'au kuma mai tattare da wadatar zucci.

Washe gari da safe bayan mun karya kummalo na koma na kwanta bacci mai nauyi ya d'aukeni ko kadan ba na tare da wata fargaba ko zullumin abinda zai faru idan ya zo garin shiyasa kwata-kwata ma ban sanya abin a raina ba don ni har so nake ma ya zo din naga yadda za ta kaya wannan shi zai nuna mini cewa yana sona da gaske ko kuwa duka karya ce da yaudara.
Sai wajan daya na rana na tashi rana gatse-gatse ina fitowa tsakar gidan da zummar wanke bakina da burushi na sami matan gidan suna ta aiki na yau na daban ne domin Sayyada na hanga a can cikin kicin ta dasa kujera tana ta suyar kaji. Mama tana gyara alayyahu ita kuma anti amarya tana tace zo'bon da yake kan wuta.......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*71*
Abinci muka ci a tare hankalinsa duk rabi yana kaina don ma ni ce karfin cin abinci. Da ga karshe sai ma ya ajiye cokalin hannunsa yana fad'in shi dan gargajiya ne bai saba da wannan ciye ciyen ba. A nutse na ce ba sai ka sanya a kawo maka abinda ka ke so ba?"
Ya yi shiru bai ce komai ba can kuma sai ya ce." Amma na ji dadin towon nan da aka sauke ni da shi a gidan kawunki Baban Saude mutumin kirki ne Amina.
Murmushi na yi kad'an amma ban ce masa komai ba.
Shiru ya dan ratsa d'akin a kafin a hankali na ji ya kira sunana. Na daga kaina na dube shi a tsanake ya furta. Da gaske fa nake da na ce miki mu d'aura alkawari."
Ina tauna abincin da ya rage a bakina na ce." Ai ban fahimci alkawarin da ka ke nufi ba.
Zamansa ya gyara babu alamun wasa a fuskarsa ya ce." Tsakanina dake babu cuta babu cutarwa duk rintsi duk wahala kada ki zauna da ni da wata zuciya ki amince da cewa ni mai 'kaunarki ne ba kuma zan cutar dake ba, wallahi tallahi Amina da wata ce ta aikata mini abinda ki ka yi mini ba na tsammanin zan sake had'a numfashina da ita. Domin ke idan ba kya ganin abinda ki ka yi a matsayin ta'addanci da yankan k'auna ni ina gani, domin kuwa abin ya jima yana yi mini ciwo a zuciya." Ya yi shiru yana kallona jin ban ce komai ba sai ya nisa ya cigaba da ce wa ."
Babu ruwana da terere da surutun mutane, ina k'ara gaya miki da wata ce bake ba sai duniya ta ji mu da ita, duk yadda na kai ga boye sirrina da rashin son yamadidi akan lamarina wannan ba zai hana ni yin hukunci ba bayan irin wanda na yi miki, to sai
Allah Ya ragewa aya za'kinta ke ce Amina wadda zuciyata take yi wa mahaukacin so. Ina sonki wannan kowanene zai shaida haka, kuma ina da burin gama rayuwata dake, ina da burin tara zuria dake koda duka za su kasance miskinai marasa mamora masu dauke da lalurar da kike kyama. Ni ina sonsu. Ya sake yin shiru na wani lokaci kafin ya cigaba da cewa." Kamar yadda Kawunki ya fad'a na sani a zaman aure dole akwai kuskure dole kuma a samu sa'bani amma ina so ki sani sonki da kaunarki ne ya sanya mini wani ciwo mai wahalar magani a zuciyata. Wannan zafin kishin da zargin da nake nunawa a kanki ba yin kaina ba ne Amina zuciyatace, na sha gaya miki ni mutum ne mai kishi da tsantsami a duk lokacin da na tuna cewa ba ni ne namiji na farko da na fara saninki a matsayin 'ya mace ba zuciyata tana yi mini wani irin ciwo wannan shine dalilin da ya sanya nake kasa sarrafa kaina, amma in bacin haka ai nasan wacece ke tun kafin aure ya ratsa tsakaninmu had'uwarmu ta farko na bijiro miki da wani lamari wanda hakan ba dabi'ata ba ce, na yi da manufar samun dace da macen aure mai tsoron Allah da gudun abin duniya. Kin fi kowa sanin ibtila'in rayuwar dana fuskanta dangane da matayen dana aura wanda da yawa mutane suka fara dora ayar tambaya a kaina. Auranki shi ya korar da wannan rud'anin ki ka yi hakuri ki karbe ni a haka da wasiwasin za ki mutu ko kuma za ki rayu. Wannan sai ya bawa sauran mata damar kawo mini hari da sunan soyayya tunda ai kin rayu tsayin shekara ba ki mutu ba. Amina in bacin Hauwa 'yar uwata ce, kuma ina gudun 'bacin zumunci da babu dalilin da zai sanya ni na aureta tunda a can baya ai guduna ta yi saboda kada ta rasa rayuwarta kamar yadda 'yar uwarta Samira ta rasa tata rayuwar. Aurena da Hajiya Maryam kuwa wannan cikasa wasiyyar abokina na yi domin a cikin abinda yake rubuce cikin wasiyyar da ya rubuta da hannunsa kafin rasuwarsa har da neman alfarmar na auri matarsa domin cigaba da kula da ita da yaransa. Alhaji Amadu ya wuce komai a wurina domin duk yadda zan fad'a miki kirkinsa sai na rage mutum ne na k'warai mai kaunata da son cigabana. Ko ni ne na riga shi tafiya ba abin mamaki ba ne don na bashi wasiyyar ya auri iyalina saboda rufin asirinmu bakid'aya. Mu zauna lafiya don Allah, ki yi hakuri da ni, zan yi hakuri dake. A yanzu ke ce uwargina da ni da sauran iyalina muna hannunki. Muddin ki ka bud'e wata kofa ta samun sa'bani a gare mu to kin kashe kanki. Sai maganata dake ta karshe kada ki sake kaini 'kara wurin kowa domin kuwa ni ba yaro ba ne, ke ba ki ji kunyar kai mutum kamata 'kara ba Amina ke ce fa ki ka yi mini lefi kuma na yi shiru ban gayawa kowa ba amma saboda k'in gaskiya sai ki tafi ki kai ni 'kara na ji ciwon hakan sosai, kuma kin ci sa'a, ina sonki da ba zan je ba wallahi zan ta barinki da igiyoyin aurena a kanki duk ranar da ki ka gaji kya dawo dakinki."

Cikin kuka na ce." Ai kai kaso hakan, mai yasa ka'ki ha'kura, ai na gaya maka gaskiya ban 'boye maka ka dalilina ba, kuma da na fahimci na yi kuskure ba 'a yi wa Allah wayo na yi nadama na ro'ki gafararsa, kaima na ce ka yafe mini, sai ka k'ullece ni, ka dinga gaba da ni, ka rufe duk wata hanyar da kasan zan hadu da kai, ta ya ya ba zan nemawa kaina mafita ba, ai Allah ma muna yi masa lefi ya yafe mana, a lokacin ya kamata ka kar'bi tubana mu sasanta junamu ta inda babu wanda ya ji ya kuma ga ni, hakan bai yi maka ba sai kawai katin d'aurin aurenka na gani, ni ma shine dalilin da ya sanya kenan na nemi iyayena domin su kira ka su ji menene matsayin aurena."

"To mai yasa ba ki sanar da mahaifinki ba har sai kin yi tafiyayyiya kin je kin gayawa wani mutum, a ganina ai mahaifinki shi ya kamata ki sanarwa da halin da ki ke ciki Amina ba wai ki d'auko maganar ki kawota har nan garin maiduguri ba."

"Shi ma ai Baban Saude ba bare ba ne, kamar yadda ya yi maka bayani uba yake a wurina. Babanmu kuma yana da kawaici sosai bai zama lallai ya iya ce maka komai ba."
Murmushi ya yi kad'an kafin ya ce." Shi wannan din da ki ka kawo masa k'arata shi bashi da kawaici kenan."
Na dube shi da wani yanayi domin maganar tasa tana nema ta d'auki wata hanya. Sai kuma da sauri ya gyara maganar da ce wa." Yana da kirki Baban Saude amma d'an tattaunawarmu na fahimci yana da wasu 'yan matsaloli ammafa ba masu muni ba ne ainun. Na dai gaya miki kada ki sake kai ni 'kara koma wajen wanene."

Na ce." To kai ma sai ka kiyaye abinda zai 'bata mini rai, ai ka dauki alkawari ni ma na d'auka. Kuma da kake cewa wasiyyar auran Hajiya Maryam aka bar maka ai ka jima kana yi mini maganarta tare da sha'awar abinda take yi wa mijinta."
Sai ya zuba mini ido da yanayi na mamaki a fuskarsa ya furta." Kada shashanci ya sanya ki sauka daga kan abinda muke tattaunawa Amina, in banda rashin hankali daga kawai na tausaya musu ita da mijinta a lokacin da yake halin ciwo sai ki canza mini magana, wato idan na fahimceki kina so ki ce da ni tun abokina yana raye nake sha'awar auranta ko ba haka ba ne."
'Dauke kaina na yi tare da d'an zumbura baki na ce." Na ga ai itama bazawarar ce mai yasa ba ka wani shiga damuwa ba, tana fita daga takaba fa ka yi gaggawar auranta, ai ko ni ban fad'i ba haka duniya za ta sanya ayar tambaya a kanka."
Fashewa ya yi da dariya yana kallona yana yi ya ce." Mijinta da ya rasu shine ya rubuta hakan a wasiyyar da ya bari, cewa daga zarar ta fita daga takaba kada na ja lokaci a daura auren. Idan ba ki yarda ba zan nuna miki takardar idan mun je gida. Sai magana ta gaba kuma Amina ai ba ni na ga Hajiya Maryam na ce ina so ba, sannan me zai sanya ni na tsananta kishi a kanta bayan nasan abokina ne ya aureta shi kadai ya yi tarayya da ita. Ba ki son sai da so ake kishi ba ne."
"To ai duk da haka itama 'yar kasuwa ce har fita

Please Login or Register in order to submit comment