Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara zuwa makarantar tukkuna watarana da daddare yake sanar da ni a takaice na ce ." Allah Ya taimaka." Daga haka ban sake magana ba. Na gyara kwanciyata ina lumshe ido.
Na ji maganarsa yana cewa." Tashi zaune ina so na yi magana dake."
Na tashi kamar yadda ya buk'ata din ban ce komai illa Ido dana zuba masa."
Ya sassauta sosai kafin ya furta." Kina ganin kamar ba a kyauta miki ba ko Amina."
Na ce." Da aka yi me?"
Ya nisa kafin a hankali ya furta." Kin san akan abinda nake magana ai."
Sai na gyada kaina a tsanake na ce." Ai kai ma kasan ba a yi mini adalci ba, ni ban iya gori akan komai ba balle akan 'ya'ya, amma itama ai ta haihu me yasa take ko'karin ta karfi sai ta raba ni da yarana. Wannan wata hanya ce da ta 'bullo da ita mai wahalar ganewa domin ni har ga Allah tunda ka auri matar nan ba zan ce maka ga abinda tayi mini na rashin kyautawa ba, idan har ma na fadi wani aibunta na yi mata sharri. Amma ta bullo da wani lamari da zai sanya mini shakku akanta ya za a yi ta k'wace mini yarana kai kuma ka dinga goyuwa da bayanta a ganinka kun yi mini adalci ko kuma dangin Babansu."
Ya yi shiru d'an wani lokaci kafin ya furta." Ki yi hakuri giwa ba wai ina goyuwa da bayanta ba ne a a Ina so na nuna mike cewa duk wanda ya nuna k'auna ga abinka kai yake so, Maryam bata da mummunan nufi akan ku balle yaranku. Ai na d'auka abinki abina ne, ban haifi yaran ba amma tunda ta tsatsonki suka fito wallahi tallahi ji nake yi kamar ni ne ubansu. Ki yi hakuri idan har hakan lefi ne, kuma kin ji hakan bai kwanta miki a rai ba yaranki za su dawo hannunki."
Yadda yake magana cikin kulawa da taushin harshe sai ya d'an ba ni tausayi kuma na tabbatar da cewa abinda ya fad'a akan yaran gaskiya ne domin ya nuna a aikace. Na goge kwallar da ta ciko idona na furta." Ai ban isa ba, idan har ka dawo mini da su za ka iya kiran Baban Saude ko anti Yagana ka gaya musu abinda ban yi ba. Ku ri'ke su kawai kai da ita Allah Ya kula mini da su."
Ya furta." Saboda ni mak'aryaci ne ko? ai magana za mu yi dake anan domin mu samu matsaya ba na so ki yi ta kallona da Maryam a matsayin masu son zuciya na ce idan hankalinki bai kwanta ba zan kawo miki yaranki kalas."
Girgiza kaina na yi tare da cewa." A a fa na bar muku wallahi Allah Ya raya su."
Ya yi shiru yana ta kallona ina goge hawayen da suka kasa tsayuwa. Sai ya matso kusa da ni yana fad'in." Maryam son yarana ne da ita Amina idan na gaya miki yadda take hidima da gidan marayu sai kin yi mamaki ko'ina hannunta yana zuwa ba zata cutar da su ba."
Hanci na ja na ce." To." Sai ya rungume ni tsam a jikinsa yana fad'in." Yi shiru Giwata daina kuka ai nasan kin yi mini sadaukarwa na gode miki Allah Ya yi mini albarka.'' Ya fad'a yana dan shafa bayana. Shiru d'akin na dan wani lokaci kafin ya ce.'' Kamalu zan yi alfahari da shi ga dukkanin alamu domin zamanshi gidan Momi ya fara wanzar da alheri koyaushe cikin koyar da 'yan uwansa hukunce-hukuncen addini yake yi, wannan dalilin ne ma ya sanya ni da ita Maryam din muka yanke shawarar kai shi makaranta ya samu takardar secondary kafin mu tura shi can makarantar da Salim yake karatu. Sannan akwai massalacin dana gina yanzu haka ma mukkulin yana hannunsa domin wancan satin aka yi addu'ar bud'e shi ko ba na gari shine zai cigaba da jan ragamar massalacin kwanaki uku kenan mun fara bin bayansa sallah."
Na daga kai ina kallonsa da sauri na ce." Kamalun kuke bi sallah guda nawa yake ?"
Sai ya yi murmushi yana fad'in." E, ai ya kai munzali kuma ya ilimantu a mu'amula da aikinsa sannan ya balaga uwa uba ya fi da yawa wad'anda suka bin bayansa a sallah ilimi da sanin al'kur'ani yaron da yake da haddar izzu sittin a kansa a malami ne, ko dai kin raina ilimin nasa ne?"
Na girgiza kaina a hankali na ce." Ban raina ba smma abin ne da ban mamaki gaskiya."
Ya ce.'' babu mamaki da ikon Allah Amina ki godewa Allah kawai amma yaron nan ya samu horo kwarai wannan dalilin ma ya sanya ni jin sha'awar taimakawa makarantar iyakacin bakin kokarina."
Na yi shiru ban ce komai ba cikin zuciyata dai ina ta tasbihi ga Allah. (Kalubale ga iyaye mussaman wad'anda yaransu suka taso da fitina kada bakinku ya saba da zagin yaro ko aibata shi da jifansa da kalmomi masu muni. Lallai Allah yakan jarrabi bawa ta hanyar da yaso yakan kuma sanya farinciki da yaye damuwa ta duka hanyar da ya so. Ubangiji Allah Ya shirya mana zuria.)

To tun bayan rarrashin da ya yi mini akan lamarin da ya sake kutso mini na d'an samu sasaauci a cikin raina. Na sake samun kwanciyar hankali kwarai a koyaushe idan Kamalu ya shigo mini cikin tsafta da kamala tare da nutsuwa babu wata damuwa ko kaidaici a tare da shi.Sai dai bangaran Hauwa kam kadaran-kadahan bata ce komai ba amma ko hirar Momi a ke yi a gidan har a gama uffan ba za ta ce ba sai dai ta yi ta jan tsaki. Itama ya d'auke mata Khalil ya mayar da shi can ta dai daure ba ta yi bore ba ban dai sani ba ko sun haura ita dashi kafin faruwar hakan. Twins ne kawai a gidan muke tare da su tunda suna bakin nono. Su din ma wasu lukutan sukan jima a gidan har sai sun bukaci nono tukkuna za a dawo mini su.
**
Haka ni da ita muka cigaba da safara ba mu Legos ba mu abuja muna raba wattani shida ita kuma Momin tana Abuja tare da yaran domin koda na yaye twins ma gidanta suka koma gabad'aya domin nan ne ya zama matattara ta yara, kuma sun yi bala'in sabo da ita da masu aikinta..

Bayan shakara biyu. Hauwa tana da yara biyu Khalil da mai sunana domin tun ranar da ta haihu uban ya yi mata huduba da Amina sai muke kiranta da Minal.

Ni ma nake samun wani cikin bisa tsautsayi da kaddara ya fita sakamakon wani mugun zazzabi da na yi mai zafin gaske lokacin duka bai fi sati shida ba. amma cikin ikon Allah fitar cikin da wata daya na sake samun wani lokacin ina tare dashi a legos. Sai ya ce sai na koma abuja Hauwa ta zo. Dana tambaye shi dalili kawai sai ya ce a gidan Baby Aish ta rasu haka zalika ma a gidan na samu matsalar ciwo mai zafi har cikinsa ya zube hankalinsa bai kwanta ba. Maganar ma sai ta ba ni dariya amma na daure ban yi ba, saboda Ina gudun ya mayar da abin rigima ina dai ta nazari akan tunaninsa kamar akwai rashin tauhidi a ciki, baby Aish ga abinda ya assasa mutuwarta. Ciki kuma da na samu ya zube wannan kuma ni dashi ba zamu taba cewa ga musababi ba, iko ne na Allah, kuma a dai gidan ai na samu cikinsu Hassana da Husaina gashi duka watanmu hud'u da zuwa ya Hauwa za ta d'auki lamarin tunda gaskiya yanzu muna zama na fahimtar juna. Ya ce da kansa zai yi mata bayani dalilinsa. Jin haka ya sanya na ce masa ba azanci ba ne yin hakan, kenan ita ba mutum ba ce, idan har yana zargin gidansa da matsala sai ya canza ba zai yiwu a ce saboda na samu ciki har ya samu matsala ya ce daga gidan ne idan ba rikici da neman tashin hankali ba. Ya ce itama tana samun wani cikin sai ta dawo.
Ganin ya'ki fahimtata ya sanya na k'yale shi domin kuwa ko bayan hali akwai girma da nauyin shekaru da suka fara turawa, yanzu nan sai ya rikice mana.

Aka yi sa'a, Hauwa ba ta yi gardama ba. kwananmu biyar da dawowa abuja suka juya tare dashi. Dama Khalil tuntuni ya bar hannunta da Minal kawai ta tafi tunda tana shan mama. Bata yaye ta ba tukkuna.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*80*
Ni da baba Tabawa muka cigaba da zama a gidan. Sa'i da lokaci yaran shigo mussaman a ranakun da babu makaranta su d'an yi mana yini kafin su koma. Na cigaba da rainon cikin da yake mugun ba ni wahala duk na k'okale laulayi ya tisani a gaba. Don ma gidan babu wata hidima da yawa ni kuma wani lokacin ba abinci nake iya ci ba. Baba Tabawa itace ke hidimar yi musu abinci da masu gadin gidan da Masa'udu direbanmu na nan.
Nakan zauna na yi ta mamakin yadda baiwar Allan nan ta had'a kan yara wanda ta haifa da wanda bata haifa ba ta ri'ke duka. Irin rikon da take yi wa yaran nan ko ni uwarsu albarka yadda zuciyata take raya mini mummunan nufi akan abinda take yi ba tsakani da Allah ba ne na'ki aminta, domin babu wata alama ta mugunta da ta ta'ba nunawa akan yaran wanda zan gazgata hasashen zuciyata.
Na kan zauna na yi ta tunani akan hakan wataran har na share hawaye idan zuciyata na kissima mini zarginta. To me ta yi mini idan ba alheri ba, muddin na cika 'yar halak kuwa duk irin abinda zuciyata ke raya mini akanta na yi tsalle na dire na ce ba haka ba ne. Amma wani abin mamaki a wasu lukutan sai na dinga jin mugun haushinta da kishi mai tsanani mussaman idan na tuna yadda maigidan yake bada muhimmanci kwarai da gaske akan abinda ya shafeta.
Ni dalilin alherinta a gare ni nakan kawar da kaina na mayar da komai ba komai ba ne, amma Hauwa kuwa ba ta iyawa sun sha yin fad'a akanta don bata iya jurewa ba. Wasu lukutan ni nake shiga tsakani na nuna masa cewa duk sanda zai yabi matarsa ya daina yi a gabanmu zuciya bata da k'ashi. Amma ya'ki dainawa. Hauwa ba ta fi ni jin takaicin abinda yake yi ba, kawai ina daurewa ne, kuma ba ta fini kishinsa ba. Idan har muka ce zamu hade mata kai mu biyu abin ba zai yi kyau ba, shiyasa dai nake ta jurewa. Amma na soma yarda da maganar da kullum take gaya mini cewa duk abinda take yi akan yaranmu ba tsakani da Allah ba ne. Shi kansa maigidan ta d'aure shi, kuma baya ta'ba zuwa ya gaya mana ta yi masa lefi duk kuwa da cewar suna samun matsala mussaman ta fannin auratayya ni ina ganewa.

***
Dawowar Salim daga karatu abubuwa suka fara lalacewa. Shine yaronta na biyu bayan Nusaiba itace babba sau daya kacal ta ta'ba shigo wa ta gaishemu, Shima kamar an yi mata dole Shekara daya da wani abu yanzu bata sake shigowa ba duk kuwa da cewa tana yawan ziyartar uwar akai-akai, sa'i da lokaci idan ta zo su Yusi sukan shigo da yaronta, amma dai ita kam ba ta da fuska da fara'a, irin na Mamanta.

Kwana biyu da dawowar yaron muna zaune ni da Baba Tabawa a falo muna hira, gefe kuma muna d'an ta'ba kallo a tibi da yake Baba Tabawa ma'abociyar son kallo ce dalilin da ya sanya ma kenan wasan kwaikwayon dadin kowa baya shigeta. Yanzu ma shi tashar arewa24 din suke haskawa. Kamalu ya shigo tsaf dashi cikin Pakistani da yake ire iren kayan da uwar rikon nasu ke sayarwa kenan, duk rabi kayan ma da suke sanyawa irinsu ne da jallabiyoyi wattanin bayane ma na ga ta yi musu sabbin 'dinkunan shaddodi da yadika. Sune sanye a jikinsa kansa da farar hula mai raga. Tun da ya shigo nake nazartarsa. Yana zama a gefena k'amshin turaransa ya kama mini hanci. Na zuba masa ido Ina kallo ban ce komai ba.
Ya dube ni a nutse kafin ya ce." Mama mun yini lafiya?"
Na amsa da "Lafiya lau ina Momin?''
A takaice ya furta." Na bar ta a gida, lafiyarta lau."
Ya dubi Baba Tabawa da take ta tsokanarsa da yake da sheik take kiransa irin yadda taji maigidan na kiransa. Itama Momin hakan take ce masa. Ya yi 'yar dariya yana gaisheta ta amsa tana fad'in." Mai zaka ci anan din duk da nasan dai Momi ba za ta barka malami da yunwa ba."
Ya ta'ba cikinsa yana dariya ya ce." Aikuwa kamar kin sani wallahi tare ma muka ci abincin rana a koshe nake. Amma da daddare dai zan ci kwad'on zogale."
Ta ce." Idan wannan ne ai mai sau'ki ne, zan yi maka in sha Allahu."
Ya ce." Na gode Baba."
Daga haka sai ya shiru bai sake magana ba, ya fito da sabuwar wayarsa Samsung da Momin nasu ta saya masa ya fara dubawa fuskarsa babu walwala.

Shiru falon ya yi. Daga ni sai shi domin Baba Tabawa ta shiga kicin domin dora sanwar dare. Kamalu tun yana yaro yake da wani irin hali na bakar zuciya da fushi. Wannan dabi'unsa ne raunanarsu kuwa yana da ala'ka da tafiyarsa karatu da kuma shekarun girma. Amma ba haushe ya ce idan ka jima ba ka ga mutum ba, to duk ranar da kuka hadu ka tambayeshi halinsa. Ni na haifi abina nasan halinsa ciki da waje. Yana da mu'amula ga wanda ya so su yi mu'amular. Amma baya jurar wulakanci a ko'ina ne, akan hakan suka dinga fad'a da Turmizi a can baya.
Duk da har yanzu bai fad'a mini abinda yake damunsa ba, ni da kaina na karanci damuwa mai yawa a tattare da shi. Amma ba zan ce masa uffan ba har sai ya magantu tukkuna."

"Mama ina ta kiran Lambar wayar Baba Hamusu bata shiga tun safe fa." Ya fad'i maganar yayin da yake kallona da wani irin yanayi.
Na ce." Wata'kila network ne, amma Hamusu ai baya kashe wayarsa, ko jiya da yamma mun gaisa."
A sanyaye ya ce." Ina tsammanin hakan."

"Neman me kake yi masa ne?'' Na fad'a idona a tsaye a kansa. Bai dube ni ba ya furta." Ina son zuwa kano din ne na kwana biyu a wurinsa" Na ce." To ka gayawa Baban?" Ina nufin maigidan.
Ya gyada kansa a nutse ya ce." E jiya naso na sanar masa kuma sai na manta, kuma mun yi waya fa, amma dai zan gaya masa ina jin tsoron ya ce a a ne Mama."

"Ka dai gaya masa mu ji mai zai ce, itafa Momin taku?'' ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce." Mun yi maganar dazu har ta fara had'a mini tsaraba."
Shiru na yi kawai ina kallonsa. Har yanzu yanayinsa bai canza ba. Na ce." Kaga ka gaya mini dalilin da zai sanya ka zuwa kano ina tsammanin ai baku wani jima da zuwa ba ko ba haka ba ne?"
Shiru ya yi bai ce komai ba sai da na sake maimaita maganarta sannan ya ce." Eh kafin tafiyarku legos ke da Baba muka je wata shida kenan yanzu. Mama ba na tsammanin zan cigaba da zama anan, can wurin Baba Hamusu zan koma?"

"Akan wane dalili?'' Na fad'a ina kallonsa. Wannan maganar za ta iya janyo rikici a gidan, ta kuma janyo mana b'acin rai ni da shi, abinda maigidan ya tsana kenan. Ya dai yarda dai ya sanya akai su su yi kwana biyu gidan Gwaggo kwana biyu gidan Hajja a dawo dasu wajan matarsa. Ni kuma ba ni da damar magana ko da ta maslaha ce sai ya juyata ya yi ta neman rigima yana fad'in don ba shi ya haifesu ba zan nuna masa iyaka, zan nuna masa bai iya ba, duk yadda zan yi masa misali ba zai gane ni ba, karshe ma sai ya ce zai kira Baban Saude dole nake jan bakina na yi shiru na kyale shi.

Gudun aure paid book ne kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba


"Mama ba zan rufe miki ba, tunda Salim ya dawo daga karatu yake yi mini wasu abubuwa na rashin kyautawa da nuna k'yama. Ba zai ci abinci tare da ni ba, ba zai kwanta d'akin da nake ba, haka zalika a cikin kwana biyun nan baya bina jam'in sallah a massalaci, ina kallonsa ya ke tafiya wani massalacin na daban. Ban san menene dalili ba, Mama amma kuma baya nunawa Yusi k'yama, wannan dalilin ya sanya ni yanke shawarar barin gidan gabad'aya domin ba na so watarana na kasa jurewa muddin a haka zamu dinga tafiya dashi babu kyakykyawar ala'ka, babu musabaha da girmama juna sai k'yama, zuciyata ba zata iya jurewa ba, Ina jin tsoron mu yi fad'a hakan ya ta'ba zumuncinku da zamantakewarku. Kin ga Momi babu komai a tsakanina da ita sai alheri Ina sonta sosai wallahi irin yadda nake sonki Mama, amma ba na so mu yi abinda duka zai bata muku rai shine dalilana."

Nasan dama ruwa baya tsami banza. Amma kuma sanin da na yi wa yaron a baya kafin ya tafi karatun ba haka yake ba. Yaro ne mai nutsuwa da son mutane irin d'an uwansa Adam ga barkwanci. Nusaiban dai ce mara fuska.
Na daure ban nuna b'acin raina a fili ba na ce." Kenan ba ku taba magana ba tunda ya dawo?"
Ya ce." Idan na mik'a masa hannu domin musabaha baya kar'ba. D'azu da safe a gaban Momi ya y hakan ya 'bata mata rai sosai ta yi masa fad'a. Shine ya tashi ya fita bai dawo ba har na fito, wallahi mama kada ki so ki ga yadda hankalinta ya tashi, shine take cewa kada na gaya miki."
Shiru na yi ina nazarin al'amarin. Kamalu bai yi lefi ba domin kuwa anan ya yi aiki da hankali da kuma iliminsa. Na kuma ji dad'in abinda ya yi da har ya iya danne zuciyarsa bai biye masa ba. Shawarar da ya yanke itace mafita muddin kuwa ana son zaman lafiya. Idan har Salim bai gane abinda yake yi kuskure ba ne, to babu mamaki wataran gagarimar matsala ta faru tunda ni nasan wanene Kamalu a fagen zuciya.
Amma yadda zan yi na sanar da maigidan halin da ake ciki shine matsalata. Na riga nasan rikice ne akwance domin kuwa baya d'aukar abinda ya shafi matarsa da wasa. Maganarsa daya amanarsa ce 'ya'yanta ma amana ne, a wannan ga'bar kuwa ya zame masa dole ya bincika domin tabbatar da gaskiyar abinda yake faruwa ya kuma gyara matsalar kafin ta yi nisa.

Na ce." Abinda za a yi yanzu shine ka d'an daure kad'an, ai ni ka burgeni sosai da har ka yi irin wannan tunanin wannan ya sake nuna mini cewa Kamaluna ya bambamta sosai da wanda na sani a baya. Ka cigaba da yi masa magana kada ka biye masa ni kuma zan yi magana da Baban nasan dai haka kawai ai ba zaka kirkiri karya don jin dadi ka gaya mini ba ko?''
"Wallahi Mama babu karya cikin maganata gaskiyar abinda yake faruwa na gaya miki, menene ribata idan na yi k'aryar kuma me ya yi mini da zan 'bata shi."
Na ce." To kada nunawa Momi damuwarka a fuska ka daure ka ji ko."
Ya ce." In sha Allah Mama.
Daga haka sai muka bar maganar muka shiga wata ina d'an jansa da wasa duk domin ganin ya manta abinda yake damunsa. Amma zahiri ni a can 'kasan zuciyata cike nake da fargabar yadda zan tunkari maigidan da maganar. Wala'ala ya fahimceni, wala'ala kuma ya juya mini manufa, amma dai tun yanzu ya kamata a ce ayi wa tufkar hanci kafin lamarin ya yi tsamari rayuka su zo suna 'baci.
Daf da magriba ya tashi ya fita da zummar shirin shiga massalaci.

Bayan kwana biyu ina cikin nazari domin har yanzu na kasa tsayar da abinda nake ganin shine daidai. Ba na so na yi magana ne a ce na goyi da bayan yarona wata'kila shi kansa zai iya ganin haka shiyasa hankalina bai kwanta ba har yanzu sai dai na gaza daurewa na sanar da Baba Tabawa abinda yake faruwa domin kuwa macace mai tsinkaye da nisan tunani.
Ta jima tana jimantawa kafin ta ce." Ai shurun ba shine mafita ba, gwara ki gaya masa tunda shine jagoran kowa a gidan ya yi wa tufkar hanci kada lamari ya yi k'wari hatsaniya ta tashi ya ce mai yasa ba a gaya masa ba. Ina ganin duk wanda zai ce kin so kanki da zummar kawo gyara to ya zalinceki domin kuwa abinda ki ka yi shine daidai, ai ba ki za'bi Kamalu kin fifita akan Salim ba, duka naki ne kamar yadda itama Momin take nunawa, to ya kamata a ce wannan 'barakar da take ko'karin kunnowa an yi maganinta.

Ajiyar zuciya na sauke bayan duk na gama sauraran maganganunta. Na ce." Shikkenan Baba, in sha Allah zan sanar da shi halin da ake ciki duk kuma yadda muka yi aki ji."
Ta ce." To shikkenan, Allah Ya maganta."
To daddare ina d'aki a kwance misalin takwas da rabi ya shigo mini cikin tsananin b'acin rai. Na tashi zaune da sauri gabana na fad'uwa. Ya zauna samar kujerar madubi na ce." Kai lafiya Kamalu."
"Mama barka da dare." Da abinda ya fara kenan. Na amsa a takaice na ce." Menene?"
Duk dauriyarsa sai da muryarsa ta yi rawa ya ce." Mama ba zan iya ba, ba zan iya jurewa ba, zan tafi kano gobe domin kuwa Salim baya neman zaman lafiya da ni."
"Mai ya yi maka kuma?" Na tambayeshi jikina sanyi kalau domin kuwa wani yanayi na shiga na tsananin tausayin yaron ba komai ne ya janyo masa hakan ba sai maraici da rashi domin kuwa duk abinda Salim yake yi yana yi ne domin ya ga a cikin rigar arziki su yake.

"Salim tare da abokansa suke yi mini dariya har na ji daya daga cikinsu yana kirana da 'kolo, dayan kuma yana cewa mini criminal." Sai hawaye suka fara kasa tsare a kumatunansa.....

Chapter 29 Bata kai kalma 2k yanzu na cika she muku a wannan chapter din.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*81*
Zuba masa ido na yi ina kallo a yayin da hawayen ke ta zarya a dakalin fuskarsa bai goge ba, ni ma kuma ban ce masa ya yi shiru ba sanin da na yi cewar kukan shine zai sassauta masa takaicin abinda aka yi masa. Lallai gagarimin abu ne ke sanya fitar hawaye a idon Kamalu tun yana yaronsa balle yanzu da shekarun samartaka suka fara kama shi dole an yi gwagwarmayar rayuwa a samu zuciya ta sake 'ke'kashewa.
Idan an kira shi da 'kolo (almajiri) ai ba damuwa ba ne, ni na ji dad'i ma da ya zama 'kolon mahaddaci kuma marubucin al'kur'ani. Kalmar criminal din ce ta hargitsa dukkanin lissafina, Salim abin har ya kai haka. Abinda ya faru shekaru kusan shida zuwa bakwai yaro ya samu nutsuwa ya zama mutum shine yanzu za a taya 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~r masa da hankali.
Cikin jan ajiyar zuciya ya ce." Mama Salim na b'akinciki da yadda Allah ya yi mini jama'a a area nan, sannan yana kishi sosai ya ga na bude massalaci manya mutane na bina sallah suna gaisawa da ni. Wannan na ji da kunnena yana fad'in duk wanda ya bi b'arawo sallah shi ma bashi da maraba da 'barawo, kuma sannan bashi da sallah. Mama yaushe wannan sunan zai goge a tarihin rayuwata"
Na ji kwalla ta ciko mini ido. Na daure ban yadda ta

Please Login or Register in order to submit comment