Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata sake zuwa ba wai da har ta yi barazanar shigar da kara kotu tana fad'in ba ta yarda da wajan da aka kai mata yaro ba sannan ba a nemi shawararta ba. Kuma shiru har yanzu dai ba a sake jin doriyarta ba sai dai suna ganin seriars film dinta mai suna *Gidan kashe ah* tana fitowa a magajiyar karuwai wai acan garin lakwaja ake shirya film din gidan karuwai.
Abin ya dinga ba ni mamaki da al'ajabi Jamila mai take nema a duniyar nan ita a maimakon ta zauna ta yi hakuri ta kula da yaranta marayu kamar yadda 'yar uwarta ta yi sai take ganin kamar cutar da kai da kuruciya ne gwara ta fita yawon bariki domin dai a matsayinta na ya mace mai sauran kuruciya bai kamata ta wulakanta rayuwarta irin haka ba. Salima ta d'auko wayarta daga cikin jaka ta lalobo film din tana nuna mini. Na kar'bi wayar ina dubawa Sahura na leko kanta muka cika da mamaki tana tsakiyar karuwai da sigari a hannunta suna buga karta ana shewa da tafi kuma wai film ne. Na yi sauri na mik'awa yarinyar wayarta ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un. Lallai idan ka ga wannan tambad'ewar akwai hakki ko kuma baki na iyaye. Ai akwai y'an film 'din masu nutsuwa da suka mayar da harkar sana'a kuma ta yi musu riga da zani wasu har da mahalli da jari amma ita hanyar da ta d'auka ba za ta yi mata kyau ba domin su kansu masu d'aukar film din suna duba dacewa akan abinda za su d'ora mutum akai wata'kila shiga da mu'amularta ya nuna musu ga abinda tafi k'warewa a kai Ubangiji Allah Ya tsarkake mana zukatanmu.

kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Washe garin ranar da Gwaggo ta yi uku a gidanta na gaskiya muka tashi da azimin farilla na Ramadan. Kowane bawa ya samu nutsuwa da kuma kad'aita kansa ga mahallici domin samu rabauta da dacewa.
Ranar sadakar bakwai addu'a kawai aka yi mata ba a zauna ba tunda dama azimi ake yi Yallabai din yana nan bai tafi ba tukkuna shi da mahaifiyarsa suna ta fitar da abinci buhu buhu da abin masarufi domin sadaka da aka sha ruwa aka fita da d'anye hadiya ga marigiyar kamar yadda na ji Hajjan tana fad'in.
goma ga azimi suna ta wannan aikin harabar gidan Hajja cika take yi da mutane har da mata abin dai gwanin ban tausayi daga waje ma jama'a ne cike buhun shinkafa ce da kudi dubu goma ga mai rabo ban san iya adadin mota nawa ya sauke ba bayarwa ake yi jama'a na k'aruwa har sai da azimi ya raba tukkuna abin ya yi sau'ki. Lokacin kwanan su baba Tabawa tara da a kasa mai tsarki tunda hud'u ga azimi suka tafi a yadda yake gaya mini yaran suna can gidan Hauwa duk da har yanzu jikinta bai dawo daidai ba akwai mai aikinta Ladidi da kuma Inna Uwani ba ta tafi ba wai sai bayan sallah. A lokacin ne na ji hankalina ya yi gidan gabad'aya saboda ban yarda da zaman yarana a gidan Hauwa ba. Na fara yi masa maganar tafiya ya ce sai ashirin ga wata yana lissafin zakka ne sai ya kammala.
Babanmu ya kira ni a waya yana ta godiya wai an kai musu abinci har buhu biyar da taliya da sukari har da gero shi da Baba Sule na ce babu komai sadaka ce anan yake yi mini albishir din fitowar Hadiza kwana biyu da suka wuce gwamnati ta yi yasa da sasaauci a gidan gyaran halin da take zaune duba da watan da muke ciki an duba iya adadin shekaru da zamanta a gidan Allah Ya taimakata ta shiga cikin wad'anda suka fito ba tare da tsananta bincike akan lefin da ta aikata ba. Magana ce ta gwamnati bisa sahalewar gomna duk abinda aka ce hukuma a gidan duniya ai k'arshen magana kenan sai dai idan an je can lahira anan Ubangiji zai fitar da sakamako. Yana gaya mini tana nan koyaushe cikin sallar dare da ro'kon Allah gafara kuma duk ta tsangwami kanta bata fitowa ta yi walwala da jama'a.
Tausayinta ya kama ni sosai na ce ya gaya mata zan kira ta a wayar Ummansu mu yi magana idan na yanke shawara dama dole hakan ta kasance fita ma gagararta za ta yi tunda kowa ya san abinda ta aikata jama'a za su yi ta kallonta wasu ma har su jefe ta ko kuma a farauci rayuwarta kamar yadda suka farauci ta wani ita da abokiyartata Hajiya Alili da har yanzu ba san a ina ta boye ba.
Da yamma ranar Hajiya Saratu ta zo domin yi mini ta'aziyya ba ta samu zuwa ba a lokacin rasuwar sakamakon ciwon kafafun da ta d'an yi a cikin kwanakin.

To da daddare kafin mu kwanta nake gaya masa halin da ake ciki tare da yi masa godiyar bisa alherin da ya yi.
Bai yi jayayya ba ya amince mini akan abinda nake so yana fad'in Hadiza 'yar uwata ce kuma gida dai sunan nasa ne amma ni nake rayuwa a ciki da yarana tunda har na aminta da zama tare da ita shima yana yi mata murna samun ku'buta tare da addu'ar Allah Ya tsare gaba.
Ban samu yin waya da ita ba sai da gari ya waye tukkuna na gaya mata hukuncin dana yanke ta dinga kuka tana yi mini godiya tare da jaddada mini a shirye take domin na ce zan turo Magaji ya zo ya d'auketa mu zauna tare a gidan Hajjan kafin lokacin da za mu tafi can abujan. Ummansu ta yi kuka kamar me a waya tana yi mini godiya ina fad'in hannu baya rub'ewa a yanke a yar Hadiza har yanzu tamu ce kuma 'kaddara tana kan kowa farincikin ayadda ta tuba take kuma neman afuwar Ubangiji lallai shi din mai gafara ne da jin kai. Kuma hakika fitowarta da wani lamari da yake kwance wanda mu ba mu san shi ba, da ya so da tun farkon lamarin ya kar'bi rayuwata don haka ni ma daga nawa b'angaran wannan kad'ai zan yi mata domin ta samu sassaucin zuciya killaceta a waje daya da ababen more rayuwa da kula domin ta dawo nutsuwa da hayaccinta. Shi kansa Babanmu rasa abinda zai ce ya yi domin da da farko ya nuna rashin yardarsa yana fad'in Hadiza ta yi girman da za a ce ta je ta zauna mini a gida ita ba yarinya k'arama ba. Akwai wani abokinsa matarsa da ta rasu ya buk'aci auranta yaransa tara marayu a yanzu auran shine rufin asirinta. Na ji gabad'aya lamarin bai kwanta mini a rai ba abokin Babanmu ai da shakarunsa kuma ko auran za ta yi a yanzu akwai buk'atar zuciyarta ta nutsu kada don an ganta cikin ibtila'in rayuwa a yi kokarin k'rasa kassara mata rayuwa saboda bata da jayayya tunda mafaka take nema kai tsaye zata amince ko da ranta baya so.
Da yake ni ce na zo da maganar kuma nake buk'ata sai ya ha'kura ya amince mini. Anti Yagana ma ba ta yi jayayya ba ta nuna goyon bayanta dangane da hakan tana fad'in idan ta huta hankalinta ya dawo jikinta shekara daya zuwa biyu sai ta dawo gida ko kuma ta yi aure.
Akan haka muka tsaya kuma a ranar da yamma Magaji ya je ya d'aukota duk abinda ya faru ga rayuwarta na labartawa Hajja har da kuka tana fad'in sannu baiwar Allah kin ga jarabawa Allah Ya yafe miki mu kuma mugun ji da gani Ubangiji Allah Ya kare mu.
Hadiza tun a gidan Hajja ta fara yin dawainiya da su Hasan sai ta kar'be ni tunda da tare muke yi da iyami Hajja na dan yin abinda za ta iya amma zuwanta sai ta kar'be ni a duk sanda zan daga ido na kalleta sai k'walla ta cika mini ido. Mace 'yar garu da ta samu gatan uwa a lokacin da take sharafi da jiki mai kyau ta koma haka Hadiza ko da can ba ni da abinda zan nuna mata tunda ta yi tashen 'yan matanci kuma bata ta'ba yin saurayi talaka ba masu arziki ne daidai gwargwado ne suke zuwa neman auranta. Fara ce tas haka suke dukansu tunda Ummansu ma fara ce ta fi ni haske tana da kirji sosai a wancan lokacin ni kuma baya na fita da tsayuwar hallita mai kyau dalili ni jikina ta ko'ina dumur yake koda na yi haife-haife nan babu inda ya saki ya ragaje alhamdulillahi. Ita kuma irin jikin Ummansu ne da ita a sake amma akwai kirji cikakke a lokacin budurci ba yanzu da suka risina ba saboda wahala da shekaru tunda kwanaki biyar kacal ta ba ni ba wani nisa a tsakaninmu amma wallahi ta fi ni tsufa hakan yana da ala'ka da wahala da rashin samun hutu zullumi fargaba da rashin 'koshi. Alhamdulillahi ni kam kullum cikin hutu nake da kuma cima mai kyau tunda tsakani da Allah idan ba a zaman makokin nan na Gwaggo ba sai na ce na fi shekara tara rabona da shan ruwan pure water sai da mugun dalili ko maiduguri na je gidan anti Yagana ruwan gora Babansu Fadila yake sayo mini har na gama zaman da zan yi a gida.
Rabon zakkar da ya fitar ta zagaye dangina kaf daga can maiduguri Baban Saude ne wakili nan kuma Sunusi ne wakilinsa babban yaron baba Sule duk wanda sako ya same shi sai ya kira ni a waya ya yi godiya domin babu hanyar da za su same shi su yi masa godiya Y
'yan biyun gidanmu da su fari ana gobe za mu tafi suka zo muka yini tare muka sha ruwa cikin sakewa a bangaran da nake har ya shigo ya same mu muna raha abin mamaki sai ya zauna a cikinmu kunya kuwa duk ta kama su mussaman Hadiza da ta kasa daga kanta ta kalleshi dalilin abubuwan da ta yi a can baya ta dinga kar'be masa kudi tana shirya k'arya. Ya dinga jan ta da magana duk domin ta sake amma ina ta kasa kanta a kasa har ya tashi ba ta dago ba.
Sahura ba ta samu zuwa mun yi sallama ba sai dai ta kira ni a waya ta yi mini godiya sosai domin itama ta kar'bi zakka da kayan abinci rigijib a wajan aikinsu
Komai nasa cikin tsari da lissafi duk yadda ya yi mini haka ya yi a b'angaran Hauwa domin da kunnena na ji Hajja na waya da Inna Uwani kan kayan abincin da aka fitar musu da zakkarsu ta ce abincin dai a sa direba ya kai mata can bauchi kudin kuma bayan sallah za ta kar'ba sai a lokacin ne ma Hajjan ta san da cewar har yanzu tana abujan ba ta koma gida ba.
Ranar da azimi ya yi ashirin muka tafi bayan mun yi sallama da Hajja Yusi ya na gaya mini cikin sallah zai zo ya yi mana kwana biyu cikin 'yan uwansa na ce to Allah Ya kawo shi lafiya.........
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*168*
Abinda ya so ya d'an ba ni mamaki bai wuce ganin ya tafi gidanta ya kwana ba. To matarsa ce har yanzu tunda bai saketa ba a tunanina ni zaman da nake yi ba su samu matsaya ba har yanzu a cikin rikicin suke tunda bai ta'ba nuna mini cewar sun daidaita ba a lokacin dana tambaye shi ina yara bayan tafiyar masu aiki umara a takaice ya ce mini suna gidanta. Ni da Hadiza muka kwana a gidan da safe muka tashi da aikin gyare-gyare zuciyata ta'ki tsayuwa waje daya sai tunanin yadda aka yi suka iya shawo kansa cikin k'an'kani lokaci duk da fusatar da ya yi akan lamarin to ko shine manufar rashin tafiyar inna Uwani a lokacin da ya koma bayan mun zo duba Gwaggo nake tunanin suka daidaita tsakaninsu amma abin ya ba ni mamaki sosai. Na yi kokarin dannewa saboda samun kwanciyar hankali da nutsuwa zuciyata tana gaya mini gwara duk rintsi su shirya domin ko da ya yi musu abinda suke so zai iya auro wata tunda ya riga ya saba zama da mata biyu. Amma yanayin yadda suka dinga jujjuya maganar ne ita da uwarta ke ba ni mugun mamaki tabbas Inna Uwani tsufa ya yi gardama kuma an yi fad'uwar ba'kar tasa.
Bai shigo ba sai wajan d'aya da wani Abu yanayin shigar da ya shigo mini da ita ya tabbatar mini da cewa daga massalaci ya fito. Babu wani abu dana nuna masa a fuska ya zauna a falo cikinmu ni da Hadiza har k'asa ta durkusa ta gaishe shi Hadiza wani irin ladabi ta koyo a gidan gyaran halin da ta zauna
Ya amsa kuwa cikin kulawa ta tashi tsaye da Usaini a hannunta za ta nufi bedroom dina Hasan ya sanya kuka yana mika mata hannu wai sai ta d'auke shi. Kwanaki shida kacal a tare damu yaran sun yi sabo da ita.
Uban ya kar'be shi daga hannuna yana fad'in." In ban da rigima da wane hannun za ta d'aukeka ka ci girma mana."
Ya dinga tsala ihu yana zillo tare da mika mata hannu shi kuma Usaini na kwance a kirjinta ya yi luf.
Na kar'be shi daga hannunsa abin mamaki ya'ki yarda wai lallai sai ta d'auke shi, kishi dai irin nasu. Haka duka ta ciccibe su a 'kui'binta ta rirrikesu da hannunta ta nufi bedroom dina tana dariya yaron ya yi shiru ya daina kuka da zanbarwa.
Ya dube ni a nutse yana fad'in." Tausayi take ba ni sosai 'yar uwar nan taki Giwa."
A takaice na ce." Mun gode sosai Allah Ya kara rufin asiri?"
Ya zuba mini ido babu halin ri'ke hannu ko runguma saboda muna cikin ibada tunda ma Gwaggo ta rasu muka fara azimi ba mu yi wata kwanciyar kirki ba saboda abubuwa da ya wasa da suka sha kansa. Ya sauke ajiyar zuciya ba tare da ya janye idonsa daga kaina ba ya ce." Zan tura miki kudi kamar yadda muka saba kowace shekara
domin ki sayi abinda ki ke buk'ata na sallah.
Yara Hauwa ta saya musu wurin k'awarta suna wurinta ta ce a gaya miki idan an jima suna shigowa yi miki gaisuwa. "
Na ce." Ban gane hausar ba?"
"Ina nufin kayan s!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!"allar yara takalma da riguna na kanti an saya akwai saura wurin telansu zai kawo cikin satin nan inshallah."
Na d'an yi jim ina nazarin maganarsa a wannan karon kenan ita ta kar'bi kudin ta saya musu kayan wajan k'awarta sanin da na yi duk salla marigayiyace Maryam ke yi musu wannan hidimar amma dai har yanzu telansu da yake yi musu d'inki yana nan shi yake yi musu ko bayan rasuwar wadda ta d'auke shi aikin ya cigaba domin ni ma wasu lukutan yakan yi mini d'inkin amma ba sosai ba watannin baya ne da ya ce a fitar da kayansu gabad'aya ya sanya a aka kawo musu sabbin 'yankati to me hana wannan karon ma bai sanya an kawo musu ba.
A tak'aice na ce." To shikkenan." Ya dube ni yana fad'in.'' Ko hakan bai yi miki ba ne?"
Na ce." Ko bai yi mini ba ai dole na ha'kura tunda zaman lafiya nake so ko, amma ai da can ba ita take saya musu ba."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." To yanzu don ta nuna ra'ayinta ai ba lefi bane ki duba kayan sosai idan ba su yi ba sai a canza musu
ku dai zauna lafiya da juna, ita mun samu daidaito da ita kuma mun yi alkawari a zaman da muka yi domin har sai da kawunta ya zo mun zauna da ita Inna Uwanin ta yi alkawari kan cewa za ta gyara tare da ko'karin kawo zaman lafiya a junanku.''
Shiru na yi ban iya ce masa komai ba saboda mamaki.
Ya tashi ya hau sama ban bi shi ba na yi zamana ina nazarin yadda abubuwa suke canzawaa daga wannan sai wannan zuciyata tana gaya mini kudi ta kar'ba masu kauri a hannunsa domin ta 'karu tunda dama neman hanyar da za ta dinga samun kudi take yi.
Ita kuwa wadda ta rasu tana yi ne da dukiyarta bata neman kwabonsa ita nata salon kenan tunda tana da arziki. Ita kuwa Hauwa na tabbatar da cewa ta yi hakane domin 'karuwarta.
Da yamma muna kicin tare da Hadiza muna shirin abu bude ba'ki suka shigo..
Na bar ta a kicin din goye da Hassan ya yi bacci na fito falon na same su a zaune Inna Uwani ta d'auki Usaini yana saman cinyarta da abin wasansa a hannu.
Na d'an saki fuskata ina yi musu barka da zuwa na zauna kujerar dake kallonsu yaran gabad'ayansu suka shigo Khalil twins da Minal wurina suka rugo a guje k'ananun shi kuma Khalil din yana ta dariya kafin ya d'an risina yana fad'in." Mama ina yini?"
Na amsa da kulawa ni ma ina dariya na ce." Kai ya na ga duk ka yi zuru-zuru azimin nan fa bai wajaba a kan ka ba."
Ya sa dariya yana fad'in." Ko bai wajaba a kaina ba ba zan asha ko daya ba Mama.
Minal tana ta'ba mini cinyata ta ce." Mama ni kin ga haka na yi." Ta had'a yatsunta biyar ta d'ora d'aya a kai."
Na bude baki cikin mamaki ina fad'in." Da gaske." Karaf Usai ta buge hannun tana cewa." Ma'karyaciya ko daya ba ta yi ba wallahi." Cikin wasa ta yi maganar don har tana dariya ma.
Abinka da yarinta ita kuma Minal din sai ta fashe da kuka tunda dama dangwalolo ce. Nan da nan Hauwa ta 'bata fuskarta na ji lokacin da ta ja tsaki mai tsayi.
Ina Uwani na fad'in." Ke kam Usaina kin fiye saurin hannu wallahi menene abin duka Kuma?"
Khalil da sauri ya ce." Ba dukanta ta yi ba fa Inna."
Hauwa ta harareshi tana fad'in." Ba mu da ido ko kaine kake da Ido don ubanka zaman da suka yi a can ma kenan ba dukanta take yi ba."
Ya yi shiru yana yin fuskarsa ya canza.
Na ce." Ai saurin hannu gare ta na gaya mata kuma 'kanwarta ce."
A d'an sanyaye ta ce." Ban doke ki ba ko Minal?"
Sai ta d'aga kanta. Tsakanin yara ba a shiga Usai din ta sanya hannu tana goge mata fuska.
Daga haka na ce." Ku je dakinku ku zauna kafin mu gama gaisawa..
Suka kama hannunta suka bar wajan.
Cikin kulawa na fara gaishe da Inna Uwani itama ta amsa a d'an sake ta yi mini ta'aziyya tare da jajanta mini rashin da aka yi. Haka itama Hauwan mun gaisa babu yabo babu fallasa ta yi mini gaisuwa kafin ta dubi Khalil tana d'an harararsa ta furta." Ba ni ledar kayan nan?"
Na dube shi da sauri wata babbar leda ce da ya shigo da ita sai ya ajiyeta gefan kujera. Ya d'auka ya mika mata ta kar'ba kafin ta kalle ni tana fad'in." Babansu ne ya bada kudi aka saya musu 'yan kanti wurin Sadiya wannan shekaran ta kawo kaya sosai ai baki mance ta ba ko?"


Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba

Na gyada kaina a nutse ina fad'in." Ban mance ta ba." Sai ta mi'ko mini tana ce wa." Na ga sun yi kyau sosai set takwas ne kowanesu hud'u."
Na kar'ba na ajiye a gefena ina fad'in." To madallah."
Suka amsa tare kafin ta cigaba da cewa." Takalma ne kawai babu sizi d'insu a wurinta shine ban ce ta aiko ba amma gabad'aya yaran an saya musu da mayafai sauran suna wurin telansu yadda ya ce cikin satin nan zai kawo."
Na ce." To shikkenan wannan na Hasan da Usaini ne kenan?" Ta gyad'a kanta na ce." Ina na su Hassana?" Sai ta d'an diririce kafin ta ce." Yana can gida zan aiko miki da su gobe ko kuma an jima da daddare.
Shiru na yi ban ce komai ba. Hadiza ta fito daga kicin da yaron a bayanta cike da walwala a fuskarta ta zauna suna gaisawa. Inna Uwani ta yi caraf ta ce." Wannan kamar 'yar uwar nan taki ko?"
Na ce." E, itace Hadiza ba?" Sai ta ri'ke bakinta tana fad'in." Itace ta lalace haka sai ka ce wadda take d'auke da siga ko kanjamau!"
Maganar ta dake ni sosai cikin fad'uwar gaba na kalleta bakina sai ya yi nauyi na kasa ce mata komai.
Hadiza cikin gaggawa ta tashi ta bar wajan domin itama da alama maganar da Inna Uwanin ta yi akanta ba ta yi mata dad'i ba.
K'asa na yi da kaina zuciyata na hantsilewa akwai dalilan da suka sanya nake d'agawa matar nan 'kafa ba wai don tana uwar kishiyata ba ina kallonta kamar Hajja tunda ciki daya suke amma an kusa kaiwa matakin da zan fara mayar mata da raddi a duk lokacin da ta yi mini wani rashin hankalin.
Ya sauko ya same mu a zaune a falon ya zauna gefana yana kallon Inna Uwani da ta k'irkiri yi wa Usaini wasa har da yi masa rawa tana dariya shima yaron yana yi. Hakan kuwa ya yi masa dad'i sosai aka ce wai mai d'a wawa sai ya shiga washe bakinsa tana fadin." Yara duk sun yi wayo kamar ba biyu ba sun yi kyau uwarsu na da kafar nono mai kyau."
Ya ce." Haka aka yi goyon 'yan uwansu ma." Ta miko mini yaron tana fad'in." Ai ban mance ba. Ubangiji Allah Ya raya mana su domin su zama cikon addinin musulunci duniya kuma ta amfana da su."
Ya dinga amsawa da Amin ya rabbi Inna Uwani Ina godiya sosai."
Suka tashi tafiya bakina ya mutu kwarai dangane da salon da suka shigo da shi. Da k'yar na ce su gaida gida ya tashi ya bi bayansu kafadarsa sa'be da yaron.
Ina nan zaune ya dawo ya zauna cikin walwala a ganinsa mun fahimci juna tunda gashi har ya sakko ya gan mu kuma yaronsa na hannu Inna Uwani tana yi masa wasa wannan ne dalilin da ya assasa masa annasuwa da farinciki bai san da cewa wani sabon salo ba ne.
Na zazzage kayan yaran ina dubawa. Eh rigunan manya ne kuma sun yi kyau sosai zan iya kar'ba na yi musu amfani da shi tunda an riga an saya na su Hassana ne ban ga ni ba. Na juya ina tambayarsa "Ta kawo mini kayan su Hassan ban ga na su Hassana ba?"
Ya dube ni da kulawa yana fad'in." A a ba ta had'o da su ba ne?"
Na ce." Eh" Sai ya dan yi jim kafin ya nutsu yana kallona ya furta." Ki bar mata su su yi sallah a hannunta idan hutun makaranta ya 'kare sai su dawo gabad'aya jiya ta fara gaya mini cewa tana son yaran su yi mata hutu.''
Girgiza kaina na yi tare da cewa." A a, yaranta dai ka kai mata su amma nawa yaran su dawo gidansu ba ni son abinda zai daga mini hankali a yanzu dai cikin ibada muke abinda ba zai yiwu ba ne.''
Ya d'an 'bata rai yana fad'in." Ke dai duk ta inda aka biyo miki ba a yi miki gwaninta Amina menene lefin nan da can kuma duk gidana ne akwai buk'atar a ko'ina yarana su sake su kuma yi sabo, ki yi hakuri ki bar mata su hutu kawai ta buk'aci da su yi a hannunta sai su dawo, ki duba kawaicin da ta yi miki a kan nata yaran mana."
Na sake girgiza kaina a karo na biyu na furta." Na gaya maka fa ba zai yiwu ba ai ni ban buk'aci zaman yaranta ala dole a tare da ni ba. Kai ka kawo mini su kuma ba zan hana su zama ba tunda gidan ubansu ne. Maslaha anan shine ka kwashi yaranta a kai mata tunda zahiri ana shiga hakkinta alamu sun nuna kad'aici ya isheta hayaniyar yara take buk'ata. Kowa ya rike nasa shine zance na gaskiya."
"Kamar yadda na isa na bata umarni ta bi ke ma haka za ki bi. Na gama yanke magana yara za su yi hutu gidan Hauwa idan sun 'kare su dawo ku cigaba da zama gabad'aya tuntuni yaranta dake suka saba kuma suna kaunarki babu wani dalili da

Please Login or Register in order to submit comment