Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce da Baba Tabawa ta tu'ka mana towo don zai fi man dadin ci akan tsabar shinkafar nan."
Ta ce."Aikuwa kin yi shawara mai kyau Amina don tunda aka sanar da ni rasuwar nan wallahi ko na sanya abinci a gabana sai dai na kalle shi ba na iya ci. Kai rasuwar baiwar Allah nan ta ta'ba ni wallahi."
Anti Yagana ta ce." Ba ke kadai ba wallahi ni kaina na gigita kwarai da aniya Ubangiji Allah Ya yi mata rahama."
Muka amsa da amin gabad'ayanmu kafin ta yi mana sallama ta fita daga d'akin, anti Yagana ta dube ni tana fad'in." Na so na tambayi Ummansu Hadiza labarinta amma na sha'afa wallahi, kuma don dai Babanmu ya ce sai sun tafi amma da ko kwana daya sai su yi tunda yanzu dole ne su kwana a hanya
ina so mu sake samun lokoci mu je mu sake dubata ko ya ki ka ce."
Na ce." Hakane anti Yagana ni kaina Hadiza tana raina wallahi, dalilin da ya sanya kenan na ce da Hamusu duk k'arshen wata ya dinga yi mata siyayya yana kai mata, zuwan namu yana da amfani ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar."
Ta furta." Ni har fargabar ganinta nake yi wallahi saboda ina tuna irin kukan da ta dinga shirga a ranar da muke je kin san da kyar aka tura ciki muka fito, na jima ina kukan zucci duk sanda na tuna da halin da take ciki nakan shiga yanayi na damuwa mace a irin wannan wurin a ajiye Amina duniyar nan ta baci duk da ba ita kadai ba ce, amma su kansu ma'aikatan wurin wallahi wasu daga ciki ba su tsoron Allah."
Cike da damuwa na ce." Anti Yagana lefin Hadiza na kisa ne ta kuma tabbatarwa da kotu gaskiyarta ba mu da wani yun'kuri da zamu yi domin ceto ta. Hakkin rai ba abin banza ne. Idan Allah Ya kar'bi tubanta kuma tana da ragowar rayuwa sai ki ga ta fito ta hanyar da ba mu yi tsammani ba. Idan kuma sun kasheta shikkenan sai ta riski Ubangijinta a wankakkiya. Ubangiji Allah Ya kare mu daga fadawa jarabawa da mummunar kaddara."
Ta amsa da Amin Ya Allah da yanayi na damuwa da nadama.

Misalin goma da rabi maigidan ya shigo tare suke da Kamalu ban yi mamakin ganinsu su biyu babu Yusi ba domin sai na ce ganina da Yusi daya kafin a d'auki gawar marigayiyar na hange shi tare da Adam a rakube a bayan kujera yana rarrashisa yanzu ma su Hajja da Gwaggo sai tambayarsa suke yi ina jin Kamalu na basu amsa da cewa yana can tare da Adam. Maigidan bai tsaya ba suna gaisawa ya haye sama hankalina gabad'aya yana kansa don haka ban yi jinkirin bin bayansa ba.
Na same shi zai shiga wanka da babban towel a jikinsa.
Muka zubawa juna ido. Na isa dab da shi na tsaye a sanyaye na ce." Ya karin hakuri tun d'azu nake ta so na yi maka gaisuwa ban samu dama ba, Ubangiji Allah Ya gafarta mata, kai kuma Allah Ya baka hakurin jure rashinta, Allah Ya albarkaci abinda ta bari."
Ya dinga amsa da "Amin Ya Allah cikin jin dadi. Ya nufi bandakin na bi bayan shi na taimaka masa wurin had'a ruwan wanka. Kallo yake ta bi na dashi babu yabo babu fallasa, amma kallon ya fara sa'bata sai na tsargu na fara tunanin ko shima ya fara yarda da abinda 'yan uwanta suke fad'a akanmu wato da bakincikinmu ta rasu. Da na tuna kallon nasa babu harara da k'yama a ciki sai na d'an samu sassauci, na fito na bar shi a bandakin domin ya yi wankan. Na zauna jigum cikin zullumi.
Ya fito yana tsane jikinsa na tashi da sauri na bude wardrobe dinshi jallabiya na fito masa da ita da gajeran wando. Na mika masa ya kar'ba na koma na zauna yana kintsa jikinsa ya ce." Ki kawo mini abinci Amina."
Da sauri na mike ina fadin." Dama abinda zan tambayeka kenan, tun yamma na ce da Baba Tabawa ta yi towo zai fi dadin tafiya."
A takaice ya ce." Kin kyauta kuwa."
Ya d'auki turare yana fesawa a jikinsa. Na sauka kasa cikin nazarin abinda ya yi a ganina wane turare zai fesa a cikin wannan yanayin da matarsa ta rasu ko kwana daya ba ta yi a kabarinta ba
Na koma saman da tire a hannuna mai d'auke da kwanonin abincin da duk abinda nasan zai buk'ata. Yana zaune gefan gado
yana waya da Sukairaju na ajiye tiren hannuna a saman daddumar da yake zama domin cin abinci...

Ina binki bashi idan kin san kina karanta littafin nan ba ki biya ni hakkina ba.


Sai da ya kammala wayar tsaf tukkuna ya zo ya zauna saman daddumar da abincin yake a shirye. Na zuba masa guda biyu madaidaita ina ko'karin zuba miya ya furta." Wanene zai cinye miki wannan towon Amina?"
Na dube shi a tsanake kafin na ce." Kai ne za ka cinye?" Sai ya gyada kansa yana fad'in." A a d'aya ya ishe ni, kada ki zuba miya a kai a b'ata shi ki yi addu'a d'ayan ma na iya cinye shi."
Ban ce komai ba na cire dayan na mayar cikin fulas na fara ko'karin zuba miyar ya ce ki zuba ta yau'kin kawai kada ki sanya mini jar miyar, ki sanya mini man shanu akai wadatacce."
Na yi yadda ya umarta Ina fad'in." To naman fa." Ya ce." Ki tsamo sai ki sanya mini."
Ban ce komai na dinga tsamo naman ina zuba masa a saman towon har ya so yayi yawa." A nutse ya ce." Naman nan ya isa haka Amina, kina so na ci abinci jikina ya mutu ko?"
Na girgiza kai a hankali na ce." Kallo d'aya na yi maka d'azu na tabbatar da cewa akwai yunwa a tattare da kai wallahi."
Ya furta." Ba ki yi karya ba rabona da abinci tun yammacin jiya kuma ban wani damu ba wallahi."
A nutse na ce." To yanzu dai ka daure ka cinye wannan har naman duka."
Hannunsa ya sanya tare da bismillahi kafin ya ce." To ke ma sanya hannunki mu ci tare zai fi albarka.
Na sanya hannuna a hankali na gutsiro na kai daidai bakinsa.
Kallona ya yi na 'yan sakkoni kafin ya bud'e bakin na sanya masa towon ya fara taunawa a tsanake
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Ina mai sunan abokina ya 'kara wayo ko.?"
Na ce." Ya yi wayo sosai su Hajja ma suka dinga mamaki girman da jikinsa ya yi suna fad'in kamar yana sha nono saboda jikinsa ya ginu babu motsewa ko wata matsalar gaskiya yana samun kulawa sosai a wurin Baba Tabawa ba shi da matsalar maraicin nonon mamansa."
Da d'an jin dadi ya ce." Na gode Allah na kuma gode muku Amina ina mutukar godiya Allah Ya saka muku da alheri

'Dan tausayi ya ba ni domin yanayin yadda ya yi maganar ya nuna mini cewa har yanzu yana jin zafin abinda Hauwa ta yi kuma abin ya dame shi abubuwa ne da yawa suka yi masa dabaibayi. Ta bakin Hajiya Saratun Hauwa ko a waje ya aurota bai kamata ta yi wannan sakarcin ba. yaro
d'anyar haihuwa ta ajiye saboda wani banzan dalili.
Na ce." Ni kam banga abin godiya ba duk abinda na yi maka ai kaina na yi wa."
Ya yi shiru bai ce komai ba yana dai ta kar'bar towon da nake bashi a baki har guda ya kusa k'arewa ya ce." Ban ga kin ci ba."
"Na ce." Sai ka koshi my love dina." Ya sa dariya wadda ban yi tsammani ba yana fad'in." Na ga sai wani ji ki ke da ni Amina."
Da d'an murmushi na ce." Tausayi ka ba ni." Ya gyad'a kansa da wani irin murmushi kwantacce a a tare dashi ya cinye malmalar towo daya na kara cire wani daga leda na cigaba da bashi bai hana ni ba. Jefi jefi muna d'an ta'ba hira mafi rinjaye kan marigayiyar ne. Da kyar na daure na soko maganar da take ta damuna na ce." Akan maganar da yan'uwanta suke yi akan mu ni da Hauwa wata'kila sun gaya maka kai ma ko?"
Ya ce." Wace magana ce kuma?"
Cike da damuwa na furta." Wai duk wanda ya shiga gidan domin yi musu ta'aziyya sai sun gaya masa irin zaman da muke da ita har suna fad'in bakincikin da muka jima muna guma mata ne ya yi sanadiyar rasuwarta."
Ya yi jim Yana kallona kafin ya ja siririn tsaki ya ce." Ke waye ya gaya miki haka?"
Kai tsaye na Mamana ce?" Ya san dama ina kiran yayarsa da sunan.
Sai ya girgiza kansa yana fad'in. " Mata dai ba a raba ku da k'ananun maganganu da fitina baiwar Allah ga sanadin mutuwarsa amma an jingina da wani lamari domin tayar da husuma ba ni so na ji bakinki a ciki wannan maganar duk abinda za su yi kada ki biye musu ku daga mini hankali don Allah domin na lura basu da kintsi dukkaninsu taron sakarkaru ne me yasa ga gaskiya 'kiri-'kiri a take gabad'aya da ni da su da ke mun san yadda ciwuka suka cinye Maryam har ajalinta ya sauka to me ya kawo wannan maganar kuma?"
Na ce." Ni ma abinda na gani kenan, kasan kuma dole ne na damu tunda ni ce a gidan yanzu, a ganina idan wasu basu yarda ba wasu za su yarda tunda Allah ne kadai ya san irin abinda suke fad'a a kanmu."
Ya ce." To kada wannan ya dame ki, tunda har maganar ta dawo kunnena zan yi wa tufkar hanci, na gaya miki dai kada ki kula su ku zubar mini da mutunci a gari."
A tak'aice na ce." In sha Allahu rabbi."

D'akin ya sake daukar shiru na wani lokaci kafin na sake yin kundubalar yin magana abin kamar wadda Hauwa ta sammace idan ma nace ba zan sake yin magana ba sai na kasa jurewa gabad'aya idan na tuna bata gidan sai na ji gabana ya buga kuma a raina sai nake ganin ai lefinta bai kai ace an rabu da ita gabad'aya ba tunda shima ai yanayi mata lefi me yasa shi da yayarsa suka fi bata rashin gaskiya.

Na ce." Don Allah tunda haka ta faru ku yi hakuri Hauwa...... Ban kai ga krasa abinda yake bakina ba ya katse ni da babban sauti." Amina." Ya kira sunana na amsa da "Na'am tare da zuba masa ido gabana na d'an fad'uwa ganin yadda ya yi bala'in shan kunu......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*


[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Gudun aure paid book complete 2k ne a telegram what'sapp Gruop Kuma 1k via 0542382124.... Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*119*
"Na sha gaya miki cewar abinda yake tsakani na da Hauwa ba huruminki ba ne. Ko kuma lokacin da zan aureta na yi shawara dake ne? me yasa ki ke so k'ara mini damuwa akan wadda nake ciki, za mu samu matsala dake akan hakan ki kiyaye ba ni son maganar Hauwa a gidan nan daga yau."
Da k'yar na ce." To shikkenan dama gani nay.... Ya sake daga mini hannu yana fad'in ." Menene lefina Amina ko kema kina so ki nuna mini abinda ta yi ba komai ba ne? ina k'ara gaya miki ni fa Samira na ce ina so ba Hauwa ba, zan gaya miki wata magana wadda ba ki santa ba har yau na kasa mantawa da matata ta fari Allah Ya jikanta domin soyayyar gaskiya ce a tsakaninmu. Ban ta'ba kallon Hauwa a madadin da za ta share mini kukan rashin Samira ba, kuma ban ta'ba yi mata kwatankwancin son da nake yi wa Samira ba. Idan na rabu da ita babu wata tangard'a da zan samu tunda ni nasan bata da wani gurbi mai girma a zuciyata don haka maganar Hauwa ta kare a gidan nan na gaya miki Amina"

Duk yadda na so ganin na daure zuciyata daga barin jin zafin yadda yake yabon matarsa ta fari data mutu kasawa na yi sai na manta ma da maganar da muke tattaunwaa akai zuciyata ta fara tsalle tana tu'kuki tsabar zafin kishin da ya taso mini na ce." Maganar Hauwa kuwa ba zata 'kare ba bari na gaya maka. Itace uwar yaranka uku, ai k'aryar so ta 'kare kuma ko kana sonta ko baka sonta ya zame maka tilas ka kalleta a matsayin wata jigo da ta samar maka da wani ginshiki da ka jima kana nema
wannan maganar da kake furtawa kamar gugar zana kake yi mana ni da ita Hauwan kawai ka fito fili ka gaya mini cewa Amina har yanzu ban samu madadin Samira ba, ai ta riga ta mutu kuma duk wanda ya riga ya tafi baya dawowa sai kawai ka ro'ki Allah Ya takaita maka kwana ka je ka risketa a can ku gina sabuwar rayuwar da za ka wanzu cikin farinciki."
Ya zuba mini idonsa yana kallona. Na juyar da kaina gefe tare da sake had'e fuskata. Shiru d'akin ya d'auka bai ba ni amsa ba. Na tsame hannuna daga cikin abincin da nake 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ bashi na ya gi tissue paper domin goge hannuna. A hankali ya ce." Ban k'oshi ba."
Zumbura baki na yi na yun'kura na tashi tsaye sai ya riko hannuna tare da janyo ni jikinshi ya mike k'afafunsa na zauna saman cinyarsa. D'auke kaina na yi domin ji na yi ma sam bana son kallonsa saboda takaici wannan a cin fuska ne a takaice, haka kawai daga bada shawara.
Ya ce." Amina kalle ni."
Kallonsa na yi babu fara'a. Ya rintse idonsa a tsanake ya ce." Kin san jini a jikin d'an adam ko?"
Na yi shiru ban tanka ba. Ya d'an matse ni a jikinshi yana sakin ajiyar zuciya cikin kunnena ya furta." A jinin jikina kike yawo. Ina can wata uwa duniya kina yi mini gizo Amina ina alkawarin soyayyar da ki ka ce za mu yi idan na dawo gida?"
Da mamaki mai yawa a tare da ni na kura masa Ido. Ya sake matse ni a jikinsa yana me sanya fuskarsa tsakankanin wuyana wurin da yake bala'in so kenan a jikina.
Jikina ya shika k'warai da aniya daga sannan na sallamawa sha'anin rijalu na sake yin lakwas ina ayyanawa a raina ko ni ce na fadi na mutu mutumin nan damuwarsa k'alilan za ta kasance babu wani abu na jin dad'in rayuwarsa da zai fasa.
Ni gabad'aya ma ban san akan wane alkawari yake magana ba domin tunda suka tafi ba mu samu sukunin yin wasu hirarrakin soyayya ba.
Saukar hannunsa da na ji a kirjina ya sanya ni zabura. Na cire hannun da sauri sai ya had'e yatsunmu wuri d'aya yana bina da wani irin kallo wanda yake ko'karin kassara ni. Nan take tausayin kaina ya rufe ni. Yanzu nan ya gama jadadda irin alhini da kewar tsohuwar matarsa jiya kuma matar da ni da Hauwa muke ganin ya fifitata a kanmu ta fad'i ta mutu yau aka binneta a kabari wai har ya gama alhinin da jimamin yana bijiro da wani shagali da jin dad'in da bai wuce na dan wani lokaci ba.
Cike da kasala ya sake mayar da hannunsa saman kirjina yana tatta'bawa ban yi nawar sake cire hannunsa ba muka kurawa juna ido da kyar na furta." Ba ka ji wani iri ba?
Lumsassun idanuwansa ya bude a dabarbarce ya ce."Na ji sun 'kara girma ko dan na yi kewarsu ne." Raina ya baci da jin amsar da yake ba ni. Wato ma bai fahimci akan abinda nake magana ba sai kawai na yi yun'kurin sauka daga cinyarsa ya kuwa ri'ke ni da kyau irin rikon da baki isa ki k'wace ba.
Sosai na bude idona a kansa na ce." Gaskiya ni ka ba ni mamaki wallahi mutuwa fa aka yi maka mai zafi har alhinin ya bar gangar jikinka kenan."
Ya gyada kansa yana fad'in." To ai ta riga ta rasu Amina, ni na isa na dawo da ita ne? Mutuwar nan kowa zai mutu to me zai sanya a tauyi rayuwa a bawa gangar jiki da ruhi abinda yake muradi kada ki manta ke fa ki ka yi mini alkawari idan na dawo za mu sha soyayya."


Na ce" Da yaushe na yi maka alkawari abinda ma duka bai fi sau biyu muka yi magana ba tunda kuka tafi."
Yana d'an shanshanar jikina kamar wani tsohon zakin da ya jima yana farautar nama ya ce. To ina jin dai a irin mafarke-mafarken da nake yi dake ne ki ka gaya mini za ki yi mini soyayya fitacciya."
Na juya da kaina takaici ya hana ni magana a haka ina jinsa yana ta turmutsa hannunsa cikin rigata. Gabad'aya kaina ya kulle na rasa da wane ma'auni zan auna wannan lamarin
ya gama goge mini duka haddar da na yi a kansa, ai na d'auka na gama karantar halayensa gabad'aya ashe da sauran abinda ban gama sani ba.
Ya d'ora bakinshi saman lebunana ya sumbata kafin ya cire a hankali da wani irin yanayi ya ce." Abin nan yana d'auke hankali Amina zai mantar da ni abubuwa da yawa, bayan kiran sunan Allah a cikin k'unci da damuwa sai wannan lamarin domin ni a wurina ma gaba yake da cin abinci, a wannan dare babu abinda zan fasa ai a haka duniyar ta ginu tun kafin mu zo cikinta ake mutuwa ake muka sunnah irin wadda za mu yi yanzu, mu ji dad'i mu gamsu kuma Ubangijin da ya ce mu yi hakan ya ba mu lada
mai yawa."
Na yi k'asa da kaina dalili ba ni da wani karsashin da zan kalubanci maganarsa ta kowace siga ya fi ni gaskiya amma ai ana barin halas da kunya wallahi har yanzu matar nan idan ta fa'do mini a raina sai gabana ya fadi.
Ya cika ni na sauka kasa yana bude fulas din abinci jikinsa har d'an rawa yake yi ya ce." Abici zan baki kici ki koshi kamar yadda ni ma ki ka ciyar da ni daga nan kuma sai mu sake ciyar da juna wani abincin na mussaman ko ba haka ba ne?"
Na ce." Gaskiya ba zan munafurceka ba a yanzu wallahi ba ni da wani karsashin da zan tari wannan lamari daka bijiro da shi. Ka yi hakuri tukkuna dukkunimu hankalinmu ya daidaita sai irin wannan nishadin ya biyo baya."
Ya gyara yanayinsa yana fad'in." Ni ina da karsashina, sannan kuma a cikin nutsuwa da hankalina nake, menene a ciki ne haramun ne, saboda kawai an yi mutuwa sai a ajiye ibadar Allah ba na son jayayya Amina a buk'ace nake ke daga ganin yanayina ma kin san da hakan to me zai sanya ba za ki sama mini da farinciki ba.
Kuka na fara yi tsakani da Allah ni ban san yadda zan yi na tari abinda yake so ba har na taimaka masa ya nisha'dantu irin yadda ya saba, har yanzu jikina babu wani kuzari ni gabad'aya ma duniyar ta fice mini daga raina.

Don dole na dinga kar'bar towon da yake ba ni a bakina ina ci ina goge kwallar da take fitowa daga idona. Da kyar na ci rabin malmala na turje na daina kar'ba muka shiga toilet a tare wai zai yi mini wanka nan ma sai da muka yi kokawa kamar sababbin amare ina share hawayen takaici haka na yi wankan yana tattabe mini jiki muka fito. Towel ne kawai a jikina a daure na d'auki kayana zan sanya ya kwace. Yana fad'in." Sanya kayan ai bashi da amfani Amina, bari tukkuna mu kammala ko?"
Ya ja hannuna zuwa gadonsa zugwi-zugwi haka na bi shi cikin sagewar gwiwa da nadamar rayuwa. Wai shin ma ya za a yi ya nisha'dantu. Tambayar da nake yi wa kaina kenan.
Ya tura ni na yi kwanciyar ringingine dogare kafafuna na yi da zummar tashi ya raba nasa kafafun a kaina ya dabaibayeni. Abubuwa na tashin hankali da gigita lissafi ya fara yi mini jikinsa na wani irin rawa. Na dinga matse jikina ina ya'ki da gangar jikina da zuciyata akan kin 'karbar abinda yake mini, amma ban yi nasara ba, cikin k'ankanin lokaci ya fitar da ni daga hayyacina na kasa gane shin a duniya nake ko ni din ma na shilla barzahu ne ban sani ba. Ki'dima kam da ficewa daga hayyaci mun yi tunda abin ai ba sabo ba ne a wurinmu ya riga ya gama zame mana jiki sosai ya gurje ni ya gamsu na gamsu babu 'karya. Ashe shima wannan lamarin ba a had'a shi da komai idan gangar jikin ya kar'bi sakon duk turjiyar da zuciya take yi akan hani bata samun nasara. Na dinga jin kunyar kaina da kaina domin kuwa ni kaina da na shiga shu'uni mantawa na yi da cewa rasuwa aka kwatsama mana a gidan sai da tunani da hayyacina ya dawo tukkuna na ji siraran hawaye na gangaro mini ina rayawa a raina idan na riga shi mutuwa haka zai samu wata macen ya cigaba da more rayuwarsa tunda ai gashi ya fad'a. Mata biyu da ya fifita a rayuwarsu har baya iya boye so da k'aunar da yake musu sun mutu yana kewarsu amma bai fasa gudanar da wani lamari ba.


Idan kin karanta ba ki biya ni hakkina ba ina bin ki bashi.

Da asuba na sauka k'asa bayan fitarsa sallah. Wanka na yi sosai da ruwan d'umi na gasa jikina. Anti Yagana duk tana zaune saman dadduma tana kallona na fito daga bandakin na kintsa jikina sannan na gabatar da sallah. Na shafa a nutse na juyo ina kallonta lokacin ta zame ta kwanta saman dadduma amma ba bacci take yi ba carbin da yake ma'kale a hannunta take ja. A tsanake na gaisheta ba tare da tashi ba ta amsa mini tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya ta furta." Gobe da wuri zan kama hanya Amina, jiya da daddare Babansu Fadila ya kira yake gaya mini mijinta ya zo ya ga masa bata da lafiya har da su k'arin ruwa."
'Yar dariya na yi kafin na ce." Anti Yagana ta kusa goya jika kenan."
Harara ta mako mini tana tabe bakinta."
Na ce." E, mana anti ai idan ki ka ji an

Please Login or Register in order to submit comment