Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk ya rufe hanyar da zata had'ani dashi to kaga zamana ai bashi da amfani yana da kyau ace a neme shi domin ya sanar da manyana abinda ya yanke akaina.....

Wannan badakala ta Amina da Tajo. Allah Ya yayyafawa abin ruwan sanyi.......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*65*
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Don kuskure kin yi, amma hakan ai ba zai sanya a d'auki wannan mummunan matakin akanki ba ai idan ba yana so ya jefa ki a wata masifar ba me zai sanya ya k'aurace miki na irin wannan watannin wannan ba daidai ba ne an shiga hurumin addinin Allah tabbas
akan hakan dole mu neme shi domin mu ji me yake nufi. Sai maganar zargi da rashin daidaituwar jini gabad'aya ma auran naku ai a baibai yake babu dacewa ai ta wani gefan kema kina da hujja Amina, na kuma ji dad'in da ki ke neme ni domin sanya ni a cikin lamarinki zan yi kokarin ganin na samar miki da farinciki in sha Allahu rabbi."

Gidan Baban Saude mai yalwa ne kuma daidai gwargwado yana da rufin asirinsa don har yanzu da rayuwa ta yi tsadar nan shinkafa 'yar gwamnati ake ci a gidansa. Taliya 'yar hausa kuwa sai dai idan sun yi sha'awa yadda yake jingine musu buhun shinkafa ta gwamnati haka yake ajiye masu kwalin taliya da makaroni na waje da sauran kayan masarufi, shi din mutum ne mai wadata iyali matsalar kawai fa'da da tsautsauran ra'ayin takura iyali domin kuwa kafin a fita unguwa a gidan Baban Saude akan jima sai dai idan da 'kwa'kkwaran dalili.
Matansa biyu kowacce da yaranta da d'akunansu ciki da rumfa ne manya. Akwai shaguna biyu daga waje wanda ciki matasan yaransa maza suke kwana cikin gidan kuma bayan d'akunan iyalinsa akwai falle falle biyu masu grima sai kicin da bandaki biyu na fitsari da kuma na ba haya sai wadataccen tsakargida mai yalwa don har da bishiya a tsakiyar tsakar gidan.
Sayyada ce kawai take zawarci dama lokacin da anti Yagana ta je mini take gaya mini ai an sasanta anti Saude da anti Zainab sun koma d'akin mazajensu amma kafin hakan sai da aka sha daru domin shi cewa ya yi raba auran zai yi. Sai da Dada ta yi masa jan ido tukkuna ya janye matakin da ya d'auka domin idonsa ya rufe baya duba kowa dama ai hausawa suka ce kowa nasa ya sani, shi yana duban 'ya'yansa yayin da mazajen suma suke duba wahalar da nasu yaran za su shiga muddin aka raba su da iyayensu. Anti Saude itace babba don ta girmi ma anti Yagana amma da kad'an kuma yaranta bakwai, ita kuwa anti Zainab haihuwarta biyar daya ya rasu hud'u a raye amma duk da haka ya ce shi sai an sakar masa yaransa kuma ya tubure lallai babu d'an da zai d'auka ya yi wa wahala kowanne yaro ya koma gidan ubansa. Gabad'aya ma sai sanya dokar kada a kuskura a sake barin yaran su shigo masa gida.
Wannan matakin da ya d'auka shi ya gigita anti Zainab tunda ita nata akwai k'ananu a ciki kuma ita kadaice bata da kishiya mijin nata ya d'auki yaran ya kaiwa yayarsa ita kuma kullum ficewa take yi kasuwa ta baza hajarta. Anti Saude ce mai kishiya kuma yaranta sun girma sannan kuma duk maza ne. Anti Zainab kuwa da mata a ciki.
Tashin hankalinta ta yi sosai babu shiri a 'boye ta je gidan Dada ta fashe mata da kuka tana gaya mata yadda aka yi tare da neman alfarma kada ta gayawa Baban nasu itace ta gaya mata.
Wannan shine dalilin da ya sanya Dada ta bud'e masa wuta akan lallai ya nemi mazajensu ya zauna dasu ya ja musu kunne amma banda maganar rabuwa a duba yaran domin kuwa hukuncin da ya yanke ba shine mafita ba tunda dole ai watarana za su sake yin aure kuma mazan ba 'kwan'kwasasu ake yi a ji ba.
Ita kuwa Sayyada da yake itace auta a mata kuma sunan Dada ne da ita dama tun kafin a yi mata aure 'yar lele ce tunda ya fahimci mugun miji take aure mara ciyarwa da kula da lafiya sai kawai ya maka shi a kotu akan ya sakar masa 'yarsa ya kuma fadi ko nawa ya kashe a lokacin da zai aureta zai biya shi tunda shi ya nemi sakin dama kuma haihuwarsu d'aya saboda farincikin Sayyadar ya bar yaron nata a hannunta domin kuwa kuka ta dira a gidan bayan alkali ya raba auran ta ce ita ba zata bada yaro ba. To da yake dama 'yar lelensa ce sai ya kyaleta ya ce mata amma muddin ubansa ya zo nemansa za a bashi abinsa.

D'aki guda ya sanya a ka gyara mini tsaf har da katifa da sabon mashinfid'i da labuleye masu kyau d'akin yana ta k'amshin turaran wuta irin na tsinke. Mama uwarginshi da kanta ta shigo ta kawo mini abinci a jere a tire na silba muka sake gaisawa bayan wadda muka yi tunda kafin na shiga masaukina sai da na shiga duka d'akunansu muka gaisa. Ta dinga tambayata mutanan gidanmu da yaran na ce mata duk kowa lafiya lau.
Sai da nayi wanka tukkuna na d'an warware na ji 'kwarin jikina na zauna a nutse na ci abinci na 'koshi na fita da tiran ina sake yi musu godiya na koma d'akin na zauna tare da fito da wayata daga cikin jaka domin tun a cikin mota ban sake dubata ba. A mace take ban san dalilin da ya kasheta ba.
Minti biyar da kunna wayar kiran anti Yagana ya shigo. Cike da fad'uwar gaba da fargaba na d'aga nasa a kunnena cikin wani irin yanayi na yi sallama bata amsa mini ba na ji tana ce wa." Ya aka yi ki ka kashe wayarki Amina tun wajan la'asar nake kiranki sai a ce mini a kashe take."
A hankali na ce." Bacci na yini ina yi kuma tunda na sanyata a caji ban sake waiwayenta ba sai yanzu ina fatan kuna lafiya ina Fadila."
A takaice ta furta." Lafiya lau, mijinki ne ya kira ni yake tambayata wai kin zo gidana na ce a a wani abun ne ya faru a tsakaninku ne?"
Cike da takaici na ce." Babu abinda ya faru anti Yagana don girman Allah idan ya sake kiranki kada ki daga wayarsa."
"Akan wane dalili zai kira ni na'ki dagawa Amina, ki gaya mini menene yake faruwa domin yanayin da ya kira ni a d'azu ya tabbatar mini da cewa akwai abinda kuke b'oyewa ke da shi."

"Saki na ya yi."
Na tsinci kaina da gaya mata hakan.
Cikin rud'u da tashin hankali ta furta." Saki akan wane dalili, kina ina yanzu domin ya tabbatar mini da cewa tun safe ki ka fito daga gidanki direbanki Ayuba ne ya kira shi a waya ya gaya masa shine ni kuma ya kira ni yake tambayata."
Cikin dauriya na ce." Anti Yagana abinda nake so dake a wannan ga'bar da muke ci da mutumin nan don girman Allah ki cire kanki idan zai kira ki sau dubu ya tambayeki abinda ya shafe ni ki ce masa ba ki da k'arfi akan lamarin ya nemi manyana su yi magana, don rainin wayo ne kadai zai sanya ya dinga nemanki ai ya san wad'anda suka bashi aurena tunda ina da uba kuma yana raye ke menene na ki a ciki."

Ta shiru na dan wani lokaci kafin ta ce." Eh kwarai kuwa ba ni da ruwa a ciki Amina shishshigi ne ma ya sanya nake kutsa kaina a sha'aninki, ba ni da hannu tabbas ni ba kowa ba ce."
Jin yadda ta juya maganar ya sanya a sanyaye na furta." Anti Yagana ki yi hakuri don Allah kada ki juya mini manufa ni da ba haka nake nufi ba."

Ta ce." To na ji, ko zan iya sanin abinda ya faru, sannan kuma ki gaya yanzu kina ina domin hankalina ya kwanta Amina sha'aninki yana nema ya fi karfina, don girman Allah ki fahimci kin girma fa kina dai kallon abinda ya samu Hadiza ko, mune manya a gidanmu ba mu da namiji babba dole mu zamu tallafi 'kannanmu da suke tasowa don Allah ki yi hakuri ki jure kamar yadda kowace mace take ha'kuri a d'akin mijinta ki zauna wannan ya zama mutuwa ce zata raba tsakaninku ki yi mana wannan alfarmar." Ta kare maganar cikin rawar murya.
Ina kuka na ce." Anti Yagana ya zan yi ne da rayuwata gabad'aya duniyar ta yi mini zafi a yanzu bana jin dad'inta. Duk yadda zan yi na yi kokarin ganin na zauna d'akina amma abin ya gagara, Allah Ya had'a ni da wani irin (Ba'aboren namiji) sunan littafin Binta Umar Abbale ku nema ku karanta ya yi mutukar dadi.
Tana kuka irin mai tafe da tsananin damuwa da takaici ta cigaba da cewa." Abubuwan da suka faru tsakanina da shi suna da yawa anti Yagana na gaji da b'oye miki na kuma gaji da zama da mutumin nan so nake yi kawai ya sauwake mini na huta idan ba so yake yi zuciyata ta buga ba."

A sanyaye ta ce." Dalili dame bakincikinsa zai kashe ki Amina, ai taura biyu bata taunuwa a lokaci daya babu yadda za a yi ace a shari'ar ma'aurata an saurari b'angare daya ni ba zan yarda da maganarki ba har sai ya zo tukkuna an zauna an zube magana sai a fahimci wanene mafi rijayen lefi."
Cikin kukan na ce." Anti Yagana ke fa macace ya kamata a ce kin dubi halin da nake ciki, ki fahimce ni wallahi ina da matsala ba wai da gangan nake so auran nan ya mutu ba ina da hujja mai karfi."

Wannan littafin na kudi ne yar uwa kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba. Ina 'yan kasuwar da suke so a tallata musu hajarsu ina yi akan farashi mai sau'ki.

"Hujjarki ai bata wuce kina gudun haihuwar yara masu cutar sikila ba dalili kuwa shine rashin had'uwar jini. Wannan ce kad'ai hujjarki wadda na sani Amina, sai kuma kishin da yake damunki tunda na ji labarin an ce ya sake yin wani auran, in bayan hakan ban san wani abu da ki ka taka ba. Sannan kuma ai kai tsaye ban ce miki baki da gaskiya ba, cewa na yi a bari a ji ta bakinsa tukkuna kafin a yanke hukunci wannan shine adalci, ai duk yadda zan so shi bayanki ne, matsalar namiji kuwa muddin ki ka ce ba za ki iya d'aukarta ba to Amina kina tare da damuwa domin kuwa kusan gabad'ayansu haka suke.
Na ce." Wallahi anti Yagana ban da Babansu Fadila a ciki, ai ya yadda ki ka kasa fahimtar damuwata tuntuni na tabbatar da cewa ba ki kai ajin da nake ba dangane da karatun namiji, maza uku fa na aura kuma kowa da halinshi wallahi ban ta'ba shan wahala a hannun Yaya Aminu da Alhaji Muntari irin wadda nake sha a hannun mutumin nan ba. Ku ne kawai kuke yi mini kallo hutu da jin dadin amma ni kadai nasan irin takaicin da nake 'kunsa."

Murmushi ta yi har sai da na ji sautinsa ta furta." Ha'kuri dai kawai na fi ki shiyasa ki ke ganin kamar ba ni da wata matsala da mijina. Amma kai tsaye ba zan musanta miki ba domin kuwa mai-d'aki shi yasan inda yake yi masa yoyo abinda nake so dake anan shine ki gaya mini kina ina yanzu hankalina zai fi kwanciya."
Kai tsaye na ce." Ina nan gidan Baban Saude yanzu haka."
Cike da zullumi ta furta." Gidan Baban Saude fa ki ka ce Amina?"

"Kina da hankali kuwa Amina, shin ko kin manta halin Baban Saude da d'aukar jidali akan abu 'kalilan zai mayar dashi babba. Mai yasa ba ki yi shawara da ni ba tukkuna kafin ki yanke wannan hukuncin sanin kanki ne Alhaji Tajudden ya yi nisan da wani mahalu'ki zai kai ya ta'ba mutuncinsa ko da babu dukiya kuwa to akwai dattijanka da girma da mutuncin da zai wuce a ce kina yawon kai shi a k'ara, kuma duk ki tsallake 'yan uwan Babanmu saboda raini ki taho wurin Baban Saude saboda dama kin tabbatar da cewa shi din ba mutum ne mai nisan tunani da tsinkaye akan lamari ba. Yanzu me ki ke tunanin zai faru idan har ya kashe miki aure wallahil-azim ba ni babu ke Amina." Ta kàrasa maganar cikin tsantsar tashin hankali da damuwa......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*66*
Sosai kaina ya d'aure da jin maganarta. Wai yau anti Yagana itace take kiran Baban Saude da mutum mara tsinkaye saboda wani na daban, ta manta cewa Baban Saude ciki daya suka zauna da Mamanmu. uwa daya uba daya ba wasa ba ne, kuma wallahi duk tsayayyar da yake yi akan gaskiyarsa yake mutane ne suke ganinsa masifafe mafadaci wanda ba shi da mutunci, kuma wallahi fahimtarsa ne kawai da ba a yi ba. Shi baban Saude irin mutanan nan ne masu tsage gaskiya duk d'acinta. Babu ruwansa a ko'ina yakan fad'i ra'ayinsa kuma ko ta mutu ko ta yi rai, tuntuni na fahimci anti Yagana bata cikin jerin mutanansa domin ko da na gaya mata zan sanar dashi halin da nake ciki da farko dakusar da ni ta dinga yi tana ganin idan har ya ji abinda yake faruwa zai iya dagula lamarin ya sake rinca'bewa. Daga haka kuma auran ya mutu abinda take ji wa tsoro kenan, wanda ni kuma a wannan ga'bar da nake ciki ban'ki auran ya mace ba kowa ya huta. Domin kuwa ban ga alfanu da cigaba a tattare da zama da wannan mutumin ba.
Ba na shakka ko fargabar had'uwarsu da Alhaji Tajon ai mutunci da sanin ciwon kai ya fi komai a rayuwar wanda yasan kansa. Baban Saude ba makwadaici ba ne ballantana yana ganin gaskiya ya take da gangan. Ai da take cewa na gaya Babanmu ko 'yan uwansa babu abinda zai iya yi balle kuma baba Sule da gabad'aya bai yi ba. Makwadaici ne na gaske babu wata ho'bbasa da zai iya yi domin 'kwatar mini 'yancina. Babanmu zan yi shedarsa ba shi da kwadayi yana da gudun duniya da kuma dogwaro da kansa. Idan an bashi zai kar'ba da godiyar Allah amma ba zai roka ba duk shaharar arzikin mutum, ya iya ri'ke talaucinsa, kuma da zai d'auki mataki tuntuni ai da ya d'auka, babu wani abu da za su iya yi mini sai dai su danne ni kamar dai yadda ita anti Yaganar take dannata.
Ni gabad'aya ma na rasa gane inda ta dosa wallahi da ban san halinta ba da sai nace itama kudinsa take kwad'ayi. To na san halinta da kawar da kai da kawaici akan abin mutum sam bata da wannan zulamar. Abin mamaki wai yau anti Yagana ce take cewa idan na rabu da wani namiji ita da ni har abada. Sai kawai na ji wasu zafafan hawaye sun k'wace mini suka fara kasa tsere a kumatuna. A hankali na ajiye wayar na silale na kwanta saman ledar dake tsakar d'akin Ina wani irin kuka mai ciwo lallai mutumin nan ya yi wa rayuwata illa ta kowane 'bangare, kokari yake yi da gaske sai ya shiga tsakanina da 'yar uwata jini daya bayan fin karfin da ya yi mini wurin raba ni da yarona duk kuwa da tsananin shakuwar da take tsakaninmu kamar ya sanya almakashi ya datse yanzu ganin Yusi ya yi mini tsananin wahala balle na ji muryarsa, wannan wace irin masifa ce!

Wajejan sha biyu na dare na tashi na je na d'auro alwala nafila na yi raka biyu cikin sujjadar karshe na fashe da kuka tare da kai wa Allah kukana akan ya za'ba mini abinda ya fi alheri a rayuwata muddin rabuwata da Alhaji Tajon akwai alheri to Ubangiji Ya gaggauta kawo k'arshen lamarin. Idan kuma zamana dashi bai kare ba ina ro'konsa ya daidaitamu cikin ruwan sanyi ba tare da an kai ruwa rana ba rayuka sun 'baci ta dalilin hakan.
Na kwanta bacci da jin sasaauci a zuciyata domun kuwa ina kammala addu'ar na ji nutsuwa ta shigeni tare da tawakkali da kar'bar duk irin abinda Allah Ya zartar a kaina.
Da safe bayan na yi wanka Sayyada ta kawo mini kayan karin kummalo d'akin da nake ta zauna muna d'an ta'ba hira jefe-jefi kafin ta fita daga d'akin domin ba ni damar karyawa a nutse.
Gama karin kummalona ke da wuya Babansu Fadila ya zo wato mijin anti Yagana lokacin Baban Saude ya fita zuwa babban gida wajan Dada domin su gaisa.
A soro na same shi a tsaye da shirin fita wajan sana'arsa muka gaisa kafin ya fara yi mini maganar da ta kawo shi domin jiya duk wayar da muka yi da anti Yagana a gabansa ne kuma shi ma a jiyan da magriba ya ga gilmawarta a tasharsu sai yake hasashen anya ni din ce domin bai gama tabbatarwa ba sai da ya dawo gida tukkuna ya tabbatar da cewa ni din ya gani bayan saukata a garin.
Nasiha da ban ha'kuri tare da kawo misalai irin na matan magabata ya dinga yi mini har yana cewa ko don yadda 'yar uwata take shiga damuwa matsananciya akan matsalata yana da kyau na jure na yi hakuri na samar mata da nutsuwa domin kuwa jiya raba dare ta yi akan dadduma gaban Allah tana addu'a da hawaye akan lamarin. Wannan dalilin ya sanya shi ma ya kasa rintsawa har garin Allah ya waye kuma ya kudire a ransa cewa zai zo ya same ni akan abinda yake faruwa.

Hakika sun ba ni tausayi sosai ita dashi kuma sun isa su ce mini na yi ko na bari ba tare da na yi musu jayayya ba. Amma a wannan karon Ina ganin ba zan iya bin umarinsu ba domin kuwa duk abun nan da ake yi shi wanda ake yi dominsa bai yi wata magana ba, bai zo ba tun bayan kiran da ya yi wa anti Yagana jiya ban sake ji daga gare ta ba.
Hakan na gaya masa na ce ya bari tukkuna ya magantu ai yanzu dama a hannunsa take idan yana da ra'ayin cigaba da zama da ni zai zo ya nemi sulhu idan kuma bashi da ra'ayi to zai aiko mini da shedar da zata nuna mini lallai ya gama zama dani, Ina ganin kamar haka ya dace a yi.
Sai ya nuna ai ba haka ya dace a yi ba tunda ai anti Yagana ta gaya masa har yanzu na'ki na fadi abinda ya yi mini kuma ba shine ya ce da ni na tafi gida ba yaji na yi na bar d'akina don haka kuwa tunda ba shine ya ce na tafi ba ai babu lallai a ce sai ya nemi inda nake domin ya ji dalilina.
Na jima ina nazarin maganar kafin daga bisani na yanke shawarar gaya masa abinda yake faruwa tunda ai shi din ba bare ba ne, sannan kuma maganace da za a zauna a zube ta shi ma makusancina ne tunda yana auran sha'ki'kiyata.

Duk bada'kalar da take faruwa na zayyana masa da irin ni ma abinda na aikata da tuban da na yi sannan kuma na tabbatar masa da cewa na gane kuskurena na kuma nemi afuwa da gafarar Allah da kuma neman sulhu da shi domin mu yafi juna amma hakan bai yi masa ba har sai da ya d'auki hukuncin kaurace mini na tsayin wattanin tare da shigowa garin ba tare da ta nemi inda nake ba .

Sosai al'amarin ya dake shi ya jima yana nazari kafin daga bisani ya dube ni da alamun tausayi da sasaauci ya ce." Ni ai duk ba ta gaya mini haka ba Amina ta dai ce mini kawai tana zargin ke ce ba ki son auran ki ke so ki kasheshi amma ba ta gaya mini dalili ba
A hankali na furta." Ai ba ta sani ba don ban gaya mata ba har yanzu saboda na san halinta da sanya abu a ranta kuma bai zama lallai ta fahimce ni ba, in banda kai da Baban Saude babu wanda na gayawa sai ko Sahura 'kawar nan tawa.
Ya ce." Lamarin na ku ne da rikitarwa Amina, kina da kuskure shi ma yana da nasa kuskuren ai dama ba za a d'auki lefi a daurawa mutum d'aya ba. Kuma gaskiya abinda ya fi tsaya mini a raina dangane da lamarin nan yawan zargin da ki ka ce mutumin nan yana yi miki babban abu ne a ganina wannan ba soyayya ba ce domin kuwa zargi yana daya daga cikin manyan dalilan da suke saurin lalata ala'ka ta auratayya. Ba zai yiwu a ce don ya aureki a matsayin bazawara kuma 'yar kasuwa ya dinga zarginki ba sam ba shi da hujja ko a wurin Allah domin kuwa bai ta'ba kama ki da wani mummunan abu ba. Sai maganar tsayin wattanin da ya d'auka ba tare da ya neme ki ba, wannan normal ne Amina akwai matan matafiya da suke shekara da biyu uku ba tare da mazajensu ba kuma aurensu bai lalace ba sai dai kin san shi addini kogi ne domin ni kaina na ji wasu malaman suna cewa idan namiji ya k'auracewa mace na tsayin wata uku hud'u biyar har zuwa shekara to aure ya haramta a tare dasu amma fa sai in dai suna kwana tare a gida daya ya aikata hakan. Idan sun yi nesa da juna kamar dai matafiyi wannan ba lefi ba ne haka daga shekara daya zuwa biyu aure yana nan. To anan za mu iya cewa auranku yana nan tunda baya garin da a ce kuna gida daya ne kuna kwana a daki daya ya k'aurace miki tabbas akwai alamun a tambayi malamai domin sanin menene gaskiyar lamari. Wannan shine iyakacin fahimtata.

littafin nan na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Sannan ke ma zan gaya miki gaskiya abinda ki ka yi bai kyautu ba domin kuwa kin shiga hurumin Ubangiji dalili kuwa ai shine mai rayawa da kashewa kuma bai zama lallai don kin haifi d'aya da lalura ba ki ce duka yaran da za ki haifa haka suke ba. A lokacin da ki ka lura da samuwar cikin sai ki bar shi kawai ki ro'ki Allah ya ba ki masu albarka kuma masu lafiya. Abu na biyu kuma kin ga mutumin nan bashi da yara shi zai so ko masu lalurar ne wannan kadai ya isa ya sanya shi ya k'ullaceki kuma ya ga duhunki domin kuwa ai zai ga kamar kina yi masa b'akinciki ne saboda wata hujja taki wadda bata da tushe balle makama, sannan da yawan mutane ba zu fahimceki ba domin kuwa za a ga ai ke ko dan kina da yaran ne ya sanya ki ka zubar masa da nasa cikin. Lefi ne babba ko wurin Allah Amina amma kuma na ji dad'i da ki ka gane gaskiya kuma ki ka nemi gafara a wurin Allah lallai Ubangiji mai afuwa ne kuma mai yafiya ne, sannan kuma shi ma Yallabai din yana da kyau ya yafe miki ya d'auki 'kaddara domin ta riga fata bai kamaci ya d'auki wannan matakin ba domin a ganina da tun farko kun kashe matsalarku a cikin gida hakan zai fi alheri ba tare da kowa ya sani ba domin kuwa irin wannan lamari baya buk'atar a ce a zauna ayi ta nanata

Please Login or Register in order to submit comment