Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kina ina har hakan ta faru. Ban haifi Kamalu da Yusi ba, amma yau zan gaya miki wani abu da nake ji game da yaran nan a zuciyata wallahi ina sonsu fiye da yadda ki ke tsammani. Yadda nake jin yaranku gabad'aya a raina haka nake jin wanda na haifa. Ina rokonki da Allah da annabi kada ki yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu. Kada ki yi yun'kurin datse k'akkarfan zumuncin da yake tsakanin Adamu da Yusuf domin kuwa d'azu Adam ya je mini cikin damuwa cewa kin tura yaran nan kano, ki yi hakuri yara su dawo mu cigaba da rayuwa cikin aminci na yi miki alkawari wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Kuma in sha Allahu Salim zai shigo ya baki ha'kuri komai ya shige da izinin Allah."

Ta gama maganar tana sanya hannu domin share hawayen da yake ta tsiyaya a fuskarta. A nutse na ce." Ki yi hakuri ki daina kuka akan wannan lamari Momi wallahi ban k'ullaceki ba, kuma ni har abada akan yara ba zan yi rigima dake ba, amma ina so ki sani ce wa muddin Kamalu da Salim na tare a Inuwa daya to sa'bani ba zai daina giftawa a tsakaninsu ba. Abinda ba na fatan ya sake faruwa. Ba wai ba ki isa ba ne, kin fi karfin komai a wurina domin ban mance alherinki ba, ki yi hakuri yara dai har abada sun bar nan in sha Allahu suna can hannun dangin Babansu sai dai su zo da ziyara. kuma ban isa na yanke zumuci da ala'ka ba tunda ai ba ni na had'a ba......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*85*
Babu wanda ya ce komai sakamakon saukowar maigidan daga sama ya canza kaya amma ga yanayin yadda fuskarsa ta ke a cude nasan duk ya ji maganganun da Kamalu yake furtawa. Bai ce mana komai ba haka zalika bai kalli inda muke ba ya kama hanyar fita cike da tsananin b'acin rai a tare da shi.
Yusi da sauri shi ma ya bi bayansa ba tare da ya yi wa kowa sallama ba.
Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Haba ai ni yau kwanan farinciki zan yi wallahi, irin wannan mutanan rashin mutunci da tijara shine daidai da abinda ya kamata da su."

Muka yi shiru babu wanda ya tanka mata. Ta dubi Kamalu da har yanzu yake huci yana numfarfashi.
A nutse ta ce." Kada ka wani damu Kamalu abinda ka yi shine daidai domin idan har da ni da uwarka za mu zauna mu zuba ido akan abin nan to wallahi tallahi babu wani mataki da uban rikonka zai d'auka. Abinda ka aikata a yanzu shine ya tabbatar mini da cewa kai dan halak ne ka haifu kuma kana kishin kanka, sannan kuma ya nuna cewa Salim sharri ya yi maka baka aikata ba, kada ka sare ko ka tsorata don suna da kud'i wallahi ba za su yi nasara a kanka ba.
Idan har Salim da uwarsa sun ce za su bi kadin jinin da ka zubar masa ni zan biya su zan kuma shige maka gaba tsayuwa gaban alkali masifa yanzu aka fara wallahi."
Na jima ina kallonta tare da yin nazari a kan maganganunta. Yadda ta d'aukaki lamarin take sake zuzuta shi shine abinda yake sanya ni tunani. Ita da Momi din duka na kasa gane inda suka sa gaba. Masifa yanzu aka fara. Wannan maganar tata ita nake ta nanatawa a cikin raina. Tabbas k'azafin da Salim ya yi wa Kamalu mai muni ne sosai, to amma ni ban shirya tsayuwa gaban alkali akan hakan ba. Kamalu dai duk da ba a shedar mutumin yau ina da tabbacin bai aikata ba. Ba ni son bala'in ya yi tsayi domin shaidan ya samu mafaka.
Tunda ni da yaro mun tauna tsakuwa shikkenan nasan duk daran dadewa gaskiya zata bayyana. Ba zan tsaya da ita domin yin shari'a akan yara ba, ba kuma zan ce mata komai ba domin bata isa ba, mijinta da ya daure mata gindi shine daidai da ni. Sai dai yadda Hauwa take zafafa lamarin da ko'karin sake rura wutar rikicin shine na kasa gane azancinta na yin hakan shin soyayya ce ko kuma da wata manufa a zuciyarta. Ba ni so akan abinda ya shafe ni auranta ya samu tangard'a amma na lura ita ba wannan ne abinda ya dame ta ba. Tunda har na riga na yanke hukunci na kuma gaya mata ya kamata ace itama ta sassauta saboda gudun afkuwar abinda zai sanyata ta shiga nadama tare da danasani.

Yusi ya sake dawowa a karo na biyu daga bakin kofa ya tsaya yana fad'in." Ka zo in ji Momi."
Hauwa ta kalle shi sama da kasa kafin ta ja tsaki ba ta ce dai komai ba. Sai harara da ta ke wurga masa. Ya sake maimaita maganarsa "Momi ta ce ka zo."
Ya ce." Ka je ka ce mata gani nan."
Har ya juya zai fita na ce." Yusi zo nan." Ya juyo yana kallona na ce." Zo."
ya zo ya durkusa kusa da ni.
Na ce."Ka za'bi Momi ko?" Ya yi shiru bai ce mini komai ba.
Cikin tsawa na sake cewa." Momi ce uwarka ba ni ba ko Yusi?"
Sai ya sa kuka yana cewa." Mama don Allah kada b'acin rai ya sanya ku yi abinda zai janyo muku nadama, Momi duk abin nan da yake faruwa wallahi ba ta da laifi, tana sonmu dukanmu na yarda Yaya Salim ya yi laifi amma kada abin ya shafeta itama cike take da takaici da b'acin rai."
Hauwa ta ce." Idan abin ya dameta tunda farko mai yasa ba ta shigo an tattauna ba." Da sauri ya ce." Bata da lafiya wallahi, shiyasa bata shigo ba a kwance take."

Yana rufe baki Nusaiba ta shigo da tawagar yaranmu a bayanta ta ci kuka ta k'oshi domin kuwa fuskarta har ta d'an tasa idonta ya yi ja wata'kila d'an uwan ne ya kira ta a waya a gaya mata. Yaranmu kaf tun daga kan Khalil Hassana da Usaina Minal suna bayanta.
Ba tare da ta gaishe da kowa ba tana daga tsaye take ce wa." Mun gode bisa abinda aka yi mana, Allah Ya saka da alheri, mu ba mu gaji fitina da tashin hankali ba domin tarbiyar da iyayenmu suka yi mana kenan, koyaushe Mominmu cikin yi mana nasihar mu zauna lafiya da kowa take yi. Mahaifinmu kafin ya rasu k'arshen maganarsa shine mu ri'ke Babanmu Alhaji Tajo a matsayin uba. Wannan dalilin ya sanya ba za mu yi fad'a daku ba domin muna kallonsa a matsayin ubanmu, kuma Shima ya rike mu a matsayin 'ya'yansa. Bayan haka kuma muna buk'atar nutsuwa kwanciyar hankalinsa, shine dalilin da ya sanya Mominmu tace mu yi hakuri. "
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da ce wa."
Sannan yaranku ga su nan Momi ba ta da lafiya, dama kokari ne kawai irin nata ni kuma na ce kowacce ta raini abinta."
Da sauri Hauwa ta ce." Sannu uwar iya, sarkin kitifi da makirci 'yar na gada idan ba ki yi ba ai baki sha nonon uwarki ba, mu so muke mu kwantar da uban rik'on naki ciwo ya kama shi shiyasa muka hana shi sukuni. Wato ke baki ga abinda dan'uwanki ya aikata ba ko har kina da bakin magana saboda ba ki da kunya ko.
Yara dama ai ba mu muka sanyata ta ri'ke ba, ita taga zata iya, mu ai taimakonmu ki ka yi da ki ka dawo mana da su dama fin karfinmu aka yi, rashin lafiya kuwa kowa ma a cikinta yake mara kunyar k'arya sakarai, wannan tabarmar kunya ki ke nad'ewa da hauka. Wanene musababbi idan ba d'an'uwan naki ba. Shi za ki jawa kunne a matsayinki na wadda take gaba da shi, cikinmu dai babu sa'arki da za ki zo ki yi wa d'ibar albarka, sai me dan yara sun dawo gidan ubansu dama ai ita ta nema ni da Amina dai babu wadda take da sha'awar barin yaronta a hannun uwarki."

Nusaiba cikin rawar murya ta furta." Kin ga ni ba sanya ki a cikin maganata ba, ko dana shigo kin ji na ambaci sunanki, wai shin ma ina ruwanki ne naga ai ba ke ce ki ka haifi yaron ba da har ki ke fuffuka duk fa abinda ki ka ji da shi wallahi daidai nake dake, ai dama an ce ke ce ki ka rura wutar ba kowa ba."
Hauwa ta zabura da sauri ta tashi tsaye tana fad'in." Ubanki zan ci la'ada waje don uwar uwarki ita data turo ki itace sa'ar yi na, duk wanda ya gaya miki ni nake turara wutar bai yi karya ba da gaske ni ce kuma sai na rurata ta ruru! ta cinyenku matsiyata masu kisan mummk'e."
Sai ta fashe da kuka mai karfin gaske ta sanya hannu ta toshe bakinta. Hauwa kuwa ko a jikinta. Na tashi na je na zaunar da ita ina fad'in." Menene haka Hauwa yarinyar nan ba sa'arki ba ce kamar yadda ki ka fada me yasa za ki biye mata."
Tsaki ta ja da k'arfi tana fad'in." Iskancin banza da wofi wai har wani fadi take yi an zalincesu su ba suga zalinci da suka yi ba kenan, ko shi wannan din ba mutum ba ne?" Ta fad'a tana nuna Kamalu dake zaune a kan kujera. Na ce." Ya dai isa abar maganar don Allah."

Ta yi shiru ba ta sake magana ba sai tsaki take ja. Ina juyawa ita kuma Nusaiban ta kama hanyar fita jikinta duk a sabule. Sai kuka take yi 'kasa-kasa tana jan hanci.
Ban ce komai ba na koma saman kujera na zauna kaina na sarawa tsabar tunani da zullumi.
Duk da abinda suka yi wa Kamalu sai da na d'an ji wani iri a zuciyata. Gabad'aya ma yaran ba su iya fad'a ba daga ita har Salim din domin kuwa da sun iya fad'a ina ga da ba su fara ko'karin neman sulhu ba shi karamin cikinsu ma Adam kenan tunda ake hatsaniyar bai ce komai ba sai dai kuka da share hawaye da tissue shine kadai abinda yake yi gwara Yusi ya zo yana kalubalantar d'an uwan nasa.
Da zai tafi kiran da Momin take yi masa ban hana shi ba, amma hukuncin da na yanke a zuciyata yana nan ban janye shi ba sai yaran sun bar gidanta da garin ma gabad'aya domin kuwa ba zan iya ba da wannan masifa ba na shirya tarar kowane irin kalubale.

Washe gari da safe Kamalu 'kalau ya shigo mini tsaf dashi cikin Pakistani yana ta kamshin turaransa da ya riga ya zauna masa a jiki
. Muka gaisa da yake a d'aki ya same ni ban kai ga fita falo ba tukkuna na ce masa ya je ya gaishe da Hauwa da Baba Tabawa ya dawo. Ya fita minti biyar ya dawo ya zauna a gefena. Na dube shi a tsanake na ce." Jiya mun gama magana da Hamusu a waya zan sanyaku a motar haya zuwa kano sai ku dinga waya dashi kafin ku sauka. "
Ya ce." Na ji dadin hakan Mama, kin ga kuma Baba bai jima da tafiya kanon ba don har d'akinmu ya same mu ni da Yusi yana tambayarmu zai je kano ko muna da sa'ko wurin Baba Hamusu.

Littafin nan na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Shiru na yi ina d'an nazari tafiyarsa kano da gaggawa irin haka tana da ala'ka da kiran Hajja dama ta ce zata kira shi babu tamtama kuwa wurinta ya tafi.
Na ce. " Hakan ya yi daidai ni ma na ji dad'i, ka je ka kira mini Yusi amma kada ka gaya masa komai."
Ya ce." To shikkenan. Ya tashi ya fita da sauri. Ni kuma cikin gaggawa na shiga toilet domin yin wanka. Ina fitowa su Hassana suka shigo tsaf gabad'ayansu Baba Tabawa ta shiryasu. Na ce." Kun zo mu gaisa ne, ashe kun san ni?"
Husaina dariya ta kama yi ta haye gado ta kwanta tare da sanya babban yatsanta a baki tana totsa.
Na ce." Ke ba ki daina tsotsar hannun nan ba dama." Ta yi shiru ba ta ce mini komai ba sai ma ta janyo rigar baccina da na cire da yake mai laushi ce ta dinga shafa rigar da hannunta.
Hassana ta je ta cire hannun daga bakinta cikin tsamin baki ta ce." Momi fa ta hana ki."
Na dube su Hassanar na cire hannun ita kuma Husainar na mayarwa bakinta. Na juya da niyyar bude wardrobe na d'auko kaya na ji kuka da k'arfi da sauri na dube su. Husaina ce ke kuka sosai ta cukume Hassana da kokawa Minal na gefe a tsaye tana kallonsu.
Wajan na nufa ina fad'in." Mai ya had'aku." Cikin tsamin bakinta tana kuka ta ce." Dutana ta yi, ina luwanta da ni."
Dariya nasa na ce." Ke Hassana mai yasa ki ka duteta?"
"Momi ta hanata tsotsar hannu." Ta ba ni amsa tana zum'bura baki.
Kamulu ya shigo ya ce." Fad'a suke yi ko Mama." Na ce." E dama haka suke yi a gidan Momin"
"Wallahi yini suke yi fad'a ai Mairo tana aiki kuma Hassana ce mai zalinci. Wataran Momi idan ta gaji dai sai ta cewa da Mairo ta goya Husaina don a samu mafita nan sai ta ce ba ta yarda ba ta dira kuka. Momin da kanta take cewa a d'auko mata zani sai ta goyata ake samun zaman lafiya."

Na ce." Momin da kanta take goyo." Yana 'yar dariya ya ce." E, ai rigimar Hassana tana da yawa fa wasu lukutan Momin ce take iya sarrafata ga gaddama da rashin yarda da mutane."
Na gyada kaina ban ce komai ba, zuciyata ta shiga zullumi da tunanin inda matar nan ta sa gaba akaina da yarana.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*


*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=ØLÜ
*86*
"Ina Yusi din yake?" Na tambaye shi ba tare da na dube shi ba.
"Gashinan zuwa, amma mama kin san ba lallai ne ya shigo shi kadai ba duk inda ya ajiye kafarsa anan Adam yake ajiye tasa. Ya ba ni amsa da dan sanyin jiki.
Shiru kawai na yi ina nazari, Adam dai ko mayya ce ta haife shi dole su rabu domin kuwa
babu wani dalili da a yanzu zai hana yaran nan barin garin nan. Na ce." Je ka falo, idan sun shigo tare ka turo mini shi." Ya amsa da "to shikkenan. Kafin ya sanya yaran a gaba suka fita.
Gama sanya kayana ke da wuya Yusi ya shigo ya sha ado cikin yadin kufta d'inkin kansa abin kallo ne ballantana takalmin da yake kafarsa. Babu shakka matar nan ta na hidima da yaran nan kuma duk abinda za ta yi babu bambanci abinda Adamu zai sanya a jikinsa shi Yusi zai sanya duk tsadarsa kuwa. Ko turarukan da suke amfani da shi wallahi sai mai karfin jari. Jikina ya yi sanyi kalau a yayin da nake duban yaron cikin Kamala da nutsuwa tare da kwarjini fatarsa luwai alamar hutu da jin dad'i sun ratsa jikinsa.
Kafin ya zauna a gefana sai da ya d'an risina tare da furta." Mama ina kwana, an tashi lafiya?"
Na amsa a nutse ina sake nazartarsa har yanzu babu walwala da sukuni a tare dashi tabbacin abubuwan da suke faruwa na damunsa. Ya nisa kafin ya sake fad'in." Momi ta ce tana gaisheki ta ce na gaya miki za ta shigo idan an jima."
Sai da nutsu sosai na dube shi babu fara'a a tare da ni na ce." Yusi ina so ka bud'e kunnuwanka da kyau ka ji abinda zan gaya maka, hukuncin na yanke kuma babu mahalukin da ya isa a wannan ga'bar da tura ta kai bango ya dakatar da ni." Na yi shiru Ina kallonsa yayin da gabad'aya ya shiga nutsuwarsa alamun fargaba da tashin hankali sun gama bayyana a fuskarsa.
Na cigaba da ce wa." Hukunci na yanke akanka kai da d'an'uwanka Kamalu za ku bar garin nan gabad'aya rikonku zai koma hannun Hamusu za ku cigaba da ri'ke mini harkokina yanzu shirin da na yi kenan domin tun jiya na gayawa Hamusu halin da ake ciki saboda haka yanzu za mu je tasha tare na sanyaku a mota in sha Allahu rabbi."

Matsananciyar damuwa ya shiga wadda baki ba zai iya misalta irinta ba. Ina kallonsa yana ta ko'karin mayar da hawayen da ya cika kwarmin idonsa amma duk dubararsa sai da ruwan hawayen ya kwaranyo kumatunsa. Murya na rawa ya ce." Mama mai yasa za ki yanke wannan hukuncin, ki dubi Allah da Annabi ki janye kada ki hukuntani akan laifin da ba nawa ba. Ki dubi k'auna da soyayyar da Momi take yi wa jininki kada ki sanya 'yan uwanta su yi mata dariya. Mama ni da Adam akwai k'auna da sha'kuwa sannan ba na so na rabu da Baba, ba zan ta'ba mantawa da hallacinsa a gare ni ba. Sannan Momi tana nan tana yi mana shirye shiryen tafiya karatu saudiya makarantar da Yaya Salim ya yi karatu, ki yi hakuri Mama, kada ki hukunta Momi da laifin da itama ranta yake soyuwa."
Ga'bo'bina ne suka yi sanyi ganin yadda hawaye suke zarya a dakalin fuskarsa. Ya kama hannuna ya ri'ke kamatau jikinsa har karkwarwa yake yi.
Na ce." Yusi ba ka ji wani iri a cikin ranka ba a lokacin da Salim yake yi wa dan'uwanka sharri, abu mafi muni fa ya jingina masa. Da farko ban d'auka abin ya yi tsanani ba na danni zuciyata duk domin a zauna lafiya. Amma Yusi ba abu ne mai wahala ba a yanzu dai na tsaya da Momi da Salim a gaban alkali domin yin shari'a dasu akan wannan mummunan sharrin da Ubangiji ya halakar da wani gari kacokan akan aikatawa. Sai dai na yi hakuri ne bisa abinda uwar rikon naku take aikatawa a kanku na alheri wanda idanu suke gani sanin bad'ini kuma sai Allah. Wannan shine dalilin da ya sanya ni tausar zuciyata akan danne maganar ba tare da na d'auki matakin kare hakkin Kamalu ba. Allah shahidi ne zai bayyana gaskiya da gaggawa. Yusi kana maganar ba za ka iya rabuwa da Baba ba shin zaka iya tuna ubanka Yaya Aminu? ko ka manta dashi ne tunda yanzu ka kasance cikin daula wurin iyayen rikonka har kake ko'karin canza shi a matsayin wanda ya zama 'kashin bayan samar da kai!"
Na yi shiru Ina mayar da hawayen dake ta yun'kurin zuba.
Shi kam kuka yake yi sosai. Cikin rawar murya na ce." Nasan ka manta da shi ko Yusi, ni da nake raye a duniyar ma ka manta da ni to balle babanka wata'kila jin dadi ya sanya ba ka yi masa addu'a tunda ka nunawa duniya ka yi sabbin iyaye."
Hawayen da nake dannewa suka goce da karfinsu duka dinga fafara gudu a kumatuna. Na ri'ke hannunsa da kyau na ce." Ka ture maganar sabo da hallaci da kyautatawa Yusi duka nasan mutanan nan biyu sun yi mini ko da ba don Allah suka yi ba to ni ma ina rokon Allah ya ba ni ikon rama musu, amma ba na ji a zuciyata za a samu zaman lafiya da juna muddin Kamalu da Salim suna zaune inuwa daya kuma a makwanci d'aya. Kun girma da kai dashi ku tafi ku taimakawa kanin babanku ku nemi arziki ta hanyar halak, ina da shaguna da dukiya a hannun Hamusu sai mu 'bullo da hanyoyin nema domin mu gina kanmu da gobenmu, watarana za ku yi aure, za ku hayayyafa a wannan lokacin ya kamata ace kun dogara da kanku Yusi ba wai a ce koyaushe kuna ra'be-ra'be a gidajen mutane ba."
Kuka kashir'ban yake yi yana fad'in." Mama na fahimci azancin ki, na gane abinda ki ke so na gane, amma don Allah Ina neman alfarma a wajanki duk rintsi kada ki yi rigima da Momi wallahi mutuniyar kirki ce, ina kaunarta kamar yadda nake kaunarki Mama, kuma duk abin nan da yake faruwa babu sanya hannunta ko da anti Nusaiba ta dawo muku da yaran nan wallahi bata sani ba lokacin tana bacci da ta tashi ta samu labari wallahi sai da ran anti Nusaiba ya 'baci da kuka ta bar gidan. Ita kanta Momi ta rasa yadda za ta yi da su. Adam ne kawai bai shiga rigimar ba, Yaya Salim da anti Nusaiba sun had'e kansu sun daina jin maganar Momi."
Na ce." Sai ka ce mara hankali Yusi, ba zan yi rigima da ita ba, to akan me? ai ta yi mini alheri, abinda dai nake so da kai shine ka samu nutsuwa ka kuma kwantar da hankalinka, maganar cigaba da karatu kuma ko ba ku fita waje ba sai ku d'ora a bayaro university ku kai matakin da kuke buk'ata in sha Allahu."
Ya rike hannuna yana kuka." Mama zan bi umarninki zan yi abinda kike so muddin hakan zai sanya ki daina wannan kukan. Jin dadi bai sa na mantaku a matsayin iyayena ba. Babanmu duk lokacin da na yi sallah ina yi masa addu'a, ban manta daku ba Mama, ni dan halak ne ban mance wahalar rayuwar da ki ka sha a kanmu ba. Har abada ba zan canza ku ba."
Na sunkuyar da kaina kasa ina tsiyayar da hawaye masu zafi da 'kuna. Gabad'aya duniyar ta gama fita daga raina saboda masifa da tashin hankali.
Tsaf ya goge mini hawayen idona yana fad'in." Ki yi hakuri Mama ki daina yi mana kuka don Allah."
Ban ce komai ba na tashi tsaye shima ya tashi tare da dafa kafadata da hannunsa.

Lokacin da muka fito falo Kamalu da Adam ne a zaune suna magana da sauri yaron ya zame daga kan kujerar da yake zauna yana fad'in."Mama ina kwana mun tashi lafiya?"
A nutse na amsa da kulawa sai ya koma saman kujerar ya zauna jikinsa duk a sanyaye. Hauwa ta fito daga d'aki da tawagar yaran a bayanta tana fad'in." Kun shirya kenan?" Kafin na amsa Adam ya gaisheta ba tare da ta dube shi ba ta amsa kamar ba ta so. Na gyada kaina tare da kallon kamalu da kansa yake sunkuye na ce." Tashi mu tafi."
Baba Tabawa ta fito daga kicin hannuntà ri'ke da madaidaicin baho da dabino a ciki. A nutse muka gaisa kafin na d'ora da fad'in." Baba zan kai yaran nan tasha zuwa kano yanzu zan dawo in sha Allahu."
Ta ce." To shikkenan sai kin dawo Kamalu a gaishe da mini da Gwaggo da kyau sai kun dawo Yusuf." Yadda take magana shi ya sake tabbatar mini da cewa ba ta fahimci nufina ba domin kuwa da ta gane hukuncin da na yanke sai ta yi magana akan hakan.
Adam da sanyi jiki ya dubi Yusi yana cewa." Za ku je kano amma babu labari Yusi babu neman rakiya, ni ma ina so na je na gaisa

Please Login or Register in order to submit comment