Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba ba, na ce." To share hawayenka ka daina kuka ka ajiye abinda yake faruwa a matsayin cigaba, domin kuwa haka siddin ba zaka cimma wata nasara ba tare da kalubale ba. Ita hassadar ai itace matakin komai. Kada ma ka damu, kuma ina mai tabbatar maka da cewa watarana Salim zai bi ka salla, zai kuma nemi fatawa a wurinka, wannan ni ce na gaya maka, domin kuwa ina nan ina roka maka d'aukaka da shura ta fanninin addini anan gidan duniya, Kamalu idan Allah Ya yarda duniya da mutanan dake cikinta za su amfana da kai."
Hannu yasa ya goge hawayen dake zuba a kumatunsa. Na ce." Ka kyale mini komai a hannuna, ka ji ko ka cigaba da hakuri, ni kaina a wannan ga'bar ba zan ha'kura ba dole a yi wani abu kai, amma kada ka nunawa Momi komai, ka bar abin a zuciyarka."
A sanyaye ya ce." Shikkenan Mama, zan yi yadda ki ka ce din, amma ni ina so na koma can kano zan fi samu nutsuwa cigaba da gudanar da neman ilimina."
Na ce." Idan har hakan shine alheri za ka koma Kamalu, ka cigaba da addu'a ka kuma bar maganar tsakanina da kai."
To a daran na nemi maigidan a waya duk da nasan ba sosai yake amsa waya da daddare ba amma yadda nake jin zuciyata ba zan iya bari sai gari ya waye ba. Wayar ta katse bai daga ba sai na yi masa text na cewa ina son magana dashi a duk lokacin da ya ga sakona.
Wajan goma da rabi kuwa ya kira ni da kansa. Na daga muka gaisa a nutse.
Na ce." Baba ina son magana da kai amma kada ka fahimce ni girman Allah da Annabi ka dubeta ta fuskar hankali da maslaha."

A nutse ya ce." To ina jinki ai ni mai hankali ne ba mahaukaci ba, kada dai ki ce mini kin yi 'bari domin kwana biyun nan mafarkai nake yi marasa kan gado, Ina ganin ma farkon watan nan za mu zo."
Na ce." Ban yi 'bari ba, amma ka sani cewa ni da kai ba mu da ikon komai akan abinda Allah Ya zartar. Idan har kaddara ta gifta cikin ya samu matsala ba za ka d'auki kaddara ba kenan?"
Ya ce." Zan d'auka mana, ai mafarkan da nake yi ne ya sanya ki ka ji na yi miki wannan maganar. Na tuba ga Allah duk yadda ya yi daidai ne."

Shiru na yi ina sauraransa har ya gama maganganunsa. Na ce dalili ne mai karfi ya sanya ni kiranka a daran nan, kuma ni kaina zan ji dadin zuwanka domin ka gyara abinda yake faruwa Kamalu ne da Salim....... Duk abinda yake faruwa na zayyane masa. Ya jima yana nanata maganar da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce." Yaushe Salim ya lalace haka, kuma abu ya faru tunda kuruciya saboda rashin hankali ka tara abokai kana gaya musu criminal?" Ya sake maimaita kalmar tabbacin hakan ya bashi tsoro da mamaki.
Na ce." Kamalu ya ce zai koma kano da zama can wurin Hamusu."
Gyaran murya ya yi tare da cewa." Wannan kuma abinda yake cikin ranki ne shekara da shekaru shine ki ka samu mafaka dalilin wannan matsalar. Na gaya miki Amina idan har Kamalu zamansa zai koma kano to Yusi ma zai bi shi. Nusaiba da Salim Adam amana ne a hannuna. Haka zalika tunda ina auranki yaranki ma amana ne a hannuna koda ubansu yana raye to balle kuma baya raye. Idan har kina ganin za ki yi iko da abinki ni ban iya ba sai na ce Allah Ya taimaka."
Na ce." To yanzu ya kake so a yi? Kasan dai cigaba da zaman Kamalu a gidan Momi akwai matsala watarana za su iya yin abinda bai da ce ba."
"Babu abinda zai faru, ki kyaleni da yaran dukkaninsu tunda kin gaya mini kin gama aikinki."
Jiki babu karsashi na ce." Shikkenan sai da safe." Sai kawai na kashe wayar domin kuwa jikina yana ba ni kamar ba zai d'auki tsatstsauran mataki ba.
Da lamarin na kwana na kuma wayi gari dashi dalilin da sanya kenan na kasa barin abin iyakacinmu. Na kira anti Yagana na gaya mata halin da ake ciki. Sosai kuwa ranta ya 'baci ta dinga fad'a tana cewa babu lallai babu dole muddin da cin zarafi da cin mutuncin da kuma tozarci Kamalu dole ya bar gidan. Arziki ai ba hauka ba ne.
Na ce." Anti Yagana tun farko fa ni dama abinda na guda kenan, shiyasa da matar nan ta bukaci zaman Kamalu a wurinta na dinga gocewa. Karin abin kuma maigidan ya'ki ya fahimceni, wai muddin Kamalu zai bar gidan sai dai su tafi da Yusi wanda na tabbatar da cewar hakan matsala ce babba. Da ya zauna mun yi magana da fahimta tuntuni da tun farko wannan matsalar bata kunno kai ba. Abu na biyu kuma ga yanayin bayanin da Kamalu ya yi mini yadda na fahimta shine shi Salim yana adawa da yadda Allah ya d'aukaka Kamalu fiye dashi, ai nasan yaron yana da kirki tun kafin ya tafi karatu dawowarsa al'amura suka lalace kishi ne shi mai yasa Allah bai yi masa ba."
Ta ce." Wannan kuma Ubangiji zai kalubalanta. Wace irin wahala da gwagwarmaya ce Kamalu bai sha ba. Yanzu kuma Ubangiji Allah Ya d'aukaka darajarsa wannan duka ba dabararmu ba ce ikonsa ne, gaskiya a wannan ga'bar ni ma bana goyan bayan mijinki Amina Kamalu dole ya tafi ya bar musu gidansu idan sun ce ba haka ba sai ya dawo hannunki shine karshen magana."

Na ce." Anti Yagana ni na fi so fa ya koma kanon ko ya dawo nan wurinku hankalina zai fi kwanciya gaskiya, domin ai ko yana gidana ba a kashe matsalar ba tunda duk lokacin da ya fita zai iya yin karo da Salim da abokansa kin ga matsalar ai bata mutu ba."
"To ni da kaina zan kira Yallabai din a waya na bashi shawara yadda za a yi. Ta fad'a tana nishin 'bacin rai."
Jin haka ya sanya na ce." Kada ki kira shi yanzu anti Yagana mu bari ya zo mu ga hukuncin da zai yanke idan babu adalci sai ki yi masa magana."
Ta ce." Shikkenan haka za a yi in sha Allah, na manta ma ban gaya miki ba shekaran jiya amaryar Babandi matar da ya aura ta uku ta haihu." A takaice na ce.'' A yi masa barka Allah Ya raya, domin ni yanzu ko lambarsa ma ba ni da ita yadda maigidan ya tsaneshi haka ya tsani mutuwarsa shiyasa na goge lambarsa daga wayata a gabad'aya duk domin a zauna lafiya.
**
Bayan sati biyu al'amura suna cigaba da tafiya da dad'i babu dad'i. Har zuwa lokacin Salim bai kyale Kamalu ba. Kusan kullum da b'acin rai yake shigo mini duk da yana ko'karin daurewa amma ina fahimta. Ha'kurina yana daf da k'arewa domin tun ranar da na kira maigidan a waya na gaya masa abinda yake faruwa bai sake nema na da maganarba duk kuwa da cewa kusan kullum sai mun yi bidiyon call. Ni ma ban sake tayar da maganar ba na bari ne kamar yadda ya ce mu jira zuwansa. Amma koyaushe idan na dubi Kamalu na ga yadda ya rage walwala da kuzari zuciyata takan yi zafi. Ina dalili haka kawai saboda gudun b'acin ran wani a 'kuntata zuciyar yaro. Babu lallai fa babu dole muddin ba zai d'auki mataki ba wallahi sai Kamalu ya tafi ya bar garin da gidan gabad'aya.


Gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ranar litinin da yamma suka sauka shi da Hauwa. Baiwar Allah ta kuma samo wani cikin domin yanayinta kadai ya tabbatar mini da cewa laulayi take yi ta yi mugun haske dama idan tana da ciki d'ashewa take yi. Macace mai kwainika Minal na da wata goma sha takwas. Allah Ya sa tana da san girma, tana yawo da kafafunta da yake abincin gwangwani take ci a can ta zama rusheshiya kataf-kataf haka take yawo uban yana tsokanarta da 'yar sukuta. ko ya kira ta da giwa wai na washeta har ta fi su Hassana girma jiki tunda su jikin irin nasa ne. Kwana biyu da zuwansu na fahimci rashin jituwa a tsakaninsu. Kamar ma basa magana da juna. Na yi dai shiru ina kallon ikon Allah. Ita yini ma take yi a d'aki sai yamma take fitowa falo shi kuma har ya yi kwana biyunsa a wajena bai ce mini komai ba.
Na cika da mamaki sosai. Lallai ma wannan mutumin wato maganar tabi shanun sarki kenan Salim ya yi daidai babu kuskure akan abinda yake yi.
Ba zan lamunta ba domin kuwa har yanzu a cikin matsalar ake sai abinda ma ya yi gaba. Kamalu bai rasa madogara ba hakama Yusi idan har ba zai gyara abinda yake faruwa ba to na yarda ya ba ni yarana su kuma can hannun Babansu Hamusu.
Cikin wannan nazarin Hauwa ta shigo d'akina ta same ni. Ta zauna gefan gado tana fad'in." Ko jikin ne?" Na tashi zaune Ina fad'in." A, a ni kam ai na warware na bar miki Hauwa."
Kwafa ta yi tare da cewa." Ban ji dad'in shigar cikin nan ba wallahi.''
Na dubeta a tsanake tare da cewa." Mai yasa Hauwa ki godewa Allah da fatan samun masu albarka."
"Humm!" abinda ta ce kenan kafin ta ce." Ban shigo domin na tunzuraki ko tayar da husuma ba. Idan kin lura da yanayin yadda muka zo da ni da maigidan babu dadi don wallahi mugun haushinsa nake ji fad'a muka casa tun a can."
Na ce." Menene kuma ya kamata ki manta da matsalar matar nan Hauwa, ki yi ta kanki haihuwa ta uku za ki yi da mutumin nan duk abinda zai yi ya je ya yi haka ya ga zai iya."

"Wallahi Amina ko kaffara ba zan yi ba matar nan ba haka ta bar mutumin nan ba."
"Mai yasa ki ka ce haka Hauwa, zato zunubi ne fa koda ya kasance gaskiya ne?"
"Amina maganar gaskiya zan gaya miki na gaji da zaman nan da muke yi na rashin 'yanci da kaskanci wallahi tallahi ba zan jiya jure ba, wannan shine dalilin ma da ya sanya ki ka ji na ce ina b'akinciki da takaicin samuwar wannan cikin na jikina, in banda ina gudun sa'bawa Allah wallahi da sai na zubar da shi.......

*Rikicin gidan Alh Tajo sai dai na ce Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi bari mu ya ya zata kaya....*
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*83*
Na ce." Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na amana. Kuma wallahi a yanzu ni Amina Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda za a had'a kai dashi a k'yamaci abina, ba na daukarsa a matsayin masoyi babban ma'kiyi nake kallonsa."

Da wani irin yanayi a tare da shi ya furta." Idan na fahimce ki kenan kina kallona a matsayin ma'kiyinki wanda ya za'bi Maryam da 'ya'yanta ko Amina."
Na ce." K'warai kuwa wallahi tallahi ba ka cikin jerin masoyana tunda har ka iya yadda da cewa Kamalu zai aikata wannan mummunan lamarin. Ba na yi maka kallon masoyi."
Ya jima yana kallona kafin ya gyad'a kansa ya nufo ni, na kuwa zabura domin kallon dodo nake yi masa na ce." Kada ka zo inda nake na rantse da Allah zan illataka."
Bai daina tafiya ba har sai da ya cimmani zai ri'ke hannuna na fizge da sauri na wancakal da nasa hannun cikin zafin nama na yi wajan madubina na zari wata doguwar kwalba ta turare na ri'ke a hannuna. Ya sake nufo ni yana fad'in." To illatani kin ji, na ce ki illatani tunda kin 'ki tsayawa mu fahimci juna. Da k'araji na ce." Har abada na sake aminta da maganar munafiki."
Ya 'bata fuska ainun yana fad'in." Kada kuma ki wuce gona da iri, kin naushe ni a ma'karfafata d'azu na kyale ki yanzu kuma kina kira na da munafiki ranki zai b'aci fa ba ni son rashin hankali."
Na ce." Ya 'baci ma ai ba tsoro nake yi ba, menene karshen hukuncin shine saki ko to ka sake ni kaga yadda ake liyafa ai ni kassara mini rayuwata ka yi zama dakai bai amfanar da ni komai ba."
Ya kuwa 'kadu da wannan furucin ya ce." Har yaran da muka haifa ba su da amfani?" Na ce." E, ai ba nawa ba ne tunda ka d'aukesu ka bawa bushshiyar matarka nata ne taje na bar mata."
Ya dinga kallona da mamaki mai yawa kafin ya sake tunkaro ni a karo na biyu na daga abinda yake hannuna zan buga masa ya yi saurin ri'ke hannun tare da k'wacewa. Muka yi cirko cirko a tsaye shima nishin yake yi kamar yadda nake yi kamar wanda ya yi tsere. Mun jima haka ya ri'ke ni katamau na ja tsaki tare da yun'kurin bangaje shi ya riko kafadata jikinsa duk ya yi la'asar. Na ce ka cika ni na gaya maka
na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu

"Ba ki da hankali har yanzu ko Amina?"
Na ce." E, ba ni dashi tunda kai din shine da kai." Murmushi ya yi ya girgiza kansa yana fad'in." Ke kam kin ci sa'a ina sonki ina ga da babu wannan da tuni mun rabu baram-baram, iskanciki da rashin kunyarki ya ishe ni. Yanzu ni ne mara hankali Amina baki da kunya ba ko."
Juyar da kaina gefe na yi ban ce komai. Sai ya girgiza kansa a nutse ya fara ko'karin jan hannuna yana fad'in." Zo mu je mu zauna domin mu tattauna."

"Ba zan zauna ba domin ba ni son had'a numfashina da kai." Na fad'a tare da buge hannunsa da yake jana. Sai kuwa ya sanya mini karfi ban ankara don kamar tanka'dani ya yi na fadi a da'bas a wurin. Kafin na yun'kura na tashi ya cimmani ya sake tura kirjina da k'arfi na kwanta kaina ya tallafo kawai yasa bakinsa a nawa ya dinga d'ura mini yawun bakinsa ba don ya ji dad'i ko don na ji yake kiss din bakina ba domin ya sanya mini yawunsa ne. Tsayin minti hud'u zuwa biyar ya cire bakinsa tare da tashi tsaye ya tsaya a kaina yana kallona idonsa ya kada sosai da tsantsar tashin hankali a cikinsu.
Na tashi zaune hawaye masu d'umi suna silalowa daga idona. Kamar mai koyon tafiya haka na dinga jan k'afa ina kuka na isa gefan gado na zauna kamar an kwad'e mini gwiwata da tabarya lallai Allah Ya jarrabeni da shu'umin mutum.
Ya biyo ni shima kamar wanda aka kuzawa ruwan sanyi jikinsa duk a sanyaye. Yana zama a gefena na yi kukan kura cikin wani yanayi na bazata na sake kai masa naushi a kirjinsa ya kuwa yi kwanciyar da bai shirya ba na zabura da sauri na d'auki fillo na raba k'afafuna akan ruwan cikinsa na danna masa fillon a hancinsa ina ihun nake fad'in." Sai na kashe ka wallahi, na yarda ni ma a kashe ni, ni ce ajalinka tunda ba zaka bari na huta ba."
Fad'a sosai muka dinga yi tiki tiki yana yun'kurin tashi ina sake turmushe shi nauyina gabad'aya na saki a kansa ina kuka. Cikin tashin hankali da nishi tare da fitowar numfashi ya fizge a guje ya dira daga gadon yana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Bai fita ba yana tsaye a bakin kofar d'akin ya ki'dime sosai ko da ya ga na sake durfafoshi bai yi yun'kurin bude kofar ya fita ba. Ina isa kuwa ya kama ni da karfin da ban san yana da shi ba. Cikin rawar murya da tsananin damuwa yake fad'in." Yi ha'kuri, ki yi hakuri na ji na yi lefi, amma ki fahimce ni ki bari na gaya miki abinda yake zuciyata kafin ki kashe ni din."
Na yi shiru hawaye na fita daga idona, ina jan hanci na ce ." Wallahi ba zan sake yadda yarana su zauna a hannunka ba" Ya ce."
" Ki fahimce ni Amina, ban za'bi bangare daya na ajiye daya ba. Ni kaina lamarin ya sanya ni a rud'ani ba kad'an ba. Shirun kuma da na yi ba ina nufin na goyi da bayan maganar Salim ba. Ina bincike ne da kuma hanyar da zan kawo gyara. Akwai nauyi mutuka da gaske na tunkareki da maganar nan. Akwai kunya na titsiye yaron nan Kamalu ina neman hujja akan maganar Salim. Kada ki zarge ni bayan ba ki san menene a zuciyata ba.

"Na gaya maka wallahil-azim ba zan yarda da kanzon kurge ba. A wannan ga'bar ko ni ko kai, Kamalu da Yusi fa ba su rasa madogara ba. Sannan Ubansu ba makwad'aici ba ne, ba mazinaci ba ne, sannan ba b'arawo ba ne. Banga dalilin da zai sanya a dinga jingina musu manya manyan sharri ba. Ban nemi ka rike mini yara ba. Haka zalika ma ban nemi matarka ta ri'ke mini yarana ba. A ba ni kayana mana dole ne, zan iya rikesu mu rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."

"To ni kuma muddin a karkashin ikona ki ke yaran nan babu inda za su je muna tare har abada, tunda ina tare dake ni ba zan iya rabuwa dake ba."
Na dube shi ina gyada kaina na ce." Haka ka ce ko?''
"Kwarai kuwa, haka na ce, sai ki yi duk abinda za ki yi tunda ke ba za ki rarrasu ba.
"Zan kuwa yi, ai ba kai ka haifar mini su, baka da wani ji'bi dasu don haka baka da hujjar da zakace dole sai ka rikesu anan zan nuna maka karfin ikona."
Ya ce." Sai ki nuna din ina jiranki..'' Daga haka ya cika ni tare da jan tsaki ya juya ya fita yana fad'in." Sakarai kawai kullum kina girma kina cin tasono."
Silalewa na yi a k'asan d'akin na yi zaman dirshan na dinga tikar kuka. An dake ni an hana ni kuka kuma an bi ni da bakar magana. Wace irin masifa ce wannan mutum bai haifi yara ba ya ce lallai sai ya rike su.
Ina cikin wannan yanayin Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta idonta jawur! Na tashi tsaye da sauri Ina kallonta gabana na fad'uwa. Minal ta dire mini a gabana tana fad'in.'' Ga takwararki nan Amina ubanta ya ce na tafi gidanmu."
Cikin kad'uwa da muguwar fargaba na ce." Ki tafi gidanku akan wane dalili Hauwa?"
"Saboda na gaya miki abinda yake faruwa." Ta fad'a tana juyawa da niyyar fita. Na bita da sauri yayin da Minal din ta tawo kataf katafi ta rike gefan hijabinta tana kuka. Na ce." Shine kuma ke sai ki tafi."
"To dama ai kamar akan 'kaya nake wallahi na gaya miki a gajiye nake." Na ce." Ita Minal din mai tayi miki to?"
"Cewa ya yi na ajiye masa yarinya."
Wani takaici ya yun'kuro mini lallai Alhaji Amadu ya mutu ya bar baya da k'ura. Iyalinsa na nema su tarwatsawa aminin nasa rayuwa. Na tabbatar da cewa ba kowane ya janyo wannan hayaniyar ba sai Salim.
Na ce." Yana ina maigidan?"
"Shi ya sani.'' Ta fad'a a takaice tare da sake nufar hanyar fita. Na ri'ke hannunta ina fad'in." Babu fa inda za ki je Hauwa."
Dariya ta yi irin ta takaici ta ce." Ai ba ke ki ke aurena ba Amina, maigida ya ce na fitar masa daga gida zaman me zan yi."
Jan hannunta na yi muka zauna kan gado na dau'ki Minal na d'ora mata a cinyarta sannan na d'auki wayata. Kiransa na yi bugun farko ya d'aga kamar yana jira.


Littafin nan na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba

Na ce." Yanzu kai don girman Allah ba ka ji kunya ba, tsofai tsofai da kai kake aikata irin abun yara?"
"Mai na yi kuma? Ke ba kya jin nauyin furta mini maganar da duk ranki ya so ko Amina?''
Na ce." Hauwa dai ko babu aure tana da 'yancin zama na dindindin a gidanka, to balle bayan wannan alakar akwai ta aure da zuria a tsakaninku, da ka ce ta tafi gida kai ba ka ji nauyi ba?"
"Bata da wani 'yancin zama a gidana sai na so, tunda ba ta ji nauyin shure maganata ba, ni ma babu wani nauyinta da zan ji, kuma ina ruwanki matarki ce?"
'Dan sassautawa na yi domin kuwa ba zan so a ce dalilina sun samu matsala ba. Na ce." Idan saboda ta gaya mini wannan maganar nan ya sanya har ka yanke mata wannan hukuncin ka yi hakuri ka ji."
Shiru ya yi bai ce uffan ba. Na ce." Ka janye abinda ka kudirta akanta domin kuwa sam bai dace ba."
"Kin yarda ta yi ba daidai ba yanzu?"
Shiru na yi ban ce komai ba. Ya sake maimaita maganarsa nan ma ban ce masa komai ba. Ya ce." To tunda bakinku daya kin ga kuwa babu amfanin zama da macan da bata buk'atar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hauwa kawai ta tafi gidansu kafin na gama yanke hukunci ta san matsayinta, tunda har za ki iya d'aukar fillo ki toshe mini hanci don na mutu ai lamarin babban ne a wurina Hauwa ta samu nasarar tayar mini da husuma ni kuma zan d'auki matakin da ya dace a kanta."
Gwiwa a sanyaye na kashe wayar ina kallonta babu damuwa a tare da ita tace." Ai na gaya miki Amina mutumin nan kaf dabi'unsa sun canza muddin akan lamarin matarsa ne yakan iya cin mutuncin kowa."
Na ce." Babu da inda za ki je." Ta yi shiru tana kallona ina laluban wayar Hajja bugu daya ta daga. Cikin rawar murya na gaisheta ta amsa tana fad'in duk kuna nan lafiya ko Amina."
Na ce." Lafiya lau Hajja don Allah ki yi masa magana matsala suka samu da Hauwa shine ya ce wai ta tafi gida."
cike da mamaki ta furta." Hauwa ta tafi gida akan wane dalili?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Cike da kulawa ta ce." Amina ki gaya mini menene yake faruwa kin ji ko kada ki rufe mini komai.''
Hawaye suka silalo mini na ce." Hajja Hauwa ba ta yi masa komai ba wallahi, asalima ma matsalar ni ta shafa saboda kawai ta gaya masa gaskiya shikkenan yake jin haushinta."
Ta ce." To gaya mini wace matsala ce, ni zan yi maganinta, Hauwa kuma ki gaya mata kada ta fito."
"In sha Allah, gata nan a kusa da ni, na hana ta fitowa."
"To hakan ya yi ina sauraranki." Tafad'a cikin nuna damuwa. A nutse na fara gaya mata tun daga farko abinda yake faruwa har zuwa yanzu da ake wannan rikicin.

Hajja ta jima cikin alhini da takaici kafin ta ce." Ki yi hakuri a matsayinki na babba kuma uwa. Amina tabbas ko ba ki fad'a ba nasan idan za a tona zuciyarki to tanan cikin kunci da b'acin ran wannan lamari. Ki jure lallai kuma ya zama dole a yi wa tufkar hanci saboda gudun abinda zai afku anan gaba na rashin dadi. Zan nemi shi zai kuma zo nan inda nake akan maganar nan domin ni kaina ban yarda da hakan ba. Sannan duk abinda zai yi muku kada ku saurareshi. Ki jadaddawa Hauwa cewa da yawuna ban amince ta fito ba. Ke kuma ki yi hakuri kin ji ko, nasan abinda da ciwo a zucci amma in sha Allahu gaskiya za ta bayyana kanta.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*83*
Na ce." Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na

Please Login or Register in order to submit comment