Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amana. Kuma wallahi a yanzu ni Amina Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda za a had'a kai dashi a k'yamaci abina, ba na daukarsa a matsayin masoyi babban ma'kiyi nake kallonsa."

Da wani irin yanayi a tare da shi ya furta." Idan na fahimce ki kenan kina kallona a matsayin ma'kiyinki wanda ya za'bi Maryam da 'ya'yanta ko Amina."
Na ce." K'warai kuwa wallahi tallahi ba ka cikin jerin masoyana tunda har ka iya yadda da cewa Kamalu zai aikata wannan mummunan lamarin. Ba na yi maka kallon masoyi."
Ya jima yana kallona kafin ya gyad'a kansa ya nufo ni, na kuwa zabura domin kallon dodo nake yi masa na ce." Kada ka zo inda nake na rantse da Allah zan illataka."
Bai daina tafiya ba har sai da ya cimmani zai ri'ke hannuna na fizge da sauri na wancakal da nasa hannun cikin zafin nama na yi wajan madubina na zari wata doguwar kwalba ta turare na ri'ke a hannuna. Ya sake nufo ni yana fad'in." To illatani kin ji, na ce ki illatani tunda kin 'ki tsayawa mu fahimci juna. Da k'araji na ce." Har abada na sake aminta da maganar munafiki."
Ya 'bata fuska ainun yana fad'in." Kada kuma ki wuce gona da iri, kin naushe ni a ma'karfafata d'azu na kyale ki yanzu kuma kina kira na da munafiki ranki zai b'aci fa ba ni son rashin hankali."
Na ce." Ya 'baci ma ai ba tsoro nake yi ba, menene karshen hukuncin shine saki ko to ka sake ni kaga yadda ake liyafa ai ni kassara mini rayuwata ka yi zama dakai bai amfanar da ni komai ba."
Ya kuwa 'kadu da wannan furucin ya ce." Har yaran da muka haifa ba su da amfani?" Na ce." E, ai ba nawa ba ne tunda ka d'aukesu ka bawa bushshiyar matarka nata ne taje na bar mata."
Ya dinga kallona da mamaki mai yawa kafin ya sake tunkaro ni a karo na biyu na daga abinda yake hannuna zan buga masa ya yi saurin ri'ke hannun tare da k'wacewa. Muka yi cirko cirko a tsaye shima nishin yake yi kamar yadda nake yi kamar wanda ya yi tsere. Mun jima haka ya ri'ke ni katamau na ja tsaki tare da yun'kurin bangaje shi ya riko kafadata jikinsa duk ya yi la'asar. Na ce ka cika ni na gaya maka
na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu

"Ba ki da hankali har yanzu ko Amina?"
Na ce." E, ba ni dashi tunda kai din shine da kai." Murmushi ya yi ya girgiza kansa yana fad'in." Ke kam kin ci sa'a ina sonki ina ga da babu wannan da tuni mun rabu baram-baram, iskanciki da rashin kunyarki ya ishe ni. Yanzu ni ne mara hankali Amina baki da kunya ba ko."
Juyar da kaina gefe na yi ban ce komai. Sai ya girgiza kansa a nutse ya fara ko'karin jan hannuna yana fad'in." Zo mu je mu zauna domin mu tattauna."

"Ba zan zauna ba domin ba ni son had'a numfashina da kai." Na fad'a tare da buge hannunsa da yake jana. Sai kuwa ya sanya mini karfi ban ankara don kamar tanka'dani ya yi na fadi a da'bas a wurin. Kafin na yun'kura na tashi ya cimmani ya sake tura kirjina da k'arfi na kwanta kaina ya tallafo kawai yasa bakinsa a nawa ya dinga d'ura mini yawun bakinsa ba don ya ji dad'i ko don na ji yake kiss din bakina ba domin ya sanya mini yawunsa ne. Tsayin minti hud'u zuwa biyar ya cire bakinsa tare da tashi tsaye ya tsaya a kaina yana kallona idonsa ya kada sosai da tsantsar tashin hankali a cikinsu.
Na tashi zaune hawaye masu d'umi suna silalowa daga idona. Kamar mai koyon tafiya haka na dinga jan k'afa ina kuka na isa gefan gado na zauna kamar an kwad'e mini gwiwata da tabarya lallai Allah Ya jarrabeni da shu'umin mutum.
Ya biyo ni shima kamar wanda aka kuzawa ruwan sanyi jikinsa duk a sanyaye. Yana zama a gefena na yi kukan kura cikin wani yanayi na bazata na sake kai masa naushi a kirjinsa ya kuwa yi kwanciyar da bai shirya ba na zabura da sauri na d'auki fillo na raba k'afafuna akan ruwan cikinsa na danna masa fillon a hancinsa ina ihun nake fad'in." Sai na kashe ka wallahi, na yarda ni ma a kashe ni, ni ce ajalinka tunda ba zaka bari na huta ba."
Fad'a sosai muka dinga yi tiki tiki yana yun'kurin tashi ina sake turmushe shi nauyina gabad'aya na saki a kansa ina kuka. Cikin tashin hankali da nishi tare da fitowar numfashi ya fizge a guje ya dira daga gadon yana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Bai fita ba yana tsaye a bakin kofar d'akin ya ki'dime sosai ko da ya ga na sake durfafoshi bai yi yun'kurin bude kofar ya fita ba. Ina isa kuwa ya kama ni da karfin da ban san yana da shi ba. Cikin rawar murya da tsananin damuwa yake fad'in." Yi ha'kuri, ki yi hakuri na ji na yi lefi, amma ki fahimce ni ki bari na gaya miki abinda yake zuciyata kafin ki kashe ni din."
Na yi shiru hawaye na fita daga idona, ina jan hanci na ce ." Wallahi ba zan sake yadda yarana su zauna a hannunka ba" Ya ce."
" Ki fahimce ni Amina, ban za'bi bangare daya na ajiye daya ba. Ni kaina lamarin ya sanya ni a rud'ani ba kad'an ba. Shirun kuma da na yi ba ina nufin na goyi da bayan maganar Salim ba. Ina bincike ne da kuma hanyar da zan kawo gyara. Akwai nauyi mutuka da gaske na tunkareki da maganar nan. Akwai kunya na titsiye yaron nan Kamalu ina neman hujja akan maganar Salim. Kada ki zarge ni bayan ba ki san menene a zuciyata ba.

"Na gaya maka wallahil-azim ba zan yarda da kanzon kurge ba. A wannan ga'bar ko ni ko kai, Kamalu da Yusi fa ba su rasa madogara ba. Sannan Ubansu ba makwad'aici ba ne, ba mazinaci ba ne, sannan ba b'arawo ba ne. Banga dalilin da zai sanya a dinga jingina musu manya manyan sharri ba. Ban nemi ka rike mini yara ba. Haka zalika ma ban nemi matarka ta ri'ke mini yarana ba. A ba ni kayana mana dole ne, zan iya rikesu mu rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."

"To ni kuma muddin a karkashin ikona ki ke yaran nan babu inda za su je muna tare har abada, tunda ina tare dake ni ba zan iya rabuwa dake ba."
Na dube shi ina gyada kaina na ce." Haka ka ce ko?''
"Kwarai kuwa, haka na ce, sai ki yi duk abinda za ki yi tunda ke ba za ki rarrasu ba.
"Zan kuwa yi, ai ba kai ka haifar mini su, baka da wani ji'bi dasu don haka baka da hujjar da zakace dole sai ka rikesu anan zan nuna maka karfin ikona."
Ya ce." Sai ki nuna din ina jiranki..'' Daga haka ya cika ni tare da jan tsaki ya juya ya fita yana fad'in." Sakarai kawai kullum kina girma kina cin tasono."
Silalewa na yi a k'asan d'akin na yi zaman dirshan na dinga tikar kuka. An dake ni an hana ni kuka kuma an bi ni da bakar magana. Wace irin masifa ce wannan mutum bai haifi yara ba ya ce lallai sai ya rike su.
Ina cikin wannan yanayin Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta idonta jawur! Na tashi tsaye da sauri Ina kallonta gabana na fad'uwa. Minal ta dire mini a gabana tana fad'in.'' Ga takwararki nan Amina ubanta ya ce na tafi gidanmu."
Cikin kad'uwa da muguwar fargaba na ce." Ki tafi gidanku akan wane dalili Hauwa?"
"Saboda na gaya miki abinda yake faruwa." Ta fad'a tana juyawa da niyyar fita. Na bita da sauri yayin da Minal din ta tawo kataf katafi ta rike gefan hijabinta tana kuka. Na ce." Shine kuma ke sai ki tafi."
"To dama ai kamar akan 'kaya nake wallahi na gaya miki a gajiye nake." Na ce." Ita Minal din mai tayi miki to?"
"Cewa ya yi na ajiye masa yarinya."
Wani takaici ya yun'kuro mini lallai Alhaji Amadu ya mutu ya bar baya da k'ura. Iyalinsa na nema su tarwatsawa aminin nasa rayuwa. Na tabbatar da cewa ba kowane ya janyo wannan hayaniyar ba sai Salim.
Na ce." Yana ina maigidan?"
"Shi ya sani.'' Ta fad'a a takaice tare da sake nufar hanyar fita. Na ri'ke hannunta ina fad'in." Babu fa inda za ki je Hauwa."
Dariya ta yi irin ta takaici ta ce." Ai ba ke ki ke aurena ba Amina, maigida ya ce na fitar masa daga gida zaman me zan yi."
Jan hannunta na yi muka zauna kan gado na dau'ki Minal na d'ora mata a cinyarta sannan na d'auki wayata. Kiransa na yi bugun farko ya d'aga kamar yana jira.


Littafin nan na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba

Na ce." Yanzu kai don girman Allah ba ka ji kunya ba, tsofai tsofai da kai kake aikata irin abun yara?"
"Mai na yi kuma? Ke ba kya jin nauyin furta mini maganar da duk ranki ya so ko Amina?''
Na ce." Hauwa dai ko babu aure tana da 'yancin zama na dindindin a gidanka, to balle bayan wannan alakar akwai ta aure da zuria a tsakaninku, da ka ce ta tafi gida kai ba ka ji nauyi ba?"
"Bata da wani 'yancin zama a gidana sai na so, tunda ba ta ji nauyin shure maganata ba, ni ma babu wani nauyinta da zan ji, kuma ina ruwanki matarki ce?"
'Dan sassautawa na yi domin kuwa ba zan so a ce dalilina sun samu matsala ba. Na ce." Idan saboda ta gaya mini wannan maganar nan ya sanya har ka yanke mata wannan hukuncin ka yi hakuri ka ji."
Shiru ya yi bai ce uffan ba. Na ce." Ka janye abinda ka kudirta akanta domin kuwa sam bai dace ba."
"Kin yarda ta yi ba daidai ba yanzu?"
Shiru na yi ban ce komai ba. Ya sake maimaita maganarsa nan ma ban ce masa komai ba. Ya ce." To tunda bakinku daya kin ga kuwa babu amfanin zama da macan da bata buk'atar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hauwa kawai ta tafi gidansu kafin na gama yanke hukunci ta san matsayinta, tunda har za ki iya d'aukar fillo ki toshe mini hanci don na mutu ai lamarin babban ne a wurina Hauwa ta samu nasarar tayar mini da husuma ni kuma zan d'auki matakin da ya dace a kanta."
Gwiwa a sanyaye na kashe wayar ina kallonta babu damuwa a tare da ita tace." Ai na gaya miki Amina mutumin nan kaf dabi'unsa sun canza muddin akan lamarin matarsa ne yakan iya cin mutuncin kowa."
Na ce." Babu da inda za ki je." Ta yi shiru tana kallona ina laluban wayar Hajja bugu daya ta daga. Cikin rawar murya na gaisheta ta amsa tana fad'in duk kuna nan lafiya ko Amina."
Na ce." Lafiya lau Hajja don Allah ki yi masa magana matsala suka samu da Hauwa shine ya ce wai ta tafi gida."
cike da mamaki ta furta." Hauwa ta tafi gida akan wane dalili?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Cike da kulawa ta ce." Amina ki gaya mini menene yake faruwa kin ji ko kada ki rufe mini komai.''
Hawaye suka silalo mini na ce." Hajja Hauwa ba ta yi masa komai ba wallahi, asalima ma matsalar ni ta shafa saboda kawai ta gaya masa gaskiya shikkenan yake jin haushinta."
Ta ce." To gaya mini wace matsala ce, ni zan yi maganinta, Hauwa kuma ki gaya mata kada ta fito."
"In sha Allah, gata nan a kusa da ni, na hana ta fitowa."
"To hakan ya yi ina sauraranki." Tafad'a cikin nuna damuwa. A nutse na fara gaya mata tun daga farko abinda yake faruwa har zuwa yanzu da ake wannan rikicin.

Hajja ta jima cikin alhini da takaici kafin ta ce." Ki yi hakuri a matsayinki na babba kuma uwa. Amina tabbas ko ba ki fad'a ba nasan idan za a tona zuciyarki to tanan cikin kunci da b'acin ran wannan lamari. Ki jure lallai kuma ya zama dole a yi wa tufkar hanci saboda gudun abinda zai afku anan gaba na rashin dadi. Zan nemi shi zai kuma zo nan inda nake akan maganar nan domin ni kaina ban yarda da hakan ba. Sannan duk abinda zai yi muku kada ku saurareshi. Ki jadaddawa Hauwa cewa da yawuna ban amince ta fito ba. Ke kuma ki yi hakuri kin ji ko, nasan abinda da ciwo a zucci amma in sha Allahu gaskiya za ta bayyana kanta.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=L
*87*
Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi. na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Kai mu jabi park."
Cike da bin umarni ya ce." An gama.
Motar ta yi shiru ni da yaran duka muna cike da zullumi mussaman Yusi da nake hankalce dashi yana goge hawaye a fakaice. Ban tsawatar masa ba domin kuwa ban san mai yake ji a zuciyarsa ba, amma zahiri wannan shine iya gatan da nake ganin zan yi musu a duniya. Ba zai yiwu a ce koyaushe rayuwarsu ta kasance cikin kyara da hantara ba. Sun fara kaiwa munzali na girma a wannan lokacin ya kamata ace mun had'u ni dasu mun gina gobe dalili watarana za su yi aure su tara iyali suma. Sannan zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar ganinsu cikin kaskanci ba, arziki Allah ne yake bayarwa su fita su nema kowa ya tsaya da k'afafunsa.
Cikin ikon Allah motar dana sanya su ta yi lodi saura bai fi mutum hud'u ba. Cike da dauriya da ko'karin kara musu kwarin gwiwa muka yi sallama na ce lallai idan sun sauka Kamalu ya kira ni tunda da waya a hannunsu.
Ban gushe daga wurin ba har sai da na tabbatar da tashin motarsu sannan na sauke ajiyar zuciya na gyara zaman nikab din da yake fuskata tunda ban fito ba sai da na sunkufe jikina ta ko'ina dalili ba na so a gane wata ala'ka da za a yi yamadidi da ni, kuma safiya ce tashar babu wadatar mutane da yawa sosai.
Kai tsaye na nufi wajan da Masa'udu ya ajiye mota.
Yana ganina ya taso daga inda yake ya bud'e mini na shiga na zauna sai a lokacin na ji wasu gagariman hawaye masu radad'i sun k'wace mini. Wato ni kuma haka kaddarata take, ina ro'kon Allah Ya ba ni ikon cinyeta ya kuma saukakawa yaran nan rayuwa ya basu hakurin maraici.
Ina komawa gidan na samu Hauwa da Momi zaune a falo, amma babu cikakkiyar sakewa a tsakaninsu Hauwa ta yi zaman gadara da ki ce kule na ce miki cass domin kuwa fuskarta tamkar kunun tsamiyar da ya kwana a rufe. Kusan a tare suka amsa sallamata.
Kwarai da gaske na yi kokarin danne abinda nake ji a zuciyata game da al'amuran dake faruwa. Na nemi wuri na zauna babu yabo babu fallasa nake kallonta ina sake nazari akan al'amuranta. Ta tsuke sosai ta yi fayau abinka da mara jiki da gasken ne bata da lafiyar domin alamu sun nuna babu wani kuzari da karsashi a tare da ita.
Ita ta fara gaishe ni a tsanake na amsa ido na a kanta ina sauraran abinda take tafe dashi ta gyara zamanta kad'an tana kallona sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali
Ta ce." Amina na shigo nan ne saboda ke domin mu tattauna abubuwan dake faruwa da yaranmu, Allah Ya ga zuciyata ban shigo cikin rayuwarku da wata niyya ta cutarwa ba, kuma ban had'a kai da Salim domin ya ci mutuncin Kamalu ba, asali ma abinda yake aikatawa ba ni da masaniya sai bayan ya aikata din nake samun labarin." Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya a karo na biyu kafin ta cigaba da cewa."
Yana da kyau a matsayinki na uwa mai hankali ki yi nazari mai kyau Amina idan hankali ya 'bata fa nutsuwa da dattako ake sanyawa domin nemansa bai kamata ace kin d'auki munanan shawarwarin da ba za su zama silar gyar........Hauwa ta katse ta cikin fusata." tana fad'in "Ai dama ban ce kin shigo gidan nan domin ni ba Maryam, ko kuma kin ji na ce miki kin shigo ne da mummunar niyya. Kin tsargu ashe ai shi mara gaskiya dama kullum cikin zullumi Hajajju ki dube ni da kyau ki ga ni, a waye nake k'warai babu wata kinaya da za ki yi mini kafin ki san Amina da yaranta ni na santa na kuma zauna da ita. Idan har mijinki ya gaya miki cewa da hannuna wurin matakin da Kamalu ya d'auka bai yi miki k'arya ba, ga ni a zaune ai ina jiran hukunci tunda ku kun iya take gaskiya da gangan."
Cikin rashin sukuni na ce." Hauwa menene don Allah, duk cikinmu nan babu yaro karami tunda har ta shigo domin mu tattauna magana dan samun daidaito bai kamata wasu maganganu mara dad'i su biyo baya ba kuma."

Ta ja dogon tsaki tana fadin
"Kina jin irin jirwayen da take yi mini ai, ai mu 'yan iska ne marasa 'yancin kai tunda mijinta haka ya nuna mata ba mu da mutunci da kima sannan ba mu da sirri komai muka yi a tambad'e ita nata sirri koyaushe cikin danda'be shi yake baya so kowa ya ji. Bazan jure d'aukar cin kashi daga 'bangaranta ba wallahi tallahi."
A nutse ta ce." Ba halina ba ne raina mutum Hauwa, kuma kamar yadda ki ke hasashe hakane maigidan ya gaya mini komai ke ce ki ke ko'karin ganin lallai sai an yi 'batacciya domin kuwa abinda muke ta bunnewa dalilin gudun rikici mai muni ke ki ka gayawa mahafiyar yaron nan, kuma ki ka cire nauyi da kunya ki ka dubi tsabar idon yaron nan Kamalu ki ka gaya masa to kin fad'a kin ji dadi kuma in sha Allahu abinda ki ke fata ba zai faru ba da izinin Allah."

Hauwa ta mike tsaye tana huci ta ce." Kin yarda yaronki mahassadi ne, kuma sharri ya yi wa Kamalu ko ba ki yarda ba, ke yanzu don girman Allah ba ki ji kunya da nauyi ba
ai ita karya fure take bata 'ya'ya wallahi ni dai Hauwa Maryam ba ki isa ki siye ni da kudi da abin duniya ba. Wannan gingimeman sharri da d'anki ya alak'anta marayan Allah dashi saboda rashin adalci da son zuciyarku sai ku ja baki ku yi shiru babu wani mataki da ku ka d'auka. Sannan kuce ba za a yi magana ba, to ni na sayi rikicin don girman Allah ki d'auki mataki a kaina. Kenan wannan ya nuna kun sake bawa yaron lasisin ci gaba da aikata abinda yake yi dalili kun nuna masa akan daidai yake, ke da mijinki kun daure masa gindi saboda kun tara abin duniya kuna ganin kun fi karfin hukuma ko? to ku d'aukaka k'ara don Allah allura ce zata tono garma menene ba mu sa ni ba Maryam na fad'a din idan ta yi miki zafi ki kaini 'kara ko kisa tsinken tsire ki tsire ni!"

Na tashi tsaye da sauri
na tare ta tare da mayar da ita kan kujera na zaunar sai huci take yi tabbacin a fusace take kuma a shirye take da duk abinda zai faru.
Hayaniya ta fito da Baba Tabawa daga kicin tana fad'in." Mai yake faruwa ne don Allah ku yi aiki da hankali da girman shekarunku kada hayaniyarku ta d'auki hankalin yaranku k'ananu har su fahimci abinda yake faruwa, kun san dai yaro da ri'ke abu a zuciyarsa...

Littafin gudun aure na kudi ne, don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Cikin numfasawa Hauwa ta koma ta zauna tana huci! ita kuma Momi ta yi 'kasa da kanta k'walla cike a kwarmin idonta. Alamu sun nuna cewa ba ta iya fad'a na cacar baki ba koda fad'ansu ya yi tsayi da Hauwa ita za ta kaita kasa.
Har cikin zuciyata ban ji dad'in abinda ta yi mata ba duk da cewa duka su biyun ban san menene a cikin zuciyoyinsu ba don haka ba daidai ba ne abinda ta yi tsinka na k'asa da kai ma tozarci ne ballantana wanda yake sama da kai ashekaru. Ni da ita duka haihuwa ce ta janyo mana domin kuwa da yara ba su had'a ba ina ganin babu wani dalili da zai sanya na yi sa'insa da ita akan namijin da ba shi da wani tabbas. Tun farko itama Hauwan da ta d'auki shawarata abinda yake yi akan matarsa ba zai dameta ba tunda ta san tafi amfanarshi fiye da ita ko a wurin tarayya ta aure ne. Kuma ita ce uwar mai sunan mahaifinsa Ibrahim Khalil, uwa uba kuma 'yar uwarsa ta jini. Hauwa ba ta fi ni kishi ba wallahi kawai na fita ha'kuri da juriya ne dalilin gwagwarmayar da na yi a rayuwa ita ba ta yi irinta ba.
BabaTabawa ta koma kicin jikinta duk a sanyaye bayan cikin hikima irin ta manya ta yi mana nasiha aka ci sa'a kuma Hauwa bata k'alubalanceta ba.
Falon ya yi shiru bayan gushewar baba Tabawa daga wurin babu wanda ya sake magana. Ita Momi din tunda ta sunkuyar da kanta kasa ba ta sake d'agowa ba tabbatacin ta ji ciwon irin tijarar da Hauwa ta yi mata.
'Dagowar da za ta yi kuwa sai ya yi daidai da kwaranyowar ruwan hawaye a dakalin fuskarta. Ba ta yi yun'kurin gogewa ba sai ta kalleni ta fara magana cikin karaya da zullumi." Amina ni na haifi Salim amma wallahi ba na goyon bayansa akan irin abubuwan da yake aikatawa na rashin kyautatawa. sannan na sake jadadda miki babu yawuna ka haifi d'a ne kawai amma ba ka haifi halinsa b..... Hauwa ta yi saurin cewa." Kuka ai yanzu ki ka soma in sha Allahu rabbi Hajiya kina
fama da gagararan d'anki da ki ka kasa sarrafawa ina ke ina iya yi wa yaran wasu tarbiya wallahi ki ji tsoron Allah da Annabi, ga shi dai da bakin ki kin fad'a cewa Salim baya jin maganar ki, sannan nan Nusaiba ta shigo har gida ta yi mana rashin kunya, ina tarbiya anan kina so ki lalata mana yaranmu ne, ko kuma kina so su yi koyi da abinda yaranki suke yi duk a had'u a yi mutuwar kasko gabad'aya ko ba haka ba ne."
Shiru ta yi ba ta ce mata komai ba. Na dube Hauwa da ta kasa zaune a kan kujera sai zabura take yi kamar ta yi tsalle a gabanta ta rufe ta da duka.
Gyada kaina na yi ban ce komai ba na mayar da hankalina kanta domin sauraran abinda take cewa." Na nunawa Salim takaici da 'bacin raina na kuma gargade shi akan kada ya kuskura abu mafi muni ya sake faruwa irin haka. Ina kwance cikin ciwo jiya na samu labarin doki-in-doka da ya shiga tsakaninsu. Wannan shine abinda ya fi tayar mini da hankali na ce

Please Login or Register in order to submit comment