Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma kin ba mu mamaki, yanzu Hauwa ko da babu aure a tsakaninki da Tajo ba za ki iya kula masa da yara ba? Ko daga waje ya auro ki bai kamata ki yi abinda ki ka yi........... Ta katseta kafin ta krasa tana fad'in." Anti Saratu ban ga lefinki ba don kin kare shi, ai nasan babu wanda zai ta'ba goyon bayana balle a nuna masa cewa bai yi mini adalci ba, ya kyare ni, ya tsangwame ni a gidansa, ya fitar da hannu ya dake ni, ya kira ni jahila mara tarbiya duk a gaban matayensa . Ya nuna musu kan dole yake zaune da ni, na haihu ya nuna mini iko akan abinda na haifa baiwa ce ni, ko kuma jaka ce, ai kudi na hauka ba ne, kuma itama Amina ai ubanta talaka ne mai yasa ya fifita ta a kaina, mai yasa yake rangwanta mata. Idan ya daukaki Maryam domin yana ganin tana da dukiya daidai take da shi, ai ta wani gefan na fi Amina usuli tunda kaf dangin mahaifina fana uwata babban family ne, ya za a yi na yi rayuwar 'yanci da jin dadi a tsakanin kishiyoyin da aka nuna sune suke da mutunci a kaina."
Ta sassauta tana fad'in." Ita Aminar ce ta gaya miki cewa ta daban ce a wurinsa. Ko kuwa kina ganin ta wuce ya yi mata shegantaka idan har tsiyarsa ta motsa, to idan har ma kina tunanin haka ki bari domin kuwa babu wata mace da za ta gaya miki cewa mijinta na yi mata yadda take so ba tare da yana guma mata ba. Shiyasa ai nake fad'in na raina wayonki da gogewarki tunda har ki ka kasa karantar yanayin zamantakewa da wanda Allah Ya had'a ki zama da shi, ba wai ina fad'a miki haka ba ne saboda Ina kin'ki ko Kuma na nuna miki cewa d'an uwana nake goyawa baya. Shima mun nuna masa kuskuransa kuma ya d'auki niyyar gyara tunda har ya tako kafarsa garin nan to tabbas ya aminta da cigaba da zama dake. Hauwa ki yi karatun ta nutsu kowane aure akwai kalubale a cikinsa ki kara hakuri akan wanda ki ke yi, ke da dan uwanki kada ki bari abokanan zamanki suga wallenki har su yi miki dariya a fakaice. Har yanzu
Amina da Maryam sun fi ko way........" Kin ga anti Saratu don Allah ki kyale ni na ji da bakincin da yake damuna kada ki kara mini dama tuntuni ni duk abinda zai faru ba kya ba ni goyon baya kin sha nuna mini Amina ta fi ni mutunci gaskiya ba zan iya komawa ba shiyasa ma na ajiye masa d'ansa ya nemi mai shayarwa."
Cike da tsananin bacin rai Hajiya saratu ta ce." To shikkenan Hauwa kada Allah Ya sa ki koma din, ki yi ta zama tunda haka kike ganin ya fi miki, yaro zai rayu ko dake ko babu ke, dana san abinda za ki yi mini kenan da ban shiga sabgarki ba, duk abinda zai sake biyo baya ba zan sake sanya bakina ba ki yi yadda kike ganin ya yi miki."
Ta mike tsaye tana fad'in. Gashi na yi hakan shine ya fi mini kwanciyar hankali da nutsuwa ba zan iya zama dashi ba idan yana tare da wannan tsohuwar mushirkar matarsa."
Ta ce." Ki je mana kada ki zage ni Hauwa tunda kin yankewa kanki hukunci wanene ya isa, Allah Ya bada sa'a."
Ta kama hanyar fita bayan ta ja mata wani tsaki mai tsayi wanda ya yi mata mutukar ciwo a zuciya. Hauwa ce yau tsare kerere a gabanta tana gaggaya mata magana har da tsaki abin ya tsaya mata ranta sosai har da 'yar kwallarta ta goge tare da d'aukar wayarta dake gefenta.
Tana kiransa ya daga Yana fad'in." Na shirya tsaf gani nan zuwa. " Cikin rawar murya ta ce." A a, ka zauna anan hotel din, ko da yake ba zan hana ka zuwa ka gaishe da Inna ba, da sai na ce ka zauna an jima kadan zan yi wanka ka turo Sukairaju ya d'auke ni."
Jikin yadda muryarta take rawa ya sanya ya ce." Wani abin ne ya faru?"
Ta gyad'a kanta tare da sanya yatsu ta goge hawayen da ya zubo mata. Domin daga zarar ta tuna tsakin wulakacin da Hauwa ta yi mata sai ta ji wani tashin hankali tunda take ba a ta'ba yi mata wannan iskancin ba da 'ya'yanta magidanta da kuma shekarunta, lallai karfin zumunci ya shallake komai amma da ba don haka ba tabbas da Hauwa ta raina kanta a yau, shikkenan daga gyara kayanka, Hauwa bata da mutunci ko kad'an.
Ta ce."Bari kawai Tajo, Allah dai ya kyauta shine abinda zan ce."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan turo Sukairaju ya d'auke ki yanzu kawai mu wuce Allah shikkenan."
Ta amsa da "Amin." Kafin ta kashe wayar a sanyaye wanda Yayi daidai da shigowar inna Uwani da jug na kunu da kwanon silva sabo dal dashi da k'osai a ciki. Ta ajiye gabanta tana fad'in.'' Ga kunun Saratu k'osan ma da zafins na d'ora miki ruwan wanka yanzu nan.
A tak'aice ta ce." To na gode Inna Allah Ya saka da alheri.'' Har ta juya za ta fita sai kuma ta tsaya tana fad'in.'' Tajon zai shigo din ko domin yanzu nan Baffansu Tijjani wanda gidansa yake kallon namu ya shigo yana gaya mini zai fita aiki na ce ya d'an jira domin su samu damar tattaunawa akan abinda yake faruwa."
Ta ce." E, zai shigo din ya jira shi" Ta fad'i Hakan ne domin ba ta san me za ta ce mata ba.
Sai ta juya ta fita da sauri tana fad'in." Bari na gaya masa to."
*2K Complete a telegram. Normal What'sapp group kuma 1k via 0542382124...Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*GARKUWAR MATA
'*
*BINTA UMAR ABBALE*
*TALLAH* https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
Kiranta kawai ya yi a waya ya gaya mata ga Sukairaju nan ya turo domin d'aukarta.
Sukairaju da ya zo ya shiga cikin gidan tunda akwai sabo dalili amintaccen yaronsa ne duk a cikin masu yi masa hidima. Suka gaisa da inna Uwani har tana yi masa tayin abun kari ya ce a koshe yake ya fita ya tsaya jikin mota yana jiran fitowar Hajiya Saratun.
Ta fito cikin shiri tunda dama ta yi wanka ta kintsa sama-sama ta iya yin karin kummalo dalilin takaicin rashin kunyar da Hauwa ta yi mata. Inna Uwani na zaune a tsakargida tana gyara kayan miya Hajiya Saratu ta fito tana fad'in." Inna tafiya zan yi."
Ta juya da sauri tana fad'in." Tafiya kamar Yaya Saratu ina Tajon yake ne shi ake jira domin Tijjani har ajiye aikinsa ya yi saboda ya gan shi su yi magana."
Ta ce." To ni kam ban san me zan ce miki ba Inna amma ina tsammanin Hauwa ba zata koma ba domin ta gaya mini d'azu da muka yi magana. Amma ki sake tuntubarta."
Inna Uwani ta saki baki tana kallonta a sanyaye ta furta." Haka tace miki ba zata koma ba Saratu?" Ta gyad'a kanta tana fad'in." Ai da hakan ta gaya mini da sauki Inna ba zai dame ni ba amma babu komai Allah Ya sa hakan shi ya fi alheri, Allah Ya raya yara."
Daga haka kawai sai ta kama hanyar fita. Inna Uwani ta bi bayanta tana fad'in." Ina Tajon yake ba zai shigo mu gaisa ba kenan?"
Hajiya Saratu ta yi shiru ba ta ce mata komai ba. Haka ta fice daga gidan inna Uwani na le'kenta Sukairaju ya bud'e mata mota ta shiga ya ja suka bar wurin. Jikinta sanyi kalau ta koma cikin gidan kamar mara lafiya.
Shi dariya ma abin ya bashi da Hajiya Saratu ta gaya masa abinda ya faru. Ya dinga gyad'a kansa yana jimanta fitsarar Hauwa ko shi ba ya iya tsalleke Umarninta kuma baya iya duban idonta ya yi jayayya da ita, sannan kuma yakan yi aiki da shawarwarinta amma yau an wayi gari Hauwa d'iyar cikinta ta ci mutuncinta saboda wani dalili. Abin ya ta'ba shi sosai mussaman yadda ya ga yanayin Yayar tasa ya yi tabbacin abin ya yi mata ciwo a rai. In banda umarni ne na iyaye bai ga dalilin da zai sanya shi zuwa bikon Hauwa ba balle rayuka su b'aci zahiri kuma ba a tara sani ga Allah da ya san abinda zai biyo baya kenan da bai aminta da auranta ba.
Tun mota suka yi magana da Hajja shi ya gaya mata cewa zai wuce Bunkure gidan Malam 'Daha malamin mahaifinsu wato Alhaji Ibrahimu. Yana nan ya tsufa sosai amma da yake tsufan ya wanzu tafarkin addini da karatun al'kurani jin sa da ganinsa duka ba su raunana ba. Sai dai matsalar kafa da ya samu amma baya ga haka babu wani abu da ya samu tawaya a tare dashi sai tsufa wanda wajibi ne ga kowane musulumi. Tun yana saurayi rabonshi da ziyartar malamin yanzu kam ya zame masa dole domin yana buk'atar addu'a bayan wadda yake yi akan kansa.
Sukairaju na sauke Hajiya Saratu a gidanta suka d'auki hanyar kauyen bunkure kamar yadda ya niyyata. Da k'yar ya iya sheda gidan dalili yawanci gonakin da suke garin an sayar an yi gine-gine na zamani tunda yanzu an samu cigaba a ko'ina kusan rabin garin ma ya zamananta da dama wasu na sauya fasalin gidajensu zuwa na zamani.
A can daga gefe Sukairaju ya ajiye motar amma bai fito ba yana ciki a zaune dalilin ganin yadda jama'a suka fara taruwa masu wuce wa suna tsayawa. Ya ce da Sukairaju ya yi sallama a kofar gidan Malam din haka kuwa ya yi ya dinga kwad'a sallama wani magidanci ya fito cikin yar shara da fatanya a kafadarsa. Suka yi musabaha kafin ya tambaye shi. Ya ba shi amsa da eh gidan Malam 'Daha ne. Sai ya nuna masa motar yana fad'in." A gaya masa ba'ko ya yi Alhaji Tajuden ne na Alhaji Ibrahimu dambatta wato abokinsa da ya rasu."
Mutumin ya washe bakinsa kafin ya nufi wurin motar da saurin gaske. Sukairaju ya bi shi cikin gaggawa ya yi saurin tare shi.
Duk abinda suke yi yana kallonsu sai ya sauke gilashin motar fuskarsa a sake ya furta." Sukairaju matsa masa hanya mana mutumina ne."
Da sauri Sukairaju ya bashi wuri shi kuma ya krasa bakin motar yana ta dariya tare da mamakin ganinsa. Ya bude motar cikin sauri ya fito ya rike hannunsa yana fad'in." Malam Rabi'u."
Ya ce." Naam Alhajin Allah dama za mu sake ganawa."
Yana dariya ya ce." Allah ya nufa gashi na ziyarce ku, na zo wurin Malam ne."
Ya gyad'a kansa yana fad'in" Ya bayan rabuwa Alhaji ya harkoki da jama'a Ubangiji Allah Ya taimaka ya kara suttura."
Ya amsa da "Amin Malam Rabi'u ya iyali fatan kowa lafiya?" Ya ce." Alhamdulillahi mata na hud'u ina da yara ashirin da biyu."
Cike da mamaki ya ce." Mata hud'u yara ashirin da hud'u Rabi'u?"
Sai ya kyalkyale da dariya yana fad'in." Kwarai kuwa Alhaji yanzu haka akwai shida mata dana aurar da su, suna d'akin mazajensu cikin aminci."
Ya gyad'a kansa yana jimanta karfin hali irin na mutanan k'auye gashi dai bashi da wani karfi irin na su amma ya ajiye mata hud'u da tarin yara."
Ya ce." Ka burge ni da gaske Rabi'u kuma kai namiji ne, yanzu dai ka yi mini jagora wurin Malam na zo mu gaisa ne."
Ya ce." Ka kyauta sosai kuwa domin idan ban mata ba yanzu ka kai sama da shekara asirin rabonka da garin nan tun marigayi yana raye."
Ya furta." Tabbas hakane domin karshen zuwan da muke yi tare da shi ne, tun bayan rasuwarsa kuma Allah bai nufe ni da sake zuwa ba."
Suka nufi cikin gidan a tare suna magana cike da jin dad'in had'uwa. Babu girman kai ko kuma nuna ni isheshshene yanayin yadda ya gaisawa da jama'ar da suka tsaitsaya yana ta d'aga musu hannu haka suka shiga gidan da aka narka 'kasa irin ta da mai d'anko wurin gida shi. Gidan mai yalwa ne sosai irin dai ire iren gidajen Malaman addini mussaman na karkara
har yanzu yana nan inda yake sai dai kwaskwarima da aka yi wa wasu guraran dalilin wasu daga cikin yaransa a ciki suke zaune da iyalinsu. Amma kuma sun gyarawa mahaifinnasu bangaran nasa tunda da alama yana yin manyan ba'ki mussaman abokai ko 'ya'yansu tunda fitacce malamin addinin musulunci ne da har yanzu tafsiri da karatun al'kurninsa ke yawo a wasu gidajen redion.
Koda suka shiga wurin nasa yana zaune kafarsa ta k'wanshe da al'kur'ani kirar warshu a hannunsa yana karatu babu wata gigita ta tsufa ya gane wanene a gabansa.
Rabi'u yana fad'in." Malam ga Tajuden na Alhaji Ibrahimu na kawo maka."
Ya yi dariya irin ta manya kafin ya ce." kuna shigowa na gane shi ai ko baTajudden na Alhaji Ibrahimu ba."
Ya ce." Ni ne Malam ina fatan na same ku lafiya ya bayan rabuwa kuma?" Ya amsa da "Alhamdulillahi ya iyali ya jama'a ya harkokin ina Hajiya Halimatu?" Yana nufin Hajja kenan.
Ya ce." Tana nan lafiya lau ta ce a gaishe ka da kyau Malam."
Ya gyad'a kansa tare da fad'in." Ina amsawa na kuma ji dadin ganinka Tajuden za mu sake saduwa kafin Allah Ya yi ikonsa."
Ya furta." In sha Allahu rabbi zan dinga ko'karin ganin na kawo ziyara Malam abubuwa sai a hankali."
Ya gyad'a kansa yana murmushi kafin ya ce."Allah Ya taimaka ya bada sa'a, na gode sosai Allah Ya yi albarka."
Ya amsa da Amin suma Amin kafin wajan ya d'auki shiru Malam Rabi'u tuntuni ya fita. Malam din ya ce." Akwai abinda yake tafe da kai ne?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kwarai kuwa Malam muna buk'atar addu'a akan komai duk da muna yi akan kanmu, amma a kwanakin nan abubuwa sun yi yawa mussaman 'bangaran iyalina a taimaka mana da addu'a Allah Ya warware mana."
A nutse ya ce." Za a yi in sha Allahu akwai buk'atar ka tsananta addu'a akan kanka, daga nan zan sanya al'majirai yin saukar al'kur'ani tsayin kwanaki bakwai sai ka yi sadaka, Allah Ya warware."
Ya amsa da "Amin Ya Malam na gode sosai Allah Ya kara girma."
Ya furta." Za ka shiga ka gaisa da mutanan gidan ko?"

idan kin san kina karanta book din nan ba ki biya ni hakkina ba to Ina binki bashi.

Ya yun'kura domin tashi Yana fad'in." E, zan shiga Malam zan yi magana da Rabi'u akan abin sadaka sai mu ga yadda za a yi."
Har ya juya zai fita ya dakatar da shi ya tsaya sai ya ce." Ya iyalin Tajuden su nawa ne yanzu yaranka kuma nawa?"
Ya ce." Allah shi gafarta Malam su uku ne yara kuma ina da biyar rayayyu d'aya ta rasu."
Ya ce." Alhamdulillahi Alhamdulillahi Ubangiji Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya raya mana su bisa tafarkin addinin islama. Idan har kana da buk'atar cika sunnar Annabi tunda su uku ne ka zo nan na zaba maka daya daga cikin yarana biyu da suka rage mini. Hakika ina sha'awar tabbatuwar zumuncina da Alhaji Ibrahimu. Duk da fad'in Allah ne kuma sunna ce mai kyau amma ba wajibi ba ne, abinda magabatanmu suka d'ora mu akai kenan lallai k'arshen duniya mata za su yawaita yayin da mazan auran za su yi 'karanci ko rashin ikon ga masu niyya. masu iko idan kuna da d'aya ku kara da ta biyu, masu biyu ku 'kara da ta uku, masu uku ku k'ara ku yi hud'u domin dakile mas'aloli masu yawa. Idan har ka niyyata tunda kana da iko kada ka manta ka zo nan zan had'a ka aure da nutsatstsiyar yarinya ko ba daga cikin yarana ba."
Cikin wani yanayin ya furta." To shikkenan Ya Malam idan da yiwuwar hakan in sha Allahu zan zo sai a san yadda za a yi na gode sosai, Allah Ya saka da alheri"
Ya amsa da "Amin cikin nutsuwa yana yi masa fatan alheri da sauka lafiya.
Yana fita ya ciko karo da Rabi'u a tsaye ya ce ya yi masa jagora cikin gidan domin su gaisa. Ya dinga mamakin yadda gidan Malam 'Daha
ya cika da tawagar yara 'yan mata da masu tasowa maza da mata sai iyayen tukuwane kangama-kangama dama can sanin da ya yi masa mutum ne mai arzikin gona ki a k'auyen don haka matsala ta abinci ba zata ta zama barazana a gare su. Malamin mahaifinsa ne kuma akwai abota sosai sai dai kowa tsarinsa daban. Mahaifinsa ko a can baya yana da wayewa sosai ta fannin boko da kuma addinin daidai gwargwado Hajja ita kad'an ta rayu bai ma ta'ba yun'kurin karin aure ba har ya rasu su biyu ya haifa. Shi kansa bai taba tunanin zai iya ajiye mata uku ba domin yadda ya tsara rayuwarsa tun daga kuruciya Samira kadai ta ishe shi, sai gashi Allah Ya na ta juya lamarinsa.
Har gajiya ya yi da amsa gaisuwa domin dai daga sashe sashe ake zuwa gaishe shi. Rabi'u ya riko hannunsa suka fita duk da haka wasu daga cikin yaran sai da suka biyo bayansu.
Bakin motarsa kuwa jama'a ne a tsaye Sukairaju yana ta fama da su. Daga bakin kofar gidan Malam din suka tsaya a dan gajiye yake fad'in." Rabi'u kana da asusun ajiyar kudi ko?"
Ya ce." E, da akwai sai ya fito da wayarsa ya mika masa yana fad'in." Bismillah yi sauri sanya mini lambar a nan zan tura abin sadaka a bawa Malam sannan abinda ya yi saura ka yi amfani dashi a kuma sallami iyayenmu da k'annanmu da suke cikin gidan a ba su su sha ruwa."
Ya kar'bi wayar da sauri yana fad'in." To Allah Ya saka da alheri mun gode Allah Ya kara arziki Alhaji."
Bai ce komai ba har gama ya mika masa waya ya kar'ba a tsaye a wurin ya tura dubu dari biyar sannan ya bashi wayar a gain ya ce ya sanya masa lambar wayarsa domin su dinga gaisawa."
Ya kar'ba a karo na biyu ya sanya masa lambar shi kuma ya yi serving da Malam Rabi'u Bunkure.
Da haka suka yi sallama cike da girmama juna. Sai da suka fita daga karkarar tukkuna Sukairaju yake tambayarsa ina suka nufa domin shi duk a tunani shi zai sake kwana a kono din ganin bai fiye son tafiyar mota ba. Ya ce." Mu d'auki hanyar gida kawai yau komai dare a gidana zan kwana Sukairaju na huce gajiyar gabad'aya."
Aikuwa da azama ya d'auki hanyar garin abuja kamar yadda aka bashi umarni.
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya d'an gyara zaman shi a mota yana nazarin maganar Malam 'Daha wai ya zo cikin karkara ya nemi aure domin cika ta hud'u. Gabad'aya ma shi yanzu babu wannan lissafin a tare da shi bai sani ba ko nan gaba. Gabansa ya fadi lokacin da ya tuna iya rigimarsa Amina tunda suka yi sallama jiya sau daya suka yi waya da daddare kafin ya kwanta ya kira ta domin gaya mata ba zai dawo ba sai gobe. Yana duba wayar ya ga kiranta ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya sanya wayar a kunnansa Amina ta tsaya masa ransa sosai shi kansa ya tabbatar da haka...
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*TALLAH!* https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Paid book ne 2k complete a telegram Whasap guruf 1k via 0542382124....Binta Umar gtbank*
*07084653262*
Muna tare da yara falo wai sun zo ganin 'kaninsu domin babansu ya gaya musu sunansa Sultan falon ya kacame Husaina da Minal har da kokawa ban ankara ba sai kukan Minal na ji da k'arfi lokacin ya yi daidai da fitowar Baba Tabawa daga d'akinta. Kukan Minal din ya zaburar da yaron shi ma ya tsanyare da kuka Baba Tabawa fadi take "A kul cizo ko Usai ba ki san 'kanwarki ba ce, ka da na sake gani kin yi cizo."
Na juya da mamaki ina kallonta yayin da nake jijjiga yaron na ce." cizonta ta yi?"
Hassana dake tsaye a

Please Login or Register in order to submit comment