Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take yi kasashen waje ta yi kwana da kwanaki ta dawo mai yasa duk hakan bai dame ka ba, idan adalci ne itama sai ka hana ta fita waje sarin kaya, sannan kuma ai yanayin jikinta irin na Samira ne siririya ce, ko ba haka kake son mace ba, ai kasha fad'a, shiyasa ka yi saurin auranta da wannan dalilin ma don ni wallahi ban yarda da wata wasiyya ba."

Ya 'bata fuska yana fad'in." Kin ga Malama ba na son rashin hankali, ke ba a zama a yi maganar nutsuwa dake sai kin soko da shirme, nasan abinda nake yi, Kuma ni tunda nake da abokina matarsa ba ta ta'ba ba ni sha'awa ba, asalima ni ne a kan gaba wurin neman auranta tare da ni dashi muka dinga zurga-zurga zuwa jos har ta zama mallakinsa. Ban ta'ba yi wa Maryam kallon wata manufa sai yanzu da kaddara ta gifta a tsakaninmu. Alh Amadu kuma ya wuce komai a wurina.

Hanci na ja, cikin takaici na ce.'' To shikkenan na ji tunda ka ce haka sai ka hana ta fita waje sarin kaya kamar yadda ka takura mini idan adalci za a yi."

Sai ya shiga girgiza kansa yana fad'in." A, a, akan me zan hana ta neman kudinta bayan a haka ta ginu, kin san yawan mutanan da suke ci da sha'a a 'karkashinta kuwa, maganar fita zuwa wata kasa wannan dama dole ta bari tunda girma ya fara hawa kanta yaranta sun fara tasawa sai ta wakiltasu, shi ma abokina yarda da cewa ba zata ci amanarsa ba ne ya sanya ya bata goyon bayan fad'ada sana'arta, kuma ke ma da ki ke yin wannan maganar ai ban hana ki kasuwancinki ba ko ba haka ba ne?"
"Ni kenan kana kokwanto a kaina shiyasa kake takura mini da zargi har da Hamusu ka dinga tuhuma har da su Allah Ya isa, ka dinga bin shafukana na intarnat kana yi mini binceka duk wani abu da na dora da zummar talla idan bai yi maka ba sai ka sanya a sauke mini, ta karfi sai da ka ruguza mini kasuwancina na media."
Numfasawa ya yi kafin ya ce." Neman rigima ne kawai irin naki Amina, abu ne a zahiri gashinan kasuwancinki dana Hajiya Maryam ya sha bam-bam, ita bata fitowa ta tallata kanta da sunan kasuwanci tunda na aureta nake bin abubuwan da take gudanarwa sannu a hankali ban hangi wani abin assha ba wanda zai janyo mana zubewar mutunci.
Ke kuma dake da kayan tallan ki ke tallatawa duniya ya ba zan d'auki mataki ba. Ko ba ni da ido da neman rahoto daga jaridu ai ina kishin kaina ba zan lamunci irin wannan business din ba, idan ba ki manta ba farko auranmu na gaya miki ki bi duk hanyoyi na halak da za su kawo miki kudi amma kada ki bi hanyar da zata janyo mini zubewar mutunci tunda kin fi kowa sanin wanene ni."

Gudun aure littafin kudi ne don girman Allah kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Shiru kawai na yi masa domin har yanzu ban gamsu da bayaninsa ba sai nake ganin kawai yana tsara ni ne saboda ban kai karfin matarsa ba ta fi ni kudi. Ita ai babbar yar kasuwace babu buk'atar ta bi irin hanyar da sauran k'ananun 'yan kasuwa ke bi domin su kafu da kiran kostoma ta riga ta kafu ta tsaya da kafafunta.
Ganin na yi shiru ban sake cewa komai ba sai ya ce." Ni da za ki bi shawarata ma ki ajiye komai ki kama ni ki ri'ke da kyau, ni kuma duk bayan shekara daya ko biyu idan Allah Ya tsawaita mana nisan kwana na dinga baki ajiya mai girma kina haife mini. Sai ni kuma na cigaba da nema muku dukiyar tare dake da abinda za mu haifa ko."
Kallonsa kawai nake yi na rasa ma abinda zan ce. Wai duk shekara daya sai kace wata kaza yanzu da shekaru suka fara tura mini ai Allah na tuba ko zan k'ara wata haihuwar bai fi uku zuwa hud'u ba idan ma Allah Ya 'kaddara. Shiru na yi masa ban iya cewa dashi komai ba saboda Ina iya fad'in wata maganar akan maganarsa ya canza mini tawa.
Ya kai hannunsa kirjina tare da fad'in." Wannan na ga ya k'ara girma, na shiga tsananin u'kuba na rashinsu Amina."
Maganar ta ba ni dariya amma ban yi ba kawai na zuba masa ido yana matsa mini kirji dake cikin riga. Cikin zuciyata na ce dama ai dole ka shiga ukuba tunda ka saba lugudarsu yadda ranka yake so, gashi amaryartaka ba ta dasu. Hauwa da nata suka bunkasa dalilin ciki tana can wata uwa duniya ashe abin maleji ne.
Ganin ban hana shi abinda yake yi ba ya sanya ya janyo kafafuna kusa da shi ya fara kicikicin kwantar da ni a kasan kafet din da muke zaune. Na cire hannunsa tare da saurin tashi tsaye. Sai shi ma ya tashi da wani irin yanayi na tsantsar fitina ya kashe hasken d'akin ya riko hannuna muka nufi katon gadon da yake girke a d'akin. Ban hana shi tattabani ba sai da lamarin ya yi nisa tukkuna na ce masa ba ni da tsarki fa. Nan na ga gigicewa har da su rawar murya wai ban yi masa adalci ba. Na yi shiru ina kallonsa ina dariyar zucci.
Yana ta abubuwa kamar wanda ya rasa hankalinsa yana fad'in" duk ma yadda zaki yi sai kin nemi hanyar da za ki biya mini buk'ata lallai ba zan iya ha'kuri a wannan dare ba Amina.........
'


*YAU DAI SUN YI ALKAWARI BARI MUGA WAYE ZAI FARA KARYA ALKAWARIN===*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*72*
'Kin rungumarsa na yi, na rabu dashi kawai wai shi dole sai ya janyo hankalina, ya riga ya san abinda yake saurin kidima ni ya mayar da hankalinsa kacokan wurin aikatawa kamar wani sabon d'an yayen da yake rikicin neman abincinsa. Sa'kon ya fara sa'bata duk yadda na kai ga basarwa sai dana gaza jikina ya fara rawa na fara
mutsu-mutsu! Tabbas na so na daure da zummar ja masa aji irin na mata amma ina lamarin ya fi 'karfina ban ma san lokacin da na tallafeshi ba a ki'dime har na so na fi shi za'kewa da kansa ya gane abinda na fad'a ba gaskiya ba ne. Sai hakan ya k'ara sanya shi sakankancewa yana buga sambatu da nishin kamar wanda ransa yake daf da barin gangar jikinsa.

Yadda muka wayi gari cikin walwala da farinciki shine abinda ya kara tabbatar mini da cewa ba a shiga tsakanin mace da mijinta domin kuwa wanda ya shiga tabbas watarana shine zai ji kunya mussaman idan ya aikata abinda zai sanya jin kunyar da gangan. Misali da ba dan Baban Saude ya yi amfani da ilimi da k'warewa wajan kawo sasanci da daidaito a tsakaninmu ba wata'kila da ya yi amfani da 'daya sigar to da ba wannan maganar ake yi ba. To shi ma sai a ka ci sa'a ya yi amfani da hikima wajan ganin ya isar da sa'kon da yake so ya isar din wanda shi ma daga 'bangaransa na fahimci abin ya yi masa ciwo sosai, kuma kamar yadda ya fad'a din na tabbatar da baya sona da buk'atar cigaba da zama da ni ba zai ta'ba bibiyata da nufin kome da sulhu ba, duk da Baban Saude bai yi amfani da tsautsauran kalamai ba, amma yadda na fahimta ya ji haushi kawai ya danne ne domin samun a zauna lafiya.Tabbas idan hakane kuwa Ina da ya'kinin zai gyara anan gaba tunda na lura ya tsani a kai shi k'ara don ko lokacin da na ta'ba Kai shi 'kararsa wurin Hajja akan lamarin Hamusu fushi ya yi da ni mai tsanani idan ban manta ba ya dinga gaba da ni sai da kyar ya sauko.

Dama tun asubahi ya ce na yi duk shirye-shiryen da zan yi jirgin karfe takwas za mu bi zuwa abuja kafin lokacin ma ya cika mun fito ni dashi a kintse Sukairaju dama tuntuni ya sanya mana kayanmu a mota.
Kafin mu isa airport din Anti Yagana ta kira ni a waya kamar yadda ta fada na ce mata ai mun riga ma mun fito muna mota zuwa filin jirgi. Sai ta ce na had'ata da shi. Ba tare da na ce komai ba na mik'a wayar tare da gaya masa anti Yagana ce take so ta yi magana dashi.
Ya kar'ba a nutse suka gaisa sai kawai ta fara yi masa godiya har ina jin yadda muryarta take rawa godiya sosai na abin alherin da ya yi wa su Dada da Baban Saude. Sai kuma alkawarin kyautar motar da ya yi wa maigidanta. Da kulawa sosai ya nuna mata cewa ta daina yi masa godiya akan abinda ya yi, ai duka an riga an zama daya don haka ba abin mamaki da godiya ba ne akan duk irin abinda zai yi mana. Ta cigaba dai da godiya dai har tana cewa dashi ya kara da hakuri dangane da zamantakewa ta dashi in sha Allahu wani abu ba zai sake faruwa ba. Ya ce mata babu komai shi ma a b'angaransa magana ta wuce hakan ba zata sake faruwa ba.

Suka yi sallama ya miko mini wayar muka dan yi magana kafin ta katse kiran. Ya dube ni a tsanake yana ce wa." Yagana mutuniyar kirki ce sosai Amina."
Murmushi kawai na yi ban ce masa komai ba, tunanina yana can wani waje na daban. Ya gaya mini ni da Hauwa ne za mu sasanta kanmu abin nufi shine za mu raba zama. Wata shida a Legos wata shida a Abuja. Abinda yake damuna shine mai yasa ita Hajiya Maryam din ba za mu raba da ita ba, ai matarsa ce ita kamar yadda muke matayensa. Ban ga dalilin da zai sanya ya ce mu biyu ne za mu dinga wannan zurga-zurgar ba. Ba na so na yi wata magana ne ya ga kamar kishi ne ko neman fitina shiyasa kawai na yi shiru amma zahiri wannan hukuncin bai yi mini ba kuma sai na rusa shi domin kuwa ba zan ta'ba yarda ya kafa abinda nasan lallai anan gaba zai zama rikici ba.
Muka isa abuja wajan sha daya na safe. Gidanshi yana nan tsaf tunda akwai hadimai tare muka shiga amma ko zama bai yi ba ya sake fita sai zuciyata ta shiga wasiwasin akan fitarsa da gaggawa irin haka. Tun d'azu a mota kafin zuwanmu airport na ji sun yi waya da ita sai nake zargin gidanta ya nufa.
Zuciyata ta cika da takaici da b'akinciki irin yadda yake rasa sukuni akan sha'anin matar nan abinda yake yi yana nema ya wuce gona da iri ban hana shi kula da matarsa ba amma yana da kyau ya daina nuna muguwar damuwa da ita a gabana domin kuwa ba zan iya jura ba.
Ina fitowa daga wanka Yusi ya shigo. Na zuba masa ido har ya k'araso wajan da nake gefan gadon yana dariya yaro ya zama wani lafiyayye ya yi haske da kyau sai kace wanda yake rayuwa a k'etare kayan jikinsa ma abin kallone. Ya zauna kusa da ni tare da ri'ko hannuna ni kam kallonsa kawai nake yi na kasa cewa dashi komai.
Ya ce." Mama ina yini."
"Lafiya lau Yusi kai ne kuwa?" Na fad'a ina d'ago fuskarsa. Sai kece da dariya yana cewa." Ni ne mama me ki ka ga ni?"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali na ce." Na ga abubuwa da yawa Yusi wanene ya gaya maka na zo?"
Kai tsaye ya ce." Baba ne Yana gidan Momi shine yake gaya mini tare kuke wai na zo mu gaisa." Yana rufe bakinsa Adam ya shigo da sallama a nutse ya k'araso wajan da muke jikinsa sanye da irin kayan dake jikin Yusi. Bashi da jikin girma da alama ya d'auko jiki irin na Mamansa ya d'an risina yana gaishe ni na amsa da kulawa. Ina fad'in" Adam mai kuke bawa Yusi ya zama d'an lukuti haka?" Ai kuwa sai ya fashe da dariya yana kallonsa ya ce." Wallahi babu komai Mama jikinsa ne irin haka momi ma kullum da asuba sai ta sanya shi ya motsa jikinsa amma baya raguwa gashinan duk ya fi mu girma.
'Yar dariya na yi tare da cewa." Abinci zai rage ciki kawai idan ba so yake yi wataran ya kasa tashi ba." Ya ce." Haka ma Yaya Salim ya ce wai sau biyu zai dinga cin abinci a rana kuma daban da irin wanda muke ci ba shine Momi ta ce a'a, a kyaleshi 'kibarsa ta kuruciya ce yana zama saurayi zai sa'be, ba zai daina cin abinci ba."
Na gya'da kaina ina d'an murmushi zuciyata kuma cike take da nazarin irin rikon da matar take yi wa yaron ko ni dai da na haife shi albarka tunda ga zahiri nan na gani da Ido. Jikina ya sake yin sanyi sosai to ai da kunya da nauyi a ce na bijiro da wata fitinar wadda zata kawo rud'ani a tsakaninmu.
Tare suka fita da zummar zuwa su yi shirin tafiya islamiyya sha biyu na rana suke shiga su tashi shida na yamma.

Gudun aure littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Shi kam maigidan ai tunda ya fita din nan bai shigo ba sai bayan la'asar wajan hud'u da rabi Ina zaune a falo cikin daya daga cikin kujerun da suke jere. Gajiya na yi da jiranshi ga yunwa ina ji a gaban idona kukunsa ya gama shirya komai a teburin cin abinci. Na tashi na je na d'iba daidai cikina na dawo falon na zauna ina cin abincin zuciyata na tunanin abin.
Shi kansa sai da ya ji nauyi da kunya a lokacin da ya shigo ya same ni, ni kadai a zaune sai tibin dana kunna.
Ya zauna a gefana yana fad'in." Amina kin ji ni shiru ko, ina can wajan Momi ne tun jiya take fama da zazzabi da mura."
A takaice na ce." Allah Ya sawwa'ke." Daga haka ban sake magana ba. Na cigaba da cin abincina cikin nutsuwa. Sai ya ce." Yusi ya shigo ko?"
"Eh Ya shigo tare da Adam.'' Ya furta." Ni ne na gaya masa ya zo ku gaisa."
Na ce." Ai kuwa ka Kyauta."
Shiru ya yi yana dan kallona da wani yanayi kafin ya ce." Mai ya faru na ga yanayinki ya canza ko ni ne?"
Ya fad'a yana matsowa kusa da ni.
Cikin zuciyata na ce aiki ya same ka.
Shiru na yi ban ce masa komai ba.
Ya tsargu sosai don gabad'aya kin sakar masa fuska na yi. Ganin haka sai ya tashi ya haye sama. Na yi zamana ban bi shi ba domin wallahi har cikin zuciyata haushinsa nake ji. Ni ba zuwan da ya yi wajenta ne yake ba ni haushi ba yadda yake d'aukar lamarinta da muhimmanci shine abinda ya fi 'kona mini rai. Yanzu ga matarsa can a wata uwa duniya d'auke da cikinsa amma ban ji ya kira ta ba tun jiya ai muna tare maganarta ma bai yi mini ba. Amma kan wannan tsohuwar yanzu sai ya gigice.
Bai sauko ba sai daf da magariba, Ina zaune a falon ina kallon wani movies da ya d'auke mini hankali
Na hangi saukowarsa cikin jallabiya da hula tashi kafiye naci a saman kanshi cikin shirin shiga massalaci.
Janye idona na yi daga kansa shi ma bai ce mini komai ba ya fice. Na sauke ajiyar zuciya a hankali na tashi na hau saman domin gabatar da tawa ibadar.
Ana idar da sallar ya shigo. Na lura yana so ya gyara abinda ya yi a d'azu shiyasa ya dawo da wuri.
A saman dadduma ya same ni a zaune na idar da sallar amma ban tashi ba. Ya zauna kan wata kujera mai kamar gado da take can wani gefe a d'akin. Yana fad'in." Idan kina idar miko mini Loptop dina ga ta nan a gefanki.
Ba tare da na ce komai ba na tashi na je na d'auko masa ya kar'ba tare da nuna mini wajan zama a gefansa.

Zama na yi da hijabin a jikina. Shiru ya ratsa wajan yana ta dube-dubensa bai ce komai ba. Sai da ya gama tsaf sannan ya rufe computer ya dube ni tare da cewa." Za mu je gidan Momi ki dubata ko?"
A sakarce na ce." Wacece Momi?" Duk kuwa da cewar na gane wadda yake kira da sunan irin yadda na ji yaran na kiranta da shi.
Ya ce." 'Yar uwarki mana, da gaske ba ta jin dad'i kin san zafin zazzabi da mura dai."
A nutse na ce." Mai zai hana ni zuwa na dubata, to Allah Ya sawwa'ke."
Ya amsa da "Amin."
Shiru ya sake biyo baya kafin na ce." Ya Hauwa kuna waya ko?
Da sauri ya ce." Sosai ma kuwa, d'azu nan kafin na shigo sai da na kira ta, wannan watan da ya mutu shine na haihuwarta har wani ya kama sakamakon scanning ya nuna bakwai ga wannan watan da muka shiga shine daidai lokacin da suka bada result. Sai dai kuma komai na Allah ne wata'kila ma gobe tana iya haihuwa ko.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*73*
Har cikin zuciyata nake jin dad'in haihuwar da za su yi domin kuwa tuntuni na yakice abinda zuciyata take raya mini game da haihuwar da za su yi, idan har ina son kaina da zaman lafiya dole na takaitawa kaina kishi akan abinda za su haifa tunda ni dai ga yadda kaddara ta zo mini. Da 'yar kulawa na ce." Hakane tunda watan haihuwar ya riga ya fita har wani ya kama cikin kowane lokaci tana iya haihuwa
don hakan ba abin mamaki ba ne a wajan Allah."
Ya ce." Allah Ya sauketa lafiya dan Annabi."
Na amsa da "Amin Ya Allah."
Sai da muka ci abinci tukkuna muka fita zuwa gidan nata.
Adam da Yusi muka samu a falon suna kallo . Na tsaya muna magana yayin da shi kuma maigidan ya nufi sama ban bi shi ba saboda bai nemi hakan ba. Ina nan a tsaye ban kai ga zama ba ya sauko yana cewa ya ki ka tsaya anan Amina.
Ban ce masa komai ba illah ido da na zuba masa. Akan wanene dalili zan bi shi ai yana da kyau a ce ya fara shiga ya sanar mata tunda ba a san a halin da take ciki ba. Idan shi mijinta ne ni kuma fa, wata'kila hakan bai zai yi mata dad'i ba.
Bayansa na bi muna hawa benan yana sake tisa maganar wai na tsaya ina ta d'ari-d'ari na'ki sakin jikina. Na yi masa shiru ban tanka masa ba. Da dai naga ya'ki ya bar maganar daf da zamu shiga d'akin na tsaya Ina dubansa babu fara'a a tare da ni na ce ." Don Allah maganar nan ta isa haka fa, ina dalili sai maimaitawa ka ke yi, ai ba daidai ba ne kai tsaye kawai mu kutsa mata d'aki idan kai babu lefi hakan ni kuma fa, ai ba mu san halin da zamu same ta ba."
Yadda na nuna 'bacin raina akan hakan ya sanya bai sake wata magana ba muka shiga d'akin. Na yi kokari sosai wajan ganin na daidaita yanayin da nake ciki.
Tana zaune gefan gado sanya da kayan bacci masu taushi a jikinta. Wata kujera dake can gefe ya nufa ya je ya zauna shi kadai nasan ya yi hakan ne domin mafitarsa yana tsoron ya zauna kusa da wata daga cikin hakan ya zama lefi shiyasa ya ke'be kansa waje daya.
Sosai muka gaisa cikin sakewa tunda dama ita din macace mai fuska da iya hurd'a da mutane. Babu wani abu na kishi da ganin kyashi da na karanta a tattare da ita. Sai dai na hangi tsantsar soyayyarsa a cikin idanunta. Domin kuwa motsi kad'an za ta juya ta kalleshi ta dinga kokarin janyo shi cikin maganar da muke yi a tsakaninmu ni da ita amma ya'ki ya sake ya dai 'kyalemu muna hirarmu. Daga karshe ma sai ya sauka kasa ya bar ni tare da ita. Anan na dinga nazarinta duk da dare ne na fahimci tana jin jiki kuma murar ta kama ta da k'arfi. A lokacin sai kawai zuciyata ta dinga raya mini wani abu wai ko ciki ta samu domin sai nake ganin yanayinta kamar na mai karamin ciki. Kirjinta ya ciko ko bireziya ce oho, ni dai sanin da na yi mata zaman makokin mijinta bata da wadatattun kirji
ita kanta ma gabad'aya ta murmure ta yi ki'ba amma ba sosai ba. Sai jikina ya k'ara yin sanyi da al'marin Ubangiji. Lallai ciki ne da ita kuma shine dalilin da ya sanya duk ya gigice tunda abinda yake nema ne ya samu.
Duk da ban tabbatar da hasashena ba amma tun a lokacin na ji na fara tausayin kaina. Zuciyata ta dinga yi mini munanan tunane-tunane. Idan ma har na samu cikin na haihu yarana ne za su tashi daban a gidan masu d'auke da wata lalura idan da k'arar kwana kuma d'aya bayan daya duk su mutu.
Da wannan tunanin na kasance har muka bar gidanta daurewa kawai nake yi amma gabad'aya zuciyata ta kasa juriya sai da na buya a toilet na ci kuka na 'koshi na dinga yin istigifari da rokon Allah ya sassauta mini abinda nake ji a cikin zuciyata.
Washe gari da safe sukuku na tashi babu karsashi a tare da ni. Haka kawai abinda ba ni da tabbas akai ya ke nema ya daga mini hankali. To menene ribar auran ne haihuwa ce, mai yasa nake jin b'akinciki dan matarsa ta samu ciki. A ganina ai abin murna da farinciki ne a gare mu bakidaya, kamar yadda nake jin dad'in haihuwar Hauwa yana da kyau itama wannan din na yi farinciki idan har hasashena ya zama gaskiya. Amma sa'i guda na ji duk tawakkalin da na fara dangane da al'amarin ya ruguje, wani mahaukacin kishi yana nema ya zautar da ni.

Shirun da ya yi mini bai gaya mini matarsa tana da juna biyu ba shine abinda ya yi mini ciwo a ganina menene abin boye mini, idan ba yana nufin wani abu ba. Ko yana gudun ya gaya mini na ji haushi ko na nuna b'akincikina. Duk da bai zama dole a ce ya gaya mini abinda ya shafe shi da matarsa ba, amma ai idan da fahimtar juna da zama na amana ba lefi ba ne don ya gaya mini sai mu had'u mu yi farincikin tare gabad'aya.
Na yi ta ko'karin ganin na danne damuwar da nake ciki amma ina sai da ya fahimci wani abu yana damuna.
Ya dinga bibiyata duk domin son ya ji abinda yake damuna kawai na ce masa babu komai. To ne zance masa ni ban iya 'karya ba balle na yi masa, babu kuma dad'i na fito fili na nuna jin haushina dan matarsa tana da ciki.
Kwana biyu a tsakani ya gaji da tambayata ya kyaleni kawai ya zuba mini ido tunda ya lura da cewar ba na son doguwar hira sai ya daina nema da ita. Amma baya fashin kwanciya da ni duk ranar girki na. A haka ya yi kwana biyu a wajena ya koma gidanta a washe garin ranar ya shigo da safe lokacin ma ban ma tashi ba tunda na yi sallar asubahi bacci ya d'auke ni mai nauyi. Shine ya tashe ni da farinciki yana gaya mini yanzu nan Hauwa ta haihu.
Ganin yadda yake cikin annashuwa da murna ya sanya ni dole ni ma na ara na yafa

Please Login or Register in order to submit comment