Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa Yusi ko ni albarka duk abinda yaranta za su sanya a jikinsu za su ci babu bambanci wannan kad'ai ya kan sanya ni jin kunya da nauyin yin tutsu akan lamarinta. Kuma sam ba ta da fitina a haka dai tana zaune da kowa lafiya ban ta'ba ganin kishi a idonta ba.
Dad'in ganinmu mun sake muna hira gabad'ayanmu ya sanya shi kashingida kan kujera yana ta murmushi tunda suka shigo bai ce komai ba sai kallonmu yake yi yanayinsa ya nuna ya ji dadin ganin yadda muka fara fahimtar juna.
Sai bayan mun nutsu tukkuna ya gyara zamansa domin mu tattauna tare da samun matsaya akan yadda za mu shirya zama. Legos ne kowacce bata so a cikinmu amma kuma tilas ya kama mu duka saboda babu yadda za a yi ace mu bar shi a can shi kadai alhalin duka muna raye adalci shine a ce a raba.
Ni ya bawa damar magana tunda ni ce gaba dasu gidan cikin nutsuwa na ce." Ni na amince zan dau'ki wattani shida idan ya so ku kuma sai ku raba kowacce wata uku ina ganin hakan zai fi."
Hajiya Maryam tana murmushi cikin nutsuwa ta ce." Anya kuwa ni zan iya akwai abubuwa da yawa da suka sha kaina anan din wallahi ba na so na yi nesa yanzu ko kad'an shi Yallabai din ya sani da za ku yi mini alfarma sai na ce ku barni a nan babu damuwa ta b'angarena in sha Allahu."
Falon shiru ya yi bayan maganarta. Yana zaune bai ce komai ba alamu sun nuna tun a gidanta sun gama maganarsu ya d'aukota ya kawota ne don ya wanke kansa kada mu zarge shi.
Na dubi Hauwa da tun da muke maganar ba ta ce uffan ba na ce." To ke me ki ke ga ni Hauwa."
A takaice ta ce." Duk yadda kuka tsara ya yi mini sister."
Sai na dube shi a nutse na ce." To ka ji abinda kowa ya fad'a menene ra'ayinka?"
"Ra'ayina shine naku giwa, ku tsara yadda kuke ganin za ku zauna babu takura idan kun yi mata alfarmar da ta nema ni a wajena daidaine amma kada wadda ta kalubalanceni anan gaba. 'Yar uwarku ce ta kuma fito ta gaya muku dalilanta nasan zamanta anan din cikinku duk kun sani, idan kun goya mata baya to duk 'karuwar ta mu ce bakidaya."
Ban yi mamaki da sunan da ya kira ni ba, domin a wasu lukutan da sunan yake kira na mussaman idan yana so ya rarrashe ni idan mun yi fada ko neman wata buk'ata. Zai ce giwa ko zinariya
Cike da takaicin maganganun da yake yi na ce." To wa ka ji ya ce bai amince ba, na d'auka ai zaman da muka yi gabad'aya don mu samu matsaya ne a junanmu, ni ta b'angarena babu damuwa tunda har na iya d'aukar rabi na basu rabin na ce su raba a tsakaninsu Allah Ya taimake ka duk wannan maganganun ba su taso ba."
Hauwa ta zum'buri baki tana fad'in." To ni ma dai haka na ga ni."
Ita kam dariya ta yi tana fad'in." Na gode sosai, Allah Ya daidaita zamanmu ya kuma amfani zuriyarmu, na gode ni zan koma." Ta mike tsaye tana gyara yafen lifayar da take jikinta.
Na ce." A haba Hajajju ai babu buk'atar godiya duka taimakon kai ne wallahi kada ki damu an zama daya gabad'aya Allah Ya shige mana gaba."
Ta amsa da "Amin." Fuskarta yalwace da fara'a ta kama hanyar fita tana fad'in." Sai na sake zuwa mu gaisa da yarona yanzu bacci yake yi ba mu gaisa sosai ba." Hauwa ta ce." To shikkenan sai an jima.

Tana fita Hauwa ta dube shi kamar za ta fashe ta ce." Gaskiya zan gaya maka irin yadda kake nunawa matar nan kamar itace take auranka ya yi yawa. Ina lefi akan kawaici da karar da muka yi mata har sai ka fad'i wasu maganganu, ai sai ta d'auka hassada muke yi mata, kuma macace mai mutunci da sanin ya kamata gatanan babu wata matsala a tare da ita."

Ya ce." Mai na yi muku kuma, shikkenan daga na fad'i magana sai ku juya mini, halinta na fad'a tana da sau'kin kai gashi dai duk ta girmeku amma bata nuna muku gadarar hakan. Sannan duk da dukiyar da take da ita bata d'auki kanta a wata tsiya ba, ta sake daku sosai ta daukeku 'yan uwa daga fad'in haka sai ya zama lefi."

Na ce." Mu ai dama ba muce maka wata tsiya ba ne, kuma duk abinda take yi ai ba a sanyata ba gani ta yi zata iya, abinda dai zan gaya maka idan zama ya sake hadamu irin wannan muddin kasan zaka goyu da bayan b'angare daya to kawai ka yi shiru da bakinka domin kuwa yin hakan zai janyo maka bacin rai za ka rikita gidanka da kanka."

Don girman Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya ce." Tunda kece Hajja sai ki ba ni umarni kin ji ko, ku abu kad'an mutum zai yi sai ku zarge shi Allah Ya sawwa'ke."
Yana rufe baki Adam da Yusi suka shigo janye da wata madaidaiciyar akwati gaban Hauwa suka ajiye Adam ya ce." Momi ce ta ce wai gashi na Khalil ne."
Ta ce." Ku ce mata na gode sosai Allah Ya kara arziki."
Suka juya za su fita muka had'a ido da Yusi sai yasa dariya ya rike hannun Adam na d'auke kaina ina fad'in." Taka zata kawo ka wurina ne yaro."
Har za su fita sai ya kira su ya dubi Yusi yana fad'in." Mai ka yi mata take harararka?"
A hankali ya ce." Babu komai Baba, ai muna shigowa kullum mu gaisa da ita ko ?" Ya fad'a yana kallon Adam da yake murmushi. Ya amsa da "E Muna zuwa." Ya ce musu ku tafi abinku rigima take nema."
Suka bud'e kofa suka fita kamar wasu 'yan tagwaye komai na jikinsu iri d'aya ne.

Kaya ne na waje irin wad'anda take sayarwa cike da akwati kayan nan kudinsu zai haura dubu dari uku domin duka babu k'ananu har da takalma da tarkace dai kala kala. Tare muka duba kayan yana zaune bai ce mana komai ba, har muka gama dubawa muka rufe akwatin bai tanka ba daga karshe ma sai ya tashi ya haye ya sama ya barmu a falon mu biyu.

To ganin yadda muka k'ulle muka zama tsintsinya madaurinki d'aya ya sanya shi shiga hankalinsa sosai. Tun ranar da muka yi zaman nan bai sake yin wata magana da ta danganci matarsa ba saboda ganin yadda muka nuna masa ba mu yarda ba a tun farkon fari. Dama neman magana ne kawai tunda na farko ai bai ga mun ware ta ba, sannan bai ga muna neman fitina da ita ba, maganace a ka zauna ana tattaunawa wadda kowa yake da hakki akai to babu dalilin da zai sanya shi ya budi baki ya yabe ta a gabanmu bayan alfarmar da muka yi mata. Macace mai nagarta kuma wadda take amfani da ilminta a inda ya dace. Duk irin kushe da kiyayyar da mutum zai yi a kanta wallahi kyawun halinta sai ya sanya wataran mai kushiya akanta ya yaba mata......
Muje zuwa =ØÞ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*76*
Ina jin kunya da nauyinta sosai, ba don komai ba sai don yadda take k'aunar abinda ya jib'anceni. Na jima ban ga mutum mai kara da kawaici irinta ba.

Daf da zamu tafi Legos muka yi waya da Sahura take gaya mini an kawo kudin Yusra an kuma sanya rana shekara daya mai zuwa. Na ce har saurayin ya gama ginin kenan ta ce mini saura kad'an. Daga sanda muka yi waya da ita na ce zan yi magana da garkuwar mata wadda dama tun asali Sahurar ce ta had'a ni da ita tun lokacin aurana da Alhaji Muntari tun daga sannan da na fahimci magangunta suna da inganci muke zumunci da ita domin daga zarar na bukaci abu zan yi mata waya zata sanya a kawo mini abinda na buk'ata din.
kano take kuma tana aika kayanta kowane gari dole za ta hadawa yarinyar maganin sanyi domin shine abu na farko da ya kamata a fara dashi sannan Yusura bata da cikar kirji sosai har dana gyaransu zan sanya ta had'a mata duka domin kafin zuwan lokacin ta murmure
Na ce da ita idan sun gama magana da ita ni kuma zan tura mata kudin in sha Allahu.
Ta dinga godiya har sai da ta sanya ni na ji haushi na ce ta bari ba na so domin kuwa Yusura haihuwarta kawai ta yi amma na fi ta cin moriya kuma ban yafe mata ba muddin ta sayi ko cokali akan sha'aninta kawai ta bar mini hidimata ta ce. Ta dinga dariya tana fad'in Lallai abin har ya kai haka. Na ce ya wuce hakama a wajena domin kuwa abinda ya shafeni.
Kafin mu tafi sai da na kira Babanmu duka na yi masa bayanin abinda yake faruwa amma ban sanar dashi matsalar da ta kaini wajan Baban Saude ba, sosai ya yi mini addu'a da fatan alheri. Ya kuma tabbatar mini da cewa ana samun cigaba ta bangaran Ummansu Hadiza domin yanzu hankalinta ya fara daidaita ta dawo hayyacinta ta ha'kura da kaddara ta barwa Allah komai. Amma har yanzu Hadiza na can gidan gyaran hali a ajiye ba a kai ga yanke mata hukunci ba ana ta neman ita wadda suka had'a kai suka yi aika-aikar wato Hajiya Alili."
Mun yi waya da anti Yagana na gaya mata za mu wuce legos ban rufe mata komai ba duk na gaya mata irin yadda muka tsara zamantakewar gidan. Ta ce mini hakan da na yi shine daidai a matsayina na babba daga cikinsu dole ni zan dinga 'kokarin d'aukar girma saboda tabbatuwar zaman lafiya.

Sati uku da komawa legos na fara laulaye-laulaye. Ciki fa ya samu abinda ake nema ban gaya masa ba da kansa ya fahimta ya dinga murna kamar me ni dai dariya kawai nake yi masa amma can 'kasan zuciya cike nake da zullumi da fargabar abinda zai kasance bayan na haihu. Shi kuma maganarsa daya Allah Ya sa tagwayene. Kullum abinda yake cewa kenan sai dai kawai na yi murmushi gefe guda kuma na tsananta addu'a akan Allah Ya ba ni d'orarre.
Ban yi tsammanin zai gayawa kowa ba kawai watarana sai Hajja ta kira ni a waya muka gaisa dama kuma sa'i da lokaci takan kira ni, ko kuma ni na kira ta mu gaisa har ta tambayeni zamanmu na ce mata komai lafiya. Cike da farinciki take magana ai maigidan ya gaya mata na samu ciki. Ta dinga ba ni shawarwari akan na kula sosai kada a sake samun matsala irin ta baya. Idan ma ina so sai ta zo ta zauna mini irin na goyon cikin baby Nana aish.
Na ce mata in sha Allahu zan kula sosai amma ta yi zamanta tunda bata da wadataciyyar lafiya bayan haka kuma abun zai zama wani iri muddin Hauwa ta ji labari ba zata ji dad'i ba, abinda haihuwa ba ta farko ba ce, babu wata matsala da za ta faru.
Da wannan na rufe bakinta ta ce mini shikkenan amma dai za ta sanya a rubuce mini al'kur'ani maigirma. Godiya sosai na yi mata muka yi sallama. Hajja macace mai dattako kwarai da gaske tana k'aunata fiye da tunanina don ma an yi yun'kurin shiga tsakanina da ita a baya.

***
Watanni shida ciki ya bayyana ya fito sosai duk wasu gwaje-gwaje da scanning an yi mini tagwayene duk mata. Ya rasa ina zai sanya rayuwarsa duk fitina irin tasa ha'kura ya yi a sati bai fi ya kwanta da ni sau biyu ba wai kada yaran dake cikina suga kamar an takura musu. Acewarsa yawan motsa ni da yake yi zai sanya su dinga shan wahala. Abin sai ya ba ni dariya da mamaki. Tun suna ciki basu fito ba yana nuna musu k'auna irin haka, ai ni ma 'yar wani ce mai yasa bai duba hakan ba, a lokacin da ban samu cikin ba yake galabaitar da ni, wato kenan kowa nasa ya sani.
A haka na yi wata shida a tare dashi a legos babu wanda bai san ina da ciki ba domin kuwa duk ya sanar da iyalinsa Hauwa har bidiyon call muke yi da ita musha hira Khalil ya yi wayo sosai yana koyar zama. Wasu lukutan ma idan na tambayeta yana Ina sai ta ce yana can wajansu Yusi idan ba nono ya buk'ata ba a can yake yini idan ba makaranta. Idan kuma da akwai idan za su tafi sai su mayar mata dashi. Da kanta ba tambayarta na yi ba take gaya mini yadda suke zaune lafiya domin a wasu lukutan ma takan shiga wajanta su hira itama kuma takan shigo. Na ji dadin hakan sosai da sosai, yanzu dai hankalinmu ya kwanta babu wani kishi na jahilici bayan haka kuma dukanninmu ba yara ba ne iyaye ne masu yi wa na kasa dasu nasiha.

Tare muka koma da shi abujan sai da ya yi sati biyu tukkuna suka juya shi da Hauwa da yaronta. Duk dauriyar da ya dinga nunawa sai da na gane hankalinsa gabad'aya yana kan abinda yake cikina kawai don ba yadda zai yi ne ya dawo da ni, ya d'auki Hauwa domin babu irin rarrashin da bai yi mini ba akan na zauna na haihu a can a gabansa a cewarsa sai hankalinsa ya fi kwanciya na ce masa a a, mun riga ai mun gama magana tuntuni babu dalilin da zai sanya yanzu a warware idan har za a yi mini adalci a lamarin wattani uku kacal za su yi a can shi da ita ta dawo a lokacin ma na haihu in sha Allahu rabbi ko da ban haihu ba to kad'an ya rage. Da haka ya ha'kura smma ba don ransa ya so ba.


Littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Bikin Hamusu ne ya tashi gadan-gadan domin kuwa yarinyar da ya jima yana nema burin mahafinta ya cika ta kammala karatunta wannan dalilin ya sanya uban ya ce a d'auki wata biyu kacal a yi a gama komai
Ya kira ni yana gaya mini duk abinda yake faruwa. Na ce masa duk abinda yake bukata ya nemi Usaini domin shi yake kula mini da shagunana ya had'a lefe abinda babu ya fitar da kudi ya saya amma ya yi mata akwatina shida ya kuma sanya mata kaya masu quality. Godiya ya dinga yi mini sosai na ce babu buk'atar hakan domin kuwa duk abinda na yi masa babu fad'uwa hakkinsa ne tunda dukiyar tare muke nema. Gini kuwa dama ya kammala abinsa can unguwar maidile ya sayi fili ya gina irin na zamani tuntuni gidan ya kammalu har bidiyo ya yi ya turo mini. Na ce masa idan sun tare ya nemi solar mai girma ya saya sai a sanya masa a gidan tunda na lura unguwar kamar sabuwa ce bata gama cika ba babu wutar nepa.

***
Bikin ya matso sosai daga can suna ta shirye-shiryen a lokacin cikina watanshi bakwai da satika. Da kyar nake gudanar da abubuwan da suka zame mini dole saboda nauyin da cikin ya yi mini ya yi girma sosai ya kara sanya ni na d'unkule. Amma ina da burin so na ga na samu halartar bikin Hamusu dalili kuwa anan shine yaron ya wuce komai a wurina ni ce uwa kuma uwar dakinsa.
Daga tambayarsa akan ya barni na je tunda ai tafiyar jirgi ce ba mota ba kuma zan motsa jikina na shiga cikin jama'a. Sai abin ya zama rigima saboda ya san ma ba bari na zai yi ba ya mayar da abin tashin hankali ya dinga sakin maganganu har sai da ya fusata ni dama haka yake so na ji haushi mu yi fad'a na kashe wayar raina a b'ace cikin zuciyata Ina fad'in idan ba zaka bari na je ba menene kuma na yin tijara kawai a ce ba zan je ba shikkenan sai magana ta mutu.

Haka aka ci aka cinye bikin Hamusu babu ni uwar biki, sai hotona da ya turo mini nan naga ashe har da su Dada da anti Yagana sun samu damar zuwa bikin. Na ji takaici sosai amma haka nan na ha'kura na yi masa addu'ar samu zaman lafiya madawwami. Amma na yi masa alkawari idan na haihu lafiya takanas zan zayarci kano saboda shi.

***
Duk abinda Ubangiji Allah Ya hukunta walau mai dad'i ko mara dad'i yana da iyaka. Kuma cikar mumini kenan yarda da kaddara kowace iri ce wannan shine yake tabbatar da cewa Allah yana sane dakai kuma duk jarabtar da ya yi maka idan ka cinye ba ba tare da ka bi wata hanyar ka sa'ba masa ba to zai maka tagomashin wanda kai kanka ba ka yi tsammanin irinsa ba.

Haihuwa na yi cikin koshin lafiya haihuwar da ta sake bud'e kofofin arziki da alherai masu yawa. Duk irin zullumi da fargabar da na kasance a ciki a lokacin da nake d'auke da cikin da haihuwar ta zo sai na yi cikin sauki da taimakon Allan da ya ba ni ajiyarsu a cikin cikina. Lafiyata lau hakan nan yaran ma da na haifa lafiyarsu lau duka ba su d'auke da kowace irin lalura daidai da irin murar nan da ake haifar jarirai da ita tagwayena ba su d'auke da ita. Tagwaitaka kuwa gadonta na yi tunda Babanmu ya yi bibbiyu sau biyu ba abin mamaki ba ne.
Tubarkala ma sha Allah shine abinda kowa yake fad'a a kansu domin kuwa yadda Allah ya gina musu jiki da lafiya tun a ciki ba wanda zai d'auka cewa 'yan tagwayene dalili wasu akan haifesu da rashin lafiya irin ta jarirai ko yan'kwanewa da yamushewar fata, su kam kalau suka fito cikin mahaifa daya kamar kuma an tsaga kara babu ita inda suka yi bambanci. Tunda aka haifesu ake ta hasashen da wa suke kama wasu suce da ni, wasu kuma su ce da babansu. Ita Hajja ma cewa ta yi da inna Uwani suke kama mai gabad'aya kenan. Jin haka ya sanya ina Uwani kasa rufe bakinta daga zarar an yi magana sai ta ce ai da ita suke kama. Can dangin Hajja suka kwaso domin ni kaina basa kama da ni balle kuma Babansu Hajja ta ce suna kama da inna Uwani shi kuma ya ce da Samira suke kama matarsa ta farko. Ni dai dariya kawai nake yi musu domin ba ni da ta cewa ganin yaran daidai da yatsuna ba su d'auko ba.
Umara ya tafi a tsakankanin haihuwar ya je ya nuna godiyarsa ga Allah subahanawu-wata'ala. Satinsa daya ya dawo ya ce zai shirya walima domin sake nuna godiyarsa ga kyautar da Allah ya yi masa. Ban so ba saboda ba na so abinda zai kawo rud'ani a zamanmu na ce masa lokacin da aka yi masa haihuwar fari ma bai yi ba sai yanzu ya kamata ya bar shi kawai umarar ma da ya yi ta isa. Fad'in haka ashe lefine a wurinsa yana fad'a na kyaleshi ya yi yadda yake so kudinsa ne kuma yaransa ne ba zan tsara masa abinda zai yi ba, Yana da kyau ya nunawa Ubangiji godiyarsa ta sigogi da yawa tunda Allah Ya yassare masa to babu ruwana idone nawa.....
Humm
Mu je zuwa dai. Tsugonan ta kare ko bata 'kare.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*77*
Rabuwa na yi dashi kawai na daina mayar masa da martani ganin iyayensa Hajja da inna Uwani a gidan, kuma daidai gwargwado suna nuna mini kulawa da kara tare da yin tiriri da yaran mussaman inna Uwani da motsi kad'an idan ana maganar kammanin yaran take amshewa tare da tabbatar da cewa da ita suke yin kama. Dukkaninsu daga ita har Hauwan na kasa fahimtar menene a can kasan zuciyarsu domin duk yadda na kai ga so lallai sai na hango cewa abinda suke yi mini ba don Allah ba ne na kasa sun 'boye sosai kuma ko da da wani kulli a ransu ba su nuna ba, amma zahiri Hauwa ta yi kyan kai da ta iya jimirin kawar da kanta daga jin haushin d'igimin da ya d'auka adalalin samuwar yaran, don gabad'aya tunda aka yi haihuwar ya rasa sukuni haka zalika mu ma haka don motsi kad'an za a yi zai ce ba a yi masa daidai ba ko kuma wata daga ciki ta yi kuka ko yana sama idan ya ji sai ya sauko Yana tambayar dalili har kunya da nauyi nake ji wani lokacin domin inna Uwani ce take dauwaniya da su Hajja tana dan taimaka mata kadan. Gefe guda kuma Hauwa na hidimar d'orawa da saukewa yini take yi a kicin saboda ba mu da mai aiki mace sai maza, na dai kudire a raina duk lokacin da na je kano to kafata kafar baba Tabawa
Sannan ni kaina Hauwa hidima take yi mini ta fannin abinci ga maigidan da tsofffin iyayenta. Lokacin da ya dinga fad'a akan me zan hana shi yin abinda yake so sai da iyayensa suka ji 'kananun maganganun da yake yi sai nema yake yi ya mayar da abin rigima da na gaji kawai sai na rushe da kukan b'akinciki ya ina cikin d'aita da rintsin haihuwa a sanya ni a gaba da tijara, kawai saboda na ce kada a yi walima shine lefi da fad'in bakaken maganganu.

Hajja da inna Uwani suka shiga maganar. Akan na rabu dashi ya yi ai abin alheri ne a tara mutane a ciyar dasu a kuma yi addu'a, dama walima aka sani a tsarin addinin musulunci ba wani abin ba ne. Ganin yadda ya samu goyan bayansu akan hakan ya sanya ban sake wata magana ba, sai da muka yi kwana biyu ba mu yi magana ba sannan muka shirya don shine ma ya dinga neman shirin ganin da mutane a gidan na kula shi domin kada suga kamar ina da mugun hali. Amma ba wani ya'ke masa baki nake yi ba don mugun haushinsa nake ji akan abinda ya yi mini.

Amaryarsa Momi akwati biyu ta yi da kaya kowacce shake wai Hassana daya usaina ma d'aya. Wallahi rasa bakin magana na yi a lokacin da na bude kayan ina dubawa. Da yake duk a gabansu ne Hauwa har tana cewa kada matar nan ta rusa jarinta akan yi wa 'ya'yan miji gwaninta. Ina dariya na ce ko daya tunda ki ka ga tana irin wannan kyautar ta yi nisa ne wata'kila yadda kike d'aukarta ta wuce haka. Hajja ta ce kuma ma dai mai son yi ce domin wasu akan su bayar sun gwammace wuta ta cinye domin Ubangiji yana duba duk wanda ya azurta baya fitar da kazantar dake cikin dukiyarsa da kansa zai fita ta hanyar tashin gobara ko ta wata sigar ta daban. Ta nisa kafin ta cigaba da cewa mijinku shi yake gaya mini cewa har gidan marayu ne da ita a can garinsu jos din tana d'aukar nauyinsu bayan makarantu da massalatai da ta gina duka hobbsi ga tsohon mijinta da ya rasu. Wannan dalilin ya sanya ni jin kaunarta a cikin raina domin kuwa macace ta gari, ina kara horarku ku zauna lafiya da ita, kuma kada ku dauketa a matsayin kishi sai yayarku domin ta girmeku ku muntata da kyau.
Sosai jikina ya kara yin sanyi da sha'anin matar wato

Please Login or Register in order to submit comment