Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni lokacin ma na gama da wani direba inda na d'auki shatar mota guda na biya..
Ya k'araso yana tambayar direban yadda muka yi duk ya gaya masa ai na riga na biya ba tare da ya dube ni ba yake gayawa direban tare za mu tafi.
Na dubi direban ina fad'in.'' Ni da na biya ka kudin motar umarnina zaka bi ko nasa."
Cikin ladabi ya d'an risinar da kansa ya ce." Ranki ya dad'e umarninki zan bi, amma yana da kyau mu tafi tare dashi tunda yana tsoronki ne kin san fuskarki da ta maigidanki ba 'boyayyiya ba ce, ni na yi mamakin ma ganinki cikin tashar nan.
Jin haka ya sanya da sauri na bude motar na shiga domin sam ban yi wannan tunanin ba yanzu abin sai ya zama magana da yayatawa kafafen sadarwa.
Na dubi Sukairaju da yake ta ko'karin sanya akwati a bayan mota na dan leka ta tagar motar a nutse na ce." Ka je ka taho da Yusi ina nan ina jiranka."
Yadda ya amsa da sauri shi ya tabbatar mini da cewa bai kawo cewa dabara na shirya masa ba.
Ina ganin ya shiga adaidaita sahu. Na dubi direban da yake jingine a jikin motarsa na ce." Ka shigo mu tafi na gama magana dashi ya koma gobe zai biyo bayana da yarona."
Ya d'an yi jim yana kallona kamar bai yarda ba, na 'bata rai tare da cewa." Ka ga idan ba za ka je zan fito na nemi wata motar menene hakane?"
Ya bude motar ya shiga ya zauna a mazauninsa jikinsa duk babu k'wari haka ya kunna motar wani abokinsa ya zo ya tsaya suka d'an yi magana kafin ya bar wajan shi kuma ya ja motar muka fita daga cikin tashar sai sannan hankalina ya kwanta.

Don girman Allah ki biyani hakkina kafin ki karanta mini littafi kada ki bar nauyin wani akanki.

Bayan mun d'auki hanya sosai na kira Hamusu domin jin a ina aka kwana nasan tunda mutumin nan ya yi ruwa da tsaki akan lamarin nan da wahala gwaggo bata kwana asibiti ba. Illai kuwa muna gaisawa ya fara da cewa." Yanzu nan da na fito daga wanka nake shirin kiranki wallahi, jiya wajan goma da rabi na samu kira daga maigidanki ya ce mini mota tana zuwa daga asibitin Malam za ta d'auki Gwaggwo babban likita zai dubata sosai. In takaice miki dai Gwaggo tana can an bata gwado kuma jiki da sauki alhamdulillahi na dawo gida domin na yi wanka, anti Amina ki kara yi mana godiya a wajansa lallai yana abinda ya dace da dukiyarsa wallahi anti Amina d'akin da aka kwantar da Gwaggo daban yake da sauran ita kadai ce ba hayaniya kuma tun jiya da daddaren likitoci suka ta zaryar shigowa dubata."
Jikina ya d'an shika kad'an jin yadda Hamusu yake yi mini bayani kamar ya fashe da kuka sai godiya yake yi. Cikin raina na ce.' Haushinka yake ji Hamusu amma saboda iya taku da neman suna ya dabaibayeka da alherinsa ta inda da wahala ka hangi kuskuransa.
Na ce." Babu damuwa Hamusu ai Gwaggwo ta wuce komai, ni ma gani a kan hanya in sha Allahu daga zarar na sauka zan kira wayarka."

Babanmu na kira na gaya masa ina kan hanya. Na kira Sahura itama na sanar da ita, daga nan sai na fara tunanin inda zan sauka, ba zan iya zuwa gidan Hajja ba gaskiya gidanmu kuma babu spece d'akin da na yi zawarci Ummansu Saminu tana kiwon kaji. Kawai sai na yanke shawarar sauka a gidana na kuntau. Yana kulle har yanzu shagon ne dai ake ta hada hada a cikinsa dama mun yi da Hamusu cewa idan auransa ya tashi zai zauna a ciki gidan to an samu tsaiko ne daga bangaran budurwar da yake nema babanta ya ce sai ta yi karatun likitanci shi kuma ya'ki ya canza wata ya dage sai ita yanzu dai an kai kudi an sa rana shakara uku mun ci shekara daya yanzu saura shekara biyu.
Sake kiransa na yi a karo na biyu na umarce da cewa ya sanya yara su wanke gidan su gyara shi sosai, shekara kusan biyu dole a samu datti. Ya ba ni tabbacin cewa kafin na sauka za a kammala.
Koda muka isa ban fito ba saboda ina gudun idanun mutane can tsallaken titin da muke na hangi masu sayar da abaya da hijab da nikab na fito da kudi na ce wa direban ya je ya sayo mini nikab.
Ya kawo mini na rufe fuskata sai kwayoyin idona kawai ake gani. Na kira Hamusu na sanar dashi. Minti talatin a tsakani ya k'araso kan sabon babur d'insa da ya saya.
Na fito daga motar Ina yi wa direban sallama shi kuma sai risinawa yake yi. Har na hau babur din na ce da Hamusu ya dakata dubu biyar na sake bashi bayan kudin motarsa dana biya shi tun a tashar garinsu. Ya dinga godiya kamar ya ari baki, har dai Hamusu ya ja babur din ban daina jiyo sautin muryarsa ba.

Mun hau titi sosai ya ce.' anti ina za mu je ne? Gida zan kai ki ki huta ko kuma asibitin zan wuce da ke."
Na ce." Hamusu kai ni asibiti na fara duba jikin Gwaggo hankali ya fi kwanciya......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky

*TALLAH!*
*Albishirinku mata ´an ™walisa matan da suka amsa sunansu mata, waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na ™awa da ™awa Waya tamkar da dubu, sha ™undum, mai suna?*
*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*
*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*
*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*
*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ´ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*
*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari ™asa_™asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da bu™ata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari ™awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ´ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da ™warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*=ØGÜ<Øûß
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse mela™abin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da ´a mace duk ramarta, da ™anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin daWi*
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da ™ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman ™arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456

*37*
Ya fad'a muryarsa har tana rawa, sai ya ba ni tausayi ni ma na ji idona ya ciko da kwalla dama daurewa kawai nake yi.

Haka muka karya a daddafe har yaran suma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ganin yadda muke cikin alhini da damuwa Yusi dai ya takure a kusurwar kujera har da kuka sai da anti Yagana ta rarrashi tukkuna ya yi shiru.
Garba almajirin anti Yagana ya shigo ya ajiye robarsa a bakin kicin ya shigo falon muka gaisa anti Yagana ta ce ya yi maza ya zuba ruwa a diro amma kafin nan ya fara wanke shi. Har ya juya zai fita sai ya tsaya yana kallon Yusi ya ce." Ka je in ji wannan din nan yama sunansa?" Ya tsaya yana tunani. fadila ta ce." Bak'on da suka zo tare?"
Da sauri ya daga kansa yana cigaba da cewa." E shi ya ce na kira shi yanzu ya je Babansa ya kira waya za su gaisa."
Na dubi Yusi da mamaki a tare da ni, dama duk safiya Yana kiran waya don su gaisa, da farko da Garba ya ce ya je na d'auka Sukairajun yana buk'atar wani abu ne bayan karin kummalon da aka kai masa.
Yaron ya tashi da saurinsa sai na dakatar dashi ina fad'in." Yusi dama Baban yana kiran waya ne ku gaisa kullum?"
Ya ce." E wataran ma har ya ce na bawa su Arif da Sultan su gaisa, ko Arif?" Ya fad'a yana kallonsa. Ya ce." Eh hakane har ya ce a gaishe daku bakidaya.''
Na gyada da mamaki fal a tare da ni. To shin wai me mutumin nan yake nufi ne? Ni ban ma ga amfanin zaman Sukairaju a tare da ni ba, kuma yaro dai ni na haifi abina ba za a yi wannan munafurcin da ni ba, ka sake ni amma ka dinga bibiyar 'yan uwana har da yaron da na haifa da wani namijin.
Na ce ." To koma ka zauna ba za ka je ba."
Anti Yagana da sauri ta ce." Akan me?" Shiru na yi kawai Ina kallonta da mamakin neman dalilin da take yi wanda ta fi kowa sani.
Tana kurbar kunun gyadar da ta tsiyaya kofi ta ce." Ki kyale shi kawai ya je, idan kuma ba so kike ki fito da komai fili ba, ta inda ya fi ki wayo kenan, yadda yake tafiyar da lamarin a siyasance sai ki zuba Ido ki ga iya gudun ruwansa."
Na yi shiru Ina nazarin maganarta. Ni dai da ta barni zan datse alakar ne daga yau din, shi ma Sukairajun na sallameshi don ban ga amfanin zamansa a tare damu ba illa dorawa masu gidan nauyi da ya yi."
Kimanin minti ashirin yaron ya yi da fita sai gashi ya shigo ya zauna yana kallon anti Yagana ya ce." Baba ya ce na gaya miki zai kira ki yanzu."
Da sauri ta ce." To shikkenan Yusifa."
Kawai na saki baki ina kallon ikon Allah. Gabad'aya abincin ma da nake ci sai ya fita daga raina na zuba mata ido a lokacin da ya kirata suna magana akan rashin lafiyar Gwaggwo.
Anti Yagana ta saki jiki da baki tana ta jadadda masa yadda Gwaggwon take jin jiki har da ce masa tana kwance bata iya motsa komai na jikinta.
Da yake handsfree ta sanya wayar ina jin muryarsa tar yana cewa." Ni muna gaisawa da Yusuf na ji ya fashe mini da kuka koda na tambayeshi shine yake gaya mini kakarsa ce babu lafiya kukan yaron ya daga mini hankali kwarai da gaske dalilin da ya sanya ma kenan na kira ki domin na tabbatar ya gaya mini duk yadda aka yi, zan yi waya asibitin Malam din duk abinda ake bukata game da mara lafiyar ba zai gagara ba idan ma gado za su bata hakan zai fi sauki Allah Ya bata lafiya."
Anti Yagana tana ta amsawa da Amin Ya Allah, mun gode sosai da kulawa Allah ya kara arziki da wadata."
Suka yi sallama ta juyo tana kallona raina a tsananin 'bace na mik'a hannu dukkunsu har shi Yusi din ba su ankara ba na kife shi da marin da na tabbatar zai gigita shi .

Kiji tsoron Allah idan har kin san baki biyani kudin littafina ba to kada ki karanta zai fi miki alheri ki ha'kura ko ki biya mai hakki hakkinta.

Illai kuwa a ki'dime ya tashi ya yi hanyar waje hannunsa dafa da kumatunsa hawaye suka fara kasa tsere a kuncinsa.
Anti Yagana ta rufe ni da fad'a tana fad'in." Sai kin je kin tsiyayar masa da ruwan ido haka kawai saboda zalinci zaki kifa masa wannan mugun marin me ya yi miki? Lefin dai ba zai wuce ya gayawa mijinki magana ba, shikkenan fa sai ki lahanta shi.''
Shiru na yi ban tanka mata ba kawai na tashi da zumar barin wajan. Yaron da yake tsaye a bakin kofa ya d'auka dukansa zan sake yi ya fita a guje yana sheshsheka.
D'aki na shiga na zauna a gefan katifa kaina a daure domin duk yadda na kai ga ganin na hasaso abinda mutumin nan yake nufi a kaina na kasa ganewa.
Shin wai ko ya manta da cewar ya sake ni ne, wane irin munafurci ne wannan da neman lallai sai ya d'ora mini lefi. Ka sake ni ka fita daga sha'anina mana.
Wayata na d'auka da sauri kiransa zan yi domin na ji shin me yake nufi da ni ne.
Kamar yana jiran kiran nawa karaf ya daga. A kaurare babu gaisuwa balle girmamawa dalili duk ya zubar da mutuncinsa a idona bana son mutum munafiki.
Na ce." Ban gane abinda kake nufi ba, ko ka manta cewa yanzu babu wata alaka da take tsakanina dakai? Ina ruwanka da bibiyar abinda ya shafe ni. Gwaggwo dai mahaifiyar mijina ce wanda mutuwa ta yi mana kutse ta shiga tsakani, na tabbata kuwa a duniyar nan ba zan sake katari da namiji mai nagartarsa ba. Kana ta bina da sharri, ka yi nan ka 'bata ni, ka bi nan ka 'bata ni, to ta Allah ba taka ba, ka ja tsumman rayuwarka, ba ma buk'atar ko kwabonka, ba na son munafurci ni."

Cikin nutsuwa kamar bai ji zafin maganganuna ba ya ce.'' Ai na mayar dake dama na yi ne domin ya zama gargadi a gare ki. Kuma ba don ke nake tsaye akan abinda ya shafeki ba, saboda wasu dalilai ne, ke ki ka haifi Yusuf amma ya fi ki hankali, kuma saboda shi din na shiga lamarin, ai na san kakarsa ce ko ba itace ta haifi Aminu Salihi ba."
Cikin takaici da b'akinciki na furta." Ban mayu ba, wallahi ban mayu ba na saku har abada ni dakai dama can ba a son raina aka yi ba, ba zaka tozartani ba wallahi ko maza sun kare a duniya ba zan zauna da kai ba, kuma ko mutuwa Gwaggwo ta yi menene abinda ya dame ka, babu ruwanka ba na son munafurci fa." Na sake maimaita kalmar munafurci domin na tunzurashi.
Bai tunzuru ba a tsanake ya ce." Sai ki yi kuma ni dai na mayar dake shekaran jiya na yi sakin jiya da safe kuma na kudire a raina na mayar dake yanzu kuma na sanar miki, don haka har yanzu kina karkashin ikona."
Da sauri ya yanke wayar kamar ya san abinda yake bakina mai muni ne tabbas da bai kashe wayarsa ba sai dai ya ji ruwan ashar a kunnansa saboda yadda zuciyata take a tunzure. Na kasa motsi daga inda nake gumi na yanko mini tsabar tashin hankali kamar yadda ya fad'a a musulunce na mayu tunda ko jini daya ban yi ba kuma ka'idar musulunci jini uku ne na fita daga idda.
Hawaye masu zafi suka fara karakaina a kumatuna. Anti Yagana ta shigo d'akin da karsashinta ganin yanayin da nake ciki ya sanya ta d'an yi sanyi ta tsaya tana fuskantata..."Menene kuma?" Tambayar da ta yi mini kenan.
Cikin k'unci da takaici na ce." Anti Yagana a wannan karon dole ki yi hakuri na d'auki mataki da kaina domin siyarwa kaina mutunci. Yadda na lura da mutumin nan bashi da mutunci ko kad'an kuma yana yi wa mata kallon wulakantattu idan ba haka ba me zai sanya ka saki mace haka kawai babu hujja mai karfi saboda kawai jin dadi gobe kuma ka ce ka mayar da ita addinin bai ce haka ba Anti Yagana ki zauna ke kanki ki dubi lamarin nan a tsanake kada soyayyar da kike masa ta sanya ki danne lefinsa ba fa daidai ba ne abinda ya aikata mini."
Jiki a mace ta ce." Na sani wallahi Amina, kuma bayan ke wallahi tallahi babu wanda ya kai ni jin ciwon sakin da ya yi miki, ni yadda na fahimta kamar bashi da ilimin addini mai zurfi boko ce kawai take dawainiya dashi shiyasa yake ganin kamar abinda ya aikata ba wani lefi ba ne. Abu na gaba kuma kin san shi, abinda ba na sha'awar ya kasance da ni a rayuwata wallahi kema ba na sha'awar ya faru dake, ba na yi miki sha'awar zawarci da lissafin aure don ma Allah Ya takaita gidan alhji Muntari ba ki haihu ba, wannan dalilin ya sanya nake ta dannarki ki yi hakuri ki zauna kowace mace tana da kalubale."
Na ce." Anti Yagana kada ki ce na ki jin maganarki wallahi na fahimci abinda kike gudu, amma dai don girman Allah wannan karon ki kyale ni da mutumin nan kada ki shiga ciki ki ja bakinki ki yi shiru kawai ki zuba mini ido."
"To wane shiri za ki yi akansa kin san dai shi namiji ne ke kuma mace tunda kuma ya ce ya mayar dake bafa yadda za ki yi dole ha'kuri ne naki."
Na sani anti Yagana ba shirin da zan yi akansa amma ba zan koma ba kamar yadda yake tsammani wallahi sai ya tako kafarsa garin nan."
Ta gyada kanta tanà d'an murmushi ta ce." Abu ne me sau'ki ai tunda yana sonki za ki gan shi kuwa.
Ban ce mata komai ba har ta kama hanya ta fice daga dakin.

Tun cikin dare na kammala shirye shirye na don haka gari yana wayewa na fito a kintse da zummar d'aukar hanya tunda d'akin da nake yana da bandaki ban fito ba sai da na shirya tsaf tukkuna. Gabad'aya suna falon ana shirin karyawa hadda maigidan a zaune bai fita ba dama ba kasafai yake fita da wuri ba idan juma'a ce.
Fitowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya na gyara yanayina don ba na so ta dakatar da ni daga kudirin da na yi. A tsanake na ce." Anti Yagana na shirya fa zan tafi kamar yadda muka yi magana jiya wallahi da Gwaggwo na kwana a cikin raina."
Tana kallona ta ce." To kin gayawa mijin naki ko dai ?"
Eh kawai na ce mata a takaice. Yadda ta zuba mini ido shi ya tabbatar mini da cewa ba ta yarda da amsar dana bata bata
Yusi yana gefe a zaune ya yi nairainarai da ido saura kiris ya fashe da kuka dan tun jiyan nan dana mare shi bai zo wajan da nake ba. Kallo d'aya na yi masa na kawar da kaina daga kansa domin Ina so na horar dashi akan abinda ya aikata ko don gaba ya kiyaye furta abinda ba shikkenan ba.
Cikin sigar zolaya Babansu Fadila ya ce." Madam ba gaisuwa ne ko na yi wani lefin ne kuma."
Cike da jin nauyi na ce." Yi hakuri wallahi na d'auka dana fito na gaisheka, gabad'aya hankalina ne baya jikina."
Ya ce." Amma dai kya bari ki karya tukkuna sai ki tafi, da za ki bari ma akwai motar da zata tashi karfe goma sha daya na safe sai na kira direban yanzu."
Na ce." Anya kuwa zan bari ai ka barshi kawai zan iya shatar motar ma gabad'aya babu damuwa.
Cikin dai zolayar dai da ya saba da sigar wasa ya ce." Au na manta Hajiya ce fa uwargidan a wurin Yallabai."
Murmushi kawai na yi na dubu anti Yagana tana tambayata yaushe zan dawo.'
Na ce." Nan da sati guda in sha Allahu zan dai kira ki idan zan taho din."
Ba ta ce komai ba ta fara tsiyaya kunun gyadar cikin wani madaidaicin fulas tana fad'in." Ki tafi dashi ko a mota sai ki kurba kina dai sauka ki kira ni."
Na ce." To shikkenan in sha Allahu......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma na #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*62*
Ganin halin da ya shiga ya sanya mini muguwar fargaba domin kuwa tunda nake dashi ban ta'ba ganinshi a cikin yanayi na rud'u da tashin hankali ba. Tabbas lokacin rasuwar baby Nana ya shiga damuwa sosai amma sai nake ganin wannan lamarin ya fi d'imauta shi fiye da wancan din. Jikina babu kuzari ko na gamin gafara na kama hanya domin fita daga d'akin saboda ban san wacesa irin fitina zamana zai haifar ba. Fargabata da tsananin damuwata kada ya fitar da maganar domin kuwa ya fi ni gaskiya da hujja mai karfi dalili ni tun farko na d'auri kaina da ban gaya masa ina da ciki ba. Idan kuwa zan kafa hujja da cewar ai na zubar da shine domin gudun haihuwar mai sikila ba kowa ne zai fahimce ni ba, da yawa ma wasu za su ga ai don ina da yaran ne ya sanya ni yun'kurin zubar da ciki ba tare da damuwata ba. Amma fa muddin an zauna an dubi lamarin ta fuskar adalci za a fahimci abinda nake nufi. Wannan kadai itace hujjata ko da kuwa maganar ta fasu na tabbatar da cewa ya fi ni hujja mai karfi domin masu k'adaita Allah da tauhidi ai za su ga gangancina domin kuwa tun fil'azal ai haka iyaye da kakanni suke yin auransu su haihu lafiya ba tare da wata rikitarwa irin ta yahudu da nasara ba.
Kai tsaye d'akina na wuce na kwanta don ba zan iya zaman falon ba dalili kwata-kwata bana cikin hayyacina ga jikina babu k'wari don har yanzu jirin bai gama sakina ba.
Anti Yagana ta shigo d'akin ta same ni a kudindine a cikin bargo lokacin ma kuka nake yi amma mara sauti sai na yi saurin rintse idona ina goge hawaye a fakaice bata fahimci komai ba tunda daga bakin kofa ta tsaya tana tambayata ko jikin ne na ce mata a a Ina hutawa ne sai ta juya ta zata fita tana fad'in bari ta kawo mini abinci na ci sai nasha magunguña.
Da kyar na iya cin loma biyar shi ma sai da ta matsanta mini tukkuna na ci sai da ta tabbatar da nasha maganin kan ka'ida tukkuna ta fita daga d'akin.
Sai bayan ishi'i su Hajja suka tafi bayan sun shigo sun yi mini sallama tare da fad'a mini cewa za su sake dawowa domin sake duba ni cikin satin da za mu shiga.
Ina daga kwance muka yi sallama cikin kulawa yadda suka nuna damuwarsu a kaina hakan ya faranta mini sosai sai dai can kasan zuciyata ina jin fargaba kad'an idan har suka samu labarin abinda na yi shin da wace fuska za su dube ni.
Tunda na fito daga dakinsa ba mu sake haduwa ba sai da garin Allah ya waye anti Yagana ta matsa mini lallai sai na rage kwanciya na fito falo na zauna kan kujera hakan zai k'arfafa mini gwiwa domin idan ina yawan kwanciya kasala da ciwon jiki ba za su barni ba.
Saboda haka ina yin wanka na shirya na fito falon na same su suna kallo har da Baba Tabawa na nemi kujera na zauna

Please Login or Register in order to submit comment