Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ibada."
Ya yi shiru bai ce komai ba amma gabad'aya jikinsa ya yi sanyi a haka muka yi sallama ta rako ni har farfajiyar gidan lokacin shi tuni ya shige mota.
Ade ya bude mini kusa da shi na zauna da ledar atamfofin Hajara da madaidaicin fulas din towona. Ina zama a gefansa ya kar'bi ledar ya ajiye kasan k'afafunsa saboda kayan sun yi mini yawa a hannu
Ade ya shiga mazauninsa muka d'auki hanya.
Har muka isa gida bai yi magana ba. Ya rage walwala da nishadi ya yi shiru abinsa tabbacin akwai abinda yake damunsa.
Na daure na fara tambayarsa ko ba ya jin dadi ne ya ce dani 'kalau yake gajiya ce kawai.
Ko da na yi masa tayin towon ma kafin mu kwanta ya ce a a shayi kadai zai sha shima cikinsa ya b'aci.
Na kyale shi kawai na zauna na ci towona na koshi na sauka da kayan na dawo na same shi yana waya da Hauwa jikin yaron yake tambayarta ga yanayin fuskarsa amsar da ta ba shi ba mai dadi ba ce.
Raina ya ba ci sosai wai shin ya ma aka yi Hauwa ta san yaron ba shi da lafiya ne abinda ba tare suke ba, ba fa da gaske ba ne karya take yi ta mayar da shi shashasha tana daga masa hankali saboda ta gane lagonsa akan yara yake yau tace wannan gobe tace wancen kwanaki ta bugo waya tace bata da lafiya yau kuma ta kirkiri ciwo ta d'orawa yaro wane irin jahilci ne wannan. Ta gama gane damuwarsa akan yara shiyasa take amfani da wannan dama. Gashi muna cikin farinciki da soyayya da kulawa lallai sai ta rusa hakan ta kira shi ya dawo wajenta shine hankalina zai kwanta.
Na bude baki ina fad'in." Idan ba ka farga da wuri ba wallahi Hauwa daf take da ta mayar da kai sakarai ko ma nace ta mayar da kai tuntuni shashasha take kallonka."
Ya dube ni da b'acin rai yana cewa." Wace irin magana ce wannan Amina ana 'karyar ciwo ne?"
Na ce." Tunda ba ta da hankali ita don ta yi hakan ai ba abin mamaki ba ne, watarana za ta iya kiran ka ta ce wane ya mutu tunda jahila ce."
Ya yi sakato yana kallona ni ma ina kallonsa na ce." So take yi ka koma gare ta domin ku cigaba da cin amarci a sabon gida, na gaya maka Hauwa ba za ta ta'ba canzawa ba kuma ba zata zauna da ni tsakani da Allah ba sai ta yi mini bita da 'kulli a rayuwata me na tsare mata."
Ya yi shiru kawai yana kallona na cigaba da cewa."Ka yarda ko kada ka yarda Hauwa 'karya take yi Sultan lafiyarsa lau."
Ya ce." Na ji, ke yanzu abinda ki ka yanke a ganinki daidai ne na gaji da wannan abin da ki ke yi mini ni nake auranki ko ke ki ke aurana?"
Da mamaki a tare da ni na ce." Me kuma na yi maka yanzu, gaskiya na gaya maka na ce ka farka ka kuma yi aiki da tunani akan abinda matarka take yi."
Ya ce." Ni ba wannan ne damuwata ba so ki ke na kwanta ki taka ni shine karshen so da kulawa da tarairaya me zan yi miki kuma abinda ya rage kenan."
Sai kawai ya kwanta ruf da ciki ya mike sosai yana fad'in." Ta shi ki hau ki bi ta kaina kawai Amina, hakan zai kara tabbatar miki da cewa kin gama da ni, sai abinda ki ka gindaya mini."
Dariya ta kama ni amma na danne ban yi ba sai na kasa gane dalilin wannan rikicin da ya bijiro da shi a yanzu ban sani ba ko maganar da mahaifiyarsa ta yi a d'azu ce ta 'kara fusata shi shine ya sar'kafe maganar ya had'ota da wata a ganinsa kenan na mallake shi juya shi nake yi."
Na sassauta sosai tare da cewa." Ni dai don Allah ka tashi kada ka sanya mala'iku su tsine mini me ya yi zafi zaka kwanta kace sai na taka ka."
Ya ce." Kin san Allah ba zan tashi ba Amina sai kin bi ta kaina kin wuce hakan zai kara tabbatar miki da cewa kin gama da ni, haba don Allah na gaji wallahi rayuwarki kawai ki ka sani ni ko oho, ki tashi kawai ki yi yadda na umarce ki."
Na yi kasa'ke ina kallonsa har yanzu yana kwance ruf da ciki. Na ce." To ai kamata ya yi ka gaya mini abinda na yi maka sai na baka ha'kuri ba wai ka kwanta ka ce na taka ba, akan wane dalili."
Yana daga kwancen ya ce." Sai na gaya miki ga abinda ki ka yi ke din yarinya ce, ai duk abubuwan da ki ka jima kina aikata mini kin sani, tunda ba k'ank'anuwa ba ce."
Na yi shiru kawai ina kallonsa saboda bakina ya mutu ma gabad'aya ya juyo da fuskarsa yana kallona har yanzu babu wasa a tare da shi ya ce." Ba za ki tashi ki taka ni ba."
Na girgiza kaina a tsanake na ce."Babu halin hakan me yasa zan taka ka Allah kada ya nuna mini wannan rana."

Na kudi ne wannan littafin kada ki karanta ba tare dà kin biya ni hakkina ba.

Ya gyad'a kansa tare da tashi zaune yana fitar da numfashi sama-sama ya jima a haka kafin ya tashi ya shiga bandaki na bi shi da kallo ina girgiza kaina ya fito d'aure da alwala ya hau dadduma.
Haka muka kwana ko hannuna bai ri'ke ba. Da safe na gaishe ya amsa a dakile ya koma ya kwanta bacci ya yi sosai sai wajan sha biyu ya sakko kasa.
Lokacin na gama had'a kayan sanyawata dana ware domin aikawa da Fati na fito da akwatin kayan domin kiran Ayuba na same shi zaune shi kad'ai ya kunna tibi abinda ba dabi'arsa ba.
Ya dube ni muka kalli juna kafin ya ce." Wannan akwatin ta mecece Amina?"
Na ce." Ayuba zan aika gidan 'kanwata Fati."
Ya yi shiru bai ce komai ba yana kallona na ajiye akwatin na bud'e kofa na fita domin kiransa.
Sai da na shigo tukkuna ya biyo bayana na ce masa ya d'auki akwatin ya kai mata sannan na ya gaya mata zan kira ta a waya zuwa dare.
Bayan fitarsa na je na zauna kusa da ni bai kalle ni ba da romot a hannunsa yana duba tashar da zai k'alla.
Na matsa kusa da shi a hankali na ri'ke hannunsa ya dube ni babu yabo babu fallasa ya mayar da hankalinsa kan tibin.
Bakina nasa a kunnensa cikin k'aramin sauti na ce." Babyn love." Ya yi shiru bai ce komai ba. Na zura yatsa a kunnansa ina fad'in. " Ko ka zama kurma ne Allah Ya ja zamaninka my heart."
Ya dube ni yana lumshe idonsa a kasalance ya ce." Menene?"
Na ce." Kai ne my love dina"
"Humm!" kawai ya iya cewa kafin ya janye idonsa daga kaina ya cigaba da daddana romot.
Nasa hannuna a cikinsa ina fad'in." Yunwa kake ji fa, tun jiya baka ci komai ba ina sane gaskiya rayuwata tana cikin had'ari."
Ya dai yi shiru bai tanka mini ba, sai ma ya fara muzurai yana d'an 'bata fuska.
Na dake sosai ina fad'in." Bari na yi maka abinci ko, wane iri ka ke so na yi maka? umm ka fad'i kalar da kake so zan shirya maka yanzu."
Ya yi gyaran murya bai kalle ni ba ya ce." Tafiya zan yi gobe idan Allah Ya kaimu."
Na ce." Na shirya kenan mu tafi tare ko?"
Ya kalle ni da sauri fuskarsa ta d'an sassauta. Sai kuma ya d'auke kansa yana cewa." Duk yadda ki ka gani Amina?"
Na ce." Farincinka shine nawa Habibi za mu tafi tare in sha Allahu."
Ya gyada kansa amma bai ce komai ba.
Na ce." Me zan yi maka fannin abinci."
Ya ce." Ki yi duk abinda ranki yake so zan ci."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." To shikkenan in sha Allahu."
Kicin din na tashi na nufa na fara aikin cikin nutsuwa mintinta ashirin a tsakani ya biyo ni lokacin ina yanka albasa ya furta. "Kawo na taya ki ko."
Kai na girgiza tare da cewa." Ka huta kawai ba ni so ka yanke hannunka ni zan yi komai na samu lada."
Ya tsaya daf da ni a hankali na ji yana cewa." Wane suna ne na ji kin kira ni dashi da zu." Yafad'a yayin da ya d'ora hannunsa saman kirjina.
Na d'an janye kad'an kafin na ce." Suna wane iri Allah Ya taimaki rayuwarka."
Ya girgiza kansa yana cewa." Babyn love da dad'i sunan. Me yasa tuntuni ba ki kira na da shi."
Na ce." Ka manta dai Ina kiran ka dashi mana a wani yanayi."
Ya yi shiru yana kallona har ina jin saukar ajiyar zuciyarsa. Ya ce." Na tuna a yanayin nan da ni dake muke ganin tamkar mu kadai Allah ya hallita a duniya ko."
Na gyad'a kaina ina murmushi na ce." E, amma idan kana so a cigaba da kiran ka da sunan sai a cigaba."
Ya ce." A a ki cigaba da kira na dashi a yanayin nan na mussaman ni tsoho ne idan yarana suka ji ana ce mini baby dariya za su yi."
Murmushi na yi ina fad'in." To haka za a yi kuwa."
A haka na gama shirya abincin muna hira da kalaman soyayya.
A daran Usaini ya zo ya kar'bi sa'kon matarsa na wurin Hajja.
Sannan na ce masa zan je gidan Gwaggo ya ce na shirya mu je tare shima zai gaisheta. Allah sarki Gwaggo ta ji dadin ganinmu bakinta kamar gonar audiga ta samu alheri na kudi a wajensa tana ta yi masa godiya har sai da ya gaji ya hana ta ya ce don Allah ta daina yi masa godiya akan yana rik'on yaran da addini ya bashi damar zame musu uba. Koyaushe idan magana ta tashi zai ce haifarsu ne kawai bai yi ba amma tunda yana aurena ubansu ne kuma addini ya mallaka masa.

***
Yadda na samu Sultan cikin walwala da wani irin kuzari da lafiya ya tabbatar da mini da cewa hasashena akan Hauwa gaskiya ne. Shi kansa uban dana d'auki yaron mussaman na kai masa shi d'akinsa ya d'aga shi sosai yana duba shi fadi yake yi ya k'ara nauyi sosai Amina kin ga dai duka sati daya rabona da shi amma ya yi mini girma a ido ashe Hauwa bata da hankali dama."
Shiru kawai na yi ban ce masa komai ba zuwa yanzu ai ya kamata ace ya gane halin matarsa muguwar ma'karyaciya ce mara son zaman lafiya.
Kwanana biyu da dawowa yara sun yi doki da murna haka zalika ma masu aiki aka kewaye ni ana ta farinciki na dawo na zama kamar ba'kuwa har Baban nasu ya dinga kishi yana jin haushi wai shi ba su damu da shi ba. Yadda ya hak'ikance yana fad'a abin ya yi ta ba ni da dariya.
Da daddare Salim da Adam suka shigo mun jima tare da su a falo muna hira nan Salim yake gaya mini ai yana da lambar wayar Kamalu har ya kira shi ma ya taya shi murna tafiya karatun da zai yi. Ikon Allah kenan gabad'aya yaran sun samu wata iriyar nutsuwa mussaman shi Salim din da ya canza ko maganarsa ma cikin nutsuwa kuma duk wadda zai furta mai muhimmanci ce. Lallai Allah yana kishin bayinsa ya sanya musu nutsuwa da tawakalli babu uwa babu uba, haka zalika babu 'yan uwan uwa nagartattu. Dangin Babansu ne kawai masu nagarta sai Kuma uban rikonsu a yanzu wanda ya zame musu bango. A wannan ga'bar shi kansa maigidan na sara masa domin ya yi namijin kokari kwarai da gaske duk abinda uwarsu ta yi masa na illatarwa ya ture ya rungumi yaran abokinsa domin cikashe wasiyyar da ya bar masa. Hakika ya zama uban marayu ni ce sheda tunda ni ma ga nawa nan ya runguma har yana b'acin rai idan an yi masa godiya bisa abinda yake yi musu.

Sati daya da dawowata komai ya daidaita a gidan mun samu nutsuwa da kwanciyar hankali tun daga kan maigayya da aiki yaran dai kaf muna tare da masu aiki muna cikin nutsuwa da walwala ba ni da damuwar komai tunda ba ni ganin gilmawarta balle ta takale ni ko ta gaya mini banzar maganarta. Ya je ya yi mata kwana biyu ya zo ya yi mini kwana biyuna haka muke yi babu canji kuma shima yana ta ko'karin ganin ya yi adalci domin dai ya nemi zaman lafiya kuma ya samu ta sashena domin ba ni da niyyar d'aga masa hankali akan komai tunda ba ni nake auranta ba abinda yake gabana a yanzu rabuwa da abinda yake cikina lafiya.
Ranar wata lahadi girkinta ne tunda gari ya waye bai shigo ba. Hakan sai ya d'an dame ni tunda bai saba da yin hakan ba yana shigo mana ya jima tare da mu a yi hira haka zalika ma ranar girkina yana zuwa gidanta ya d'auki wani lokaci kafin ya shigo mana.
Na fara nemansa a waya gashi dai tana shiga amma sai a katse na kira ya fi sau shida idan ta shiga sai a katse.
Ga yara tun safe sun tafi tahafiz sai yamma balle na tura Khalil gidan. Bai kira waya ba kuma bai shigo ba abin dai da mamaki.
Wayarsa kuma na kira ana kashe mini. Ban zarge shi kai tsaye ba sai dai zuciyata ta shiga wasi-wasi akan hakan.
Gefin magriba ya kira ni na daga da sauri na ji muryarsa a dashe don da 'kyar ma yake magana yana yi tari na sar'kafe shi yake gaya mini baya jin dadin ya tashi da mura da zazza'bi har da tari. Har da ba ni ha'kuri bai shigo ba kuma bai kira ni ba."
Gabad'aya jikina ya mutu na dinga yi masa sannu. Tabbas bai iya mura ba tunda ta ta'ba kama shi a gidana farko-farkon auranmu na yi jinyarsa.
Na ce masa idan an jima za mu shigo tare da yaran gabad'aya mu duba ka Allah Ya sawwa'ke." Ya amsa da Amin muka yi sallama.
Na zauna cikin damuwa da mamaki. Hauwa ce kenan ta dinga kashe mini waya a maimakon ta d'aga mu yi magana take ganin k'yashin yin hakan. Humm! shine yake ganin za mu zauna lafiya da ita har yanzu bai san wacece matarsa ba Gabad'aya lamarinta ni yanzu tsoro yake ba ni wallahi da jefa ni cikin fargaba. Ba ni da nufin zalintarta ko cutar da ita shiyasa ma muddin nasan ranar girkinta ne ko ya shigo wajena ba ni sakin jikina da shi balle tsautsayi ya sanya mu shiga hakkinta.......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124.... BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*159*
Bayan isha'i na fito cikin hijabina har k'asa kai tsaye d'akinsu Baba Tabawa na nufa, ita da Taburni suna zaune cikin fahimtar juna suna hira Sultan na tsakiyarsu da abin wasansa yana ta wasa gefe guda kuma flat ne da abinci a ciki da alama nasa ne za ta bashi wasa ya d'auke masa hankali
Gaisawa muka sake yi kafin na ce." Sultan za a ba ni aro za mu je gabad'aya domin duba Babansu ne ba shi da lafiya yana ta fama da mura da zazza'bi."
Baba Tabawa ta ce." Subahanallahi ashe ba shi da lafiya dama?"
Na ce." Yau dai ya tashi da ciwon shiyasa ai bai shigo mun gaisa ba." Taburni cikin mutuwar jiki ta furta." Tabbas kuwa, don Allah a yi masa sannu da jiki Hajiya Allah Ya sawwa'ke."
Na amsa da Amin zan gaya masa in sha Allahu."
Muka fito daga d'akin tare da Baba tana ri'ke da yaron tana fad'in." Hajiya Amina ko dai mu je tare ne ya yi miki nauyi ga yanayin jikin naki kema Allah dai ya budi ido lafiya."
Na ce." Bari Khalil ya fito ya d'auke shi ai na ce miki tare duk za mu je da yaran."
Ta ce." To hakan ya yi. Muna tsaye yaran suka fito tare da Mairo dama kafin na shiga sallah na sanar da su. Kowacce da hijabi a wuyanta. Khalil ya fito shima na ce ya d'auki yaron. Suka yi gaba gabad'aya na bi bayansu.
Muna fita farfajiyar gidan masu hidima da gidan suka fara rige-rigen gaishe ni, ina ta amsawa da kulawa, tunda babu lefi tsakaninmu da su akwai mutunta juna sosai.
Masa'udu da yake akwai sabo a tsakanin da yaran dalili shine yake jigalar kai su makaranta
yana ta tsokanar Usaina itace mai tsotsar hannu tana hararsa tana fad'in." Na daina kai ne kake yi ai kai ka koya mini.
Ta k'aramar k'ofa muka fita gabad'aya can muka hangi mota za ta shiga gidan Momi Hajiya Maryam kenan duk da ban gane wanda yake ciki ba amma ganin motar ta tsaya ya sanya ni ma na tsaya. Adam ya fito daga cikin motar ya karaso har wajan da nake tsaye yana dariya yake ce wa." Mama ina yini, ina za ku je haka da daddare, da yaran duka?"
Ni ma cikin murmushi da kulawa na ce." Za mu duba babanku ne baya jin dad'i."
Yanayinsa gabad'aya ya canza ya furta." Ai ba mu sani ba wallahi me yake damunsa?" Ya fad'i maganar a rikice da damuwa a fuskarsa.
Cikin nutsuwa na ce." Mura ce da zazza'bi ka kwantar da hankalinka Adam ba a kwance yake ba."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Mama mura ai ciwo ne mai tsanani tunda har Annabi Muhammadu s.a.w ya yi magana akanta bari na yi magana da anti Nabila tana cikin mota na je daukota daga airport ne sai na zo mu je tare na duba shi."
Na gyad'a kaina ban ce komai ba shi kuma ya juya a gaggauce ya nufi inda motarsa take.
Mamaki nake yi ashe har yanzu Nabila na gidan tare da su. Ko da yake hakan ma ya yi daidai tunda har suka aminta da zamanta wata'kila ta fi sauran 'yan uwan maman nasu gaskiya da kuma k'aunarsu tsakani da Allah duk dai ba a tona zuciyarta an gani ba A
amma dai tsayin wata kusan takwas da rasuwar Maryam take zaune tare da su ban ta'ba jin wani k'orafi ba nasam idan da akwai matsala to tabbas Nusaiba za ta gaya mini."
Ga mamakina sai na ga sun fito daga motar tare da ita. Duk da dare ne amma akwai haske manyan fitilu mabambamta a estate din ta hasken nake hangenta tun daga nesa a yayin da suka jero da tare da Adam din ta ci wata uwar kwalliya cikin wani lece wanda aka yi masa d'inki riga da siket matsatstsu ta k'ara ki'ba ta cika ta ko'ina d'inkin da yake jikinta ya gama bayyana hallitun jikinta tunda ba ta yi amfani da babban mayafi ba da takalmi mai tudu a kafarta wanda yake hade da wata madaidaiciyar jaka mai adon duwatsu masu kyalli. Kana dai ganinta ka ga manyan zawarawan da suka ci suka kuma tayar da kai zawarawa irin na Abuja masu kafacity amma yanayin dressing dinta ya gama bayyana cewa ba ta da mafad'i domin kuwa da da akwai shi ina ganin hakan ba zata faru ba. Irinsu na nan da yawa da suke 'batawa zawarawan da suke gefe a killace domin kare kansu.

Na janye idona a daidai lokacin da suka 'karaso wajan da muke tsaye da yaran. Cikin sakin fuska da kulawa ta furta." Hajiya Amina mun yini lafiya ya yaran duka yanzu Adam ke gaya mini Yallabai babu lafiya wallahi ni ma dawowata kenan gida sati na biyu a dubai."
Na ce." Lafiyarmu lau alhamdulillahi ya su Hanif wallahi kuwa amma da sauki ai ba akwance yake ba mura ce da zazza'bi ke damunsa.
Da yanayi na alhini irin na al'ada ta furta." Mu je ni ma sai na duba shi, Ubangiji Allah Ya kara sau'ki."
Na ce." Amin Ya Allah." Kusan tare muka jera tafiyar ni da ita. Adam ya bi yaran suka yi gaba tunda sune suka san gidan ina jinsa shima yana tsokanar Usai akan dai tsotsar hannu tana ta zum'bura ba'ki idan ya riko hannunta ta fizge ta koma gefe. Nabila sai dariya take yi tana fad'in. Usai iya rigima kenan ashe ba ta daina tsotsar hannun nan ba."
Murmushi na yi wanda babu nisha'di a cikinsa na ce." Tukkuna dai zata daina idan girma ya zo da sauki ma a hakan ai ta rage.
Gidan bai kai wanda nake ciki girma da tsaruwa ba. Amma dai daidai gwargwado an narka masa dukiya shima tun daga wajensa zuwa cikinsa komai na iko ne falon ya tsaru da sabbin kayan more rayuwa kamar dai yadda na gani a hoton da ya d'ora.
Suna zaune shi da ita a falon tana gefansa a zaune ta yi gayu sosai cikin shadda da surfani an yi d'auri mai hawa-hawa sannan an sha yari da sarka da abin hannu. Da yake shadda ce sai ta kara mata kumburi da kwarjini ramar ta 'buya. Yana cikin jallabiya da Loptop dinsa a gabansa gefe guda kuma fulas din shayi ne a ajiye da karamin cup a kusa da shi.
Muka shiga tare gabad'ayanmu. Ta yi wani bala'in shan kunu ta amsa sallamar sai kuma ta yi kasa da kanta.
Shi kam rufe computer ya yi ba shiri saboda yaran gabad'aya kaf wurinsa suka nufa.
"Baba sannu, Baba ina yini baba ya jikin naka?"
Abinda suke ta fad'i kenan Minal har tana ta'ba wuyansa tana cewa." Zazza'bin ma ya sauka ko?" Tana kallon fuskarsa
Yana dariya ya ce."DIN bai sauka ba tunda kun zo zai gudu garinsu.
Hassana ta ta'ba wuyansa a karo na biyu kamar yadda Minal din ta yi ta ce." Babu zafi jikin naka Baba Allah Ya ba ka sau'ki."
Ya amsa da Amin yana ri'ke hannunta, ita kuma Usaina fad'i take yi Baba maganarka wani iri kasha tomtom kaji baba!"
Na ce." Wai ba za ku samu nutsuwa ba ne haka ake duba mara lafiya?"
Suka nutsu tare da samun waje suka zauna. Khalil ya nufe shi da Sultan a hannunsa yana fad'in." Baba barka da dare ya jikinka?" Ya amsa yana cewa." Na ji sau'ki Babana." Ya mika hannunsa ya kar'bi Sultan da yake ta wangale masa
baki yana dariya da gwalantun kiran sunansa.
Khalil din ne ya fara gaisheta a hakimce ta amsa tana wani fizge kanta. Daga nan kuma yaran suka shiga gaisheta ganin yadda yayansu ya yi ta amsa tana ta'be baki.
Maganar Nabila ta katse nazarin da nake na ji tana ce wa." Allah Ya taimake ka an yini."
Ya dube ta babu yabo babu fallasa ya amsa da lafiya a takaice ya ce." Yau ki ka dawo ne?"
Ta furta." Eh wallahi dawowata kenan Adam ya d'auko ni a airport."
Ya yi shiru bai ce komai ba Adam ya shigo dama a waje muka bar shi lokacin da za mu shiga an kira shi a waya.
A nutse ya kàrasa gabansa ya durkusa har kasa yana gaishe shi ya dafa kansa yana amsawa da kulawa ya ce." Mama na gani da yaran gabad'aya ashe ba ka ji dad'i ba Ubangiji Allah Ya kara afuwa."
Ya furta." Na ji sau'ki ai tunda na sha magunguña sai dai rashin karfin jiki kuma na gode sosai Allah Ya yi muku albarka."
Ya amsa da "Amin.
Ita ta fara tashi tana d'an duban Hauwa ta ce." Madam ina yini ba mu gaisa ba."
Shiru ta yi ba ta amsa ba. Sai ma ta d'auki wayarta tana dubawa. Adam ya dinga fad'in." Ina yini tana jinsa sarai sai daga can kuma ta amsa ba tare da ta dago kanta ba.
Nabilan ta yi gaba da zummar fita kafin Adam d'in ya bi bayanta.
Falon ya rage mu kad'ai Hauwa dai ko nahiyar da nake bata kalla ba balle na samu arzikin gaisuwa abin ya ba ni dariya sosai wai ita matar gida tunda ni na zo a ganinta ni zan gaisheta.
A marairaice na ce." Ya jikin naka?"
Ya tsira mini ido cikin wani yanayi kafin." Ya furta." Ba zan ce miki komai ba giwa, wato idan zan rasu baki damu da ni ba ko?"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali cikin 'yar shgawaba na ce." Ka duba wayarka ka ga iya adadin kiran da na yi maka gabad'aya ni da yara yini muka yi da damuwa ba ka shigo ba kuma ba ka ce za ka yi tafiya wani waje ba.
Ya lalubi wayarsa yana cewa." Wajen da ba k'asa nan ake gardamar kokawa bari na duba."
Ya shiga duba wayar yana fad'in." Ban ga kiran ki ba kin kare kan ki ne kawai."
Ya

Please Login or Register in order to submit comment