Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ki ba ni lambar wayarta ki ne."
Maganata ce ta dawo da ni hankalina. A didirirce na ce." To bari na baki." Ban kawo komai a raina ba na fara fad'a mata lambata ta yi serving tana fad'in." Ke yar wane gari ce? Mu dai 'yan Kano ne."
"Na ce." Ni ma 'yar Kano ce, an haife ni a cikin unguwar kabuga."
Maganar Hajjan tasu ta d'auki hankalinmu ni da ita gabad'aya ina take fad'in 'Yar nan shin kina da aure ne?"
Tambayar da ta yi mini kenan. Gabad'aya sai muka zuba mata Idanuwanmu.
"Murmushi Hajiya Saratun ta yi kafin ta ce Hajja kenan, har na fahimci abinda yake kasan zuciyarki."
Shiru muka yi gabad'aya ni dai haka kawai sai na ji gabana na bugawa.

Hajiya Saratun ta Nisa cikin wani yanayi kafin ta cigaba da cewa "Kin yi wa mutumin sha'awarta ko? ke duk maccen da ki ka gani sai ki ce kin yi wa Tajo sha'awa, shi kuwa wannan ina ga haka zai koma ga Allah bai yi aure ba."
Da saurin gaske ta furta." Bakinki ya sari danyan kashi Saratu, wai mai yasa ke ba ki iya magana ba ne, kada ki manta fa muna cikin kasa mai tsarki gaban ka'aba, amma kina nema ki jefi d'an-uwanki da baki irin haka."
Cikin dariya ta ce." Allah Ya baki ha'kuri Hajjata."
Sai ta kalle ni.
"Amina kina da aure ne? Hajja tana tambayarki.
Lokaci guda bakina ya fara rawa, dan wani bala'in kwarjini suka yi mini......."A a yanzu dai bani dashi amma ina shirye shiryen y......"Ai ba a daura ba ko?"
Hajja ce ta katse ni."
Na ce." E ba a daura ba Hajiya amma an kusa."

Sai ta riko hannuna katamau! " Don Allah ki auri Tajo kin ji 'yar nan, na yaba da hankalinki, kuma duk na ji irin addu'oin da ki ke yi akan neman miji nagari, ki sanya a ranki adduarki ta kar'bu shiyasa Allah ya hadamu anan, don Allah don Annabi ki taimakeni ki auri yaron nan kin ji ko."
Gwiwa ta dinga rawa kafafuna sukayi mugun sanyi jin yadda matar take ta hadani da girman Allah har jikinta na rawa. Muryarta na wani irin karkarwa wai sai na amince tukkuna zata sakar mini hannu.
Hawaye suka kwace mini da rawar murya na ce." Hajiya ni ba budurwa ba ce bazawara ce, aurena biyu, ina da yara biyu, sannan ba a auran na taso a gaba ba, neman kudi nake yi duk domin iyaye da yarana, don Allah ki yi hakuri ku bar maganar nan."

Sai kawai itama ta fashe da kuka. Tana ce wa." Ai taimako na ce ki yi, duk abinda kike buk'ata na rayuwa kin samu a wurin Tajo, ni na haifi abina wallahi bashi da matsala, lafiyarsa lau, kaddara ce kawai take d'awainiya dashi, amma in sha Allahu daka kanki komai ya zo karshe "

"Hajja wace irin rigima ce wannan, dan Allah ki sakar mata hannu, kada hankulan mutane ya dawo kanmu, dole sai an bi komai a hankali, idan Allah ya kaddara sai ki ga an yi amma ba wai yanzu a tursasata amincewa ba."

Gabad'aya muka dubeta a lokacin da take maganar ni ina can tunanin abubuwa masu yawa. Mahaifiyarsa tana nan tana shaidarsa mutumin kirki ne, bata san manemin mata ba ne.
"Saratu haka kawai na ji yarinyar nan ta kwanta mini a raina, na tabbata addu'ar da na yi ce Allah ya kar'ba a take, ko kina so na mutu banga abinda Tajo zai haifa ba."
A sanyaye ta ce." Ina so mana Hajja, amma kamata ya yi a bi komai a hankali."

Duk maganar da suke yi hannuna yana cikin nata ta ri'ke kamatau! da kyar na furta." To shikkenan Hajiya zan yi shawara in sha Allahu, duk abinda muka tattauna da mahaifina sai na sanar daku."
Ta sassauta rikon da tayiwa hannuna Kin tabbata."
Kaina na d'aga mata tare da furta"In sha Allahu rabbi, na yi hakan ne domin ta cika ni ba wai don na amince da bukatartata ba.

Maganar da Hajiya Saratu take yi a waya itace ta d'auke mana hankali gabad'aya.
"Cikin dariya take fad'in." Ga mu nan a tare ai ta samu wata yarinya wai dole sai ta aureka tana nan ta ri'ke ta tamau don rigima, to kai Tajo ai ka yi mata kuma."
Da yake hands free ne muna jin muryarsa yana fad'in." Matar aure kuma a ina?"
Ta ce. Anan muka had'u da ita, ni ma kuma na yaba gaskiya na yi maka sha'awarta."
" Ku ajiye maganar nan Saratu, kada ku kawo 'yar mutane ta rasa rayuwarta, na ha'kura da auren nan fa, ba ni ma sha'awarsa gabad'aya."
Abinda ya fad'a ya daga hankalin mahaifiyartasa ta kar'bi wayar ta fara yi masa fada akan me zai sa ya furta haka.
Ha'kuri ya dinga bata har ta sassauta. Yana fad'in." Ina sa ran yau da daddare zan shigo garin sai na ga matar na amince, indai hakane burinki Hajja."
Ta juyo tana kallona." Kin ji shi ya amince ko, kema kin amince ko Amina?"
Shiru na yi ban iya furta komai ba, kawai Ina mamakin karfin hali, da rikici irin na tsufa. Haka kawai daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki. Ni abinda ya fi d'aga mini hankali ma yadda duk matan da ya aura suke mutuwa. Ta ya za a yi Ina ji Ina gani na kashe kaina, akan wane dalili, tabbas dana san taimakon da na yi mata haka zai janyo da na yi gaggawar barin wurin ban tsaya mayar da magana da su ba.
Babanmu na hango Yana zuwa wurin da muke tsaye.
Yana karasowa na ce." Hajja ga Babana nan tare muke da shi." Da sauri ta saki fuskarta. Na ce." Baba wannan mahaifiyar Alhaji Tajo ce wannan dan kasuwar, ita kuma wannan 'yar'uwarsa ce."
Cike da girmawawa ya gaisheta ya d'ora da fad'in." Mun gode sosai da karamancin da akayi mana, Allah Ya saka da alheri, ai yaro ma tuni muka tura shi makaranta yana nan ya shiryu yana ta yi wa al'kur'ani hidima."
Ita dai murmushi take yi don bata gano akan abinda yake magana ba.
Hajiya Saratu ta ce." Kada dai ki ce kuna da alaka da yaron nan Kamalu wanda ake zargin sun yi masa b'arna a kamfaninsa wattanin baya"

Babanmu da sauri ya ce." E, itace mahaifiyarsa ai, yaranta biyu marayu ne ubansu ya rasu, sai Allah ya jarrabi babban da fitina ake ta fama dashi, amma dai yanzu alhamdulillahi."

Girgiza kai Hajjan ta yi ta ce." Lallai akwai shirin Allah a cikin al'amarin nan, shiyasa ya shirya haduwarmu a wuri d'aya, idan an jima Tajo din zai sauka, idan ya so sai ku zo masaukinmu ku same mu domin akwai muhimmiyar maganar da zan tattauna da ku."

Babanmu fuskarsa ta yalwata da fara'a, irin wanda na jima ban ga irinta ba, tun kafin ma ya ji akan abinda ake nemanmu, sai godiya yake yi. Ni dai Ina tsaye sai kace dasashen itace babu abinda yake aiki a jikina sai zuciyata. Domin babu irin sa'ke-sak'en da ba ta yi mini, wai shin me yake shirin faruwa da rayuwata ne?" Ba zan ce da na sani ban zo ba, amma hankali ya tashi ainun ganin yadda jikin Babanmu yake rawa, a hanyarmu ta zuwa masauki yana ta Addu'a Allah Ya sa alheri ne.

Farincikin da mahaifina ya shiga shi ya kara sagar mini da gwiwa na dinga tunanin hanyar da zan bi wurin ganin na yi wa al'amarin da yake shirin tunkaro ni tutsu.

Daf da magariba baba ya sake komawa massalaci domin yin sallah. Ina kallonsa ban yi yun'kurin bin sa ba dalilin rashin karsashi da kwarin jiki. Zuciyata babu irin sake-saken da ba ta yi mini na zuwana garin. Tana raya mini dana san abinda zai faru kenan da ban zo ba.
Matar nan da gaske take nema take yi ta 'ka'kaba mini d'anta wanda babu shi kwata- kwata a tsagin rayuwata. Bai yi mini ba, baya burgeni ko kad'an, kudinsa kuma babu su a gabana. Ina so na samu namijin da Yayi daidai da ra'ayina, mai rufin asiri daidai gwargwado. Wanda yake da ilimin zamantakewar rayuwa da fahimta kamar Yaya Aminu. Amma me za a yi da irin auran su Alhaji Muntari da Tajo, a ganina babu ci-gaba sai dai koma baya.
Auran nutsuwa da kwanciyar hankali ya fiye mini auran sanannan mutumin da duniya ta suturtashi da arziki a zahiri, amma kuma a badi'ninsa mutumin banza ne.
Yadda ake masa kallo kamili babu wanda zan fito na gayawa abinda ya aikata mini ya yarda. Shiyasa barin maganar a cikina ta fiye mini alfanu.

Yanzu dai babbar damuwata yadda zan sa'bule ba tare dana 'batawa Babanmu rai ba, uwa uba waccan matar da ta kwallafa rai a kan na auri d'anta.

Ringing din wayata ya katse mini tunani lamba ce sabuwa kuma special irin ta manyan mutane. Zuciyata na harbawa na daga wayar da sallama a bakina. Muryarta ta karad'e mini kunne.
'Yarinyar kirki Mamanki ce, ai ni na cewa Saratu ta sanya mini lambarki sai mu yi magana, za ku zo ko?"
Duk lokacin da matar za ta yi mini magana nakan rasa kuzari a tare da ni, uwa uba bakina ya kan yi mini nauyin furta mata maganar dana san zata bata mata rai.
Da kyar na iya furta." Baban namu Yana massalaci Hajiya."

"To kin ga Tajo din ma ya iso muna nan a tare ku kadai ake jira, ai shi ya amince ya ce ma ko gobe a daure sai a nemi albarkar ranar tunda Juma'a ce."

Gabana ya dinga duka! Na shiga rawar baki da kyar dai na iya furta."Hajiya don Allah ki yi hakuri kada ki ce na yi miki gardama wallahi ban shirya aure yanzu ba, akwai muradaina da yawa da nake so na cika, kuma ko bayan haka ma mutumin nan ya fi karfina, ni din ba kowa ba ce, haka zalika mahaifina ma ba kowa ba ne a duniyar nan."

Murmushi ta yi a hankali ta ce." Yanzu nan Saratu ta gama yi mini bayani a kanki, mu ba mu kyamaceki ba Amina, me zai sanya ke ki kyamace mu, Tajo gashinan a zaune da bakinsa ya furta Yana sonki domin Shima ya yaba da dabi'unku, kada ki sanya wasu tunane tunane a ranki in sha Allahu alheri ne auran nan naku."

Bakina ya mutu na kasa cewa komai. Ina dai jinta tana sake kashe mini jiki da nasihunta.Wasu hawaye masu d'umi suka fara tsiyaya a kumatuna . Wai shin wace rayuwa ce take Shirin fuskanto ni.Tunda nake ban ta'ba rayawa zuciyata auran mutumin nan ba amma lokaci guda kaddara tana nema ta canza tunana.

Mota suka turo da ita aka d'aukemu ni da Babana.
Masaukin da suke mallakinsa ne saboda wasu alamomi dana gani a wurin.
Yawanci ma'aikatan hausawa ne suke yi musu hidima.

Yar uwa wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba. Hakki dai sunansa hakki komai 'kankantarsa mu kiyaye da hakkin junanmu.

Katafaran falo ne mai d'auke da kayan alatu na more rayuwa. Duk wani abu na morewa da jin dadi akwai shi. Sanyi da wani masifaffan kamshin da nakasa tantance turarene ko 'ya'yan itatuwa ya dinga surnanowa hancina. Hotonsa dana mahaifiyarsa gasunan kala kala a manne a falo. Akwai kuma wasu biyu da yake tare da sarkin garin wanda yake a yanzu.
Hakan ya kara tabbatar mini da cewa lallai Yana da Ido a garin saudia domin gidan ya yi kama dana shahararran balaraben da ya ci ya tayar ya tada a kai a kasar.
Guiwata ta kara yin sanyi kawai sai na zubawa sarauta Allah Ido domin lamarin nema yake ya fi karfina.

Cikin mutuminci da karramanci muka gaisa Hajiya Saratu tana ta tsokanata na rasa abinda zan ce mata. Idan ma na yi yun'kurin yin wata maganar sai jikina ya mutu ganin k'aunar da suke nuna mini basu 'kyamace ni ba.
Hajiyar kuwa bakinta kamar gonar audiga ta sanya an cika gabanmu da abubuwan ci kala kala. Babu abinda ya ba ni sha'awa a ciki. Babanmu dai Ina kallonsa Yana kurbar shayi Yana had'awa da gashashshiyar kaza.

Shigowarsa falon ita ta d'auki hankalinmu gabad'aya. Yana cikin jallabiya fara kal hannunsa rike da wayoyinsa ya zo ya gifta ta kusa da ni kamshinsa ya buge ni. A hankali na bi kafafunsa da kallo farare tas madaidaita ba zaka ce 'kafar namiji ba ce saboda kyau kamar jini zai billo.
Ya d'an tsaya tare da mikawa Babanmu hannu Yana fad'in." Barka da zuwa."
Babanmu ya rike hannunsa sosai yana amsawa.
Ya nemi wuri ya zauna kusa da mahaifiyarsa. Da kyar na daure na danni zuciyata na dube shi.
"Ina yini."
Ya d'an kalle ni babu yabo babu fallasa ya amsa "Lafiya lau ya kike?"

Shiru na yi ban amsa ba. Kawai ma sai na ji kwalla ta ciko idanuna Wannan mutumin ba sa'ana ba ne, bana ra'ayina auran irinsa. Wata'kila ma yana da HIV tunda manemin mata ne.
Hawaye ya fara silalowa a kuncina. Dana san wannan masifar zan riska da na bawa Alhaji Muntari ha'kuri duk tsiya gwara zaman gidansa wallahi.
Ina ji Hajiya tana yi wa Babanmu bayani. Wai ta ji ni a gaban ka'aba ina ta ro'kon miji nagari Wanda zai kula dani ya rike mini yarana. Shine na bata tausayi ta yi sha'awar had'a aurena da d'anta.
Babanmu bai yi wani dogon nazari ba ya amince har da cewa ko gobe a daura.
Na kasa jurewa kuka ya kwace mini da k'arfi na ce." Hajiya ku gafarce ni, ba fa budurwa ba ce ni, bazawara ce, ina da damar za'bawa kaina abinda nake so, don Allah ku kyaleni ban shirya aure yanzu."

Cikin zafin nama Babanmu ya ce." Dama aure shirya masa ake idan ya zo. Kin je gaban Allah kina rokonsa ya Baki miji nagari ya amshi kukanki ya baki mutumin da kowace mace zata yi Sha'awarsa a matsayin mijin aure, shine zaki butulce masa, wato kin fi so kenan ki cigaba da zaman kanki kina yawo zagade-zagade, kina tallata surarar jikinki a duniya ko Amina, ba zan boye miki ba, salon neman kudin nan naki Yana bata mini rai don dai ba yadda zan yi ne, hanyar abincinmu ne gabad'aya. Ni ne mahaifinki na fi so na bud'e Ido na ganki a d'akin mijinki, idan don mu iyayenki da yaranki kike neman kudin to ki bar shi, Ubangiji ya dubi zuciyarki ya had'a ki da Wanda zai kula dake ya kula damu bakid'aya, muddin da hakkina a kanki Amina ki amince da buk'atar da aka kawo miki."

Cikin mashahurin kukan da yake fitowa daga can cikin cikina. Na ce." Baba ku tambaye shi, ai gashinan a zaune yana da tarin matsaloli, ni na san wasu daga ciki, Shima ya san na sani. Ba zan iya auransa ba domin zan jefa rayuwata a rikici."

Ganin kukan da nake yi ya sanya Hajja kuka itama har tana had'awa da tari. Tana so ta yi magana tarin ya sarketa kafin wani lokaci jikinta ya fara rikicewa gabad'aya suka rufo a kanta har da Babanmu.....Sai na nami kukan da nake yi na rasa jin sautin nishinta har inda nake zaune. Babanmu ya juyo inda nake Yana fad'in." Zo nan kusa da ita, tana kiranki."
Na tashi da saurin gaske gabana na bugawa! Na tsorata sosai ganin yadda jikinta ya rikice lokaci daya, ina tsoron kada ta mutu sanadin wannan lamari.

Babanmu ya matsa mini na zauna kusa da ita. Sai ya zamana mun sanyata a tsakiya ni dashi ya rike hannunta daya ni ma ina ri'ke daya. Hawaye ya ziraro daga gefan idonta. Sai na sake tsorata tausayinta ya rufe ni. Wane irin so matar nan take yi mini haka. Kuka na fara yi mara sauti ina dan shafa hannunta a hankali a hankali tana so ta yi magana amma ta kasa yi sai dai zirararan hawaye dake fita. A raunane tare da mikawa Allah lamarin nasa bakina daidai kunnanta na ce." Na amince Hajiya na amince, zan zauna dashi in sha Allahu koda kuwa karshen numfashina ne yin haka, na yarda gobe a daura dan Allah kada abinda na fad'a ya dameki, na amince har a cikin zuciyata....
'
*GARKUWAR MATA*
BINTA UMAR ABBALE
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram normal What'sapp group #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*BOOK2*
*5*
WAIWAYE
Alhaji Tajudden Ibrahimu 'Danbatta kusan zan iya ce muku ya gaji mahafinsa ne wurin gwagwarmaya. Dalili kuwa shine Alhaji Ibrahimu har yau har gobe idan an tashi jero sunayen jajurtattun mutanan da suka yi wa kasarsu hidima dole sunansa ya fito a ciki. A wancen zamanin ya yi da jikinsa kuma ya yi da aljihunsa a matsayinsa na dan kasuwa da yake da kud'i da akidar boko da ilimin addini tare da na zamantakewar rayuwa. Yana daya daga cikin jajurtattun da suka k'watowa kasa 'yancinta. Matarsa daya Halimatssadiya yar uwarsa ce domin da mahafinsa dana nata uwa daya uba daya suke. Mutum ne mai ra'ayi da akida shiyasa ya tsara rayuwarsa yadda yake so kuma Allah Ya amince masa da hakan.
Matarsa daya yaransa biyu har ya koma ga Allah dalilin da ya sanya kenan ko bayan rasuwarsa ba'a yi wata hatsaniya ba. Kaf danginsu suna da rufin asiri kowa yana da nasa babu mai hangen na wani yawancinsu ma sun fi ci da biro 'yan kasuwarsu kalilan ne. Jigo dai a cikin family din shine Alhaji Tajo tunda shine dan kasuwar da ya yi shura a najeria har da wasu kasashen ma.
Tun bayan kammala karatunsa ya fara gwagwarmaya kasuwanci domin shi baya ra'ayina aikin gomanti kamar yadda sauran danginsa suka raja'a. Yi wannan yi wancan, kama wannan saki wancan. Haka ya dinga fadi tashi har Allah kafe shi, ya mallaki kamfanoni akalla sun haura tara tare da gidajen mai sama da biyar bayan manya manyan motocin sufuri wanda suka zama hanyar samun arzikinsa a duniya.
Sai da ya shekara talatin da tara a duniya tukkuna ya fara sha'awar yin aure ba dan bashi da ra'ayi ba sai don sanin cewar ba a hada gudu da susar duwawu!.
Matarsa ta fari auran zumunci suka yi yar kanwar hajiyarsu ce dake zaune a bauchi can dangin mahaifiyarsu su Hajja kenan, a tsarin rayuwarsa yana son mace yar boko kuma yar gayu wadda bata cika jiki da yawa ba, ya fi buk'atar siririya amma mai cikar 'kirji kuma doguwa ko fara ko ba'ka.
yana bala'in son Samira domin itace first love din shi soyayya suka yi sosai kafin ta kai su ga aure. Sai da wata kudira ta Ubangiji ranar da aka daura auransu da daddare ciwon ciki ya murd'eta bata kwana ba rai yayi halinsa.
Tashin hankali wanda ba'a sa masa rana. Ya gigice ya d'imauce! Har ya kusa zautuwa dalilin bala'in son da yake mata kuka kariris ya dinga yi a lokacin gabad'aya ya kasa sarrafa kansa. Haka dai akayi ta koke koke da jimami aka barwa Allah domin shine mai gudanar da komai.

Bayan shekaru hud'u da rasuwar Samira bai kara sha'awar yin wani auran ba, ya cigaba da bunkusa kasuwancinsa duniya na kara suturtashi da taguwar arziki Allah kuma yana kara sahale masa. Hajja ta zaunar dashi kan batun iyali dalili girma ya fara cimmasa shekara arba'in da hud'u ya kamata ace ya tara yara a halin yanzu. Bai yi jayayya da umarninta ba yace ta nemo masa yarinya mai nagarta sai ayi auran.
Haka kuwa akayi Hajja ta sake binkito masa a dangi amma wannan karon family din Babansu ne Alhaji Ibrahimu.
Ayusha yar yayan mahafinsa ce kusan ma itace yar autar gidansu a mata.
Ya amince duk da bata kwanta masa a rai ba, zai yi ne domin farincikin ta.
Aka gudanar da komai baya kasar yana can India harkokin kasuwancinsa. Amarya ta tare a dankareran gidanta ba ango. Kwana goma da d'aurin auran ya dawo. Wata ijaba da hukunci na Allah dawowarsa da kwana daya don ba wani Abu da ya shiga tsakaninsu dalilin gajiyar da ya kwaso bai tunkareta da wata buk'ata ba. Ayusha ta tashi da matsanancin zazzabi wanda ya dinga sumar da ita tana farfadowa. Babu jinkiri bare bata lokaci aka nufi babban asibiti da ita. Ashe tana da zazzabi typhoid dama yakan tayar mata sa'i da lokaci sai dai wannan karon ya zo da 'karar kwana satinta daya a asibiti rai yayi halinsa.
Babu wanda bai tsorata da wanna lamari ba. Kafin kice kwabo kowa ya fara juya al'amarin ana dangatashi da makaru 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ ko dai shafar aljanu da sauransu. Da yake ya riga ya yi suna a duniya duk yadda akayi ga boye sha'aninsa baya boyuwa sai duniya ta ji. Nan take jaridu da kafafan sadarwa suka samu abin yi. Kowace majiya da irin 'karyar da zata girba. Akwai masu cewa ma aljanar da ta aure shi ta gindaya masa sharad'in bashi ba aure. Wasu kuma suna cewa asharadin dukiya da shahararsa babu aure. Shiyasa duk matar da ya aura zata mutu. Zantuka masu kyau da muni suka dinga dawowa kunnansa. Uffan bai ta'ba cewa ba, har kura ta lafa jama'a suka mance da al'amarin, don ma a lokacin harkokin media basu yi karfi ba wata'kila da har yanzu maganar Bata mutu ba.
Hajja ta ki hakura duk da shi din ya sare da lamarin auran. Ta samu inna Uwani kanwarta ce uwarsu daya ubansu kuma itace mahaifiyar Samira ta je mata da buk'atar a yi masa madadi da Hauwa kanwar Samira ce don itace ma take bin ta a shekaru. Inna Uwani ta dinga zille-zille tana kaucewa, yau ta ce wannan gobe ta ce wancan. Duk lokacin da Hajja za ta tuntubeta da maganar sai ta kawo uzuri. Daga karshe ma sai ta dinga Jin wasu zantuka na tashi a cikin dangi inna Uwani da ita Hauwan suna fad'in haka kawai suna ganin kashi da rana ba za su taka ba. Tunda sun rasa Samira sun bar

Please Login or Register in order to submit comment