Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai yasa hannu ya d'auki Yusin din yasa a kafadarsa yana d'an jijjigashi kamar yaron goye. Ya dube ni.
"Idan ba kya so ni ki bar mini shi. Wannan marin da ki ka galla masa ko ni ki ka yi wa irinsa sai na gigice, ke fa ki ka haifi abinki."
Kallonsa na yi muka had'a ido. Yanayin yadda yake maganar shine ya tabbatar da ransa ya baci.

Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Ki dubi yadda yake ajiyar zuciya mugunta ce wannan tsagwaronta. Ko ba haka ba ne?" Ya fad'a yana kallon Sahura.

Da sauri ta ce." Ni ma fad'an da nake yi mata kenan.
Ya juya da yaron a kafad'arsa. Ofis d'insa ya shige dashi.

Sahura ta kalleni jiki a mace ta ce." Wai don Allah me ya faru ne na ga kin fito a fusace! Ni fa jikina duk ya mutu wallahi."

Sahura ki bari kawai wannan mutumin bashi da hali wallahi. Mutumin banza ne.
Cikin zare Ido ta ce." Mutumin banza kamar Yaya?"
"Ki bar maganar kawai Sahura amma Allah sai ya saka mini."
Ina rufe baki suka fito daga ofis din.
kudi da wani irin biscuits ne a hannun Yusi. Ya dubi Sahura cikin nutsuwa ya furta." In sha Allahu ranar litinin jibi kenan zan sa a kawo muku yaronku har gida, Allah Ya kiyaye faruwar haka anan gaba."
Cikin tsananin farinciki ta fara godiya. Bai tsaya amsawa ba ya bar wurin. Ganin haka ya sanya ni ma na kama hanyar fita ina mamakin abinda ya yi babu wanda zai yarda da cewa shine mai neman keta mini haddi.

Ta biyo bayana hannunta ri'ke dana Yusi har tana had'awa da dan gudu domin na yi masu nisa daf nake da fita daga wurin. Ta iske ni tana dan sauke ajiyar zuciya.
Ban dubeta ba hankalina yana kan tsayar mana da abin hawa. Zuciyata a takure, gabad'aya sai duniyar ta fice mini daga rai ganin yadda rayuwar ke gararanba da ni.
Har muka shiga adaidaita sahu tana ta tambayata abinda ya faru a tsakanina dashi. Na yi shiru ban ce mata komai ba. Sai ta ajiye maganar ta fara kwarzanta kyawun hali da nagartar da ya nuna mana. Nan ma ban ce mata komai ba, tana gaya mini kudin da ya bawa Yusi har da dala irin ta amarica biyu a ciki bayan naira dubu sha bakwai data lissafa. Na dubeta tare da furta." Za ki wuce gidanki ne, ko za ki je ku gaisa da su mama.
"Mu je can gidanku Amina akwai maganar da zamu tattauna."
D'auke kaina na yi ban sake magana ba har aka sauke mu, ita ta bada kudin motar muka wuce kamar wasu kurame, yanayi na gabad'aya ya sagar mata da guiwa. Sai satar kallon fuskata take yi.
Muna shiga gidan Yusi ya ruga d'akin Ummansu Hadiza da gudu yana gaya mata ranar litinin Kamalu zai dawo. Sai gasu gabad'aya sun fito tsakar gidan da murna a tare dasu.
Sahura ta tsaya tana yi musu bayani. Ni kuma na bude d'aki na shiga ina jinsu suna ta fad'in." Dama ai an shedi mutumin yana da kirki kwarai da gaske, suna ta gode masa.
Na nemi wuri na zauna, har yanzu kafafuna ba su daina rawa ba. Duk lokacin dana tuna k'azamar maganar da mutumin nan ya yi mini sai na ji kamar na rushe da kuka. Na dinga duban jikina, wai ko zan ga alamar karuwanci a tare da ni. Babu ko daya domin dai shigar mutunci nayi mayafina mai kauri da fadi ya rufe mini kaf ilahirin jikina. D'inkina kuwa riga da zani ne na atamfa. Babu wata alama ta 'karanta ko rashin kamun kai a tattare da ni.....
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*BOOK2
*3*
Hawaye masu d'umi suka kwaranyo mini a kumatu. Sahura ta shigo ta same ni a haka, na kalleta sai zuciyata ta sake tsinkewa. Hawayen suka tsananta zuba. Ta zauna kusa da ni tare da ri'ke duk hannuwana biyu.
"Kawata d'an girman Allah ki gaya mini menene, ko wani abun ya yi miki da ki ka shiga, kin san shaidan ba abinda ba zai aikata ba.

Hancina na ja. Hawaye gaja-gaja a kumatuna na ce." Sahura mutumin nan nema na ya yi da fasikanci wai na zama yarinyarsa, wallahi tallahi ban yi masa sharri ba. Sahura dan Allah me ya gani a tare da ni wanda ya nuna masa ni 'yar iskace."

Jikinta ya yi kwatakes ta dinga kallona gabad'aya ta gaza yin magana tsabar mamaki da rud'ani.
Na sake yan majina a karo na biyu "Na fad'a masa idan har sai ya yi fasikanci da ni zai fito mana da to yara, ya sa a rataye su kawai."

"Kawata na yarda ba za ki yi masa sharri ba. Na san halinki, duk kiyayyar da kike yi masa haka kawai ba za ki kirkiri abinda bai yi ba ki ce yayi, Amma don Allah maganar nan ki barta kada ki gayawa kowa, ni ma na yi miki al'kawari babu wanda zai ji. Kin san idan kin fito kin fad'a wa duniya ba yarda za a yi ba, karshe ma ki jefa kanki a masifa, ki kyale shi da halinsa. Tunda dai Allah Ya tsare ki shikkenan, amma zahiri na girgiza da jin wannan batu, wato Allah A zahiri fir'auna a zucci. Kai amma mutumin nan ya
ba ni mamaki wallahi."

Hannu nasa na goge kumatuna. Jiki a sanyaye na ce." Babu wanda zan gayawa ai, in sha Allahu sai Ubangiji Ya bi mini hakkina, na bar shi da Allah, idan halinsa zai bayyana kowa ya ga sani".

Sai yamma can Sahura ta tafi dan ko gidansu bata shiga ba saboda daf ake da kiran sallah magariba.
Ina idar da sallah Hamusu ya shigo, nan muka zauna muna tattauna maganar. Yana gaya mini ai tun yana kasuwa ya samu labari. Alhaji Tajo din da kansa ya sanar a shafinsa na fece book. A lokacin 'yan jarida suka samu abin yayatawa amma inda gizo ke sa'kar ba duka yaran ya bada umarni saki ba, Kamalu ne kawai, hakan sai ya janyo cece-ku-ce a kafafan sadarwa. Ni dashi muka yanke shawarar da muke ganin itace mafita a garemu baki daya. Makarantar horo da ladabtarwa zamu aika dashi dake can k'aramar hukumar k'iru.
Dama gwaggwo ce abin ji, amma jin hukuncin Allah da muka gaya mata sai ta sake k'arfafa guiwar yin hakan. Na gayawa Babanmu shima ya bada goyan baya tare da fatan alheri.
don haka ana sako yaron da kwana uku muka gama had'a masa komai yana kuka da komai Hamusu ya tasa k'eyarsa domin kai shi makaranta. Cikin zuciyata na bi shi da fatan alheri da addu'ar Allah Yasa karshen fitinarsa kenan. Ina kuma yi masa addu'a Allah Ya sa ya zama kangaran, mahaddacin al'kur'ani mai girma.
tun Yusi na kuka da damuwa har ya warware. Saboda Ina gaya masa d'an'uwansa yana can makaranta zai zama babban malami, sannan ba zai yi almajiranci ba, sa'an nan kuma ba za a daure masa kafafu ba. To
sai ya kwantar da hankalinsa domin yadda na lura babbar matsalarsa a ce Kamalu Yana bara, irin yadda ya ga wasu al'majiran ke yi.

****
Kwanaki suka shud'e aka fara lissafin wattani babu wata 'kwakkwarar magana daga 'bangaran Alhaji Muntari. Har yanzu shi a zaman da ake yi na kira shi na bashi ha'kuri. Gashi har na yi jini uku, na yi iddah bai ce komai ba Baba Sule yayi masifar har ya gaji. Idan ya zo gidan ma ko gaisuwata baya amsawa.
Hankalina ya kwanta. Ba ni da wata fargaba a yanzu. dama Kamalu ne to Alhamdullahi makarantar da aka kai shi muna samun labarin sauyin rayuwar da ya samu sosai daga bakin malaman. Sai na cigaba da gudanar da harkokina kamar koyaushe na fitar da kudi masu yawa na sayo atamfofi masu tsada da shaddodi har da leces na tayar da jari na kaina.
Sai da na kammala din'kunan tukkuna na kira Ya Falmata a waya na gaya mata zan an aiko da kaya. Ta ji dadin haka kuwa dama nemansu ake yi, mussaman wadda take take turawa a Abuja ta kirata a waya ya kai sau nawa.
Ko sati daya ba a yi ba, kayan suka kare Ya Falmata ta had'a mini kudina tsaf dubu dari takwas ta tura mini. Tare da buk'atar wasu.

Na kira Hamusu kan maganarmu ta kwanaki ya nemo mini shago mai yalwa wanda ya kasance a bakin titi zan kama haya sannan ya samu mini k'wararrun teloli da suka iya d'inki na gida da na waje mussaman irinsu sinigal mali da nijar.
Samun telolin bai yi wahala ba, nan da nan aka same su dan har sun haura adadin dana buk'ata.
Shagon ne duk wanda za a samu sai a loko, ni kuma na fi son na bakin titi. Sai ya cigaba da nema cikin ikon Allah aka samu amma yana hade da gida. A titin kuntau. Kuma maigidan ya ce ba zai bada hayar shagon kadai ba dole sai da gidan dubu dari uku a shekara.
Na je na duba wurin, al'karya ce ta jama'a, kuma unguwa ce ta masu hannu da shuni, Ina ganin za a samu alheri a wurin.
Na yi shawara da Babanmu ya amince. Na kira anti Yagana ma na gaya mata ta yi mini fatan alheri.
Sai kawai na roki Allah sa'a, na biya kudin. Karin farincikina ma shagon kato ne zan iya zuba kekuna sama da biyar a ciki.
Zuciyata ta fara raya mini wani abu, hakan ba haramun ba ne, sai dai illar dake ciki, da kuma fassarar da jama'a za su yi mini akai. Allah Ya rufa mini asiri a yanzu na bawa miliyan biyar baya kuma neman kudin nake yi, ba a san abinda gobe zata haifar ba. D'akin da nake bashi da yalwa ga zafin tsiya, Ina ganin zan komai gidan da shagona yake sai na samu 'yar tayin zama. hankalina zai fi kwanciyar da hakan. Ina kallon duk abinda yake faruwa ba, bayan haka zan samu saukin zurga zurga tunda ba ni da abin hawa.
Wannan shawarar ita na gayawa Babanmu. Ya jima yana dawurwura kafin ya amince. Na ce zan tafi da Usaini. Sannan zan nemi alfarma Sahura ta ba ni Yusura.
Da kawu Sule ya ji sai ya hau fada yana cewa na yi arziki zan guji gida na tafi uwa duniya na yi zaman kaina. Allah ya ce Annabi ya ce, dole idan zan tafi na d'auki daya daga cikin yaransa mata.
Na ce hakan ba matsala ba ne Fiddau ta shirya kayanta sai mu tare gabad'aya.
Itama Sahura bata musanta mini ba, ta ba ni Yusura har tana cewa babanta ya ce ya bar mini har auranta. Na yi dariya sosai ina fad'in Allah Ya ba ni ikon sauke nauyi.

Cikin ikon Allah komawata kuntau sai ta fashe mini. Domin na nemi sa'a a wurin Allah, na kuma mika masa al'amura ya kuma dubi zuciyata.
Harkoki suka bud'e mini neman kudin nake yi haikan. Bayan manyan dinkun nan da nake yi ana fitar mini dasu. Har zannuwa Ina sayarwa. Na sanya aka yi mini singbord mai d'auke da tambarin shagona A&A fashion designer wato (Amina Aminu kenan) a jikin bannar din hotona ne cikin ado da kwalliya irin na mutanan nijar da sinigal sun yi masifar kyau. Wani irin jiki ne da ni mai d'aukar ado babu wanda zai ce na ta'ba aure balle yara biyu.
Singbord daya aka sanya shi a farkon titi. Na biyu Kuma aka sanya shi a kusa da shagon.
Hakan sai ya k'ara haskaka lamarin. Cikin unguwar da sauran dake makotaka da ita suka fara kawo mana aiki.

Ba na kwatanta yin hakan akan Fiddau da Yusura dalili iyayensu Amana suka ba ni. Kuma 'yan mata ne, akwai mutanan da ba su da fahimta. Hankalina bai kwanta ba sai da na tabbatar sun cigaba da karatunsu, boko da islamiyya duk makarantun kudi ne har Yusi. Sune dai suke yi mini hidimar gida idan sun dawo, Usaini kuma yana tare da yaran shagona.
Ni kuma aikina tallata kasuwancina a kafafan sadarwa. TikTok fece book Instagram Whasap da sauransu. Sutturuna suka yawaita dalilin fashion din da nake nunawa a duniya bagraoud muke samu a cikin gidana mai kyau a yi mini hotona masu kyau cikin dinkuna kala kala na watsa a Media tare da lambobin wayarmu da location dinmu.
Hakan ya kar'bu mutuka gaya dalilin kyawun suffata. Duk kayan da na sanya sai sun zauna mini.
Kafin wani lokaci na tara followers na ban mamaki. Sai ya zamana 'yan film suka mayar da shago da gidana sansaninsu.

Jin haka hankalin Babanmu ya tashi ainun! Takanas ya zo da sassafe ya rufe ni da fad'a irin wanda bai ta'ba yi mini irinsa ba.

"Amina kada ki ga na zuba miki Ido ki nemi ki zubar mini da mutunci a duniya. Ina samun labarin duk irin abinda kike aikatawa. Wato watsa hotonanki da kike yi media hakan bai wadatar ba har sai kin had'a guiwa da 'yan film me kike so ki zama a duniya, Ashe shine dalilin da ya sanya ki ka nemi da ki kebance ke kad'ai domin ki yi abinda ki ke so ko? To ki kiyayeni wallahi, zan sa'ba miki muddin baki daidaita hankalinki ba, ni ba zan yarda ki juya ni ba don kina ri'ke da gidana hakan ba zai sanya na zuba miki Ido ki zubar mini da mutunci ba."

Duk yadda na so Babanmu ya fahimce ni ya ki sauranta. Ransa a b'ace ya tafi domin ko abinci ma bai zauna ya ci ba.
Na kira anti Yagana na gaya mata duk yadda ake ciki. Ni dai 'yan film din nan ba ni nake gayyatosu ba, zuwa suke yi su kawo aikinsu. Ta ba ni shawarwari masu yawa da kuma addu'oi. Wannan fad'an da Babanmu ya zo ya yi mini akwai sanya hannun mak'iya sune suka tunzura shi, amma dai ta jadadda mini cewa na kiyaye sosai na kuma yi takatsantsan.

Ban fasa tallata kasuwancina ba, amma na kiyaye mu'amulata da 'yan film d'in tunda hakan zai janyo mini matsala.
Allah buwayi gagara misali. Wato duk lokacin da Ubangiji yace kasance akan bawa babu mahalu'kin da ya isa ya dakatar. Zuwa yanzu na bud'e shaguna uku biyu ana hada hadar dinkuna dayan kuma cike yake da zunnuwa mayafai da takalma. Hamusu shi yake ri'ke da shagon zannuwan yayin da Usaini yake tsaye akan biyu.
Na yi k'arfi sosai Allah ya yi mini abinda dole na gode masa. Gidan da nake ciki maigidan ya siyar mini dashi miliyan shida da dubu dari biyu. Abinda nake dashi a yanzu sun haura miliyan ashirin bayan jarin da nake juyawa. Wannan dalilin ya sanya na yanke shawarar biya mana umara ni da Babanmu domin ina so na je d'akin Allah na yi godiya a gare shi.
Ranar dana gayawa Babanmu na biya masa umara da Azimi zamu tafi sai ya fashe da kuka. Yana fad'in." Amina ashe ina da rabon zuwa makka. Ashe a jikinki zan huta Amina, kin ri'ke mini gida, kina kula da ni, kin hana ni shan wahala. Yau kuma kin yi mini albishir din zuwa d'akin Allah. Amina ina ro'kon Allah ya yi mini albarka. Ya bunkusa kasuwancinki ya yara mini zuriararki. Burina a duniya ki yi aure Amina domin Ubangiji ya gama yi miki komai na Jin dad'in duniya."
Na ce." Baba ka daina kuka, duk abinda na zama a duniyar nan kune sila. Aure kuma lokaci ne idan ya zo dole ne zan yi ko ina so ko ba na so, ka yi tayi mini addu'a dai."
Har na baro gidanmu Babanmu bai daina ya sanya mini albarka ba. Matan gidan kuwa kowacce ta watsar da makamanta, idan na je kamar zuma kowa yana so ya jingina da ni.

****
Uku ga Azimi muka tashi zuwa kasa mai tsarki. Fiddau da Yusura kowacce ta tafi gidansu. Domin zamansu su kadai a gidan bai dace ba, dalilin da ya sanya kenan na ce su je gida idan na dawo sai suma su dawo, dama an yi hutun makaranta..

Tunda muka isa kasa mai tsarki koyaushe ni da Babanmu muna harami, dan shi wasu lukutan ma anan yake kwana ni ce nake komawa masaukinmu. Sai dai da safe idan na je na same shi.
Godiyata ga Allah bata yankawa kafin na fara rokar wani abu sai na yi godiya bisa ni'imar da ya yi mini. Sannan na shigar da bukatata. Miji nagari shine burina a yanzu wanda zai ri'ke ni tsakani da Allah ya kuma ri'ke yarana. Ban wuce aure ba kamar yadda kowa yake gaya mini, to idan Allah ya kaddara mini dole sai na 'kara wani auran a duniya ina rokansa ya azurta ni da nagari wanda mutuwa ce zata raba.
Wannan addu'ar ita nake ta nanatawa hannuwana dafe da ka'aba hawaye na kwaranyo mini.

Kunnuwana suka jiyo mini sautin kukan dattiijuwa tana fad'in." Allah wannan yaron bawanka ne, kafi ni sanin abinda yake lullube a cikin sha'aninsa. Ka yi masa komai a duniya Allah ina ro'konka ka bashi ikon duba matar da zai raya sunna da ita. Allah idan bashi da lafiya ta wannan fannin Ubangiji ka bashi lafiya. Ya rabbi Allah idan asiri akayi masa matansa suke mutuwa Allah ka kawo karshen lamarin nan. Ya Ubangiji Allah Ina da buri a duniyar nan kafin ka d'auki raina naga yaran wannan yaro. Allah Ka kawo karshen wannan lamar........Bata k'arasa ba wata mata dokekekiya ta bangajeta duk a kokarinta na zuro hannunta ta dora a kan ka'aba. Abinka da jikin tsufa babu kwari a take ta zube a kasan wurin. Da saurin gaske na bi ta na kamata ta tashi da kyar tana numfashi. Wata mace mai kama da ita ta kutso wurin ta ri'ke gefan kafad'arta tana fad'in." Hajiya sai da na ce miki kada ki shiga jikinki babu kwari, kuma wasu mutanan ba hankaline da su ba. Allah yana jinki a duk inda za ki yi addu'a."
Na ce." Wallahi wata mara hankali ce ta bangajeta, kuma ba ta san ma ta yi ba."
Muka fito sarari da ita kekenta yana can gefe muka zaunar da ita a akai sai numfashi take yi da alama ma bata da cikakkiyar lafiya.

"Sannu fa mun gode sosai ."
Murmushi kawai na yi. Na juya da niyyar barin wurin sai na tsinkayi maganata a karo na biyu bayan godiyar da ta yi mini.
"Kamar na san fuskarki, kina yin film ko?"
Girgiza kaina na yi. "A'a ba na yin film Hajiya."
"Amma dai kamar Ina ganin hotonanki na yawo a kafafan sadarwa mussaman Instagram da TikTok fece book da sauransu."

Babu wata damuwa na ce." E, ni ce, Hajiya Amma ba na film Ina gudanar da harkokin kasuwanci na ne a sahar."
Ta girgiza kanta da murmushi a fuskarta ta furta." To Allah Ya taimaka ya bada sa'a, idan kina neman wata gudumawa sai ki neme ni zan baki lambar wayata. Sunana Hajiya Saratu Ibrahimu 'Danbatta."
Gabana ya fad'i. Tsira mata Ido na yi na 'yan sakkoni, ashe kallon tsoro na yi mata da farko sai yanzu na hangi kamarsu daya da Alhaji Tajo.
Jikina ya mutu sosai. Ashe dattijuwar mahaifiyarsa ce. ita kuma wannan din diyarta ce.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*BOOK2
*4*
"Ko

Please Login or Register in order to submit comment