Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ba su sani ba sun 'bace.
Ina nan tsaye cikin tararrabi kimanin minti ashirin Ummansu Hadiza ta dawo daga yawon shiga makota babu Minal babu dalilinta
Muka koma cikin gidan jikina a mace k'warai da gaske Ummansu Saminu ta sauke abinci ta ce." Ya kamata ki sanar da babanta Hajiya Amina."
Na zauna saman turmi a nutse ina fad'in." Bari mu jira dawowar Ashiru ba ni tsammanin yarinyar nan nisa ta yi. Ina rufe baki kuwa sai muka ji kukanta daga soro na tashi tsaye da sauri.
Ashiru ya shigo da ita a hannunsa ta yi wujiga-wujiga ta ci kuka ta k'oshi har da tabon fad'uwa a goshinta da alamun jini kad'an
Na kar'beta da sauri ina dudduba jikinta gabana na ta fad'uwa ta ri'ke ni tamau tana shasheka ina jin Ummansu Hadiza na tambayarsa a Ina ya same ta ya ce tsallaken titi wani mutum yana yawo da ita a hannu zai nausa da ita titin tudun yola
Na zaunar da ita tare da cire mara riga jikinta da zullumi da fargaba na tube mata wando pant na duba gabanta alhamdulillahi babu wata alama.
Ummansu Saminu ta juye ruwan da yake cikin fulas din shayi na surka na yi mata wanka ta zuba musu abinci suka ci cikin rashin dad'i ta b'ingire ta kama bacci. Na kasa cin komai saboda tashin hankali tabon da yake goshinta shine ya fi d'aga mini hankali kuma har yanzu zabura take yi. alamun a tsorace take har yanzu.
Sai da na yi sallar la'asar tukkuna na ci abincin dafuduka ta shinkafa har da kifi da ruwan pure water. Na d'auki wayata domin kiran Ayuba ya zo ya d'auke mu na mayar musu da 'yar su. Ina laluben lambar direban shi kuma ya kira hannuna ya shiga rawa na daga ban iya cewa komai ba saboda tashin hankali sai nake ganin wata'kila labari ya riske shi abinda zuciyata take raya mini kenan duk da cewar yarinyar ba a san 'yarsa ba ce amma zuciyata ta kasa tsayuwa waje daya.
"Yanzu haka Hauwa tana Dambatta na sanya an kaita Ayuba zai zo ya d'auke ku saboda ganin garin da hadari ina fatan kin kammala uzurin da ya kai ki."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Na gama." Ya kashe wayar bai sake cewa komai ba.
Na dubi yarinyar har yanzu bacci take yi suna kusa da ita sun kasa sakin jikinsu kamar ma sun gaji da zaman gidan suna so a tafi. Ko da na tambaye su amsar da suka ba ni kenan mu tafi.
Na sauke ajiyar zuciya wadda ba zata lissafu ba. A haka na mayarwa da yarinyar kayanta dana cire mata. Ummansu Saminu ta shigo d'akin tana fad'in." Har yanzu ba ta tashi ba ko?"
Kaina kawai na iya daga mata.
Ta d'an dubeta cikin nazari kafin ta ce." Har yanzu a tsorace take kin ga ni duk da tana bacci jikinta rawa yake yi tana zabura wata'kila garin gudun hadari da iska ta fad'i ko wani ya gwabgeta gashi hadarin ya washe ba mu samun ruwan ba Allah sarki ai an auna arziki ma tunda ba a yi nesa da ita ba. Na lura yarinyar ta fi yan'uwanta rawar kai in ba haka duka fa suna zaune a tsakargida suna ta wasa a tare amma fitowata daga kicin na ga babu ita a wajan ta fita kuma maimakon ta tsaya a waje ta nausa.
A takaice na furta." Tsautsayi dai kawai amma sam ba da ita na yi niyyar zuwa ba wallahi Babansu ya kawo mini ita cikin mota tana kuka sai ta bi ni."
Ta gyad'a kanta tana cewa." Hakane abinda ya yi kiranta kenan da mutuwa ce ma haka za a shigo da gawarta."
Gabana ya fadi jin abinda take fad'i itafa dama can haka take ba ta tauna magana kafin ta furta gabagadi ce. Allah Ya kiyaye. Daga yau ma ba ni ba zuwa ko'ina da yarinyar duk rigimar da za ta yi kuwa balle wani tsautsayin ya faru.
Ashiru ya shigo yana gaya mini ga Ayuba can ya zo. Na ce ya d'auki yarinyar ya kaita mota. Na tashi da bismillah muka fito tare da yaran Ummansu Hadiza ta fito daga d'akinta da carbi da alama ba ta jima da idar sallah ba fad'i take yi yarinya kun zo lafiya lau za ki tafi da tabo a goshi abin nan bai yi mini dadi ba wallahi Amina Allah Ya kiyaye gaba."
Na amsa da Amin Ya Allah. Akwai gyare-gyaren da nake so a yi muku a gidan amma dai zan yi waya da Babanmu tunda yau din bamu samu haduwa ba
wata'kila ma gobe ko jibi a fara aikin saboda ba ni son a ja dogon lokaci cikin satin da za mu shiga nake so a kammala komai mu d'auko amarya ta tare a d'akinta.
Ummansu Saminu ta dago labule da sauri ta fito tsakargidan ta tsaya ba ta ji dadin yadda na tsaya muna sake tattaunawa da Ummansu Hadiza ba. Ita kuwa sai dariya take yi tana nuna farinciki a zahiri dai ko da tana jin haushi da bakinciki ba ta fito fili ta nuna ba tana ta daurewa hakan ya kara tabbatar mini da cewa lallai ta tuba kuma duniya ta koya mata hankali sannan neman zaman lafiya da sulhu take yi a gidan.

Muka shiga mota Ayuba ya ja muka d'auki hanyar gida zuciyata cike da zullumi haka zalika ma jikina cike da rashin kwari da karsashi ban iya 'karya ba kuma ba zan fara akan wannan dalilin ba domin kuwa ko da na yi domin na kare kaina watarana abinda na rufe zai iya bayyana ga yaran nan da bakinsu ba ya yin shiru ga kuma tabo na daujewa a goshin yarinyar ko shi ya isa ya nuna aya. Don haka idan ya nemi dalili zan gaya masa. Yarinya dai ban yi niyyar zuwa ko'ina da ita ba ya kawo ta cikin mota ya ajiye tsautsayi ya kira ta ba kuma a son raina ba.
A gidan muka same shi shi kadai zaune a falo da waya a hannu alamu sun nuna dakon jiranmu yake yi.
Ayuba ya dire yarinyar a k'asa dama shi ya daukota tunda har da muka iso bata tashi ba sai yanzu ta fara wuri-wuri na ri'ke hannunta da kyau ganinmu a gida ya sanya ta d'an nutsu ya juyo yana kallonmu. Ayuba ya juya ya fita da sauri.
Kasa ce masa komai na yi na kama hanyar d'akina yaran suka nufi wajen da yake zaune babu wani kuzarin kirki a tattare da su gabad'aya.......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*156*
Cikin nauyin jiki na cire hijab din jikina na zauna gefan gado har yanzu zuciyata bata samu nutsuwa ba dalili nasan lallai ne akwai abinda zai biyo bayan abinda ya faru. Zamana da minti goma ya shigo shi kadai d'akin. Muka dubi juna kafin ya furta." Da gaske ne abinda yaran nan suka fad'i."
Na gyad'a kaina tare da cewa." E, da gaske ne." Domin fad'in gaskiya shine abinda ya kamace ni." Ya yi shiru yana yi mini wani irin kallo na cigaba da cewa suna tare duk a wuri d'aya ta zame ta fita ba tare da kowa ya ankara ba.''
Ya tare ni da sauri ta hanyar fad'in." Ke kina ina har hakan ta faru?" Na ce." Ina d'aki a zaune tare da matan gidan su kuma suna tsakargida suna wasa."
Ya ce." Babu wani abu anan face sakaci da rashin kula Amina me yasa kin san cewa ba su ta'ba zuwa waje ba ki yi nesa da su. Har sai da ta 'bace ta yi nisa tukkuna duka za ku ankara da cewa ba ta gidan saboda kun shagalta gabad'aya."
Na danne haushin da ya ba ni na ce." Duk yanayin kular da zan yi a kansu idan Allah ya aiko tsautsayi babu yadda za mu yi kuma kada ka ga lefina fa yarinyar nan ban yi niyyar zuwa ko'ina da ita ba ka d'aukota ka kawo mini cikin mota. Me yasa don tsautsayi ya faru a kanta a ce ba za a yi mini uzuri ba."
Ya fusata sosai yana fad'in." Ba ki yarda da cewar rashin kula ba ne kenan. Ya za a yi ki je da yara wajan da ba su saba ba ki sake su ke kina wani waje a zaune kuma ki ce a yi miki uzuri akan wane dalili ke ba za ki yi lefi a nuna miki kuskuranki ba kenan."
Na ce." Ba zan fasa fad'in tsautsayi ne ba. Kuma na iya kasancewa akan kowa amma abinda nake so na gaya maka akan yarinyar cewa tana da rawar kai fiye da 'yan uwanta me ya kai ta fita ta bar su tunda tare suke duka a zaune a waje daya suna wasa. Lefin ai ba nawa ba ne gabad'aya."
Ya gyada kansa yana cewa." Tunda kin ce haka wallahi babu inda za ki kara zuwa da yaran nan."
Na tare shi da sauri ina fad'in." Aikuwa ba ka isa ba kaffara ta hau kan ka."
Bai ce komai ba ya juya ya fita cike da b'acin rai.
Na ja tsaki ni ma cikin b'acin ran na tashi domin cire kayan jikina sun yi mini nauyi yamma ta yi sosai don daf ake da kiran sallar magriba. Na sanya doguwar riga cotton mara nauyi da hula na fito falon shiru ban ji motsinsu ba na yi tunanin ko suna sama tare da shi.
Kicin na shiga na dora farar taliya haka kawai nake sha'awar cin ta da manja da yaji da kifi.
Na kammala na fito still ban ji wani motsi ba d'akina na shiga na yi sallah ban sake fitowa falon ba sai da na yi Isha'i na fito babu motsinsu.
Kai tsaye saman na hau na bud'e d'akin nasa babu kowa shiru. A lokacin ne na gazgata abinda zuciyata take raya mini ya kwashe yaran ya yi gaba da su kenan.
Ga abinci na dafa har da su. Na dibi daidai yadda cikina zai d'auka na kira Ayuba na juye musu shi da masu gadi
Abincina na ci na k'oshi na samu yar nutsuwa na kira anti Yagana na gaya mata shawarwarin da na yanke ta sake
bada goyon bayanta sosai amma ba lallai ne ta samu damar zuwa bikin ba tunda tana tare da maijego ba ta yi arba'in ba.
Mun jima tare da Babanmu a waya muna magana har yana yi mini jajen 'batan Minal duk abinda na yanke na gaya masa ya yi ta sanya mini albarka har muryarsa tana rawa.
Bana tsammanin zan kira shi domin na tambayi dalili. Mu tafi a haka kawai domin neman dalilin ma zai kara masa kwarin gwiwa ne.
Hamusu na wakilita kamar yadda na gayawa Babanmu a washe garin ranar aka fara aikin gidan domin sabunta wasu abubuwan. Aikin gidan Usaini ma an cigaba da gyara bangaran amarya kamar yadda na yi masa alkawari duk dai a washe garin ranar da nake gidan namu. Da yamma sai ga Fati ta zo mini da yaranta su biyar yadda na gan su a lalace ita da yaran gabad'aya sai da tsigar jikina ta tashi Fati mai garin jiki da san girma duk ta tsiyaye yaran babu suttura ta arziki duk sun kod'e sun d'angale yaduka masu arha wanda take goyo uku da wata riga irin ta gwanjo hannun da wuyan ya yi masa yawa da wando wanda aka rage gefansa da zare da allura. Tana sauko shi daga bayanta zarni ya cika mini hanci domin dai ba ta sanya masa pampers ba ya kuma yi mata fitsari a jiki da zanin goyon gabad'aya.
Na zura mata musu ido jikina a sanyaye wai shin wace irin rayuwa muke ciki ne a yanzu ki ga mace da 'yan shakaru kad'an ta tsofe ta lalace saboda rashin kula da wahalar gidan aure.
Suka dinga bi daya bayan d'aya suna gaishe ni ina amsawa tausayinsu na tsirga mini wannan rayuwa Allah Ya saukaka mana ita sai na tuna lokacin da ubansu ya fito auran Fati Ummansu ta dinga murna tunda a lokacin yana tashen samun kudi sai dai babu arabi babu boko haka ta tsige mata makaranta duka ajinta biyu a sakandire ta ce karatun ai babu dole ta yi mata aure lokacin Babanmu sai yadda ta yi da shi.
Tana ta washe bakinta take cewa. " Daga gidanmu nake Umma ta ce ai kin zo garin ga ma abin alherin da ya faru na ce bari na kawo miki yara ku gaisa."
Cike da kulawa na ce." Kin kyauta sosai Fati na ji dad'i kuma ina fatan duka kuna lafiya ." Na tambayeta hakan kamar yadda al'ada ta gada amma a zahiri ai duk wanda zai ga Fati ya san ba ta cikin nutsuwa.
Ta yi d'an murmushi tana fad'in." Lafiya lau anti Amina."
Na dafa kafadarta ina cewa." Ki gaya mini idan da wata matsalar Fati ba ki jin dadin auran nan ko."
Ta kuwa fashe da kuka har jikinta na rawa na rugumeta sosai a jikina idona ya ciko da ruwan hawaye yaran suka yi tsuru suna kallonmu na kyaleta ta ci kukanta ta k'oshi kafin ta dago ta goge fuskarta.
Na ce." Gaya mini ko da akwai taimakon da zan iya yi miki."
Ta ja hanci tana fad'in." Babansu ya karye a kasuwa tuntuni anti ga yara a tsakaninmu ba na ma tunanin rabuwa da shi tunda lokacin da yake da shi ya yi mini kuma idan na ce zan kashe auran ban san wanda zan aura anan gaba ba kuma zan yi ta tunanin yarana zuciyata ba zata nutsu ba.amma wallahi anti Amina yunwa tana damun mu ni da yara sannan sai matsalar gidan haya wani abokinsa ya bashi shawara ya sayar da gidansa suka saro kaya karshe kudi ya narke masa duka suka lalace Bai tsira da komai ba. muna gidan haya muna shan tsangwama da gori. Anti Amina ba zan rufe miki ba yunwa ta assasawa Faruku d'auke-d'auke tun bai kai shakarun haka ba ko idan ma'kota sun aike shi ya rage kud'i ya boye. Ba ki ga yaran da yake bi ba yanzu sai na kwana uku biyar har sati ban sanya shi a idona ba. Har shaye-shaye yake yi fa anti Amina."
Ta rushe da kuka tana riruke hannuna.
Faruku shine babban yaronta ya zama saurayi yanzu domin ya girmi ma Kamalu tunda duka sun riga ni aure da haihuwa haihuwarta bakwai da biyar ta zo mini.
Na zura mata ido ina tuna abubuwan da suka shud'e a shakarun baya. Lallai Fati tana cikin jarrabawa. Ban yarda na yi magana ba sai da na daidaita kaina tukkuna na mayar da hawayen da ya ciko mini a kwarmin ido domin kara mata kwarin gwiwa na fara yi mata misali a kaina da sake jadadda mata cewa babu abinda bashi da karshe kuma dukkan tsanani yana tare da sauki.
Yanzu dai babban tashin hankali matsalar yunwa domin itace musabbabin dole kuma a magance ta idan ba haka ba d'aya bayan d'aya yaran za su d'auki hanyar da yayansu ya d'auka
Duk matsaltsalunta da ta gaya mini na gazgata domin ita dama halinta daban da na Hadiza sannan ba kasafai take biyewa Ummansu idan tana wani abin ba abinda dai ta dinga yi mini a lokacin kuruciya na rashin kunya wannan dama d'abia ce ta yaran da suke da uwa a gida mussaman idan an nuna musu su kad'ai ne 'ya'ya masu 'yanci ba kuma su samu tarbiya ba ko a wancan lokacin dama ni su Hassana ne da Usaina ne mutane na mun fi shiri da su haka duka muka dinga rayuwar a gidan to yanzu ga yadda rayuwa ta juyawa kowa.
A dai yadda take a yanzu ko bata bud'e baki ta fad'i damuwarta ba duk mai hankali zai gane cewa tana buk'atar taimako kuma ni ta burge ni sosai da ba ta yi tunanin watsar da yaranta ba. Ta yi hankali sosai saboda idan ta fito shi kansa zawarcin wata babbar jarabawa ce sannan wanene zai kula mata da wannan yaran.
Na ba su abinci suka ci suka koshi ina sake kwantar mata da hankali da bata tabbacin zan yi mata iyakacin bakin kokarina idan har ta yanke shawarar sana'ar da za ta yi zan taimaka mata da jari.
Da za ta tafi na bata dubu goma sannan na sanya Ayuba ya d'auketa a mota domin ya kaita gidanta na kuma tabbatar mata cewa idan hidimar bikin nan da za mu ta kammala zan yi mata Aiken kayan abinci.
Ta yi kuka kamar kamar me har sai da ta karya mini zuciya haka muka rabu da tsananin tausayin halin da take ciki a raina. Watarana sai labari in sha Allahu rabbi.
Ni kadai na sake kwana a gidan hakan bai dame ni sosai ba tunda dama na saba da hakan tuntuni kafin zuwan Baba Tabawa.
Mun yi waya da Hamusu yana gaya mini lefe ya hadu na ce ya kai musu can gidanmu su gani shima angon ya duba idan akwai abinda yake so ya kara a ciki to kafin ya kawo mini ni ma na gani
Mintina kad'an da gama wayarmu shi kuma ya kira na d'auka cikin ko'karin daidaita muryarta. Ya amsa sallamar da na yi na ji yana fad'in." Muna Abuja gabad'aya da yaran yau Hauwa za ta tare a gidanta akwai gidana jikin massalacin da na gina wanda Kamalu ya dinga limanci shekarun baya kin gane shi ko?"
A takaice na ce."A a." Ya furta." Yana cikin estate din na mu can gaba. Nan zata cigaba da zama ke kuma ki zauna a wanda muke ciki yanzu."

Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." To."
Ya d'an yi shiru kafin ya ce." Idan kin kammala Uzurin bikin naki sai ki sanar da ni ko?"
Na ce." Ba ni tsammanin zan dawo ko bayan bikin sai na haihu tukkuna."
Ya yi shiru yana jina bai ce komai ba.
Na ce." Ka ji abinda na ce ko?"
Ya nisa kafin ya furta." To na ji." Ya kashe wayar bai ja maganar ba. Dariya ta su'bce mini ganin ya zama wani sukuku da shi ya daina ja'ina ni kuma na fad'i hakane kawai domin na tunzura shi tunda haihuwa da saura nan gaba kusan wata biyu kuma ba ni haihuwa a wata tara sai na goma ya shiga nasan ya amsa ne kawai ba wai don ya amince ba sai don gudun tashin hankali da alama shiri yake nema.

****
To komai ya yi farko yana da k'arshe haka zalika duk abinda aka sanyawa rana sannu a hankali zai zo a yi a kammala mun yi bikin Usaini cike da annashuwa da walwala an yi komai cikin rufin asiri kuma duk abinda yake na al'ada an yi wa amarya. Gidanta na sanya a shirya mata shi sosai da kayan d'aki daidai gwargwado. 'yan uwan mamansa da Ummansu Hadiza Sahura ta jagorance su d'auko amarya domin ni ko kai kayan lefen ma ban samu sararin zuwa ba saboda hidima da gajiya sai da tare da kwana uku tukkuna na sanya Ayuba ya d'auke ni a mota ya kai ni gidan.
Ta rugunme ni kuwa tsam a jikinta tana murna tana fara'a irin wadda ta saba. Ita dashi Usainin duka sun ba ni mamaki ganin yadda suke jifan junansu da kallon soyayya kamar dama can suna son juna aka yi auran.
Na jima a gidan tare da su domin tun safe nake har yamma na nuna mata abubuwa da dama tare da sanya mata lambar wayata a cikin sabuwar wayar da ya sayo mata na ce duk abinda ya shige mata duhu ta kira ni ta gaya mini.
Sai da na yi magriba tukkuna na kira Ayuba ya zo ya d'auke ni. Muka yi sallama da begen juna.
Kwana biyu hankalina ya kwanta gajiya ta fara warwarewa Ayuba na bawa kudi ya sayo kayan abinci komai da komai na umarce shi zuwa gidan Fati kamar yadda na yi mata alkawari lokacin da ta zo mini.

****
To tunda muka yi waya kwanaki biyu da tafiyarsu bai sake nema ba har aka ci biki aka cinye babu wata magana da ta ratsa tsakaninmu tun bayan wadda muka yi da a k'arshe na ce masa sai na haihu nan tukkuna zan cigaba da zaman abuja. Ban fad'a da niyyar hakan ba kawai tsokana na yi niyyar yi amma ganin ya share bai ce komai ba ni ma na sake gyara zama duk da cewar dai hankalina yana kan yarana amma nasan za su samu kulawa wurinsu Baba Tabawa tunda ya d'auke Hauwa daga gidan.
Da yamma sai ga kiran Nusaiba muka gaisa sosai tana tambayata yaushe zan dawo ta zo har sau biyu sai masu aiki da yara har ta na yi mini Allah Ya sanya alheri ta ji labarin na yi biki.
Ina jin dadin yadda yarinyar take girmama ni sosai na ce mata ina nan tafe a kusa in sha Allahu. Muka yi sallama cikin mutunci.
Duk dai a daran ranar ina duba wayata sannu hankali na ga ya d'ora status ban ta'ba ganin ya d'ora hoton soyayya ba kai hotonsa ma ba d'orawa yake yi balle na iyalinsa ko na yara. Jefi jefi dai yakan d'ora abu nai muhimmanci walau bangaran business din shi ko kuma tunasarwa tun bayan katin d'aurin auransa da ya d'ora satikan da suka wuce kuma shima bai fi da minti ashirin ba ya goge a lokacin da yake cikin rashin nutsuwa kafin ya samu mafita sai shakarun da suka wuce lokacin auransa da Hajiya Maryam nan zan ce naga hotona barkatai a status dinsa.
Sai kuma yau da ya d'ora hotona masu yawa. Na farko farko nasa ne dana Samira Yayar Hauwa matarsa ta fari tun na kuruciya lokacin da suke soyayya. Sai kuma na Hauwa da yaranmu gabad'aya na k'arshe ita dashi ne a sabon gida aka yi musu ya rungumeta ita kuma ta zagaye hannunta a k'ugunsa suna dariya gabad'aya. 'Kasan hoton ya sanya alamar heart da farkon sunansa da na ta.......Nan da nan na ji wani tashin hankali ya yi mini dirar mikiya na nemi yawu na rasa a bakina wani kishi mashahuri ya turnuko mini. Idan ma da gayya ya yi domin ya dyaga mini hankali tabbas ya samu nasara domin lokaci guda na ji tashin hankali tunanika masu yawa suka fara bijiro mini a kaina wato suna can suna cin amarci a sabon gida har da hoto gashi nan katafaran falo wanda ya ji kaya na alfarma, da bai samu nasarar yin sabon aure ba ai gashi ya tare a sabon gida da matarsa suna sha'katawa har da rungume juna da d'aukar hoto cikin nisha'di da annashuwa. Na ji tamkar an d'auki tabarya an rarrad'e mini kafafuna na ajiye wayar ko datar ma ban kashe ba na kwanta ina ko'karin sarrafa zuciyata dangane da yadda take hantsilawa tsabar kishi da tashin hankali. Da na ce sai na haihu zan dawo ashe hakan wata dama ce na bashi domin ya huta.
Can kasan zuciyata na ce mini kada abinda ya yi ya dame ki Amina tunda ta wannan sigar ya b'ullo ku cigaba da tafiya haka har kin manta da halinsa kenan
idan bai sake yi miki maganar ba ki yi masa shiru bari ki haihu anan lafiya cikin 'yan uwa.
Abinda zuciyata take gaya mini kenan. Wani sashe kuma na'kin amincewa da hakan domin kuwa gabad'aya hankali da tunani na yana can idan har na bari muka ci gaba da tafiya a haka Hauwa za ta yi mini dariya buk'atarta ta biya.
'Ko dai ita ta d'auki wayar tasa ma ta dora hotonan domin tasan lallai zan ga ni." Zuciyata take sake gaya mini haka.
Na girgiza kaina ko Hauwa ba ta d'ora hotonansu ba shi ma zai iya d'orawa domin ya jefe ni cikin damuwa, tunda duk ya bi hanyoyin da zai lallasa ni bai samu sa'a ba ya biyo ta wannan sigar.
Na sake shiga Whasap din hannuna na rawa ban ma san me zan duba ba kawai sai na ga an goge hotonan ma gabad'aya babu su. Na sake shiga damuwa da nazarin hakan shine ya d'ora ko Hauwa domin ni a ka diora tunda an lura na ga ni sai aka goge wannan shine amasar, amma har yanzu tunanina ya kasa tantance mini wanda ya yi hakan a tsakaninsu.

Na jima ina addu'a samun sau'kin zuciya kafin na yi shirin kwanciya

Please Login or Register in order to submit comment