Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anti Yaganar. Sai ga Hadiza tana kuka haik'an tana cewa." Anti Yagana kin jima kina nuna mana wariyar launin fata, duk abinda ya danganci Amina kin dinga korarmu kenan ba kya so mu ra'bi inda take sai kace zamu cutar da ita. Dama can kin tsaneni ban san abinda nake yi ba, shi ma Baban namu da ya gaya muku haka bai fahimci yadda ciwon yake ba, amma Fati bata da lafiya kamar yadda na fadawa Aminar gobe ma za mu koma asibitin da ita"
Anti Yagana ta ce." Ai kin iya karya kamar kudin guzuri Hadiza, ni yaushe zan yarda da maganarki gashi saboda baki da mutunci kina karyata Ubanki. Idan kudi kike so ki tambayata mana na san abin duniyarta bai rufe mata Iido ba zata baki sai kawai ku shirya karyar ciwo, itama Fatin da bata da hankali har ta zauna kuke ko'karin dora mata wannan ciwon mai wahalar magani naga wautarta da rashin hankali. Ta numfasa kafin cikin bacin rai ta cigaba da cewa." Wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe wallahi kada ki kuskura ki yi magana da mutumin nan akan ya baku kud'i tunda na lura abin kunya gaba kuka bashi ba baya ba, amma in ba haka ba me zai sanya ku shirya hanyar tsinka mana mutunci a irin wannan gidan, ita kanta 'yar uwartamu Amina duk ranar da mijin nata ya fahimci k'arya kuka shirya shikkenan girmanta zai ragu a idonsa. Idan wata buk'ata ta taso miki a matsayinki na bazawara ki kira ni ki gaya mini zan yi miki daidai gwargwado ko ki kira ita Aminar ki gaya mata dama kun fi kusa, amna kada ku kara irin wannan haukan."
Maganganun anti Yagana sun yi wa Hadiza zafi mutuka da gaske. Ita anti Yagana haka take idan ranta ya baci duk abinda ya zo bakinta fad'a take ko ka mutu ko kayi rai bai dameta ba.

Cikin kumfar baki da tayar da jijiyar wuya don har sai da Anti Sakina ta fito daga d'akin ta tsaya a dokin kofa jin hayaniya na tashi. Hadiza cigaba da cewa." To anti Yagana da kike cewa duk abinda ya same ni na gaya miki ko an fada miki ni ma haka zan zauna a tsiyace, bari fa ki ji arzikin nan Allah ne yake bayar dashi ba wani d'an iska ba, itama Aminar ai takarsa tayi bata gada a wajan uwa da uba ba. Kuma wanda ta yi kafin aure ai na zina ne wanene bai sani ba, fasikanci tayi tana tallata surar jikinta a duniya wanene ya san iya adadin manyan mutanan da suka nema ta har ta tara dukiyar. Idan lokacina ya yi wallahi daka ke har ita sai kun jira aikin banza aikin......Ai ba ta jira ta krasa ba ta kashe wayarta jikinta yana 'bari ta zauna a saman kujera tana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wai Hadiza ce take kiran Amina da karuwa saboda abin duniya.
Ba ta yi mamaki ba domin dama can sun nuna mata kiyayya. Tunda take bata ta'ba nuna bambanci tsakanin 'yan uwanta ba, duk ta daukesu daya da Aminar da suka fito ciki daya. Ko yau Amina ta yi lefi kwatankwacin irin wanda Hadizan ta yi sai ta ci mutuncina wata'kila ma nata ya fi na Hadizan, amma ta girgiza mutuka da gaske da jin wannan furucin daga bakinta..
Ba ta ha'kura ba dai ta kira Fati a waya suka gaisa sosai nan ta fara tambayata yanayin ciwon nata.
Fati ta ce." Typhoid ne ya matsa mini anti wallahi har sai da naje gida akayi mini 'karin ruwa kwanana biyar sannan na dawo. Amma yanzu da sau'ki sosai jikin."
Anti Yagana ta girgiza kai cikin damuwa ta ce.' Allah ya kara sauki Fati ki yi hakuri da yadda kika samu rayuwa kowane bawa akwai kaddarsa ki zauna ki kula da yaranki ki basu tarbiya sosai tunda duk rintse ko babu dad'i mijinki zai baku ku ci to kiyi ha'kuri kada ki yi sha'awar fitowa domin lamarin ba zai miki kyau ba, duk abinda kike buk'ata ki gaya mini ta waya muddin bai fi karfina ba zan yi miki in sha Allahu rabbi."
Cike da jin dadi ta ce." To na gode sosai anti Allah ya saka da alheri. Su kayi sallama bayan ta yi mata al'kawarin tura mata kudi a daran ranar tunda tana da lambar asusunta wanda dama sa'i da lokaci tana yi mata alheri.
Wayarsu da Fati ya tabbatar mata cewa itama bata san abinda Hadizan ta shirya ba wanda har ta jingina mata ciwo. B'angaran ita Fatin din kuwa Hadiza ta bukaci asusunta aro inda ta ce mata mijin Amina ne zai bata jarin Amma ita Fati din bata ganin alert sakamakon matsalar da asusun ya samu sai dai duk sanda aka tura mata kudi a kira ta a gaya mata an tura abu kaza dama ba wani ajiya take yi dashi ba shiyasa ma bata ta'ba transfer ba. Yanzu ATM din yana hannun Hadiza tana ta zurga-zurgar zuwa banki domin fitar da kudin.

Anti Sakina ta fashe da dariya tana daga tsaye a dokin kofar dakinta ta ce ." Yau dai karshen kumbiya-kumbiya ya kare kunnena ya ji abinda kuke ta boyewa. Ke yanzu don Allah Hadiza ba ki ji kunya ba. Shi fa sharri dan aike ne, duk inda ya je zai dawo. Ki ci ki sha daga taskar Amina amma kike bin ta da kazafi irin na zina. Kin je gidanta kin share watanni kin yi bul bul hakan bai ishe ki ba sai da ki ka damfaro makudan kudi da karyar ciwo, amma saboda 'kin gaskiya kin zo kina kumfar baki wallahi duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba tasa ma ko d'umi ba zata yi ba, kun ji kunya daka ke har uwarki kuma wallahi tallahi sai na gayawa babanku abinda kuka yi."
Hadiza cikin fitsara ta ce." To ki gaya masa mana sai me idan kin gaya masa aikin banza da wofi 'yar b'akinciki ai mun fi kusa da ita tunda uba muka had'a ke kuwa fa."
Anti Sakina ta ce." Sakarai kawai haka zakiyi ta zagari a gari tunda zuciyarki bata da kyau."
Ummantasu tana ji suna cacar baki ba tace komai ba, ba kuma ta da niyyar tsawatarwa da Hadizan akan ta yi shiru tunda duk lalacewarta ai matar ubanta ce.
Daga karshe dai anti Sakinar ita ta gaji ta yi shiru hakan ma ya faru ne sakamakon shigowar Usaini shine babban d'anta, ya hanata magana tare da tura ta d'aki ya fito bai kalli inda Hadizan take tsaye ba tana ta zuba ruwan ashariya kamar 'yar maguzawa. Dama basa magana sakamakon yana jin haushin rashin kunyar da takewa babarsu shiyasa kawai ya fita daga harkarta. Saminu ne idan yana gidan bai fita yawon gwangwan d'insa ba yake shigarwa Umman tasu har akwai ranar da ya d'auko d 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~utse irin na wuta daga waje ya saita Hadizan ya jefa mata Allah ya kiyaye ya sauka a gefan kafarta. Ta kama shi da duka kuwa shi kuma yana ta d'ura mata ashariya, da k'yar Ummansu ta kwace shi daga hannunta.

***
Wani irin zaman lafiya muke yi kamar ba sabon ango ba sai wani lallaba ni yake yi yana ji da ni. Ban yi mamaki ba domin duk namijin da zai kara aure indai mai ilimi da hankali ne yakan fito da dabaru domin tausar zuciyar uwar gida. Aka ba ni kudin dannar kirji miliyan sha biyu da kujerar umara. Na dinga godiya kuwa ina ta Tsallen murna sam na ki nuna damuwata duk kuwa da cewa abin yana ta damuna. Na ji dadin kujerar umarar dana samu hankalina zai fi kwanciya idan na dan yi nesa har su gama cin amarcinsu tukkuna. Sahura ta dame ni akan lallai ni ma fa sai na kara gyarawa da muna waya kwanaki na ce mata ni koyaushe a cikin gyara nake ni kaina na sheda ni'ima ta wadace ni. Ina Kuma jimanta yadda zan yi tsayin kwana bakwai ba tare da shi ba domin kuwa Allah ne da kullum duk dare sai mun yi, a wasu lukutan ma har breakfast muke yi kafin na sakko daga samansa nasa shine kawai idan na tuna yake damuna domin kuwa na yi mugun sabon da zan ji jiki mutuka da gaske.

Inna Uwani tuni ta tafi tunda d'aurin auran ya rage sati daya ta tattara ta tafi bayan ta kwamushi kudi a wajensa, shi dai Allah ya taimakeshi abin duniyarsa bai rufe masa ido ba, gashi bai iya kyauta ba da yawa yake bayarwa.
Yau saura kwana biyu d'aurin aure mai kitso da k'unshi ta zo har gida ta yi mini ja da baki. Kitson kuwa cewa na yi tayi mini irin na mu na bare bari na gaba tayi mini tunda ba lefi akwai sumar.
Ya kuwa burge shi sosai saboda rashin abinyi har sai da ya lissafa kitson tamaninin da daya ne. Ni dai dariya kawai nake yi masa. Duk kiran da Hauwa za ta yi masa baya d'agawa a gabana, sai ma ya sanya wayar a jirgi ya share.
Cikin zuciyata na yi ta jin dad'i ganin babu boka babu Malam na kame zuciyar abina wanda ni kad'ai na san sirrin faruwar hakan.
Wato kishi bala'i ne ban ta'ba gazgatawa ba sai da maigidan ya kira ni a waya yake tabbatar mini da cewa an dauransa da Hauwa yanzu amma ba zai sake kwana ba komai dare a gida zai dawo.
A lokacin k'irjina nauyi ya yi mini bayana ya rike ulcerta tana neman tashi wadda tun ina budurwa rabon data motsa mini. Na daure zuciyata sosai domin Ina so na cigaba da nuna masa Ina maraba da zuwan amaryarsa amma har cikin zuciyata na ji dad'in jin ya ce ba zai sake kwana ba, domin kuwa babu abinda ya zo mini a raina da ya gaya mini an dauran auran sai zai iya nemanta tunda ai ta zama mallakinsa.
Cikin 'yar dariya dana kalato na furta." Kai kuwa ranka ya dad'e ka kwana ma gobe da wuri sai ka taso."
Ya furta."A a zan dai dawo domin Ina da damuwa ke kanki kin sani hidimar nan ce ta d'auke mini hankali amma tunda an d'aura alhmdullhi itama gobe zasu kawota......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*25*
A shagwa'be na ce." Mutumin da yake da sabuwar amarya shine yake cikin damuwa, gaskiya ban yarda ba dadin baki ne."
Murmushi ya yi tare da cewa. Za ki gayawa 'yan garinku ai."
Na ce." Baba ina Hajja ne ka gaya mata na yi kewarta Yusi kuma bana nemansa tunda ya manta da ni."
Yana dariya yake ce wa." Hajja na can wurin 'yan uwanta Yusi kuwa yanzu ya tashi ya fita zuwa wurin abokansa kin san shi da saurin sabo ya samu abokai anan din ."

Sai na tsinci kaina da cewa. " Amma tare zaku dawo?" Gabad'aya hankalina ne bai kwanta ba nasan family dinsu babu mai kaunata sai shi sai mahaifiyarsa da 'yar uwarsa Hajiya Saratu mai sunan mamana. Dalilin da ya sanya ma kenan na'ki binsa a lokacin da zai tafi babu irin rarrashin da bai yi mini ba na ce a a bana zuwa.
Ya ce." Ai ba tare muka tafi ba kin ga da kunya na je na cewa Hajja ta ba ni shi mu tafi ko."
A sanyaye na ce." Hakane kuma."
Kamar ya fahimci abinda yake cikin raina sai ya ce." Ki yi hakuri babu abinda zai same shi in sha Allahu rabbi."
Da sauri na ce ." Ai ban ce dama wani abin zai same shi ba baba, yanzu me kake so ka ci?"
Duk abinda ki ka yi mini zan ci, ina da yin sallar la'asar zan taso in sha Allahu."
Na ce." To shikkenan Allah Ya tsare sai ka dawo."
Cike da karsashi da kwarin gwiwa na ajiye wayar ban tsaya jinkiri ba na fara had'a abinda zan sha domin rikita masa lissafi....08089965176 Muna da ingantattun magunguan mata masu masifar rikita maigida.
Na shirya masa towo miyar ku'bewa domin shi ma'abocin cin abincin gargajiya ne baya rabo da shan farau farau da dumame! shiyasa nake ajiye masa da safe na d'umama kafin ya fita ya ci.
Gidan ya yi mini girma sosai domin ni ka'dai na kwana da rana ne nake jin karakainar masu aiki magariba kuwa tana yi na shiga d'aki na rufe don ma gidan cike yake da masu tsaro shiyasa na dan samu sasaauci.

Na san dai tunda jirgi ya biyo ba zai wuce takwas na dare ba ya sauka, amma abin mamaki sai gashi har wajan goma da wani abu babu alamanunsa, na d'auki wayata domin kiransa na ji lafiya a kashe duka layukansa basa shiga. Ban kawo komai ba a raina ba, amma na fi tunanin ko bai samu tashi da wuri ba. Bashi da jirgi na kansa amma yana da alfarma dalilin matsayinsa da kowane lokaci zai iya tasowa.

Sha biyu na dare tana bugawa na fitar da raina da dawowarsa, raina a k'untacce na k'ara lalubar lambobin wayarsa har yanzu a kashe suke basa shiga. Lokaci guda zuciyata ta fara yi mini sa'ke-sake akan canza shawara ya yi kenan bayan ya sanya ni yi masa abinci har da shan maganin mata shine zai kashe wayarsa ba ma zai kira ni ya gaya mini dalilinsa ba.
Na kwanta ina ta juyi marata ta dame ni da ciwo sai had'e cinyata nake yi ina mi'ka tsabar bu'katuwa tabbas dana san ba zai dawo ba da ban sha komai ba.
Da 'kyar bacci ya d'auke ni mara dad'i da armashi don haka kiran sallar farko na tashi sai da nayi wanka tukkuna na d'aura alwala na fito.
Ina idar da salla na sake lalubar wayarsa is switchup, cike da tsantsar takaici da b'acin rai na ajiye wayar na koma gado na kwanta ina ha'de jikina domin har yanzu a dame nake dama idan nasha hadin yakan yi sati a ko kwana biyar bai daina aiki ba. Hawaye suka zubo mini nasa hannu na goge ina ayyanawa a raina wata'kila ita ta hana shi dawowa, ai dama an ce amarya ko ta buzuzuce sai an yi d'okinta, 'karin takaicina ma da ya kashe wayoyinsa tabbacin baya buk'atar a dame shi da bakinsa ya fad'a yana da damuwa kuma na san ko ta mecece babu yadda za a yi ya ga amarya a kusa dashi bai ta'ba ta ba.

Sai wuraran bakwai da wani abu ya kira ni. Da kamar kada na d'auki wayar saboda yadda nake jin haushin abinda ya yi mini.
Na daga a can kasan makoshi na ce." Ina kwana?"
Da sauri ya amsa yana cewa." Allah Ya taimake ki na yi lefi ko?"
Cikin dauriya na ce." Lefin me?"
"Jiya mun yi dake zan dawo ban samu tahowa ba saboda inna Uwani ta ce mini na tsaya kawai mu taho tare da amaryar tana sallama da 'yan uwa ne, shine dalilin da ya sanya ki ka ji shiru."

A nutse na ce." Shine dalilin kashe waya ko? Ai ka bugu ka gaya mini halin da ake ciki." Babu wata damuwa a tare dashi ya furta." Na yi lefi ki yi hakuri, na kashe wayar ne saboda ina buk'atar hutu don wallahi kin ji na rantse miki sallar Isha'i ma sai da tsakiyar dare dana farka na yi ta, domin bacci ne mai nauyi ya d'auke ni."
"Humm! kawai na ce domin har yanzu ban yarda da abinda ya fad'a ba.
Ya cigaba da cewa." Ni na kammala shiryawa tsaf ita nake jira kin san shirinku na mata, tare ma za mu taho gabad'aya harda Hajja wai ta fasa zama."
Na daure zuciyata na ce." To Allah Ya kawo ku lafiya, na d'umama maka towonka ko?"
"Ki d'umama mini idan mun sauka zan ci in sha Allahu."
"Shikkenan to sai kun dawo." Na kashe wayar ban jira ya sake cewa komai ba, domin duk bin k'wakwkwafina ya'ki ya nuna mini yana zumudin amaryarsa wanda ni Kuma zan kafa masa hujja da hakan. Kishi ma sai ya dinga sanya ni wasi wasi ina tunanin wata'kila ma tana zaune a kusa dashi ya kira ni yake tsarana ni da dadin baki.

Ina aiki abin yana cigaba da damuna a zuciya gabad'aya a rikice nake don tunda nasha maganin nan jiya nake cikin matsananciyar sha'awa, abin ya hadu ne da jin dadi da kuma adadin shekarun na da nake a yanzu ina kan gniyar buk'ata, bayan haka kuma ya yi mini mugun sabon da mutukar bai kasance ni ba a kullum zan iya shiga wani haliin. Falalu na kira domin ya cigaba da abinda na fara don yanayin jikina ba zai barni na ayi abu daidai ba.


Wannan littafin na kudi ne sister kada ki karanta mini shi ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Ina wanka ina tunanin halin da zan kasance tunda dole dai na ha'kura dashi tsayin sati tunda budurwa ce abinda musulunci ya bata kenan. Ban san yadda zan yi ba don gaskiya ba abinda nake buk'ata sai namiji a cikin yanayin da nake ci.
Sai wajan uku na rana suka sauka.
Ban yarda yanayin da nake ciki ya sanya mini nawa da kasala ba balle wani daga cikinsu ya ga kamar kishi ne.
Na tar'be su da fara'a har ita amaryar da samu kujera ta 'kame ta ci uban gayu kamar wadda zata je gasar sarauniyar kyau harda alkyabba. Shi bai tsaya ba kaitsaye samansa ya nufa domin kallo d'aya na yi masa na fahimci akwai gajiya a tare dashi.
a daidai lokacin dana fito daga kicin da tire a hannuna na ji tana ce mata "Ai ni ma tafiya zan yi, dama dalilin zamana goyon cikin Amina ne to ta haihu Allah ya tabbatar da aurenki da Tajo zaman me zan yi kuma, Ina dai kara gaya miki kada na ji kada na gani Hauwa nasan halin kowa daga cikinku don Allah ku zauna lafiya."

A nutse na ajiye Tiran abincin na ce." Haba Hajja ya na ji kina fad'in tafiya za ki yi, ki yi zamanki mana."
Ta girgiza kai tana ko'karin d'aukar gorar ruwa na d'auka na bude mata ta furta." Gwara na tafi Amina ai daka ke har ita Hauwan ba yara ba ne na san ba za ku ba ni kunya ba."
Cikin nutsuwa na ce." In sha Allahu rabbi Hajja."
Ta ajiye gorar ruwan bayan ta 'kurba a nutse ta ce." Dama ba ni da matsala dake Amina tunda zama ya had'a ni na ga halinki, itama Hauwa haihuwarta ne kawai ban yi ba kowa yana da dabi'a mai kyau a cikinku, don haka don Allah ku ri'ke amanar junanku, ku zauna lafiya kada ku yarda ma'kiya su ji halin da kuke ciki."
A daidai lokacin da take wannan maganar ya sauko daga saman yana waya ya yi wanka yana sanye cikin farar jallabiya idonsa da gilashinsa as'usul.
Ya zauna kusa da Hajja Yana cigaba da wayar da yake yi.
Duk muka yi shiru domin yanayin yadda yake fad'a a wayar shi zai tabbatar maka da cewa akwai matsala.
"Me yasa baka sanar da ni tuntuni ba sai yanzu da kake gudun kada asirinka ya tuno shine ka kira ni kake ko'karin kare kanka, ban yarda da kai ba Isiyaku bakinku daya da Sammani, kuma wallahi tallahi idan na yi bincike na tabbatar da gaskiyar abinda kuka aikata ran kowa sai ya baci a cikinku."
Ya kashe wayar bai saurari abinda yake cewa ba. Hajja ta ce." Wani abin ne ya faru kuma?"
Babu sukuni a tare dashi ya ce.'' Hajja ki dubi tsayin shekarun da nayi da Sammani amma yau an wayi gari yana daya daga cikin mutanan da suke kokarin kai ni kasa tare da janyo mini zagi a duniya."
Ya gyada kai cikin damuwa ta ce.'' Sammanin kuma me ya yi maka, ka yi bincike sosai kada ka yanke hukunci cikin rashin sani, Ina ganin Sammani ba zai cutar da kai ba.
Murmushi kawai ya yi ya ce." Hajja kenan, mutum fa ya kan iya canza hali a wasu lokotan saboda wasu dalilai amma yanzu ace kamar Sammani da na d'auki ragamar kula mini da harkokina na bashi shine zai dinga danne ha'kokin mutane ya gina kansa da gumin marayu. Kwanaki ya kira ni yake gaya mini rasuwar wani ma'aikacinmu, a ka'ida ne daman duk wanda yake aiki a 'karkashina namiji ko mace ya rasu na kan fitar da kudi masu kauri na bawa magana, ko kuma idan ina buk'atar sabbin ma'aikata zan sallami wad'anda karfinsu ya kare na kuma basu jari domin su juya dan cigaba da kula da iyalinsu. Lokacin da ya sanar da ni rasuwar 'Dayyabu Haruna jajirtacen ma'aikaci na ne wanda kwazonsa ma ya sanya muke shiri sosai na fitar da kud'i miliyar biyar na wakilita shi Sammanin kamar koyaushe ya je gidan marigayin ya yi ta'aziya a madadina ya kuma basu wannan kud'i dana bayar ashe sai ya sanya a lalitarsa, sai yanzu ake sanar da ni iyalan marigayin sun shiga gidan redio suna koke-koke tare da aibata, jarida har ta fita yanzu haka."
Sukairaju daya daga cikin escot d'insa ya shigo da jaridu biyu a hannunsa. Tun kafin ya k'araso wurin da muke yake fad'in." Kin gani ko, Hajja kin ga maganar da nake miki."
Sukairaju ya rusina tare da mika masa da sauri ya kama hanyar fita ba tare da ya ce komai.

Ni kam idona kansa a lokacin da yake duba jaridun ransa a tsananin b'ace don sai na ce ma wannan shine karo na biyu da naga tsananin fushinsa na farko lokacin da na kai k'ararsa wurin Hajja na biyu kuma wannan abin da ya faru.
Jiki a mace na yi kasa da kaina kwalla ta ciko idonsa ashe zargin mutumin nan kawai nake yi

Please Login or Register in order to submit comment