Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buk'ata daga wurina ni zan mallaka miki."
Hanci na ja tare da cewa ." Ni bana buk'atar dukiyarka kawai Ina tsoron yarana su zama marayu gaba da baya. Na yi bincike sosai a kanka an ce aljanna ce ta aureka, kuma ba zata bari ka zauna da mace ba, shiyasa duk macen daka aura sai ta mutu. Bayan haka kuma ni babu tsarin auran namiji d'an duniya a rayuwata."

Cikin b'acin rai ya ce." To ni kuma muddin mahaifiyata tana raye a duniyar nan ba zan yi jayayya da ita ba. Ni kaina ba sonki nake yi ba, saboda ni mutum ne mai tsantsami. Kin yi tarayya da maza biyu har kin haihu kafin ni. Mai zai sanya na takale ki kai tsaye na gaya miki babu wata mu'amular aure da zata ratsa tsakaninmu. Mutuwa kuma ko kin aure ni ko ba ki aure ni ba za ki mutu. Wannan itace maganata dake ta karshe. Zan kuma kira mahaifinki na sanar da shi, duk da shi d'in ma na lura kin fi 'karfinsa. Amma dai shine ya haifeku wata'kila zai iya gaya miki ki ji. Idan na zo ba na son bata lokaci ki zauna cikin shiri."
bai jira na ce wani abuba ya kashe wayarsa....
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram, normal gruop what'sapp kuma #700*
*Hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*7*
Kuka na ci na koshi domin shine kadai abinda zan yi na samu sau'ki a zuciyata. Tunda aka d'aura aurena da mutumin Alhaji Tajo nake ganin abubuwa iri-iri. A gidanmu da jama'ar gari. Matan babanmu wani irin girma suke ba ni sosai, magana cikin taushi balle Baba Sule kullum sai ya zo gidanmu ya rarrasheni da taushin murya, har yana fad'in na godewa Allah da baiwar da ya yi mini. Domin mata da yawa suna can suna ta neman damar dana samu ba su samu ba.
Can 'bangaran Mamanmu ma lamarin ya yi musu dad'i sosai domin da muka yi waya da anti Yagana a cikin maganganunta ban ji inda ta yi kushe da suka akan mutumin ba. Sai ya zama ni kadai ce nake 'kin auran a zuciyata ina kuma dannewa.
Ya Falmata kuwa magana take yi akan ya za a yi da harkokinmu. Na ce mata ta bari na samu nutsuwa tukkuna. yanzu ma shagunana yara ne suke kula mini dasu. Hamusu dai shine jagora.
Har gida na je na yi Gwaggwo bayanin yadda lamarin ya faru. Ta k'arfafa mini guiwa kan na ha'kura kawai domin daka ganin yadda lamarin ya faru shirin Allah ne saboda a mafarki babu wanda ya ta'ba tunanin babban mutum zai iya aurena, ta ce na yi hakuri na bar mata Yusi zata ri'ke itama ta dan samu me d'ebe mata kewa tunda nesa za mu yi wata'kila kafin a gan mu sai an yara. Ba kunya ba tsoron Allah na fashe mata da kuka tabbacin dai ban yi na'am ba.
Ganin haka ya sanya ta janye kudirinta. Ta ce mini zata fita amma ba zata dade ba. bayan fitarta na yi kwance a rumfarta hawaye na zullumi da tunanin abinda zan fuskanta a gaba yana ziraruwa daga idona. Na ji shigowar sa'ko wayata. Koda na duba sai naga shi ne. Yana fad'in wai duk wani posting dana san na yi a social media kama daga Instagram TikTok fece book na cire. Tsaki na ja na ajiye ba ni kuma da niyyar cirewa domin da za a daura auran ba a yi haka da ni ba. Ba zan daina harkokina ba .
Allah sarki Gwaggwo ashe bakin asibiti taje ta had'o kayan tsumi kawai naga ta dora katuwar tukunya akan wuta. Can ta fito da budurwar kaza da kayan dahuwarta har da ciccibi.
Ta yini tana aiki ta kammala tsaf ta dire mini kwanuka a gabana. tsumim kuma ta samu jarkoki uku ta zuba a ciki tana fad'in duk kwanakin da zai yi ba zai lalace ba.
Da wata ce kai tsaye zan ce mata ba zan ci ba wallahi, amma da yake Gwaggwo ta wuce komai a wurina ban musanta ba, hakan nan na ha'kura na zage na ci kazar data dahu da magani. 08089965176. Ciccibin ne na ce na tafi dashi gida da jarkokin tsumin sai nasha a hankali.

Ina kuka tana yi Yusi ma yana nasa haka muka yi sallama tana ta yi mini addu'oi da samun dawammamen zaman lafiya.

To kaf harkokina na damkasu amana a hannun Hamusu dalili shi na aminta dashi. Usaini ma na san yana da amana, amma dai hankalina yafi kwanciya da Hamusun. Ya yi mini alkawarin kula mini da dukiyata da kuma kawo mini cigaba sannan duk abinda yake tafiya zai dinga sanar da ni.
A daran na kira Sahura a waya mukayi sallama. Misalin tara da rabi sai ga maman Bokola matar data koya mini d'inki ashe ta shigo unguwar da yake ta tashi tsayin shekara uku kenan. kuma babu wanda ya san inda ta koma. Na yi cigiyar lambar wayarta har na gaji. Ta ce mini ta ji labarin wanda na aura ne shine da ta shigo garin ta ce bari ta zo ta yi mini murna.
Na yi godiya sosai mukayi musayar lamba sannan na d'auki kudi masu kauri na bata nace ta kara guziri tunda yanzu a can kudu take da zama wato Benin. Har sai da tayi kuka ganin alherin da nayi mata. Ni kuwa murmushi kawai nake yi ina mamakin kukanta itace silar zamana abinda ban yi tsammani ba. Dubu hamshin din dana bata ai ba zan ta'ba biyanta ba. Muka yi sallama.

Ina idar da sallar asubahi ya kira ni. Da kamar kada na daga wayar na danni zuciyata na dauka. Ba mu yi wata duguwar gaisuwa ba ya fara da ce wa." Kin shirya kayanki ko?"
"Eh." Na bashi amsa a takaice. Ya nisa kafin ya ce ba damuwa ni ma zan sauka misalin sha biyu sai mu bi jirgin yamma."
"To shikkenan." Bai sake wata maganar ba ya kashe wayar. Ni ma na kashe tawa na ajiye a gefe na sa hannu ba bubbugi fillon da Yusi yake a kwance . Ya tashi da sauri yana tambayata tafiya zamu yi. Na ce." Yusi babu salati da addu'ar tashi daga bacci ko."
Sai ya hau motsi da bakinsa. Bayan ya kammala ya dube ni, a raunane Ya furta." Mama mafarki na yi da Yayana yana biyo ni a bayana." Sai hawaye shaaaa! Suka fara gudana a kumatunsa. Ya cigaba da cewa." Kin ce zamu je makarantar mu duba shi ko Mama, gashi kuma yanzu kin yi aure za mu yi nesa da gari na ji ana cewa Legos da nisa. Ni dai ki barni a hannun Gwaggwo duk lokacin da baba Hamusu za shi duba shi sai ya tafi da ni."
Kuka yake sosai da sosai. Ni kaina daurewa nake yi, kuma a yadda na tsara shine daga na dawo daga umarar nan zan je na duba shi, sai dai kana taka Allah yana nasa.
Ban yadda hawayen da yake kwarmin idona ya zubo ba. Na janyo yaron jikina sosai na rungume cikin taushin murya da rarrashi na ce." Za mu je ne in sha Allahu, ni ma Yayanka yana raina Yusi na gaya maka fa yana can yana karatu yayi hankali zai zama malamin al'kur'ani, ko baka so ya zama abinda duniya za ta yi alfahari dashi."
Cak ya tsayar da kukan da yake yi, Ya dago kansa yana kallona ya ce." Mama da gaske ki ke ko?"
Na gyada kaina tare da gayyato murmushi a saman fuskata nace." I, mana ai ina yi masa addu'a sosai, kuma don na yi aure a nesa dashi zai hana ni na manta dashi ba. Don haka ka kwantar da hankalinka ka ji ko, kai ma ka dinga yi masa addu'a."

To maganganun da na yi sun dan sanyawa yaron nutsuwa. Da kuzari ya tashi ya fita domin dauro alwala. Ni kuma na fara had'a kayana da nasa cikin akwatu. Sai a lokacin hawayen da nake dannewa suka fara zuba. Kasa jurewa na yi kwata kwata domin kaina ya riga ya daukin zafi. Tunaninka iri iri sun dabaibaye ni. Na rasa da wane irin ma'auni zan auna wannan rikitattacen lamarin da ya ritsa da ni a sa'i daya ban shirya ba.
Babanmu ya shigo ya ritsa ni a d'akin. Fad'an da bai ta'ba yi mini ba a duk aure auren da na yi yau shi ya dinga yi mini. Kukana ya tsananta domin sai nake ganin kamar ba a yi mini adalci ba, har zuciyata tana zargin Baban namu akan rintse Ido saboda abin duniya. Shi fa mai kudi duk binciken da za a yi a kansa mai gaskiya ne. Dalilin kudinsa sun shafe masa wata mas'alar. Ba wanda zai fito ya ce yana da aibu saboda sutturar da Allah ya yi masa.
Ni na san yana da matsala tuna kafin aure ya ratsa tsakaninmu ya gwada mini na gani. Duk namijin da yake neman mata rayuwarsa ba zata ta'ba kyau ba. Idan na fito na fad'i haka babu wanda zai yarda da maganata.
Direba ya turo da mota ya d'auke ni. To ko a cikin motar ma kasa daurewa na yi na yane fuskata da mayafin jikina ina goge hawaye da hannuna.
Kwata-kwata babu ajandar aure a tsarina a halin yanzu. To amma kaddara ta gifta wanda ban isa na tsallake taba tunda da 'kafata na taka naje inda take. Wahidun k'har Allah kenan mai juya lamari.

A harabar gidan Hajja muka same shi da jama'a da yawa. Da saurin gaske na kawar da kaina, domin kallo d'aya na yi masa na ji gabana na bugawa. Na ri'ke hannun Yusi da yake ta yun'kurin bud'e motar ya fita. Direban da kansa ya zagayo ya bude mana muka fito. Ya d'auko madaidaiciyar akwatina yana kuma ko'karin kar'bar jakata na hana shi. Da sauri yayi gaba da akwatin. Ni kuma cikin nutsuwa na fara takawa ban yi mamakin yadda jama'ar dake wurin ke risina mini ba. Da yawa sun san ni a hoto da sauran kafafan sadarwa.
Koda na isa wurin da yake sai na dan risina a nutse na furta." Barka da yamma." Ya amsa da "Barka dai." A takaice hankalinsa yana kan wani mutum da yake ta yi masa bayani auran da zai yi wa yaransa kuma bai yi musu kayan gado ba.
Da hanzari na shige don yanayin da ya nuna a fuskarsa kamar bai so na tsaya a wurin ba har na gaishe shi. Jin tsoron abinda zai biyo baya ya sanya na bar wurin da saurin gaske.
Na same su su uku a zaune Hajja da Hajiya Saratu sai wata mai kama da hajjan sak da alama 'yar'uwarta ce.
Hajja ta dinga dariya ganin ni da Yusi fadi take." Amaryar Tajo ta iso fatan alheri a gare ki Amina. Allah Ya albarkaci auranku."
Sosai na yi kokarin sakin fuskata duk domin faranta zuciyar dattijuwar na zube a gabanta da fara'ata na ce." Hajja ina yini ya kufan jiki?"
Ta amsa tana me janyo Yusi cinyarta tana cewa." Kai anan za a bar mini kai ko?"
Yana dariya ya fara gaisheta.
Na juya a tsanake na fara gaishe dattijuwar da take kusa da ita. Babu yabo babu fallasa ta amsa mini Hajiya Saratu ita tun kafin ma na kai ga gaishatan ta gaishe ni duk kuwa da cewa itace gaba da ogan. Hakan ya kara sagar mini da guiwa domin duk inda ake neman karamci da kawaici mutanan sun kai, babu girman kai da d'agawa a cikin sha'aninsu.

"Ayyo! Wannan itace dama, ai ina hasashenta duk da cewa Hauwa ta nuna mini hotonta, na ce ai ba social media nake yi balle na ganeta sai yanzu kuma dana ganta a zahiri na ganeta ina yawan ganin hotonta akan titina ikon Allah."

Dattijuwar dake kusa da Hajja ce ke wannan maganar tana 'kebe baki.
Sunkuyar da kaina na yi sai na ji Hajjan tana fad'in." Ai 'yar kasuwa ce sosai kuma ta sanu akan harkokinta, ai ni irin wad'andan matan burgeni suke yi muddin zasu rike mutuncinsu."

Sai kawai ta ce." Hum Hajja kenan, fate fate ake tonawa kawai Allah ya rufa asiri."
Falon ya d'auki shiru lokacin zuciyata ta dinga tsalle kiris nake jira matar ta sake wata magana na kare kaina domin na fahimci wani irin kallo take yi mini na marasa tarbiya.

Ya shigo cikin hanzari Yana fad'in." Wanka kawai zan yi mu tafi na bar uzurirrikana da yawa a can." Sai kuma ya tsaya yana cewa." A a Inna Uwani yaushe ki ka zo?"
"Kwanana biyu a garin nan. Na ji labarin ka yi aure shine na zo yin Allah sanya alheri, ashe wannan itace amaryar?"
Yana 'yar dariya ya ce." Itace inna Uwa, ina Hauwa ba tare kuka zo ba."
Ta kawar da kanta tana cewa" To me Hawwa zata zo ta yi maka Tajo, humm Allah ya Kyauta."

Murmushi ya yi kawai a gaggauce ya shige yana cewa'' Bari na yi wanka na fito.

Ta kasa daurewa sai ta fara fad'in." Duk tsiya dai gwara ta gida, kuma budurwa nutsatsiyar bafulatana. Ai kowane maganarci yana so ya samarwa zuri'arsa uwa ta gari. Babu wayewa ga auran 'yan social media wad'anda suka kwashe kayansu daga gaban ma'aiki."

Hajiya Saratu ta ce." Inna Uwani wace irin magana ce wannan kuma? Babu dadi cin zarafi ga mutumin da bai yi maka komai ba. Wannan auran hukuncin Allah ne. Kuma tun farko mun so ki bashi Hauwa tun kafin ma ya yi aure na biyu ki ka ce ba zaki bashi ba, saboda Salima ta mutu itama kada ta mutu. Har dake fa masu fad'in yana da aljana to me zai sanya kuma bayan Allah ya aurar dashi ga za'binsa ki damu. Yau kusan sati daya da d'aurin auran nan alheri muke ta gani. Don Allah kada ki kawo mana rud'ani."
Sai ta rushe da kuka tana cewa." Saratu fitsara za ki yi mini akan na fad'i gaskiya har kina cewa har da ni a masu yi wa Tajo zagon kasa ko kin manta uwarsa ce ta saki nono taba ni."

Hajja tace "Saratu kyaleta kada na sake jin kin ce komai. Ke kuma Uwani ki tayar mini da ciwona kin ji ko?"
Shiru tayi tana sha'kar hanci tare da sanya gefan d'ankwalinta tana goge hawaye, tana girgiza kanta tana ta kallona. Ni kuma ta kasan idona nake hangenta.
Kusan daskarewa na yi a wurin ganin yadda muraran matar ta nuna zazzafar kiyayyarta a kaina.

Ya fito tsaf cikin manyan kaya. Wurin ya cika da kamshinsa. Ganin inna Uwani na share fuska sai ya ce." Me ya faru ne na ga fuskokinku duk a b'ace.
Hajiya Saratu ta furta." Maganar Hauwa ta taso da ita. Inna Uwani ta so dama ranta ya baci ne kawai."
Ya zuba mata Ido a tsanake ya furta." To idan wannan ce matsalar ki share hawayenki. Bari mu ga abinda Allah zai hukunta anan gaba idan da rabo sai ayi yadda ki ke so."

"To ai haka ya kama a gaya mini. Ni ban k'yamaci matarka ba Tajo, amma dai ka dawo gida ka yi auran alkunya da fita kunyar jama'a." Ba tare da ya ce mata komai ba ya kalle ni." To zamu tafi yanzu." Ya dubi Hajja da gabad'aya ranta yake a b'ace kan abinda 'yar uwarta ta yi. Ya ce." Za mu tafi Hajja a yi mana addu'a."
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE [6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram akwai normal What'sapp group #700 ga wad'anda karatu a talgrm yake yi musu wahala hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*6*
Lamarin da ya janyo hayaniya da kace-na-ce, mussaman a social media kowa na fad'in albarkacin bakinsa. Wasu na ganin Alhaji Tajo alfarma ya yi mini ya aure ni. Wad'anda kuma suka san tarihinsa na baya suna ganin kawai kwanana ne ya k'are tunda har kud'insa suka rude ni na aure shi bayan nasan matsalarsa.
Ni dai tunda aka d'aura auran nake ta zubar da hawaye gabad'aya na rasa a da wane ma'auni zan auna lamarin. Wace irin k'addara ce wannan mai sammatsi. Ina zaune a wani d'aki da yake cikin gidansa domin tun jiya da muka zo ni da Baba Hajjan tace mu zauna kawai kayanmu ma dake can masaukinmu sai turawa akayi aka d'aukosu. Ina jin messages (sakkoni) na ta shigowa wayata ban duba ba dalili na riga na san ba ni da nutsuwar da zan bada amsa abinda dai na yanke a zuciyata shine duk wanda ya tambayi ya akayi hakan ta faru zan ce masa ban sani ba. Shigowar Hajiya Saratu d'akin da kaya a hannunta ya sanya da sauri na goge hawayen kumatuna.
Sai ta girgiza kanta ta karaso wurin da nake tana fad'in." Ki yi hakuri don Allah ki daina wannan kukan Amina. Wallahi tallahi kin ji rantsuwar Muslimi ba zamu cutar dake ba. Duk abinda hajiyarmu ta kaunace shi ya zame mana dole mu 'kaunace shi. Kuma albishirin da zan yi miki shine kin yi miji, ba don Tajo d'an'uwana ne ba nake gaya miki haka, mutum ne da rabin mutum. Zai baki kulawa sosai, kuma zaki samu jin dadin rayuwa dake da yaranki. Ki kwantar da hankalinki, kuma jita-jita na mutane ya daina damunki ki barwa Allah lamarinsa tunda ke kanki idan ki ka yi wa lamarin nan duba na tsanaki za ki san shirin Allah ne."

Murmushi kawai na iya bakina ya yi nauyin da ba zan iya ce mata ba na son d'an'uwanta ba. Gashi kuma ina jin nauyinta domin tana da irin sunan Mamana. Kawai sai na sunkuyar da kaina kasa. Ta ajiye mini kayan da ta shigo dashi tana fad'in." Ki shirya yanzu nan ya kira ni a waya na gaya miki za su shigo tare da abokanansa za a yi hoton tarihi."
Tana gama maganarta ta juya ta fita daga d'akin a gaggauce.
Ledojin na bude dogayen riguna ne manya irin na larabawa da hijabai masu kyawun gaske. Da band'aki a cikin d'akin na shiga na yi wanka na fito na zura d'aya daga cikin dogayen rigunan a jikina. Na d'auki karamin hijabi iya kafad'a nasa. Turare na d'auka akan madubi na fesa a jikina na nemi wuri na zauna zuciya gabad'aya a cunkushe.

Sa'kkonin da aka turo mini ta inbox na fara dubawa. Wanda na yi wa duban tsanaki na Anti Yagana da Sahura. Tambayata suke yi shin labarin da suka ji yana yawo a gari da gaske ne. Kuma ya akayi hakan ta faru.
Na basu amsa da gaske ne. Amma ni ma ban san yadda aka yi ba, kawai su taya ni da addu'a. Idan kuma kwanana ya kare suka kula mini da yarana."
Nasa hannu na goge hawayen da ya shiga zarya a kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da aka turo kofar d'akin a bazata na daga kaina muka yi Ido hudu. Ya mayar da kofar ya rufe ruf. Ya nufo wurin da nake cikin shigar larabawa harda alkyabba irin tasu.
Gabana ya dinga bugawa da k'arfi da k'arfi. Zuciyata tana harbawa kamar zata faso kirjina ta fito.
Daf da ni ya tsaya masifaffen kamshin turaransa ya fara surnanowa hancina.
"Amaryar Tajo." Maganar ta daki kunnena. Hanci na ja ban dago kaina ba balle na kalle shi.

Wannan littafin dai na kudi ne Hajiya

Please Login or Register in order to submit comment