Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali na saman ina tunanin ko ya sauko ko wane hali yake ciki.
Yusura ta kawo mini abinda suka yi na karin kummalo na kasa cin komai saboda bakina har yanzu babu d'aki. Baba Tabawa ta d'umama mini ragowar towon jiya bashi dai da yawa tunda Hajja ta tafi da wani amma ya isheni kuma ni kaina na yi mamakin yadda na ci sosai a lokacin na ji karfin jikina ya k'aru... Cikin wani yanayi na tambayi anti Yagana maigidan ya sauko tunda tun safe suna falon ta ce mini ya sauko har sun gaisa ya fita amma bai jima ba ya sake hawa saman bai kara saukowa ba kuma.
A gogon da yake falon na duba sha daya da rabi domin kada ta fahimci akwai 'baraka ya sanya na tashi ina fad'in bari na hau mu gaisa. Kai tsaye na nufi benen da zullumi mai yawa a kirjina.
Kofar d'akin kawai na tura ta bude bai murza mukkuli ba, Yana zaune a gefan gado ya shirya sosai cikin milk din shadda tazarce da aiki mai kyau a gaban rigar hularsa tana ajiye a gefe amma as'usul gilashinsa na ka'ida yana idonsa. Magana yake yi a waya a lokacin da na shiga d'akin na samu wuri gefansa na zauna amma gabad'aya na gagara kallonsa saboda tsananin yadda nake cikin damuwa.
Jin yana ambaton sunan Maryam ya sanya ni shiga tunani daga bisani Kuma na gane da Hajiya Maryam suke yin magana matar abokinsa da ya rasu kwanaki. Sun jima suna tattauna abinda ya danganci mamacin yanayin maganganunsu ya tabbatar mini da cewa suna tattauna yadda za a raba abinda ya bari tunda mahaifiyarsa ta na raye kuma yana da 'yan uwa. Dole Mamansa ta gaje shi koda kuwa 'yan uwansa ba su gaje shi ba dalili akwai maza biyu a cikin yaranshi.
Bayan sun yi sallama ya dube ni babu yabo babu fallasa amma bai ce komai ba sai ya cigaba da latsa wayarsa yasa a kunnansa ina dai zaune Ina jin shi Hauwa ya kira a wayar cikin kulawa na ji suna magana don ba na jin abinda take cewa tunda kamar ya yi kasa da murya ne don shi ma idan ta fad'i magana sai ya sake tambayarta abinda ta ce saboda maganarta can kasa take fita. Sai na juyar da kaina gefe ganin kamar ba ya so na ji maganar da suke yi na ji yana gaya mata daga nan din kai tsaye bauchin zai taho zuwa yamma ta tsammaci zuwansa tunda tafiyar mota zai yi.
Jikina ya d'an yi sanyi Jin yadda yake lalla'bata da rarrashi har da kalamai irin na tausayawa da sadaukarwa. Sai na tsargu da jin abinda yake yi wanda na tabbatar da cewa wanzuwata a wurin ya kawo hakan. Na ji haushi sosai amma sai na danne domin kuwa a yanzu fushi ba nawa ba ne dalilin abinda na tabbatar da cewa ni ce mafi rinyen lefi dole a wannan ga'bar ko ban fito na gaya masa na aikata ba na nemi hanyar shiri da kuma ko'karin kwantar da matsalar don gudun fasuwar maganar.
Ya ajiye wayar a kusa dashi bayan sun kammala ya d'auki agogonshi dake saman drowar yana daurawa bai ce mini komai ba. Na daure na ce." Ina kwana Baba?"
Hankalinsa na kan abinda yake yi ya amsa da "lafiya ya gajiya." Sai na yi shiru ina dan satar kallonshi a fakaice. Sukairaju ya dan buga kofar kafin ya bashi umarnin shigowa ya turo a hankali cikin ladabi ya tsaya daga can nesa yana fad'in." Sir ka kammala ne?"
Ya mike tsaye da hularsa a hannunsa yana gyarawa ya ce." E, na kammala zo ka d'auki wad'annan." Ya fad'a yana nuna masa Loptop dinsa dake ajiye da 'yar jakarshi."
Da sauri ya yi abinda aka sanya shi ya bude kofar ya fita daga d'akin. Yana ko'karin sanya hular a saman kan sa ya ce." Ni zan tafi Amina, Amma kafin nan zan je Bauchi wurin Hauwa domin dubata ina fatan ba ki da matsala ko?''
Na mike tsaye da rashin karsashi na ce." Ba ni da matsala Baba amma ina so mu yi magana dangane da abin nan da ya furu na ga kamar ba ka yarda da kaddara ba don Allah kada ka tafi da 'kullacina a cikin ranka."
Ya dube ni sosai wanda tun shigowata d'akin bai yi mini irinsa ba.
"Kin aikata hasashen Dr Iliyasu ko ba ki aikata ba, wannan amsar kawai nake so na ji daga gare ki."
Shiru na yi ina kallonsa shi ma yana kallona ido cikin ido. Mun d'an jima a haka kafin daga bisani na janye nawa idon daga cikin nasa zuciyata na dan harbawa ko alama ban hangi sasaauci a cikin idanuwansa ba.
"Shirunki da yanayin yadda alamun rashin gaskiya suka bayyana a tattare dake ya bayyana mini ce wa." Dr Iliyas ba karya ya yi miki ba saboda haka ni kawai sai dai na ce na barki da Allah."
Daga haka sai ya kama hanyar fita daga d'akin. Da saurin gaske na cimmasa idona cike da hawaye masu radad'i na furta." Maganar bari da Allah ba adalci ba ne, ka yi duk hukuncin da kake ganin za ka yi mini tunda ka'ki kar'bar kaddara, amma kwata kwata ka daina had'ani da Allah

"Shi kadai ne zai yi mini maganinki tunda ai kin gagara Amina kin nunawa duniya cewa baki da na gaba dake kin fi 'karfin kowa ciki har da mahaifinki ni dai muddin ina da hakki akanki to fa ba zan daina cewa Allah Ya saka mini ba."
Ya sanya hannu zai bude kofar domin fita na sake tare hanyar a karo na biyu cikin jarumta na ce." Ubangiji ba mutum ba ne kamar kowa kuma akan yi masa lefi a tuba ya yafe duk sharri da bala'in da kake nema dashi da izinin Allah ba zai same ni ba domin kuwa wanda ya hallice ni ya fi ni sanin menene a zuciyata Ina ce dai idan na gaya maka gaskiya shikkenan ai ikon hukunci ko azabtarwa ko d'aukar rai duka ba a hannunka suke ba. Na yi kuskure tabbas a lokacin da na tabbatar da cikin a jikina na yi kokarin fitar dashi kamar yadda Dr Iliyas din ya gaya maka. Dana fahimci bai zube ba sai na ha'kura kawai na barwa Allah kuma na ro'ke shi gafara a sa'in da na kuskure masa kuma ina da tabbacin ya gafarta mini, abinda zan iya gaya maka kenan domin a duniyar nan babu wanda baya kuskure Ina me baka ha'kuri hakan ba zata sake faruwa ba."
Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da al'ajabi ni kuwa ban ji komai ba domin kuwa na lura rufe maganar da nake yi bashi da wani amfani gwara kawai na sanar da shi gaskiyar lamari tunda ya fi ni sanin hujjata ta yin hakan.
"Hakan ba zata sake faruwa ba." Wannan maganar ya fad'a kafin a gaggauce ya bud'e kofar d'akin ya fice da saurin gaske.
Na jima ina nazarin maganar da ya furta sai na shiga zullumi da tunanin domin ya yi ta ne a d'ukunkune karshen dai hukunci shine saki a shirye nake da kar'bar gakan daga wajensa.

Da yamma muna zaune a falo anti Yagana suka yi waya da Babanmu nan take sanar dashi kwana biyu ni ce ban ji dadi ba shine dalilin da ya sanya ba mu sake zuwa ba tun ranar da aka sallameshi daga asibiti. Na ce mata ta gaya masa na ji sau'ki don zai iya tashin hankalinsa jin ba ni da lafiya
Duk da ta gaya masa haka kuwa washe garin ranar sai da suka zo duba ni tare da Baba Sule sun jima a gidan muna tattauna sha'anin Hadiza domin kuwa kowa ya riga ya mik'a wuya don a zaman kutu na farko da aka yi ba a hangi sasaauci a tare da alkalin ba. Yanzu tana can gidan kaso kafin shari'ar ta kammalu a yanke mata hukunci. Bayan sun tafi da kad'an sai ga Gwaggo Hamusu ya kawota to ita tare muka yini har dare sai bayan Isha'i, tukkuna ya taso daga shago ya zo ya d'auketa a babur ya kai ta gida.
Sai da na warware sosai sannan na gayawa Sahura abinda ya faru da ni amma ban gaya mata cewa ni ce sila ba. Ta jajanta mini sosai tana fad'in Allah bai yi rayayyu ba ne itama haka tasha wannan wahalar lokacin da nata tagwayen suka zube ta ce mini za ta zo ta duba ni ranar da babu aiki.

****
To tafiya ta mik'a sosai don yau sati uku kenan da abinda ya faru amma tsakanina da maigidan muguwar gaba ce ta 'kullu. A zahiri shi ya d'auki lamarin da zafi na sani kowaye aka yi wa haka ba zai ji dad'i ba amma ya kamata ace ya yi hakuri ya kar'bi tubana tunda na gane abinda na yi ba daidai ba ne. Na kira shi ya kai sau bakwai tun bayan tafiyarsa na tura text amma daga karshe ma sai ya sanya ni a black list idan na kira duka layinkansa busy. Ban damu ba da farko saboda a ganina duk fushin da zai yi na dan wani lokaci ne zai ha'kura ya sauko ya kar'bi tubana ni kuma na kiyaye a gabana. Na dai ji dad'i sosai da ya rufe maganar bai gayawa kowa ba dama kuma kusan haka halinshi yake yana da zurfin ciki mussaman akan mas'ala irin wannan.


Littafin nan na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Duk da damuwar da ta fara yi mini 'kawanya ban yarda anti Yagana ta fahimci wani abu ba har dai ta tattara ta tafi bayan an yi zaman kotu daya da ita inda ake tsammanin zama na gaba za a yanke hukunci na karshe.
Bayan tafiyar anti Yagana Ummansu Hadiza ta zo mini a ki'dime tana kuka sosai duk ta figale ta lalace wai na taimaka na daukarwa Hadiza lauya domin kuwa a cikin lauyoyin gwamnati an rasa wanda zai kar'bi case din ganin haka ya sanya kowa yake tunanin zama na gaba Hadiza za ta san matsayinta.
Na rasa yadda zan yi da ita domin dai Ina ji Ina gani ba zan daurewa karya gindi ba. Hadiza ta fad'a da bakinta tana da hannu dumu-dumu shedu sun shaida to me zai sanya haka kawai na d'aukar mata lauya saboda son zuciya. Kuka take yi sosai tana gaya mini halin da Alhajiji yake ciki shi ma yana can hannun 'yansanda a jos suna azabtar dashi mahafinsa da 'yan uwansa da suka uba daya sun ce babu ruwansu ga Hadiza ma za a yanke mata d'aurin rai da rai."
Na rasa kalmar da zan yi amfani da ita wurin rarrashinta domin kuwa Allah ne kadai ya san irin rad'adin da take ji a cikin zuciyarta.
Ban yaudareta da zumar zan yi mata abinda take buk'ata ba. Na dai rarrasheta da tausasan kalamai na kuma jadadda mata ce wa ta mikawa Allah lamarin sannan kuma ta tsananta da addu'a Ubangiji zai kawo mata d'auki.
Da zata tafi na bata dubu talatin na ce kuma Ayuba ya kaita har gida don abincin ma dana sanya a kawo mata bata ci ba sai juye mata na yi a leda ta tafi dashi.

***
Yau wata biyu kenan da tafiyarsa wanda ya yi daidai da abinda ya faru da farko da na ce ba zan kara kiran shi ba amma yau tunda garin Allah ya waye na tashi da wata irin kewa da sha'awa. Na zauna ina tunanin abinda ya janyo mini shiga yanayin tunda na farko ni ina gujewa sha da cin duk abinda zai daga mini hankalina babu namiji a kusa da ni. Amma yau din nan na wayi gari da tsananin kewa kuma tasa da son jin wani abu daga gare shi.
Duka na bi layinkansa ina busy har yanzu bai cire ni ba, na duba shi a ta whasap na ga ya sauka tun kwanaki uku da suka wuce.
Sallama na yi masa cikakkiya da addu'ar Allah Ya sa ya amsa mini a duk lokacin da ya bud'e ya ga sa'kona.
Na kasance koyaushe cikin duba shi ta whasap din tsayin kwanaki tara da tura sa'kona bai hau ba sai yau. Na ga alamun ya duba sallamata amma kuma bai ce komai býÿÿÿ































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~


a ya ma sauka.
Sai na sake tura masa wata sallamar again ina ta addu'a Allah Ya sa ya magantu.
Bai duba ba sai da gari ya waye tukkuna nan ma dai bai amsa mini ba.
A takaice dai sai da na yi masa sallama sama da biyar ya bud'e ya ga ni amma ko d'aya bai amsa ba.
Raina ya 'baci ainun. wannan mummunan dabi'arsa tasa ta gaba tana mugun b'ata mini rai. Kuma na fahimci yana da rike abu a zuciyarsa ba kasafai ake bashi ha'kuri ya ha'kura a lokaci daya ba.
Sai kawai na share shi gabad'aya ni ma na fita daga sabgarsa duk kuwa da cewa tunani da kewarsa na d'an damuna amma dai Ina yun'kurin dannewa domin tsira da sauran mutuncin da ya rage mini......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*64*
Wannan kukan da nake yi ya zama me mini dole ne na yi shi domin yinsa kad'ai zai sanya mini jin sasaauci a zuciyata. Amma kuma tilas ne fa na yi wani abu akan wannan lamarin namu domin sanin matsayin da nake a zamantakewarmu.
Haka dai na yi hakuri na danni zuciyata da 'karfin addu'ar da na dimanta na d'an ji sa'ida a cikin raina, amma dai duk da haka idan lamarin ya fado mini a raina na kan shiga wani yanayi mara dad'i.
Na cigaba da kasancewa cikin tunani da nazarin yadda zan b'ullowa alm'arin. Kai tsaye shawarar da na yanke a raina itace zan nufi maiduguri gidan Baban Saude na san shi kad'ai ne zai dube ni ya kuma fahimci halin da nake ciki. Nasan kuma zai ri'ke ni kamar 'yar cikinsa a wannan karon ba zan ce zan yi zaman kaina ba balle a canza mini manufa a iya tunanin da na yi shine gidan Baban Sauden dai shine marufar asirina babu wanda zai zarge ni da wata niyya na ke ko'karin kashe auran. Ba zan gayawa anti Yagana komai ba itama sai dai kawai ta ji labarin ina garin. Kuma na tabbatar da cewa babu wanda zai zo ya ce zai tursasa ni akan abinda ba na so muddin na ci sa'a Baban Saude ya kar'bi kukana ina da ya'kinin zai iya yin gaba da gaba da Alhaji Tajon sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Ina ta shirye-shiryen tafiya ban gayawa kowa ba shawarar da na yanke shine Yusura za ta koma hannun mamanta itama baba Tabawa zan sallameta da alheri mai yawa, masu gadin gidan da Ayuba dama ba ni na ajiyesu ba. Ina shakkar Babanmu ya samu labari abinda na tabbatar da cewa ranshi zai b'aci matu'ka da gaske. Hakan ba zai sanya ni na janye ba domin kuwa Babanmu zuciyarsa ba irin ta kowa ba ce ba zai iya ta'buka komai ba ko da kuwa an zube magana an tabbatar da cewa ni ma ina da gaskiya ta wani gefan ana cutar da ni.
Sati uku da d'aurin auransa inda wa'adin rantsuwar da na yi akan rashin zuwansa ya kusa cika saura sati daya kenan wattanin bakwai da barinsa garin.
Hajiya Saratu ta kira ni a waya tana gaya mini Hajja babu lafiya har sun je da ita Egypt sun yi sati daya sun dawo gida amma jikin da sau'ki yanzu. Na ce mata wallahi ban sani ba da tun wuri na zo na dubata. Mamaki ta dinga yi wai saboda na ce mata ban sani ba, ganin kamar tana so ta fahimci wani abu ya sanya na yi mata sallama tare da bata tabbacin in sha Allahu Ayuba zai kawo ni gobe na dubata.
Kwana biyu a tsakani Ayuba ya kai ni gidan Hajja na dubata jiki da sauki alhamdulillahi ta warware don tana zaune ma ana ta hira, ni ma na saki jikina sosai domin ko da wasa ban nuna akwai wata matsala ba. Cikin hirar da muke yi ne na d'an fahimci wani abu ashe maigidan ya zo garin har ya yi kwanaki ya koma a cikin tsakankanin wannan lokacin bayan sun dawo daga Egypt .
Shiru na yi da suna maganarsa ban iya cewa komai ba domin kuwa ni ban san ma ya zo har ya tafi ba, amma can 'kasan zuciyata abin ya tsorata ni sosai ya kuma sanya mini shakku anya maganar Sahura bata tabbata ba kuwa ko dai da gaske ne matar nan Maryam da ya aura tana asiri tunda mijinta har ya mutu da ita kadai ya rayu.

Wannan littafin na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba

Tunanina ne ya katse a lokacin da na ji Hajja tana maganar ai ya je can bauchi wurin Hauwa wadda take daf da haihuwa ko yau ko gobe domin kuwa sun yi waya da inna Uwani ta ce mata kwanansa biyu a can kafin ya tafi.
Jikina ya 'kara yin sanyi kwarai da aniya tabbas mutumin nan ya sake ni furta mini ne kawai bai yi ba saboda mugunta ya jingine ni a gefe d'aya.
Ina jin su suna ta hirar abinda ya shafe su, idan ta had'o da ni na sanya musu baki amma kuma zuciyata cike take da mamaki lamarin to sunce ya zo ya kwana amma me yasa basu fahimci cewar ba ma tare ba. Idan har ya zo din ai a gidana ya kamata ya sauka bayan ya duba mahaifiyartasa. Wani sashe na zuciyata ya ce mini tunda ki ka ga basu fahimci komai ba to wata'kila bai gaya musu wata matsala ba kuma ai yana da gidajen a garin da guesthouse bai zama lallai ya kwana a gidanki ba, idan ya yi musu sallama da zummar tafiya wurinki ai ba zasu fahimci komai ba."
Wannan hasashen na zuciyata shi ya zauna daram a k'wa'kwalwata. Wato abinda ya yi kenan har ya yi kwanakinsa anan din ya tafi bauci wurin matarsa ba su gane komai ba. Ganin haka ya sanya ni ma na cigaba da nuna fara'a da annashuwata ban yarda yanayina yayi sauyarwar da za su gane akwai matsala ba. Da suna hirar Hajiya Maryam amaryarsa ni ma na sanya bakina Ina biye musu domin kuwa ga dukkanin alamu ta samu karbuwa a wurin Hajja tana sonta don sai fad'in alherinta take yi. Tabbas matar ta san takan zama tare da duniyanci domin kuwa koda bata asiri zai wahala duk wanda ya kusanceta ya ga laifinta domin ta iya mu'amula da kyautatawa. Gashi dai 'kiri-'kiri sun mayar da ni sauna ita da shi sun kar'be mini yarona duk tsananin sha'kuwar da take tsakanina da Yusi idan mun had'u sai na zama bak'uwa a wurinsa. Yadda ma za a yi ya dawo hannuna a yanzu shine abinda ya fi daga mini hankali da sanya mini fargaba domin kuwa yadda ya d'aukaki mutumin nan kamar shine wanda ya haife shi. Haka zalika ma ta b'angaransa shi Yallabai din ya sanya yaron a cikin ransa wanda yake nuna kamar ya ma fi ni iko da shi.

Yini na yi sai yamma na yi shirin tafiya Allah sarki Hajja ta had'a mini Turaruka masu tsada da k'amshi na jiki da kuma na wuta dana tsinke.
Zuciyata ta tsinke k'warai da gaske domin kuwa na tabbatar da cewa ta ji labarin bada'kalar da take faruwa hankalinta zai tashi wanda hakan ka iya yin barazana da lafiyarta. Na kuma gane dalilin da ya sanya shi kansa yake 'boyewa saboda tabbatuwar kwanciyar hankalinta tunda ni din ta gaban goshinta ce in banda yanzu da magauta suka yi yawa amma zahiri Hajja tana sona k'warai, kuma tana son zamana da d'anta.

(Ga masu buk'atar a tallata musu hajarsu ina yi cikin farashi mai sau'ki a yi mini mgn 08089965176)

Ranar da na shirya tafiyar laraba ce wadda na tabbatar da cewa Sahura tana wajan aiki ba za ta yi yun'kurin zuwa ta dakusar da ni ba sai dai ta dawo gida ta samu Yusura da Baba Tabawa. Akwati biyu na yi ta kayana na hada komai dana tabbatar da cewa zan buk'ata. Muka yi waya da Hamusu na gaya masa zan je maiduguri ya cigaba da kula da komai wanda dama hakan aikinsa ne. Bai kawo komai a cikin ransa ba muka yi sallama. Na umarci Ayuba ya fito da mota kai tsaye gidan Sahura muka nufa aka yi sa'a Idiris yana gidan bai fita kasuwa ba tukkuna tunda lokacin da muka fito daga gida tara da rabi na safe. Tun a mota muka yi sallama da Baba Tabawa na bata dubu hamsin na ce ta ri'ke a hannunta amma tunda na sanya mata lambata a sabuwar wayar dana saya mata duk lokacin da take da wata matsala ta kira ni ta gaya mini zan tura mata da kudi. Ta kama hanya ta tafi gidanta kad'an da gidan Sahura. Ita Yusra sai da muka shiga gidan tare sauran yaran duk suna makaranta a gurguje na tsaya muka gaisa da maigidan yana tambayata lafiya dai na ce masa kalau zan je maiduguri shine dalili. Na mik'awa Yusra dubu biyar ta kar'ba jikinta duk a sa'bule na kama hanyar fita a gurguje ina cewa dashi ya gayawa Sahura zan kira ta a waya idan na isa.
Tashar kasuwar kwari na ce da Ayuba ya kaini. Ya tsaya yana jayayya wai na fadi inda nake so na je zai kaini tunda akwai wadataccen mai a motar kuma aikinsa ne hakan idan oga ya ji labarin hakan zai yi sanadin rushewar hanyar abincinsa.
ganin yana yi mini taurin kai ya sanya na rufe shi da fad'a sosai na ce ya sauke ni muddin ba zai yi abinda na ce dashi ba. Ganin yadda raina ya b'aci ya sanya shi jan motar bai sake magana ba kuma kai tsaye inda na umarceshi ya nufa da ni.
Muna isa na bude motar na fito. Shi ma ya fito da sauri ya d'auko mini akwatinana. Mota guda na d'auka domin ba zan iya jira ba. Ban ma tsaya yin sallama da Ayuban ba na ce da direban ya shigo mu tafi. Ina kallonsa ya koma motar jikinsa a sanyaye kuma har direba da nake cikin motarsa ya ja muka tafi shi bai bar tashar ba.
Tun a mota na kira Baban Saude dama kwanaki uku da suka wuce mun yi waya dashi na fara gaya masa halin da ake ciki ya ce mini maganar ba ta waya ba ce sai na zo tukkuna sai mu tattauna. Na sanar dashi cewa gani nan akan hanya ya yi mini fatan alheri da sauka lafiya.
Sai daf da magriba muka isa maiduguri na sake d'aukar mota har kofar gidan Baban Saude yana tsaye a kofar gida fuskarsa kadaran kadahan har na fito daga motar direban yana sauke akwatinana. Ya k'araso wajen da muke tare da kiran yaronshi dake wasa a can tsallake ya rugo da gudu wajan ya umarce shi ya d'auki akwatin kayana ya shiga dashi gida.
Yaron ya d'auki babbar akwatin da sauri ya nufi gida da ita. Shi kuma ya sunkuya zai d'auki k'aramar. Da sauri na ri'ke tare da cewa." Haba Baba bari zan shiga da ita."
Ba tare da ya ce mini komai ya saki akwatin na d'auka muka jera muna tafiya yana fad'in. " Kin ci sa'a yau kwanana uku da dawowa kuma na kan d'auki sati ko kwana goma ban koma ba, Amina wannan lamarin naki ai abun a zauna ne domin kuwa ba karamin abu ba ne. Ni namiji ne amma ba na goyon bayan azzaluman maza."
Murmushi na yi tare da furta." Wallahi Baban Saude tura ce ta kai bango ha'kurina ya kare akan lamarin nan, domin kuwa duk yadda na so ganin na zauna abin ya ci tura kamar yadda na gaya maka yau wata bakwai kenan rabona dashi kuma

Please Login or Register in order to submit comment