Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sadada har ta samu damar yi mini text kuma cikin nutsuwa bata kalubance ni akan had'a baki muka yi da mijinta ba.
Na kwana da tunanin hakan a raina sai da gari ya waye tukkuna na kira ta a waya ta daga babu jinkiri muka gaisa sosai cikin ko'karin kare kaina na fara yi mata bayanin abubuwan da suka faru tun farkon neman auran har zuwa yanzu. Ta dinga fad'in ai na d'auka ni dake babu rufi Aziza babban abinda ya ba ni haushi kenan yadda kike biye masa kema ki ka yi mini shiru wato sai dai kawai na ji an d'aura auran kenan kun yi mini adalci.
Na shiga bata ha'kuri da tausarta Ina nuna mata cewar ban san ta yadda za a yi na iya tunkararta da maganar ba domin ni duk a tunani na mijinta ya gaya mata.
Ta ce mini bai gaya mata ba ita ta fahimta da kanta yana neman aure da kuma ta yi bincike ta gane Halisa ce k'anwata.
Yadda muka fahimci juna sosai a wayar ya sanya mini kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyata na amince da cewa Maryam ta sakko ta kuma yi na'am da cewa kishiya abokiyar zama ce kuma hukuncin ne na Allah....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*

[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *07084653262*
Wallahi Amina duk yadda na so da ganin na sakar mata jiki kasawa na yi duk tsananin sabon kuwa da yake tsakaninmu sai ta dinga ba ni tsoro daga zarar na kalleta sai na tuna irin mawuyacin halin da Halisa ta shiga. Duk da zato zunubi ne amma tsakani da Allah kenan na fi gazgata cewa itace ta jefi Halisa ta kuma juyar da hankalin mijinta akan lamarin gabad'aya. Haka nan muka yini da ita kadaran kadahan domin hausawa suna cewa idan ba ka iya kama b'arawo ba shi sai ya kama ka shiyasa kawai na kyaleta ban iya ce mata komai akan lamarin ba tunda ai a duniya muke akwai kuma ranar tsayuwa idan har ita ta cutar da Halisa ta d'ora mata muguwar jinyya mai wahala ubangiji zai fitar da hakki.
Muka rabu kowa zuciyarsa cike da tunani domin kuwa ko bata fito ta fad'a tabbas ta fahimci na canza mata ba kamar yadda muke a da can baya.
Lokacin da na gayawa Babansu Madina zuwanta da kayan da ta kawowa Halisa da yara ya yi godiya kawai daga haka bai sake cewa komai ba Amina kin san su maza ba su yarda da irin wannan muddin ba gani suke yi a zahiri ba domin da farko da na gaya masa nuna zargin Maryam akan ciwon dake damun Halisa ya dinga fad'a yana cewa shikkenan lalura ba zata samu bawa sai a jingina hakan da wani mutuniyar kirki ce wadda ba ta da abokin fad'a sam baya tsammanin za ta aikata haka.
Duk yadda na so na fahimtar da shi ya kasa fahimta nagartatta kawai yake fadi shi ma ya sheda ayyukan alherinta a zahiri.
To sai kawai na kyale shi domin ba zai yarda ba zai ce muna neman tayar da fitina ko mu had'a shi da abokinsa.
Tun daga ranar da ta zo taga sauyi a tare da ni sai ta janye jikinta itama. Amma ba gabad'aya sa'i da lokaci tana kirana a waya mu gaisa ko kuma na ga aike mussaman idan zata turo kaya garin nan to za ta had'o da sakon yara mai delivery ya kawo mini har gida. Duk shekara kuwa idan ta fitar da zakka tana turo mini ta ce na duba family din mu wanda suke da k'aramar sana'a na ba su domin su tashi da kafarsu. Wannan shine zan fad'a akan Maryam Amina amma ban ta'ba zarginta akan dukiyarta ba dalili nasan macace mai zafin nema mussaman a lokacin da iyayensu suka rasu ya kasance girma ya hau kanta duk itace take tsaye a kan 'yan uwanta kuma mijinta ya tsaya mata sosai har ta kafu kwarai ta tsaya da k'afafunta ko a lokacin da muke mu'amula sosai nasan tana da manyan shaguna uku daya a garinsu biyu a garin Abuja. Amma yanzu labarin da nake ji a tsakanin matan abokan mijinmu ta mallaki wurare da yawa a rassa daban daban da ake mata hurd'a ta kasuwanci. Lokacin da na samu labarin auranta da Alhaji Tajo na yi mamaki sosai ya aka yi ta amince da zama dashi a matsayin ma'aurata bayan yana da iyali ita kuma da bata son kishiya. Sai babansu Madina yake gaya mini wasiyyar da Alhaji Amadu ya bari kenan amma ba zan boye miki ba wallahi na shiga tashin hankali ganin da na yi mata a yau sai na ji gabad'aya duniyar ta fice mini daga rai lallai d'an Adam ba a bakin komai yake ba. Dama na sanar da Halisa kafin mu zo shine fa ta ce idan har na zo na ce tana gaisheta da sannu da jiki wallahi lokacin da nake gaya mata sakon Halisan sai hawaye shaaa suka sauka a kumatunta har na yi danasanin gaya mata ta ba ni tausayi sosai lallai Allah ya jarrabeta da ciwo mai wahala muna ro'kon Allah Ya bata lafiya ya kuma yafe mata kuskuranta."
Ajiyar zuciya na saki a hankali na ce." Amin suma Amin, muna nema mata afuwa da sasaauci wurin Allah, ai d'an adam sai dai idan ba hallice shi a duniya ba Hajiya amma tunda annabawan Allah suka kuskurewa Ubangiji kowane bawa ba zai tsallake ba, sai dai mu yi addu'a akan Allah Ya sa kada son zuciya ya sanya mu cutar da wani tabbas ban so jin wannan labarin ba wallahi ba zan boye miki ba hankalina ya tashi amma komai dalili yake yi. Momi ta aikata abu mafi muni shirka shine had'a Allah da waninsa cutar da wanda bai ji ba kuma bai gani ba. Idan na ce miki ta yi mana wani abu mai razanarwa na yi mata sharri domin ni dai a zamana da ita ban hangi wani babban lamari kwatankwancin na Halisa ba. Kamar yadda kika fad'a macace mai alheri domin ta ri'ke mini yarana da ubansu ya rasu don 'karamin ma ya fi shekara shida a hannunta babban ne bai wani jima ba wani dalili ya katse zamansu a hannunta. Idan kin ce ta gwanance wurin kissa da kisan mummk'e wannan zan bada sheda akan haka domin halin da muke ciki kenan da ita koda take kwancen nan maigidan hankalinsa yana wurinta kuma tsayin zamansu gaskiya bai ta'ba kawo mana wani korafi ko aibu a kanta ba asalima boye sirrinta yake yi ko fad'a suka yi ba ma ganewa. Gabad'aya ya za'be ta ya fifita akanmu. Kuma kin ga ni dai a zahiri mun fita kuruciya da komad'a amma wallahi a kanta ko 'ya'yanta sai ran kowa ya 'baci a gidan nan. Ni matsalata da ita kenan. Amma ta fanni asiri ni ban yi imani da cewa jifanta zai yi tasiri a jikina ba koda tana yi din wallahi ba a zaune nake ba nima ina ko'karin kare kaina da addu'a da neman tsari. Ban 'ki ba shi maigidan domin a wasu lukutan abubuwan da yake yi kamar mai rangwamin hankali. Amma duk ba wannan ba yanzu ta lafiyarta ake yi domin sai da lafiya ake komai. Duk abinda muke zargi ko hasashe a kanta idan har tana aikatawa muna roka mata gafara daga wajan Allah mu ma ba mu wuce mu tsinci kanmu akan hanyar da ta bi ba ba mu da wayo ko dubara sai ta Allah. Allah ya yafe mata da mu bakidaya."
Ta amsa da Amin Ya hayyu ya 'kayyymu, ai in banda na zo na ga halin da take ciki hankalina ya tashi wallahi babu wani dalilin da zai sanya na tashi maganar nan in banda yanzu kin ji babu wanda na ta'ba zama da shi na gaya masa sai dai zargi da hasashe da mutane suke yi a kanta, sannan da wasu maganganu da na ji ana yi a kan ku wai kun had'e mata kai ba ku sanyata a cikinku kun wareta kin san maganar duniya bata 'buya shine fa abin ya ba ni mamaki cikin zuciyata nake fad'in yadda nasan Maryam da wayo da kissa anya za ku iya kai ta 'kasa kuwa."

Da mamaki mai yawa na ce." A a wallahi ba mu ware ta ba sharri ne kawai irin na mutane amma ke don Allah a ina ki ka ji wannan maganar."
Tana yar dariya ta furta." Wallahi a gari na ji ni ma shine nake ta mamakin Hakan saboda nasan Maryam ba zata ta'ba yarda ta yi boranci a tsakaninku ba."
Na girgiza kaina da damuwa mai yawa na ce." Aikuwa masu fad'in haka sun d'auki hakkinmi ba mu ware Maryam ba wallahi, sharri ne kawai irin na mutane idan an ce babu jituwa a tsakaninmu na yarda amma babu maganar mun had'e mata kai ko mun ware ta."
Ta ce." Allah Ya kyauta dai yanzu gashi Halisa yaranta hud'u fa a gidan Murtala shine ai nake cewa Allah ya tsine abinda ba zai wuce ba."
Kafin na bud'e baki na yi magana suka shigo su biyu maigidan ne da mijin nata Alhaji Sulaiman. Sai yanzu na sheda fuskarsa lokacin haihuwar twins da ya shirya walima na gan shi ya zo da kuma lokacin d'aurin auransa da Momin na ga hotonsu a tare ashe shine.
Suka iso wurin da muke zaune Alhaji Sulaiman din ya fad'in." Uwargida ta gidan Tajo ina 'yar uwar taki take ne?"
Ina d'an ya'ke na ce." Hauwa tana ciki ba ta jima da tashi ba, ina yini ya hanya mun gode sosai fa."
Ya ce." Ai ta ce za ta shigo ku gaisa ina can tsaye ina jiranta kusan minti talatin me kuka tattauna ne?"
Ya krasa maganar da barkwanci sai na yi dariya ganin mutum ne shi mai raha ba irin abokin nasa ba na ce." Hira muke yi ta duniya idan kana so ku ji abinda muka tattauna sai ku gaya mana abinda kuma ku ka tattauna a waje."
Sai kuwa ya fashe da dariya yana dukan kafadar abokin nasa kamar wani kurma yana tsaye yana kallonmu cikin dariyar dai ya ce." Ka ji fa mutumina to mu ai ba zai wuce sabgar kasuwanci muka tattauna ba ko ba haka ba ne?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ita fa kishi ne da ita shiyasa take bugun cikinka ko tana tunanin aure zan 'kara."
Hajiya Aziza ta yi caraf ta ce." A haf yanzu gashi babu wanda ya matsa bakinka ka fad'a abinda yake zuciyarka kenan zaka kara aure tunda ya baka labarin yana neman cike gurbi ko."
Yasa dariya yana cewa." Wallahi ya gaya mini kuma wai budurwa ko?''
Ta ce." Budurbazar dai ba budurwa."
Sai suka fashe da dariya a tare. Na yi sakato da baki Ina kallonsa yadda yake ta kyalkyala dariya yana tambayar Hajiya Aziza wai menene budurbazar ita kuma tana ta jin haushi domin daka ga ni da gaske mijin nata auran zai yi kuma budurwa."
Yana dariya ya dube ta yana fad'in." Ke in banda abinki ai abinda ake ya yi kenan kuma tsoho da kudinsa sai ya sha shagali ko ba haka ba ne mutumina."
Alhaji Sulaiman yana gyara babbar rigarsa ya ce." 'Kwarai kuwa Alhaji to menene sunna ce fa mai karfi kuma iyayen yaran nan ma yanzu sun fi so su bawa irin mu aure."
Na ce." Makwad'aitan iyaye ba, amma gaskiya kuna da budurwar zuciya kai fa har jikoki ne da ka, amma shine za ka d'auko musu magana."
Maimakon maganata ta bashi haushi sai ma ta bashi dariya tunda na lura mayen dariya ne tunda ya shigo bakinsa a bud'e yake ya ce." To shine me? Amina daga kawai ina da jikoki uku sai aka ce na tsufa a ah ni yanzu ji na nake yi kalau da ni wallahi."
"Um!" Kawai na ce na juyar da kaina gefe abin yana damuna. Ko dai Shima neman auran yake yi ne ganin ba a tambaye shi ba ya fallasa asirin zuciyarsa. Wata zuciyar ta ce mini a a hankalinsa fa yana kan matarsa ba ma shi da nutsuwar duba wata mace da sunan aure matarsa da yake tsananin so bata da lafiya. Anya wannan hasashen na zuciyata ya yi daidai kuwa.
Na ji maganarta a tsakiyar kunnena tana fad'in. " Amina za mu gudu kuma ba ki ba ni lambar wayarki ba. Da sauri na dube ta sai na ganta a tsaye tana gyara jakarta dake rataye a kafadarta.
Na mike tsaye da sauri ina fad'in." Har tafiyar ta tashi kenan, to mun gode sosai Ubangiji Allah Ya ba ku ladan ziyara da dubiya." Ta amsa da Amin tana miko mini wayarta. Na karba na sanya mata lambata ba don raina ya so ba dalili na fahimci tana da surutu idan ba haka ba mai zai sanya daga zuwanta babu wanda ya tambayeta ta fara zuba. Gabad'aya ma ni sai na ji zuwanta bai yi mini dadi ba na farko labarin da ta ba ni akan Momi ba wai na k'aryatata ko na gazgatata ba, nasan hakan na iya faruwa abin ya tsaye mini a rai ainun! sai kuma wannan wasan da ya kasance wanda suke daukarsa kamar barkwanci ni kuma abin ya d'an sosa mini rai wata'kila da gaske shima neman auran yake yi kuma budurwa tunda gashi abokinsa yana fad'a mutum da kudinsa kuma iyayen yara yanzu sun fi so su bawa mai aure yaransu a ganinsu za a fi kula da su.
Iyakacin rakiyar da na yi musu bakin kofar falo lokacin ma dab ake da kiran magriba. Shi ya bi su a baya ni kuma na koma ciki kai tsaye d'akina na shiga na zauna gefan gado tare da tallafe ha'ba. Oh hasashen da ake ta yi akan matar nan yana nema ya zama gaskiya tabbas akwai abinda take yi ko ta sanya malamanta ke yi mata akan jama'a, ai 'yar kasuwa ce mai hurd'odi da yawa mafi akasari kuwa duk eani dan kasuwan da ya yi shura a duniya yana neman jama'a walau ta hanyar Allah ko ta hanyar halaka. Ni dai nasan ina tsananta rokona ga Allah akan ya kawo mini kasuwa da jama'a masu k'aunar abinda nake sayarwa ko a can baya ma da na dinga fafutukar tsayuwa da kafafuna addu'ata kenan Allah ka d'ora ni akan masu sayan kayana, Ubangiji Allah ka haskakani Allah ka ba ni nasibi da jalabi abinda nake roka kenan a wurin Allah ban ta'ba kauce hanya domin tara mutane ta kowace siga ba. Tabbas ana neman jama'a ana kuma karawa da farin jini da kwarjini babu shakka akwai daya daga cikin abu biyun nan da na fad'a tana yi ko kuma tana sanyawa a yi mata. Asirin mallaka kuma za ta iya yi masa tunda labari yazo akan cewa ba ta son kishiya idan ba mu fita ba to ita ta fita zakka a cikinmu ta zama mad'aukakiya a wurinsa. Wannan shine tunani na akanta.

Bayan sallar Isha'i ya shigo ban ji ma da idar da sallah ba ina ma zaune saman daddumata da carbi mai lamba makale a hannuna. Sai da ya jira na kammala tukkuna muka shafa addu'a a tare ya ce." Abinci za ki ba ni yunwa nake ji wallahi tun safe rabona da abinci Amina."
Ina ninke dadduma ban kalleshi ba na ce." Tun safe lallai da ka sani kawai ka d'auki azimi."
Ya d'an riko gefan hijabin jikina cikin sigar tsokana ya furta." Idan na yi azimi ke kanki kin san gajiya nake yi da daddare ba ni iya aikata komai kuma yau na jarabtu dake."
Ya'ke na yi ban ce komai ba. Ya sake janyo hijabin nawa a karo na biyu har sai da na yi tangal-tangal na ce." Menene hakane?"
Ya cika gefan hijab din yana fad'in." Je ki kawo abincin mu yi magana."
Ban ce komai ba na fita kai tsaye kicin din na nufa Baba Tabawa ta gama shirya komai jallof din shinkafa ta yi ta ji alayyahu da busashen kifi ta yi kyau sosai tana ta kamshi ta had'a zobo shima da ya ji kayan kamshi Baba Tabawa akwai tsafta da gwanancewa wurin shirya abinci mai rai da lafiya. Na shirya masa duk abinda ya kamata a tire na d'auka na fita daga kicin da takaicin abubuwa da yawa a raina.
Yana kwance saman gadona yana waya na dire tire din hannuna tare da zama can gefe ya d'an jima yana wayar kafin ya kammala ya sauko kasan kafet yana fad'in." Ki zo mu ciyar da juna mana."
"Ka ci kawai zan ci an jima."
Bai sake magana ba ya zuba abincin da kansa bai nemi dana zuba masa ba lemon ma shi ya tsiyaya abinsa ya yi Bismillah a nutse ya fara cin abincin. Na d'auki wayata ina dubawa sai na tsinkayi maganarsa yana fad'in." Hirar me kuka yi ne da Aziza Amina?"
Ya fad'a tare da dubana. Na kalleshi da mamaki namiji da son jin gulma kai tsaye na ce." Hirar matarka muka yi.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: Ya ce." Hirar matata kuma?"
Na ce." E, mun yi hira akan lalurarta da kuma wata mas'alar da ta shafe ta.''
Ya d'an kalle ni kafin ya mayar da hankalinsa kan abincin da yake gabansa ya furta." Ku fa mata ba a raba ku da gulma Amina wace mas'ala kuma?"
Da mamaki na ce." Ka ji ka da wata magana ai yanzu gulma ta tashi daga kan mata ta koma kan maza wallahi."
Ya kalle ni na wani lokaci kafin ya ce.'' To ba ni na sha wace mas'ala ce?"
Yadda ya fadi maganar cike da son jin labarin sai ya ba ni dariya sosai na ce." Ka gani ko? dama na gaya maka gulma ta tashi da ka kan mata."
Sai ya 'bata rai yana cewa." Me ki ke nufi ?" Nasa dariya tare da cewa." Ai ban ce maka magulmaci ba misali na yi kawai."
Murmushi ya yi kafin ya cigaba da cin abincin d'akin ya d'auki shiru na wani lokaci na ji gyaran muryarsa na dube shi ya gama cin abincin ya ta so ya zo kujarar da nake zauna ya nani'ke ni sosai yana fad'in." Bari na zauna kusa dake sosai zan fi fahimtar gulmar yadda ya kamata."
Murmushi na yi ban ce komai ba. Ya kamo hannayena yana dubawa kafin ya ce." Wai ke ba ki jin kunya ne?"
Na kalleshi da sauri kafin na ce." Me kuma na yi maka?"
Ya bud'e tafukan hannayensa yana fad'in." Ya kamata ace hannayena da naki sun bambamta ki dinga yin lallai na gaya miki yana yi mini kyau."
A jiyar zuciya na d'an sauke a nutse na ce." To zan yi in sha Allahu.''
Wayarsa aka kira ya je ya d'auka daga tsaye ya amsa kiran na d'an wani lokacin kafin ya kammala yana kashe wayar yake fad'in." Lokacin madam ne yanzu kashe wayoyin zan yi gabad'aya sai Allah Ya kaimu kuma."
ina kallonsa ya kashe duka wayoyin nasa kafin ya dawo ya zauna kusa da ni yana cewa." Ba ni labari."
Sosai na dube shi kafin na ce." Kasan Halisa k'anwar Hajiya Aziza?"
Ya d'aga kansa yana fad'in." Kwarai na san sunanta amma a zahiri ban ta'ba ganinta ba.
Na gyada kaina a sanyaye na furta." Labarin abinda ya faru da ita ya ta'ba mini zuciyata."
Sai ya ce." Ta ba ki labarin Alhaji Amadu ya ta'ba nemanta ne?"
Na ce."E, wallahi, amma yadda aka kusa sabauta mata rayuwa shine abinda ya rikita ni, kai Allah dai ya yafe mana."
Cike da rashin gane inda na dosa ya ce." Shikkenan kuma saboda Allah bai kaddara an aureta ba sai a sabauta mata rayuwa komai yin Allah ne fa, tabbas na ji labarinta wurin alh Amadu lokacin jim kad'an da rasuwar matata ta biyu Ayush ba na gari ma yake gaya mini yana neman auran kanwar Aziza matar Alhaji Sulaiman daga baya kuma ya ce mini ya janye saboda wasu dalilai."
Na ce." Bai gaya maka gaskiya ba matarsa ce ta jefe ta ta d'ora mata muguwar jinyya mai razanarwa."
Ya gyad'a kansa kafin ya furta." Abinda ta gaya miki kenan?"
Na ce." Kwarai kuwa, Kuma gaskiya akwai 'kamshin gaskiya a maganarta domin wallahi zan gaya maka a sammace kake Maryam ta gama da kai."
Dariya ya fara yi yana kallona kafin ya furta." Ai ni kafin ki ga mace ta gama da ni wallahi sai ta yi da gaske Amina."
Na ce." Au haba?''
"K'warai kuwa, yanzu dai mu bar wannan maganar mu yi ibada domin mu samu lada."
Na ce." Magana fa ba za a bar ta ba, saboda kasan gaskiya Hajiya Aziza ta fada shiyasa kake bagarar da maganar wallahi ko ka 'ki ko ka so Maryam mashirika ce."
Da sauri ya ce." Subahanallahi!"
Na juyar da kaina gefe na ji yana fad'in." Ki daina ba ni so ranar lahira Ubangiji ya tsayar mini dake domin ki bada sheda shin kin ta'ba ganinta tana shirka da Idonki."
Na girgiza kaina a hankali kafin na ce." Ban ta'ba gani ba ayyukanta ne suka nuna haka a zahiri."
Jim ya yi yana nazari kafin ya ce." Kin ga wad'annan maganganun Amina na jima ina jin su akanta tun kafin ma na aureta da yawa an kawo mini suka akanta na rintse idona domin cika wasiyyar da abokina ya bari na kuma yi imani da cewa babu wani kulunboto da za ta yi yayi tasiri a kaina don haka kada ki gazgata kema tunda ba ki ta'ba gani da idonki ba, ki dubi alherinta kawai idan ma tana yi wannan tsakaninta ne da Allah."
Shiru na yi na wani lokaci kafin na ce." Allah Ya kyauta amma tsakani da Allah wasiyyar nan da aka bar maka ba ta yi mana rana ba shi kuma duk cikinku ya rasa wanda zai bar wa wasiyyar auran matarsa sai kai, anya babu lauje cikin nad'i kuwa."
Ya 'bata ransa sosai Yana fad'in." Amina ba ni son abinda zai daga mini hankali a yanzu, na gaya miki maganar nan tun farkon fari wallahi tallahi babu wani dalili da zai sanya na ci amanar abokina wai da ransa na kwadaitu da matarsa kuma shi ya rubuta wasiyyar nan da hannunsa ni kuma na yi kokari cika ta domin na gaya miki ko ni na fadi na mutu zan yi farinciki ace shi ya maye gurbina a wurin iyalina dalilin aminci da sha'kuwar da take tsakaninmu."
Na ce." To na ji amma ai tun kafin ya rasu kake yabonta tare da fad'in kyawawan halayenta har cewa kake yi ta iya soyayya."
Ya dafe kansa kafin ya ce." Na fadi hakane saboda ki yi koyi da ita domin ni mutum ne mai son a kula da ni a kuma tarairayeni da soyayya. Zan gaya miki gaskiya wannan ma yana daya daga cikin dalilan da suka sanya nake yabonta saboda ba ta tsallake umarnina kuma duk abinda na nuna masa soyayya tana yin fiye da yadda na yi idan kara na ajiye bata tsallakewa ke kanki da ta fahimci ina sonki ta taya ni sonki domin ban ta'ba ganin kishinki a tare da ita ba."
Murmushi na yi na takaici na yi shiru ban ce komai.

Idan ki ka karanta ba ki biya ni hakkina ba ina bin ki bashi.

Ya rike hannuna yana fad'in." Maganar nan don Allah kada a sake tashinta matar nan tana cikin halin rai da rayuwa ni dake da duk wani makusanci a gare ta adduarmu take buk'ata, kada ki yadda zantukan mutane su rusa miki tunani da Imani, ita kuma Hajiya Aziza na raina wayonta wallahi ai Maryam sanin da nayi 'kawarta ce sosai Aminiya abokin b'arawo ai b'arawo ne Amina mai zai sanya daga zuwa kawai ta gaya miki abinda ya jima.. Ubangiji ya hana fallasa asirin bawansa mussaman idan bawan nan ya yi tabbatacccen tuba."
Da mamaki na ce." Har yanzu dai ba zaka daina take gaskiya ka fifita karya ba ko, kai tsaye ka ki ka aminta da zantukan da suke yawo a gari akan matar nan, kai ma da bakinka ka fad'a cewa an gaya maka amma sai kame-kame kake yi kana kare ta Hajiya Aziza ai ba ta yi lefi ba tunda komai dalili yake yi.".
Ya ce." Ba wai kare ta nake yi ba Amina na ce miki Allah ne ya yi hani da cewa idan daya daga cikinku ya aikata kuskure ku yi shela a duniya mussaman idan bawan nan ya tuba babu wanda yake shiga tsakanin mahallici da bawansa."
"Ka tabbatar da cewar ta tuba?"
Da tsawa ya ce." Ke Amina maganar nan ta isa

Please Login or Register in order to submit comment