Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga zumunci mu tare musu a gida ba. Ina lefin wata biyun da mukayi ai ya isa. Tun Hadiza na daurewa har sai da ta fashe da kuka tana cewa." Anti Yagana menene don na ce zan zauna na kula da 'yar uwata. Ba ni fa da nauyin kowa a kaina ba miji ba yara. Ko don ba ciki daya muka fito tare ba shiyasa zaki dinga nuna mini banbanci. Ko ina da wani aibu ne."

Cikin rashin jin dadin abinda Anti Yagana ta yi mata na ce." Hadiza ba haka ba ne, ba ki fahimci Anti Yagana ba, amma kada ki yi mata wannan fassarar don Allah, menene babu komai ki yi zamanki mana, na gode sosai da kulawarki a kaina, Allah ya bar zumunci."
Anti Yagana tana jin mu ba tace uffan ba sai aukin tsaki da take ja. Na riga na gama fahimtar duk inda ta dosa. Tana jin tsoron zaman Hadiza ne kada ta zo ta aikata wani abin da zai sanya girma da mutunci mu ya zube a idon maigidan.

****
Duk wani shirye-shirye na tafiyar anti Yagana maigidan ya kammala mata domin cewa ya yi a jirgi zata koma gida in sha Allah dan ba kasafai ya fiye son tafiyar motar nan ba.

Gudun aure na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Saura kwana biyu ta tafi rikici ya balle a tsakanina dashi domin har ga Allah nayi iyakacin bakin kokarina wurin ganin na danne abin a zuciyata hakan ya gagara. Tun lokacin da muka sasanta jununmu nake masa soyayya ta tsakani da Allah irin wadda ba na so ko kuda ya kusanceshi. A zahiri tashi ce ta fito fili, amma ni gani nake yadda nake bala'in sonsa da kishinsa baya yi mini kwatankwacin hakan. Kuma ina ganin komai na rayuwata zan iya bud'a masa ya san dashi ba zan rufe masa ba, zan iya bayyana masa sirrina ganin yadda ya d'auke ni, da kuma matsayi maigirma da ya ba ni a zuciyarsa. Duk wanda zai ba'kunce mu na second guda zai fahimci cewa akwai k'auna sha'kuwa da mutuntawa a tsakaninmu. Dalilin da ya sanya ma kenan na ajiye hakan a raina cewa. Babu wani abu da ya dangance shi da zai boye mini sai gashi yau ya nuna mini cewa namiji ne fa shi kuma dabi'ar nan fa ta kumbiya kumbiya da Allah ya hallice su da ita ba zata canza ba. Hauwa dai yar uwarsa ce ni ban isa na raba tsakaninsu ba, amma wallahi ban taba tunanin suna waya ba domin bai ta'ba nuna mini hakan ba, yarda dashi ce ta sanya ma ba kasafai nake d'aukar wayoyinsa ba duk da cewa yakan ajiyesu a wurin da nake zaune ko ya tashi ya fita daga d'akin ya bar su. Da can na yi zarginsa dalilin abinda ya yi mini farkon haduwarmu, amma da zama ya yi zama a tsakaninmu sai na gazgata rantsuwarsa inda yake ce mini bai taba kusantar zina ba, kawai ya jarraba ni ne akan wata bukatarsa don samun abokiyar rayuwa. Ashe ha'kan Inna Uwani ya kusa ya cimma ruwa ban sani ba, ina ta zaune sake da baki.
Abinda ya faru shine bayan mun gama sunna sai bacci ya kwashe ni domin ba wuya bacci haka nake yi don yanzu ko auratayya muke yi bana wani katabus shi yake kidansa da rawarsa wasu lukutan ma ina gyangyadi zai kammala. Abinda ya faru kenan bacci ya kwashe ni, shi kuma ya shiga bandaki domin yin wanka. Cikin ikon Allah kiran wayarsa da akayi wadda take saitin kaina na bud'e Ido firgit sakamakon karar da ta cika mini kunne. Na tashi da sauri idona ya sauka kan fuskar wayar wanda sunan Dr Hauwa ya fito rad'au kan screan din. Gabana na bugawa na tsirawa sunan Ido a sa'ilin kuma na nemi baccin da yake cikin idona na rasa na yi tarmazai ina ta duba sunan dr Hauwa. Ban d'auki wayar ba har sai da ta katse na d'auka na shiga wurin kira naga iya adadin kiran da tayi masa ba zai k'irgu ba. Na duba shi ma naga ya kira ta sosai. Na duba messages gasunan kala kala ta turo masa na gaisuwa da fatan alheri da kuma na soyayya Amma ba kowanne yake bata amsa ba domin kusan guda talatin bai fi uku ya rubuta godiya ba. Hakan bai sanyayar mini da zuciya ba domin na san ba kasafai ya fiye son rubutu ba ya fi kiran waya ko a Whasap ne sa'kkonin mutane sukan yi kwana da kwanaki kafin ya ware ranar da zai dubu su. Wasu ma baya reply sai dai ya kira mutum a waya.
Na ajiye wayar na koma na kwanta zuciyata na tsalle da tafarfasa. Ni kaina ban san haka nake da zafin kishi ba sai yau idona har ya ji yake yi mini wani 'kullutun abu ya danne mini makogwaro.
Koda na ji fitowarsa daga bandakin ban bude Ido ban kuma motsa ba. Ina jin lokacin da ya d'auki wayar ya zauna saitin kafafuna yana dubawa ban bud'e idona ba amma duk wani motsinsa Ina ji.
Kawai sai na tsinkayi maganarsa yana cewa." Hauwa ya kike, ina wanka ne lokacin da ki ka kira, Ina inna Uwani ya aikin naki."
Ashe kiranta ya yi domin a tunaninsa bacci nake yi.
Tana tsaka da bashi amsa na bud'e idona tare da tashi zaune Ina kallonsa. Ya dube ni yana fad'in." Bari zan kira ki an jima sai mu yi maganar oke."
Ya kashe wayar ya ajiye yana fad'in." Madam tashi ki yi wanka mana."
Na dube shi fuska a turbune...." Menene na katse waya da sauri kana cewa za ku yi magana an jima. Hauwa ce fa, to menene abin boye mini, ko ni din na isa na hana ka ka aureta ne.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*TALLAH!*
<Ø2ß<Ø3ß<Ø?ß&þ
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*16*
Ya girgiza kansa yana ce wa." Ba ki isa ba, muddin ina da ra'ayinta. iko kuma ina dashi, bayan hud'u har 'kwarkwara zan iya yi."
Na ce." Haka ake son namiji ai, dama ai na jima da sanin target dinka Yallabai, don girman Allah ka auro ukun a lokaci daya to me zai dami Amina."
Ya jima yana kallona da fuska irin ta b'acin rai. Yana da juriya a wasu lukutan idan sa'insa ko rigima ta had'a mu yakan sakar mini ya share duk maganganun da zan ya'ba masa kuwa. Amma a wasu lukutan yakan yi fushi ya kuma nuna mini b'acin ransa. Yadda na fahimta tsayayayyar da nake masa ta fara tunzura shi.
Ya furta." Ki shiga hankalinki fa Amina, ki daina ganin kamar na mayar da kaina sauna akanki ki nemi ki yi mini rashin kunya zamu sanya kafar wando daya a tsakaninmu. Tabbas ina sonki amma hakan ba zai sanya na zuba Ido kina cin kasuwa a kaina ba, ke ba ki da aiki sai bakin kishi, motsi kad'an sai kin tuhume ni, haifata ki ka yi da zaki dinga titsiye ni da maganganu irin wannan. Na gaya miki ina da ikon mata hud'u a yanzu. Ba zai yiwu Allah Ya halasta mini abu ba wata mace ta tsorata ni ba. Ni ba sakaran namiji ba ne. Hauwa k'anwata ce, kuma ina da damar auranta a yanzu muddin inda ra'ayin hakan so ki samawa kanki nutsuwa tunda ban tauyeki ba."

Na ce." To ka fito fili ka fad'a mana zaka auri Hauwa sai me? Ai ni dama ban ce ni din 'yar'uwarka ba ce, to me ya had'a ni da kai dama in banda k'addarar aure. Me ya hanaka auran Hauwan tuntuni. Matar da ita da uwarta suka guje ka a baya sai yanzu zasu dawo rayuwarka saboda wata manufa. Idan zaka auro duk 'yan gidansu Hauwa bai dame ni ba wallahi." Na kàrasa maganar ina buga cinyata da yin wani irin nishi!

Cikin fusata ya buga katifar gadon na dan tsorata kuma gabana ya buga na matsa gefa. Fuskarsa ta canza sosai da fushin da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Ya ce." wallahi kin ci arzikin abinda yake cikin ki amma da ba don hakan ba sai na sa'ba miki, ni za ki dubi tsabar idona ki gayawa magana dan Ubanki, ban haifeki ba. Inna Uwani sa'arki ce, ko ni zan iya duban tsabar idon mahaifinki na gaya masa magana. Na taba cin zarafin wani a halinki baki da mutunci ko Amina, kin ga damata kina gaya mini duk abinda kike so zan baki mamaki."
Duk maganganunsa ba su yi mini ciwo illa zagin da ya yi mini hawaye ya b'alle mini ina kuka nake ce wa. " Ni kake zagi ko? Ai duk a cikin maganganuna ban yi maka sharri ba, gaskiya na fad'a kuma ban zage ka, amma ka dubi tsabar idona ka zagi Ubana, ka haife ni ne?"
Tsaki ya ja mai karfin gaske ya tashi ya fara hidimar sanya tufafi a jikinsa. Lokacin Hauwan ta sake kiran wayar amma bai yi yun'kurin d'agawa ba, na ce." Ka zo ka d'auka mana 'yar uwarka jininka tana kiranka a waya, ni bana son munufarci.
Bai saurare ni ba sai da ya gama shiryawa tukkuna ya zo ya zauna a kusa dani ya d'auki wayarsa ya kirata. Muryar da ni kadai yake yi wa amfani da ita idan muna bargo daya da ita ya yi wa Hauwa magana......"My love menene uhmm! ki samu nutsuwa za a yi, in sha Allah akwai maganganu masu muhimmanci da zan tattauna dake in sha Allahu idan na samu sukuni karshen watan nan zan zo bauchin sai mu tattauna ki gaishe mini da Inna Uwani."
Tana bashi amsa ya tashi da wayar a kunnansa ya kama hanyar fita. Cikin gaggawa da mugun sauri na yi nufin dirowa daga gadon bargon da yake kafafuna ya tad'e ni na fado rigib!
Ya juyo a razane a lokacin ni kuma na yun'kura na tashi duk da ciwon da jikina yake yi mini hakan bai hana ni tunkararsa ba. Da sauri ya bude kofar ya fita dan yadda ya nuna mafisar ta ishe shi haka in ba haka ba ya tsaya mu yi mana. A baranda na riske shi don bai kai ga sauka ba. Na ri'ke shi ta baya kamar mai shirin yin kokawa. Zuciyata sai tunzura ni nake yi, na rasa wane hukunci zan yi masa kuka kawai nake yi na ri'ke shi katamau! Hankalin Hajja da Anti Yagana ya yo saman domin gunji nake yi ba kad'an ba.
Shi kuma duk ya diririce! Sai kamo ni yake ko'karin yi yana cewa." Ki bi fa komai a hankali, kin ga an yi ne? da za ki tayar da hankali, ni dai ban cuceki ba."
Ganin Hajja tana nufo benan na fara cewa." Don zaka yi aure sai ka sanya ni a gaba kana zagin ubana, me ya yi maka? Ina lefinsa da ya haife ni, ni ka zage ni mana amma ka daina ambato sunan mahaifina kana zagi ai bai nema a wurinka ba, a wurin Allah yake nema, wallahi Hajja na gaji ba zan iya ba." Na kàrasa maganar da kuka mai karfin gaske....

Hajja ta dube shi da mamaki a tare da ita ta. Kafin ma ta furta wata kalma anti Yagana da take ta jefo mini harara ta ce." To idan auran zai yi ai ba za ki hana shi ba, wane irin wulakanta kai ne wannan Amina." Hajja ta ce.'" A a Yagana a yi magana ta hankali mana, iyaye ai ba abin wasa ba ne, kina jin fa abinda ta fad'a."
"Wallahi tallahi idan duk jikina kunnene ba zan yarda da cewa ya zageta ba, Hajja na san halin kayata."
Hajja ta girgiza kai tana dubansa ta ce." Tajo ashe aure za ka yi ba labari."
Yar dariya ya yi irin ta takaici yana ko'karin cire rigarsa dake ri'ke a hannuna ya ce." Ban tashi yin ba dai kawai ta ji muna waya da Hauwa shine ta daga hankalinta.
Sai ta dube ni tana dan murmushi wanda na kasa tantance ko na menene ta ce." To ki yi hakuri kin ga kina tare da lalura, kishi a yanzu ba na ki ba ne, fatan mu dai ki sauka lafiya."
Sai na yi kasa'ke ina kallonta. Anti Yagana taja tsaki ta bar wurin na san haushina take ji kan abinda na yi.
Ganin haka sai shima ya silale Ina kallonsa ya sauka da saurin gaske. Hajja ta fara rarrashina akan na nutsu kada na daga hankalina tunda ai banga an yi ba.
Sai a lokacin kunya da nauyin matar suke kama ni. Idan na ce zan yi irin wannan dibar albarkar to zahiri zan bata kwa'bar da na yi.
Hakama ina shiga d'aki anti Yagana kamar ta dake ni tana cewa. Wallahi kada ki bari ki kai mutanan nan karshe Amina, in banda rashin mutunci da samun wuri ina ruwanki da shiga lamarinsa da 'yan uwansa, idan auran ma yace zai yi menene abin damuwa, mutumin da bai tauyeki ba shine zaki tona masa asiri har da cikwukwuye masa riga saboda kawai kin ga suna sonki, ko kuwa sa'anki, babba dashi irin haka, waye ya gaya miki yanzu ana irin wannan kishin na hauka, ba ki ta'ba ban haushi ba irin yau wallahi.
Na nemi gefan gado na zauna jikina a sabule hawaye na silalowa daga idona na ce." Anti Yagana zagina fa ya yi wai don ubana, ina ga duk rikicin da za mu yi dashi idan cin zarafin iyaye ya shigo sai inda karfina ya kare wallahi."

"Bango ki ka kaishi, ai tunda na zo gidan ina fuskantar irin zaman da kuke yi, wasu lukutan kamar kece kike auransa abinda kika ce shi za a yi, dama ai mai ha'kuri bai iya fushi ba.
Na ja hanci raina na cigaba da suya domin na gama fahimtar cewa anti ba zata saurari uzuri na ba, kuma har yanzu ta kasa gane abinda nake ji a zuciyata game da maganar Hauwa. A dake ka kuma a hanaka kuka. na kwanta kusa da Hadiza da take ta bacci duk maganganunmu bai sai ta motsa ba, anti ta cigaba da maganganu tana fad'in. " Ina ce ba daga gidan kishiyoyi ki ka fito ba, Alhaji Muntari wannan bagidajen mutumin ba matansa biyu ba, kece fa ta uku kin san ba kya son kishiya me yasa ki ka aure shi, sai wannan saboda kin fahimci lagonsa akanki kike dabdala a kansa. Wallahi ki ki yayi fushin irinsu, kuma idan ki ka ce ta irin wannan salon za ki dinga nuna kishinki zaki fice masa daga rai. Ko waye ya gaya miki anayi wa namiji irin haka ya cuceki idan zaki farka ki farka."
Cikin kuka na ce." Anti Yagana don Allah ki kyaleni haka ba ki san abinda nake ji ba ne, shiyasa kike yi mini wannan maganganun lamarin bai zo kanki ba ne."
"To shikkenan ki yi mini rashin kunya don na gaya miki gaskiya ba sai kin kara ganina a gidan naki ba, duk abinda za ki yi, ki je ki yi rayuwarki ce, ke za a yi ta lissafawa aure, ace kowane d'a da ubansa."
Hawaye ya kara shararo mini shiru na yi mata ban sake cewa komai ba. Ita tunda ta ce haka ba ta sake wata maganar ba, ta fita falo wajen Hajja.

Ko'karin daure zuciyata na yi duk da abinda yana sasakata ban nuna ba ina so mu rabu lafiya don ganin yadda take ta jin haushina tana fushi da ni, na dinga bata ha'kuri har sai da huce tukkuna, na hada mata abubuwa masu yawa da kudi haka ma maigidan dubu dari biyu ya bata wai ta sayawa yara alawa. Koda zata ta tafi kasa daurewa na yi kuka na dinga yi haik'an! kamar 'kan'kanuwar yarinya Ita kam bata wani nuna alhini a zahiri ba amma dai na san cikin zuciyata tana jin rashin dadi. Ina kallo su Hadiza da Yusi suka tafi rakata filin jirgi, ni kuwa ya ce na zauna kawai a gidana. Haushinsa ya kara nauyi a zuciyata. Ita kanta Hajja sai da ta goge kwalla domin gaskiya sun shaku sosai da Anti Yagana.

Duk yadda na so da na manta da abin kasawa na yi domin sai nake ganin kamar ni ya takewa hakki. Akwai cin fuska a cikin abinda ya yi mini, dalilin ma da ya sanya kenan na yanke shawarar akan ba zan sake lamunta yayi waya da wata mace a cikin gidan ba koda kuwa ma'aikatansa ne. Idan har yana so ya zauna da ni lafiya. Ni ba namijin da zan zauna ya zagi Ubana gobe kuma na washe masa baki wallahi sai na nuna masa kuskuransa ba ruwana da kudi da shekarunsa iyaye ba abin wasa ba ne. Tare nake zaune da mahaifiyarsa ban ta'ba gaya mata bakar magana balle har na dubi tsabar idonsa na zageta. Ubana bai yi masa komai ba, ba kuma zan yarda ya saba da zaginsa ba ai kud'i ba hauka ba ne.

Sati biyu babu jituwa a tsakanina domin duk yadda ya so da ganin mun shirya naki bashi fuskar hakan. Gaisuwa ce kawai take hadamu idan na sako daga samansa ba na sake komawa sai wata safiyar ina kula sosai domin kada Hajja ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu.
Tun yana rarrashina har dai ya ha'kura ya zuba mini ido. Muka cigaba da zama a hakan. Ranar wata lahadi na tashi da ciwon kwankwaso domin tunda cikina ya shiga wata na bakwai nake jin sauye-sauye a tare da ni. ji nake yi kamar haihuwar fari don ba karamin wahala nake ci ba.
Da kyar na yi wanka na zura jallabiya wajejen takwas da kwata na nufi saman nasa.
Na same shi yana ta waya na zauna na yi kasa'ke ina sauraransa ya kammala ya dube ni. Uffan bai ce mini ba. Na turbune fuska da kyar na ce." Ina kwana.''
Ya yi mini shiru bai amsa ba."
Na ja hanci takaicinsa kamar ya kashe ni domin dai na fahimci da Hauwan yake magana da sassafe 'yar iska ko uban me take gaya masa oho."
Na ce." Wai me kake jira ne kai ba yaro ba haka zalika itama ba yarinya ba tsohuwar guzuma ce fa ko yau a d'aura muku aure sai muga k'aryar wayar sassafe."

Babu sukuni ya ce." Saurin me kike yi madam an kusa in sha Allahu rabbi."
Sai na ji kamar ya soka mini mashi a wuya. Na ja tsaki tare da kawar da kaina gefe."
Ya ce.'" Wai ke daman haka ki ke ne, ba ki da kunya?"
Shiru na yi ban ce masa komai ba."
Ya sake girgiza kai a karo na biyu ya furta." Ba tsoronki nake ji ba, kuma duk take takenki na gane wallahi ba zan rabu dake ba dan zan yi aure, kuma zan fito miki da asalin kalata tunda baki da mutunci."
Hawaye suka 'kwace mini na ce." Ni ce ma ba ni da mutunci ko? Wallahi idan kuwa kana son zama da ni cikin salama sai ka bi dokokina domin kuwa ba zan zauna ka dinga raina mini hankali ba. Ka zage ni ka zagi Ubana akan wane dalili. Ni bana asiri amma zan had'aka da Allah idan har rabuwarmu itace alheri Allah Ubangiji ya tursasaka ka ba ni takardata.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*TALLAH!*
<Ø2ß<Ø3ß<Ø?ß&þ
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da

Please Login or Register in order to submit comment