Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga kicin din babu ma kuzari da karsashin da zan iya gudanar da wani abu.
Na tashi da sauri jin kiran waya na d'auka da sauri shine na sanya a kunnena har muryata na rawa na amsa sallamarsa kafin na ji shi a dake yana fad'in." Wane yaro ne ki ka ce za ki nemawa auran yarinyar nan.''
Jin wannan maganar daga bakinsa na ji sanyi ya cikin zuciyata na daidaita maganata ganin yadda yake furta tasa da isa na ce." 'Kanina ne Usaini dazu na kira shi na gaya masa kuma mu yi maganar genotype domin shine akan gaba kafin komai. (AA) genotype blood group (o)" Duka na zayyano masa wannan bayanin babu hadiyar yawu.
Ya furta.'' Ya kuke da shi Usainin kuma menene sana'arsa kin tabbatar dai da nagartarsa ko domin yanzu amanar yarinyar tana hannuna. Na ji maganar daidaituwar jini amma ina so kada ki rufe mini da son lallai aure ya tashi daga kaina ya koma kan waninki, ki gaya mini halinsa dalili mas'ala irin ta aure mussaman irin wannan da ta zo a jirkice ba a rufi ana fayyace gaskiya daga kowane bangare da ni da ke gabad'aya mun sheda nagarta da tarbiyar yarinyar nan shi wanda ki ke nemawa auran nata nake so na ji bayani na gaskiya a kansa kada ki rufe mini komai a kansa."
Na ji kaina ya wani sara saboda tsananin mamakin maganganun da yake furta mini. Wato da irin abinda zai saka mini kenan. Kwanaki uku da suka wuce ya zama kamar wani mahaukaci saboda tarin damuwa da tashin hankali. Na shiga cikin matsalarsa na bashi shawara domin samun mafita shine yanzu zai juya maganar ta wata siga daban neman mafitata ne ya sanya na ce zan nemawa dan'uwana auranta saboda shi kada ya aureta tunda Ina kishi akan yarinyar. Wannan shine karatun kawai domin duk yadda ya yi maganar a kudindine na fahimta tunda ni ba mahaukaciya ba ce.
Na daure sosai tare da danne tashin hankalin da yake yun'kuro mini na ce." Usaini kanina ne ubanmu daya ba zaka san shi ba gaskiya tunda shi namiji ne kwarai don samun kamarsa a cikin maza a yanzu dai sai an tona yaro ne mai zuciya kuma ba makwad'aici ba. Koyaushe cikin neman na kansa yake yi. Yana da shagon sayar da zannuwa a kasuwar kwari.
Sannan ya tsayar da sallah ya yi karatu daidai gwargwado na addini dana boko baya sata kuma baya shaye-shaye, wannan shine abinda na sani a kansa. Amma idan kana shakku za ka iya kiran waya idan kana da ido ko wanda kake mu'amula da shi cikin unguwarmu ta kabuga ka ce a yi maka binkice akan Usaini Salisu maihula na lungun itacce sunan layinmu ya yi suna haka zalika ma gidanmu ya yi suna babu wanda bai sani ba tun daga bakin titi zuwa cikin lungun Babanmu fitacce ne."
Ya yi jim daga daya bangaran ina sauraran amsarsa gabana na fad'uwa saboda tashin hankali mutumin nan mara mutunci ne tsantsa kuma mai mance alheri da ni yake magana."
Na ji yana fad'in." Ni da Sukairaju na yi wa sha'awarta shima ai kin sheda nagarta da cancantarsa ko na jima dashi Amina bai ta'ba cin amanata ba."
A takaice na ce." Da shi da Usainin duk daya ne ni a wajena idan ka yarda da cancantarsa a yi dashi kawai Allah Ya tabbatar da alheri."
Ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in." A a ayi dai da Usanin kawai tunda yanzu shine sakamakonsa ya bayyana kuma kin tabbatar mini da cewa babu matsala na aminta a yi da shi din.''
Na ce.'' Idan an biya sadakin zan biya ka idan ka dawo a basu dubu dari biyu. Duk abinda ya kamata na al'ada wanda suke yi za mu yi musu."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba nasan haushin maganata ya ji. Na sake ce wa." Ka na jina ko idan kuma dari biyu ta yi kad'an daga dari uku zuwa abinda ya yi sama ka biya zan baka kudinka idan ka dawo."
Sai ya kashe wayar bai ce komai ba. Na ja tsaki tare da ajiye tawa wayar zuciyata na tsalle tsabar takaici da b'akinciki da ya guma mini. Wai mutumin da ya rasa mafita ya gigice tare da zama sullutu shine ya yanzu saboda ya samu kansa yake ko'karin juya alheri zuwa sharri. Duk yadda nake 'kin auran a cikin raina ban ta'ba fitowa fili na nuna masa ba saboda gudun irin haka da yake ya iya sharri da lauya zance yana fad'in saboda kada ya aureta na ce ina nemawa d'an uwana auranta. K'warai wannan magana ta tsaya mini a cikin raina ko da na shiga kicin domin d'ora abinci ina tunaninta da mamakin fitowarta daga bakinsa........
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*153*
Haka na kammala aikin da takaici da kuma farincikin nasarar da Usaini ya samu wajan samun damar mallakar Hajara a matsayin matarsa uwar yaransa anan gaba. Akwai daidaito ta kowane bangare a tsakaninsu babu cuta babu kuma cutarwa yadda yake a nutse haka itama yarinyar take a nutse kuma babu rawar kai da iyayi na 'yan matan yanzu matsalar kawai babu zurfin boko a tare da ita wannan
kuma bai kai ace an damu dalilin rashin samuwarsa ba tunda da akwai na addinin zai kori duk wata tangard'a da za a samu a zamantakewar auran nasu wadda ba mu fatan hakan in sha Allahu rabbi.
Wajan uku saura na kintsa jikina sosai kwalliya na yi irin wadda na jima ban yi irinta ba na zuba lece brown a jikina wanda ya ji stones ta ko'ina ga kyau ga kudi na yi amfani da set din gold dina da ban jima da saye ba.
Tare muka ci abinci da yarinyar kamar koyaushe tana yi mini hirar 'yan uwanta da alama ta yi kewarsu nasan duk yadda aka yi sun iso yanzu suna gidan Hajja.
Ina idar da sallar la'asar ya kira ni dama dakon kiran nasa nake yi domin na ji a ina a akwana.
Ya ce mini an d'aura amma Malam D'aha ya ce angon ya je yana nemansa.
Yadda yake magana kamar wanda aka yi wa dole ni ma na amsa da kalar sigar da yayi mini
Ya nisa kafin ya sake magana." Ga ni nan a kan hanyar dawowa gida."
A takaice na ce." Sai ka dawo."
Na riga shi kashe wayar ban jira ya sake wata maganar ba.
Kai tsaye Babanmu na kira dama da safe na sanar da shi halin da ake ciki ya ce tunda mijina ne zai kar'bi auran to a bashi dama zuwansu ba shi da amfani dalili ga yadda lamarin ya kasance amma bayan d'aurin auran za su je wajan malamin domin godiya.
Na sanar da shi an daura sannan na tabbatar masa da cewa zan shigo gidan gobe domin mu tattauna da mahaifiyarsa akan yadda za a shirya hidimar biki."
Ya yi ta yi mini godiya da sanya mini albarka Ina kara jin k'warin gwiwa a cikin zuciyata tare da addu'ar Allah Ya taimake ni na cigaba da tallafar 'yan uwana.
Muna gama waya na kira angon na gaya masa cewa an daura ya kuma zo da daddare ina son ganinsa domin mu yi magana akan abinda ya rage na aikin gidansa da yake ginawa.
Mun jima muna waya da anti Yagana tana fad'in idan mun tsayar da magana na kira ta na sanar da ita halin da ake ciki.
Na sauke ajiyar zuciya tare da kashe wayar bayan mun gama da ita. Kiran sa ya sake shigowa a karo na biyu na daga amma ban ce komai ba. Na ji yana fad'in." Kashe mini waya ki ka yi saboda me?" Na yi shiru kawai sai ya cigaba da cewa."
abubuwan da ki ke yi mini sun ishe ni wallahil-azimin zan d'auki mataki mai tsanani a kanki Amina."
Shiru na yi ban iya ce maaa komai ba ganin yana neman fitina a irin wannan lokacin da ya kamata a ce ya kasance cikin walwala a yadda yake nuna 'kunci da damuwa a baya amma kacokan yana neman ya huce takaici a kaina shin wai ko dai yana son yarinyar nan dole ta sanya shi ha'kura saboda rashin daidaituwar jini wannan abubuwan da yake yi sun fara sanya mini zargi da shakku a kansa tunda ai zuciyarsa a kirjinsa take ba a bayyane take ba balle mu ga abinda yake 'boyewa kamar kishi yake yi.
Ya karaci maganarsa ban ce komai ba haka ya ha'kura domin duk yadda ya kai ga so na gaya masa da wanda nake waya har na katse tasa ban gaya masa ba na kyale shi dai ya shigo gidan sai mu yi wacce za mu yi ai waya ta yi kad'an.
Har bayan isha'i bai shigo ba na fi zargin yana gidan Hajja dalili Hauwa da yaran kuma tare za su kwana tunda nan ta zo ta same shi. Usaini ya zo kamar yadda na umarce shi yaro sai annashuwa yake yi ya nuna mini kara da hallaci kwarai ya kar'bi abinda bai ta'ba ganinsa da ido ba cikin girma da mutunci wannan dalilin ya sanya mini sake d'aukar al'amarin da muhimmanci kwarai da aniya. Ya nuna mini gidan nasa a waya ya yi nisa sosai don an yi rufi an sanya k'ofofi a wasu d'akunan da yake filin babban ne part biyu ya yi yana gaya mini d'aya bangaran zai sanya Babarsu ne idan ya gyara mata sai na ce masa mu fara gyara na amarya tukkuna duk abinda ya kamata na ado da k'awata a gida a yi lissafi da ma'aikata daga nan zuwa ranar wata juma'ar a yi kokarin kammalawa domin ba ni son yarinyar ta yi dogon zama a gidansu.
Muka yanke magana a kan haka.
Hamusu na kira a lokacin na ce ya had'a masa lefe akwati shida a sanya manyan kaya daga kan atamfofi zuwa leces abinda ba mu da shi a shago a sayo a had'a a kawo mini na gani.
Ya ce mini za a yi kokarin hadawa kamar yadda na buk'ata.
Muna tare da Minal a falo wajan tara da minti goma na dare ina dokon shigowarsa yaran sune a kan gaba kafin su shigo shi da ita.
Minal ta buga tsalle a guje ta nufi bakin kofa suka rukunkume juna Hassana da Husaina suna cikin wasu 'yan kanti sabbi masu kyau sosai da wani karamin hijab a wuyansa daga inda nake zaune nake k'are musu kallo na ga sun sake yi mini tsayi ko dai don na kwana biyu ban gan su ba ne oho sun dai yi mini kyau k'warai Khalil na cikin shadda riga da wando da aiki a gaban rigar har da hula a kansa. Ita kuma tana cikin abaya baka mai jajayen dutsuna ta yafe mayafinta a wuyanta har da gilas baki a idonta da jar jaka da taka 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~lmi.
Na juyar da kaina cikin nutsuwa na amsa sallamar da ta yi suka 'karaso falon ita da yaran gabad'aya shi kuma ya haura sama ba tare da ya ce komai ba.
Ta zauna kan kujerar da take fuskantata fuskarta a sake kamar ba itace Hauwa mai k'uncin rai ba. Ta zare gilashin idonta tana duba na sosai ta ce."Amina ina yini mun same ku lafiya."
Na amsa a tak'aice ina nazartarta.
Sukairaju ya shigo ya tsaya daga bakin kofa akwati biyu ya ajiye madaidaita don basu da girma kayansu ne a ciki daga nan ya juya ya fita da sauri.
Hankalina ya d'auke wajan amsa gaisuwar da yaran suke jero mini Usai ta zo ta dafa cinyata tana ta kallona sai kuma ta dora kanta a saman cinyata. Na dora hannuna a kanta ina le'ken fuskarta. Hassana cikin narai-narai da ido ta ce."Mama ki ka ce za ki dawo gobe."
Ta fadi maganar muryarta tana rawa kamar za ta yi kuka lokacin na tuna da alkawarin bogi da na yi musu a lokacin ma tun ina maiduguri.
Na ri'ke hannunta amma ban ce mata komai na kira Khalil da hannu Ina fad'in ."Zo mu sake gaisawa."
Ya kuwa taho da sauri yana dariya yake fad'in. Mama mun yi kewarki fa sosai kullum muna labarinki shiyasa da muka zo muka ce mu dai nan a wajenki za mu kwana."
Na ce." Ni ma na yi kewar yarana sosai Khalil ina su Mairo baba Tabawa da Sultan."
Ya ce." Duk suna nan lafiya sun ce a gaisheku Sultan ba shi da lafiya yana zazzabin hak'ori Baba ya ce a bar shi a gida kada a zo da shi."
Na gyada kaina ina dubanta lokacin da take yin magana cikin yar dariya ." Aikam yara sun yi kewarki a gida Amina shi kansa ma gidan kewarki yake yi."
Murmushi na yi ina duban Minal da wayata a hannunta tana latsawa ko kusa da uwar ba ta je ba gefe guda kuma ina nazarin abinda yake so ya faru domin ga dukkanin alamu ba yaran ne kadai suka zo mini kwana ba har da ita tunda ga akwatin kayansu nan."
Na danne tare da furta." Kun ci abici a gidan Hajja ko kuwa na kawo muku."

littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Ita ta ba ni amsa duk da ba ita na tambaya ba na ji tana cewa." A alhmdullhi ai sai da muka ci abinci muka fito mun gode sosai."
Na yi shiru ban tanka mata ba ina ta sauraran labarin Mairo a bakin yaran da sa'kon gaisuwar da suka ce a gaya mini.
Wajan goma daidai na tashi na hau saman domin tunda ya hau bai sauko ba ga yara suna so su kwanta. Yadda tsarin gidan yake dama can babban falo ne da dakuna manya biyu a cikinsa toilet da kicin wanda yake d'auke da store wadatattu.
Saman kuwa dama can d'akuna biyu ne amma daya ne a gyare wanda yake mu'amula a cikinsa tun farkon tarewarta a gidan zaman mace daya ne babu takurawa yanzu kuma Khalil ya zama d'an saurayi ya d'an fara girma babu buk'atar a had'a shi da mata a d'aki daya tunda tun can abujan aka raba musu d'aki.
Yana zaune da jallabiya a jikinsa ya yi wanka yana waya shigowata bata hana shi cigaba da wayarsa ba amma kafatanin hankalinsa yana kaina har na zauna daga dan nesa da shi waya yake yi da Alhaji Sulaiman yana yi masa bayanin yadda al'amarin ya juya har aka d'aura auran da waninsa ya yi masa fatan alheri a yayin da yake ta amsawa da Amin Amin can kuma sai ya yi shiru yana sauraransa na ji yana fad'in." Anya kuwa Alhaji ba dai yanzu ba tukkuna wad'annan ma fama nake da su amma za mu cigaba da neman zabin Allah."
Daga haka suka yi sallama ya juyo yana kallona 'kuri! Na sake tamke fuskata tare da tariyo maganganun da ya gaya mini dazu amma bari mu ajiye wannan mas'alar a gefe kafin nan ina so na ji dalilin da ya sa ya kawo mini matarsa cikin gidana bayan da bakinsa na ji yana gaya mata babu waje a ina zai sauke ta. Ba ni buk'atar Hauwa gabad'aya a rayuwata bana tsammanin zan iya sake sakin jikina da ita domin bata daga cikin mutanan da Ubangiji ya ce idan sun tuba ku yafe musu Hauwa bana jin za ta yi taubatun nusu'a akan zamantakewa ta tsakani da Allah."

Ya dube ni yana fad'in." Hajja ta ce ta zo cikinmu gabad'aya tunda yaran sun dage anan wajanki za su kwana can kuma ita kadai za ta kasance, amma ni ma na fi buk'atar su zauna a can gidan Hajja saboda ba ni son fitina fa na gaji idan ba so kuke na mutu ba."
Na ce." Ai ita kanta Hajjan ta san gidan ya yi mana kad'an ni wallahi tallahi na gaji da wannan rashin adalci da son zuciya ba ni son had'a numfashina da matar nan domin zahirin k'iyayya ta nuna mini na bar mata can gidan na zo nan na zauna domin zuciyata ta samu nutsuwa ta sake biyo ni ko sai ta yi wa rayuwata illah tukkuna za a gane abinda nake nufi."
Ya 'bata ransa ainun yana duba tsabar idona ya ce." Rashin kunyar ta tashi daga kaina Amina ta yi tsalle ta tafi kan mahaifiyata kenan ko, gidan ki ko nawa da za ki yi mini iko da abinda nake da iko da shi, ki gaya mini gidanki ne ko nawa na ce?"
Ya fad'a cikin 'karaji har yana dukan hannun kujerar da yake zaune.
Duk da na tsorata daga ganin yadda ya burkice na dake sosai ban sarayar da mutuncina ba na ce." Gidanka ne ai dama ban ce gidana ba ne amma dai ni ce yanzu a cikinsa kuma na ce ba ni buk'atar zama da wata a cikinsa. Idan lallai sai ka zauna dani a irin hukuncin da na yankewa kaina na rayu ni kadai da yarana a waje daya babu wata bagidajiya da za ta d'aga mini hankali ko ta nemi halakar da rayuwata. Kuma kada ka sake ka yi mini k'azafi akan maganar da na fad'a domin ni ban ga ta inda na kausasa harshe akan mahaifiyarka ba."
Ya sake hasalowa yana fad'in." A ciki nake dake domin kin jima kina yi mini rashin kunya kala-kala saboda kin samu dama akaina ko kin lura ina sonki da yawa za ki samu damar taka ni yadda ranki yake so kin zo geji muddin ki ka ce za ki sanyo mahaifiyata cikin wannan rashin mutuncin naki wallahi ranki idan ya yi dubu sai ya 'baci."
Na sake aro jarumuta da jajurcewa domin dai duk wannan hargitsin da yake yi bai karya mini lagona ba ko na tsorata na furta ." Kada fa ka yi mini sharri akan abinda ban yi ba babu cin mutunci balle rashin kunyar da kake magana a tsakanina da Hajja wannan alkawari ne na daukarwa kaina."
Ya ce." Idan ba rashin kunya da rashin arziki ba mai yasa za ta bata da umarni ki ce ba daidai ba ne har kina fad'in ita kanta wannan ai wulakanci ne da nuna mutum bai isa ba."
Na girgiza kaina cikin ko'karin nuna masa ba haka nake nufi ba na ce." Idan wannan maganar dana furta akan Hajja ta hasala maka zuciya Allah Ya baka ha'kuri amma zan fita yanzu tunda da sauran dare a gidanmu zan kwana nan gidan Hauwa ne da yaranta kamar yadda wancen ma ya zama nata.
Na yun'kura na tashi a hankali yaran dake cikina suna naushin marata duk da ciwon da nake ji na yi azamar kama hanyar fita.
Ya cimma ni dalili da kyar nake iya cire 'kafa.
Ya tari gabana da b'acin rai a fuskarsa ya furta." Ba za ki bari mu huta ba ko Amina, ba ki duba nauyin da ki ka yi, kin ki ki bari mu fahimci juna har mu raini yaran dake cikinki kin dusashe mini farinciki da annashuwata kina nema ki dasa mini b'akinciki me na yi miki ne?"
Na daga kaina na dube shi a hankali na ce." Ka bar ni na huta ni ma?"
Ya yi shiru bai ce komai ba da akwai alamar sasaauci a fuskarsa. Ya rike hannuna daya na fizge tare da ratse shi zan wuce ya san janyo ni da sauri tare da sanya ni a jikinsa. Na sake cirewa rik'on karfi ya yi wa hannuna. Yana jana ina turjewa so yake mu je mu zauna a gefan gado.
Na ce." Ai babu buk'atar wani zama na samun maslaha da daidaito a tsakaninmu tunda har yanzu baka fi karfin gidanka ba. Zaman sulhu da samun mafita ba za a yi shi da ni ba a yanzu zaman 'yanci zan yi da kare kaina."
Ya ce." Na gaya miki tuntuni Hauwa ta gyara ta daina duk wasu abubuwa na rashin kyautawa kada ki manta da irin yadda na fifitaki a kanta na nuna miki kulawa da k'auna a kanta ki ka fitar da hannu ki ka tsinka mata mari a gabana. Na hana ta d'auka mataki ta kuma hanu. Wannan bai isheki ba Amina."
Na ce." Ai baka burge ni ba daka sani ka bari ta rama marinta ko kai ka rama mata tunda ka ji mata haushi. Ka daure mata gindi tunda baka musanta abinda ta fad'a ba a kaina kawai ka mayar da abin wasa. Mataki ma ban gama d'auka a kanta ba wallahi muddin ba ta fita daga rayuwata ba."
Ya rungumo kafada jikinsa yana dan rawa har yana gyara mini sar'kar wuyana ya ce." Ni ban d'auki maganganunta da muhimmanci ba saboda nasan wacece ke, nasan ta fadi haka ne domin ta 'bata miki rai da kishi irin naku na mata me yasa maganarta za ta dame ni tunda na fi kowa sanin da baiwar da Allah ya yi mini na rabauta dake giwar mata shige mu zauna mu yi magana wadda za ta kawo mana sasanci.......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700...VIA 0542382124.... BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*154*
Ganin yana neman wuce makad'i da rawa ya sanya na tankwa'be hannunsa ya sake mayarwa tare da tarairayoni jikinsa sosai na yi 'kokari wajan 'kin barin abinda yake yi mini ya yi tasiri a tare da ni muka zauna gefan gado a tare yana ta sauke wata irin ajiyar zuciya wadda na kasa tantance ko ta mecece. Raina a b'ace na zura masa ido domin sauraran abinda zai fad'a abinda na sake kud'irewa a raina shine ko sama da 'kasa za ta had'e ba zan zauna da Hauwa ba tunda ba tare a ka hallice mu ba. A wannan karon na shirya sosai koda Hajja za ta sanya bakinta ba ni tsammanin za ta sake samun wannan alfarmar.
Sai da ya daidaita kansa sosai ya furta." Za mu yi kwana biyu da Hauwa anan zuwa jibi zamu tafi tare da ita da yaran gabad'aya ba dai akan maganar raba gida kike magana." Ya fad'a yana kallona.
Na gyad'a kaina ba tare da na ce komai ba. Ya sake sauke ajiyar zuciya yana ce wa." Za a yi yadda ki ke so amma ya zama dole kema ki bi umarnina tunda kin san bai zai yiwu ki zauna anan ba mu muna can
kuma duk wasu d'abiu da ki ke yi a yanzu ki ajiye a gefe ba zai yuwu ki dinga juya ni ba Amina kin san dai ba ki isa ki kafa mini doka na bi ba ko?"
Ta'be bakina na yi tare da juyar da kaina gefe wai ban isa na kafa doka ya bi ba. Ita din yake bi ai a yanzu na tu'ke tunda bai san alheri ba. Dole ne aka ce na zauna da wata Allah Ya gama hore masa ta ko'ina idan ya'ki raba ma mazauni bai shirya kashe rikici ba.
Ya juyo da fuskata yana fad'in." Ki kalle ni mu yi magana domin fahimtar juna nake so mu yi ni dake saboda na gaji da wannan halin da ki ke yi mini ina ce akan an bani auran wannan yarinyar ne Hajara ki ka canza gabad'aya ni fa ba yaro ba ne giwa na baki shekaru sama da goma sha biyar duk yadda ki ka kai ga gogewa na fi ki kuma bai wai ina tsoronki ba ne."
Na dube shi sosai ina cewa." Ni dama na ce ka ji tsorona ne? Wallahi ka ji tsoron Allah a cikin dukkanin lamarinka ka dinga gaskiya yanzu ba ka ji kunyar duban idona ka dinga fad'a mini irin haka ba me yasa ka ke da mance alheri ."

Ya ce." Ni kin d'auke ni mak'aryaci kenan."
Can k'asa na ce." Iyi."
Ya sake sanya hannunsa ya juyo da fuskata yana ta'ba le'bena kafin ya furta." Ni ki ke yi wa Allah Ya isa Amina."
Na cire hannunsa ganin kamar yana so ya shagaltar da ni, na ce." Don Allah ni ka rabu da ni babu fa wani kalami da za ka yi mini na ji dad'i tunda ka rasa Hajara sai ka nemi wata ba yanzu na ji kana waya da abokinka ba ya baka kanwar amaryarsa sai ku yi anko ina ruwana."
Ya girgiza kansa yana cewa." Ko zan yi aure anan gaba sai da amincewarki ke za ki duba mini wadda ta dace."
Na kalle shi a sakarce wai shi dole sai ya yaudareni da kalaman bakinsa. Na ce." Ya

Please Login or Register in order to submit comment