Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wadataciyyar sallama a tsakaninmu.
Bayan tafiyarsa da kwanaki uku Hauwa ta dawo a gidan Hajja ta sauka na samu labari ne a wurin Hajiya Saratu a lokacin dana kira ta a waya da kuma sutturuna na can da aka kawo mini na kira Hajiya Saratu ne a waya domin na sake wanke kaina tunda ita ta fahimce ni.
A ranar kuma na kira shi duk da bai ne me ni ba, amma nasan yanzu ya huce daga fushin da yake yi tunanina ne ma ya rabu kashi biyu ban sani ba da Yusi ya koma ko kuma ya bar shi a gidan Hajja nasan dai da wahala ya bar shi a can din saboda makaranta kuma akwai sabo mai yawa a tsakaninsu zamansu a tare zasu debewa juna kewa.''
Wallahi ban zaci abin ya kai haka ba a ganina ban cancanci haka ba a wurinsa idan fa da adalci shima ya so kansa ne idan kullum zai dinga zuwa nan yana komawa yana da ikon yin haka tunda jirgi ne kawai bashi dashi amma yana da kudi kuma yana da alfarma a ko'ina,idan ya so duka karshen wata zai iya zuwa ya yi mana sati daya ya koma.
wasa wasa dai yau kwanaki goma kenan da komawarsa bai kira ni a waya ba kuma bai amsa kira na ba.
Abin ya fara damuna wannan ai kin gaskiya ne da gangan!

E mana son rai da gangan domin kowaye ya ji wannan batun ya san son zuciya ne. Sai kawai na rabu dashi dama sautari idan yana irin wannan fushin na bashi ha'kuri ya ki ji share shi nake yi domin daga zarar ya fahimci damuwata akan abinda yake yi sai ya sake tsanantawa daga na watsar dashi sai kuma ya fara neman shiri.
Sabgarsa na fita saboda na tabbatar da cewa ban yi abinda ya kai ayi mini irin wannan wulakancin ba.
Sati guda ban neme shi ba ranar litinin da misalin uku da rabi na rana ya kira waya lokacin ma tana hannun Yusura tana game ta kawo mini.
Babu damuwar komai na gaishe shi cikin nutsuwa domin idan na nuna masa na ji ciwon abinda ya yi mini zai ji dad'i tunda haka yake so ashe daliline ya sanya shi kirana ba wai ya kira ni domin ya ji yaya nake ba. Kanin mahaifin Hauwa ne ya rasu shine za a yi ayari har da Hajja gobe zuwa can bauchi shine yake ba ni umarinin na shirya gobe da wuri direban gidan Hajja zai zo ya d'auke ni mu tafi tare tunda ni nan bai ajiye mini direba ba sai dai gidan cike yake da masu tsaro.
Jin gaisuwar mutawa ce ya sanya ban yi jayayya ba na ce masa to kawai bai kuma jirayi komai daga gare ni ba ya datse wayarsa cikin raina na ce za ka yi ka gama.
Ina zaune Ina zullumi yadda zan shiga cikin dangin Hauwa da wane irin ido zan dube su domin dai Hauwa ce tasu ba ni ba, bai zama lallai su fahimci hakkina ba tunda itace 'yar uwarsu.
Idan kuma na ce ba zan je ba zai iya zama gagarimin lefi ta yadda za a kama ni da hujja a ce ni ce ba ni son zaman lafiya da Hauwa.
A daran na kira anti Yagana na gaya mata ta yi mini fatan alheri na sanar da Babarmu ma shima dai addu'ar zuwa lafiya da dawowa lafiya ya yi mana

Littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Da safe da wuri muka shirya don ba mu kai ga karyawa ba ma direban ya iso haka muka tafi da abin karin can gidan hajjan idan mun je sai mu karya kafin mu tafi.
Ban samu wata tar'ba muhimmiya daga wurin Hajja ba, babu wannan k'aunar da nake ganinta a cikin idonta, babu dai k'yama kuma babu sakin fuska muka gaisa kadaran kadahan. B'angaran Hajiya Saratu babu wata matsala sai ma rashin jin dadin abinda Hajja ta yi ya bayyana a fuskarta. Ban nuna damuwata a sarari ba na danneta dama na riga nasan duk daran dadewa inna Uwani sai ta farraka tsakanina da Hajja tunda a zahiri ta fito ta nuna kishin hakan, amma ni a ganina abinda na yi bai kai ace kowa ya kasa yi mini uzuri ba sai dama idan da wata a kasa. Na ji dad'i da ban ajiye ba balle na yi fargabar wata matsala ta kutsu ta rabuwa na yi danasani zan kuma kiyaye faruwar hakan tunda dama da soyayyar Hajja nake gadara an shiga tsakani.
Koda Hauwa ta fito a kintse cikin shiri har da yar k'aramar akwati ni kam ban yi guzurin komai ba sai a lokacin ma na tuna za mu iya kwana fa tunda gidansu ne bai zai yiwu ace mu je mu dawo a ranar ba.
Babu yabo babu fallasa muka gaisa tana zauna kujerar da Hajja ta tashi tana duba wayarta na dinga nazarinta a fakaice ta kara haske ainun abinka dama da farar fata ya yi bul-bul irin na mace mai yaron ciki duk wannan ramar babu ita kirjinta ya ciko sosai kamar wadda take rayuwa a ketare. Na d'an janye idona a hankali na sauke ajiyar zuciya Ina nazarin yadda za ta kaya domin dai ni ba zan ce direba ya mayar da ni domin d'auko kaya ba idan kwanan ya zama dole na nemi shop na sayi koda abaya ce.
Zaman mota ya sanya kafafun Hajja yin tsami da kyar ta fito daga motar tana kukan kafafunta na yi mata zugi.
Ni na taimaka mata muka shiga gidan Hajiya Saratu da ita Hauwan suna bayanmu Yusura kuma tana gefena ri'ke da jakata a hannunta.
To an ce duk inda mai kudi yake yana da wani irin kwarjini da haiba abinda ya faru kenan saukarmu a gidan rasuwar ke da wuya maza daga waje suka dinga shigowa suna gaishe da Hajja ni kaina wasu daga cikin dangin Hauwa sun mutuntani gaisuwa ta mutunci muka dinga yi da su. wad'anda na fahimci kuma ban ishe su kallo ba ni ma bana kallonsu amma na yi kokarin samun inna Uwani a gefe na gaisheta domin sai satar kallona take yi kuma ba ta ce mini komai ba. Ta amsa babu yabo babu fallasa sai na ja gefe guda na kame kaina Yusura na gefena don ma Allah Ya yi mini kwarjini da haiba da ban san abinda zai faru ba. Akwai wasu dana lura suna ta shige da fice a d'akin da aka sauke mu kuma na fahimci sa'anin Hauwa ne irin 'yan uwan nan da aka tashi tare daya dai daga cikinsu da ta gaza ha'kuri ta dube ni da dan murmushi irin na munafurci sai ta kalli Hauwa dake kwance lakadan tana lasar lemon tsami saboda yawun da yake cika mata baki tana tambayarta wai Yusura 'yata ce dan an ce dama ina da yara biyu.
Sai ta bata amsa da cewa itama bata sani ba.
Hajiya Saratu da ta fahimci kamar da cin fuska ta yi tambayar ta ce." Sadiya idan 'yarta sai me, ina ce kema kina da 'yan matan yaran nan don Allah ku dinga yin shiru dangane da abinda bai shafeku ba."
Ta na dariya ta ce." Anti Saratu daga tambaya sai a yi mini fassara ayi ha'kuri to."
Ta d'auki wani fulas da yake cike da funkaso ta fice daga dakin.
Hajja ta dan dube ni a nutse ta ce." Wai ni Amina yarinyar wacece ne wannan?"
Na ce." Yarinyar Sahura ce Hajja ai ta jima a hannuna tun tana kan'kanuwa."
Ta ce." Ayya, ai shi Yusi ya'ki zaman nan fafur da Baban nasa zai tafi har da kuka sai ya bishi Shima ya daure masa gindi wai saboda makaranta.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*53*
Murmushi na yi a hankali na ce." Ni kaina Hajja na manta yaushe rabon da naga Yusi ko gidan da na tare fa bai zo ba."
Ta ce." Ai duk lefinku ne kun yi abu a 'kunshe waye zai san halin da kuke ciki, ina sane ni ma ban zo ba, da ya yi mini jagora na duba Gwaggo na yi dawowata gida.."
Da mamaki a tare da ni na ce." Hajja Yusi ne ya yi mini jagora har gidan Gwaggo."
'"Kwarai kuwa shi da direbana kafin su tafi shima baban nasa sai labari ya ji mun je mun dawo."
Na yi kasa da kaina cikin jin nauyi na ce." Ki yi hakuri Hajja hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allahu rabbi.
Shiru ta yi ba tace komai ba. Hajiya Saratu kuwa sai murmushi take yi ta ji dadin yadda Hajjan ta saki fuska har muna hira wannan yana nuna mini ko da asirin har yanzu akwai sauran kaunta a cikin zuciyarta.

Sai bayan ishai tukkuna muka tafi gidan inna Uwani dalili gidan da akayi rasuwar a cike yake da jama'a kasancewar gobe ne za a yi addu'ar sadakar uku. Babu nisa a tsakanin gidan mutuwar da gidansu Hauwa gabad'aya muka nufi can din har da ita.
Hajja ta ce gobe da wuri idan an yi addu'a sai mu kama hanya mu tafi gida sosai na ji dadin hakan don haka inna Uwani tana shigowa tana gaya mata abinda ta yanke ta nuna rashin jin dadinta akan hakan har dai ta gaza yin shiru tana gaya mata ita me yasa idan ta je mata take wata da watanni ina lefin ma mu yi sati daya sai mu tafi.
Jin abinda ta ce ya sanya mini fargaba don gaskiya bana so ko kwana daya mu kara a garin bayan wanda Hajjan ta yanke.
Yanayin yadda inna Uwani ta nuna b'acin ranta ya sanya hajjan ta ce idan an yi addu'ar gobe jibi sai mu tafi lokacin dai duk wanda ya kamata a gaisa dashi an gaisa.
Dukda hakan dai inna uwani ba ta ji dad'i ba ta so a ce mun zauna mun yi sati guda kamar yadda ta buk'ata.
Jin shawarar da suka yanke ya sanya na fara tunanin nemawa kaina mafita dole gobe ma mu shiga cikin mutane kuma ba zai yiwu na sake komawa da kayan jikina ba ba don komai ba sai don na siyawa kaina mutunci.
Na gayawa hajiya Saratu abinda yake da akwai da buk'atar son ta yi mini jagora mu fita a daran tunda da sauran lokaci dare bai yi ba.
Hajja ta kama fad'a sosai irin wanda bata taba yi mini ba gabad'aya taki kar'bar uzurina tana fad'in ai nasan ba yadda za a yi mu yi tafiya irin wannan mu je mu dawo a ranar na ce mata mantawa na yi sai da muka fito daga gidan tukkuna Allah ya tunasar da ni. Ina jin inna Uwani da tunda muke maganar ba ta ce komai sai da ta ji hajjan tana yi mini fada tukkuna ta sanyo bakinta wai ko dai ba na son zuwa aka tursasani. Takaici da b'acin rai bai barni na sake wata magana ba, na yi shiru kawai da bakina Ina mamakin yadda yanzu gabad'aya Hajja ta daina fahimtata ta kuma daina tausaya mini.
Haka dai muka fita ni da Hajiya Saratu ran mu duka a b'ace domin ita kad'ai ce ta dubi uzurina ta kuma fahimce ni ita Hauwa ma bata iya cewa komai ba har aka yi maganar aka gama kuma tana kwance a wajan amma uffan ba ta ce ba.
Direban da muka zo dashi ne ya fita da mu. Garin ba bak'on Hajiya Saratu ba ne ta san wurare da yawa don haka ma ba mu yi nisa da hawa titi ba muka ci karo da wani shop a d'aya hannun na cewa magaji direba ya shiga damu ciki.
Dogwayen riguna na sayo mana ni da Yusura na had'o da hijabai biyu da takalmi flat ko rabin awa ba mu yi ba muka koma gidan Hajiya Saratu tana kara ta tausata don gaskiya yanayinta gabad'aya ya nuna takaicin abinda aka yi mini tana gaya mini ita kanta ta rasa abinda yake damun Hajja a tsukin nan don ta fahimci kamar tana shakkar Inna Uwani dalilin ma da ya sanya ta fara dora zarginta akanta
Na nuna mata babu komai kawai amma can kasan zuciyata abin yayi mini ciwo kawai da gaske, zan yi kokarin ganin na taushi zuciyata har mu tafi wani abu bai faru ta b'angarena ba.
Mussaman aka kunna genareto saboda mu. Gidansu Hauwa sai na ce da kadan ya dara namu gidan kwaryar sama ce take dukan ta kasa. Gidan kuma na had'aka ne mutum uku ne amma kowa da nasa bangaran wanda ya rasu ne kawai gidansa a waje. Mahaifinsu ya rasu kuma shine babbansu sai dai gabad'ayansu 'yan boko ne babu wani dan kasuwa a ciki suna ci da biro da takarda rufin asiri na abinci ne kawai kuma a cikin sa'aninta dai Ina ganin ita kad'ai ce take auran mawadaci sauran duk sai a hankali suna kula da kansu ne dalilin aikin gwamnati da suke yi sai dai yadda na lura suna da hadin kai da k'aunar junansu ba kamar na mu gidan ba.
Wajan goma da rabi har mun kwanta ni da Hajiya Saratu da Yusura muna d'aki daya ita Hajja da 'yar uwarta suna tare Hauwa kuwa ba na ce ga inda take ba tunda ko lokacin da muka dawo ban ganta a falon ba. Muna d'an ta'ba hira kad'an kad'an Hauwa ta shigo da wayarta a hannunta tana fad'in." Har kun kwanta ne?"
A tsanake na dubeta na ce." E wallahi."
Sai ta miko mini waya tana cewa." Maigidanki ne yake so ya yi magana."
Na yi sakare Ina kallonta yana so ya yi magana da ni bashi da lambata ne?" Abinda zuciyata take tambayata kenan.
Ta sake maimaita maganarta tana cewa'' Wata'kila ya kira layinki bata shiga ba kin san matsalar network, ni dai yanzu ya kira ni ya ce na hada shi dake."
Ban ce komai ba na amshi wayar sai ta juya ta fita ni da Hajiya Saratu muka bi ta da kallo. Ita dai girgiza kanta ta yi a hankali ta koma ta kwanta ni kuwa na tashi zaune da wayar a hannuna ina tsammanin kiran nasa.
Minti biyar da fitarta ya kira. Na daga a nutse na ji yana cewa." Kin kai mata wayar?"
"Eh ta kawo mini barka da dare?"
Na fad'a tare da ko'karin danne damuwata."
Ya d'an diririce ban san dalili ba can kuma na ji ya amsa yana cewa." Dazu na kira Hauwa a waya ta ce mini kun fita ke da Hajiya Saratu ina kuka je?"
Babu mamaki a tare da ni saboda nasan zai iya yin abinda yafi haka na furta." Ta yi mini rakiya ne na sayo abu a shop saboda ban yi guzurin kaya ba don ban yi zaton zamu kwana ba."
Ajiyar zuciyarsa na ji kafin ya ce." Kada ki kara shiga wani shago da zummar sayan kaya Amina hakan yana nufin abubuwa da yawa, kin san dai ba zai yiwu ace ku je bauchi ko dawo a ranar daya ba, me yasa ba ki bawa maganata muhimmanci ba a lokacin dana kira ki na gaya miki ki shirya ki bi su."
Na hasala da jin yadda yake ko'karin d'ora mini lefi shekkenan ni ba zan yi kuskure ba, kuma ai da ya gaya mini bai ce mini na hada kayana kwana za mu yi ba."
Na ce." Shine me? ai lefin ba na kowa ba ne naka ne ko ka gaya mini na hada kaya zamu kwana? da ka kira ni ka sanar da ni na bijire maka ne, na ce to shikkenan ban yi maka jayayya ba saboda kuskure karami sai kuma a gaza fahimtata."
"Ban kira ki don ki gaya mini magana ba Amina, na ce kada ki sake shiga shago ki ce za ki sayi abu ina da dalilina."
Shiru na yi ban ce masa komai ba sakamakon yadda na ga Hajiya Saratu ta tashi zaune tana kallona da yanayi na damuwa.
Sai kawai na datse kiran ban tsaya na saurari sauran maganarsa ba, wane irin dalili ne dashi wanda ya wuce na tozarci shikkenan don ina a matsayin na matarsa ba zan shiga shago na sayi abu ba ni din wacece. Itama Hauwa ta so faruwar hakan hakan ne amma menene na gaya masa ga inda muka tafi bai kira ni a waya don ya nuna ya ji dadin karar da na yi musu ba ya kira ni yana tuhumata akan wane dalili.
Ban iya daure kukan da yake ta yun'kuro mini ba na fara share hawayen da yake gudana a kumatuna Yusura ta yi lamo akan katifa tana kallona kamar ta taya ni kuka.

Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Hajiya Saratu ta dafa kafadata tana rarrashina a yanzu ita kadai ce take nuna damuwarta a kaina Hajja kam sai a hankali 'yar uwarta ta samu galaba akanta.
Hauwa ta shigo domin ta kar'bi wayarta ta same ni Ina kuka muna tattauna abinda yake faruwa da Hajiya Saratu sai ta yi kasa'ke tana kallonmu a lokacin Hajiya Saratu ta rufe ta da fad'a tana cewa." Ki ji tsoron Allah Hauwa yadda ki ke ko'karin gyara auranki to na hore ki ki gyara na 'yar uwarki wadda ki ka zo ki ka sameta da mijinta, bayan abinda ku ke yi na karkashin kasa har sai kin yi mata bita da kulli kin san fa duk abinda ya faru me zai sanya don ya kira ki a waya sai ki gaya masa shikkenan mutum baya kuskure..
Babu wata damuwa a tare da ita ta ce." Sai na yi karya kenan ko anti Saratu na ce masa gata nan a kusa da ni ko me? Ya tambayeni ina take na ce masa kun fita tare zata sayo kaya ko ba haka na ji kuna maganar ba. A lokacin da na yi masa karya ya ce na bashi ita kuma na yi yaya kenan, kuma na ji kina cewa muna yin abu ta k'arkashin kasa, ita din da kike shedarta kina da tabbacin ba ta yi ne? ai alhaki koikoyone wata'kila abinda ta yi ne ya waiwaiyo mata, ni wannan ai sai dai na kalleta kawai 'kiri-'kiri tana nuna mini 'kyama ta kuma fito da hassada da kishinta muraran a kaina ciki dai da izinin Allah sai na haifehe ko ana so ko ba a so gwara ma mutum ya ha'kura ya barwa Allah ikonsa

Maganganun Hauwa sun yi mini nuni da cewa tabbas ta ji ciwon abinda na yi wanda har hakan ya sanya suka hade mini kai ita da mijinta. Amma kuma sun yi tsauri ga hajiya Saratu wata'kila ko ta manta da cewa ita din yayar mijinta ce fa ba kanwarsa ba, a tunanina ko kanwarsa girma da shekarunta bai kai ace ta tsaya a kanta da fitsara.
Ni idan ta yi mini kishiyarta ce ba abin damuwa ba ne tunda da kishi a tsakaninmu amma ni da ban had'a jini dasu ba ba zan ta'ba yi wa mai shekaru irin na Hajiya Saratu rashin kunya ba.

Abinda ya haddasa musu rikici kenan a tsakaninsu sai ya zamana ni na shiga tsakiya kuma a ta dalilina komai ya faru Hajiya Saratu fadi take yi "Ba za ta je ta zauna miki ba din, ko ita ce ta yi miki cikin, ai ni Amina ta yi mini daidai duk abinda za ku ce akanta kun dade baku fad'a shegiya mara kunya ki dubi tsabar idona ki dinga nema ki zage ni saboda kin samu kanki ko, idan kin manta bari na tuna miki ni Yaya nake ga Tajo ba k'anwa ba balle ki ce za ki gaya mini magana son ranki Ubanki zan ci domin ba na ciki da iskancinki shashasha mara wayo kawai, ai iliminki bai amfana miki komai ba sai rashin dubara......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*55*
Sai zamanta ya rage mini kad'aici mussaman idan Yusura ta tafi islamiyyar dana sanyata anan bakin titi domin ta cigaba da dora haddarta kasancewar dama ta yi saukar al'kur'ani wattanin shida da suka wuce wanda ya yi daidai da lokacin da ta zana jarrabawar fita daga secondary da kaina na yi tunanin sanyata a makarantar saboda zaman a haka bashi da amfani zata sake d'aukar darrusa masu muhimmanci kafin lokacin auranta tunda makarantar ba wai al'kur'ani kawai suke koyarwa ba har da sauran littafain na addini za ta kara sanin tsarki da hukunce-hukuncensu.

Ranar da Sahura ta zo yini muka yi muna magana daya har dai na gaji na yi mata shiru domin kuwa ba zan ta'ba yin abinda take so ba don ban ga abinda na yi ba ai na d'auka sai mutum ya yi lefi tukkuna zai ta bibiyar wanda ya yi wa domin ya yafe masa.
Ita kanta tasan maganata akan daidai take ba zai yiwu ace sun mori juna sun jiyar da kansu dadi ciki ya samu ace ni kuma dake gefe na je na yi musu wahala ba, ai ba yarinya ba ce balle ace kuma ita din menene bata sani ba tunda malamar asibiti ce duk wanda zai zage ni ya dad'e bai yi ba abu ne mai mutukar wahala wata mace ta aminta da hakan.
Ita Sahura wai kada mutane su yi mini wata fassara ko a juya maganar ace ina yi mata b'akinciki don ta samu cikin haihuwa wanda ni kuma wallahi babu wannan a cikin raina komawa ne kawai ba zan yi ba, ni ma a lokacin da na samu nawa haka nayi ta fama dalilin ma da ya sanya kenan nake d'agawa Hadiza kafa saboda wahalar da ta yi mini.

Wai lallai sai na kira shi na bashi ha'kuri na gaya mata ha'kuri kuma na nawa lamarin da ba yau akayi shi ba an kusa wata biyu to me zai sanya na damu kaina. Ina nan dai da kudirina wata uku na cika idan bai zo ba to kuwa zan san inda dare ya yi mini ai ko addini wannan abin da yayi ba daidai ba ne kuma daf yake da ya lalata auransa.
Duk hujjar da ta kawo mini zan soke ta dole sai ta ha'kura ta kyaleni ta tafi da b'acin rai dalilin da na ki na yi abinda take so.
Babanmu da Baba Sule suka zo ranar wata jumaa bayan an sakko daga massalaci na ji dadin zuwansu sosai na shirya musu abinci mai kyau suka ci suka koshi suna ta yaba gidan da fatan alheri na dinga nazarin Baba Sule gabad'aya duk ya susuce tufafin ma dake jikinsa kamar ba wankakke ba takalmi irin soso shine a kafarsa. Babanmu ne kawai cikin sutturar arziki tsaf dashi, sai na ji kunyar hakan a cikin zuciyata ko babu komai Baba Sule uba ne duk lalacewsa kuwa, duk ranar da babu ran Babanmu dole shi din zamu k'alla a matsayin Ubanmu kuma idan da kara duk wata taguwa da zan dinkawa Babanmu shima ya kai ace na had'a dashi ganin da na yi masa babu kintsi ya sanya jikina yin sanyi domin yanayinsa ya nuna yana buk'atar agaji ilai kuwa ashe damuwa ce mai yawa a tattare dashi dalili ubangidan nasa Alhaji Muntari ya karye jinya ta cinye masa kudi ga tarin bashin mutane dake kansa komai ya karye masa wasu sun ha'kura wasu kuma sun ce sai an biya su, wannan dalilin ya sanya gidan da yake ciki aka sanya shi a kasuwa domin biyan bashin da yake kansa. Yadda Baba Sule yake mini bayani lamarin ya bani tsoro mutuka da gaske yanzu uwargidansa anti Maimuna ita kadai ce ke jinyarsa anti Jamila ta gudu garinsu Bichi bayan ta turasashi ya saketa

Please Login or Register in order to submit comment