Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutane suna daukarwar kansu zunubi a duk lokacin da suke munana zato akan mutum alhalin ba su da sheda kawai zargi suke yi da k'age. Sai na tuna irin maganganun da Sahura ta dinga fad'i a kanta a lokacin auransu da maigidan ya zama dole kuwa Sahura ta yi nemi gafarar Allah domin kuwa ta yanke hukunci akan abinda ba ta ta'ba ga ni ba.

To walima ta kyau sosai, kuma ta samu halartar manyar mutane malamai da ma'aikatan gwamnati har ma da 'yan siyasa. Sahura ta samu zuwa itama yan gidanmu kuwa Babanmu ya samu halarta tare da Baba Sule sai anti Sakina da Fati. Anti Yagana da Yafalmata sun zo Baban Saude kuma a lokacin baya gari sai da ya kira ni a waya ya yi mini barka ya kuma kira maigidan shima ya yi masa barka. Hamusu ma ba a bar shi a baya ba ya zo shi kadai Amma domin da ya gaya mini za su zo tare da Gwaggo na ce masa a a saboda tafiyar mota ce Kuma bata da lafiya sosai na yi alkawarin idan na yi arba'in da kaina zan kai mata yaran ta sanya musu albarka.

An yi hidima sosai yara sun samu alheri irin wanda ba zai misaltuba hotonsu kuwa yana ta yawo a kafafen sadarwa tare da yayansu Khalil da ya yi wayo har yana gudu da kafafunshi.


A daran ranar gajiya ta kayar da ni, ana yin sallar magriba da kad'an baccin gajiya ya kwashe ni. Maganarsa ce ta tashe ni na bude ido Ina kallonsa yana tsaye sai kuma ya zauna a gefana na tashi zaune ina d'an hade jikina tare da d'an matsawa. A tak'aice na ce." Ina yini." Ya amsa cikin kulawa yana ta kallona har na tsargu. Na ce." Wani abu ne ya faru?"
Ya girgiza kansa a tsanake ya furta." Na gode mini giwar gidana."
Murmushi na yi wanda babu nisha'di a cikinsa na ce." Godiyar ta mecece?"
Ya fito da wayarsa hotonan yaran yake kallo yana murmushi kafin ya nuna mini na kalla ban ce komai ba. Sai na ji ya ce." Kin biya ni Amina, na kuma yafe miki abinda ki ka yi mini abaya." Ya nisa kafin fuskarsa ta sake yalwata da annashuwa ya furta." Da ki ka tashi ba ni yara sai ki ka ba ni biyu kuma masu kama da Samira Amina na gode, na gode wallahi idan na kalli yaran nan ina jin wani irin farinciki mara misaltuwa."

Don Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Sosai na iya danne tsaki da harshe da gand'ar bakina ke ko'karin furzarawa. Na ce." Na farko dai ba ni za ka yi wa godiya ba Allah za ka godewa domin shine ya baka ba Amina ba. To ai yanzu ka fadi dalilin da ya sanya ka dimaucewa akan yaran bawai a karan kanka ba ne, a a saboda suna kama da wata can daban. Hakan bai dame ni ba dama hausawa sun ce kyan d'a ya gaji ubansa, ka daina gode mini ka godewa Allah ko ka je ka tashi Samiran daga kabarinta ka ce kana yi mata godiya dalili yaranka sun yi kama da ita." Tunda na fara maganar ban tsahirta ba sai da na dire tukkuna tsakin da nake ta dankwafewa sai da na furzar dashi domin idan bai fita ba akwai matsala, na koma na kwanta abina.
Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da takaici kafin ya ce.'' Yanzu ina Samiran take Amina?"
Na ce." Oho!
Sai ya gyad'a kansa ya tashi yana fad'in." Ni ba zan yi rigima dake ba domin na gane so kike ki tsinka ni a cikin mutane don haka ki huta lafiya." Ya juya da niyyar fita. Na kuwa bi bayansa da harara ban so ya kyale ni ba a lokacin na so ya tanka na amayar da b'acin ran da ya guma mini ahe da biyu yake ta abubuwa akan yaran saboda suna kama da inna Uwani da kuma 'yarta. Hawaye suka zubo mini na haifi yaran na ci wuya kuwa ta laulayi da zafin haihuwa amma ko yatsuna babu wadda ta d'auko Allah na tuba ka yafe mini.

Gida ya watse ya rage mu kad'ai. Ni da Hauwa muka cigaba da rainon yaran a wasu lukutan kuma Hajiya Maryam tana aikowa a d'aukar mata su, har su d'an jima a wajenta kafin su dawo.
Kwanana arba'in da takwas na shirya zuwa kano. Amma ina jimanta yadda zan yi dawaniyar yaran ni kadai dama burina idan na isa na samu Baba Tabawa mu yi magana idan ta amince mu tafi tare domin zamanta a tare da ni zai taimaka kwarai tunda kaf gidajensa daga na Legos din har na abujan babu mai aiki mace duk maza ne. Hajiya Maryam ce kawai naga tana da masu aiki dattijuwa mai suna Taburni Mairo kuma itace take yin dawaniya da yaran idan an akaisu can wajenta.
Ya ce Hauwa ta shirya sai mu tafi tare. Sosai na ji dadin hakan kuwa ban yi nauyin baki ba na yi masa godiya sosai ya ce kwana hud'u kawai ya ba mu dama za mu yi mu dawo. Kwanakin sun yi kadan amma ban iya gaya masa ba saboda Ina gudun ya ce ya fasa ma gabad'aya tunda har yanzu yana jin haushin abinda na yi masa sharewa kawai ya yi saboda yasan idan ya ce zai rama sai mun yi dan karamin ya'ki a gidan. Ni kuma fahimtar a kusa yake ya sanya nake ta lallabawa kada ya ce ba zan je ba.

***
Alhamdulillahi lafiya lau muka sauka a kano. Gidana na sharad'a muka sauka inda muka iske shi tsaf Baba Tabawa da Yusura sun gyara ko'ina har an yi mana abinci. Na yi mamaki kwarai da gaske nasan wannan aikin ba na kowa ba ne sai Sahura domin mun yi waya da ita ana i gobe tafiyar har ta na yi mini tambayoyi ashe abinda ta shirya kenan. Hidimar tace yin cefane mai kyau ta kuma sanya a yi mana abinci mai rai da lafiya. Cikin zuciyata na sake kud'ire wani alheri da ya jima a cikin zuciyata.
Da daddare Ayuba ya shigo mana da kayan abinci ya kai a store bisa umarnin maigidan ne ya tsaya muka gaisa sosai kafin ya juya ya fita.
Ko da na gayawa Baba Tabawa kudirina ba ta yi jayayya ba ta ce ta amince za ta bi ni duk inda zan je, yadda na nuna mata tausayi da kulawa a lokacin da take neman d'auki yanzu ne daidai lokacin da za ta biya ni. Ina dariya na ce mata ai ni don Allah na yi mata ba don ta biya ni ba. Daga ranar kuwa ta shiga hidima da yaran bakid'aya.
To duk inda ya kamata na je a tsakankanin kwanakin da ya ba ni mun je ne tare da Hauwa domin duk inda na ajiye kafata itama nan take ajiye tata. Baba Tabawa na goye da Hassana ni ina goye da Usaina ita kuma Hauwa tana ri'ke da Khalil a hannunta.
Ayuba ne ke jan mu a mota rana ta farko a gidan Gwaggo na yini sai yamma muka yi mata sallama muka nufi gidanmu anan muka yi magariba. Sannan muka nufi gidansu Sahura dake kusa damu muka gaisa sosai da mamansu ta d'auki yara ta sanya musu albarka.

Washe gari a gidan Hamusu muka yini amarya ta zama 'yar gari Hamusu kuwa ya rasa Ina zai tsoma ransa ya kai ya kawo ya siyo wannan ya ajiye ya siyo wannan ya ajiye bayan uban girkin da ya sanya aka yi mana. Sai da na ga abin ya yi yawa tukkuna na yi masa magana sannan fa ya dan samu nutsuwa.
Dubu ashirin na bawa amaryarsa na ce ta sayi janbaki ta kar'ba tana godiya ta rako mu har bakin gate.
Da muka fito tare da shi nake tambayarsa ya ake ciki da karatun Turmizi tunda shine ya shige gaba wajan kai shi makaranta kamar yadda maigidanmu ya yi alkawari nan yake ba ni tabbacin alhamdulillahi an samu cigaba kwarai da gaske domin hankalin yaron ya fara dawowa jikinsa domin lokacin da aka kai shi makarantar ma baya hayyacinsa dalilin irin shaye shayen da ya fara yi ya hadu da wad'anda suka fi shi wayo suka bashi kwayoyi har hankalinsa ya gushe garkuwar jikinsa ta raunana. A Tasha aka je aka d'auko shi yana zagari da kai kawo tare da sururai. Ya ce ko wancan watan da ya je dubasu ya same shi garau kuma ya kama karatu ka'in da na'in domin malaman a tsaye suke a kansa kuma makarantar cike take da tsaro babu ta inda yaro zai haura ya gudu.
Kamalu kuwa farkon watan da zamu shiga zasu sallameshi da izinin Allah dama kuma shi mun gama magana dashi zai zauna a hannunsa domin taimaka masa da cigaba da gudanar da harkokin da muke yi na kasuwanci.

Rana ta uku kuwa da wuri muka fita saboda gida biyu nake so mu je, gidan Sahura da gidan Alhaji Muntari can muka fara zuwa saboda nasan idan gidan Sahura muka je da farko bai zama lallai ta bari mu fito da wuri ba.
Alhamdulillahi na ji dadin ganin yadda anti Maimuna ta samu nutsuwa ta kafa sana'a kala uku tana sayar da itace manyan d'auri sannan ga buhuhunan gawayi anan a jibge kusa da itacen sai manja da man kulli da take sayarwa galan-galan. Lokacin da muke je duka yaran suna makaranta tunda da safe ne. Na tambayeta Salima ta ce itama ta samu koyarwa a wata nursery dake bakin titi gaskiya ne a lokacin da Babansu yake raye ya yi kokarin sanya su a makaranta da wannan yarinyar ta tsira gashi har wasu suna amfana da iliminta kuma tana samun kwabo da dari.
Na tambayeta Jamila ta ce mini ta ji dai kwanaki an ce ta yi aure amma kuma tana zaune aka zo aka gaya mata wai an ganta a wani hausa film da ta yi bincike sai ta tabbatar da itace din auran ne ya mutu ta shiga wasan hausa.
Sai abin ya ba ni dariya da mamaki cikin zuciyata na ce to Allah Ya kyauta.

**
Yini zur muka yi a gidan Sahura ta dinga yi mana soye-soye har da su wainar fulawa. Ta soya mama dubalan cikin bokiti wai mu tafi dashi. Da daddare kuma ta hana mu tafiya sai da gama awara nan ma ta cika mana fulas wai idan muje gida sai mu ci a madadin abincin dare. Sahura kenan sarakan kirki da kyauta......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*78*
Washe gari ranar da za mu tafi kenan da wuri ya yi waya ya ce sha biyu ta yi mana a filin jirgi domin ya gama yi ma shiri, dama na gaya masa tare muke da Baba Tabawa ya ce babu damuwa, don haka da wurwuri muka shirya na ce Ayuba ya kai ni gidan Baba Sule domin shi kad'ai ne ban je na gaishe ba, ita kanta Hadiza na so na kai mata ziyara amma lokaci bai ba da damar hakan ba, sai da na bawa Ummansu kudi na ce a yi mata siyayya a kai mata.
A gurguje muka gaisa da Baba Sule da iyalinsa na yi musu alheri daidai Gwaggwo sannan muka nufi gidan Hajja wanda daga can din sai kuma mu wuce airport.
Hajja bakinta kamar gonar audiga ganinmu a tare kanmu a had'e sannan ga 'yan jikokinta da take ta burin Allah ya nuna mata su.
Ita kyautarta dama ta turarece domin idan ta je saudiya su take sayowa da dayawa duk wanda ya ziyarceta ta bashi, ta had'o mana da yawa na jiki dana wuta tana ta yi mana addu'a da fatan alheri cikin tsananin farinciki mara misaltuwa.

Ganin da sauran lokaci da muka fito daga gidan Hajja na ce da Hauwa mu je gidan Hajiya Saratu don ni sai na ce zuwana gidanta d'aya tunda nake tunda bata fiye sabga ba yaranta duka biyu maza ne kuma babban yana can Egypt yana aiki da matarsa da yaransa. Mai bin sa kuma yana chana yana aikin koyarwa a wata makaranta, da yake wanda take aure dan boko ne sosai.
Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba yanayinta ya nuna dai kamar ba ta son zuwa. Nan na fahimci cewa har yanzu akwai rashin jituwa a tsakaninsu tun daga lokacin da suka samu sa'bani akaina basu daidaita ba. Zaman amana muke yi a yanzu dole a tsakaninmu duk wanda ya hangi kuskure daga b'angaran d'an uwansa idan har da amana bai kyautu ace ya yi shiru ba mussaman idan aka yi duba da cewa ta dalilina suka samu matsala gashi zumunci ne mai karfi a tsakaninsu.
Tun kafin mu shiga mota na nuna mata fa yana da kyau ta gyara domin kuwa kaf Hajiya Saratu ba'asar yin ta ba ce, ta wuce matsayin Yaya a wurinta sai dai uwa, gashi kuma yayar mijinta ce dole ita za ta yi hakuri ta nemi hanyar daidato domin su gyara zumuncinsu tun kafin yaranta su fahimci halin da ake ciki.
Jikinta ya mutu sosai a lokacin da nake yi mata maganar ba kuma ta yi mini jayayya ba ta ce mu je din, dama ai ita bata d'auka da zafi ba, ita Hajiya Saratun ce ta ga kamar har yanzu bata huce ba domin koda ta haifi Khalil ba ta je mata barka ba. Na ce mata kada ta duba wannan kawai ta yi 'ko'karin gyara kuskuran da ta yi a baya.
Takuwa ji dad'i sosai da muka je gidan nata, kuma duk yadda Hauwa take d'ari-d'ari da ita sai ba ta nuna mata komai ba a fuska ba, ta sakar mata fuska kamar babu wani abu da ya ta'ba faruwa na saba'ni a tsakaninsu. Sosai na ji dad'in ganin yadda suka samu daidaito da fahimtar juna. Muka rabu cikin girma da mutunta juna ta yi mana alheri sosai tunda dama can a sanin da na yi mata itama hannunta a bud'e yake.

***
Bayan komawarmu da kwanaki uku na kira Hamusu a waya na ce masa ya fitar da kudi ya kuma nemi kwararrun ma'aikatan da za su gyara gidana na kuntau sannan ya sayi set din kayan d'aki da kujeru da gado labuleye masu kyau ya sanya a shirya gidan. Idan komai ya kammala kawai ya kaiwa Sahura mukkulin na mallaka mata shi gabad'aya tunda dama takardun suna hannunsa sai ya bata. Shi kansa ya taya ta murna sosai ya kuma bani tabbacin zai kammala komai a cikin sati d'aya.

To mun yanke shawara har da maigidan kan cewa tare za su sake komawa da Hauwa saboda yanayin garin koyaushe cikin ruwa ake yi duk da gidansa ya sha bam-bam da sauran gidajen da suke garin legos amma dai hankalinsa ya fi kwanciya da mu zauna anan abuja zuwa wattani shida lokacin yaran sun yi k'wari sosai..
Na ji dadin hakan sosai kuma na yaba da yadda suke nuna mini kulawa dashi da matarsa. Sai dai tunda muka yanke wannan shawarar nake cin 'kaniyata a hannunsa duk ranar girkina nakan ji jiki kwarai da gaske baya daga mini 'kafa, idan na yi magana sai ya ce abinda ma ya kusa tafiya. Haka na yi ta hakuri dai har ya kammala musu shiri suka tafi sannan na samu sa'ida.

**
Cike da mamaki Sahura ta kira ni a waya tana tambayata wai Hamusu ya kai mata mukulli da takardun gida in ji ni, na ce mata 'kwarai kuwa gidana na kuntau na mallaka mata halak malak. Sai ta rasa bakin magana ta yi shiru ta kasa cewa komai ba. Sai da na sake yin magana tukkuna na ji sautin muryarta cikin rawa kamar za ta yi kuka tana yi mini godiya na ce kin wuce haka a wurina Sahura dukiyata taki ce kuma ki shirya zuwa umara in sha Allahu farkon Azimi maigidan ya baku kyautar kujera ke da Anti Yagana da Baba Sule.
Sai ta fashe da kukan da take ta b'oyewa na kashe wayar ina dariya da mamakin kukan da take yi a ganina ai Sahura ta wuce duk wannan abin a wajena yadda nake jinta a raina kamar anti Yagana da muka fito ciki d'aya.

Gudun aure littafine na kudi ki ji tsoron Allah ki biya ni hakkina kafin ki karanta


***
Ubangijina ya jarabce ni da abubuwa da yawa a lukutan baya wanda har nake ganin kamar ni kadai ce nake cikin masifa da ibtila'in rayuwa. Na yi kuka kamar ruwan idona zai tsiyaye yadda na ji dad'i na kuma godewa Allah shine ban ta'ba had'a Allah da waninsa ba, shi kadai na k'adaita na kai kukuna wurinsa domin kuwa nasan shine mai iko da kowa.
Allah na gode maka wannan kalmar ba zata ta'ba yankewa daga bakina ba har na koma ga mahallicina. Yadda Allah Ya kar'bi adduata a yau da Kamalu yake zaune a gabana cikin Kamala da suttura tare da tsantsar nutsuwa da wadataccen ilimin Islama a tattare da shi. Kamalu ya girma ya zama saurayi mai tattare da tsafta nutsuwa da ladabi. Ban iya daurewa ba rungumeshi na yi sosai a jikina ina kuka ina tuna mahaifinsu har shi ma ya kasa daurewa ya fara taya ni Baba Tabawa dake goye da Hassana a bayanta ta fito daga kicin da saurin domin sautin kukan namu har can ta tsaya tana ba ni baki wai na daina yin kuka Allah ya kamata na godewa domin duk abinda yake faruwa hukuncinsa ne. Da kyar na yi shiru shi ma ya rike hannuna gam ya kasa saki.
Cikin wannan halin Yusi da Adam suka shigo domin lokacin da aka kawo mini Kamalun ba sa nan. Wani tsalle Yusi ya yi ya rungumeshi suka fadi a wajan Adam ya dinga yi musu dariya. Shi ma Kamalun dariya yake yi wa Yusi ganin yadda duk kwalla ta cika kwarmin idonsa.
Ya dube ni yana tambayata wai wane irin abinci Yusi yake ci ya kumbura irin haka, ko bashi da lafiya ne. Na ce masa lafiyarsa lau hutu ya samu da jin dadi. Adam dai yana tsaye yana ta dariya da yake yaro ne mai sakakkiyar fuska kamar ta Mamansa. Kamalu ya gyara hannun rigarsa ya daga k'wajinsa na hannun dama duk a mur'de ya dubi Yusi yana cewa ka ga ni da nake cikin hatsi ina kuma aikin gona da motsa jikina dubi kwanjina malam haka ake son namiji ya kasance.
Adam ya ce abinda ake gaya masa kenan amma kullum sai ya ci nama ya zuba suga da madara da vombita da yawa ya tea Momi na bashi goyan baya.
Yana dariya yake cewa ku raka ni na je na gaishe da Momi ni ma." Ya mike tsaye ya shiga tsakiyarsu suka kama hanyar fita. Ni da Baba Tabawa muka bi su da kallo cike da wani irin farinciki a zukatanmu bakid'aya.

Abin mamaki da d'aure kai. Tun ina tsammanin dawowar Kamalu har na cire rai domin kuwa sha daya na dare har ta gota. Zuciyata ta shiga yi mini nazari ko kallo suka yi ne, ko kuma dai yaran sun d'auke masa hankali sam ban kawo cewa matar gidan ce ta hana shi dawowa ba sai da na kira ta a waya na tambayeta tukkuna kai tsaye ta ce mini zai kwana cikin 'yan uwansa ne. Mamaki mai yawa ya lullube ni amma ban iya cewa da ita komai ba muka yi sallama har tana cewa a shafa mata kan twins.
Da zullumin lamarin na kwana a cikin raina. Don haka gari yana wayewa ban yi kasa a gwiwa ba na kira maigidan a waya da muka gaisa na gaya masa fa makaranta sun sallamo Kamalu yanzu haka muna tare da shi anan abuja jiya Ayuba ya kawo mini shi. Sai ya ce ai Hamusu ya kira shi a waya ta gaya masa. Daga can makarantar ma sun sanar da shi. Na ce zai yi sati sati daya anan domin mun gama yanke magana da Hamusu zai zauna a can wurinsa domin dora shi akan harkokin da muke yi.
Bud'ar bakinsa sai ya ce bai amince ba dama ai tuntuni ya gaya mini idan yaron ya dawo zai had'ashi da d'an uwansa su tashi tare . Idan kuma ina ganin hukuncin da ya yanke bai yi mini ba sai na yanke nawa tunda duka 'ya'yana ne.
Na dinga kokarin nusar da shi hakkin da dangin ubansu suke da shi akan yaran, idan fa magana za a yi ta gaskiya yana da kyau a ce suma an basu damar yin abinda suke so da yaran. Ya fahimci dalilina amma sai ya mayar da abin rigima . Ganin haka ya sanya na kashe wayar raina a b'ace.
Ni wannan 'karfa-'karfa da ake yi mini akan yarana ya fara isata wallahi duk na gane take-takensa shi da matarsa wata'kila ya yi mata kyautar yaron tuntuni ban sani ba, tunda haka ya bata Yusi ba tare da neman izinina ba.
Wannan lamari ya janyo mana sa'insa sosai a tsakaninmu, wanda har sai da na gaza ha'kuri ina kuka na kira Hajja na gaya mata ta yi masa magana ta ba ni ha'kuri sosai ta ce za ta sanya a kira mata shi a waya.
Ranar kuwa da suka yi waya Baban Saude ya kira ni tare da rufe ni da fad'a irin wanda ban ta'ba tsammani ba. Shiru kawai na yi Ina sauraransa wato tunda na kira mahaifiyarsa to shi ma bari ya had'a ni da nawa iyayen. Baban Saude ya gama nasa fadan. Anti Yagana ma ta kira ni tana yin nata tana ce wa ba ni da wato har yanzu kuma har yanzu na kasa gane irin k'aunar da mijina yake yi. Idan duk zai d'auki yaran da zan haifa ya bawa matarsa ai ta cancanta ne tunda kowa ya shaida ita din uwar marayu ce. Har da Allah Ya isa ta yi mini idan na kuma tashin maganar da kanta zataje ta yi wa Gwaggo bayani tana da tabbacin samun goyon baya da amincewa daga wurinta.
Kuka na ci na 'koshi na ha'kura na kyalesu kullum dai da safe suna shigowa mu gaisa. Shi ma kuma kamalun ya fi sakewa a can saboda yaran don ma shi Salim yana can saudiya yana 'dora karatunsa sai 'yan yaran Nusaiba Sahib da Yasmin da ake kawo su duk ranakun weakened.

Kiran Hamusun na yi a waya na yi mass bayani duk yadda al'amirin ya juye. Sai ya dinga dariya cike da nuna rashin damuwarsa yake ce mini wannan ai ba wani abu ba ne hakan ma da aka yi daidai ne da kuma hujja mai k'arfi.
Dole na ha'kura na zubawa sauratar Allah Ido, amma kuma ban ta'ba nunawa matar wani abu a fuska ba, dalili ta wuce na ya'keta akan komai ba, wanda ya riga ya ce yana son naka ai kai yake k'auna.....


Tofa wata sabuwa =3
Shin wai mai Hajiya Maryam take nufi ne, alheri ne ko kuma sharri Allah ne kadai yasan abinda yake cikin zu'kantan bayinsa.....
'
Muje dai zuwa.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*79*
'Kwarai na danne hakan a cikin raina domin duk 'kwa'kwata na kasa gane abinda yake cikin zuciyarta dalili koyaushe alherinta a gare ni ru'banya yake yi. Ni dai kawai na zama kamar mutum mutumi tare da zubawa sarautar Allah ido, ita da mijinta suka yi duk yadda za su yi wurin mayar dashi makaranta domin ya samu shedar kammala secondary tunda wannan da ya gama sun fi karfi akan al'kur'ani da sauran littafan addini. Ban ce musu komai tunda bai sanya ni a ciki ba kawai dai na yi masa shiru har sai da yaron ya

Please Login or Register in order to submit comment