Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dire ta ce sai ya saketa har suka shiga kotu alkali ya yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata ya kuma tilastashi sakinta tunda gaskiya ba namijin da kowace mace za ta yi sha'awar zama da shi ba ne.
Anti Yagana ta cigaba da cewa." Ai tana fita idda ta lallaba Dada ta tafi makka wata shida fa yanzu tun bikin Fadila
Na ce." Allah sarki Ya falmata zuciyarta a tsaye take irin ta Baban Saude ba ta son zama koyaushe tunaninta ya za a yi ta juya biyar ta koma goma. Amma ni da ta yi shawara da ni zan ce mata ta yi zamanta anan ta cigaba da sana'arta kamar zai fi alheri."
Ta ce." To ta dai ce shekara uku kacal za ta yi ta dawo sai dai mu yi mata fatan alheri kawai."
Na ce." Ubangiji Allah Ya taimake mu bakidaya anti Yagana ke kuma me ki ke sayarwa?" Na tambayeta cikin sigar tsokana."
Ta ce." Babu komai hankalinta a kwance har sai da na yi dariya na furta.'' Babansu Fadila ne ya tsaya miki anti Yagana shiyasa kike wanke goma ki tsoma biyar ba ki da matsala."
Ta ja tsaki tana fad'in." Amina ai sai mutum ma ya rasa wace sana'ar zai yi wallahi maza daga waje duk sun k'wace mana abin yi."

Na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." Anti Yagana ba ni so ki kasance daya daga cikin matan nan da barmani coge take yi wa wa'ka (Sakarai baki da wayo) na yi dariya ina fad'in." Ki yi nazarin abinda za ki sayar na baki jari don Allah."
A tak'aice ta furta."Aikuwa na gode sosai ai ba ki ga yadda Fadila take cinikin ruwan sanyi ba cikin nan da take d'auke da shi ya hanata fara zuwa koyan d'inki don har mijin nata ya sayo mata form na makarantar."
Na ce." Ai ni ya burge ni sosai da ya ke so ta yi Sana'a dalili kuwa rayuwa juyawa take yi ga kuma yadda duniyar ta zama komai ya yi tsada tunda karamin ma'aikaci ne za su taimake ki kan su anan gaba"
Ta ce." K'warai kuwa hakane ni ma in sha Allahu zan yi nazarin abinda zan sayar idan na yanke shawara zan sanar da ke."
Da jin dad'i sosai na furta.'' Yawwa anti Yaganata ko ke fa" Dariya ta yi kawai muka yi sallama cike da barkwanci da k'aunar juna irin ta jini.
Wayar mu da anti Yagana ta kara mini karsashi da kuzari na tashi na je na dauro alwalar la'asar ganin uku da rabi har da minti biyar jim kad'an bayan idar da sallata Dr Sailuba ta kira ni ta iso tana falo na ce mata ta shigo d'aki ta same ni mun saba sosai da ita tuntuni.
Ta shigo kamar yadda na buk'ata ta zauna can kujerar dake gefe a d'akin. Na tashi na same ta muka gaisa cikin kulawa na ji dad'i kuwa da ta zo da abin gwajin bf ta yi mini jinina normal bayan ta gama kai tsaye ta tambaye ni ina da ciki na ce mata eh. Cikin raina ina tunanin fa ranar da Hajiya Maryam ta rasu na same shi tunda mun yi kwanciyar aure a daran ranar idan kuwa hasashena daidai ne bai fi kwana arba'in ba tunda itama gobe za ta cika arba'in da rasuwa.
Bayan magriba ta aiko mana da magunguñana kamar yadda ta fad'a mini kafin ta tafi muka sake yin waya tana yi mini bayanin yadda zan yi amfani da nawa maganin da kuma bayanin na Sultan tunda shi ma ta duba shi kafin ta tafi zazza'bin hak'ori ne yake damunsa magunguña ta had'a masa masu kyau tana fad'in daga zarar an bashi maganin zazzabin zai sauka don haka muka yin sallama a wayar na tashi na fita da ledar maganin nasa hannuna. Suna kicin ba su fito ba tunda na duba d'akin babu kowa har ita Nusaiban na same a kacame suna ta aikin kwa'ba fulawa har da Mairo dama yaran gabad'aya ganin Nusaiba ya sanyasu zuwa wajenta tunda akwai sabo kuma yadda take hira da yaran ya tabbatar mini da cewa ko a can baya da suke tare da mahaifiyarta bata tsangwame su ba hakan ya nuna sun yi sabo domin da babu kulawa da ja a jiki nasan babu yadda za a yi su je wajenta za su guje ta ne da kallon rashin sani kamar yadda suke yi wa Hauwa.
Da yake kicin ne mai girma mai d'auke da na'urorin sarrafe-sarrafe hakan bai sanya sun takura ba.
Baba Tabawa da Taburni suna ta aikin towon dare kamar yadda na umarta. Mairo da Nusaiba suna kwa'be-kwaben fulawa.
Na saki fuskata sosai Ina kallonsu suna cikin nishadi lallai d'an adam rahama ne a ko'ina sai na rasa ma gaisuwar wanda zan amsa manyan na yi haka zalika ma yaran na yi na bi duka na amsa ina fad'in." Nusaiba wannan funkason zai yi dad'i har miyau na ya tsinke."
Ta kuwa sanya dariya tana fad'in." Kai anti."
Na dubi Baba Tabawa ina fad'in. " Ga maganin Sultan Dr Sailuba ta aiko da shi a bashi abincinsa sai ba shi yanzu."
Rufe bakina ke wuya Hauwa ta shigo kicin din ta fara bin ko'ina da kallo babu wanda ya yi yun'kurin gaisheta Baba Tabawa ta zo zata kar'bi maganin tana fad'in." Jikin nasa da zafi har yanzu." Ta juya da sauri tana fad'in ko dai bari na fara dama masa kamun nasa. Da yake kamu ake yi masa na nikakkiyar gyad'a ya fi son sa akan duk sauran abubuwan da ake bashi kuma shine yake kara masa kuzari da lafiya babu kuma rama a tare da shi.
Na ji maganarta a cushe tana fad'in." Ba shi da lafiya ne?''
Ba tare da na dube ta ba na ce." Eh.'' A takaice na mi'kawa Baba Tabawa ledar magungan kafin ta kar'ba sai ta yi gaggawar warce ledar daga hannuna. Duka muka bi ta da kallo da mamaki.
Ta fito da magunguñan tana duba su. Na zura mata ido da tsananin takaicinta kamar na mangareta haka nake ji a raina wai ita likita amma mara tunani da kangado .
Ta gama duba magunguñan tsaf ta miko mini na kar'ba ina girgiza kaina duk abinda zan yi a yanzu wallahi ba don ita nake yi ba. Baba Tabawa ta kar'bi maganin daga hannuna. Hauwan ta dube ta tana fad'in." Ba ni shi na duba shi."
Sai ta dan dube ni a tsorace wata'kila tana fargabar ta bata shi ya bude ido ya ga fuskarta tunda ta gaya mini ya ta'ba shid'ewa a kwanakin baya.
Na daga mata kai alamar ta kwanto shi daga bayanta ta bata shi kamar yadda ta buk'ata.
Na ji tsakinta tana fad'in." Sai kin nemi izininta za ki ba ni d'ana na gani Baba Tabawa ko kin manta ni ce na haife shi ne ikon Allah sai kallo ni Hauwa"
Babu wanda ya tanka mata Baba Tabawa ta kwanto yaron daga baya wanda ya yi daidai da lokacin da ya bude ido ya fara kusurkusur sai kuma ya sa kuka. Nasa hannuna a wuyansa da zafi.
Itama ta mika hannunta domin kar'barsa kukansa ya tsananta kuwa ta rike shi yana fizga irin ta yara yana mika hannu domin komawa wajan Baba Tabawa. Kukan da yake yi ya tsorata ni sosai ita kuma ta'ki ba bawa Baban shi gashi dai ta fahimci so yake ya koma hannunta. 'Dif!! kamar an yi ruwa an d'auke ya yi shiru jikinsa ya shika lakaf! Idanunsa suka kakkafe. Suma ya yi.... Ta gigice ainun da sai ta fashe da kuka tana kallonmu na yi gaggawar kar'bar shi daga hannunta muka yi tiri-tiri a kicin din har muna bangazar juna ni da ita Baba Tabawa kuwa tuni ta fara hawaye tana fad'in.'' Suma ya yi.
Kafin mu yi wani yun'kurin Taburni ta nufi friji ruwa mai sanyi gaske ta d'auko ta gumtsa a bakinta ta fesa masa da karfin a gaske a fuskarsa ya saki nishi! Numfashinsa ya fara hawa da sauka. Ya motsa kafafunsa. Muka fita daga kicin din a gaggauce ni da su gabad'aya rasa inda zan nufa na yi da yaron a hannuna d'akinsu Baba Tabawa na nufa hankalina a tashe yaron nan ya mutu ko ya samu wata matsalar mun shiga uku a gidan nan gabad'aya..... Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*137*
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ita na dinga nanatawa a cikin raina ina zaune gefan gadon da Baba Tabawa take kwanciya da yaron hannuna. Duka sun yi cirko-cirko a kaina yayin da ita Hauwan take bakin kofar d'akin a tsaye ta gagara shigowa amma kallo daya za ka yi mata ka tabbatar da cewa a cikin tashin hankali take.
Numfashinsa yana ta hawa da sauka kafin a hankali ya bud'e idonsa yana juya kansa ya ga Baba Tabawa sai ya fara mik'a mata hannu alamar ta d'auke shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke cikin raina ina tasbihi da godiyar Allah.
Ta kar'be shi a gaggauce ta sanya shi a kafadarta tana dan jijjigashi sai lokacin hankalin kowa ya kwanta ganin yadda yanayin yaron ya daidaita na juya babu Hauwa babu dalilinta dama kuma ba ta iya shigowa ba a bakin kofar d'akin ta tsaya.
Minal ta je tana jan zanin baba Tabawa tana fad'in." Mutawa ya yi Sultan din shikkenan ya mutu ko?"
Da sauri na janyota ina girgiza mata kaina alamar a a gabad'aya yaran duk sun yi tsuru-tsuru ganin yadda muka ki'dime don shi Khalil har da yin kuka kuma bai biyo mu d'akin ba.
Na ce Baba Tabawa ta zauna dashi a d'akin ta bashi abincinsa gabad'aya muka fita. Smma ko da na koma dakina kasa zama na yi minti goma a tsakani na sake fitowa Hauwa na samu a tsaye a jikin kujera ita kad'ai don duk sun koma kicin din domin cigaba da ayyukan da suke yi. Muka dubi juna na wuce ta ban ce komai ba na ji ta kira sunana cikin damuwa na juya amma ban amsa ba ta zo ta tsaya daf da ni tana fad'in" Don Allah Amina kada ki gayawa maigidan ina neman wannan alfarma a wajenki."
Na zura mata ido cikin nazartar maganarta ashe mara kunyar 'karya ce. Na ce." To akan me zan gaya masa Hauwa da dai Allah Ya d'auki rayuwarsa ne wannan zama dole ya san dalili yanzu kam tunda Allah Ya sa ya dawo hayyacinsa sai ayi ko'karin kiyaye gaba."
Ta gyad'a kanta tana fad'in na gode. Ban saurareta ba na shige dakinsu Baba Tabawa tana ta kici-kicin bashi kamun data dama masa yana cinyarta a zaune yana kamo hannunta. Na sake sauke ajiyar zuciya ta jin dadi ganinsa kalau har ma yana d'an wasansa. Na zauna har sai da ta gama bashi ta gyara masa jikinsa da bakinsa tukkuna na bude maganin na fara nuna mata yadda za ta bashi koda ta kammala sai ta sanya shi a kafad'a ya yi gyatsa sannan ta d'auki towel dinsa ta goya shi. Yana ta gwalantu irin na yara.
Fitowata daga d'akin ya yi daidai da lokacin shigowarsa. Dama ya ce da wahala ya kwana. Na yi kokari sosai wajan daidaita yanayina na yi masa barka da zuwa ya amsa da kulawa yana fad'in.'' A kawo mini abinci Amina." Ya kama hanya zai hau samansa da wata leda viva a hannunsa. Yaran gabad'aya suka fito daga kicin har da Mairo jin maganarsu ya sanya ya dakata ya tsaya aikuwa suka nufe shi da sauri ya rirri'kesu yana dariya suna ta jero masa sannu da zuwa.
Ina kallo ya dubi Khalil cikin nazari ya riko hannunsa yana fad'in." Kai matsalata da kai zurfin ciki da miskilanci ko akwai abinda yake damunka?"
Ya yi shiru yana sunkuyar da kansa. Karaf muka ji Minal na ce." Sultan ne ya mutu ko Hassana, shikkenan ya mutu, shikkenan ya mutu." Ta dinga fad'a tana tafa hannunta.
Na ji kamar an rad'e mini guiwata da tar'barya. Nusaiba ta fito daga kicin din ganinmu a tsaye ya sanya ta d'an daidaita yanayinta ta dan risina tana fad'in.''Baba sannu da zuwa?"
Ba a hayyacinsa ya amsa ba saboda maganar Minal ta dake mu gabad'aya sai Khalil ya fara hawaye. A lokacin ne ya kara kid'imewa yana fad'in." Sultan ne ya rasu Amina?".
Na ce." A a lafiyarsa lau me yasa za ka yarda da maganar yara." Ni kaina na fad'i maganar ne wadda nake da tabbacin cewa ba zai yadda da ita ba amma don ya gazagata na ce da Mairo ta kira Baba Tabawa.
Ta kuwa fito da yaron goye a bayanta na ce." Kwanto mini shi." Ta yi yadda na umarta tana gaishe shi ya amsa babu sukuni. Inda yake na nufa da yaron a hannuna yana ta bacci. Na ce da yaran su je su yi sallar Isha'i su ci abinci da sauri suka bar wajan shi kuma ya kar'bi yaron muka haura saman a tare.
Leda viva dana kar'ba a hannunsa a lokacin da zai kar'bi yaron a hannuna na ajiye can gefa ya zauna da shi a hannunsa yana dudduba shi yake fad'in na dawo da farinciki sakamakon albishir din da Dr Sailuba ta yi mini Amina amma kuma me yasa za a yi mini a haka har yanzu a cikin gigita nake wallahi dalili ta yi mini bayani shima bai ji dad'i ba yana zazzabi hak'ori hakane ko?"
Na ce." E, yau tun safe ya tashi da zazzabin dalilin da ya sanya ni kiran Dr Sailuba kenan amma tsakani da Allah me yasa zaka yarda da maganar yara?"
Ya furta." Me yasa ba zan yarda ba lallai ne fa akwai abinda ya samu yaron nan ko ga yanayin yadda na ga tsoro da firgici a idon Khalil yarinyar nan Minal ba za ta yi karya ba."
Na ce." Ai ga yaron nan a hannunka ka duba shi sosai ka gani."
Ya kuwa fara duba shi har da cire masa kayan jikinsa ya bar shi da pampas yana jujjuyashi shi kuma sai dariya yake yi cikin ikon Allah zazza'bin ya sauka don dana ta'ba jikinsa babu zafi.
Na yi murmushi ina kallonsa na furta." Me ka gani a tattare da shi."
Ya saki ajiyar zuciya yana fad'in." Ban ga komai ba amma har yanzu ban yarda ba akwai abinda ake b'oye mini."
Na ce." Don Allah mu bar maganar nan mu yi wata ka ji."
Ya tsira mini ido na dan wani lokaci kafin na ji yana fad'in." Kin kyauta Amina ke ba za ki daina abinda ki ke yi ba ko?''
Nasan akan abinda yasa ya fadi haka na ce." Ka yi hakuri don Allah ina da ciki Dr Sailuba ta gaya maka ko?''
Ya gyad'a kansa yana cewa ta gaya mini amina amma mai yasa ki ke yi mini haka ba na fa jin dad'i tuntuni na gaya miki mai zai sanya abin alheri ya same ni a dinga b'oye mini wannan zalinci ne da d'aukar hakki wallahi."
Na ce." Ka yi hakuri ba zan sake ba."
Yaron na kar'ba ina mayar masa da kayansa. Shi kuma ya cire agogon hannunsa ya zare gilas din da hular kansa ya tashi tsaye tare da cire babbar rigar ya ajiye saman gado. Toilet ya nufa bai sake ce mini komai ba na sauka kasa da yaron na mayar dashi wajen mai rainonsa. Kicin din na nufa sun kammala komai na shirya masa abincin kamar yadda ya buk'ata da ya shigo
Na same shi yana sallar Isha'i na ajiye tiren a wurin da yake zama sai da ya jima saman daddumar yana addu'a kafin ya shafa ya taso yazo ya zauna na fara ko'karin zuba masa abincin yana ta kallona.
yana ci muna hira gidan Malam 'Daha da irin sallahun gaisuwa da godiyar da suka bashi zuwa gare ni. Nan yake yi mini bayanin abinda yake cikin leda viva da take ajiye gefe naje na daukota kayan dake ciki na fito dasu sassa'ken gargajiya ne da saiwowi gasunan kala daban daban. Ya fara yi mini bayanin yadda za a yi da ruwan rubutun dake d'aure a waya farar leda irin mai zurfin nan za a dafa maganin a tace a sha tsayin sati daya kullum karamin kofi d'aya. Babu maganar sauran asiri a tattare dashi kamar yadda malamin ya yi masa bayani matsalar dai aka samu har ta ta'ba masa lafiyarsa wannan mummunan d'aurin da aka yi masa tunda dama an yi shine akan manufofi da yawa. Idan har an dage da magani da kuma addu'a karfi da mazantakarsa zai dawo fiye ma dana baya. Sai dai ya ce kada wata mu'amula irin ta aure ta wanzu har sai an gama shan maganin tukkuna.
Ai a daran ban bari gari ya waye ba na dafa maganin na tace shi sosai na zuba cikin wani dogon jug guda biyu na kai saman nasa na ajiye kullum da safe za a sha kofi d'aya idan ya yi karin kummalo.
Da safe kafin na fita falo Sahura ta kira ni a waya cikin annashuwa da farinciki take fad'in." Amina don girman Allah ki taya ni da godiya wurin Yallabai jiya na kar'bi takardar gidan da ya yi mini alkawari zai ba ni anan hotoro wajan ma'aikatarmu gida mai kyau Amina ginin zamani gashi ya sanya an zuba mini komai tarewa kawai zan yi."
Sai ta rushe da kuka.' har sai da na ji wani iri a raina na ce." Haba Sahura menene kuma na kuka don Allah ai kin wuce haka a wajenmu don girman Allah ki daina wannan kukan ba na so."
Na ji ta tana fad'in." Ya zama dole na yi kuka Amina na dad'i ne wallahi na rasa inda zan tsoma raina ba ki ga gidan ba mai yalwa da wadatattun d'akuna ga ababen more rayuwa kuma wai gidana ne mallakina."
Na ce." To menene a ciki ai komai rabo ne, ki godewa Allah kawai."
Ta ce." Shine abin godiya a koyaushe amma dai ya zama tilas na godewa wanda ya zama sanadi."
Sallama muka yi da ita ban kuma yi kasa a guiwa ba yanzu zan je na sake jadadda masa godiyata.

na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Sai da na leka su Baba Tabawa tukkuna na duba Sultan ta yi masa wanka yana ta bacci cikin net dinsa muka gaisa sosai da su ina tambayar jikinsa ta ce ai ya warware sosai don jiya ma kwata kwata bai kwana da zazzabin ba har gari ya waye.
Na godewa Allah a cikin raina na fito saman zan nufa na samu Hauwa a kan kujera ita kadai a falo a zaune muka kalli juna na ganta a hargitse duk ta muzanta na janye idona da sauri daga kanta ai hausawa suna cewa.' Duk wanda ya hana uwarsa bacci to shi ma watarana bai zai rintsa ba kana ganinta kaga wadda take cikin tashin hankali da damuwa ashe tana son yaron ta cillar dashi ta tafi gashi yanzu 'kiri-'kiri tana kuka da nadama 'ya'yanta suna gudunta har dai mai suma saboda ta daukeshi Khalil da Minal kuwa ba na tsammanin ma suna yi mata magana domin duk gidan kamar mujiya haka ta zama.
Ina hawa saman ya ce na had'o masa shayi haka na sake sakkowa na shiga kicin na had'o kayan shayin na fito still dai tana zaune a kujera shiru ta d'an ba ni tausayi amma kadan ban kalleta ba na ji ta kira sunana na tsaya tare da dubanta.
Maganar dai jiya ta sake maimaita mini kada na gaya masa don ta d'auki sultan ya suma."
Na b'ata Raina ina fad'in." Wai me zai sanya na gaya masa ne Hauwa? me ki ka d'auke ni ne?" idan har ya san abinda ya faru to ki tabbatar babu yawuna smma ai kin san a gaban yara aka yi kuma irin wannan lamarin da wahala ya 'buya."
Ta yi shiru tana gyad'a kanta ba ta ce komai ba. Na kad'a kaina kawai na haura saman da mamakin yadda ta yi sanyi ta zama wata Saliha bana tsammanin ma jiya ta rintsa saboda yadda na hangi tashin hankali a idonta.
Sai da na bari ya kammala shan shayin tukkuna na tsiyaya masa maganin a madaidaicin Kofi da kamar minti ashirin da biyar a tsakani ya sha maganin har yana yin gyatsa yana fad'in." Na gode uwar biyu.'
Na janye kayan tea din daga gabansa ina murmushi na ce." A madadina da Sahura muna kara godiya zuwa gare ka Ubangiji Allah Ya kara suttura da rufin asiri Allah Ya sa a mizani na gode sosai Allah Ya saka maka da alheri."
A tak'aice ya furta." Ni ma na gode sosai Allah Ya saka miki da alheri Ubangiji Allah Ya sa mu rayu tare har karshen numfashina."
Amin na furta. Ina kallonsa zuciyata na d'an dokawa kan zuciyata na sa'ko mini wani lamari na ji maganarsa yana fad'in." Yau Maryam ta cika kwanaki arbarin da rasuwa ko?"
Na ce." K'warai kuwa Nusaiba sun yi abin sadaka da sassafe su Masa'udu suka fita da shi zuwa bakin titi tana can tana baccin gajiya dakinsu baba Tabawa."
Ya gyada kansa a nutse Yana fad'in." Babu wani Abu da nake buk'ata a game da dukiyar matar nan Amina amma ya zama dole mahukunta suka shiga ciki tunda duka mun gama harhad'a abubuwan da ta mallaka ni da yaronta Salim sutturanta kuma na gayawa Nabila tunda har yanzu tana gidan a zaune tare da yaran Salim da Adam na ce su raba a tsakaninsu abinda ya danganci furniture na d'akunan gidan da na'urorin dake kicin dinta yaran sun ce a bar musu a gidan abinda na gada daga ciki na bar mu su. Wad'annan manyan kadarorin nata da kudin da muka gani cikin wannan dirowar tata sune alkali zai kasafta ba ni buk'atar komai na bar musu abinda dai nasan ba zan ta'ba yafe mata ba shine ko'karin mayar da ni rago mai rauni da ta yi. Idan har lafiyata da mazantakata irin ta d'a namiji ba ta dawo daidai ba Allah Ya isa ban yafe ba wallahi."
Na yi gaggawar danne dariyar da take so ta kufce mini sosai na daidaita yanayina don ganin yadda yake magana cike da alhini da saduda da damuwa.
Na daure na ce." Maryam ba kai kadai ta cutar ba my love har da ni fa."
Ya yi saurin kallona kafin ya gyara zamansa ya riko hannuna yana murzawa ya furta." Shiyasa ai kullum idan na yi sallah nake neman sakayya a wajan Ubangiji ta cuce ni Amina idan na gaza miki ta wannan fannin zan k'wareki kawaici da hak'urinki zai k'are nasan watarana za ki nemi hanyar rabuwa da ni saboda rashin samun wani babban lamari wanda ya tasirantu da gangar jikinki."
Na ce." Haba dai ka daina yin wannan tunanin in sha Allahu rabbi zaka samu lafiya ka ma fi da k'arfi da mazantaka kamar yadda malamin nan ya fad'a kai dai mu cigaba da yin maganin sau'ki zai zo in sha Allahu."
Rungume ni ya yi sosai a jikinsa yana fad'in." Na gode sosai matata tuntuni na gama sheda cewa soyayyar gaskiya ki ke yi mini amma ba na jin dad'i a cikin raina a duk lokacin da na nemi ki na gaza kawar miki da bukatarki hankalina na tashi ina kuma tausaya miki a cikin zuciyata."
Cikin dauriya na ce." Babu komai fa kada ka tayar da hankalinka ina tare da kai duk rintsi in sha Allahu."
Ya sake matse ni tsam-tsam yana sauke ajiyar zuciya tare da sumbatar wuyana kamar dai koyaushe. Yana d'an yamutsa wasu wuraran na jikina.
Na janye a hankali Ina kallonsa yanayinsa ya canza sosai wanda yake nuna zallar buk'ata.
Ya dinga sauke nishi a hankali a hankali Ina kallonsa ya mike babu wani karsashi a tare da shi ya tafi ya je ya kwanta a gado. Yadda alamu suka nuna wannan shara'din da aka gindaya ya yi masa tsauri Allah kuma ya sanya ya iya jurewa zuwa sati dayan........
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK.*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*138*
To a daddafe dai ya iya bari wa'adin da Malam 'Daha ya gindaya ya cika. Ranar da maganin ya k'are kamar ya zuba a ruwa a k'asa ya sha saboda murna abin ya dinga ba ni da dariya da mamakin yadda

Please Login or Register in order to submit comment