Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma abinda aka ce masa muna yi da gaske mu ji haushi mu gyara yana yabon Maryam din tare da cewa mu yi koyi da ita. Lallai Hauwa ta yi mini kara sosai duk da nasan ko bata fad'a ba ta ji zafin hakan da farko daga baya kuma da ya fahimci gaskiya har ha'kuri ya dinga bata. Ta yi shiru har ya gama bata yi yun'kurin ta mayar masa da raddi ba, duk kuwa da cewa lefin ta bai kai a ce an yi mata wannan titsiyar ba, amma ta jure duk domin yi mini kawaici hakan ya sanya ni jin kunyarta kwarai da gaskiya wannan dalilin ne ma ya sanya muna shiga gidan na dube ta a nutse na ce." Hauwa ki yi hakuri don Allah bisa abinda Baban Saude ya yi da farko haka halinsa yake wallahi. Na kuma gode sosai da karar da ki ka yi mini."
Murmushi kawai ta yi kafin ta furta." Wallahi ko kad'an ban ji haushinsa ba Amina, idan da wanda nake jin zafinsa a raina bai wuce mijinki ba shine ma'kiyana lamba daya, kuma Baban Saude ai ya yi mana abinda iyayenmu suka kasa yi mana Amina, wallahi na tabbatar da cewa ko Inna Uwani na gayawa matsalata bai zama lallai ta dubi gaskiyata ba, shi za ta bawa gaskiya ta d'ora mini lefi, to balle na samu iyayena maza ina nufin 'yan uwan mahaifina wallahi a cikinsu babu wanda zai iya tunkararsa da sunan kwatar mini mutunci saboda yana da kud'i. ai ni Baban Saude ya yi mini kuma babu shaushinsa ko kad'an a cikin raina."

Tana gama fad'in haka sai ta shige dakinta ta barni a tsaye ina bin hanyar da ta bi da kallo. Na jima a tsaye a bakin kofar falon kafin na sauke zazzafar ajiyar zuciya na kama hanyar d'akina zuciyata cike da nazarin hanyoyin da zan bi wurin ganin mutumin nan ya yi kukan zucci. Idan da hali ma ya yi na zahiri zuciyarsa ta cika da damuwa tunda shi ya sayi hakan da kansa. Yadda ba ya so ana yawon tiritirin kai shi k'ara bayan yana aikata lefi, to ni ma abinda na tsana kenan a rayuwa kuma tun farko-farkon auranmu na gaya masa ba na so ya'ki dainawa. Zai gane idan kai ni kara shine zai daidaita ni.

Ranar dai gidan na mu tsit ya kasance kowacce tana d'akinta dama ni da Baba ne muke zaman falo Hauwa ba sosai ba kullum tana d'aki a kwance. Tunda na koma na kaiwa baban Saude sak'on su Dada
ban sake fitowa ba sai bayan magariba Baba ta kammala komai tana zaune ita kadai a falon tana kallo da carbi a hannunta. Gaisawa muka sake yi dalili ita haka dabi'arta take duk bayan sallar farilla sai an yi gaisuwa.
Ban fi minti goma da zama ba Hauwa ta fito da waya a kunnanta tana fad'in." E gata bari na bata sai ku gaisa ." Ta miko mini wayar tana fad'in." Inna ce take magana."
Cike da fad'uwar gaba na amshi wayar ina kallonta taje ta zauna saman kujera
Muka gaisa da inna Uwani cikin kulawa da sakin fuska har muka kare gaishe-gaishenmu ban ji ta yi wata magana ba wanda da farko na d'auka Hauwa ta gaza juriya ta sanar da ita abinda yake faruwa.
Wayar ta kar'ba suka d'an yi magana kafin su yi sallama ta kashe tana kallon baba Tabawa ta ce." Indomin nan nake so Baba duk dai tsugar mini da ciki take yi amma idan ba ita na ci ba na jin dadi. Amma ki hada mini da dankalin turawa ki sanya wadataccen kifi."
Na ce." Hauwa Indomee fa basir ce da atini idan kin manta na tuna miki gashi sai ki ce a sanya mini attaruhu ya ba zata tsugar miki da ciki ba, ki rage cin ta don Allah."

Littafin nan na kudi ne sister kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"To mai zan ci Amina, ita kadai nake jin sha'awa wallahi ban ta'ba ciki mai azabar laulayi irin wannan ba, da farko fa shiru kamar ba zan yi ba Amma cikin sati biyun nan ina jin jiki k'warai."
Na dube ta sosai ta dashe lebanta duk ya bushe ta ba ni tausayi. Dama kuma can tana da laulayi wannan ne ya yi tsanani.
Baba ta tashi ta kama hanyar kicin din na ce" don Allah Baba Tabawa kada ki biye mata ki sanya attaruhu kad'an kuma kada ta yi da roman nan."
Tana yar dariya ta ce." Haka kuwa za a yi, Hauwa ni ma na daina biye miki gaskiya."
Ta dube ni tana ce wa." Kin san roman shine abinda ma na fi so na dinga lasa dad'i yake yi mini."
Na ce." Mu bar maganar nan Hauwa, ni fa jikina ya yi sanyi ina fatan dai ba ki sanar da inna Uwani wani lamari ba ko."
Girgiza kanta ta yi a hankali ta ce." Babu abinda na gaya mata wallahi, mun yi waya ne mun gaisa ta ce na ba ki wayar ku gaisa."
Ajiyar zuciya na sauke domin har cikin raina na yarda da maganarta.

To a ranar bai shigo mana ba sai da garin Allah ya waye tukkuna ban kai ga fitowa falon ba ya shigo yaran kaf dinsu a tare da shi da yake asabar ce suna gida babu makaranta sai sha biyu na rana suke tafiya tahafiz su tashi shida na yamma.
K'amshinsu ya cika mini d'aki da uban da yaran sun sha gayu. Ido kawai na zuba musu Khalil ya fara gaishe ni kafin sauran suma su tsuguna k'asa kamar yadda suka ga ya yi "Mama ina kwana." Suka dinga jerowa ina amsawa. Khalil din ya ja baya suma sai suka ja baya suka tsaya kusa da shi. Na jima ina nazarin abinda suka yi kafin na furta." Khalil ja su ku tafi wurin Mamanka ku gaisa."
Bai ce mini komai ba sai ya dubi Baban nasu da yake tsaye a jikin kofa shi bai shigo ba shi bai fita. Ya d'aga masa kai alamar su je can wurin Hauwa.
Na sauke ajiyar zuciya cikin jin d'an sasaauci lallai ya fara sassautowa da d'aukar matakin gyara wata'kila daga haka a hankali yaranmu su dawo a hannunmu.
Da sauri kuwa yaron ya ja su suka fita cike da nishadin da suka shigo da shi.
Ya shigo dakin sosai ya tsaya a jikin mudubi kawai yana kallona Ganin haka ya sanya ni da sauri na tashi na bar wurin, bandaki na shiga duk kuwa da cewa ba ni da wani uzuri, kawai ba ni son kallonsa ne..
Ban fito ba sai da na d'auki kusan mintina sha biyar tukkuna na fito na samu d'akin babu kowa. Tsaki na ja kawai na wuce na je na zauna zuciyata a cunkushe da tunani, ni kam idan ma shiri yake nema a yanzu ban shirya ba domin kuwa ina so na ji dalilinsa na d'auke mini kwanar aure ya kai wa wata, idan ita Hauwa yana ganin babu aure a tsakaninsu, ni ai ba zaman idda nake yi ba. Duk fad'an da za mu yi ya dawo gida ya kwana idan girkina ne. 'Karyar neman tashin hankali yake yi, yanzu ya gama tasa rigimar ni kuma zan yi tawa akan abu biyu yawon kai ni 'kara da yake yi da kuma d'aukar mini kwanar aure, ko ba zai yi komai da ni ba, haka zalika ko ba zai kula ni ba ya shigo dai gidan ya kwana shine magana, ba za a ginu da wannan rainin hankalin ba.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*


[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: <2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*1k akan telegram via 0542382124... Binta Umar gtbank*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*100*
Ban yi tunanin zai sake shigowa ba da daddare
muna zaune a falo gabad'aya har da Hauwa wadda take ta fama garzar yalo da Masaudu ya sayo mata can cikin kasuwa. Kamar koyaushe ya tsaya suna gaisawa da Baba Tabawa kafin ya haura samansa. Hauwa ta tarkata shirginta ta nufi daki ba tare da ta cewa kowa komai ba. Girgiza kaina kawai na yi saboda takaici wannan abin da suke yi ita da shi.
Ina zaune ban motsa ba Baba ta ce." Hajiya ko za a hadawa maigidan abinci ne?" Na ce." Ba na jin yana da buk'ata Baba daga gidan matarsa yake."
Ta yi shiru tana kallon wani waje kafin ta sake dubana tana fad'in." Ko za ki tambaye shi dai."
Na ce." Baba kyale shi don Allah, idan yana da bukata daya shigo zai yi miki magana tunda kun dan jima kuna magana kafin ya haura samansa, kin san ba shi da 'koron baki."
Ta jijjiga kanta ba ta sake cewa komai ba sai ta tsirawa tibi Ido nasan ba ta so hakan ba don babu yadda za ta yi ne.
Kashe wayata na yi don ba na so na ga kiransa. Bai sake saukowa ba har muka tashi daga zaman falon baba Tabawa dai babu wani karsashi a tattare da ita muka yi sallama.
Sai da garin Allah ya waye tukkuna na kunna wayar haka na kwana babu sukuni.
Ina bandaki ina wanka na ji motsi ban kawo cewa zai biyo ni bandakin ba kawai sai ganinshi na yi ina tsaye tumbur da ni. Hankalina ya tashi ainun wata kunya mashahuriya ta ritsa da ni. Gani na dinga yi kamar ya keta mini alfarma nan da nan na ji idona ya fara kawo ruwa. Duk da ruwan kumfar sabulun da ya yi wa jikina sansani hakan bai hana ni yin gaggawar raromo towel dina da yake sakale ba. Na fara kici kicin daure jikina tsananin yadda hannuna yake rawa ya sanya towel din faduwa kasan wurin ruwan da yake zuba ta saman shayar da na kunna ya jike shi.
Raina ya b'aci mutuka haka na sunkuya na dau'ko towel ya yi jagab jikina babu kuzari na kashe shayar kafin na ya'ba towel din a jikina a hakan a jike. Ya tsaya kusa da ni a nutse kawai ya zura mini idanuwansa .
Na daure na furta." Amma dai kasan haramun ne abinda ka aikata ko?"
Ya yi shiru bai tanka mini ba kawai dai ya zura mini idonsa kaf ilahirin jikina rawa yake. Can kasa-kasa na yi tsaki tare da d'an janye jikina. Ya sake biyoni har sai da kirjinmu ya hadu. Hannuna ya kamo kafin ya duba tafin hannun kamar mai neman wani abu. Ya cika ya kamo na hagun shi ma yana dubawa. Cike da mamaki nake dubansa Ina nazarin abinda yake yi. Yadda yake sauke ajiyar zuciya shine abinda ya fara d'aga mini hankali.
Ko'karin sanya ni yake yi a jikinsa ina dojewa, na lura lallen da akayi mini shi yake ta bibiko. Kokawa muka fara yi a toilet din sai kace wasu sababbin amare
har sai da ya cire mini towel din ya yi jifa dashi can gefe, na rasa yadda zan yi da kaina na lura so yake na biye masa mu cigaba da kokaye-kokayen domin ya samu damar ta'ba mini jiki, gabad'aya duka na muzanta
ganina a haka cikin hasken rana ko auratayya zai yi da ni da safe ko da rana yakan sha wuya kafin ya ribace ni na amince domin na tsani ya ga zahiri na a gaske duk da na tabbatar da ce wa babu wata makusa a jikina da za ta janyo mini 'kyama a wurinsa amma haka siddin nake gudun haka.
Saman tumbina da ya dan tasa ya d'ora hannunsa bai ce mini komai ba ya fara wasa da hannunsa a wurin har ya so ya zarce can kasa. Na matse gefe cikin zafin nama kafafuna na wani irin rawa.
Ya sake biyoni a karo na uku. Sai kawai na silale a kasan wurin na zauna tare da takure jikina. Babu wani lamari da zai wanzu a tsakanina da shi a halin yanzu tunda har yanzu ba ni da tsarki kawai dai zai d'aga mana hankali ne.
Ganin yadda nake kuka tukuru ya sanya ya juya ya fita can kasa na ji shi yana fad'in." Ki fito mu yi magana sai mu sake gaisawa."
Bayan ya fita na yun'kura na tashi tsaye har yanzu kafafuna ba su daina rawa ba, sabon wanka na sake yi. Dana kammala na rasa yadda zan yi na fito tunda towel din da zan d'auro ya jike babu wani a toilet din sai 'kananu kuma babu wanda zai ratsa ni. Na rasa yadda zan yi haka na jure na bude kofar amma ban fito ba ina hangensa a gefan gadona a zauna yana duba k'aramar wayarsa.
"Ka miko mini towel ko zani ka ji."
Ya dago ya dube ni da sauri amma bai ce komai ba, na sake maimaitawa ina janye idona daga kansa. A nutse ya ce." Lallai za ki shekara anan a tsaye idan ni zan miko miki towel Amina."
Jin haka ya sanya ban k'ara cewa komai ba. Na yi kundubalar fitowa haka haihuwar uwata. Da kyar da hard'ewar kafafu na isa wardrobe dina. Ina jinsa yana ce wa." Ni da kayana a ce za a boye mini, to wane lungu da sa'ko ne ba ki kama kaina kin d'ora a wurin ba, da hannunki fa ki ke miko mini idan kin manta wannan kirjin naki cinyesu ne kawai ban yi na taune ba, kina ba ni ina sha fiye da yadda raina yake so."
Ban ce masa komai ba har na gama kintsa jikina yana ta sakin maganganu masu tsananin nauyi wanda na tabbatar da cewa wasu na aikata da sani na, wasu kuma ban san lokacin da na aikata ba domin kuwa bayan ni da shi sai Ubangiji da ya hallicemu ne kadai ya san irin ta'barewa da haukan da muke yi idan muna auratayya."
Na dube shi bayan na juyo da fuskata, gabad'aya yanayinsa ya canza duk ya shiririce idonsa sun risina sun kankance tare da wani irin yanayi. Yana ta ko'karin dannewa amma abin ya gagara. Koda na zauna a gefansa sai ya janyo ni da k'arfi jikinsa na karkwarwa ya fara fadin." Na zata zan iya dauriya Amina, mai zan samu ne, ina ta shirye-shiryen tafiya legos tunda na lura babu tsarki a tare da ke."
Na cire hannunsa da yake cikin rigita a nutse na furta." Ai ba ni da abinda zan iya baka a halin yanzu."
Ya mayar da hannunsa cikin rigar yana fad'in." Ke ce kuwa ki ke da abubuwan bayarwa my love dina."
Na yun'kura na tashi hannun nasa ya sa'bule ya fito daga cikin rigata shi ma ya tashi da sauri na matsa gefe can nesa da shi." Wallahi ba ni da abinda zan baka, ba za ka samu hadin kaina ba muddin ba ka daina had'a ni da iyayena ba, na ga ji da rashin adalcin nan da kake yi mini, ni ba baiwa ba ce, idan kai 'karata shine zai sanya na shiryu to lalacewa zan yi bari ma na gaya maka gaskiya."
Ya zuba mini ido da wani irin b'acin rai a saman fuskarsa ya furta." Haka ki ka ce ko?"
Na ce." 'Kwarai haka na ce, ni da kai, duka babu yaro karami, kamar yadda ba ka so ana tiririn kai ka 'kara wurin magabatanka ni ma haka, ka san halin Baban Saude haka siddin ya zo ya ci wa Hauwa mutunci ai ni ce mai laifi tunda ba ka yarda cikin zubewa ya yi ba, amma ita Hauwa ai taimako ta yi, mai ta yi maka ka saketa kana bin ta da mugun nufi."
Ya jima yana kallona na lura takaici da b'acin rai ne suka taru suka yi masa dabaibayi.

Na ce." Don haka wallahi ni ba baiwa ba ce.''
Yana gyada kansa ya furta." Zuwan da Baban Saude ya yi domin yi muku nasiha ya tashi a banza ko?"
Na ce." Ai kai ma ba jin nasihar kake yi ba, zalinci idan abin yi ka cigaba, ba zan jure ba wallahi."
Ya furta." Wane zalinci na yi miki ba ki da yunwa balle ishirwa ba ki da matsalar sutturar sanyawa, sannan idan kina da bukata ta d'abia ina kawar mini da ita shikkenan ba za ki yi mini lefi na nuna bacin raina ba."
Na ce." Ai na gaya maka ba da gangan cikin ya zube ba, mai yasa ba ka yarda ba har sai da ka kira Baban Saude. Idan ni da kai girma bai sanya mun gyara matsala idan ta taso mana ba to mu cigaba da tafiya a haka ni ba zan gaji ba."
Ya shiru na wani lokaci kafin ya ce." Ni kuma na gaji zaman lafiya nake nema, sannan saboda ba kwa tsoron Allah ke da Hauwa ku bud'e baki ku ce ina dukanku ba ku ji kunyar yi mini sharri ba Amina."
"Ai kaima ka fada ka mare ta, ni ma na gani ta ina muka yi maka sharri."
"To na ji, ke kin manta ta'addancin da ki ka yi mini ko?"
Ya fad'a yana tsare ni da Ido. Shiru na yi tare da zum'bura baki
Ya ce." Ni me yasa ban kai k'ararki ba?" Yafad'a yana juyo da fuskata. Na dube shi ina fad'in." Ai da sai ka gaya masa."
Ya girgiza kansa a hankali cikin sigar rarrashi ya furta." Idan ma kin kashe ni duk a cikin soyayya ce ni babu wanda zan gayawa, amma tsakaninki da Allah na taba dukanki?"
A dan sanyaye na ce." A a sai dai zagi.''
Cikin neman sulhu ya ce." Wannan ma tsautsayi ne da b'acin rai kuma kema kin rama ko kin manta?"
Na ce." Yaushe na zage ka?"
"Ranar da ki ka tura su Yusi kano ki ka ce uban waye ya ce Maryam ta ri'ke miki yara, kin zage ni kin zagi ubana zagin ya yi mini ciwo sosai wallahi."
'Kasa na yi da kaina ganin yadda ya yi kalar tausayi da nadama. Amma duk da haka abinda yake yi din ba zai sanya na janye kudirina ba. Domin mutum ne mayaudari wanda ya iya rarrashi da kalamai idan yana so ya cimma wata nasara."
Ya sake matsowa jikinsa sosai yana ta daga rigar dake jikina. Ya ce.'' Ni yanzu kwanciyar hankali nake nema nafiso mu sasanta kafin ace na koma legos, mu shirya kanmu kin ji giwa komai ya wuce."
Baki na zum'bura na ce." To yanzu ya kake so ayi, ai dama ni ba ni da matsala indai za ka gyara ka dinga adalci ka daina abubuwan da kake yi."
"Na ma gyara tuntuni na kar'bi kuskurena, zan kiyaye." Yafad'a a rikice Yana rungomu kafadata. Na janye jikina tare da cire hannunsa dake saman cinyata na ce." Shikkenan Allah Ya ba ka ikon yin adalci."
Sai ya yi kasa'ke yana kallona don yadda nake ture shi daga jikina Ina yin baya ya yi masa ciwo. Muka zubawa juna ido ni dashi gabad'aya ya zama kalar a tausaya masa. Mun jima a haka kafin ya gyad'a kansa
bai sake ce wa da ni komai ya tashi tare da kama hanya zai fita. Cikin zuciya na ce.'' Shikkenan ka ji idan da dad'i, ita matar da ka ratayawa fulawar soyayya ta iya da kai kawai gabad'aya ni ban ma yarda da nadamarka ba....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: <2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*2k complete a telegram. What'sapp group 1k*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*101*
Muka cigaba da tafiya a gidan babu annashuwa da jin dad'in da ma'aurata kan jiyar da junansu. Ya sauko sosai ya yi tubis da shi domin salon horon da na d'auka ba karami ba ne.
Gashi har yanzu bai cewa Hauwa komai ba dangane da zamanta a gidan domin da ya mayar da auransu a k'alla zai samu jin sau'ki ta 'bangaranta. Ya mayar da ita bai mayar da ita ba Allah ne masani, suna dai zaune a haka ita tana wasan 'buya dashi shi kuma yana nuna mata isa da iko irin na d'a namiji tabbas ko bai fad'a ba nasan jiranta yake ta kai kanta ita kuma girman kai ya hanata ta lallaba ta bashi ha'kuri. Amma yadda yake ta kokarin ganin mun zauna lafiya ni da shi na tabbatar da cewar ya d'auki shawarwarin Baban Saude domin ya rage wasu abubuwan

Please Login or Register in order to submit comment