Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba idan ba haka ba zan d'auka da kaina duk abinda ya faru a gidan nan ka yi kuka da kan ka."
Ya ce." Babu abinda zai faru sai alheri Hauwa idan kin kashe Amina ko kin yi mata wata illar sai dai na taya ki da addu'a domin kuwa da hannuna zan d'ankawa hukuma ke."
Ta ja hanci ba ta ce komai ba.
Na fara ko'karin tashi domin barin wajen ya rike hannuna tamau ya d'an kalle ni kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kamo hannunta yana fad'in." Ku shirya don Allah ba don ni ba kada ku yi gaba ko ku illatar da juna."
Na dube shi da mamaki wai yau shine yake yi wa wani wa'azin kada ya yi gaba. Abar da ta zame masa d'abiaa.
Na zame hannuna daga cikin nata tunda ya hade mana yatsu ne ya rintse da nasa gabad'aya.
Ya furta." Haka zan kawo yarinyar mutane cikinku da girmanku da shekarunku kuna a matsayin iyayenta masu yi mata gyara ta same ku kuna nuna kiyayyar juna.
Wani bala'in haushinsa ya kama ni. Hannuna na cire daga cikin nasu na tashi tsaye ya dago yana kallona bai ce komai ba na kama hanyar fita raina a b'ace. Ita Hauwa shirin take nema domin tunda ta ji ya riketa har yana rarrashinta ta yi lakwas kuma ko lokacin da ya had'a hannunmu waje daya ba ta yi yun'kurin cire nata ba. Ba ni tsammanin zan sake zama da Hauwa a inuwa daya idan lallai sai na cigaba da zaman aure da shi ya zama tilas ya yi abu daya daga cikin biyun nan ko na koma gidana na kano ko kuma ita ya canza mata gida......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*



[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*145*
Wannan shine abinda na yankewa kaina sanadin da ya janyo mana rikici mai tsanani tsakanina da shi domin na rantse masa da Allah ba ni sake zama da Hauwa a gida d'aya kuma wannan dalilin ya sanya shi kai ni 'kara abinda zai biyo bayan haka ba zai yi mana kyau gabad'aya ba.
Bai d'auki ga'barar kaini karar ba da ya yi iya yin sa domin ganin ya tankawari ni na ha'kura ya kasa sai ya kyale ni ya fara neman shiri da Hauwa duk domin na ji haushi da farko ina zaman falon ganin haka ya sanya na daina zama sai da dalili ita kuma mahaukaciyar sai ta d'auka tsoronta nake ji ina gudun ta rama marin da na yi mata. Daga lokacin da ta fahimci akwai 'yar tsama a tsakaninmu ta dage sosai wajan ganin ta kara juyar masa da tunani wanda gabad'aya rashin nutsuwa da ficewar hayyaci ya ya gigitar masa da rayuwa yana daurewa ne kawai saboda yana so ya nuna mini ba ni kad'ai ba ce matarsa a banza domin duk abinda suke yi shi da ita bai dame ni ba abinda da dai na yanke a cikin raina yana nan ban janye ba akwai wa'adin da d'iba muddin bai yanke shawara ba zan fita na bar gidan.
rashin sakewa da walwala ta ya assasawa yaran da masu aikin damuwa da farko su Baba Tabawa sun d'auka ba ni da lafiya suka dinga shigowa daya bayan d'aya suna duba ni. Amma da suka fahimci akwai damuwa sai duka jikinsu ya yi sanyi mussaman da suka lura da yadda Hauwa ta saki jikinta take yin annashuwa a gidan kamar ba itace mai matsiyacin 'kuncin rai ba.
Baba Tabawa tun da can ma muka dan yi maganganu na fahimta don haka ta zame kanta ta same ni a d'aki tana ce mini sai na dage da addu'a da neman tsarin jikina domin dai ta gama fahimtar Hauwa ba ta kaunata kuma idan ta samu dama za ta iya aikata komai a kaina.
A tunaninta wannan k'uncin da nake ciki Hauwa ce ta yi mini asiri domin shiga tsakanina da maigidan. To ba a 'kin ta mutum na amsa mata da to kawai ina kara jaddada mata addu'a kullum a cikin yin ta nake.
Ana haka Fadila ta haihu anti Yagana ta kira ni tana gaya mini ta samu 'ya mace na ce mata ina tafe.
A daran ranar duk da ba girkina ba ne na hau saman da na fi sati daya rabon da k'afata ta taka shi sai dai shi ya biyo ni d'akina yawan sa'in da muke yi a tsakaninmu ya sanya ya daina shigowa domin baya jin sukari a duk lokacin da zan mayar masa da martani magana ce mai zafi wadda za ta yi masa ciwo a raina.
Cikin jallabiya na same shi a can wurin da yake zama da Loptop din sa a gabansa. Ita kuma ta ci gayu da k'ananun kaya matsatsen wando iya gwiwa da wata riga mai hannun shimi breast dinta duk ya ta'be ta d'auki wata hular gashi ta sanya sai kace irin tsotstsun arnar nan. kan sa yana kasa yana ta aiki ita kuma tana motsa masa shayin da ta had'a masa.
Na yi sallama cikin gaggawa ya dago kansa ya kallo bakin kofar. Ido ya zura mini yana amsa sallamar ita kuma ta sai ta had'e ranta ta yi kasa da kanta can ciki ta amsa sallamar.
Gabad'aya kafatanin hankalinsa yana kaina har na zauna kujerar da take fuskantarsa a nutse amma babu walwala a fuskata na ce." Barka da dare."
A tak'aice ya amsa da "Barka dai ya kike?"
Ban bashi amsa ba na cigaba da cewa." Fadila ce ta haihu jiya gobe zan je maiduguri in sha Allahu.''
Kai tsaye ya ce. " To shikkenan sai a shirya tafiyar ko?"
Kasa na yi da kaina ban ce komai ba mamaki dai nake yi yadda ya amince nan da nan bai yi jayayya ba can kasan zuciyata na gaya mini hanyar shiri yake nema shine dalili.
Na yun'kura na tashi da niyyar fita daga d'akin ya dubi Hauwa yana fad'in." Ban ji kun gaisa ba kuma kin yi mini alkawari kan cewa za ki gyara kuskuranki haka dai ki ka gaya mini kwana biyu da suka wuce ban ga ni a aikace ba ."
Na yi gaba ban tsaya jin abinda za ta ce ba. Ai wanda ya ce baya sonka da farko daga baya ko ya zo ya ce yana sonka to k'arya yake yi ya fadi hakan ne domin cimma wata manufa tasa Hauwa ba zata ta'ba k'aunata ba dalilin da ya sanya kenan nake so na nisanta kaina da ita. Idan da gaske zuciyarta babu damuwa mai zai sanya daga na shigo ta 'bata rai jikinta ya mutu saboda ganina.
Na shige na yi tafiyata ina jin sa yana magana ban juyo ba.
Sai da na leka d'akin yaran na same su duk sun kwanta Mairo na ta gyaran wardrobe dinsu aikin kenan ta yi tsifar kai ta wanke da yake Taburni ta iya kitson hannu itace take yi musu idan an kawo wankin kayansu ta goge ta shirya musu ta ba ni tausayi sosai ita kadai a zaune duk sun kwanta dole a rage mata wani aikin mussaman gugar kaya mai wankin idan ya wanke ya goge ta samu hutu ga tashin asuba haka suke ta fama.
Na ja musu kofar na nufi nawa d'akin da sau'kin zuciya domin Ina so na d'an matsa daga wajan da nake zaune ko zuciyata za ta yi sanyi na tsani na bud'e idona na kalleshi ko na ji muryarsa saboda tsabar haushin da yake ba ni a yanzu. Har ni zai yi wa burga to Ina abin yake Hauwa dai macace amma a rashin mata domin dai da gabad'aya ta sullunce babu wata komad'a a tattare da ita idan har yana so ya tsorata ni ko kuma ya sanya mini kunci ya auro wadda ta fi ni komai shine zan daga hankali don yana soyayya da Hauwa a banza nasan duk buge ne.


don Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina b.


Wanka na yi na sanya kayan bacci na yi kwanciyata a gado ina Kiran sunan Allah.
Na ji ya turo kofar d'akin ya shigo.
Na zuba masa ido har ya zo ya zauna a gefan kafafuna yana fad'in." Kin mayar da ni sakarai mara mutunci ko Amina Ina yi miki magana kin yi banza wulakancin nan ya isa haka wai me ki ka taka ne?"
Shiru na yi ban tanka masa ba ya cigaba da cewa." Hauwa duk ta d'auki matakan gyara kuskuranta kamar yadda ni ma na d'auki matakin gyara akan zamantakewar da muke gudanarwa a gidan nan zan yi kokarin kwatanta adalci."
Na ce." To wannan kuma damuwarka ce idan ba ka yi adalci ba duka za ka ci a lahira."
Bai mayar mini da martani ba saboda ya saba jin irin wad'annan maganganun na fitowa daga bakina sai ya d'ora akan maganarsa yana cewa." A wannan lamarin da yake faruwa kece matsala domin kin d'auki wata hanya ta daban wadda na kasa gane inda ki ka dosa na gaya miki ba ni da ra'ayin raba gidana nafiso yarana su tashi tare domin su shaku."
Na tashi zaune ina kallonsa na ce." To sai ka rabu da matsala mana dole ne kana da da yadda za ka yi a kaina tunda na zame muku matsala ka yakice ta ka huta, ba zan zauna da Hauwa a gida daya ba wannan shine abinda zuciyata ta yanke mini.
Ya furta." Ni kuma ba zan raba gidana ba Amina ni dake shege ka fasa."
Na koma na kwanta tare da cewa." Duk yadda kake jin kanka baka fi karfin hukuma ba idan ba za ka raba gida ba to sai ka ba ni da takardata."
Ya furta." Wannan zoben da na sanya miki a yatsa shi yake nuna cewa ni dake mutuwa ce za ta raba auran zobe muke yi."
Na ciro zoben na ajiye masa shi saman cinya ina fad'in.'' Ai ban san manufarka ba kenan ga abinka nan."
Ya d'auka da mugun haushi da takaici a tare da shi ya dinga jujjuya zoben yana kallona har ya so ya d'an ba ni tausayi na d'auke kaina daga kansa.
Ya ce." Na gode." Ya mayar da shi hannunsa kafin ya sake kallona a karon da bashi da adadi ya ce." Gobe ki ka ce za ki je maiduguri ko?"
"Umm!" Na furta can kasan zuciyata.
Ya tashi tsaye yana cewa" Sukairaju zai kai ki a mota za kuma ki ga sa'ko cikin acct d'inki sai da safe."
Ya kama hanyar fita na ce." Da yara zan tafi domin ina so su ga dangina."
Ya juyo da saurin gaske yana cewa." Wannan ne kuma ba ki isa ba babu inda za ki je mini da yara. Ke dai ki je Allah Ya ba da sa'a."
Na tashi zaune ina cewa.'' Mai kake nufi yaran nan na ta'ba nuna maka wani iko a kansu tunda na haife su baka da hujja domin ba naka ba ne kai kadai dangina zan kai su domin kowa ya gan su."
Ya ce." Ba za su je ba na fad'a ke dai tunda kin zama isashshiya ga hanya nan ki tafi, yaran ma da ba wani damuwa ki ka yi da su ba yanzu za ki ce za ki je da su wani waje su zauna a gidan ubansu kawai."
Raina a b'ace na ce." Maidugurin ne wani waje kada ka manta fa asalina ne."
Ya ce." Wani waje ne mana ko akwai wani nawa a garin duk danginki ne ke ce ta maiduguri 'yan biyu kuma na kano ne garin Dambatta."
Ya fita da sauri tare da jan kofar da k'arfi.
Bacci rabi da rabi na yi da sassafe duk na gama shirye-shiryena kaya set goma na sanya a akwati na ce Khalil ya kira mini Masa'udu ya shigo ya tsaya bakin kofa muka gaisa na ce ya d'auki akwati ya kai mota.
Na koma na sanyo hijabi dina har kasa lokacin yaran sun gama shirin makaranta amma ga dukkanin alamun Khalil ya gaya musu tafiya zan yi tunda shi ya fita da akwatina.
Suka fito Minal ta rushe da kukan gaske sauran sun yi cirko cirko Usai da yatsa a baki tana tsotsa na cire hannun ina fad'in ke ba za ki daina tsotsar hannu ba sai tasa kuka tabbacin a kusa take dama.
Taburni da Baba Tabawa suka fito Mairo ta fito suka tsaitsaya yaran suna ta kuka har da Khalil ina kallonsa ya tsuguna bayan kujera.
Na ji giwata ta yi sanyi ainun dama kamar kiris suke jira domin koda na tsiri zaman d'aki haka suke shigo mini d'aya bayan d'aya idan sun taso daga makaranta.
Shi da Hauwa suka sauko yayin da nake gayawa Baba Tabawa Fadila ce ta haihu zan je ba wani abu ba ne.
Hauwa fuskarta a sake ganin abinda yake faruwa ko tana zargin yaji na yi oho a gabanta dai jiya na yi masa maganar tafiya maidugurin amma ban san abinda ya assasa mata sakin fuska ba duk dambarwar da uban yake yi da Minal akan ta sake ni ta'ki sai ihu take yi Hauwan ta zo tana jan hannunta da yake yarinyar a zababbiya ce idan tana kuka sai ta gartsa mata cizo a hannu. Aikuwa ba shiri ta sake ta matsa gefe. Babu halin na ciccibeta na rarrasheta kamar lukutan baya idan tana kuka d'aukarta nake yi yanzu kuma jikina ya yi nauyi cikin da nake d'auke dashi wata shida ni kaina nauyi yake mini bana iya sunkuyon kirki.
Na ja hannuna duka yaran suka biyo ni dakina.
Na zaune gefan gado su uku duk sun tsaya a gabana 'yan biyu da ita Minal din ta uku Khalil ne bai biyo ni ba. Tausayinsu ne ya kama ni ta kar'fi da yaji Hassana da Husaina sun koyi ha'kuri don yadda suke shakkata ba sa shakkar ubansu wasu lukutan idan suna kiriniya da ido na yi musu gargadi suke shiga hayyacinsu shiyasa ba sa yin iya shegankatar da Minal din take yi dalilin uban yana lelenta ba kuma fin sauran ta yi a zuciyarsa ba kawai yana fad'in sunana ne da ita wai yana yi mini kara..
Kawai na ji hawaye ya silalo mini duk wannan k'aunar da shakurar da take tsakanina da yarinyar nan dole na bar wa Hauwa 'yarta domin yaran da na haifa kawai zan hada kan kayana mu tattara a waje daya bana tsammanin barinsu a gidan idan Hauwa tana ciki za mu tafi tare da yarana da mai aikina baba Tabawa kenan su Taburni da Mairo idan suna da ra'ayin cigaba da zama da Hauwa su zauna.
Ya shigo dakin sai na yi gaggawar goge kumatuna. Minal na ta fad'in." Mama zan bi ki unguwa, Mama zan biki unguwa."
Ya tsaya a gefe yana fad'in." In banda neman fitina Amina ai sai ki bari su tafi makaranta tukkuna ki fito ki tafi tunda kin san lallai ne za a iya samun wannan matsalar.
Na yi shiru dai ban ce masa komai ba. Ya zo ya ja hannun yarinyar da ta d'ora saman cinyata Yana fad'in." Yi shiru za ku je unguwa ko?"
Ta daga kanta. Ya dubi 'yan biyu da suke tsaye a kusa da ni sai ya girgiza kansa cike da jin haushi ya kamo hannayensu yana cewa." Zan kai ku da kaina ku je karatu ku dawo da daddare da kaina zan fita da ku yawo kuna so ko?"
Suka daga kai babu wani karkashi a tattare da su.
Jim kad'an da fitarsu ya dawo d'akin ina zaune ban motsa ba tsabar yadda jikina ya mutu. Kawai ya mayar da kofa ya rufe ya tsaya yana kallona sai da na gaji tukkuna na dube shi na dan wani lokaci.
Ya yi kwafa yana cewa." Wato da tafiya za ki yi ban isa ki yi mini sallama ba ko?"
Shiru na yi uffan ban ce ba. Ya cigaba da cewa.'' Yaushe za ki dawo kwana nawa ki ka yanke?"
Na ce." Sati biyu."
Ya girgiza kansa yana cewa." A a ban amince ba a yi sati daya dai Hajiya sati biyun da ki ka d'iba a cikinsa nake tsammanin daurin aurena da yarinyar nan Hajara."
Na ce." To ni ina ruwana ni ka aurowa ita da sai lallai ina nan ko iyayenta ni suka bawa."
Ya ce." Kada ki gaya mini maganar banza da wofi Amina kina d'aga mini murya fa ya ina yi miki magana cikin lumana domin mu fahimci juna kina so ki zage ni wallahil-azimin na gaji da wannan rashin mutuncin da ki ke yi mini a gidana."
Can kasa na ce." Sai ka d'auki mataki ai."
Ya yi shiru yana kallona nasan ya ji abinda na ce kawai ya rasa yadda zai yi da ni ne."
Ya ce ki duba jiya da daddare na sa miki miliyan bakwai ki yi guziri ga 'yan'uwa na can garin naku. Biyar kuma sayi kayan kwalliya na danne kirji kamar yadda al'ada ta nuna Hauwa ma na bata."
Na dubi tsabar idonsa ina fad'in." Ba ka isa ka saye ni da kudi ba wallahi bari ka ji da can ba ni kudin dannar kirjin kake yi mata biyu ka auro kafin wannan cikinsu kwabonka baka ta'ba ba ni ba don haka ban ga dalilin da zai sanya wannan karon munafurci zai sanya ka ba ni kudinka ba."
Jikinsa ya yi sanyi ya furta." To shikkenan na ji zan ciko miki 10m sai ya zama sha biyar ba biya ki shikkenan ko?"
Na ce." Ba ka ji mai na ce ba kenan ba ka isa ka saye ni da kudi ba wanda ka tura mini ma yanzu zan dawo maka da abinka Allah Ya rufa mini asiri."
Sai ya yi shiru hankalinsa a tashe na ji yana fad'in." Allahuma ajirni fi musibati Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ya bud'e kofar d'akin ya fita cikin gaggawa.
Ni ma na tashi da sauri na fito na hange shi yana hawa sama falon babu kowa na fice daga gidan.
Sukairaju na tsaye jikin mota da alama fitowata yake jira tunda tun dare maigidan ya sanar masa da tafiyar ya shirya tsaf. A gurguje muka gaisa da masu hidima da gidan ya bude mini motar na shiga na zauna ina addu'a a cikin zuciyata ya shiga mazauninsa shima kafin ya kunna motar daga can maigadi na ko'karin bude gate din gidan....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*146*
Gida a kawo Fadila tunda haihuwar fari ce kuma dai gidan nata ba shi da wani spece inda Allah ya ta'kaita nasa ne ba ya haya ba ce wai hausawa suna fad'in guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni. Duk da haka ya yi kokari tunda d'aki uku ne da kicin da bandaki sai dai dak'unan duka ba ma su yalwa ba ne.
Haihuwa da lafiya akwai anya farinciki yarinyar tana zauna da babyna a hannu tana bashi nono na cika da mamaki kwarai da gaske wai yau Fadila ce ri'ke da jinjiri har tana shayar da shi gani ni uwarta gotai-gotai da ni ban gama haihuwa wato idan da Kamaluna ma macace haka za mu jera haihuwa da shi duk da Fadila ta girme shi sosai amma dai da mace ne a yanzu da ake yi wa yara auran wuri wata'kila da tuni na aurar ni ma
Yusuran Sahura ma tana can da nata tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe wai a haka ma ta yi 'bari na wata hud'u.
A washe da safe Sukairaju ya d'auki hanyar komawa gida bayan ya karya kummalo. Yawan shige da ficen da ake yi a gidan dangin mijin yarinyar da danginmu suna zuwa ganin jarari Hakan bai ba mu damar 'kebewa sai a daran ranar dana kwana biyu a gidan tukkuna muka zauna muna tattauna al'amura masu yawa. Nan na gaya mata irin abubuwan da suke faruwa tsakanina da Hauwa da shawarar da na yanke sannan da auran da yake shirin yi a tsukin kwanakin nan tunda ya ce satin na sama suka yanke za a daura aure.
Ta dinga mamaki tana fad'a kamar ta ari ba ki wai shi bashi da bakin da ba zai ce ya yi wa yarinyar girma ba ai ana barin halas don kunya wannan babbar asara ce da jin kunya idan har ya amince aka daura masa aure da yarinyar da ko shakka ba ta yi ta ji jinkanya da shi.
Abin ya dinga ba ni dariya ganin yadda ta hakikance da gaske tana ta fad'a tana cewa girmansa ya zube a idonta tunda ya shigo da son zuciya dama can yana so idan ba haka ba daidai gwargwado ya yi wa malamin alheri mutumin ya rushe masa gida ya zamanantar dashi tare da sabunta tsangayu irin na zamani aikuwa ya yi abin a yaba masa kuma idan biya zai yi akan hidimar da ya yi masa ya biya shi mai zai sanya kawai a d'auki yarinya a bashi ya kuma sanya hannu ya kar'ba har yana cewa don babu yadda zai yi ne wannan karya ce tsantsa da yaudara.
Da muka wayi gari ma ta tashi da mita shiga fita dari sai ta yi maganar tana cewa kin yi daidai ya kawo yarinyar su zauna da Hauwa a gidan ke ya canza miki wani idan ma ba zai yarda ki zauna a gidanki na kano ba ai yana da iko anan abujan sai ya samar miki da wani. Irin wad'annan masifun ne ya sanya wasu mazan ko basu da wadata suke rabawa matayensu gida to balle shi da yake da suttura da wadata tunda har abinda Hauwa take yi ya'ki ya'ki cinyewa kawai ya rabawa kowa mazauni sai a samu zaman lafiya.
Na ji dad'i sosai ganin yadda wannan karon anti Yagana ta goyu da bayana na saki raina sosai ina jin sasaauci Kuma ban kunna wayata ba yau kwana biyu kenan wanda nasan yana can yana ta lalubena a wayar bai samu ba.
Sai da na yi wanka na karya kullumalo tukkuna na fito falon na sami yarinyar tare da kawayenta na makaranta sun zo ganin jaririya suna ta tsokanarta sai suka ba ni sha'awa muka gaisa ina yi musu dariya cikin raina ina cewa duk yadda za ta kai ga baku labarin nakuda ba za ku fahimta ba sai ta riske ku tukkuna.
Anti Yagana tana ta gyara kaji a kicin nace." In ban da abinki anti Yagana ai sai ki kira ni na taimaka miki."
Ta ce." Ke ma ba lafiyar ce dake ba Amina na gode Allah ni da ya hore mini lafiyar wannan hidimar ta same ni Dada ciwo ya dabaibayeta nasan da ita za ta zo ta zauna mini"
Na ce." K'warai hakane shirin da na yi yanzu zan tafi can babban gidan ne na duba jikinta zan dan zaga dangi mu gaisa."
Ta furta. Hakan yana da kyau."
Kujera na ja na zauna na kama mata aikin Muna gyara kajin a tare na ce." Na lura yaron nan da yake auran Fadila yana da zuciya wallahi gashi nan komai ya yi na al'ada."
Ta gyad'a kanta tana cewa." K'warai Kam tunda ta haihu yake hidima domin da ta fara nakudar ma bai iya kaita asibitin gwamnati ba kudi ya fitar ya kai ta wanda za a bata kulawa wallahi sai da ta haihu ya kira ya gaya mana."
Na furta." Irin wad'annan matasan ya kamata ace an d'auki aure an ba su masu zuciya da dogaro da kansu da kuma ko'karin ri'ke iyali daidai gwargwado."
Daya daga cikin yan matan kawayen nata ta fito tana fad'in.''Mama ana kiran ki wayar ki." Ta mika mata wayar na riga ta kar'ba domin hannunta gaja-gaja yake fa jinin kajin da take gyarawa.
Ina duba fuskar wayar naga sunan Alhaji Tajuden da haka ta yi serving lambarsa
Na daga tare da sanya mata a kunne ina ji yana gaisheta da mutuntawa kamar yadda ya saba itama ta amsa cikin nutsuwa har tana tambayarsa yara ya ce duka suna lafiya sannan ya yi mata barka da arziki kafin ya fara tambayarta ina nake ya yi ta kirana a waya baya samuna.
Ta dube ni kafin ta ce masa gani nan a zaune. Sai na ji yana cewa da ita ta gaya mini na kunna wayata akwai muhimmiyar maganar da za mu yi.
Ta ce masa to in sha Allahu suka yi sallama.
Ta d'an dube ni a sanyaye tana fad'in." Na ji shi a sanyaye yana magana babu nutsuwa Amina kada dai ki ce da biyu ki ka zo nan garin kar ki ce da ni yaji ki ka yi akan wannan matsalar domin idan bacin

Please Login or Register in order to submit comment