Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan da duk abinda zai shiga tsakaninta da mijinta a kan hakkinki kawai ya kamata ki yi magana, amma ki yi kokarin kawar da kanki daga barin ji da ganin abinda yake yi a kanta."
Baba Tabawa ta jijjiga kanta cikin alhini da damuwa ta furta." Don Allah ku zauna lafiya, wallahi ba na jin dad'in abubuwan nan da suke faruwa."
Tsaki ta ja kafin ta ce." A shirye nake da abinda zai biyo baya Amina, wallahi yadda na tsani mutuwata haka na tsani matar nan, munufuuka ce, mai son zuciya gabad'aya ta juyar mana da kan miji, ai kafin ya aureta muna zaune lafiya da sauki akan abinda yake yi yanzu, babu wadda yake gani da mutunci face ita. Ta dabaibayi shi ta ko'ina ta asirce shi sannan ta zo tana sadda kai kasa tana magana cikin alhini kamar wata mai gaskiya wallahi zuciyarta babu Allah
kuma abinda na fad'a ai ba k'aharu ba ne, ni ma ji na yi ana fad'a a duniya." Daga haka sai ta tashi ta shige dakinta cike da neman tashin hankali.

Ni da Baba Tabawa muka bi ta da kallo cike da tsantsar mamaki. mai ya yi zafi haka, a ganina abinda take yi ai ni ya kamata na yi amma ban yi ba, ita lamarin nata yana nema ya wuce gona da iri fa, ba na so ta janyowa kanta gagarimin rikicin da zata yi nadama a gaba domin kuwa wad'annan maganganun sun yi tsauri kwarai da gaske kuma sun yi muni.

To ita rigima dama akwance take shiyasa tashinta bashi da amfani domin kuwa muddin ta tashi akan sha mutukar wahala wajan samun ruwan da zai kasheta. A wasu lukutan ma ana kashetan shaid'an da mukarrabansa suke shiga cikinta su yi kane-kane, su bugi wannan bangare su bugi wancan b'angare.

Lokacin da na ga kiran wayarsa hankalina ya tashi sosai dalili ban san mai yake 'kunshe a cikin kiran nasa ba, daga jiya zuwa yau abubuwa masu muni sun faru wanda na tabbatar da cewa muddin ba a kai zuciyoyi nesa ba to rayukan kowa zai 'baci har da wad'anda ma ba su ji ba, ba su ga ni ba.
Na daidaita yanayi kwarai da aniya ban bari raunina ya bayyana ba na d'aga wayar a nutse gaisheshi na fara yi bai amsa mini ba ya ce." Kai ni 'kara wurin Mahaifiyata bai gamsar da ku ba har sai kun had'a ba ki kun cutar da baiwar Allah ko Amina?"
Na ce." Ban fahimci maganarka ba."
"Nabila ta kira ni yanzu ta cikin tsananin damuwa tana fad'in irin abinda kuka yi mata yanzu daidai kenan Amina, ko kina so ki nuna mini hassadarki a fili domin Allah Ya suturta Maryam ta fi ku kyau da ilimi da gogewa ta fi ku dukiya da kyauta da tausayi, kana ta fi ku mutunci da karrama dan adam. Idan har za ku yi kishi akan soyayyar da nake yi mata wannan ba zai dame ni ba, tunda zuciyata ita ta za'ba a madadinku, amma ba zan lamunci cin zarafi da sharri ba, zan shige mata gaba domin ganin an hukuntaku bisa sharrin da ku ka yi mata mai mutukar muni da razanarwa......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=L
*89*
A nutse na ce." To shikkenan muna sauraran sammanci a shirye muke ita Maryam tana da kai Tajo, Amina da Hauwa kuma suna da Allah da Annabinsa sai maganar da ka ke yi akan cewa muna yi mata hassada wallahi tallahi ni ban ga abin 'kyashi da b'akinciki a tare da wannan kwalmad'addiyar matar taka ba mai kama da mai cutar kanjamau ba, kudi da kake magana tana da su
kasan daidai gwargwado nima ina da su na halali babu wata mummunar hanyar da na bi wurin nemansu gumina ne, halak dina ne, babu wani mahaluki da ya ta'ba ba ni kwabonsa da zummar na yi jari, Ubangijina ya rufa mini asiri sannan
Ya taimake ni ban ta'ba ro'konka abin hannunka ba ina ga dana ta'ba neman wata alfarma a wurinka to da
cin zarafin da za ka yi mini sai ya fi haka. Ban ta'ba cewa Tajo tallafa mini ba. Eh tabbas talaka ne ubana amma ba mai mutuwar zuciya ba, kuma kai kanka ka san ba a tsiyace ka aure ni balle ka goranta mini. Allah Ya yi mini rufin asirin da babu wani mahalukin da ya isa ya firgita ni da dukiyarsa. Kai kanka baka da abinda za ka burge ni ga gigitani dashi ta fannin arziki balle matarka. Ko yanzu ka sake ni ba ni da kaico wallahi domin ina da madogara don naga kamar kana tunanin zan yi b'akincikin rabuwa da wannan daular da aka ajiye ni a cikinta. Idan kana da ja akan maganata to jarraba sakina kaga abinda zai faru.
Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya cike da tsananin bacin rai na cigaba da ce wa." Tunda ka zama dan aike jani talau ka gaya musu mun shirya da ni da Hauwa mu tafi kotun koli idan ba 'haka to mai ya kawo rami? Menene na damuwa don an ce mata matsafiya ashe da gaske matsafiyarce to ka gaya mata jinina dana yarana wallahi tallahi ya fi karfinta sannan wallahi ita dai ba takai maccen da zan yi wa hassada ba sai kuma abu na karshe wanda nake so ka sani cewa ni Amina Tajo ba a gabana yake ba balle har raina ya sosu domin hankalinsa ya karkarta can wani gefe, ai ita soyayya guda d'aya ce tun ta 'kuruciya kuma tuntuni na bada ita a wani wuri har abada kuma wani namiji ba zai ta'ba samunta ba a wajena."
Tsaki ya ja cikin kame-kame ya ce." kuna abu sai ka ce jahilan farko. Duk da wanda ya ji wannan sakarcin da kuka yi ba zai yi muku kallon girma da mutuntawa ba."

Da sauri na ce." Ahaf to mu din mun gaya maka cewa muna so a yi mana kallon girma ne. Ai ba mu iya abu don duniya ta yaba mana ba. Riya ai babbar masifa ce da take saurin cinye dukiya da imani, Allah muke so ya yaba mana ba wasu jahilai b...
kashe wayarsa ya yi da sauri bai bari na krasa maganarta ba. Ban damu ba, ni ma na ajiye tawa wayar zuciyata kamar ta tsage saboda tsananin tashin hankali da mamaki!

To ni ina ruwana da har sunana ya fito a rigimarsu asalima lokacin da suka fara bana wurin mai yasa ita Nabila ta yi jimilla ta had'amu mu biyu. Shin da yawun ita Momin hakan ta faru ko kuwa. Wannan amsar ba ni da mai bai ni ita dole sai shi ko ita Nabilar da ta kira shi a waya ta sanar da shi abinda ya faru.
kafafuna suka dinga kyarma tsabar rud'u da al'ajabi wannan masifar fa ita na dinga gujewa saboda yanzu har ga Allah ba ni son abinda zai daga mini hankali domin zuciyata ta jima tana shakar damuwa da rikici da tashin hankali. Bayan haka kuma Ina tuna irin alkawarin da na yi wa Baban Saude ba ni so ya ga kamar na sa'ba maganarsa shiyasa nake ta ko'karin ganin na danne Hauwa domin kada lamarin ya yi tsamarin da zai kwa'be. Ni dai aka yi wa da yarana, na yanke hukuncin da nake ganin shine daidai da abinda ya dace a rayuwarmu shikkenan magana ta mutu idan zai lashi takashin matarsa ko a kwalar rigita shi ya ga zai iya.

Cike da mutuwar jiki na ja jikina a hankali na zauna gefan gado gabana na bugawa da karfin tun d'azu a lokacin da
Hauwa da Nabila suke musayar yawu nake jin marata na murda mini kad'an kad'an. Yanzu kuma sai abin ya kara tsananta gabad'aya ma saboda rashin nutsuwa da kwanciyar hankali na mance cewar akwai ciki na wata hudu da sati daya a jikina.

Na daddafa a hankali na shiga toilet na tsuguna da zummar fitsari jini ya biyo baya. Gabana ya yi tsananin buguwa wanda ya yi daidai da karuwar zubar jinin saman wandon da ke jikina.
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! kalmar da na fara ambata kenan na tashi da kyar fafafuna na rawa na mayar da pant dina na fito tsakiyar d'akin na tsaya ina dawurwura alamun zubewar ciki ne ba wani abu ba.
Jikina na gyara cikin gaggawa na fito falo Hauwa tana d'aki sai Baba Tabawa a falon da yara sun zagayeta tana basu labari.
Kai tsaye d'akin na bi Hauwa tana kwance saman gado da wayarta a hannunta har yanzu babu sukuni a tare da ita ta tashi zaune tana kallona kafin ta ce." Ina kuma za ki je na gan ki da hijabi."

Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." Hauwa babu lafiya 'bari zan yi wallahi yanzu haka maganar nan da nake yi miki jini ne yake zuba asibiti zan je. Ta yun'kura ta tashi da gaggawa tana fad'in." Bari na sa hijab muje Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Da sauri na fita daga d'akin jin yadda wani abu mai nauyi ya fado cikin pant dina. D'akina ana shiga da gaggawa na zarce toilet na yi sauri na tsuguna abun ya fado kafin wani mashahurin jini ya biyo baya da tsananin ciwon k'wankwaso da gwiwa. Bangon bandakin na dafe tare da rintse idona da k'arfi na kira sunan Allah ina jin shigowar Hauwa d'akin da yake ban rufe kofar toilet din sosai ba kawai sai ta shigo ta kamani itama sunan Allah kawai take kira tana fad'in." Shikkenan gashinan ma ya fita cikin sau'ki sannu bari yanzu na tura Masa'udu ya je pharmacy ya sayo miki wasu magungua ba sai mun je asibiti ba in sha Allahu, Allah Ya takaita miki wahala duk abinda ya yi saura zai fito cikin salama idan an yi amfani da maganin."

Ban damu da jin abinda ta ce ba tunda na san aikinta ne. Ni kaina dama ba ni son zuwa asibitin dalili ban shirya ya ji yanzu ba.

Ita da Baba Tabawa suka gyara toilet din tsaf. Baba Tabawa dai sai jajantawa take yi har da 'yar k'wallarta tana fad'in." Namiji ne gashinan har Ubangiji ya fara yi masa hallita. Hauwa da suke aikin tare uffan ba ta ce mata ba ta yi mata shiru kawai. Ina zaune a gefan gadon Baban ta zo ta fita da wata leda a hannunta tana fad'in. "In banda abinki Hauwa ya za a yi a jefa d'an mutum a masai ina gaya miki gashinan Ubangiji ya fara fitar masa da hallitarsa.
Ido na bi ta da shi Hauwa ta fito daga toilet din tana fad'in." Magana ai ta mutu Baba ki je ki kai a bunne shi tunda haka aka koya miki a makarantar islamiyarku ta mutanan da."
Na dube ta a tsanake na ce." Abinda ya fita za a binne?"
Ta gyada kanta tana fad'in." Haka ta ce, shine ta tattare ta zuba a leda wai ita dai ba da hannunta za a zuba d'an mutum a masai ba."
Murmushi kawai na yi na ce." Hauwa kin san mutanan da camfi, wasu fa har yanzu suna wanke mahaifa tsaf su shiryata da likkafani su bunne. Ko musulunci an ce bata da wani amfani
Ta ja tsaki tare da furta." Mu a asibiti ma wallahi tattarasu muke yi a buhu a kai bola. Bata da wani amfani face zaman da ta yi da d'anka a ciki."

Shiru ya biyo bayan maganarta kafin ta numfasa a hankali ta ce." Wallahi Amina sai na ji ina ma ace ni ce na samu wannan matsalar kin san Allah ba na k'aunar cikin nan da yake jikina zan iya zubar da shi ni ma."

Da sauri na kalleta tare da furta." Ni ai ba da gangan na zubar ba Hauwa tsautsayi ne tare da tashin hankali da kuma rashin nutsuwa ya zubar da shi, yanzu lamarinki yana ba ni mamaki da tsoro wai shin me ya yi zafi ne don Allah don Annabi."

Ta yi shiru tana kallona da wani irin yanayi na damuwa. Na gyada kaina ina zullumi da tunanin yadda zan sanar da mai cikin ya zube ya amince kai tsaye ba tare da ya juya lamarin ba shine kawai abinda ya fi damuna a yanzu domin zai iya kulla mini sharri a wurin magabatana tunda dama yana jin haushina.
Ita kuwa na fahimci yanzu gabad'aya ta daina tsoronsa balle ta daga masa kafa

Sai da na ci abinci tukkuna ta gwada mini duk yadda zan sha magunguan da ta bayar a rubutuce aka sayo mini sannan na kwanta ita kuma ta tashi ta fita. Bacci ne mai nauyin gaske ya d'auke ni wanda cikinsa na kasance cikin hargitsin mafarkai marasa ma'ana.
Shigowar kira a wayata dake gefena shi ya tashe ni cikin firgici na tashi zaune wanda ya yi daidai da tsinkewar jini da k'arfinsa wanda nake da tabbacin ya huda zanin jikina kuma babu makawa sai ya shafi mashinfidin da yake kan gadona.
Wayar na d'auka na duba Hamusu ne da sauri nasa a kunnena. Jin shi cikin nutsuwa ya sanya hankali ya dan kwanta kad'an na amshi gaisuwar da yake miki kafin na tambaye shi su Kamalu da fara'a mai yawa a tare da shi ya ce mini gamu a ciki tasha a tare dama kiran da na yi miki kenan yanzu za mu wuce gida."
Na sauke ajiyar zuciya tare da furta." Alhamdulillahi, ka gaishe mini da Gwaggo idan an jima da daddare na d'an samu nutsuwa a lokacin zan kira ka sai mu krasa tattauna yadda za a yi."
Ya ce." To shikkenan anti sai na jiki in sha Allahu."
Kashe wayar na yi na ajiye saman bedlamp kafin na zuro kafafuna kasa a hankali. Baba Tabawa ta turo d'akin ta shigo. Sai na sauke ajiyar zuciya domin na ji dadin shigowartata.
Ta nufo ni tana fad'in." Sannu ai na shigo ya kai sau biyar ba ki tashi ba ga la'asar ta yi babu kyau bacci a irin wannan lokacin......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=L

*90*
Na ce." Tunda na sha magunguan jikina ya mutu amma dai ciwon marar da sauki alhmdullhi sai jinin da yake zuba shine abinda ya d'an ba ni tsoro.
Ta ce." Ai wannan dole ne sai a hankali zai dinga janyewa." Ban ce komai ba na tashi a hankali na nufi bandaki ina fad'in." Baba ki dan fito mini da wasu kayan tare da audiga sai ki miko mini."
Ta amsa cikin kulawa. Wanka na yi da ruwan d'umi na gasa jikina sosai na shirya a toilet din na fito. Lokacin har ta cire zanin gadon da ya baci ta shimfida mini wani tare da sanya turaran wuta. Ina fitowa ta shiga bandakin da bedsheet din a hannunta.
Bata fito ba sai da ta wanke zanin gadon tare da kayan da na cire ta fito dasu a boket ta fita can haraba domin shanyawa.
Sai bayan sallar magriba Hauwa ta sake shigowa ta duba ni, tana tambayata idan da matsala na gaya mata na ce mata babu komai na ji dadin magunguan dana sha
Mun kai kimanin minti talatin a tare muna tattaunawa kafin ta fita.
A lokacin na samu sararin kiran Hamusu a waya gaishe ni ya sake yi kafin cikin inda-inda ya ce "Dama yanzu nake cewa bari na kira ki a waya gani nan tare da Gwaggo ma."
Na ce." Allah sarki ba ni ita to mu gaisa."
Tana kar'bar wayar cikin kulawa na gaisheta tare da tambayar yanayin jikinta ta amsa itama da kulawa.
Sai da na d'an nisa tukkuna na fara yi mata bayanin duk abinda yake faruwa. Bata katse ni ba har sai da na kammala maganata kafin daga bisani ta ce." Hamusu duk ya yi mini bayani Amina kuma ai maigidan naki ma bai jima da tafiya ba mun jima muna tattauna magana akan lamarin rayuwar nan hakuri ake yi da d'a da dukiya duka babu wanda ya san mai amfanarsu sai Allah, kema ban ga lefinki ba don kin yanke wannan hukuncin ba ki yi lefi ba kin nuna jarumta kwarai da gaske."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Shine dalilin da ya sanya na ce su dawo nan wurinku su zauna mu fadada harkokinmu na yau da gobe sai had'a hannu da Kawun nasu Hamusu wurin ganin sun kawo mana cigaba gabad'aya."
Ta ce." Kwarai hakan yana da kyau sai dai ni abu daya da ki ka yi anan shine yadda ki ka yanke hukunci ba tare da sanin mijinki ba, Amina ba ki yi daidai ba anan ai ya gaya mini cewar shi ma da kin sanar dashi ga hukuncin da ki ka yanke ba zai hana ki ba tunda da nan da can wurin naku duk daya ne. Sannan kuma Amina ina kara tausar zuciyarki da kyautata ha'kuri a rayuwa saboda duk mutumin da ya nuna k'aunar abinka ya gama maka komai mu babu abinda za mu cewa bawan Allah nan domin kuwa ya rike mana ke tsakani da Allah kuma ya kula da abinda ki ka je masa da shi ya rike kamar shi ya haife shi. ki yi hakuri kin ji ko, daga yau kada ki 'kara yin hukunci ba tare da kin shawarci mijinki ba sai ya ga kamar kin nuna masa iyakarsa ne.

Jiki a sanyaye na ce." To Gwaggo ina jin dai Hamusu bai yi miki bayanin abinda ya faru ko?"
Ta ce." Ya gaya mini mana shi ma mijin naki da ya zo ya sake yi mini bayanin duk abinda yake faruwa tsakanin yaran."

Kaina ya yi masifar daurewa jin abinda take ce wa, gabad'aya tunanina sai ya tsaya cak! ya aka yi ya san abinda na shirya ko dai Hamusu ne ya munafurce ni ya gaya masa. Ita kuma Gwaggo mai take nufi da wannan maganar wato ita ba ta kishin nata kenan, tun asali ban santa da son abin duniya ba balle na ce ya rud'e ta da kudinsa.
Na ji maganar Hamusu yana cewa anti abinda ya faru shine d'azu bayan na dauko yaran nan a tasha sai na zarce dasu kasuwa domin saya musu kaya da abubuwan buk'ata kamar yadda ki ka bada umarni. A hanyarmu ta dawowa wallahi Sukairaju ya d'auko Yallabai a mota zuwa airport ya hange mu don shi bai ma gan mu ba shi Sukairajun ne ya gaya masa shine fa ya sanya shi ya biyo bayanmu har gidan Gwaggo. Babu yadda zan yi anti dole ta sanya na gaya masa komai a gabansa Gwaggwo ta yi fad'a sosai domin kin san ni da ke ba mu gaya mata matakin da muka dauka ba, anan ta sake tabbatar masa da cewa ita ta bashi yaran tun lokacin kwanciyarta a asibiti kuma kyautar tana nan ba ta janye ba.
Wannan dalilin ya sanya shi d'aukarsu amma ya ce zai a jiye su a gidan Hajja tunda ba kya son zamansu a abujan. kyauta kuma ya kar'ba har abada."
Wani irin takaici marasa misaltuwa ya lullubeni. Mutumin nan ya zame mini bala'i ta kowace siga dole sai ya tan'kwarani. Ban san lokacin da wasu lafiyayyun hawaye masu zafi suka fara silalowa kumatuna ba. Kashe wayar kawai na yi na ajiye ina jan hanci zuciyata kamar ta buga. Lallai Gwaggwo ta iya yankan k'auna da nuna iko da gadara. Wai me yasa mutanan da suke hofintar da na su ne koda kuwa sun tabbatar da gaskiyarsu. Gwaggo bata san halin mutumin nan ba shiyasa take yabonsa har take yi masa kyautar d'an mutum. Tunda mutumin ya kutso rayuwata yake ko'karin raba ni da nutsuwa da farincikina. Ba na samun wata d'aya a cikin annashuwa ba tare da wata matsala ba. Yarana ni na haife su amma 'kiri-'kiri yanzu ba ni da iko da su, ban san inda aka yi haka ba. Hannu nasa na goge hawayen dake sauka a kumatuna sasaauci guda daya da na ji a zuciyata yaran na can hannun Hajja nasan suna hannu nagari ba za su wulakanta ba. Amma idan son raina ne gabad'aya yarana su bar shiga alfarma kowa su ci da guminsu su tufatar da kansu ta guminsu su kuma mori lafiya da kuruciyarsu. Ba ni da damar wata magana domin ba zan iya nuna rashin amincewata da abinda Gwaggwon ta zartar ba domin tunda yaran suke hannuna bata ta'ba nuna mini wani iko mai tsauri a kansu ba. Lallai mutumin nan ya dahu da sharri da ladabin 'yan shaye-shaye. Allah Ya saka mini.

Don Allah kada ki karanta littafin nan ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Can kamar saukar tsawa! na ji sautin muryarsa a falo. Gabana ya fadi sosai domin kuwa wannan sautin ba na sa ba ne aro shi ya yi. Asali muryarsa sanyi ne da ita ko fad'a yake yi asalin muryarsa ba zata gigitaka ba sai dai zafin ba'kaken maganganunsa.
Ban yi yun'kurin fita falon fa saboda bala'in haushinsa da nake ji a raina nasan dai dole zai shigo d'akin ya same ni. Baba Tabawa ta a shigo a gaggauce tana fad'in." Idan za ki iya fitowa falon ki fito Amina, mijinku ya shigo yanzu amma abin babu dad'i tsakaninsa da Hauwa."
Na ce." Ka kyale shi kawa Baba, fitowata ba zata amfanar da komai b.... Ban kai ga rufe bakina ba na ji kukanta cikin reshi tana fad'in." Ka kashe ni kawai Allah Ya isa tsakanina da kai."

Baba Tabawa ta ce. A gabana ya kai mata mari kusan uku a fuska.
Na diro daga gadon da gaggawa "Mari" Na furta da mamaki mai yawa, ai ba halinsa ba ne. Bar shi da ba'kar gaba da bakaken maganganu amma baya dukan mace. Bai ta'ba kai hannunsa jikina ba.
Daidai lokacin da ya ke ce wa." Ke kadai ki ka zo, kuma ke kadai za ki fi ce mini daga gida. Yara kuma ita na yi niyyar bawa Maryam zan bawa, ban yarda na bar muku su anan ba."

Tana kuka ta ce." Ai gadon rashin tarbiya muka yi da ni da kai. Tunda abinda ya yi Hauwa shi ya yi Tajo. Hajja ta saki nono ta bawa Uwani ni dai duka babu na

Please Login or Register in order to submit comment