Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wad'ancan dalilah masu girma. Duk wayewarsa a gida yake yi a d'aki kuma tare da iyalinsa akwai gogewa a wannan fannin kam yanzu ya yi mata wannan wulakancin tana sake ma'kale masa sautari maza sun fi naci da bibikon macan da take wahalar da su wadda take nuna musu so da k'auna kuma sai su d'auketa sakarai su yi ta wasa da hankalina kamar dai yadda yake yi mata a yanzu ta kasa ganewa.
Na dube shi ina fad'in." Ashe ga dalilin da ya sanya ka kasa fitowa ka gaya mata gaskiyar abinda yake zuciyarka. Tana yi maka irin wannan zantukan na rashin mutunci ai ka ga duk ranar da ka fito fili ka gaya mata ba ni da ra'ayin auranki za ta daina turo maka kai kuma ba ka so ta daina kana so ta turo ka karanta domin ta motsa maka sha'awa ko? Ba ka ji kunya ba don girman Allah. Wataran fa sai dai ka ga ta d'auki hoton wani sashi na jikinta ta turo maka tunda baka tsawatar mata ba ka yi shiru hakan ya nuna mata cewa ta cigaba kana so tunda yar iska ce ita wallahi tallahi ka yi bala'in bani mamaki."
Ya yi shiru jikinsa a mace ya kar'bi wayar yana dubawa messages din da ta tutturo. Ya jima yana karantawa daya bayan d'aya kafin ya dube ni yana fad'in." Bai zama lallai ki yarda da abinda zan fadi ba. Amma ki sani cewa ban ta'ba tsayuwa na duba messenges dinta ba balle na fahimci abinda yake a rubuce. Wannan stickers din kuma idan kin lura wasu sun bud'e da kansu wasu kuma ba su bude ba, ba ni da lokacin wannan sakarcin nata kuma ban san da cewa bata da hankali ba sai yanzu."
Na jima ina kallonsa da ko'karin gazgata maganarsa za ta iya kasancewa gaskiya ne abinda yake fad'i tunda wasu sticks din ni na bud'e su da hannuna Rubutu da karantawa abu ne da dama can yake bashi wahala k'aramar magana idan zai yi ya fi gane ya kira waya zaman sa ma a online babban jidali ne domin da ya hau baya mini goma cikakku yake sauka sai wata goben Kuma idan kuma ka gan shi a online tabbas akwai muhimmin abu.
Na ce." Ka dai ji tsoron Allah wallahi tallahi kuma ka suturta furfurarka ka haihu mata gasunan a gabanka duk abinda za ka yi ka tuna Allah Ya na ji yana kuma yana kallonka sannan kaima kana da zuria.
Ya yi bala'in shan kunu! yana fad'in." Me ki ke nufi ne Amina duk bayanin da na yi miki ba ki aminta ba, har yanzu kin kasa fahimtar abinda zan yi da wanda ba zan yi ba, bayan rantsuwa da Allah da na yi hakan bai yi miki ba kina ganin akwai abinda na boye wanda nake aikatawa, idan har na fahimci maganarki anan kina so ki ce mini ina neman matan banza a waje?"
Na ce." Ni ban fad'i hak..... Ya katse ni ta hanyar buga gefan katifa da hannunsa na kalle shi cikin kad'uwa da mamaki yanayinsa gabad'aya ya canza. " Ya furta." Ba ki fad'a ba na yi miki k'arya kenan kuma za ki k'aryata kan ki ne, gashi kina misali akan yarana idan na 'bata na wasu ni ma za a 'bata nawa. Duk tsayin shekarun da na yi a can baya ban yi aure ba kuma ban yi zina ba sai yanzu da girmana da kuma shekaruna. Kin jima kina kausasa mini kalamai irin yadda ranki ya so, ba ki da mutunci wasu lukutan ba ki daraja ni, kuma ba kya kar'bar kuskure da ajizancina. Idan ina neman mata tsayin zamana dake duk takatsantsan dina watarana za ki gane hakan me yasa ba ki da kirki ne Amina."
Cikin tashin hankali nake kallonsa ganin yadda gabad'aya ya rikice har zufa yake yi kamar ba wanka ya yi yanzu ba fitowarsa ya kashe Ac din dake d'akin.
A rikici da b'acin rai ya nuna ni da yatsa yana cigaba da cewa. " Idan har zan nemi matan banza bari na gaya miki yadda nake fitacce
masu aji da tsabta zan nema irina ba irinsu wannan matar ba da kuka matsanta mini a kanta ba, ina so ki kara sani ni mutum ne mai kishi idan ba dole ba da kuma 'kaddara ba ba ni so na yi tarraya da abu wani ma ya zo ya yi, ban ta'ba sha'awar wannan harkar ba duk tarin ni'imar da Ubangiji ya yi mini, abinda kuma ki ke fata ya kasance kan abinda muka haifa ba zai faru ba tunda ban yi ba Allah ba zai jarrabe ni ba."
Daga haka ya tashi tare da d'aukar hularsa ya sanya ya nufi ma'adanarsa da yake ajiye gilasansa ya zari daya ya sanya ya kwashi wayoyinsa ya kama hanyar fita babu annuri a fuskarsa.
Shiru na yi bayan fitarsa na gaza tab'uka komai saboda mamaki yadda ya burkice. Can k'asan zuciyata na ce mini tabarmar kunya ce fa yake nad'eta da hauka domin ya k'waci kansa duk hargagin banza ne. Na yi shiru sosai ina sake nazarin maganganun da ya furta. Tabbas kamar yadda ya fad'i mutum ne mai tsananin kishi. Tun bayan haduwarmu ta farko a ofis dinsa da ya zo mini da maganar banza bisa wata hujja tasa to tun daga lokacin ban sake ganin wani abu na sakarci da b'acin suna daga wajensa ba. Yana da ibada daidai gwargwado sadaka kyauta ciyarwa kulawa da marayu wasa da dariya da iya mu'amula.
Da'biarsa mummunan da na sani gaba da k'ullaci kuma cikin ikon Allah da zama ya yi zama a tsakaninmu ya rage. Ban ta'ba cin karo da wasu alamu da za su nuna shi din manemin mata ba ne gaskiya idan na ce na gani na yi masa sharri tunda a yanayin yadda yake mu'amulantarta a shimfida ma wannan ya isa sheda da tabbatar mini da cewa bashi da lokacin bibiyar wasu matan a waje. A yanzu dai idan na fahimci abinda ya hasala shi bai wuce don na ce ya ji tsoron Allah ba saboda shima ya haifa wannan maganar itace ta tunzura masa zuciya har ya fita da b'acin rai! Mai tsanani hakan na tabbatar mini da cewa ya ji ciwon maganar sosai kuma abinda duk ya fad'a gaskiya ne yau kan an kira ni da mara mutunci mara kirki dole na bada ha'kuri Allah Ya sawwa'ke.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE



[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*165*
Ban yi zaton fushin zai tsananta da yawa haka ba. Tunda a daran ranar da lamarin ya faru na bashi ha'kuri tare da nuna masa na yi kuskure sai ya dinga ciccijewa haka muka kwana bai ce mini komai ba da gari ya waye na gaishe shi ya amsa da k'yar. Still da ya fita ya dawo da yamma nan ma na sake bashi ha'kurin bai huce ba. Abinci ya'ki ci na dare da jiyan da yau a gidan Hauwa yake zuwa ya ci. Ganin kamar kwantar da kan da nake yi ina bashi ha'kuri yana Kara masa kuzari da karsashin yi mini wulakanci sai kawai na 'kyale shi Hauwa ta kar'bi girki ya je ya yi kwanaki biyu ya dawo mini babu fuska har yanzu zai amshi gaisuwata amma akan dole ko na hau saman na same shi sai ya tsiri aiki a loptop ko ya kira yara su yi wasa. Abin ya fara ba ni dariya da mamaki. Na yarda na yi kuskure kuma ban kyauta ba na nemi afuwa sai a yafe mini ai a cigaba da cud'a rayuwar amma sai ya samu hanyar hura hanci da d'aga kai ganin ina binsa da kwantar da kaina dama dabi'arsa ce haka idan ana ba shi ha'kuri sai ya kara hawa ba zai sauko ba.
Gaisuwar ma sai na daina na zura masa ido ko ni nake da girki ba ni hawa saman abinci kuma tunda ya daina ci na daina kai masa.
Muka cigaba da tafiya haka tsayin sati biyu babu wani sukuni a tattare da shi domin alamu sun nuna ya fara gajiya yana ta kame-kame.
Da daddare na yi shirin kwanciya tsaf ina zaune Ina bawa Hasan nono shi bai yi baccin ba tukkuna ya turo kofar d'akin ya shigo cikin jallabiya k'amshin turaransa ya mamaye d'akin gabad'aya ya had'u da wanda na yi amfani da shi.
Na d'aga kaina na kalle shi muka had'a ido sai na yi 'kasa da kaina dama ni ban zafafa ba ai ya nemi wuri ya zauna a gefena babu yabo babu fallasa na sake kallonsa muka had'a ido a hankali na ce." Sannu."
Bai amsa ba ya d'ora hannunsa saman goshin yaron yana fad'in." Minal ta ce mini ba shi da lafiya?"
Na ce." Lafiyarsu lau fa ta ji yana dan tari d'azu shine take tambayata wai bashi da lafiya na ce mata kalau yake."
Ya kar'be shi daga hannuna yana fad'in." Tari ba ciwo ba ne Amina."
A takaice na ce." Ciwo ne amma ba irin wanda nake tunani ba. Nono yake sha sai ya d'an 'kware shine bashi da lafiya in ji ta."
Ya d'an yi shiru na wani lokaci kafin ya furta." Jiya Hauwa a asibiti ta kwana bata da lafiya!"
Na dube shi da sauri " Bata da lafiya?"
Ya gyad'a kansa ya ce." Ciwon ciki ta yi sosai daga karshe dai cikin nata ne ya fice! amma alhamdulillahi ta samu sau'ki tana gida."
A d'an sanyaye na ce." Ban sani ba wallahi, kai za ka gaya mini kuma kana jin haushina."
Ya ce." Gashi yanzu na gaya miki ai."
"Allah Ya bata lafiya." Na fad'a cikin jin wani yanayi ta ba ni tausayi wallahi domin ta kallafawa ranta cikin Allah bai yi zai zo duniya ba.
Shiru na tsayin lokaci kafin ya kwantar da yaron kusa da d'an uwansa. Ya gyara kwanciya a gadon. Na dube shi yana lumshe idonsa yau anan za a kwana kenan.
Bai ji ma da kwanciya ba ni ma na kwanta a gefensa tunda dama na yi shirin kwanciyar.
Ya bude idonsa yana kallona ni ma shi din nake kallo wai akace labarin zuciya a tambayi fuska duk kame-kamen da yake yi na gane. Ya d'an janyo ni kusa da shi can k'asa na ji maganarsa yana fad'in.'' Kin yi mini abubuwa da yawa na kyautatawa da kuma alheri ba kuma zan mance ba."
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Wad'annan maganganun da ki ka yi a kaina sun yi mini zafi k'warai da gaske ina so wannan ya zama na farko ya kuma zama na k'arshe kada ki kara dangantani da haramci da abinda Allah ya la'anta. Ki san irin maganar da za ki dinga gaya mini wadda ta dace da wadda ke kanki kin san kuskurene. Ba ni da nufin auran Nabila a cikin raina na fad'a muku maganar ba d'aya ba sau biyu ba wallahi ba ta ta'ba ba ni sha'awa ba balle har na yi tunanin yin zina da ita ba zan boye miki ba har yanzu idan na kalleki na tuna abinda ki ka jingina mini raina yana b'aci wallahi."
A hankali na ce." In sha Allahu, Allah Ya ba ka ha'kuri."
Ya sauke ajiyar zuciya tare da d'an matse ni a jikinsa shikkenan daga lokacin kuma sai komai ya sauya..
Wai aka ce fad'an masoya hutu ne.
Da gari ya waye duk da bai sake yi mini maganar Hauwa ba amma ni da ita na kwana a raina domin yadda ya ke fadi ta sha wahala sosai kafin ma cikin ya fita tunda har sai da aka kwanta a asibiti kwana da yini.
Sai da yamma na shirya lokacin yara duk suna makaranta muka tafi da Mairo saboda yaran ita goya Hasan na ri'ke Usaini a kafadata.
Mai aikinta Ladidi tana ta goge -goge ita kadai a falon muka gaisa ta ce mana tana ciki a akwance na ce ta shiga ta gaya mata.
Minti uku ta fito tana sanar da mu cewa gata nan. Ta nufi kicin da sauri.
Mun kai kusan minti goma sha biyar a zaune kafin ta fito daga cikin bedroom dinta ta d'ashe sosai kamar wata mara jini duk sanda take da ciki haka take irin wannan mugun hasken fau! yanzu abin ya hadu da d'aita domin da alamu cikin nan a k'alla zai yi wata hudu zuwa biyar ta sanya rai.
Ta ba ni tausayi sosai ta zauna kamar mara laka a jiki babu kuzari da karsashin tana fad'in." Ashe kune in banda shiririta irin na Ladidi ai da sai ta gaya mini cewa ke ce."
Na ce." Ba sai ta san ni ba Hauwa."
Ta d'an yi murmushi kafin ta ce." E hakane bata ta'ba ganinki ba sai dai labarinki wurin yara."
Na gyad'a kaina ina sake nazarinta a nutse na ce. Ya jikin Ubangiji Allah Ya baki lafiya Allah ya mayar da abinda aka rasa."
Ta amsa da "Amin suma Amin na gode sosai."
Mairo ta gaisheta da jiki ta amsa tana kallon Hasan dake goye a bayanta sai kuma ta dube ni tana yar dariya ta ce." Sun k'ara wayo sosai yaran nan Amina."
Na ce." Sosai ni ma na ga girmansu wata uku muke yanzu."
Ta ce." Hakane kam."
Ta yi shiru tana lumshe Idonta na ce." Za mu tafi Hauwa Allah Ya kara afuwa."
Ta bude idonta tana kallona a daidai lokacin dana tashi tsaye ta ce." Na gode sosai."
Muka kama hanyar fita ni da Mairo. Na ji tausayinta gaskiya abin babu dadi.
Da ya dawo ya ji labarin na shiga dubata ya yi murna sosai yana fad'in da haka kuke yi tun farko ai da na ji dad'i Amina."
Kwana biyu ba sai jikin nata ya kara rikicwa ba ranar girkina ne da daddare wajan sha biyu da wani abu lokacin muna shirin kwanciya ta kira waya cikin mayuwacin hali ciwon kai matsananci jini kuma ya tsinke mata.
Tare da ni da shi muka nufi gidan a ki'dime lokacin ma ta fice daga hayyacinta mai'aikinta na ta ihu jini ya bata jikinta da bedsheet din da take kwance a kai.
Muka gigice ni da shi domin dai kamar babu rai a jikinta.
Jikina na tairairayota ina kiran sunanta ko'ina a sake. Ya fita da sauri yana kiran waya.
Kuka na fara yi ganin yadda take wata irin jijjiga ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! taune lebanta take yi hakan ya tabbatar mini da cewa jijjiga take yi domin duk rik'on da muka yi mata ni da Ladidi sai da ta fi karfinmu.
Ya shigo da kansa ya ciccibeta tunda dama ba wani nauyi ne da ita ba. Na ce ya bari tukkuna a kintsa mata jiki domin a 'bace take da kaina na gyara mara jikinta cikin wannan yanayin ya fita da ita rai a hannun Allah muka bi bayansa Sukairaju ya kunna mota. Ya ce da mai'akin ta koma gidan tare muka tafi asibiti a daran emagency da yake sananne ne a take manyan likitoci suka rufu a kanta.
Muka kwana a zaune da jiran saurare sai gefin asubahi tukkuna wani likita ya fito ya ba mu tabbacin cewa sun shawo kan matsalar da ikon Allah yanzu haka har an daura mata jini jini tana da buk'atarsa.
A lokacin ne hankalinmu ya kwanta ya ce Sukairaju ya mayar da ni gida saboda yara ni ma hankalina yana kansu amma duk da haka sai nake ganin kamar ina matsawa za a ce mini babu ita.
Babu wanda na gayawa halin da ake ciki har yaran gabad'aya. Sai Baba Tabawa itace ta sani tunda a hannunta na bar su hassan. Har yaran suka tafi skull ba ni da kuzari na kira shi ya fi sau biyar a safiyar yana gaya mini ta ji sau'ki bacci ma take yi shima gashinan zai dawo domin ya yi wanka.
Da 'kyar na iya yin karin kummalo na zauna a d'akina sukuku don yaran ma dana lura za su dame ni da koke-koke na ce da Mairo ta zo ta d'auke su. Na zauna ina ta tunanin rayuwa yadda Allah ya jirkitar da hallitar Hauwa jiya kadai shine abinda ya tsaya mini a raina. Muna ta hauka rai da rayuwa da jin dad'i duka ba a hannunmu yake ba. Hawaye suka ziraro mini kaina ya d'auki caji da tunani da zullumi tare da nadama da addu'ar kada Allah Ya d'auki rayuwarta a yanzu ina so mu yi nisan kwana tare mu raini yaranmu.
Wajan tara da arba'in ya shigo. Ganinsa cikin nutsuwa ya sanya ni sauke ajiyar zuciya ba mu yi wata magana cikakkiya ba har sai da ya yi wanka da breakfast tukkuna na fara tambayarsa jikin nata ya ce.''Ta ji sau'ki alhamdulillahi jininta ya hau sosai sanadin damuwar da ta tsanantawa kanta ba ta bacci ga ciwon kai mai tsanani abinda ya fita Allah ya yi ba rayayye ba ne na gaya mata tun ranar da lamarin ya faru tana ta kuka da tsananta damuwa idan da rabo ai za a samu
wani."
Na ce." Sosai kuwa in sha Allahu za a samu damuwar ai bata da amfani tunda itace ta haddasa mata shiga wannan yanayin.
Ya ce." Abinda nake so ta gane kenan, za mu cigaba da ro'kon Allah Ya kawo mana masu albarka."
Na ce." In sha Allahu rabbi."
A takaice dai sai da ta yi kwana bakwai a kwance a asibiti tukkuna ta warware sosai kullum sai na je na dubata ban taba d'auke rana d'aya ba. Inna Uwani ta zo kwana biyu da suka wuce babu yabo babu fallasa tsakanina da ita Muna gaisawa sai dai babu wani sakin jiki da juna. Yara ma sun je sun dubata sau d'aya masu aikina ma haka.
ranar da suka bata sallama da wuri na je ban kuma jima ba na dawo gida.
Sai dai ganinsa tsaye a bakin gate din gidan Hajiya Maryam shi da wasu 'kwarori guda biyu da jami'an tsaro abin ya ba ni mamaki da d'an tsaro duk da yana da masu tsaro a kewaye da shi da gidajensa amma ganin shi da wad'annan da kuma 'kwarorin sai abin ya ba ni tsoro yanayin da suke ciki ya nuna kamar akwai matsala.
Na hangi fitowar Nusaiba da Adam daga cikin gidan fuskokinsu dai babu nisha'di. Sukairaju ya shige da motar ciki bayan an bud'e gate din hankalina ya kasa kwanciya ko da na shiga ciki gidan kai tsaye d'akina na zarce ban bari sun san na dawo ba. Allah dai yasa lafiya.


Na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba

Minti goma sha biyar a tsakani ya shigo ya biyo ni har cikin d'akina yana ta fad'a. Ashe wad'an-nan k'warorin abokanan business din Nabila ne mazauna jahar lafia sun kashe wani d'an uwansu suka gudu ita kuma tsautsayi da azal ya sanya da suka kira ta a waya suka ce sun shigo Abuja za su zo su yi magana akan wata harka ta alheri ta gayyace su zuwa gida a jiya da daddare a yadda take fad'a cewa ba ta ta'ba tunanin za su kwana ba balle har ta ba su mafaka domin da suka gama tattaunawa ta yi ta yi da su su tafi suka 'ki suka wayi gari a zaune. A jiyan da daddare akwai wanda jama'an tsoro suka sanya domin yi musu bincike da yake Ubangiji Allah baya bacci kuma cikin gaggawa yake tona asirin hakkin rai mutumin ya gaya musu ga inda mutanan suka fake nan. Abinda ya tsananta domin har itama Nabilan na cikin tasku saboda bincike dole ya bi ta kanta tunda sun ce har da ita da kuma sanya hannunta alhalin k'arya suke yi. Tana cikin gidan taki fitowa sai da ta ji duka tukkuna yanzu sun tasa keyarsu gabad'aya can garin nasarawa lafi'a. Allah Ya tsare mana imaninmu.
Da ya gama gaya mini ya shige toilet domin yin wanka ya barni da tu'ajibi da mamaki wai 'ya mace ta'ki kama kanta saboda masifar son abin duniya. Ba a hana mace yin kasuwanci ba amma a yi mai tsafta da aji da kuma ilimi. Gashi dai sun dilmiyata cikin case dinsu bayan su kansu sun san bata da hannu a ciki. Wannan shine
abinda ya yi rayuwar Hadiza illa kenan.
Ya fito daga toilet din yana cigaba da fad'a tare da jaddada mini cewa ba zai ta'ba sanya hannunsa a cas din ba tunda ba shi ya aiketa ba hanya yake nema dama tunda rayuwar da ta d'aukarwar kanta kenan shikkenan babu ruwansa abinda dama ya sanya shi barin ta a gidan a zaune saboda yaran sun buk'aci hakan ne shikkenan gida za a rufe idan Salim ya tashi aure yana da ra'ayin gyara wani bangare daga ciki sai ya zauna da iyalinsa tunda sun ce ba sa so a sayar kuma ba sa so zuba y'an haya. Adamu zai ba shi za'bi zaman kano gidan Hajiya Ayya wurin kakarsa ko kuma zama anan wurinmu duk wanda ya zab'a daidai ne.
Ko da ya tambaye shi kuwa yaro ya ce kano gidan Hajiya Ayya ko gidan Hajja. Ya ce gidan Hajja ya fad'i hakane saboda Yusi ya ce zai yi waya da kakar tasu domin sanar mata da halin da ake ciki.
Lamarin nan na jima yana ba ni mamaki da tsoro duniya ta lalace yanzu mutum akan abinsa dukiyarsa sai a halaka shi tunda bincike ya tabbatar da cewa akan kudinsa ne suka kashe shi gashi dai tare suke su uku kuma kowa ya sansu a tare amma an wayi gari sun kashe shi. Abin tausayi da jimantawa ita Nabilan da Allah ne kadai zai fitar da ita. Shiyasa ko abota za ka yi kasan da irin wad'anda za ka yi.
Saurin yarda da sakin jiki ga mutumin da baka sani ba sai ya janyowa rayuwarka barazana. Allah ya k'ubtar da ita tunda babu gata ta ko'ina ba uwa babu uba, yan kudin nata da take nema ba su isa su fitar da ita daga wannan masifa ba ga yaranta biyu duk maza sun zama yan samari wata'kila ganin sakarcin da take yi ne ya sanya ubansu kar'be su suna can jos din tunda a can ne ta yi auran kafin ta fito.

Yau kwanaki biyar kenan da fitowar Hauwa daga asibiti Hajja ta zo dubata a gidana ta sauka sai da ci abinci tukkuna ta huta sannan muka nufi gidan tare tunda ni ma tun bayan an sallamota daga asibitin ban sake duba ta ba.Kafin mu isa gidan Hajja na jaddada mini jikin Gwaggo babu dad'i kwanakin nan itama tana fama domin ta kwanta a asibiti na kwana uku kafin a sallamota ban ji dad'i ba kuwa ba a gaya mini ba Hamusu bai sanar da ni ba haka zalika ma Yusi. Raina ya baci sosai amma ban nuna mata ba tunda babu halin kalubalantarta. Duk da saura kwanaki mu shiga ramadan hakan ba zai hana ni shirin zuwa dubata ba jikinta ba ta d'an jima a tsaitsaye tana ciwo ashe har da kwanciya a asibiti gashi masu aiki na shirin tafiya umara kamar yadda maigidan ya yi musu alkawari a farkon farkon watan azimi.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*166*
Sosai na yi dana sanin bin Hajja zuwa gidan Hauwa da ina da masaniyar abin da zai faru. Wannan shine dalilin da ya sa da yawa wasu daga cikin mutane ba su son yin auran zumunci a tsakanin yaransu koda kuwa akwai soyayya mai karfi a tsakanin yaran akan samu suka da kalubale daga wurin dangi kowa na fad'in albarkacin bakinsa akan zumuntar da za a had'a ta aure wadda ake da burin ta d'ore ta ginu ta kuma kara karfin zumunci tare da albarkar haihuwar yara.
Mafiakasari shi auran zumuncin bai fiye yin armashi ba wani tun daga farkon k'ulla shi ake fara cin karo da rigingimu mabambamta wanda ka iya janyo rabuwar kai da tashin hankali tare da zama a teburin sulhu idan ma ba akai zuciya nesa ba har hukuma kan iya shiga domin kawo sasasanci dalili daga kowane bangare yana ganin ba a yi masa daidai ba.
Wannan tashin hankalin ya sanya da yawa iyaye suka gwammace su aurawa na waje yaransu domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali duk da cewa rikicin aure da matsaltsalunsa abu ne da ya zama ruwan dare ko da babu dangantaka a tsakani a duniya

Please Login or Register in order to submit comment