Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ai ban ga dalilin da zai sanya ki kashe wayarki ba."
Na ce." E, to ba yaji na yi ba amma dai Ina tsammanin ba ni komawa Abuja kai tsaye daga na bar nan kano zan sauka gidana na sharad'a tunda ya'ki fahimtar abinda nake nufi."
Ta gyad'a kanta tana cewa." Ba ni son hakan ya haifar miki da wata matsalar Amina amma ni kaina a son raina nafiso a raba muku muhalli sai hankalina ya fi kwanciya.
Na furta." Duk mai hankali da tsinkaye abinda zai duba kenan matsawar muna zaune a inuwa guda da Hauwa ba za a taba samun zaman lafiya ba Shima ba zai huta ba tunda ni dai na zame mata ciwon ido anti Yagana wallahi har mamakin yadda Hauwa take zafafawa kanta a kaina ni kuma ba ta raina kwata kwata ban kuma dauketa a matsayin kishiya da zata daga mini hankali ba. Kawai yanzu nutsuwa da kwanciyar hankali nake buk'ata shiyasa na ce ba ni buk'atar zama da ita a gida daya."
Ta furta." Hakane akwai hujja mai karfi a tare dake ni ma ina bayanki amma yanzu tunda ya ce ki kunna wayarki za ku yi magana ki kunna din mu ji mai zai ce."
Na ce." To shikkenan zan kuna."
Sai da muka gama aikin gyara kajin tukkuna ta d'ora a wuta na wanke hannuna da omo sannan na koma d'akin na d'auki wayata na kunna minti goma sha biyar a tsakani ya kira na daga a nutse na yi sallama ya amsa na gaishe shi nan ma ya amsa babu annasuwa. Kafin ya d'ora da fad'in." Yarinyar Minal tun bayan da suka dawo daga makaranta ta samu ba kya gidan kwanta zazza'bi ya rufe ta ya hau ya sauka har takai da sai da aka yi mata karin ruwa Amina ida ta rasu wallahi ba zan yafe miki ba."
Gabana na d'an fad'uwa na ce." Ban gane abinda kake nufi ba."
Ya ce." Kin ji abinda na fad'a Amina ai kin san ba ki da gaskiya shiyasa ki ka kashe wayarki tsayin kwana biyu."
Na ce." Mayya ce ni ma shiyasa na kama kurwar Minal na taho da ita nan maiduguri to don Allah idan ta rasu ka d'aure ni har igiya ta yi rara."
Ya ce." Abinda za ki ce kenan?"
Na ce." To me zan ce maka ka ce yarinya bata da lafiya saboda na taho da kurwata idan ta mutu ba za ka kyale ni ba to ka d'aure ni don Allah shine abinda za ka yi."
Ya kashe wayarsa jin yadda na bud'e masa wuta idan ba rashin mutunci ba kawai ya kira ni yana ko'karin gaya mini magana ni na d'orawa yarinyar ciwo wane irin bala'i ne wannan ne."
Tsabar takaici da damuwa ban iya zuwa dubiyar Dada ba a ranar saboda jikina ya riga ya gama mutuwa da rashin lafiyar yarinyar da kuma abinda ya gaya mini a kan hakan.
Can wajen sha d'aya ya sake kira na na daga ban ce masa komai ba na ji yana fad'in.'" Za ku gaisa ko?'' Da yaran yake na ji muryar Usaina tana kiran Mama na ce." Naam Usai ina Hassana." Ta ce gata nan." Minal fa?"
Ta ce." Ta yi bacci ta fad'a muryarta tana rawa.
Na ce." Ya jikin nata."
"Da sau'ki ta fad'a kamar za ta fashe da kuka. Na ce." To ba ni Hassana itama mu gaisa ko Ina Khalil?''
Ta ce." Yana 'kasa da Hassana." Na ji maganarta. "Mama ina yini."
Na amsa "Lafiya lau Hassana ina dariyar da babu nisha'di na ce." Ya kuke ina Mairo." Ta ce." Tana can k'asa Minal ba ta da lafiya."
Na ce." Allah Ya ba ta lafiya na kusa dawowa."
Da sauri ta ce." Yaushe?"
Domin na kwantar musu da hankali na ce." Gobe." Ina ji suka fara tsalle da dariya. Ya kar'bi wayar daga hannunta yana fad'in." Me yasa za ki gaya musu haka Amina kwananki nawa da tafiya."

littafin nan na kudi ne yar uwa kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

A tak'aice na ce." Biyu." Ki ka ce za ki yi sati daya ko kin fasa."
"Ban fasa ba." Na fad'a kai tsaye ina ji yana magana da yaran kan cewa su sauka k'asa wajan Mairo. Na daina jin motsinsu. Ya cigaba da cewa kin ga kuwa idan ba ki dawo gobe ba za su d'auke ki makaryaciya domin kuwa yaro baya mance magana kina dai jin tsalle da murnar da suke yi."
"Umm! kawai na ce na yi shiru.
Ya d'an yi gyaran murya kafin na ji shi yana fad'in." Yanzu kin tsane ni Amina ban yi miki komai ba wai menene lefina anan tare dake duka aka dinga wannan d'auki ba dad'in akan kwantar da ni da Maryam ta yi Malamin nan ya tsaya tsayin daka a kaina har sai da ya tabbatar da tabbatuwar lafiyata na cigaba da rayuwa da iyalina. Yanzu don Allah bai cancanci komai ba ban yi tsammanin zan samu wannan turjiyar daga wurinki ba tunda ai da farko ba haka ki ka nuna mini ba."
Na ce." Har yanzu kuma ba ni da damuwa akan hakan ba. Ai kai ka ga zaka ka iya amma dai Ina gaya maka ba zan zauna a gidan da zaka haye kan k'aramar yarinya kamar Hajara ba babu ni a cikin wannan rashin sanin ciwon kai ba kuma zan kara had'a inuwa da Hauwa ba. Ka canza mini mazauni idan ya zama lallai sai ka zauna da ni."
"Shikkenan za ki zauna gidanki na kano tunda hakan ki ke so amma ki sani za ki dinga d'aukar dogon lokaci kafin ki gan ni."
Na ce." Babu damuwa ai." Ba tare da ya sake wata magana ba ya kashe wayarsa.
Da safe da wurwuri na je na duba jikin Dada alhamdulillahi ta warware sai dai jikin girma idan abin ya motsa mata amma yini muka yi muna hira tana gaya mini abin alherin da ya yi musu a lokacin da ya zo dubata wattanin baya.
Bayan sunan Fadila da kwana biyu na fara shirin tafiya tunda mun gama magana dashi kan yanke zamana a kano abinda dai ban yarda da shi ba shine barin yarana a gidansa na abuja da Hauwa dole za mu zauna akan hakan sai ya ba ni yarana wallahi ta ri'ke na ta.
Ya kira ni yana gaya mini na tafi gobe domin shi ma a goben yake so ya shiga garin kanon saboda juma'ar da za ta zo za'a yi d'aurin auran a Bunkure kamar dai yadda ya gaya mini da farko.
To kawai na ce masa. Ban kuma tafi a ranar da ya ce ba sai a washe garin ranar tukkuna Babansu Fadila da kansa Ya d'auke ni a mota zuwa kano.
Gidan Hajja na yada zango anan shi ma ya kwana da sassafe yana karin kummalo ya d'auki hanya.
Hajja ta dinga rarrashina tana tausata ban san me ya gaya mata ba amma yanayin yadda take rarrashina ya nuna mini cewa kamar ya gaya mata wata magana a kaina wadda take nuni da cewar ni ce yanzu ba ni son zaman lafiya tunda Hauwa ai ta mato a kan sonsa kuma dama kulawarsa da tarasa ne a baya ya sanya take yin hauka da tsananin kishi yanzu kam tunda tana samun abinda take so a wajensa yana juyata son ransa ba zai fad'i aibunta ba. Kuma a lokacin da ta fahimci akwai rikici a tsakaninmu ta bud'e wuta da kissa da ko'karin kafa kanta a wajensa.
Ban katse ta ba na yi shiru Ina ta sauraranta tana cewa itama ta fi so na zauna anan din Hauwa da amarya kuma su yi zamansu a can abuja
Sai yamma direbanta magaji ya d'auke ni a mota lokacin shi bai dawo daga bunkure ba duk da ba ranar ne daurin auran ba na lura da yadda yake ta rawar jiki da kai kawo har an yi masa invitation irin na wata da kuma na kati ya d'ora a status dinsa.
A daran na kira Sahura na ce ta zo gobe da wuri dole sai ta taimaka mini mun gyara gidan.
Can misalin sha daya saura na dare ya shigo gidan.
Na gama shirin kwanciya ya shigo dakin ya same ni. Ya zauna gefena da alamar gajiya a tare da shi da kuma yanayi na damuwa da ta riga ta zame masa jiki
yadda bai yi mini magana ba haka ni ma ban yi masa magana ba d'akin ya d'auki shiru na tsayin wani lokaci
Na ji yana fad'in." Amina ya kamata mu yi gwajin nan na jini ( gyonotp) da yarinyar nan ko?"
Shiru na yi ba tare da na ce masa komai ba. Ya dube ni yana fad'in." Yadda Malam D'aha ya d'aukaki wannan lamarin ba na tsammanin idan an ci karo da wata matsalar wadda ka iya rusa auran ya janye ku'dirinsa sanin halinsa na magana d'aya da kuma 'kin yarda da zamani da hasashen yahudu da nasara........
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*147*
Na d'an jima ina kallonsa tare da yin nazari a kan maganarsa na kasa tantance shin shawarata yake nema ko kuma umarni. Sai kawai na yi shiru ba wai don ba ni da amsar da zan bashi ba maganar ce kawai ta sake jefa ni cikin mamaki tunda har yana maganar gwajin jini (gyonotype) ya shirya kwanciya da yarinyar duk da k'arancin shekarunta kuwa.
Na yi shiru tare da juyar da kaina saboda tsabar takaici. Ya sake maimaita mini maganar . Sai na dube shi a sakarce na ce." Kai duk shige da ficen da kake yi ba ka yi gwajin jinin ba."
Ya d'an b'ata ransa yana fad'in.'' Amina ba kya yi mini lafazi cikin dad'in rai ko kina magana da sa'anki ne abubuwan fa da ki ke yi sun take shari'a kuma suna yi yawa."
Na d'an daidaita yanayina ina ce wa." To shikkenan na ji yanzu me kake so na ce?''
Ya sauke ajiyar zuciya tare da matso ni sosai ya kama hannuna ya rike sai kuma ya had'e yatsunmu ya matse gam. A dan tausashe ya furta." Ke ce abokiyar shawarata shiyasa da na fara wannan tunanin na tuntubeki dacewar yin gwajin jini ko ya ki ka ce."
Wani abu ya sake tokare mini wuya."
A tak'aice na ce." Hakan yana da kyau."
Sai ya cigaba da cewa." Ba ni fatan sake auran macce wadda za mu yi ta haifar yara masu lalura Amina wannan cikin da kike d'auke shi yana raina koyaushe da tunanin abinda za ki haifa mini nake mai lafiya ne ko mara lafiya saboda wannan ciwon gaskiya ne akwai shi. Ba ni so a 'daura auran nan jinina dana yarinyar bai jitu ba ta zama k'aramar bazawara domin ba zan iya kar'bar kaddara a karo na biyu ba wannan shine."
Na dai yi shiru ban ce komai ba ba wai don ba ni da abin fad'a ba.
Ya sake matsowa jikina yana magana can kasa." Ya ki ke ganin ya za mu yi,?"
Na dube shi babu yabo babu fallasa na ce."Fisabillahi me kake so na ce akan hakan?"
"Ki ba ni shawarar yadda zan yi." Ya fad'a yana d'ora bakinsa a dokin wuyana.
Na ce.''To shawarata ku je ku yi gwajin jinin ina ga kamar zai fi alheri."
Na ji hucin numfashinsa yana cewa." Idan an samu matsala na yi yaya da malam 'Daha."
"Sai ka yi masa cikakken bayani zai gane!" Na fad'a ina d'an janye jikina jin wani abu ya fara yi mini yawo.
Ya ce." Ba zai yarda ba Amina."
Na ce." To gaskiya kaima kana da lefi me yasa tun farkon fara maganar ba ku yi gwajin ba idan an tabbatar da daidaituwar jini sai a yi godiya ga Allah idan kuma jinin bai inganta daidai yadda ake so ba sai ka datse maganar da wuri ka kawo masa hujjoji da misalai."
Ya furta." Ba ni da nutsuwa fa Amina tun sanda ya ba ni kyautar yarinyar na rasa sukuni gabad'aya domin ni kaina ba ni son auran irin k'ananu haka koda da k'addarar sake wani auran a tare da ni wadda ta fita shekaru zan aura amma wannan tayi yarinyata da yawa."
Na ce." Hakan kuma bai hana ka nemi shawara wajan gwajin jini ba ko duk da ta yi yarinyata ai ka shirya takarta ko ba haka ba ne."
Shiru ya yi bai ba ni amsa ba.
Wai ni zai yi wa kalaman yaudara na janye jikina ya sake rukunkume ni yana tatta'ba wasu sassa na jikina tare da sauke ajiyar zuciya.
Gabad'aya nema yake yi ya daga mini hankali a halin kuma da nake ciki ba ni buk'atarsa ko kad'an jikin dai yana so walwala da annashuwar da zata bari a tari lamarin ne babu.
Babu yadda bai yi da ni ba a daran a kan dole sai ya kwanta da ni na ce a a gajiye nake ba zan iya ba.
Dole ya ha'kura da asuba ya sake nemana da rarrashi da kwantar da kai ya fara ko'karin gaya mini wasu maganganu wanda suka danganci Hauwa na katse shi da sauri na nuna ba ni so ban san yaushe ya zama munafikin namiji ba ina ruwana Hauwa tana gamsar da shi bata gamsar da shi ba abinda ya dame ni ba ne.
Na ci da kulafuci kamar dambun kuturu ya ma'kale ni na kasa motsi babu yadda na iya haka nan na kyaleshi ya yi abinda yake so kamar zai shid'e saboda gigita lissafinsa gabad'aya ya kwance.
Da kaina na shiga kicin tunda ya sanya an kawo mini komai na bukata. Na soya doya da kwai da tea sannan na dafawa kaina indomee.
Nan d'akina muka yi breakfast din babu yabo babu fallasa amma dai na kasa sakin jikina duk zantukan da yake akan auran nan da zai yi kawai ina jinsa ne da kunne dalili nema yake yi ya rainawa mutane hankali tunda yadda yake nunawa ko jininsa dana yarinyar bai daidaita ba zai iya yin jayayya da malamin ba yadda tun farko ya amince masa to abu ne mai wahala daga baya ya je ya ce masa ga matsala wadda daga baya turawa suka bijiro da ita tunda ai ko a zamanin annabawa ba a san da wani gwajin jini kafin aure ba haka kuma duka iyaye da kakanni suka ta so.
Da haka dai ya yi wanka ya kintsa ya fita yana gaya mini ya yi baki daga kamaru idan ya gama dashi da wuri zanje bunkure a takaice na yi masa addu'ar dawowa lafiya
Sai wajan daya da rabi Sahura ta zo lokacin ne ta taso daga aiki. Sai bayan da muka ci abinci muka yi sallah tukkuna muka fara aikin gyaran gidan wanda kusan zan iya cewa itace karfin aikin ta shasshare mini ko'ina tas aka yi mopping gidan ya dawo hayyacinsa.
Sannan fa muka zauna ina zolayarta ta yi ki'ba tana ta'be baki kuma da gasken ta yi kiba wallahi alamu sun nuna bata da damuwa tana cin gashin kanta. Idan farko akwai damuwar yanzu makomar auran Idiris ta bayyana ya sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali domin dai alkali ya tilasta shi sakin yarinyar kamar yadda iyayenta suka buk'ata dalili shedu sun shaida babu abinci ingantacce a gidansa sannan kuma alamu na nuna cewa shi din yafi karfinta ta fannin auratayya. Ya kuma yanke masa kudin da zai dinga aikawa yarinyar na goyon ciki har sai ta haihu ta shayar masa da abinda ta haifa kafin ta yaye ya kar'bi d'ansa a bisa adalci.
A wannan matsayar aka tsaya da shi. Tana gaya mini da gumu ta yi gumu ya rasa yadda zai yi ya gaya mata halin da ake ciki.
Na ce." To Sahura tunda dai ya yi nadama sai ki yi hakuri don Allah kada dukan ya yi masa yawa ki kaddara cewa rabon haihuwa ne ya sanya shi rakito auran yarinyar nan."
Ta ce." Ai ban hana shi kwana a gidana ba Amina kwanciya da ni ne na ce ba zai yi ba. Kuma gidan da ki ka ba ni ya balle ni kwado ya sanya matarsa sun kwashe kaya sati biyu da suka wuce na sanya a zuba mini 'yan haya a ciki. Abincin dai ina ba shi idan na yi ga waje nan ya kwanta ya tashi amma babu mu'amula ta aure.
Na ce." To kin sake bashi lasisin yawon dare kenan?"
Ta'be bakinta ta yi ba tace komai ba. A daidai lokacin kira ya shigo wayata ina dubawa na ga maigidan ne na ajiye ta katse ya sake kira na d'auka tare da daidaita maganata. Na ji yana fad'in." Na fasa zuwa bunkuren nan Amina gani nan dawowa gida."
A tak'aice na ce." To.'' na riga shi kashe wayar na ajiye a gefana ina tsaki
Ta bata rai tana fad'in." Menene haka don Allah."
Na ce." Da aka yi me?"
Ta gyad'a kanta tana cewa." Wallahi tallahi ki ji tsoron Allah akan mutumin nan Amina."
Sosai na zuba mata Ido da mamakin maganarta haka kawai ba ta san irin zaman da nake yi dashi ba tana cewa na ji tsoron Allah akan sa. Ko da yake dama can ita 'yar dakinsa ce bata ta'ba ganin lefinsa. To mai baka kuma ya ninke munanan halaye ya bayyana kyakykyawan ya za a yi ta fahimci aibunsa tunda ba tare take rayuwa da shi ba.
Ta cigaba da cewa." Menene abin tsaki don ya gaya miki cewa zai dawo gidansa ne fa."
Na ce." Hajiya kamata ya yi ki tambaye ni dalilin dawowata nan ba kawai kai tsaye ki fara tuhumata ba ke matsalata dake kenan ba kya taba ganin lefinsa.
A d'an sanyaye ta ce." Menene to?"
Duk abinda yake faruwa na gaya mata tun daga kan matsaltsalun da yake tsakani na da Hauwa da auran da aka bashi a bunkure.
Ta yi sakato da baki tana kallona gabad'aya bakinta ya mutu da kyar ta ce ni haukan da Hauwa take yi bai dame ni ba Amina sai maganar auran nan da ki ka ce zai yi ai na gane yarinyar da ki ke gaya mini ko ba itace ta kawo mini abinci a lokacin da naje ba."
Na ce." E ita ce.''
Ta zura mini ido tana kallo kafin ta ce." Ai ko nono ba ta dashi wannan yarinyar ba ta isa aure ba don bata da 'barage ba na tsammanin ba ta fara jinin haila."
Na ce." To ya kar'bi dai auranta sai ya cigaba da raino amma dai da kamar wuya tunda d'azu yake gaya mini wai za su yi gwajin gyonotype kin ga kuwa da sha'awar sabon waje a cikin ransa mussaman budurcin k'aramar yarinya irin wannan ba na tunanin zai zura mata tsayin wasu shekaru."
Ta ce." Don Allah ki daina fad'in haka Amina kunya ma nake ji wallahi yanzu shi sai ya iya tu'bewa a gaban wannan tatsitsiyar?"
Na ce." To me ye a ciki Amina wallahi ki daina mamaki da sha'anin maza abu ne mai sau'ki a wajansa."
Ta yi zugum tana dubana kafin ta ce." Lallai mutumin nan ya ba ni haushi wallahi gaskiya abin bai yi mini ba ya kuma shirya cinye muku fuska yarinyar 'yar cikinku ta kalleku a banzance tunda ai duk ranar da ya kwanta da ita to gabad'aya ba ku da bambanci wallahi.
Na yi shiru Ina nazarin maganarta tabbas hakane ranar da ya kwanta da Hajara to itama daga lokacin za ta ji kanta a matsayin matar gida daidai da kowa. Ba ni fargaba akan tarbiyar yarinyar amma yau da gobe idan zama ya yi zama dole wasu daga cikin d'abiunta su canza dalili itama tana ji kanta cewa matar gida ce."
Sahura bakinta ya mutu duk kaud'in nan nata a kansa bakinta murus ya yi tana jin haushin haka ta yi la'asar ta yi mini sallama ta tafi. Ba ta jima da barin gidan ba ya dawo. Ya yi wanka a dakinsa na sama ya canza ya kaya na shan iska ya sauko kasan ya same ni zaune a kujera Ina kallo ya zauna kusa da ni yayin da kamshin turaransa ya game wajan gabad'aya.

Na dube shi kad'an kafin na janye idona ban ce komai ba.
Sai ya riko hannuna yana cewa." Ta karfi da yaji dai kin zama bebiya giwa wai me ya yi zafi ne uhum?''
Ban ce komai ba na zare hannuna. Ya kamo yatsan da ya sanya mini zoben nan ya sumbuta ya ciro shi daga yatsansa ya sake mayar mini yana fad'in." Ban yi zuciya ba amma ya kamata ki sassauta mini ki yi mini adalci akan duk abubuwan da suke faruwa ke kan ki kin san abinda ki ke yi ba daidai ba ne ko?"
Na ce." Adalci wane iri kake so na yi maka na hana ka kar'bar auran da aka baka ne? A lokacin daka gaya mini addu'a na yi maka kuma dole sai ka yi hakuri a wannan lokacin tunda ni kaina ba jin dad'in jikina nake yi ba."
Ya d'ora hannunsa saman cikina yana fad'in." Na sani amma me yasa ki ka cire duk wani subsidy a kaina kin daina sona ne."
Ban iya kallonsa ba saboda takaici. Ya juyo da fuskata yana cewa." Zan fasa auran nan fa wallahi ba zan iya ba."
Na yi shiru dai ban ce komai ba daidai lokacin ne Hauwa ta kira shi yana d'agawa ta fara kuka tana fad'in." Minal ce ta suma!"
Ya ki'dime sosai hannunsa har yana karkarwa yana tambayarta ya ake ciki yanzu. Yadda take bashi amsa ya sanya na fahimci cewa k'arya take yi wallahi.
Kawai dai za ta fake da ciwon yarinyar ne ta daga masa hankali.
Ya kashe wayar da tsananin tashin hankali yana fad'in." Ki yi wa Allah da annabi ki tashi mu tafi yarinyar nan Minal tana sonki Amina kada hakkinta ya kama ki tunda ta dalilinki komai yana iya faruwa kada mu yi rashinta.
A nutse na ce." Ka je ka kawo mini su nan gabad'aya zan ri'ke su Ina nan akan bakana ba ni sake zama da Hauwa. Idan kuma za ka canza mata gida ni ta bar mini wanda take ciki sai na koma."
Ya ce." Ba ki ji an ce suma take yi ba. Na gaya miki cewa jikinta ya'ki dad'i wallahi tunda ki ka bar gidan nan."
Na ce." Ni da hankalina sarai babu abinda Hauwa za ta k'irkira ya firgita ni. Minal kuwa Ina tsammanin ma uwarta ba ta kaini sonta ba."

wannan littafin dai na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya yi shiru yana kallona na wani lokaci kafin ya haura samansa. Na dubi agogo biyar da rabi jim kad'an ya sauko cikin manyan kaya babbar riga da 'yar ciki.
Cikin zuciyata na ce." Aiki ya same ka in dai Hauwa ce sharrinta yawa gare shi neman kudi ma wataran sai ka yi da gaske za ka yi."
Ya tsaya gabana yana fad'in." Rarrashi da ban ha'kuri babu irin kalar da ban yi miki ba. Ba a yi maccan da zan dinga kwantar mata da kai tana gara ni kamar gare-gare ba. Ki sani Amina kina da magabata kuma hukuncin saki a hannuna yake sai na ga dama zan yi. Wallahi tallahi zan d'auki mummunan mataki akan abinda ki ke yi mini.
Na ce." Sanar da magabatana halin da muke ciki shi zai kara dagula maka lamari domin wallahi ba zaka taba samun kaina ba. Shekara nawa ina ha'kuri dakai tare da bin umarinnka ina so ko ba ba na so. So kake yi na zauna da Hauwa wataran ta d'auki makami ta farauci rayuwata. Ko za ka gaya mini cewa har yanzu ba ka fahimci irin tsananin kiyayyar da take nuna mini ba. Ka kawo mini yarana na ri'ke a hannuna domin ba zan iya barin su a tare da ita ba za ta iya yi musu lahani ta kowace siga.
Idan ba za ka iya rabuwa da ni ba to bar ni anan din ni wata daula ba damuna ta yi ba. Idan za ka shekara ba ka zo in da nake ba babu damuwa na sahale maka."
Ya cire gilashin idonsa ya sanya hankici ya goge ya mayar dashi idon nasa. A d'an rikice ya sake cirewa ya goge kafin ya sake mayar dashi. Na d'auke kaina a raina ina fad'in zautuwa yanzu ka fara yin ta ka wani binjimo babbar riga. Gaskiya na karyawa Hauwa d'ankwali a wannan ga'bar da alama ta d'auki hanyar rama kashin da ya bata. Na yarda Minal bata da lafiya amma haka kawai zuciyata ba ta amince mini

Please Login or Register in order to submit comment