Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za'ba, Allah Ya saka mini."
Ya sake kai mata mari ta goce tana fadin." Ni ma rabon shan wahala ne ya sanya ni auranka, kuma in sha Allahu mun rabu kenan har abada, kuma ka sani cewa wannan masifar daka 'kunsa mini sai ta bi rariya."

Tsakaninsu na shiga duk kuwa da rashin kuzarin da nake ciki ina fad'in." Menene haka don Allah, kada fa zuciya ta d'ebe ka ka zo kana nadama, me ta yi maka kake dukanta."
Ya ce." Matsa gefe Malam ina ruwanki wa ma yace ki fito?"
Na ce." To shikkenan had'a mu gabad'aya ka doka sai ka huce takaicinka, ai ba da hannu za ka yi dukan ba kasa wayar redio kawai."

Baba Tabawa ta dinga fad'in." Don Allah Yallabai a yi hakuri babu girma a wannan lamarin kada yaran nan su ankara su fito, ka yi hakuri a matsayinka na babba kuma jagora."

Cike da b'acin rai ya furta." Baba wad'annan matan ba su da mutunci wallahi sun hana ni nutsuwa mussaman 'yar iskar yarinyar can Hauwa ta rikita mini gida menene amfanin zamana da ita tunda ba ta son zaman lafiya."

Na ce." Ita kuwa take da amfani wallahi ka je ka 'kara tunani idan kana cikin hayyacinka Hauwa ba abar wulakantawa ba ce."
Ya yi shiru yana muzurai kafi ya dubi Baba Tabawa tare da ce wa." Ki had'o mini kan yaran nan ki biyo bayana da su. Da sauri cikin bin umarni ta ce." In sha Allahu ranka ya dad'e.
Ya juya ya fita da saurin gaske.
Na dubi Hauwa da mataccen jiki sai kuka take yi gabad'aya ta fice daga hayyacinta. Kafadarta na dafa ina fad'in." Me ya faru?"
Tana goge fuska ta ce." saki na fa ya yi kuma na saku har abada wallahi."

Ta wuce dakinta da sauri. Cikin sagewar gwiwa na bi bayanta ta shiga bandaki sai na zauna gefan gado har ta fito wanka ta yi ta fara shiryawa tana yi tana kuka. Na ce babu fa inda za ki je wallahi ai saki daya ne ki zauna ku daidaita."
Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba kuma ba ta fasa shirya kayanta cikin akwati ba.

Na yi jigum da mataccen jiki, wato dai mutumin nan in dai akan sha'ani na Momi ne baya ji baya gani, ai ban ta'ba tsammanin zai iya sakin Hauwa ba, a iya tunanina je ki gida ki huta kawai zai yi mata tunda itama zahiri ta yi abubuwa da yawa da za su tunzura shi idan kuma har an yi duba da matsananciyar dangantakar da take tsakaninsu tafi karfin wannan tozarcin duk kuwa da abinda za ta yi masa karfin zumunci da albarkar zuri'ar da ta ratsa tsakaninsu ba ta cancanci hukuncin saki daga wajensa.
Ina zaune zukud'un ina tunani lallai kamar maganar Hauwa da 'kamshin gaskiya ko dai matar nan ba a haka ta bar mutumin nan ba, kansa a juye yake wallahi domin gaba da gaban da muke yi dashi yanzu na karance tsaf ba a nutsuwarsa yake ba
yakan rufe ido ya yi cin mutunci ga kowa muddin aka ta'ba ta ko wani abu da ya dangance ta......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.Normal what'sapp Gruop kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*


*TALLAH*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=ØLÜ
*91*
Don kyautawa tabbas Hauwa bata kyauta ba ni ma tun a wurin na nuna mata rashin goyan baya, kuskure ne mai k'arfi k'azafi ko tabbatar da abinda ba ka da shaida akai. Iyayen baiwar Allah nan daga ni har ita ba mu da masaniyar abinda ya kashe su. Mijinmu ta aura kawai bayan haka duka ba mu da wata ala'ka da juna. Wata'kila ita Hauwa ta jima tana bin 'kwakkwafi akan Momi din idan ba haka ba ta ina take samun irin wad'annan labaran masu muni. Tabbas idan gaskiya ne to Momi abar gudu da k'yama ce, idan kuma kishi ne ya rufe idon Hauwa ta k'irkiro maganar ta fad'a bata kyauta ba ta aikata abinda ba shikkenan ba, amma a ganina a matsayinsa na namiji jagora mai nisan tunani bai kamata ya zartar da wannan d'anyan hukuncin ba.
Gabana ya buga da karfin gaske a lokacin da na tuna irin abinda yake kwance ciki ya zube na nasa yara a mota ba tare da yawunsa ba. Idan ya sake ni akan hakan ba zan wani damu ba, ai na yi abinda na yi daidai gwargwado sai na ha'kura da auran ma gabad'aya idan na mutu na riski Yaya Aminu a matsayin matarsa ta aljanna tunda ban tafi da zargen igiyar auran wani ba.
Sai dai tsorona da fargabata shine ina shakkun ya sanar da Baban Saude domin kuwa yanzu shine yake tsaye akan al'amarina tun bayan sasancin da ya yi mana a shekarun da suka gabata. Kuma ba tun yau ba na lura da k'akkarfan zumunci da abotar da ta 'kullu a tsakaninsu. 'Bacin ran Baban Saude da tijararsa ita kadai nake gudu amma don ta kalubalen wannan mutumin baya damuna.
Jan kofar da Hauwa ta yi shine ya dawo da ni hayyacina na daga kaina da sauri na ga gilmawar fitarta da akwati madaidaiciya. Da azama na tashi na bi bayanta Allah Ya sa falon babu kowa tunda ya kwashe yaransa Baba Tabawa kuma tana dakinta. Na ri'ke akwatin ina fad'in." baki da hankali Hauwa ina za ki je a wannan daran ki yi tunani fa a abuja ki ke."
Ta ce." Sai me idan a Abuja nake zan iya kwana a tasha a halin yanzu domin na yi rantsuwa ba zan kara kwana a wannan gidan ba Amina."
Na ce." Ke ma fad'a kawai ki ke yi, an ji ya sake ki, amma ai gidan d'an uwanki ne kuma uban yaranki, sannan addini cewa ya yi idan an saki mace ta zauna a dakinta ta yi idda idan da sauran rabo mijin zai iya mayar da ita kafin kammaluwar iddar don haka babu inda za ki je."
Shiru ta yi tana kallona can kuma sai ga hawaye shaa! murya a sarke ta furta." Wai saki Amina, ni mutumin nan zai furtawa saki ai ina ganin ko zai saki kowa wallahi ni ban cancanci hakan ba.
Murmushi na yi Ina nazarin maganarta, ashe shiyasa ta mike kafa take iyashege saboda tasan ta taka tudu biyu a iya wautarta duk iyashegen da za ta yi masa ba zai iya sakinta ko wani hukunci mai tsauri ba. Rauni da gajeran tunani shine abinda yake cutarmu mu mata amma duk inda muke tunanin akan sha'ani na maza wallahi sun shallake nazarinmu, mussaman na mu mijin da ya kasance makiri. Gabad'ayansu Allah
ya hallicesu ne daban da hallitar mata. Kuma dai dole duk isa da kasaitar mace sai dai idan ba ta yi auran ba.
Ta nemi wuri ta zauna tana share hawaye na zauna gefanta a sanyaye na ce." Ke ma fa kina da laifi Hauwa tunda naga irin abubuwan da ki ke yi nasan lallai akwai abinda zai faru wanda gabad'aya ba zai yi mana dadi ba. Na sha gaya miki ki fita daga sabgarsa da matarsa idan ma tsuguna mata zai dinga yi babu ruwanki da su amma kin 'ki ji, kin ga a cikin igiyoyin auranki uku daya ta girgiza ita nata suna nan daram!
Sai ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka cikin jajantawa kanta ta ce." Sai na gayawa mahaifiyarsa wallahi."
Da sauri na ce." Aikuwa da kin da'bawa kanki wuka Hauwa, kin san ya tsani fa a kai shi k'ara wannan yana masifar 'kona masa rai,kuma yana daya daga cikin abinda ya tunzura masa zuciya tunda ai dawowarsa kenan ya zo ya huce fushinsa a kanki nasan
kuma dole Hajja ta bi ba'asin komai idan har za a yi adalci a lamarin dole ke ma a nuna miki rashin gaskiyarki. Kuma da yawa mutane za su ce kin shigar mini fad'a ne mun taru mun had'e mata kai muna azabtar da ita fassarar da za a yi mana kenan. Ba za a taba duba kisan mummuken da take yi mana ba ta 'karkashinsa tunda sigar da ta biyo wurin wargaza mana zaman lafiya da nutsuwa mai wahalar fahimta ce ba kowane zai gane abinda yake can kasan zuciyarta ba sai Allah."

Ta bude fuskarta tana kallona ta ce." To yanzu ya ki ke ganin zan yi, ni dai wallahi gabad'aya hankali yana gida na gama shirya tafiya Bauchi."
Na ce." Ki yi zamanki ki kyale shi kuma don Allah kada ki sanar da inna Uwani kada sanadiyar hakan zumuncinsu ya raunana kin san mas'ala ta auran zumunci tana da wuyar sha'ani.
A sanyaye ta ce." Shikkenan ba zan gaya mata ba amma wallahi matar nan yadda ta sanya ya sake ni saboda ita sai na wulakantata."
Da mamaki mai yawa na ce." Wane irin wulakanci kuma Hauwa, ai kin gama wulakantata domin duk wasu maganganu masu muni kin jingina mata sai me ya yi saura. Ni fa wallahi masifar nan ta ishe ni haka
don Allah ki samu nutsuwa gabad'ayanmu fa babu yaro, yanzu ke za ki gyara auranki da zumuncin da yake tsakaninki da shi, na gaya miki idan kina so ki samu nutsuwar zuciya don girman Allah ki fita sha'aninsa da matarsa, da sannu idan muna da hakki za mu gan su a rana."
Shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba, ta dai sunkuyar da kanta kasa tana tauna lebanta tabbacin abin da ya yi mata ya yi mata ciwo a zuciyarta.
Sai wajejan tara da wani abu tukkuna muka rabu ta shiga d'akinta da zummar shan maganin ciwon kai ta kwanta dalilin kukan da ta ti'ka, abinci ma ni na bi bayanta da shi kafin na fito falo na zauna na ci nawa muna hira jefi jefi da Baba Tabawa wajan goma da rabi ya shigo Baba Tabawa da saurin gaske ta yi masa barka da shigowa ya amsa babu wata kyakyawar kulawar da yake yi mata domin mutuniyarsa ce sosai a wasu lukutan har barkwanci suke yi ita dashi amma abin mamaki ko yau ni ma ban ji dadin abinda ya yi mata ba.
Ta dube ni tana fad'in." Ni ma kuna nema ku shafa mini kashin kaji Amina, Yallabai kamar fa haushina yake ji duk yadda nake ko'karin ganin na gyara ku abin zai shafe ni.
Yadda ta yi maganar da alhini da damuwa sai ta ba ni tausayi da dariya na d'an yi kad'an kafin na daidaita kaina na ce." To ke ina ruwanki Baba, kawai dai ransa ne a b'ace shiyasa ki ka ga bai amshi gaisuwarki da kulawa ba, kada ki wani damu ai ba ki da lefi."
Ta yi shiru tana jijjiga kai har da tallafe ha'ba. Na yi dariya sosai ina fad'in " Hajiya Baba Tabawa ta mu ta gargajiya."
Ta dube ni da yanayi na zullumi amma ba ta ce komai ba. Daga can barandar samansa na ji maganarsa na juya da sauri yana tsaye hannunsa zube a cikin jallabiyar dake jikinsa ya ce." Zo."
Na yun'kura na tashi da tahamidi da kuma addu'ar rinjiye wannan lokacin nake jira, na kuma ji dad'i da ba a ja dogon lokaci ba gwara a yi ta ta 'kare kawai.

Na d'auka idan na shiga d'akin zan gan shi a rikice cikin matsananciyar damuwa, abinda ya ba ni mamaki bai wuce ganinshi a zaune a gefen gado da waya a kunnansa yana magana cikin rarrashi da wata kalar murya wadda tun tsayin zamana da shi ban san shi da ita ba.
Jikina ya d'an shika kad'an amma lokaci d'aya ban bari ya fahimci raunina ba, na zauna gefansa hankali da jina yana kansa domin fahimtar da wa yake waya.
Kasa gane kowacece na yi domin da da farko na d'auka Momi ce sai da na ji yana kiran Maman Hanif tukkuna na yi tsai ina tunanin wacece wannan kuma. Tunani na ya katse lokacin da na ji sautin maganarta cikin reshin kuka ban dai ji mai take gaya masa ba, amma gabad'aya yanayin yadda take magana shi ya tabbatar mini da cewa cikin tsananin b'acin rai take. Na dinga nanata sunan a cikin raina Maman Hanif domin na kasa gane wacece can nazarina ya hasaso mini Nabila kanwar Momi ce tabbas ita ce babban yaronta sunansa Hanif hakane yakan zo wurinsu Adam a duk lokacin da aka yi hutun makaranta.
Ajiyar zuciya na sauke na sake kai duba na gare shi ya tak'arkare yana ta rarrashi da ban ha'kuri na gyada kaina ina jimanta matsayin momi da alhalinta a zuciyarsa. Maganar abinda ya faru tsakaninta da Hauwa suke tattaunawa da 'kyar dai da jibin goshi da irin rausayar da kai da muryar da yake yi ya rarrasheta ta ha'kura tare da kudirin janye 'karar da suke ko'karin shigarwa akan Hauwa. Na ji dad'i dai da bai gaya mata irin hukuncin da ya yanke ba ba domin a yadda yake a zaburen nan abu ne mai sau'ki ya gaya mata cewa ai ya saki hauwa ba. Wasu lukutan kuma zurfin cikinsa yakan burge ni ya kuma yi masa amfani. Tabbas Hauwa bata kyauta ba, kuma ni ban ga laifinsu ba don sun ce za su kai ta 'kara matsalar kawai idan har aka bari hakan ta faru gabad'aya rayukan kowa ne zai b'aci shiyasa Annabi ya yi hani da tayar da masifa domin idan ta tashi kafin ta kwanta sai an d'auki wani lokaci.
Ya kashe wayar ya dube ni fuskarsa kadaran kadahan. Kafin ya yi gyaran murya ya ce." Ina alkawarin da muka yi ni dake ranar da baban Saude ya yi mana sulhu....
Kafin na ce wani abu kira ya shigo wayata dake saman cinyata.
Hajja ce sai na d'auka a tsanake muka gaisa da kulawa kamar koyaushe ta ce." Ai ya zo mun jima da shi kuma ya gaya mini dukkanin abinda yake faruwa dalilin da ya sanya na ce ba zan bari har sai gari ya waye ban yi magana dake ba. Da farko dai ina mai kara baki ha'kuri ina kuma kara yaba miki bisa ko'karin ganin kin yi hakuri da duk umarnin dana ba ki. Babu shakka kin nuna mini cewa ke din 'yar halak ce na gode sosai Allah Ya yi miki albarka Amina sai dai a wannan lokacin ba zan tauye miki hakki a matsayinki na uwa mahaifiya ba. Ko daya ban ga lefinki ba domin tsira da mutunci ai yafi tsira da kudi babu wani dalilin da zai sanya yara su zauna a wurin da babu daraja kuma babu mutunci. Hajiya Maryam tun kafin Tajo ya aureta shedar da muka yi mata mutuniyar kirki ce kuma har yanzu akan hakan muke kallonta. Amma tabbas tarbiyar yaranta akwai nakasu ba wai na za'bi Kamalu na fifita shi akan Salim ba. Kafin na kira ki a yanzu na zauna da Kamalu cikin hikima na tambaye shi ya kuma yi mini bayani tsakaninsa da Allah wanda nake da tabbacin haka siddin ba zai kirkiri karya domin ya 'bata Salim ba." Ta d'an yi shiru tana sauke numfashi kafin ta cigaba da cewa." Sannan mijinku na nuna masa kuskuransa sosai duk da ya kawo mini hujjarsa amma ni bata gamshe ni ba saboda banga dalilin da zai sanya ya ce a rufe miki abinda ya shafe ki ba. Kenan babu adalci a ciki koda ya yi hakan ne domin yin nazari akan lamarin kafin ya yanke hukunci ta 'bangaranki ba za ki ta'ba gamsuwa da cewa bai hofintar da naki ba, ma'ana ya karkarta a bangare daya da tabbacin nan ne da gaskiya. Abu ya faru wanda ya sosa ran kowa ina kuma sake baki ha'kuri domin a ko'ina ina irin wannan matsaltsalun suna faruwa. Kin yi daidai da ki ka turo yara nan ni kin burge ni kwarai kuma kin yi hankali da ba ki tunkari Maryam da tashin hankali ba. Ina so ki gaya mini abinda yake ranki don Allah kada ki ji kunyanta da kuma nauyi yaran nan kin amince da zamansu a hannuna kamar yadda mijinku ya ba ni su amana ko kuma na sanya Magaji direba gobe ya mayar da su gidan Gwaggwon gobe, idan har hankalinki zai fi kwanciya da hakan don Allah ki gaya mini gaskiyar abinda yake cikin ranki."
Sosai jikina ya yi la'asar na gaza cewa komai saboda tsabar nauyi da nazarin ya zan yi na ce mata ba ni son zamansu a hannunta wanda nasan ba wurin da za su cutu ba ne.
Maganarta ta dawo da ni hankalina. Na ce." Hajja ni dama zamansu ne kawai ba na so anan din tunda har suna nan wurinki babu komai wallahi ai dake da Gwaggon duk daya kuke a wurina na amince su zauna Hajja Allah Ya taya ki riko."
Cike da farinciki ta furta." Aikuwa na gode sosai da wannan alfarma dana samu, ni ma zan samu ladan rik'on maraya ashe na gode Amina, in sha Allahu kuma yaranki ba za su yi kukan maraici ba, Allah Ya yi miki albarka kin jima kina yi mini alfarma ni kuwa da me zan saka miki "
Tak'arasa maganar da rawar murya. Sai hankalina ya tashi jin tana shirin fashewa da kuka na ce." Haba Hajja ni din taki ce fa balle kuma yara don Allah ki daina yi mini godiya babu ita a tsakaninmu, addu'ar da ki ke yi mini da ita kika saka mini ita kadai ma ta ishe ni wallahi."
Can k'asa-k'asa na ji tana fad'in." To na gode sosai sai da safe." Sai ta kashe wayar. A sanyaye na ajiye tawa a saman cinyata jikina duk ya mutu Hajja kuka take yi da gaske dalilin da ya sanya ma kenan ta katse wayar da sauri. Sai kawai ni ma na ji ruwan hawaye ya ciko idanuwana wani kutittiran abu ya tsaya mini a wuya. Lallai matar nan ta wuce ta nemi alfarma a wurina na tsaya yin jayayya da gaddama ba zata cutar mini da yara ba. Wannan maganar zuciyata ke ta nanata mini. ........
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*TALLAH*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 n

*93*
"Maganar
Hauwa ai bata shafe ki ba Amina don haka babu ruwanki wannan tsakanina da ita ne kawai tunda ta ce ba ta ji to sai mu zuba ni da ita shege ka fasa."
Ya fad'a yayin da yake sake janyo ni jikinsa. Na janye a hankali na ce."Ya zaka ce babu ruwana bayan kai ma kasan a saboda ni da abinda ya shafe ni kuka samu sa'ba ni har da rabuwa ai gaskiya ba zan iya yin shiru ba domin abinda ka yi bai dace ba. Kamar yadda take ha'kuri da kai ya kamata ace kaima ka yi hakuri da halayenta ai zaman auran kenan."

"To yanzu ya ki ke so ayi?"
Ya fadi hakan cikin 'kosawa da maganar domin gabad'aya yanayinsa ya nuna ba itace a gabansa ba.
Na ce." Ka mayar da ita tunda ciki ne da ita sanin kanka ne a musulunci babu kyau sakin mace da ciki, kuma idan Hajja ta ji hakan ranta ba zai yi mata dad'i ba gaskiya."
"Ai ita Hauwa ba ta duba haka ba Amina, kuma cikinku wallahi kada wadda ta kuskura ta gayawa Mahaifiyata akan hakan rai zai 'baci."
"Ai kai zaka gyara matsalar gidanka kafin ta fita waje idan ba ka so Hajja ta ji abinda ka yi sai ka yi gaggawar gyara kwabar da ka yi."
Ya 'bata rai yana fad'in." Kina so ki ba ni umarni kenan?"
"Ba umarni ba ne ban isa ba, shawara ce nake ba."
"To ba zan d'auka ba har sai kun je ke da ita kun bawa Maryam da 'yar uwarta ha'kuri akan abinda ku ka yi musu. Na rashin kyautawa."
Ido na zuba masa ina kallonsa da mugun takaici.
Na gyada kaina tare da janye idona daga kansa ban ce komai ba..
Sai ya cigaba da ce wa." Wannan shine kawai, ki ja ta tunda tare kuke kulle-kullenku sai ku je ku ba su ha'kuri domin mun yi magana da Nabila ce wa gobe za ta koma jos, to kafin ta tafi din sai ku gyara kuskuranku, ni kuma sai na mayar da ita dakinta."
Na juyo fuskata a d'aure " Wannan kuma shine ba zai yiwu ba, idan hakurin da ka ba su bai isa ba, shikkenan don Allah ka cikashewa Hauwa sauran igiyoyinta da suka rage, idan hakan ma bai yi maka ba sai ka had'a har da ni gabad'aya."
Ya ce." To kada ki sake yi mini magana akan abinda ya shafi tsakanina da Hauwa, ba ke ki ke auranta ba, ni ne babu ruwanki wannan shine maganarmu dake ta k'arshe akanta."
Na dinga kallonsa zuciyata na sake suyuwa da kutun takaici da b'akinciki. Wannan wani abu ne da zai yi masifar wahala a ce Hauwa ta je ta bawa Momi da Nabila ha'kuri saboda iya zaman da na yi da ita na gane cewa macace mai mugun girman kai da kifad'i, ga taurin kan tsiya, bai shirya kwantar da rikicin ba, domin da ya shirya mutuwar matsalar ba zai 'bullu da wannan abinda ya san lallai da wahala ya yiwu.

Jin an kira shi a waya ya sanya na tashi na fita daga d'akin ba tare da na sake cewa komai ba, matsalarsu ce can ta family iyakacina shawara, kuma ni ban tura Hauwa cewa ta yi abinda take yi ba, akan kanta take yi saboda wata manufa tata da kuma masifar kishi, duk wanda zai zarge ni da hannu akai ya d'auki hakkina. Ba zan sake cewa masa komai ba.

Bai kwana a gidan ba a ranar sai washe gari wajen daya da rabi ya shigo cikin kayan shan iska da cazbaha a hannunsa ga dukkanin alamu daga massalaci ya fito mabiyin sunnah ne sosai da zazzafar akida da rashin son bidi'a da yawa. Bai fad'a ba amma tuntuni na gane ce wa mugun dan izala ne tunda yawanci abokanshi larabawan nan na madina duka 'yan ahalissuna ne.
Muna falo duka a zaune ya shigo ya d'an tsaya ana gaisawa ya amshi ta kowa a d'an sake. Ina kallon Hauwa bayan sun gaisa ta tashi a sanyaye ta shige daki. Sai na ji wani iri a raina, na yi shiru tare da yin k'asa da kaina ina jin suna ta labari da Baba Tabawa kamar yadda suka saba. Ya jima a tsaye a wurin suna magana ban tofa tawa ba. Kafin ya haura samansa.
Baba Tabawa ta juyo tana kallona da wani yanayi na alhini da damuwa ta ce." Irin wannan matsalar nake ta guje muku faruwarta Amina, rayuwar nan gabad'ayanta 'yar ha'kuri ce,

Please Login or Register in order to submit comment