Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallar azuhr"
Hannuna ya rike ya had'a yatsunmu wuri d'aya bakinsa yana motsi na gane addu'a yake yi kafin a hankali ya tashi zaune yana fuskantata ya ce." Bacci na ke yi mai dadi da mafarkinki"
Ina murmushi na ce." Haba, ai gani a tare da kai?"
Ya d'aga mini girarsa." Wallahi na yi mafarki kin haihu."
Na zuba masa ido da murmushi a fuskata na ce." To me na haifa?"
Ya gyada kansa." Wannan kuma Allah bai nuna mini ba, ni dai kawai naga kin haihu hannunki ri'ke da jariri a cikin towol."
Na girgiza kaina ina raya abubuwa da yawa a cikin zuciyata. Ni kaina Ina so na haihu dashi ba na k'yamar hakan kamar Alhaji Muntari. Kuma ba ina so na haihu da Alhaji Tajo don dukiya ba, a a sai don bashi farincikin da yake muradi a koyaushe..
Na dube shi a hankali na ce." Baba ko dai don kasa hakan a cikin ranka ne shiyasa kake mafarki."
Ya girgiza kansa yana cewa." Ko kad'an, ai tunda na aure ki ban ta'ba mafarkin kin haihu ba sai yau, wata'kila Allah ne ya amshi adduata."
Shiru kawai na yi Ina kallonsa fuskata ba ta canza daga yanayin da take ba. A tsanake na furta." Ni ma zan so
hakan Baba."
Ya yun'kura ya sauka daga gadon ya nufi bandaki yana fad'in." Allah zai cika mana burinmu amma dai zan kara zage damtsena."
Dariya ta kwace mini na bishi da kallo yana ko'karin bude bandakin ya juyo yana dubana ya ce." Kina yi wa dattijo dariya ko Amina."

Na ce." Wane irin damtse zaka sake zagewa Baba kana fa kokari kawai dai Allah ne bai kawo ba."
Ya ce." Zan dai zage na gaya miki."
Na ce." To shikkenan." Ya bude bandakin ya shiga, ni kuma na tashi na gyara shimfidar gadon tun bayan shiryawarmu ban sake bari wani ya gyara masa d'aki ba.
Na d'ibi wayoyinsa na dora kan dorowa sannan nasa freshnar. Na zauna har ya fito daga toilet din yana tsane jikinsa yake fad'in." Kin ga na tashi da wata irin yunwa Amina, ko yau daya zaki tuka mini towon dawa, na ci girkin amarya."
Na ce." Me zai hana sai na shiga kicin yanzu, daga yau ma zan dinga yi maka girka.
Ya furta." Da kuwa na ji dad'i."

Littafin gudun aure ne na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Na tashi a hankali na isa inda yake ya na ta shafa mai a sannan jikinsa na lakaci wani a hannuna ina fad'in." Bari na shafa maka a bayanka."
Shiru ya yi bai ce mini komai ba har na fara shafa masa man yana ta kallona ta madubi sai na ga ya dan rintse idonsa ya bud'e ya dube ni ta mudubin muka had'a Ido, sai ya daga mini gira yana fad'in." Alwalata zata karye Amina bar shafa man nan. Yanzu idan na ce zan take ki zan yi asarar jam'i a massalaci, amma idan na dawo za mu had'u."
Da sauri na cire hannuna daga wuyansa na ja da baya ina cewa." Ai ban san kana d'aure da alwala ba."
Ya ce." Ba za ki sani ba dama tunda ban gaya miki ba."

"Hakane bari na shiga kicin din Baba." Yana ko'karin fito da jallabiya daga ma'adanar kayansa ya ce." To Allah Ya yi miki albarka."
Na amsa da "Amin." Sannan na bud'e d'akin na fita cikin nutsuwa.

Da yake duk wani nau'in abin buk'ata akwai ban sha wahala ba wurin sarrafa masa abinda ya bukata. Na kammala komai tsaf na shirya a babban tire na d'auka na fita daga kicin zuwa lokacin na san ya dawo daga massalacin. hakane kuwa yana saman sofa yana duba laptop wadda take kan cinyarsa. Na dora tire din abincin a tebur din da yake gabansa.
Ya dube ni da murmushi a fuskarsa ya furta." Sannu.'' Na amsa cikin kulawa kafin na nemi wuri na zauna ina kallonsa ya a rufe Laptop din yana tattare hannun rigarsa yana cewa." Yau zan ci girkin amarya.
Na yi murmushi a nutse na fara had'a masa. yana cewa." Tun kafin ma na ci miyau na ya tsinke, na kwana biyu ban ga irin wannan towon dawar ba."
Na ce ." Idan ma kana so sai na baka a baki."
Ya dube ni yana dariya ya ce." Da na ji dad'i kuwa.
Ban ce komai ba da na gama hada abincin na zauna daf da shi da flat din a hannuna na gutsuro tuwon tare da dangwalo miyar na ce." To bude bakinka."
Da sauri kuwa ya bude bakin na ce." Yi bisimillah." Ya yi da sauri yana yi mini wani irin kallo sai murmushi yake yi. Nasa masa towon a baki ya fara taunawa idonsa gabad'aya a kaina. Ya ce." Yau kin yi mini kyau fa my wife."
Na ce." Ni ma haka my love dina."
Yanayin yadda nake tarairayarsa yana mutukar kidima shi don a daddafe ya gama cin towon sai kai hannunsa yake jikina wai dole sai ya cire aftar dress din dana dora a kan kananun kayan. Idonsa kacokan akan kirjina. Ni kaina na san breast dina na bashi sha'awa don har sai da ya gaza yin shiru wataran yake cewa da ni kamar ban ta'ba shayarwa ba. Bashi da rufi ko kad'an, ko a wurin sex ne baya k'wange kuma baya yin shiru yana nuna nishad'insa sosai.
Ni kam bai bari ma nasa komai a cikina ba ya kidi'ma ni da salonsa ban a iya turjiya ko jayayya don har ga Allah ni ma ina zumud'in kasancewarmu koda za mu yini zurr!

Bayan sati Hamusu ya kira ni yake gaya mini lokacin ziyararsu Kamalu ya yi, na ce ai kam wannan karon da ni za a yi tafiya. Koda na gayawa Yallabai din sai ya ce shima dashi za a je. Na kasa boye murnata na rungume shi a kirjina kam ina sumbutarsa sai ya dora kansa a kirjina tare da matse ni a jikinsa sosai.

Alhamdulillahi dama komai ya yi farko yana da karshe, sannan babu abinda yafi karfin Allah. Yanayin yadda muka samu Kamalu ya faranta mana rai sosai, yaro ya nutsu ya kara girma da hankali, farincikin hakan ya sanya hawaye zubo mini na rungume shi Ina kuka. Shi kam banda murmushi babu abinda yake yi hankalinsa gabad'aya yana kan d'an'uwansa Yusi da shi ma murnarsa ta kasa buyuwa.
Har 'kasa ya durk'usa ya gaishe da kanin uban da kuma ogan tafiyar wanda shi ma ya dinga murmushi ya riko shi yana shafa kansa yana ta yi masa addu'a tamkar d'an cikinsa.

Sanin fuskarsa farin sani a duniya ya sanya tun daga bakin gate din jama'a ne har cikin makarantar malaman kuwa bakinsu ya kasa rufuwa.
Mun samu a k'alla awa daya da rabi a makarantar kafin mu yi Shirin tafiya. Yallabai din ya keb'e da shugaban makarantar suka tattauna muhimman abubuwa kafin ya yi wa dalibai da mahukanta tsangayar alheri mai dumbun yawa, ya kuma ce idan buk'ata ta taso ta neman taimako a tuntube shi.
Na d'auka da zamu tafi Kamalu zai nuna damuwarsa ko kad'an sai gashi shine har da rako mu bakin mota. Yusi kam sai goge fuska yake yi yana tafiya a hankali Baban nasa ya dube shi yana dariya yake tsokanarsa ko a bar shi ne a makaranta shima. Yayi shiru dai bai ce uffan ba ya je ya jingina a jikin mota yana kallonmu har muka gama sallama da Kamalu aka mayar dashi ciki.
Da yake Hamusu a makarantar muka same shi yanzu ma motarsa daban, amma sai da muka rage masa hanya zuwa babban titi tukkuna maigidan ya bashi dubu hamsin ya ce ya shiga mota domin komawa gida. Mukayi sallama dashi yana ce mini akwai abubuwan da yake so mu tattauna dangane da harkokinmu amma zai kira ni tunda yau lokaci bai ba mu dama ba.

Gamu a garin kano amma kiri kiri mutumin nan ya ki ya barni na gaisa da 'yan uwa da abokan nan arziki, ina so naga Babanmu Sahura da Kuma Hajja. Ya ce a a Hajja suna tafe ita da Inna Uwani a satin da zamu shiga. Dole na ha'kura direbansa wanda shine ya je ya d'auko mu daga airport ya mayar damu muka shiga jirgi muka koma gida tare da escort dinshi Sukajiru.
***
Mafarin fara samun rashin jituwarmu zuwan Hajja da kanwarta inna Uwani. Ba ni da matsala da Hajja tunda duk wata k'auna da kulawa ta nuna mini ita. Amma duk wasu hanyoyi da Inna Uwani take bullo dasu na sani tunda ni din dai ba yarinya ba ce. Duk motsin da zan yi akan idonta. Duk kuma maganar da zan fad'a sai ta juya mini ita ta gaya mini babu dadi mussaman idan Hajja bata wuri to inna Uwani ta dinga yar mini da magana kenan, ba ta yi a gaban 'yar uwarta da maigidan tana nuna musu ai tana kaunta. Hakan ya sanya ma ban cika zama a falon ba idan suna zaune har maigidan sai na yi zamana cikin d'aki wataran sai Hajja ta kira ni nake fitowa. Ba na son tashin hankali ko kad'an, kuma ba na so na raina ya 'baci har ta kaini ga mayarwa da matar martani wadda hakan na san ba zai yi wa kowa dadi ba. Shiyasa muddin da ita a wuri ba na fitowa. Yau satinsu biyu da zuwa amma na k'augata su tafi ba wai Hajja na gaji da ita ba sai ita inna Uwani wadda na gama gano take takenta maigidan ya kawo 'yarta cikin gidan mu zauna mu biyu tunda tasha fad'a girman gidan ya wuce ace mace daya ce a ciki ba mata hud'u ba
Shi kansa a tsukin nan haushinsa nake ji domin sai nake ganin kamar duk abinda matar take yi da saninsa kuma ko a fuska bai ta'ba nuna mata cewa bashi da ra'ayin auran Hauwan ba.
Abu biyu ya hade mini a lokacin guda habaice habaicen Inna Uwani da kuma rashin kuzarin da yake damuna. A satin da ya gabata ya kamata ace na yi al'ada amma ban yi ba, na ji sauye sauye a jikina da yawa wanda ya sanya nake tunanin ko ciki ne da ni.

Yammacin ranar asabar ina kwance a d'aki na rufa da bargo zazzabi ne ya rufe ni a sa'ilin don ma kada Hajja ta fahimci wani abu ne ya sanya na shigo d'aki na kwanta. Kira ya shigo wayata dake saman dirowa, koda na duba maigidan ne, nasa a kunne ba tare da na ce komai ba. Haka kawai ko muryarsa ba na son ji domin sai nake ganin kamar akwai wani abu a zuciyarsa da yake boye mini. Zuciyata ta gama aminta da hasashen da nake yi akan cewa ya samu abinda yake so a wurina shiyasa ya rage ba ni kulawar da farko yake ba ni.

Shi ma babu sakewa a maganarsa yake cewa da ni na zo na same shi a samansa. Ban ce masa komai ba na kashe wayar na kai minti goma kafin na tashi da kyar na sanya hijabi na fito. Suna zaune suna kallo har da Yusi na dan saki fuskata. Hajjan ta dube ni tana tambayata bacci na yi ne, sai na bata amsa da cewa "E" kawai, ita kuwa inna Uwani a lalace ta dube ni kafin ta kawar da kanta.
Na d'auke kaina ni ma ban tanka mata ba na wuce zuwa saman maigidan.
Na same shi a zaune Yana aiki da computer ban ce komai ba na zauna nesa dashi. Shi ma bai dago ba har sai da ya gama abinda yake tukkuna ya dube ni muka had'a ido. Babu sakin fuska ya fara tuhumata akan abinda ya gani a tare da ni wanda ya zama sabo a wurinsa. Tuhumata yake yi akan har raini ya fara shiga tsakaninmu.
Na dube shi zuciya na zafi na furta." Me nake yi maka na raini, sannan kuma wane canji ka gani a tare da ni da zaka tuhume ni akan hakan? Ni na gaji rayuwarta ta baya tafi mini dadi wallahi."
Ya zuba mini idonsa Yana kallo kafin daga bisani ya taso ya zo ya zauna kusa dani ya ce." Ni na kasa gane inda kika nufa a cikin kwanakin nan Amina tunda su Hajja suka zo ki ka canza mini ba kya ba ni kulawa babu tarairaya gaisuwa ma sai kin ga dama. Yau kwana takawas rabon dana had'a shimfida dake menene matsalar ki ne?"
Kawar da kaina na yi ban tanka masa ba. Ya sanya hannu ya juyo da fuskata muna kallon juna ya furta." Me na yi miki umm! ki gaya mini sai mu samu maslaha ba na son fushin nan naki my love....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*15*
Nan da nan 'kwalla ta ciko idona ta fara zuba. Ina ina jin nauyin na ce masa ba na so ya auri zabin Yaddikonsa kuma kanwarsa, abinda yake ta damuna kenan, domin na gama fahimta duk kwane kwanen da Inna Uwani take yi kenan, shi ma kuma kamar yana da burin cika mata muradinta. A tunanina idan na nuna masa rashin amincewata na so kaina da yawa. To ni kaina na kasa sarrafa zuciyata domin wani mugun kishinsa nake ji a zuciyata ba kuma na so kowace mace ta rabi inda yake.
Ganin ina kuka kashir'ban sai hankalinsa ya tashi ya rungume ni a kirjinsa yana jijjigani kamar karamar yarinya sai ruwan kalamai yake yi mini a kunne. Wannan ma yana d'aya daga cikin dalilan da suka sanya ba na so wata mace ta kusance shi domin iyakar soyayya mutumin ya iya.
Daga rarrashin sai lamari mai girma ya gifta. Dama kuma akwai buk'atar hakan, tunda tun bayan shiryarmu ba mu taba kwana ba tare da mun kusanci juna ba. Sai gashi yau kwanaki takwas kenan babu wannan, shi din ma ya isa ya taka muhimmiyar rawa wurin dasa k'unci a zukatanmu. Ban dora alhaki akan kowa ba sai akan Inna Uwani domin itace take ko'karin rusa mana farincikinmu. To ko lokacin da muke biyawa juna buk'ata bai iya yin shiru ba. Yana gaya mini kamar yau din ya fara sanina domin ya gamsu fiye da kowace rana. Ni ma ban boye masa ba na nuna masa na yi kewarsa kwarai sa'annan kuma na gaya masa abinda nake hasashe na samuwar cikin da yake ta mafarki. Ai sai ya kara kid'imewa Yana ta addu'ar Allah Yasa shi din ne. Koda muka yi wanka muka sauka kasa kawai sai na ji yana gayawa Hajja cikine da ni. A okaci guda na diririce kunya mai karfin gaske ta kama ni.

Cikin jin nauyi da kunyarsu na yi kasa da kaina. Shi kam bai ji nauyi ba ya riko hannuna muka zauna a kujera yana fad'in." Ciki ne da ita wallahi, yanzu nan ta gaya mini, Hajja wannan ranar tarihi ce wajena ku taya mu addu'a Allah Ya sauketa lafiya.
Hajja baki a har kunne take cewa." Addu'a ta zama dole Tajo, ai ni ma ranar ta zama tarihi a wajena ba zan manta da ita ba."
Budar bakin Inna Uwani ta ce." Ina ce ita ba ta fari ba ce a wajanta ko."
Hajja ta ce." Kwarai kuwa ta uku ce, ai mu kamar ta fari ce a wajenmu Uwani."
Sai ta yi ya'ke wanda hausawa suke kira da ya fi kuka ciwo tana fad'in." To Allah Ya raba lafiya." Gabad'aya suka amsa da Amin. Ban da ni, da na tafi tunanin abubuwan da suke faruwa.
Samuwar juna biyu a tare da ni sai ya kara janyo mini k'auna da soyayya a wurin uwar mijina. Dashi kansa maigidan wanda a wasu lukutan har tausayi yake ba ni, idan na ga yadda yake kaffa-kaffa da ni, sam baya son b'acin raina. Idan yana gida baya bari na yin komai kullum muna tare da juna a cewarsa yana jin d'umin abinda zai haifa.
Wasu lukutan har b'uya nake yi na share hawaye domin tunda cikin ya yi k'wari zuciyata take ta yi mini sa'ke-sake marasa kyawu. Koda abin ya dame ni na kira Anti Yagana a waya na gaya mata ina yawan mafarkai da munanan tunanai take cewa da ni mafi akasari masu ciki sukan samu irin hakan. Amma dai na dage da addu'a. Ni kam cikin Yusi da Kamalu ban yi irin wannan wasi-wasin a raina ba.

Hajja ta samu wurin zama domin kuwa cewa ta yi ba zata tafi ba har sai na haihu tukkuna lokacin watansu hud'u da zuwa. Inna Uwani ta yi ta yi da ita su tafi tace mata a'a, sai na haihu. Sai kawai ita ta yanke shawarar tafiya domin dama kamar akan kaya take dalili ta tsani ta bude ido ta fa gilmawar matar gidan da ciki, da kuma yadda masu gidan suke ki'dime akan hakan. tana ganin komawarta gida shine maslaha a wajenta domin ta je su tattauna yadda za a yi, don ta fahimci kamar sai ta biyo ta bayan gida tukkuna ha'kanta zai cimma ruwa.

Tafiyar inna Uwani da kwana biyar. Anti Yagana da Hadiza suka zo. Anti Yagana sai da ta fara sauka a can gidanmu dalili ta kwana biyu ba ta je. Nan fa Hadiza ta ma'kale mata wai lallai sai sun taho tare. Sai a lokacin ma ta san auranta ya mutu tana cikin iddah ne. Da ta tambayata dalili duk ta kwashe komai ta gaya mata. A lokacin ta yi mata fad'a sosai irin na 'yan uwantaka. Ummansu tana zaune tana ji amma ba tace komai ba, ita bakin cikinta yadda a komai yaranta ne a baya. Kallo d'aya ta yi wa Yagana ta gane cewa lallai tana cikin hutu da jin dadi, dama kuma ko lokacin da ta auri mijinta mai rufin asiri ne.
Da sahalewar Babanmu suka kamo hanya suka taho. Maigidan kuwa ya dinga fad'a yana cewa mai yasa suka biyo motar haya daga Kano zuwa Legos ba su kira su sanar da ni ko kudin ticket sai a basu su biyo jirgi su zo.
Duk wani abu da ya dangance ni yana mutukar daraja shi da martaba shi. Tun da ya fahimci cewa anti Yagana itace babba a gidanmu yake girmamata gashi dai ya kusa haifarta amma idan zai gaisheta sai ya dan risina. Dalilin da ya sanya ma kenan ta guji zaman falo take zamanta a d'aki, takan ce mini Amina mijin nan naki kunyarsa nake ji wallahi tallahi wani idan ya ga abinda yake yi sai ya d'auka kin wanke kin bashi ya shanye. Ba na so jama'a su gazgata zarginsu akan cewa matan barno suna asiri. Kin ga dai mutumin nan babu wani abu da muka taba yi masa na mallaka, ban sani ba ko kin yi a boye Amina abin yayi yawa.
Na dinga dariya ina fad'in wallahi ko d'aya anti Yagana shi haka yake fa bashi da wani girman kai da ma'aikatansa sai ya zauna ya ci abinci dasu. Ni kaina dan ya durk'usa mini ba wani abu ba ne. Ta ce." Idan ya durk'usa miki wannan tsakaninku mijinki ne, amma ni kam ina kin kunyar abinda yake yi mini. Mutumin da manya suke zube masa amma idan zai gaishe ni sai ya rankwafa."
Na ce." Anti Yagana duk wanda ya dangance ni to wallahi yana da daraja a wurinsa. Karin abin ma kuma wannan cikin na jikina ya sake janyo mini girma a wurinsu da mahaifiyarsa. Wallahi ban yi masa komai na gusar da hankali ba."

Ta girgiza kanta tana fad'in. " Lallai Amina Allah ya share miki hawaye sai kiji tsoron Allah , ki kyautata masa kamar yadda yake kula dake, ki tsare masa mutuncinsa da dukiyarsa. Na tabbatar da cewa son da yake yi miki na Allah da Annabi ne, ki yi iyakacin bakin kokarinki wajan yi masa biyayya."
Na ce." In sha Allahu Anti Yagana na gode."
To duk wannan zantukan da muke yi Hadiza tana zaune ba ta ce komai ba illa zare Ido ta kalli bakin wannan ta kalli bakin wannan haka ta dinga tana ta sakin ajiyar zuciya. Hadiza kenan duk wani motsi da zata yi na san manufarsa domin kuwa tare muka tashi a gida daya daki daya, babu yadda zata yi ne shiyasa ta sakar mini domin kuwa Allah ne yake ikonsa.

Anti Yagana da Hajja jininsu ya hadu sosai idan suna hira tamkar uwa da 'yarta. Halinsu ya zo daya sannan kuma tunani da nazarinsu ya zo daya. Ina jin dadi sosai a duk lokacin da na gansu a tare suna hirarraki irin na rayuwa. Ita kuwa Hadiza dama ta samu bata aikin komai sai ci da kuma bacci abinda take so ya samu basu cika wata biyu ba ta murje ta yi bul daidai da fatar jikinta sai da ta canza. To ko yaushe tana cikin Ac ga abinci mai kyau.
Lokacin da anti Yagana ta shirya tafiyarsu sai Hadiza ta yi tsalle ta dire ta ce ba zata ta tafi ba sai na haihu tukkun. Hajja kuwa ta goya mata baya. Maigidan ma haka ya ce ta zauna tunda bata da aure. Ni dai ban ce komai ba domin na riga na san ba don ta kula da ni ta nace sai ta zauna ba domin biyan bukatarta ce. Na yi ta dariya ina kallonta a lokacin da suke ta jayayya da anti Yagana tana cewa ba haka Babanmu ya bata umarni ba, don haka dole sai sun tafi tare. Maigidan ya sauko daga sama da yake asabar ce baya fita da wuri ya riski jayayya. Ya ce anti Yagana ta yi hakuri zai kira Baban namu ya yi masa bayani. Ba don ranta ya so ba ta ha'kura. Aikuwa muna shiga d'aki ta rufe Hadiza da fad'a tana cewa." Ba zai yiwu

Please Login or Register in order to submit comment