Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da mota a hannunsa. Tsakanin k'waryar birnin kano da k'auye bunkure bai zai wuce awa daya da rabi zuwa biyu ba.
Misalin biyar na yamma ya kama hanya ya tafi bayan magriba da kad'an ya dawo da sa'kon.
Duk abinda na umarci Hamusu ya yi mini yakan yi kokarin yin iyakacin bakin kokarinsa kamar yadda na buk'ata din shadda ce kalar sararin samaniya dakakkiya zanenta irin na manyan mutane dinkin ma fitacce ne da hula zannar bukkar ta karshen tsada da takalmi daidai kafarsa maigidantsaya kamar dai yadda na gaya masa ga yadda nake so.
Na ji dad'i sosai bayan isha'i dana nutsu na kira shi a waya ina sake yi masa godiya sai hakan ya bashi dariya da mamaki yana fad'in abinda ya yi bai kai na yi masa wannan godiyar ba nafi karfin haka a wajensa.
Na yi murmushi kawai na kashe wayar cikin zuciyata nake
fadin lallai da matasan samari irin Hamsu za su zama masu tsoron Allah da Amana da an rage masu zaman banza. Hamusu tun kafin na kai k'arfin haka yake tsaye akan dukiyata ban ta'ba kama shi da zamba cikin aminci ba ko ya danne mini kudi duk shekara muke buga lissafi a fitar da abinda aka zuba a fitar da ribar da aka samu a biya duk wanda yake da hakki hakkinsa. Yanzu da su Kamalu suka koma can al'amarin sai ya kara bunkusa Hamusu na kula da shagon zannuwa da ma'aikatan da suke yi mana d'inki shi kuma Usaini na kula da shagon da muke harkar huluna kala daban daban. Yayin da muka bude sabon shagon sayar da takalma cikin kasuwar kwari wanda Yusi da Saminu suke kula da shi Kamalu kuma hankalinsa ya fi karkata wajan yawon neman sani akan abinda ya shafi da'awa da hadisai Annabi s'aw shikkenan yawon bin malam sunnah yana kuma zuwa legal kwalejin addinin musulunci.

Cikin matan gidan na zauna kamar jiyya muna ta hira sosai suna ba ni sha'awa ganin yadda suke gudanar da rayuwarsu a sau'kake ba kuma su zafafa kishi ainun irin na wasu matan k'auyen ba.
Kayan suna kusa da ni Malam Rabiu yana shigowa na sanya Hajara ta yi mini magana da shi kafin ya shiga bangaransa ya zo muka gaisa sannan na bashi kayan tare da gaya masa na Yallabai ne.
Bai jima ba a wurinsa ba kuwa ya fito da kayan a hannunnsa ya nufi sashen malamin da d'an sauri.

A daran ranar na yi bacci sosai irin wanda na kwana biyu ban yi shi ba hakan kuwa baya rasa nasaba da nutsuwar da na samu da asuba da na yi sallah ban koma ba.
Gari yana yin haske Hajara ta shigo da abin kari da kuma kayan makarantar boko a jikinta litiinin ce dama muka gaisa ta ce Inno ta dora mini ruwan wanka ita zata tafi makaranta.
Na ce ." To na gode sosai Hajara sai dai za mu tafi baki nan kina makaranta ko?"
tana murmushi ta ce." Eh shiyasa na shigo mu yi sallama wata'kila kafin na dawo kun tafi Allah ya tsare ya kiyaye hanya."
Na amsa da Amin Ya Allah. Har ta juya zata fita na kirata ta dawo na ce." Ajinki nawa ne?'' ta ce." Aji na uku a sakandire."
Na gyad'a kaina jakata da take saman katifar dake shimfide a d'akin na d'auka ina da kudi a ciki dubu biyar na mik'a mata ta nok'e wai ba zata kar'ba ba tana dariya ta juya zata fita na tashi da sauri na ri'ke hijabinta jakarta ta makaranta na saka kudin ni ma ina dariya na ce" Ki dinga sayan aya da rake a makaranta na gode sosai kin ji, Allah Ya ba ki miji nagari."
Ta amsa da Amin tana jin kunya ta fita da sauri.
Sai da na karya tukkuna na yi wanka na shirya tsaf na fita domin gaisawa da matan gidan da kuma bankawana.
Malam Rabi'u ya zo yana gaya mini Malam na kira na. Na bi bayansa cikin nutsuwa dama kuma da hijabina a jikina.

littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Koda na shiga d'akin alamu ya nuna mini tare suka yi karin kummalo da malamin domin kayan karin na gani a gabansu sun gama suna magana. A nutse na zauna gefe d'aya na dubi malamin na gaishe shi ya amsa da kulawa kafin na juya shi ma na gaishe shi muka had'a ido. Sosai ya yi mini kyau cikin kayan ya yi fes dashi kamar sabon ango duk da shi din ma'abocin gayu da tsafta ne amma sai nake ganin yau ya fiye mini koyaushe kyau da kwarjini.
Na ce." Baba ina kwana ya jikin." Ya amsa da sauki alhmdullhi."
Na janye idona daga kansa don ganin shi bashi da niyyar janye nasa wasu lukutan idan yana yi mini irin wannan kallon nakan ji nauyi da kunya akan kaina balle kuma da mutane a wurin.
Cikin nutsuwa ya fara yi mini bayanin rubutu da daurikan magunguan da suke gabansa. Rubutun cikin wata jarka ne yayin da daurikan maganin ya kasance uku daya asha da zuma kullum da safe daya kuma a tsiyayi rubutun kofi daya a zuba karamin cokali sai ya sha idan zai kwanta. dayan kuma a ruwan wankansa za a zuba duka tsayin sati hud'u. Ya sake d'auko wata madaidaiciyar jarka itama cike da rubutu shi kuma kullum da daddare idan zai kwanta za a shafe masa jikinsa da shi.
Sosai ya yi mini bayani ya kuma ce mini na kula kada a tsallake rana d'aya.
Godiya da ni dashi muka dinga yi wa malamin har sai da ya dakatar damu yana dubansa ya ce." Har yanzu a matsayin uba nake a wurinka shin ko ka manta ala'ka da dangantakar da take tsakanina da mahaifinka. Godiyata ga Allah da Ya sanya ina raye wannan kaddara ta same ka. Allah Ya lamunce mini da taimakonsa aka samu mafita don haka tsakanina da kai babu godiya Tajuden yadda zan tsaya akan matsalar yarana hakan nan zan tsaya akan matsalar yaran abokan k'uruciyata."
Wannan kalaminsa ya kashe mana jiki gabad'aya muka yi sallama da shi muka fito
Wannan karon ma ya tsaya tsakiyar tsakargidan kamar wancen lokacin da za mu tafi yana yi wa iyalin malamin sallama.
Na shiga d'akin na fito da 'yar akwatina ina fad'in." Mun gode sosai Allah Ya saka da alheri Allah Ya biya ku da aljanna."
Gabad'aya suka dinga amsawa suna yi mana fatan alheri kamar koyaushe ya riga ni fita na bi bayansa Inno har bakin soro na farko ta rako ni tana fad'in." Allah Ya tsare ya kuma kiyaye hanya Hajiya Amina."
Yaransa suna jikin mota a tsaye sai suka ba ni tausayi ganinsu a jeme kwana biyar da tufafi daya a jikinsu ko sun yi wanka shi suke yi mayarwa abin ya ba ni tausayi ainun. Amma kuma kallo daya za ka yi musu ka ga annashuwa da farinciki a fuskokinsu sai washe baki suke yi suna sallama da Malam Rabi'u da ya biyo bayanmu. Sukairaju ya bud'e masa motar amma bai shiga ba ya tsaya suna magana da Rabi'un ganin haka ya sanya ni shiga na zauna kimanin minti biyar ya shigo da Bismillah a fuskarsa.
Ajiyar zuciya na sauke bayan mun hau titi na dan lumshe idona ina ambaton sunan Allah Ubangiji Allah kada ka kara maimaita mini wannan tashin hankalin da shiga.
Har muka isa gidan Hajja bai fi sau hud'u muka yi magana ba dalili akwai yaran shi don Sukairaju ma yana daf da shi shiyasa ya kama kansa ya dai gaya mini cewa shi ya hana su Hajja zuwa ayau din ita a yadda ta so su zo sai mu sake juyawa tare.
Kawunansa biyu muka samu a gidan Hajja Alhaji Sa'idu da Alhaji Haruna wanda shi baya gari ma al'amuran suka faru sai da ya dawo tukkuna ya samu labari.
sai kuma Inna Uwani ita kad'ai ce ban ga Hauwa ba sai 'yar uwarsa Hajiya Saratu.
Sun d'an jima tare da shi suna tattauna mas'aloli da yawa kafin su tafi.
Shi ma ba su jima da tafiya ba ya tashi yana fad'in zai shiga ya kwanta gidan tunda yana da wajensa na mussaman a gidan wanda ya shirya shi domin yin rayuwa da matarsa ta farko Samira Allah bai kaddara zama ba.
Ina Uwani ta kasa yarda mu had'a Ido ban san dalili ba daga zarar na daga kaina ana hira sai ta yi saurin sunkuyar da kanta kasa na dinga tunani akan abinda yasa take yin haka. Har dai abin ya zo yana ba ni dariya babu mamaki tana jin kunyanta ne da tsoron kada na tona mata asiri a wurin yar uwata tunda yanzu an yi walkiyya asirin Hajiya Maryam ya tono to ita kuma tasan na ganta da idona tana yarfa masa ruwan rubutu mai d'auke da magani a hanyar wucewarsa a shekarun baya. Cikin zuciyata nace jininka ma yana yun'kurin cutar da kai ina ga kuma wani daga waje wanda yake karyar so. Ai soyayya ta gaskiya itace ka so mutum tsakani da Allah ka so abinda yake so, ka gaya masa gaskiya a duk lokacin da ya kauce hanya. Ka k'yamaci munanan ayyukan da yake yi kuma ka yi kokarin nuna masa hanyar daidai. Babu wata soyayya ta gaskiya da za ta sanya ka illatar da wanda kake so ta hanyar son rai wannan zalinci ne a so ba cikakkiyar k'auna ba.
Muna nan zaune wajan daya da rabi Yusi ya dawo daga makaranta suna da lakca da sassafe ya fita ba don ya so ba.
Muna gaisawa yana tambayata ina Baba. Hajja ta ce ya fita harabar gidan Sukairaju zai nuna masa inda yake. Aikuwa ya tashi ya fita da sauri anan ya bar tarkacensa na makaranta ya fita da sauri bai damu da tsokanar da ake yi masa ba.
Ni hakan bai ba ni mamaki ba tunda na dade da sanin matsananciyar soyayyar da take tsakaninsu. Shi Kamalu baya ma garin gabad'aya a jiyan da yamma suka tafi Abuja wurin wannan malamin professor Ma'kari.
Da yammacin ranar dai ya tura Sukairaju can gidanmu na sharad'a da kayan shi a can ya d'ebo masa duk abinda ya zama lallai zai buk'ata a son ransa mu tafi can mu biyu Hajja ta ce a a mu zauna anan din na tsayi sati tukkuna ko sati biyu idan ya so idan ma abujan za mu koma shikkenan.
Ganin haka sanya ni sanar da Sahura tunda ni ma ina da kaya a can ta sake d'ebo mini. Na kira Hamusu na ce masa ya sayi yaduka masu matsakacin kudi kala bibbiyu ya bayar da d'inki Sukairaju da D'ahuru da kuma Ade ya san biyu Ade din ne bai sani ba na ce shi ma ba shi da tsayi sosai Amma dai duk ya fi su ki'ba da kad'an. Na tausaya musu da zama da kaya daya babu dadi kamar akwai cutarwa.

A daran ranar na fara ko'karin yi masa amfani da rubutu da magunguan da malamin ya ba shi tunda ya jadadda mini sosai kuma a gabansa. Babu matsalar zuma ya had'a da ita gangariya ce farar sa'ka wannan da safe ya ce ya sha kafin ya ci komai.
Da za mu kwanta ne a lokacin da za a shafa na shafawar a duk jiki na ga shegantaka ya cire jallabiya har da gajeran wandon ya zauna a haka na ce babu kyau kallon tsaraicin mutum ya ce ai yana jin lokacin da malamin ya ce sai babu komai a jikinsa za a shafa rubutun har yana kara jadaddawa ya ce ki shafe mini ko'ina na jikina.
Ya kwanta abinsa babu kunya ba tsoron Allah da jin nauyin abinda ya yi. Na jima kaina a sunkuye da rubutun a hannuna. Ba wai shafawar ce matsala ba yadda zan kalle shi a haka shine damuwar na tashi na je na kashe fitila na dawo da lalube na zauna na fara shafa masa a haka a cikin duhun. Bai yi yun'kurin yi mini komai ba har na gama bai kuma yi magana ba a takaice na ce." Na gama.'' Ya lalubi wayarsa ya kunna hasken yana ko'karin tashi zaune na d'auki wandonsa na ciki na bashi ya sanya sannan yasa jallabiyar ya koma ya kwanta.
Sai da na yi wanka da alwala tukkuna na kwanta gefansa wanda duk a tunanina bacci yake yi. Ya janyo ni sosai ya rungume tsam. Haka muka kwana bai yi yun'kurin yin wata mu'amula ta aure da ni ba sai dai duk juyi zai sake rike ni a jikinsa ya sanya bakinsa wuyana ya sumbuta da haka har asubahi ta yi muka tashi kusan a tare......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*



[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Littafin kudi ne akwai complete 2k a Telegram normal What'sapp group kuma 1k akwai a arewa pen domin biyan kudin karatu......0542382124....Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*131*
A ranar da muka wayi a gari a gidan Hajja muka dinga kar'bar mutane mabambamta ciki har da su anti Yagana Babanmu da Sahura wadda ta kawo mini kayan dana ce ta d'ebo mini.
Babanmu dai bai wani dade sosai ba ya tafi babu yadda ban yi da shi ba akan ya zauna ya huta ya kuma ci abinci sai asa direba ya mayar dashi gida ya ce a a tafiya zai yi ba zai zauna ba. Ina jin dadin yadda yake ko'karin kama mutunci da kuma girmansa ba ya ta'ba yadda ya yi abinda zai zubar mana da mutunci gabad'aya.
Yini muka yi tare da su anti Yagana Ummansu Hadiza da Sahura ana ta hirar duniya Ummansu Hadiza dai ta yi shiru kanta a kasa sai dai ta yi d'an murmushi yanayinta gabad'aya babu dad'i zantukan da su anti Yagana suke yi akan Hajiya Maryam da irin zagi da tofin alatsinen da suke yi mata shine ya dan dameta wata'kila tunda itama tana ta'ba harkar bin malaman yasa ta damu tana ganin kamar anti Yagana da gayya take zage-zagen tun muna yara muka tabbatar da hakan yanzu ne da duniya ta juya mata baya ta gane babu sarki sai Allah ta daina, to babu kudin yi ma a yanzu amma ba zan ta'ba mantawa ba ita har zannuwanta take sayarwa ta tafi wajen malami.
Sai yamma Garba ya d'auke su a mota domin mayar da su gida ina jin anti Yagana tana gayawa Hajja za ta sake dawowa kafin ta tafi domin da Hajjan cewa ta yi wai su zauna su kwana.
To ita Sahura da mijinta duk da har yanzu ba wai sun shirya ba ne ta dai koma amma a yadda take ba mu labari ta'ki sakin jiknta da shi har yanzu kuma shi bai fasa shirye-shiryen auransa ba da ya rage wata biyu a daura tunda budurwa ce yarinyar da zai aura.
Shine fa take gaya mata cewa za ta dawo kafin ta tafi wanda ni nasan ta fadi hakane kawai amma ba dawowar za ta yi ba.
Kwananmu hud'u a gidan Hajja mutumin ya warware sosai ya ma fara fita yana duba ma'aikutunsa nan yana kuma yin baki a kai-akai.
Ranar da muka cika sati daya a gidan Hajja da sassafe ya tafi
bunkure bayan la'asar ya dawo sai da ya yi wanka ya ci abinci tukkuna yake gaya mini wai an bashi sa'ko ya kawo mini. Na ce sakon menene ya ce bai sani ba yana mota wata yarinya ce wai Hajara dariya na yi ina fad'in." Ai k'awa na samu a gidan.
Ya gyad'a kansa bai ce komai ba. Can kuma ya ce gobe za mu tafi Abuja Amina hankalina na kan yara.
Na d'an yi shiru Ina kallonsa mun yi waya da Kamalu shekaran jiya tunda yana garin tare da ayarin abokansa masu neman da'awa. Ya ce mini ya je gidan domin duba yaran suna nan lafiya lau har Hauwa ta ba shi turare.
Mamaki na yi sosai Hauwa ta koma kenan amma ba ni tsammanin iyayen sun sani da shi mai gayya da aikin da ko maganarta ma baya yi. Kenan idan tana gidan a ganina yaran ba za su yi kad'aici ba fad'in haka daga wajensa ya tabbatar mini da cewa bai san cewa ta koma ba. Yadda bai san lokacin da ta tafi ba haka zalika ta koma bata gaya masa ba ya makomar auran na su take ni dai har yanzu daga wajensa ban ji wata tartibiyar magana ba. Amma na tabbatar da cewa ba zata koma ba tare da sanin mahaifiyarta ba.
Na ce masa hakan ya yi ni ma hankalina yana kan yaran yanzu duk da nasan ba su da wata matsala dalilin samun k'wararriyar mai raino.
Tun bayan tashinsa yau sati daya kenan bai ta'ba neman yin sunna da ni ba sai dai yakan rungumeni ya tatta'ba abinda yake so a jikina har mu yi bacci a wanda ni kuma hakan ya kan jefa ni yanayi na damuwa da buk'ata dalili sha'awata takan motsa sosai na shiga wani yanayi na gigita. Ban ta'ba kawo cewa matsala ba ce sanin da na yi masa gwarzo ne sosai a wannan gefen jajurtacce ne wanda duk fitinar mace yakan k'ureta. Sai a yau da muka lula cikin shau'kin da muka kwana biyu ba mu riski kanmu ba a ciki ba. Sosai muka kai k'oli a lokacin ya yi ta ko'karin ganin mun yi kamar yadda muke yi amma abin ya ci tura ya fara da k'umaji da karsashi amma kash jim kad'an jikinsa ya mutu ya gaza tab'uka komai na yi iyakacin yina domin ganin mun cigaba da nemawa kanmu mafita amma hakan bai samu ba k'arshe ma kirif mirginawa ya yi ya kwanta gefena ya kama bacci abinda bai ta'ba faruwa ba kenan.
Na tashi zaune tare da sanya rigata ina kallonsa gabana na faduwa. Me yake Shirin fad'uwa kuma. Tarihin rayuwata dashi babu ranar da ya ta'ba gaza mini a shimfida duk yadda nake ji da fitina ya fi ni, koyaushe ma cikin kirkiro abubuwa yake yi wanda yake jefe ni d'imauta da shau'ki.
Kasa ha'kuri na yi sai da na tashe shi ya tsarkake jikinsa tunda ka'idarmu ce ni da shi ba ma kwanciya sai da tsarki.
Da safe duk yadda ya so ya danne damuwarsa sai da fuskarsa ta nuna abin shima bai yi masa dad'i ba. Na yi ta nazari akan abinda ya faru a jiyan shin asirin ne bai sake shi ba ko kuwa wata sabuwar matsalar ce ta kunno mana.
Da rana da kaina na bashi abinci a baki da yake towon shinkafa miyar taushe ne idan na gutsiro nasa masa baki sai ya had'a da yatsuna ya tsotse a haka ya rikita ni sosai ina daurewa har sai da yanayina ya canza gabad'aya kwanciyar nan tasa ta sanya shi k'aro fitintinu fannin romance. Amma kuma kamar wanda aka dasa wa tsoron yin auratayya da ni. Haka muka ciyar da juna abincin kamar sababbin amare muna ta soyayya muka sake hawa gado nan ma abinda ya faru jiya da daddare ya sake kasancewa. Da mazantakar sosai irin ta d'a namiji yake dumfarata amma jim kad'an da farawa sai ya yi realizing jikinsa ya mutu!

Gudun aure littafin kudi ne Hajiya kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ni dai kamar zan yi dan k'aramin hauka na fashe da kuka ina kallonsa a kwance gabad'aya hankali ya tashi ban ta'ba cikin da ya sanya ni masifar son jima'i ba tun yana karaminsa sai wannan.
Ya tashi ya kamo ni ya riga ya gane akan abinda nake yi wa kuka na kasa daurewa domin abin sabo ya zo mini abinda nake ci na ture amma yanzu ana dan sammi ni kad'an wanda yake tayar mini da kwad'ayina. Ya fara kici-kicin ko'karin sake jarrabawa babu ma mazantakar kamar ta farko ban kuma ji abin yaje can har inda ya cancanta ba. Hawayen takaici ya dinga ziraro mini ta gefen ido. Ya gama jagwalgwalani babu biyan buk'ata ya sauka shima kamar ya d'ora hannu aka ya kurma iho ya shiga bandaki.
Na tashi zaune rungume da bargo a jikina na kasa danne kukan yin sa nake yi tukuru domin gabad'aya jikina ya riga ya nuna ga abinda yake buk'ata kuma bai samu ba. Ina da sha'awa daidai misali amma abin ya kara tu'azzara sakamakon cikin da nake d'auke dashi wanda shi bai ma san da shi ba.
Ya fito ya same ni a haka ya sanya kayansa ina zaune yana fad'in."Kin ga halin da na tsinci kaina a ciki ko Amina."
Na dube shi ina jan hanci ban ji haushinsa ba sanin da na yi ai da ba haka yake yi ba tabbas akwai matsala ko asirin ne har yanzu bai gama rabuwa da shi ko kuma dai wata matsala daban.
Na ce." Kai me kake tunani da hakan?"
Ya d'an yi jim kafin ya furta." Jiya zuwan da na yi bunkure yana da ala'ka da hakan Amina aikin da Maryam ta yi wata'kila har da wanda zai hana ni mazantaka da gamsar da iyalina wace irin masifa ce wannan Amina? Maryam ba sona take yi ba wannan mugunta ce."
Ya krasa maganar kamar zai rushe da kuka har da 'yar kwalla a idonsa.
Na ce." To yanzu me malamin ya ce?
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan cigaba da amfani da magunguan da ya had'a mini da farko ai yau kwana takwas kenan kuma na sati biyu ne idan na kammala ya ce sai na yi magana da shi domin tabbatar masa da cigaban da aka samu. Amina na fi ki shiga tashin hankali domin ban shirya rabuwa dake ba"
Ya riko hannuna ya matse sosai yana fad'in." Ko mu k'ara jarrabawa yanzu?"
Da sauri na girgiza kaina na ce." A a mu bari ka gama amfani da maganin da rubutun sai mu sake gwadawa amma ka daina maganar rabuwa ba zan iya ba ni ma."
Ya d'an rungomo kafadata yana fad'in." Ji bi kukan da ki ke yi fa Amina nasan wacece ke tsakanin jiya da yau ke kadai ki ka san halin da kike ciki tun d'azu da muna cin abinci na fahimci damuwarki."
Na sanya hannu da sauri na goge kumatuna ina fad'in." Ka daina fad'in haka ni ba wannan ne damuwata

Please Login or Register in order to submit comment