Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'in." Anti Amina don Allah ku rufa mana asiri don Allah anti Amina."
Na ri'ke hannunta har na ji yana karkarwa na gane akan abinda take yi wa kuka da tashin hankali kada maganar nan ta fita mutane su gazgata zarginsu.
Sosai na ri'ke ta ina fad'in." Ki kwantar da hankalinki Nusaiba, yadda Ubangijin da ya hallice ta ya rufa mata asiri a lokacin da take raye ya amince da jama'a su ambaci alherinta da kyakykyawan fata har ta rasu to ban ga dalilin da zai sanya don ganin wani sirrinta da ya kasance tsakaninta da Allah ya sanya ni fad'i a gari ba. Na yi miki alkawari kan cewa ni dai babu wanda zai ji haka daga b'angarena, muna ro'kon Allah Ya yafe mata, mu kuma rayuwarmu ta yi kyau a duniya da lahira ."
Ta dinga godiya cikin rawar murya da tashin hankali.
Na ji maganar Salim yana fad'in." Wannan takardun gidan da ta saya ne a kano da filaye uku sai na shagunanta biyu dai na san haya ta kar'ba amma watannin baya kafin ta kwanta ciwo ta ce mini sun gama magana tana so ta biya kudin duka su zama mallakinta."
Ya ce." To tunda ka ga baka ga shedar mallaka ba a cikin wannan takardun da suke hannunka wata'kila ba ta biya su ba, amma dai ka bincika mana wanda suka bata hayar wajan mu ji daga gare su kafin nan sai a had'a kan komai a zauna domin sauke mata nauyi."
Ya amsa a sanyaye yana had'a kan takardun ya mik'a masa ya kar'ba ya mayar cikin dirowar da kudin da sarkokin. Sauran biyun da suka zama na karshen fitowa kama bai mayar da su ba. Tsabar fargaba da tashin hankali a duk lokacin da na dubi mutum-mutimin da ya sha d'auri tamau sai gabana ya fad'i lallai bokan da ya sassa'ka suffofinsu ba 'karamin hatsabibi ba ne. Fuskar Baba sak da yanayin jikin itama suffarta sak rai ne kawai babu a tare da su amma an had'e su waje daya an nannad'e da likkafani da jan zare sai da na k'ura ido ma tukkuna na hangi da wasu 'yan mici-micin layu sun saje da jan zaren ne shiyasa ban gansu ba ga wasu manyan mukullai an had'a an kulle.
Ina can cikin tunani na ji maganarta tana fad'in." Anti mun tafi."
Da sauri na daga kaina ina fad'in." Ki gaishe mini da yaran Nusaiba."
Ta amsa da in sha Allahu kafin su fita da sanyin jiki.
D'akin ya kasance shiru bayan fitarsa.
Ya juyo yana kallona muka zubawa juna ido na dan wani lokaci. Ji na yi zuciyata ta tsinke haka kawai sai na ji ina tausayinsa wace irin masifa ce wannan ni Amina matar nan ashe d'aure mutumin nan ta yi sai ta yi aikin akan ga'ba dama aka ce asiri yana tasiri sosai mussaman idan ya tarar da hali.
Ya d'auki abin zai kwance da sauri na ce." Ka ajiye kada ka ta'ba"
Ya kuwa ajiye da sauri a tsorace yana kallona.
Na ji hawaye sun zubo mini wannan d'aurin ba k'arami ba ne tunda har ta yi masa wannan boyon ina jin tsoron duk ranar da aka warware d'aurin ya fadi ya mutu ko kuma ya kwanta jinyyya mai tsanani mafiakasari irin wannan mugun aikin wad'anda suka yi sune suke da makarinsa.
Kuka kawai na dinga yi hankalina ya yi bala'in tashi ainun muna cikin masifa ni da yara Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ya zo ya rirrike ni hankalinsa a tashe yana fad'in." Menene abin kuka Amina na amince Maryam ta cutar da ni ta mini illah a rayuwata amma godiyar da nake yi ga Allah yadda ya zaunar mini dake ba ki bar ni ba. Har kullum idan na daga kaina na dube ki sai na ce alhamdulillahi a zuciyata na kuma yi alfahari da kasantuwarki matsayin matata abokiyar rayuwata. Na gode Amina, Na gode kin so ni kin zauna da ni a lokacin da mata suka guje ni, kin yi mini biyayya bisa abinda ranki ba ya so, kin daraja mahaifiyata kin kyautata mata a yau ina gaya miki bayan mahaifiyata ke ce ta biyu a cikin matan da nake alfahari da su, ina so mu kasance tare anan gidan duniya da kuma na lahira."
Kuka na ya sake tsananta jin irin zantukan da suke fitowa daga bakinsa. Gabana ya cigaba da bugawa tsigar jikina na tashi na sanya duka hannuwana biyu na matse shi sosai a jikina ina fad'in." Rayuwarmu da ni da yara za ta shiga garari idan babu kai a cikinta Maryam ta illata mu muddin warware wannan d'aurin da yake tsakaninku ya haddasa masa maka mummunan ciwo. Ko ba ka gaya mini ba kwanciya ciwon da ka yi a kwanakin baya yana da ala'ka da irin ayyukan da ta yi a kanka a jikina na ji hakan mutuwarta abubuwa suka fara lalacewa.
Ya ki'dime sosai yana d'an jijjigani da rawar murya yake fad'in." Ba abinda zai faru, na yarda Maryam ta yi mini illah Amina amma bata samu nasarar kai ni k'asa ba, ga ni ina raye tare dake ta jefe ni sosai ta ko'ina ta dabaibayi ni da d'aurin baki domin kada na hangi lefinta amma ni jin dadina da bata nemi hanyar da zata illata mini ke ba Amina kamar yadda ta ci laya akan Hauwa Allah Ya d'auki ranta kudirinta bai cika ba. Ba ki da hakkinmu da ni da ita shiyasa bata ma yi tunanin cutar da ke ba. Tsafi gaskiyar mai shi na gazgata hakan ne a kwanakin nan da suka wuce da muka je da wani malaminta ya warware ayyukan da ta sanya shi ya yi aikana wannan shine dalilin da ya sanya ni wannan kwanciyar na dinga bacci da ciwon jiki. Ban zalinceta ba amma ni ta zalince ni ta hanyar d'addaureni ta ko'ina babu gaira babu dalili tare da haddasa mini rikici da husuma ta karkashin kasa a gidana. Tunda har ki ka ga na tashi yanzu bayan warware wancen makarun da ta yi mini to warware wannan ma ba zai zama cutarwa a gare ni ba in sha Allahu."
Na dago ina dubansa tare da cewa." Da bakinka fa ka ce tare ku ka je da malamin da ya yi aikin ya warware da hannunsa. To shi wannan din kana da makarin warware shi, ka dubi abubuwan da suke jikinku kai da ita kuma likkafani ne ya yi muku sansani da kai da ita. Wata'kila ta yi aikin ne akan idan ta riga ka mutuwa duk ranar da aka kwance d'aurin da yake tsakaninku kaima ka bi bayanta, idan hakan ba ta samu ka kwanta ciwo mai tsananin gaske."
Ya yi shiru yana kallona a d'an tsorace! sai ya sake matseni gam a kirjinsa yana kiran sunan Allah tare da sake duban idan gunkin mutumin-mutumin na su yake ajiye.
Muka kasance cikin shiru da zullumi jikinsa ya yi bala'in mutuwa ya yi mini wata matsa tsam kamar yana jin tsoron a k'wace ni.
Minti goma a haka muka wanzu babu magana ya cika ni tare da zuwa ya d'auko wayarsa. Ya zauna yana fad'in." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Kimanin minti biyar yana waya da Malam Rabi'u kafin su yi sallama ya dube ni yana fad'in." Akwai gaskiya a cikin maganarki Amina. Ba ni da masaniyar akan malamin da ya yi wannan aikin don haka dole zuwa kano ya kama ni can kauyen Bunkure wajan Malam D'aha abokin mahaifina ne in sha Allahu ina da yakinin shi zai warware mini wannan d'aurin kuma babu abinda zai same ni da izinin Allah."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." To ita fa waccan kwalbar mai layu a ciki."
Ya ce." Har da ita za mu je gaban Malam din duk abinda yake da akwai Allah zai bayyana shi."

A daran ranar ban iya rintsawa ba har ya ma fi ni tawakkali a wannan ga'bar hawayen idona kuwa ya kasa tsayuwa domin sai nake ganin kwance wannan tsatstsauran d'aurin da yake tsakaninsu zai kassara masa rayuwa idan bai fadi ya mutu ba to ya yi mutuwar tsaye tunda bata raye a duniya to kowace mace ta yi asara. Abinda na ke ji a raina kenan shine kuma ya hana ni sukuni don daga zarar na tuna irin wahalar da ya sha kwanakin da suka wuce sai hankalina ya sake tashi zuciyata tana ta raya mini cewa wannan likkafanin da yake d'aure a jikinsu ita dashi akwai alamar tambaya a kansa tunda duk inda aka ce an yi wa mutum asiri da likkafani ko an binne a makabarta abu ne mai munin gaske. Tsakanin d'azu da safe da yanzu da muke cikin talatanin dare dana juya na kalle shi zan ji wani bala'in tsoro da tausayi da kaunarsa a cikin zuciyata idan ya mutu ni da yara mun shiga masifa wace rayuwa ce za ta biyo bayan faruwar hakan, me zai faru? Maryam ta so zuciyarta ta cuce ni ta cutar mana da yaranmu.
Na jima a sujjada ina kuka ina ro'kon Allah har sheshshekar kukana ya tashe shi ya kira sunana na juya na dube shi yana fad'in." Me yasa wai kike wannan kukan ne? Na gaya miki ba ni so ni shine kadai yafi damuna ki zo ki kwanta babu abinda zai same ni."
Kasa tashi na yi daga saman daddumar na cigaba da jan hanci ina share hawayen da nake ta ko'karin tsayar da shi amma ya'ki yatsuwa.
Ya sauko ya zo ya zauna gabana har da tankwashe kafa. Na kalleshi baccinsa ma yake yi shi kamar abin bai dame shi ba.
Ya ri'ko hannayena cikin kulawa yana fad'in." Ban san haka kike sona da yawa ba Amina, Maryam ashe k'aryar so take yi mini tunda har za ta iya cutar da ni ta hanyar yi mini mugun k'ulli mai razanarwa.
Ha'kikanin so shine irin wannan wanda ki ke yi mini. Kuma na tabbatar da hakan ba tun yau ba daga wajenki Amina, abu daya za ki yi mini yanzu shine ki ji maganata ki share hawayenki ki tashi mu je mu kwanta."
Ya sanya tafin hannunsa ya goge mini fuska kafin ya ri'ke hannuna na tashi da kansa ya cire mini hijab din wuyana muka nufi gadon yana ri'ke da ni sosai a gefansa....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*

[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<2<3
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram. Wshap Gruop 1k via 0542382124....Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*126*
Kwanciya muka yi a tare a gadon ya d'auki kaina ya d'ora saman kirjinsa sannan ya d'ora hannunsa a jikina a hankali ya ja bargo ya rufe mu gabad'aya. Rufe idona kawai na yi ba da niyyar bacci ba domin kuwa babu shi a idona wanda nake da tabbacin shi din bai sake komawa ba har aka kira sallah.
A tunaninsa bacci nake yi ina ji ya sauke kaina a hankali ya mike ya nufi toilet na tashi zaune ina kallonsa har ya gama abinda yake yi ya fito. Ya d'an tsaya yana kallona na d'an wani lokaci sai kuma ya girgiza kansa kafin ya kama hanyar fita ba tare da ya yi magana.
Sauka k'asa na yi a d'akina na yi wanka na yi sallah a gurguje na kimtsa jikina don babu yadda za a yi ayi wannan tafiyar babu ni.
Na sake komawa saman na shi sai na same shi har ya yi wanka ya shirya yana zaune gefan gado cikin kaftani gilas da hularsa a gefe yana waya dai da Rabi'un da suka yi magana jiya yana sanar da shi gasu nan zuwa.
Sai da ya gama tukkuna ya dube ni na zauna gefansa tare da gaishe ya amsa cikin kulawa ya dago fuskata muka kurawa juna ido. Kallon da yake yi mini ya kara karya mini zuciya hawaye suka zubo. Ya fara fadin." Kash! menene haka kuma? ki dubi idanunki sun kumbura Amina ni kam na tsanani wannan kukan wallahi." Ya fad'a cike da yanayi na damuwa da tashin hankali."
Sosai na fashe da kukan da karfin gaske ina fad'in." Ni fa wallahi tare za mu tafi."
Ya ce." Akan wane dalili, ai nima ba kwana zan yi ba kuma in sha Allahu da k'afafuna zan dawo gidana, kada ki yarda da abinda zuciyarki take raya miki Amina tunda har na riga na tsallake na baya to wannan ma zan tsallake in sha Allahu."
Na girgiza kaina ina fad'in." Ban yarda ba kawai dai mu je tare na raka ka hankalina zai fi kwanciya."
Ya ce." To yaran fa?''
Ya fad'a yana goge mini kumatu. Na ce." Su zauna wurin su Mairo ai da mutane a gidan ba za su ci karo da wata matsala ba in sha Allahu tunda dama babu wani sabo mai yawa a tsakaninmu."
Ya girgiza kansa yana cewa." To ai so nake ku saba yanzu ki zauna cikinsu sosai ki kula mini da su hankalina zai fi kwanciya ki zauna a gida na je na dawo Amina irin wannan rigimar taki ce fa ta sanya ban sanar dake na farko ba."
Na ce." Sai ka jefa zuciyata cikin damuwa ba, menene abin boyewa."
"To in banda abinki ai abin alheri shi ake shela, sharri kuwa ba abin fad'i ba ne."
Ya ri'ke hannuna yana duba zoben azurfan da ya sanya mini a yatsana."
A d'an sanyaye ya ce." Kin amince na je na dawo ko matata?"
Girgiza kaina na yi tare da fad'in." Wallahi ban amince ba tare za mu je gashi ma na shirya."
Ya yi jim na dan wani lokaci kafin ya furta." Tunda dai har kin rantse ba zan karya miki ita ba."
Na sauke ajiyar zuciya Ina fad'in." Na kawo maka abinda za ka ci ko?"
Ya ce." Ke 'din kin ci?"
girgiza kaina na yi. Ya furta." To je ki kawo sai mu yi breakfast din tare."
Na tashi da azama na sauka k'asa ina jin dad'in yadda ya amince tafiyar da ni.
To ba mu isa 'kauyen Bunkure ba sai gefin la'asar tafiyar mota ce K
kuma ta samu k'wararran direba Ade wannan karon tare aka tafi da shi su uku da Amintattun yaransa Sukairaju da D'ahuru.
Ko da nake cikin a garin kano kafata bata ta'ba taka garin ba sai a wannan karon. Yadda dama muka shirya shine idan har abin ya zo da sauki mun kammala abinda ya kawo mu gidan malamin sai mu wuce can gidana na sharad'a mu kwana idan ya so idan mun gaisa da Hajja zuwa jibi sai mu tafi.
Mun samu tar'ba ta mussaman a gidan Malam D'aha. Na ga kara da karamaci irin na mutanan kauye domin kuwa ina idan da sallar magriba aka cika gabana da kwanukan abinci har daga ma'kota. Mafiakasari towo ne na masara dana dawa sai wata langa da aka kawo mini ita daga baya cike da dambu na tsaki wanda ya ji zogale da gyad'a yana ta k'amshin mangyad'a zuryan da yajin barkono a gefe.
Ya ba ni sha'awa sosai na kuma yi masa cin yaushe gamo na toshe cikina da shi duk tarin yunwar dana nad'a a tsukin nan sai da na rasa yadda zan yi da cikina. A daddafe na yi sallar Isha'i. Ina idarwa wata matashiyar budurwa ta shigo doguwa mai duhun fara ba ta da jiki sosai akwai yarinta a tare da ita ta sake gaishe ni na amsa ina fad'in ta kwashe kwanukan abincin da ta dinga kawo mini gasu nan shida a jere.
Ta tsuguna tana bubbud'awa ta dube ni tana fad'in." Ai d'aya kawai ki ka ci Hajiya."
Na ce.'' Ina zan kai wannan abincin yar uwa wannan ma na gode sosai kuma wallahi ya yi mini dadi 'kwarai da gaske."
Ta yi murmushi ba tace komai ba ta fara had'a kan kwanukan tana fita da su.
Na d'auki wayata dake gefena na duba na ga network dina ya d'auke gabad'aya wata'kila yana da ala'ka da yanayin d'akin da nake ciki tunda na 'kasa ne kuma a k'asa yake sosai.
Gabad'aya hankalina yana can b'angaran malamin tun zuwanmu da muka shiga tare na gaishe shi na fito ban sake jin wani motsi ba sai ta hayaniyar iyalin gidan da shige da fice da ake ta yi na d'aukar abinci daga almajiran malamin.
Gajiya na yi da zaman d'akin na fito tsakar gidan na samu jama'a a cike da yake mai yalwa ne kwarai matan gidan su hud'u suna can daga gefe suna cin abinci a tare wasu daga cikin yaran kuma sun ci sun gama wasu na cin na su. Kwanuka gasunan birjik a bakin manyan tukwanansu.
'Yar budurwar nan da har yanzu ban san sunanta ba na ji tana fad'in." Bandaki za ki shiga.''
Kafin na ce komai daya daga cikin matan gidan ta ce." Hajara zuba mata ruwa maza a buta Hajiya alwala za ki yi ne?"
Na ce." A ai na yi sallah na fito na sha iska ne." Yarinyar da aka kira sunanta da Hajara ta d'auko tabarma da sauri ta shimfida mini can gefe na je na zauna ina yi mata godiya cikin ikon Allah zamana ke da wuya network din duka layukana ya dawo.
Na fara neman number Sahura muka gaisa sosai ta sake yi mini gaisuwa nan nake sanar da ita cewar na shigo garin zan kira ta zo gida ta same ni zuwa gobe.
Muna sallama na nemi number Hajja da ta shiga sai ta katse na kira ya kai sau biyar nan na gane network din yake hawa da sauka wai ina so na gaya mata cewar za mu shigo gobe.
Na dauki kimanin minti talatin da zama a tsakargidan wanda ya yi daidai da lokacin tara na dare da minti biyar.
Daga can b'angaran malamin na ji maganarsa alamun zai fito na sauke ajiyar zuciya a hankali idona a kan hanyar suka fito tare da wannan Rabi'u da yake yawan kiransa a waya wanda shine ya kan gaba wurin tararmu lokacin da muka sauka a garin.


littafin gudun aure na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Suka fito tare da kuzarinsa ya tsaya cikin kulawa yana yi wa matan gidan sallama na tashi ina gyara mayafina na d'auki jakata can inda suke zaune na nufa ina fad'in." Za mu tafi, na gode sosai da karamaci Allah Ya saka da alheri, na dubi Hajara dake zaune cikin 'yan uwanta na ce." 'Yar uwa sai Wani lokacin ko na gode da kulawa."
Ta washe bakinta tana fad'in." Ku gaida gida Allah Ya tsare hanya."
Na ce." Amin Ya Allah tare da yin gaba ganin ya riga ni fita ina jin matan da yaransu suna ta yi mini fatan alheri.
Ina fita daga can wajen motar da mu ka zo Sukairaju nake hange da D'ahuru sai Rabi'un suna taga-taga kafin na hangi Baban ya yi wata irin fad'uwa irin ta ruf da ciki da kirji.
Ade ya fito daga mota a ki'dime! yayin da gabad'aya suka rufu a kansa duk da yake dare ne amma ai irin na karkara ne da suke da wadatar kwanciyar hankali ba irin cikin gari ba hakan ya sanya mutane fara tsayuwa a wajen.
Ban san inda nake jefa k'afafuna ba kawai dai na tsinci kaina a tsakiyarsu lokacin da suke ko'karin ciccib'arsa. Rabi'u yana fad'in da k'afafunsa ya fito kuna dai kallo magana ma muke yi da shi ya yanke jiki ya fadi."
Jikina ya dinga kyarma na tsuguna ina d'ago kansa yana karyewa ganin haka ya sanya ni ihu! ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Baba Baba, na dubi Sukairaju a gigice ina fad'in." Ku d'auke shi mu tafi asibiti."
Rabi'u ya ce." Cikin gidan za mu mayar da shi Hajiya ."
Daga haka suka fara kici-kicin ciccib'arsa Sukairaju ya cire gilashin idonsa da wayoyinsa tare da wallet dinsa ya sanya cikin aljihunsa su biyu shi da D'ahuru suka kama saman shi ta wajen kansa. Rabi'u da Ade suka rirrike k'afafunsa a haka ina kallo suka taitayeshi suka koma dashi cikin gidan suna ta Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.
Na bi bayansu k'afata na karkarwa shikkenan kuma tunda har kansa ya karye ya mutu.
Kai tsaye d'akin malamin suka nufa da shi gidan ya rud'e sosai da hayaniya duk kowa a tsaye na bi su ina kuka na fitar hankali. Babar yarinyar nan Hajara ta zo ta ri'ke ni ta baya ina cire hannunta tana sake ri'ke ni fadi take yi "Yi hakuri ki yi masa addu'a kin ji, Allah ya ba shi lafiya."
Na dube ta ina cewa." Ya mutu ko?"
Sai ta girgiza kanta cikin ko'karin kwantar mini da hankali ta ce." Bai mutu ba ke waye ya gaya miki."
Hawaye ya sake tsinke mini na ce." Kansa na ga ya karye ko'ina na jikinsa ya shika. Kin ga ai lafiya lau ya fito har muka yi muku sallama ko?''
Ta daga kanta cikin alhini ta ce." E, kwarai kuwa amma hakan ba shi yake nuna cewar bashi da rai ba zai tashi in sha Allahu."
Na ri'ke hannunta tamau ina fad'in.'' Ta cutar da ni, ta cutar da yaranmu ta zalince shi, ya yi mata alheri ta saka masa da sharri. Ta gigita mini rayuwata."
Kawai sai itama ta fara kuka ta rungume ni a jikinta tana cewa." Ki yi hakuri ki samu nutsuwa mu je can wajenmu ki zauna ki nutsu kin ji ko, ki yi wa mijinki addu'a."
Hajja ta fad'o mini a rai. Na sake fashewa da kuka mai gunji!
Ta kama ni sosai muka nufi d'an wajenmu a hankali take ta fad'in." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un. Na kama ni ma idan ta ajiye na d'auka.
Ta zaunar da ni saman tabarma tana cewa Hajara ta d'auko mata mafici.
Ta kar'ba ta fara fifita mini har yanzu ba ta cika ni ba domin ni kaina nasan ba a hayyacina nake ba gabana duf-duf kawai yake yi mini daga zarar na yun'kura zan tashi sai ta riko ni.
Gabad'aya yaransu da manya sun yi cirko cirko a gaba.
Da wani irin sauti na ce." Wayyo Allah anti Yagana kina ina?" Na silale saman tabarmar na kwanta hawaye suka dinga biyo gefan idona. Na riga fa nasan mutumin nan ya mutu kawai a fito a gaya mini ne ba za a yi ba.
Na riko hannunta ina sake tambayarta a karo na biyu ta girkiza kanta tana cewa." Na gaya miki fa bai mutu ba Hajiya yana da rai in sha

Please Login or Register in order to submit comment