Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da burushi na sami matan gidan suna ta aiki na yau na daban ne domin Sayyada na hanga a can cikin kicin ta dasa kujera tana ta suyar kaji. Mama tana gyara alayyahu ita kuma anti amarya tana tace zo'bon da yake kan wuta.......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*69*
Ina gama wanke bakin na shiga cikinsu muna aikin tare cikin zuciyata Ina tunanin ko saboda zuwan mutumin nan ya sanya Baban Saude yin wannan hidimar. Shiru dai na yi ban tambayi komai ba har muka kammala aikin gabad'aya towon farar shinkafa tas da miyar taushe wadda ta ji gyada da alayyahu gefe guda ga soyayyan man shanu nan da ya ji albasa. Ga soyayyun kaji nan masu yawa wanda Sayyada ta yi aikinsu.
Bayan mun gama komai tsaf na share gidan na wanke shi tas lokacin Baban Saude ya fito daga dakinsa da zummar wankan Juma'a. 'yan samarin gidan ma daya bayan daya duk suka shigo suka yi wanka suka yi shirin massalaci. Ana saukowa Baban Saude ya shigo da dadduma a kafad'arsa ya tsaya daga bakin kofar d'akin Mama lokacin muna ta aikin daura zobo a leda ya ce maza a fito da abincin nan akai wa almajiran massalaci kamar dai yadda aka saba. Salmanu shi ma yaronsa ne shi ya shigo ya rataye daddumar a kan taga kafin ya kinkimi kular towon ya fita da sauri Abahuraira shi ma ya shigo ya d'auki kular da aka zuba miyar a ciki ya fita da ita.
Da yake girkin anti Amarya ne itace ta had'a masa abincinsa a babban tire ya ce ta kai d'akin dai ta ajiye zai sake fita domin yana da ba'ko. Umarninsa ta bi ta yi yadda ya ce mata.

Muna cin abinci ina nazarin yanayin yadda Baban Saude ya tsara gidansa da rayuwarsa komai a tsanake babu harido babu hauka kawunan iyalinsa a had'e babu ba'kar gaba balle kishi mai tsanani. Sayyada ce take gaya mini ai duk ranar juma'a akan yi abinci mai kyau a kai massalaci akalla ya fi shekara goma yana wannan aikin ladan amma a cewarta na yau na daban ne domin kajin da ya sayo sun ninka wanda yake saya duk Juma'a. Jin haka ya sanya na gazgata zargina saboda zuwan Alhaji Tajo ne domin karramashi. Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baban Saude yana da kyawun zuciya kuma ba shi da niyyar kashe mini aure ko tozarta mutumin nan
Sai dai idan har ni na bu'kaci hakan.

Bayan la'asar hud'u da arba'in da shida Baban Saude da kansa ya fita domin zuwa airport ya taro shi. Kafin ya tafi sai da ya leko ya sanar da ni tukkuna sannan ya tafi.
To sai a lokacin ne jikina ya d'anyi sanyi na dan dinga jin fargaba amma ba sosai ba. Wanka na yi na shirya cikin doguwar riga amma ban yi wata kwalliya ba turare kawai na fesa a jikina na zauna gefen katifa da wayata a hannuna ina dubata. Tun ranar da ya d'ora hotunan d'aurin auransa ban kara ganin status d'insa ba, dama kuma ban ta'ba gani din ba, hakan sai ya k'ara tabbatar mini da cewa don na gani ne yasa tunda a lokacin ina ta neman hanyar da zamu shirya.

Koda na tuna irin wulakanci da rashin arzikin da ya dinga yi mini a lokacin sai raina ya 'baci na ja tsaki tare da gyara kwanciyata a katifar ina tunanin akan wannan tsohuwar matar ya ki'dime matar da ko wadataccen nono ba ta dashi k'aramin jiki ne da ita bata da wani tudu ta baya a tsuke take har gwara Hauwa da 'yar cikar 'kuruciya a tattare da ita. Ai na godewa Allah da ya sanya duk su biyun babu wadda za ta nuna mini kyawun jiki ta ko'ina har yanzu da komad'ata.
Ina daga cikin d'akin a kwance na ji shigowarsu ina jin muryar Baban Saude sama sama amma ban ji abinda yake cewa ba. K'amshin turaransa har d'akin da nake kwance k'amshin da hancina ya jima bai shak'a ba.
Zaune na tashi ina laluban mayafin rigar da take sanye a jikina gefe guda kuma gabana na d'an bugawa kad'an kad'an yanayin jikina ya fara sauyawa da wani lamari na daban..

Sai da na yi namijin ko'karin wajan ganin na rinjayi zuciyata don gudun kada ta kunyatani a gabansa. Ba ni da halin cire son da nake masa a zuciyata domin da damar a hannunata take ni kuma nake sarrafa zuciyata to ina ganin da ba wannan maganar ake yi ba. Ni kaina nasan Ubangijina ya jarrabe ni da kaunarsa inda Allah Ya taimakeni rauni na bai ta'ba barin na nuna masa mahaukaciyar soyayyar a fili ba, Ina ganin da ya fahimci haka wulakancin da zai yi mini sai ya fi wannan.

Kusan minti talatin da zuwansa Ina zaune a d'aki ni kadai ina ta tunanin mai yake faruwa a d'akin Baban Saude kuma ban ji ya kira ni ba, can na ji maganar Dada da sauri na tashi na fita na tsaya a bakin kofa tana d'akin Mama suna gaisawa ina tsaye a bakin kofa hannuna ri'ke da labule hankalina na bakin kofar d'akin Baban Saude takalma na gani uku a bakin kofar d'akin a zube ina tsammanin har da Babansu Fadila za a yi zaman domin na ji muryarsa a dakin. Dada ta fito daga d'akin Mama tana magana wadda ban fahimci me take cewa ba ta dube ni muka had'a ido sai ta ja tsaki kafin ta furta." Dube ta da ido a tsaye kamar an kama 'bera a massalaci, ashe abin naki duk karya ce."
Na bita da kallo ina gyara yanayina da tunanin maganarta to mai ta hanga a tare da ni da har take fad'in wannan maganar.
D'akin Baban Saude ta nufa tana cigaba da yin k'ananun maganganu wanda kad'an na tsinta daga ciki tana ce wa." Mu a lokacin mu ina muka san wani kai 'karar miji balle yin jayayya dashi da ganin daidai ake da juna, ai duk macan da tace ba zata yarda ta zauna a kasan mijinta ba tana tare da wahala shiyasa auran yanzu ai baya karko.''
Na dinga kallonta da bugawar zuciyata to me kuma ya kawo wannan maganar idan dama ba ta shirya tsinka ni a wurinsa ba, Ina ce ai tun kafin a yi wannan zaman Baban Saude ya gaya mata abinda ya faru. Shine kuma za ta zo ta canza magana. Gabana ya cigaba da fad'uwa na koma cikin d'akin na zauna jikina duk a sanyaye hakika ban ji dadin gayyatota da aka yi ba domin kuwa za ta iya fad'in wasu maganganun da zai sake bashi kwarin gwiwa, kuma da take cewa su a da ba haka suke yi ba to yaushe zata had'a mazan da dana yanzu, ai yanzu lamarin rijalu ya lalace domin kuwa da yawa daga cikinsu basa tsoron Allah wasu ma idan baka fito ka nuna musu cewa daidai ake ba to ba za a zauna lafiya dasu ba. Da yawa akwai mazan da sun fi so idan sun ce kule a ce musu cass! a hau sama a fad'o a tare a buga a goga hakan ya fi musu dad'i, amma wallahi idan suka samu mace saliha mai bin su sau da kafa sun fi yi mata iyashege da shegantaka.
Hankalina yana kan agogon da yake kafe a bangon d'akin biyar da rabi yanzu ina lissafi lokaci a k'alla yanzu ya yi awa daya da zuwa amma ba a neme ni ba, ai na d'auka ni ma za a zauna da ni domin idan ya fad'i abinda ban yi ba na kare kaina kuma a shirye nake da na amsa lefin da na yi na bashi ha'kuri.
Har na cire tsammanin cewa za a yi zaman da ni na ji muryar Baban Saude daga cikin d'akinsa yana kwala mini kira. Na amsa da sauri tare da tashi zumbur na d'auki mayafin rigar jikina na rataya a wuyana na zura takalmi na fita.


Littafin nan na kudi ne, don girman Allah kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

A nutse na shiga d'akin tare da sallama gabad'aya suka amsa har da shi da yake zaune a gefan Baban Saude Dada da babansu Fadila kuma suna zaune a waje daya. Gefe guda kuma kwanukan da suka ci abinci ne a ajiye. Gefan Dada na zauna ina 'kara daidaita yanayin da nake ciki.
A nutse na dubi Babansu Fadila na gaida shi ya amsa da sakin fuska kamar yadda muka saba gaisuwarmu cikin mutunci.
Sai da na sake daidaita yanayina tukkuna na dubi gefan da yake zaune muka had'a ido da juna domin dama tun shigowata na lura da cewa idanuwansa suna kaina. Na ce." Barka da yamma ya hanya?"
Ya amsa babu yabo babu fallasa da "Barkanmu dai ya kike?''
Shiru na yi ban sake cewa komai ba, d'akin ya d'auki shiru na sakkoni kafin Baban Saude ya yi gyaran murya a nutse ya dube ni yana ce wa" Amina tun kafin na kira ki zuwa nan mun tattauna abinda ya had'a mu anan mijinki kafin ya fadi aibunki sai da ya gama fad'in alhenki sannan ya fad'i dalilin da ya sanya shi yi miki wannan hukuncin domin horone a gare ki. Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Kamar yadda ki ka tuba ki ka kar'bi kuskuranki haka nan shi ma a yanzu kafin shigowarki na nuna masa illa da rashin dacewar abinda ya yi, domin kuwa ganganci ne mai girma tare da yun'kurin lalata aure kauracewa mace na tsayin wannan wattanin. Hakan ba daidai ba ne, kuma an yi wa addini tare da koyarwar Ubangiji kutse. Ni ba malami ba ne amma a iya sanina wannan abin da ya aikata kuskure ne, kuma gashi nan a zaune ya yarda kuskuran ya yi amma ya fadi hujjarsa wadda ba yi tsamarin ace an yi wannan kauracewar ba.
Annabin rahama bai hore mu da mu hora matayenmu ta hanyar kaurace musu tsayin wani dogon lokaci ba. Ya hore mu a duk lokacin da iyalinmu suka
mana wani abu na kuskure. Annabi S.a.w Ya ce." Ku nesanta kanku gare su na takaitacen lokaci ko kuma ku k'aurace musu a shimfida ku buge su kadan da gefan rigar jikinku. Gashi nan a zaune ya nuna mini ya yi nadamar abinda ya aikata amma ya fadi hujjarsa ta yin haka a cewarsa idan ya kasance a kusa dake a koyaushe zai iya d'aukar matakin da rayukan kowa zai 'baci wannan shine dalilin da ya sanya ya k'aurace miki na tsayin wannan watannin ammana tare da bin sha'aninki domin sanin halin da ki ke ciki.
Ya yi shiru kafin ya sake numfasawa ya cigaba da ce wa." Kamar yadda ki ka yi mini alkawarin cewa za ki cigaba da zama dashi a haka to ina horanki da cewar wani abu makamancin abinda ki ka aikata kada ya sake faruwa idan kin samu ciki irin na haihuwa ki barwa Allah domin dukkanin hukunci yana hannunsa.
Mijinki ya tabbatar mini da ce wa shi ma har yanzu yana sha'awar cigaba da zama dake domin yana sonki wani dalili mara karfi ba zai sanya shi rabuwa dake ba ko da kuwa Allah bai kaddara masa haihuwa ba. Saboda haka Dada da maigidan Yagana za su zama shaida a tsakanin zaman nan da muka yi wanda nake da burin Allah Ya sa ba za a kara maimaitama shi ba a tsakaninku, idan matsala ta fuskantoku za ku yi maganinta a junanku tunda dukkaninku ba yara ba ne."
Ya juya ya dubi inda yake zaune cikin nutsuwa ya furta." Ranka ya dad'e kamar yadda dai na gaya maka da farko cewa wannan yarinyar marainiya ce mahaifiyarta 'kanwata ce ni kuma a matsayin uba nake a wurinta. Don Allah ka ri'ke ta amana domin babu wani dalilin da zai sanya ka aureta cikin sutturarta ka dinga dora ayar zargi a kanta. Koda a gidan karuwai ka auro mace yana da kyau a ce daraja ta aure ya sa ka mutuntata to ballantana Amina da tun tasowarta a nutse take duk da irin jarabawar rayuwar da ta fuskanta a baya hakan bai sanya ta sarayar da mutuncinta ba. Sanin da na yi mata ita din za'kwa'kwa'kura ce mai himma da zuciyar neman na kanta amma ba a ta'ba yi mata shedar banza ba. Matarka ce idan da rabo watarana za ta zama uwar 'ya'yanka don haka muna neman wannan alfarma a wurinka a matsayinka na mai nisan shekarun da suka fi nata a duk lokacin da ta yi maka lefi wanda ba ma fatan haka sai ka kira ni a waya ka gaya mini, ni kuma zaka ga yadda za mu kwashe da ita. Maganar gaskiya Alhaji Tajo idan Amina ta sake aikata maka wani lefin makamancin wannan ka sake d'aukar matakin da shari'a ta haramta zahiri ni zan shige mata gaba ko'ina domin a a kar'ba mata hakkinta." Shiru ya ratsa d'akin kafin ya sake nisawa babu wata fargaba bare shakku ya cigaba da maganarsa. "Sannan Kuma sai abu na gaba, a madadin ni da mahaifinta da sauran 'yan uwana
Muna sake baka ha'kuri bisa abinda ta aikata maka ta yi kuskure zahiri wanda ko waye a ka yi wa hakan ba a kyauta masa ba, yadda ka ce ka yafe mata a gabanmu, Allah Ya sa hakan take a zuciyarka yanzu zan sanyata ta sake baka ha'kuri domin tabbas yin hakan shi ya dace da ita, tunda gabad'ayanmu maslaha da kwanciyar hankali muke nema.....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*
*70*
Jikina ne ya yi sanyi jin abinda yake ce wa, na yi shiru tare da sake yin k'asa da kaina ina jin Dada tana ce wa." Kuma ka rufa mata asiri baka tona mata ba, Allah Ya yi maka albarka mun gode sosai ka ji ko, Allah Ya saka da alheri, don Allah kada ka sanar da iyayenka da 'yan uwanka saboda kada su tsaneta a zahiri kowa zai ga ta yi maka mugunta tunda ita ai tana da yara da wani namijin, kaine abin tausayi da jaje, mun gode bisa rufe maganar da aka yi Ubangiji Allah Ya shi maka albarka."
Sai ta fashe da kuka ta sa gefan mayafinta tana share hawaye cikin kukan take ce wa." Uwarki tana kwance a kabarinta amma nasan a dalilin wannan zaman sai an tasheta ta ji abinda ki ka aikata, ai ita biyayyar aure ce ta kasheta ba ta ta'ba sa'bawa ubanki ba har ta koma ga Allah, ga Yagana nan tunda take da mijinta shekara da shekaru bai ta'ba kawo mana 'kararta ba, sai ke ko Amina, dama ai Yagana ta gaya mini kin ce badamuwarki ba ce don a lissafa miki aure, ai ba a kanki a kafara ba, to wallahi ba za mu yafe miki ba idan har ki ka sake kashe wannan auran, babu mu babu ke."
Baban Saude dariya ce ta kama shi jin irin zantukan da take yi ya ce ." Ai magana ta riga ta kare Dada menene na kuka kuma, babu wani dalili da zai sanya a tashi uwarta daga makwancinta, in sha Allahu ta nan lafiya lau kamar yadda muka je muka rufe ta, tana cikin rahamar Allah."
Ji na yi zuciyata ta tsinke dalilin kukan da Dada  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~take shar'ba wanda na tabbatar da ce wa mikin da ya jima da warkewa daga zuciyarta ne a ka fama mata, dama duk lokacin da ake yin wani taro a family dinsu sai sun yi kuka idan suka tuna da ita. Wannan lamarin da yake faruwa ne ya tayar mata da hankali ya sanya take ti'kar kuka kamar yanzu aka yi mata mutuwar.

Kuka na dinga yi a hankali ina jan hanci. Can kasa na ce." Baban Saude in sha Allahu babu abinda zai sake faruwa wannan al'kawari ne na yi maka zan yi iyakacin bakin kokarina akan abinda ka ce mini." Na yi shiru tare da sake jan majina na dubi wajan da yake zaune wanda kaf hankalinsa yana kanmu ni da Dada, da alama kukan da muke yi din ya fara sosa masa rai na ce." Don Allah ka yi hakuri in sha Allah ba zan sake aikatawa ba, sannan kuma ni ma don Allah ka yi mini adalci ka zauna da ni lafiya ka daina 'kullacina idan na yi maka wani abin yin hakan shi yake k'ara tunzura mini zuciyata, har na aikata abinda baka so."

A nutse ya furta." Kada ki damu magana ta shige in sha Allahu rabbi, za ki shirya tare za mu koma kamar yadda na yi wa Baban Saude bayani ai babu amfanin zaman tunda an sasanta mu ko?"
Baban Saude ya ce." 'Kwarai kuwa, ai ko ba ka furta hakan ba dama ni ma niyyata kenan na ce ka dauketa ku tafi, shine abinda ya dace."
Ya gyada kansa a tsanake ya sake duban Dada da take ta faman yi masa godiya sai ka ce wadda ya yi wa gagarimar kyauta, ita godiyarta yadda ya sakaye sirrin bai tona ba, har ma mahaifiyarsa bai gayawa ba.
Ashe godiyar da take yi zata sake ru'banyuwa domin kuwa kyautar kujarar umara ya yi musu ita da Baban Sauden. Shi kuma Babansu Fadila ya yi masa alkawarin bashi zungureriya mota domin fad'ad'a harkokinsa na sufari. Ashe kafin na shigo sun jima suna tattauna al'amura na rayuwa anan ya fahimci yana buk'atar tallafi domin cigaba da gudanar da sana'arsa.

Dama wajan kyautar ban girma ai ba daga nan ba, mugun kirki ne da shi tare da yin irin kyautar bazata wadda Allah yake so. Shi kansa Baban Saude da yake abin ya zo masa a bazata kasa rufe bakinsa ya yi, ya yi masa godiya sosai tare da addu'oi masu yawa. Na ji dad'i kwarai da alherin da ya yi musu hakan ya kara goge takaicinsa dake cikin zuciyata kuma ba ni damar yin jayayya dole na bi umarni kamar yadda suka buk'ata bayan isha'i na hada kayana tsaf Salmanu ya fita da akwatinana ni kuma na tsaya yi wa matan gidan sallama da godiya Sayyada tana fad'in in sha Allahu za ta zo mini ta yi mini kwanaki.
Muka rabu cikin kewar juna da kuma mutunta juna.
Ashe tare suke da Sukairaju yana jikin mota a tsaye yayin da shi Yallabai din da Baban Saude suke tsaye a bakin kofar gidan suna magana. Babansu Fadila ya tafi ina tsammanin. na dan tsaya a hankali na ce." Baban Saude shikkenan za mu tafi na gode sosai Ubangiji Allah Ya kara girma, Allah Ya saka da alheri."
Ya ce." Amin suma Amin Amina, Allah Ya sauke ku lafiya, ki kula ki kuma ki kiyaye da kyau."
A hankali na furta." In sha Allahu rabbi. Da sauri na yi gaba jin kuka na nema ya k'wace mini. Kafin na krasa bakin motar Sukairaju da saurin gaske ya bude mini na shiga na zauna ina goge hawayen da suka fara zuba a kumatuna.

Kaina a kasa Sukairaju ya bude masa kofar motar ya shigo a tsanake yana tattare babbar rigar da take jikinsa. Ya zauna sosai kusa da ni yayin da 'kamshin da yake fita daga jikinsa ya game motar gabad'aya Lumshe idona na yi a hankali na bude tare da sauke ajiyar zuciya a hankali da jin fargaba da fad'uwar gaba kad'an kad'an. Wani iri yanayi na fara ji a tattare da ni, na tashin soyayya tare da kewa dalili kuwa shine dama tun fil'azal k'amshin da ya zauna a jikinsa yana daya daga cikin abinda yake saurin tayar mini da hankali.
Jikina na d'an janye hankali na had'u da jikin motar domin ina ganin kusancin da yake tsakaninmu shi ma yana taka muhimmiyar rawa. Sukairaju ya d'an juyo a nutse ya ce." Sir za mu wuce hotel din da muka sauka ne?"
Ya gyad'a kansa a yayin da yake d'an gyara zamansa a gefana ya ce ." 'Kwarai kuwa ai tafiyarmu sai gobe tukkuna dole nan d'in za mu kwana."
Sai ya juya da sauri ya cigaba da jan motar cike da bin umarni.
Shiru ya ratsa tsakaninmu babu wanda ya dubi juna.
Kiran da ya shigo wayata shine ya ratsa shiru da ya ratsa. Ya dube ni a hankali wnda tun shigowarsa motar bai yi mini irinshi ba amma bai ce mini komai ba. Na d'auki wayar dake saman cinyata tare da duba mai kiran anti Yagana ce. Numfashi na sauke babu kuzari na sanya wayar a kunnane ban san kuma mai take tafe da shi ba, yanzu har fargaba nake yi naga kiranta.
" Kina ina yanzu?" Abinda ya fito daga bakinta kenan, ko amsa sallamata ba ta yi ba. A takaice na ce." Ga ni a mota tare da Yallabai za mu tafi."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." Na so a ce kin zo nan domin akwai taimakon da na sanya a ka yi miki rubutu ne da tofi."
Shiru na yi tare da d'an satar kallonsa sai na ga hankalinsa yana kan wayarsa Allah Ya sa ma ban bud'e handsfree ba amma dai duk da haka ina fargaba saboda yana da kaifin ji, itama anti Yagana tana da matsala wallahi.
Na ji tana fad'in." Kun jima da tafiya ne, amma dai ba yanzu da daddaran nan za ku d'auki hanyar abuja ba ko." A takaice na ce." Sai gobe haka na ji yana cewa yanzu za mu nufi masauki."
Ta ce." To shikkenan zan kira ki da safe za mu yi magana in sha Allahu rabbi.

Wannan littafin na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"To, kawai na iya ce mata na kashe wayar tare da d'ora ta a saman cinyata. Anti Yagana rigima kenan yanzu da ta tabbatar da cewa an sasanta zan koma ta daina hantarata.
Shiru ya cigaba da wanzuwa a motar shi Sukairaju yana can yana abinda yake gabansa. Ni da shi kuma kowa girman kai ya hana ya yi wa d'an uwansa magana.
Lokacin da aka kira wayarshi ban kalleshi ba amma gabad'aya hankalina yana kan saurarar maganar da yake yi a waya. Matarsa ce Hajiya Maryam ta kira shi. Na yi shiru mamaki da tsoro yana shigata. Yadda yake kashe murya da tausasa harshe wajan mayar mata da amsa shine abinda ya fi d'aukar hankalina. Jikina ya shika k'warai da aniya domin abinda yake yi ko saurayi dan shekara ashirin da biyar albarka. Idan ni na zama towon tushe ai ya ji nauyi da kunyar Sukairaju domin yaronsa ne a ganina bai kamaci ya saki baki yana fad'in wasu manyan kalmomi na soyayya da turanci ba.
Duk yadda na yi wajan ganin na ji a hakan ba komai ba ne a cikin zuciyata kasawa na yi don sai nake ganin kamar ma da gayya da cin fuska yake yi mini hakan. Da ta kira shi sai ya gaya mata yana uzuri a ganina bai kamata ya biye mata ba tunda dai ta san muna tare sai dai idan bai gaya mata cewa bikona ya zo ba, tunda duk yawancinsu munafukai ne ba su ta'ba yarda su fito da ainihin abinda yake kasan zuciyarsu.
Ban san lokacin da na ja tsaki mai tsayi ba na dan gyara zamana tare da cire gefan rigarsa da ya had'u da mayafin da yake jikina.
Had'e fuska na yi sosai a karo na biyu na sake yin wurgi da gefan babbar rigarsa da ya sake sauka a cinyata a dalilin gyara zamansa da ya yi. Sai ya juyo yana kallona still da wayar a kunnansa bai katse ba. Ban yarda na hada ido dashi ba amma yanayina kad'ai shi ya

Please Login or Register in order to submit comment