Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

love dama kaine fa baka fahimce ni ba, amma idan an yi duba na tsanaki za a gane maganata a kan hanya take amma tunda haka kake so na amince da ra'ayinka. Ubangiji Allah Ya ba mu masu albarka."
Ya tsira mini ido yana kallo domin so ya tabbatar da abinda yake zuciyata. Na ce." Wallahi na amince har cikin zuciyata.
Sai ya sauke ajiyar zuciya ya dan saki fuskarsa. Kafin ya fara yun'kurin tashi dani a jikinsa na rike wuyansa yayin dashi kuma ya tallafe k'uguna wanda kafafuna suke ma'kale da nasa k'ugun. Haka muka nufi gado ina ta raramo bakinsa ina sawa anawa.
A daran ni dashi ban san wanda ya fi gwadawa wani soyayya ba. Mun ji dadin junanmu sosai mun gamsu da juna fiye da kowane lokaci.

Washe gari da safe kenan kafin na sauka kasa yake gaya mini maganar d'aurin auransa da Hauwa a farkon watan musuluncin da za mu shiga don har manya sun gama komai ya tura mata komai na hakkinta. budurwa ce amma mai shekaru don yadda yake gaya mini ta haura talatin da biyar hakan ya tabbatar mini da cewa ta dan girme mini. Ya nuna mini hotonta dake wayarsa tana sanye da kayan likitoci domin ma'aikaciyar asibiti ce. Sannu a hankali ba tare dana tambayeshi ba yake ya gaya mini yadda suka yi da ita.
Wai tana son a yi shagulgula irinsu dinner da dai sauransu shi kuma ya ce baya so kawai a d'aura aure ta tare.
Ni dai murmushi kawai nake yi ban tofa tawa ba domin wani abu ne yake ta tsunkulina a can kasan zuciyata wanda na san ba komai ba ne face kishi.
Inda Allah ya taimake ni ma na fita diri da zubin jiki mai kyau tunda ni ko'ina na jikina a cike yake dam. Ita kuwa bata da kirji k'ananu ne sannan bata da baya a tsaye take sai dai akwai kyawun fuska kwarai da gaske kuma doguwa ce don tafi ni tsayi sosai amma kuma akwai wayewa irin ta 'yan boko. wannan kuma ni ma ina da nawa ilimin daidai gwargwado.
Da ya ce mini ya bata miliyan goma kudin kayan lefe da kwalliya ban damu ba dalili ni na san na samu fiye da abinda ya bata a lokacin d'aurin auranmu a yanzu da jarina da nake juyawa da irin alheran dana samu ta 'bangaransa sun tasarwa miliyan arba'in, alhamdulillahi babu abinda zan ce da Ubangiji.
Ganin ban ce komai ba sai ya dube ni cikin lallami ya sake cewa." Kema na baki kudin kitso da lallenko?"
Na kalleshi da murmushin dana kakalo babu nishadi na ce." E ni ma ai zan gyara kafin amaryar ta zo, ko da yake ai ba zan kamo kafarta ba a wajanka."
Ya riko hannuna yana fad'in." Duk abinda zan gaya miki ai ba zaki yarda ba amma kina can cikin zuciyata rayuwata ba zata inganta ba sai dake."
Dariya maganarsa ta ba ni. Na ce." Lallai kam to na gode, yanzu me kake so ka ci domin na shiga kicin na yi maka."
"Kunun tsamiya da kosai."
Na ce." An gama ranka ya dad'e."
Na tashi da sauri Ina cewa." Nan da minti talatin zan kawo maka."
Ya bi ni da kallo a yayin da nake ko'karin fita daga d'akin yana cewa." Allah Ya yi miki albarka."

Ina sauka kasa na samu Hajja da inna Uwani a zaune suna magana. Sakkowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya. Inna Uwani ta sunkuyar da kanta yadda na lura bata son had'a Ido dani. Cikin zuciyata na ce ni bana daya daga cikin mutanan dake fallasa asirin mutum. Idan halinkine wataran masu gidan zasu ganki, kuma in sha Allahu babu abinda zai same ni.
Na gaishesu gabad'aya suka amsa Hajja sai murmushi take don ta ji dadin ganina na fito daga wajan maigidan.
Domin na kara mata nishadi na ce." Zan shiga kicin shiryawa maigidan abin kari."
Ta ce." To shikkenan Allah ya yi niki albarka Amina.
Sosai nake jin dadin Addu'ar da take yi wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya nake ji a zuciyata duk rintsi duk wahala zan zauna tare dasu a gidan.
Bayan na kammala komai na kai masa sai na sake saukowa domin naje na yi wanka....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gam 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~a nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*22*
Dama tare muke da Hadiza a d'aki daya ina shiga d'akin na sameta tare da Yusi suna hira da yake yau asabar babu makaranta sai wajan sha daya tukkuna yake tafiya islamiyya sai yamma kuma ya dawo.
muka gaisa gabad'aya a gurguje na shiga toilet domin watsa ruwa. Ina ciki na dinga jin magana kasa-kasa Hadiza ce take waya kuma na ji tana ambatar sunana. Ban kawo komai a raina ba domin dan zaman da na yi da ita na fahimci cewa dole akwai k'auna irin ta 'yan uwantaka a tsakaninmu ba zata cutar da ni ba. Ina fitowa take cewa da ni." Fati ce babu lafiya, tana kwance a asibitin Malam Aminu an yi gwaji sakamakon ya fito tana d'auke da cancer mama. Hankali ya tashi ainun domin kuwa nasan ciwon yana da illah.
Cikin damuwa na ce." To yanzu ya ake ciki ya jikin nata."
Cike da alhini don har sai da hawaye suka zubo a kumatunta ta ce." Kin san mijin nata ba wani kudi ne dashi ba akwai dai rufin asiri kuma tunda suka tara yara nauyi ya yi masa yawa da kyar ma yanzu suke samun ci abinci yanzu yaranta biyar.
To shine yake gayawa Babanmu shi ya gaji ba zai iya cacar asibitin Malam ba domin bashi da iko a dawo da ita gida ayi mata na hausa kawai. Shine Ummanmu take gaya mini yanzu." Tasa hannu goge hawayen da yake ta zarya a kumatunta.

Na ce." Ba za a yi haka ba Hadiza ni menene amfanin arzikin nawa ai saboda irin haka nake nema ba dare ba rana in sha Allahu babu abinda zai gagara, ki kira mini Ummantaku a waya yanzu sai mu yi magana."
Da sauri ta d'auki wayarta dake ajiye ta kirata.
Na kar'ba muka gaisa na ce." Ashe Fati ce bata da lafiya Umma amma me yasa ba a gaya mana da wuri ba."
Da damuwa a tare da ita tace." Yanzu ne tura ta kai bango shiyasa na ce Hadiza ta taho gida domin ta taya ni jinyarta ga yaranta a gabana uban yana nuna gazawarsa nema ma yake ya sakar mana dawainiya."
Na ce." Yanzu nawa ake bukata a asibitin wajan yi mata aikin."
Ta ce." Ai kin san jan kudi irin na asibitin Malam wai suna buk'atar miliyan shida domin yi mata aikin saboda kada d'ayan ma ya harbu.''
Na ce." To ku kwantar da hankalinku in sha Allahu rabbi zan sanya Hamusu ya je asibitin ya biya kudi.....Kafin na krasa ta ce." Ki dai sanya shi ya tura a acct din ita Fati din kin san mijin nata da zargi kada ya juyawa mutane magana idan ya zo sai na yi masa bayani kece ki ka biya kudin aikin, zan yi wa babanku bayani ma."
Na ce." To shikkenan zan kar'bi acct din a wajan Hadiza Ubangiji Allah Ya bata lafiya."
Ta amsa da "Amin Ya Allah, mun gode sosai Amina Allah Ya yi miki albarka."
Na ce." Babu godiya a tsakaninmu Umma Fati kanwatace don na yi mata abu ba komai ba ne.
Mukayi sallama na kashe wayar na mik'a mata wanda har zuwa lokacin kuka take kashir'ban tana share hawaye kamar wadda aka ce mata Fati din ta mutu.

Na ce." Hadiza ki yi shiru don Allah, a yanzu Fati babu abinda take buk'ata sai addua. Kuma in sha Allah idan kudi suna magani, na yi alkawarin zan yi daidai gwargwadona sai kuma mu bi ta da addu'ar samun lafiya daga wurin Allah domin shine yake saukar da cuta, ya kuma bada sau'ki."
Ta goge hawayen fuskarta tana sake yi mini godiya. Ban ce komai ba na nufi wardrobe dina domin sanya kayana a jikina.

Da tunanin rashin lafiyar Fati na yini a cikin raina. Gashi na yi ta kiran wayar Hamusu domin mu san yadda za a yi bata shiga ban san menene dalili ba. Amma na bari da daddare sai na kara trying na ji, Hamusu baya kashe wayarsa a duk lokacin da aka kira shi ana samunsa.
Daddare ina d'akin maigidan Hamusu ya kira, ban yi mamaki ba domin lokacin dana kira shi ban same shi ba sai na kawai tura masa text wanda na san koda matsalar network ne idan ya saki zai gani.
Lokacin maigidan yana bandaki don shima bai jima da shigowa ba, kuma baya zaman cin abinci sai ya yi wanka tukkuna.
Na daga wayar da zuciya daya Ina fad'in. " Hamusu lafiya ake ta kiran wayarka bata shiga."
Ya ce." Wallahi anti Amina yini akayi ana ruwa anan duk network din layina ya sauka sai yanzu ya dawo.
Na ce." Ni ma na zargi hakan shiyasa na ce bari na yi maka text na san zaka ga ni.
Daidai lokacin da yake ba ni amsa shi kuma ya fito daga band'akin... Na ce." Wallahi kuwa d'azu muka yi waya da Ummansu cewa jikin nata ya yi tsanani, asibiti sun bukaci kudi zan dai yi maka magana ta Whasap idan an jima sai muga yadda za a yi."
Ya ce." To shikkenan anti ina sauraranki.''
Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefena na dube shi yana zaune kan sofa yana dan mutsika cream a jikinsa. Amma canzawarsa ta ba ni mamaki fuskarsa babu annuri bai kuma kalle ni ba ya ce." Wanene ma Hamusu ne?"
Ya fad'a babu annashuwa a tare dashi. Kallonsa nake da mamakin tambayarsa ai na d'auka a iya dad'ewarmu dashi ya fahimci wanene Hamusu tunda har tafiya mun had'a shi a lokacin da muka je duba Kamalu a makaranta wanda har alherin kudi ya yi masa, amma yanzu saboda tada zaune tsaye yana tuhumata.
Shiru na yi ban iya ce masa komai ba.
Ya sake cewa." Wanene Hamusu Amina?"
A nutse na ce." Kanina ne shi, abokin kasuwancina kuma mahaifinsu Yusi ne tunda kanin Ubansu ne."
Ya zuba mini ido da ce wa." Ni ban haifesu ba kenan shiyasa kike so ki nuna mini iyakata."
Na ce." Ba haka nake nufi ba."
"Okey wace magana na ji kuna yi fitowata daga bandaki ki ka katse har kina cewa zaku hadu ta whasap."
Cikin ko'karin kama mutuncina na ce." Ba wata magana ba ce ranka ya dad'e wani abu ne da shafe ni."

Ransa ya sake 'baci." Okey shi Hamsun ne yake auranki da har ni ban isa ki gaya mini abinda ya shafe ki ba sai shi, ni namijin hotiho ne ko, sai a shimfida nake namiji amma a zamantakewa ba ni da amfani ko."
Na ce." Wai don Allah me yasa kake nema ka canza mini magana ne nifa ba hak...
Ya buga hannun kujerar da yake zauna yana kallona da kishi da b'acin rai ." Ke ba ki ji kunyar yin magana da wani namiji a d'akina ba Amina, wai me yasa kike nema ki raina mini hankali ki mayar da ni shashasha, ni zaki ciwa fuska a gidana, a kuma d'akina ki dinga waya da wani dan iska, har kina kashe waya saboda kada na ji abinda zaku tattauna, ba ki d'auke ni mutum ba ko."
Cike da mamakin fusatarsa na ce." To da kuma ka ce baka gane shi ba, Hamusu ne fa ba wani ba, a tunanina ko zaka zargeni da wani namajin ba zaka zargeni dashi ba tunda kanin uban yarana ne, kuma kasan dole a kowane lokaci alaka ta had'a ni dashi dalilin Kamalu da Yus..... "Me yasa baki aure shi ba." Ya katse maganata yana huci ya cigaba da ce wa." Idan zargi zan yi akanki shine mutum na farko da zan zarga domin alak'ar(ALAKAR ZUCCI) Littafin marubuciya (Maidamu) kada ku bari a baku labarinsa. domin alak'ar da take tsakaninki dashi ta yi muni, wane irin cin fuska ne wannan."
Shiru na yi ban ce masa komai ba, amma raina ya gama baci da irin abinda yake yi mini, wani lokacin yana kasancewa mai sanyi da sau'kakawa a cikin al'amuransa, amma a wasu lukutan idan yana masifa har mamaki yake ba ni, sai ya rufe idonsa kamar bashi da ilimin Arabi da boko."

"Ba za ki gaya mini akan abinda kuke magana ba ko?" Ya fad'a yana tsatstsare ni da Idonsa. A nutse na ce." Fati ce bata da lafiya shine aka bukaci kudi a asibiti za a yi mata aiki, to dama akwai kudina a hannunsa shine na ce ya cire ya tura musu."
Ba tare da ya kalleni ba ya ce." Wacece Fati?"
" 'Kanwata ce, itace take bin Hadiza a dakinsu."

"Shine ba za ki sanar da ni ba saboda kina so duniya ta zage ni ko?kin san dalilin da ya sanya suka kira ki a waya suka gaya miki domin sun san kina aurena akwai hanyar da zasu samu mafita, sai ki ka za'bi kiran kanin tsohon mijinki, kina gaya masa ya basu kudin maganin ko?"
Kaina na dafe da yake sarawa. Na dago na kalleshi Ina auna maganganunsa da basu da tushe balle makama. Na tsira masa Ido ina ayyanawa a raina cewa babu mamaki rikicin tsufa ne ya fara kama shi amma idan ba haka ba ya za a yi ya nemi ya canza mini manufa bayan ba haka ba ne a cikin zuciyata.
Ya ce." Kin yi shiru saboda kema kin san ba ki da gaskiya ko?"
Na dai yi shurun ban tanka masa ba, saboda ba mu jima da sasantawa ba, ba na so akan wannan 'karamin dalilin da yake nema ya mayar dashi babba mu koma 'yar gidan jiya.

"Ba za ki ba ni ha'kuri ba kenan?"
Cikin dariyar da ban san lokacin da ta sub'ce mini ba na ce." Ka yi hakuri Baba, ba zan sake ba."
Ya girgiza kansa tare da mikawa ya nufi wardrobe dinsa yana cewa." Saboda kina waya da Hamusu ko kayana baki d'auko mini ba na gode miki Amina."
Wallahi shaf na manta domin hankalina ya tafi wajan ganin na samu Hamsun a waya an gama komai.
Daidai lokacin dana isa wajan da yake tsaye ya d'auko k'ananun kaya t-shart da short nicker na kar'ba daga hannunsa tare da cewa." To mu je na shiryaka."
Ya kuwa biyo ni zalo zalo! muka zauna a gefan gado yana ta kallon fuskata yayin da ni kuma na take ta danne dariyar da take yun'kuro mini.
Bayan na taimaka masa ya shirya sai ya dube ni babu wasa a fuskarsa. Ya ce.'' Ki goge lambar Hamusu daga wayarki."
Da mamaki na ce." Me yasa Baba?"
"Ki goge dai kawai akwai dalilaina."
Ganin da gaske yake yi ya sanya ni ma na shiga nutsuwata sosai na ce." Kai ma kasan hakan zai yi wuya, mu yi maganata gaskiya da gaskiya my love, ba na neman fitina domin ba za ta yi mana dad'i ba, Hamusu ba kowa ba ne a wurina face d'an'uwana abokin kasuwancina, sannan kuma kafi kowa sanin dangatakar da take tsakaninsu da mijina na fari uwa daya uba daya suke, bayan wannan ba ni da wata alaka dashi, Ina ganin baka da hujja mai karfi da zaka ce lallai sai na goge lambarsa daga wayata.

Ya zuba mini ido da tsananin b'acin rai yake ce wa." Ba ni da hujja mai karfi ko?"
Juyar da kaina na yi daga barin kallonsa domin na lura maganata ta yi masa zafi.
Ya d'auki wayata dake ajiya a gefena, na bishi da kallo amma ban yi yun'kurin kwacewa ba, ina kallo ya goge lambar Hamusun daga wayar ya dube ni." Ban yafe miki ba idan ki ka sake magana dashi, na san goge lambar ba zai dame ki ba tunda zai kira ki wataran saboda yana da taki. Idan ki ka ci amanata Allah Ya yi mini sakayya.
Hawayen da nake dannewa suka zubo. Na ce." To sai ka gaya mini zargina kake yi ko me? Ka san ko zan yi neman maza ba zan yi da Hamusu ba, domin kuwa kafi kowa sanin halina.
"Ni ba na zarginki, kawai na datse alakarku ne domin mutuncina da kike ko'karin ki zubar mini."
Na gyada kaina ban sake ce masa komai ba na tashi na bar masa d'akin.
Da takaicin abin na kwana a cikin raina, amma hakan bai hana ni zuwa na gaishe shi ba yana zaune wajan da yake hutuwa, muka gaisa babu sukuni bai dube ni ba ya ce." Ki dama mini kunun tsamiya dashi nake sha'awar karyawa."
Ban ce komai ba na tashi na fita. Minti talatin na gama tsaf na kai masa na ajiye tire din zan fita ya ce." Sannu." Kanzil ban ce ba na fita. Kicin din dai na koma na d'auko wanda na hadawa Hajja na kai mata har dakinta tunda lokacin bata fito ba. Kafin na shiga na ji maganarsu ita da 'yar'uwarta inna Uwani suna tattaunawa akan abinda ya shafi hidimar da take gabatosu. Muka gaisa ko da wasa ban nuna cewa na ji abinda suke cewa ba, kuma na yi kokarin ganin na boye bacin raina.
Na fita na nufi d'akina. Hadiza tana ta had'a kayanta a cikin kwataki na ce." Hadiza wai tafiyar ce ba zaki bari sai wani satin ba."
Ta ce." Zan dawo ai Amina, gabad'aya hankalina ne ya yi gida ina so naje naga jikin Fatin.'
Na ce.'' Ni ma in sha Allahu bada jimawa ba zan zo, Ubangiji Allah Ya bata lafiya"
Ta amsa da Amin." Kayan jikina na cire ina shirin shiga wanka ya shigo d'akin.
Lamari mai girma ne yake kawo shi d'akina dalilin da ya sanya ma kenan dana ganshi gabana ya fad'i.
Hadiza da sauri ta risina tana gaishe shi. Ya amsa fuskarsa a sake Yana dubanta da kulawa ya ce. " Ashe Fati ce bata da lafiya."
Ta ce. Eh wallahi yanzu ma shirin tafiya nake yi domin zuwa dubanta."
Sai ya kalleni yana cewa." Zata tafi amma ba ki gaya mini ba."
Shiru na yi. Ya kawar da kansa yana cewa da ita." Nawa ne abinda aka buk'ata?"
Cikin inda-inda ta ce." Miliyan shida ne?"
Ya ce." Me yasa ke ba ki same ni kin gaya mini ba, tunda ita ban isa ta ta sanar da ni ba."
Ta yi shiru tana dan murmushi ya ce." Ba ni lambar asusun da za a sanya kudin sannan zan sanya a kai ki gida don ba zan yarda ki bi motar haya ba."
Cikin sauri ta gaya masa lambar acct din Fati mai suna Salisu Fatima Fedlity bank.
Ya ce." Zan saka in sha Allahu idan kin je gidan ki gaishe mana dasu kafin mu zo."
Ta amsa da sauri tana cewa." In sha Allahu kowa zai ji, Ubangiji Allah Ya saka da alheri ya kara arziki mai amfani ."
Bai amsa ba ya fita daka d'akin.
Ta dube ni tana cewa." Amina don Allah ki kara yi mana godiya, ke kam Allah ya kashe ya baki, shi so yake yi ma ki fad'a masa hidimar 'yan uwanki ya yi miki."
Na dubeta babu yabo babu fallasa na ce." Hadiza ba wannan ba, ki nutsu dan Allah kada don kin ga ya ce haka ki nemi zubar mana da mutunci don girman Allah duk abinda kuke buk'ata ku gaya mini ba zai gagareni ba, amma ba na so ku tambayeshi yin hakan sai ya rage mini kwarjini da martaba a idonsa."
Ta ce." Eh kuma hakane to zan kiyaye in sha Allahu."
Na tashi na shiga toilet din da tunaninka masu yawa a kwanyata.

Hadiza kuwa kwafa ta yi cikin zuciyata tana ce wa'' Mutuncin banza da wofi ya dad'e b ai zube ba, saboda b'akinciki mutum yana so ya yi alheri kina dakusar dashi, sai mun tambaye shi din ki yi duk abinda za ki yi....
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*TALLAH!*
<2<3 *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu

Please Login or Register in order to submit comment