Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi saboda kowa da irin fahimtarsa wasu suna gyarawa ne wasu kuma na 'batawa."
Tun a 'karshen maganarsa na fahimci gugar zana yake yi mini akan Baban Saude wata'kila kafin zuwansa nan din anti Yagana ta gaya masa halinsa shiyasa yake yin shagu'be shi ma yana nuna rashin dacewar kawo maganar wajan Baban Saude ni kuma gabad'aya duka sun kasa gane dalilina. Ban kawo 'karar Alhaji Tajo wurin Baban Saude da zummar ya wulakantashi ba, ni kaina nasan wargi ma wuri shi ka samu. Baban Saude idan yana yi wa wasu ya zauna lafiya ina ganin kwarjini gami da haiba irin na Tajudden ya wuce a ce ya yi masa tijara mai muni. Ina dai da tabbacin cewa za su yi musayar yawu irin na fahimta domin a samu matsaya akan abinda yake faruwa.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*67*
Wajejen sha biyu na rana Sahura ta kira ni a waya a nutse na d'auka muka gaisa amma babu cikakkiyar walwala a tare da ita fara da cewa." Yanzu sis ashe dai sai da ki ka sanya kafa ki ka shure shawarata ko? jiya na dawo daga aiki na tarar da Yusra a gida da yamma Baba Tabawa ta shigo tana gaya mini kin yi tafiya zuwa maiduguri gaskiya ba zan boye miki ba ban ji dad'in abinda ki ka yi ba domin kuwa yanzu nan muka gama waya da anti Yagana ýÿÿÿ‚
ƒ




ˆ

Š

Œ

Ž









˜

š

œ

ž
Ÿ
 
¡
¢
£
¤
¥
¦
§
¨
©
ª
«
¬
­
®
¯
°
±
²
³
´
µ

·
¸
¹
º
»
¼
½
¾
¿
À
Á
Â
Ã
Ä
Å
Æ
Ç
È
É
Ê
Ë
Ì
Í
Î
Ï
Ð
Ñ
Ò
Ó
Ô
Õ
Ö
×
Ø
Ù
Ú
Û
Ü
Ý
Þ
ß
à
á
â
ã
ä
å
æ
ç
è
é
ê
ë
ì
í
î
ï
ð
ñ
ò
ó
ô
õ
ö
÷
ø
ù
ú
û
ü
ý
þ
ÿ
tana tambayata wai ko nasan wani abu da yake faruwa game dake."
Ta nisa kafin ta cigaba da cewa." Na ce mata kin gaya mini amma kin ce sirri ne, shine ta ce to na bar shi ba sai na gaya mata ba tunda amana na kar'ba a wurinki. Sai kawai ta kashe wayar a sanyaye Ni kuma gaskiya na ji rashin dadin hakan mai yasa ki ka boye mata abinda yake faruwa da rayuwarki Amina bai kamata ace har sai ta fito duniya tana neman dalili ba."
Murmushi na yi mara armashi na ce." Sahura hakan da na yi shine kwanciyar hankalina da kuma samun nutsuwata don Allah kada ki ka ga lefina kada ki 'kullace ni, addu'a kawai nake so ki taya ni da ita, sannan maganar anti Yagana kuma ni na fi kowa sanin halinta kwata-kwata ba ta kar'bar uzurina in dai akan mutumin nan ne to bata ta'ba fahimtata kamar yadda ke ma ba kya gane nufina. Wannan dalilin ya sanya ban gaya mata ba domin lefinsa za ta take da k'afarta ta rufe gabad'aya ta d'auka ta d'ora a kaina, to shiyasa ko da na yanke shawara ban nufe ta ba kai tsaye na yi tafiyata a gidan Baban Saude."

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." To ke yanzu me ki ka yanke a zuciyarki rabuwar ki ke ganin itace mafita a gare ki ko kuwa, tunda kina ganin kin fi karfin ki d'auki shawarata Amina to ni menene sai kin gaya mini ba'kar magana a fakaice. Kowa rai ya yi dad'i ai barin mai shine. Ni dai tun tasowarmu ban ta'ba saninki da wannan mugun taurin kan ba, sai da Allah ya rufa miki asiri ki ka ji kina kama 'yan-canji tukkuna ki ke ganin karanki ya kai tsaikon da za ki iya cin mutuncin kowa. Tuntuni na sha gaya miki aure ibada ne shiyasa iyayenmu koyaushe suke jaddada mana mu kyautata ha'kuri domin kuwa shine kaso mafi rinjaye a zamantakewa irin ta aure. Na gani da idona na ji labari a bakin da ba zai kirkiri 'karya ba oga yana sonki irin son da yake da wahalar samu. Yana ta tataki yana yi miki duk abinda ki ke so. Kin zubar masa da ciki saboda tsabar son zuciya kin tafi yawon kai shi k'ara gari ya gari har maiduguri kamar wannan mutumin Amina anya kina da hankali kuwa..... Ba tara kàrasa ba na katseta da saurin gaske domin kuwa zuciyata ba zata iya jure hatsaniyar da take yi mini ba. Sahura bata ta'ba ba ni haushi ba irin yau. A fusace na furta." Na kai shi k'arar Sahura shi din wanene Annabi ne ko kuma walliyin Allah da har ake gudun 'bata masa rai. Ina ruwana da dukiyarsa mutum ne fa kamar ni mai tarin zunubai mai kashi da fitsari, mai yasa zan tsaya jin tsoro da shakka a kansa tunda yana tsuguno a masai kamar yadda nake yi. Ai da yana da bambamci da sauran hallita ne sai na saurara masa. Na gane dake da anti Yagana so kuke na zauna 'bakincikinsa ya kasheni to akan wane dalili. Shi kadai ne namiji a duniya da har zan jira yana b'ata mini rai, bai fi karfin na kai shi 'kara ba wallahi tunda ni dai abin hannunsa bai bude mini ido ba. Yarana suna buk'atata to ban ga dalilin da zai sanya na zauna wata hallita tana kuntuka mini ba." Na kare magana ina nishi saboda tsananin b'acin ran ganin yadda mutumin nan yake nema ya shiga tsakanina da makusantana.

Itama da tsananin b'acin rai ta furta." Ni ina nema a wurinsa kuma ina ci da sha a karkashinsa na gode miki da ba'kaken maganganu da kuma gori, ki cigaba da yin fito na fito da umarnin Allah da kafarki za ki taka siradi tunda mutumin nan kin zalince shi kin kuma sa'bawa Ubangijin da ya hallicceki."
Jin muryarta tana rawa ya sanya na sassauto a hankali na ce.'" Sahura don girman Allah kada ki juya mini bayana, ki tuna irin gwagwarmayar da muka yi a baya, kada ki yadda mutumin nan ya raba zumuncin da yake tsakaninmu don Allah ki fahimceni wallahi yana zalintata. Na yi lefi na bada ha'kuri, na tuba ga Allah to a yafe mini mana menene za a dinga yi mini gashin 'kuma a fakaice idan dama mutum bai taki wani abin ba.

Ta yi shiru na dan wani lokaci kafin ta ce." To shikkenan na ji, yanzu me ki ka yanke akan abinda ki ka yi?"

"Ban yanke komai ba Sahura sai abinda Allah Ya zaba mini, idan har rabuwar itace alheri ina farinciki da hakan, idan kuma akwai sauran zama a tsakaninmu to gaskiya ba zan koma ba lallai sai ya fahimci cewa abin fa da yake aikatawa kuskure ne, sai ya dauki matakin gyara da alkawari tare da sharad'in hakan ba zata sake faruwa ba.

Murmushi ta yi irin na takaici kafin ta ce." Amina wani lokacin ina mamakin tsaurin idonki wallahi to wai Baban Sauden ki ka wakilita da ya kira Yallabai din ya titsiye shi akan kuskuran da mafi rinye ke ce mai shi. Idan fa an bi ta 'barawo to a bi ta mabi sawu na gaya miki tun ranar da na zo gidanki wallahi ke ce mai lefi mai yasa za ki zubar masa da ciki saboda wani banzan dalili da bashi da tushe. Son zuciya ne fa wannan tsagwaronsa ki ka nuna masa a zahiri saboda ke ai kina da yaran shi kuwa fa. Ki bari ki haihu mana ki ga abinda za ki haifa da lafiya ko babu kawai sai ki yankewa Allah hukunci, ba zan gaji da gaya miki ba, baki da gaskiya."
Cike da tsantsar takaicin kasa fahimtata da ta yi har yanzu
Na ce." Ban kyauta ba din Sahura duk abinda za ku yi ku yi din, haba na gaji da magana daya wai ana aure dole ne ko kuma tilas aka ce sai na zauna da mutumin nan da za ku bi ku tsangwameni. uwata ce ke da za ki kira ni a waya kina gaya mini maganar da ranki ya so, ko kuma ke ce ki ke zaune da mutumin nan ne, kwata-kwata kun kasa fahimatata, na yi kuskure na nemi afuwar Allah amma gabad'aya kuna juya mini magana saboda kawai wani dalili naku. Ina kara jadadda muku shi ai ba sahabi ba kuma ba Annabi ba ne da ba za a 'bata masa rai ba. Ko annabawan Allah suna kuskure balle wani bawa kuma Allah Ya yafe musu saboda haka a yanzu daga ke har anti Yaganar ba na buk'atar ku fahimce ni, duk abinda za ku yi akan lamarin kun jima ba ku yi ba." Ina gama maganata na kashe wayar raina a mafisar b'ace. Tunda muke da Sahura ba mu ta'ba musayar yawu mai zafi irin wannan ba. Haba na gaji da jan magana d'aya muddin ba za su gane hujjata ba to sai mu yi ta tafiya a haka ba zan sake yarda wata ta kira ni a waya ta 'bata mini rai ba.


Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Da takaicin abinda yà faru tsakanina da Sahura na yini duk yadda na kai ga ko'karin ganin sun fahimceni ita da anti Yagana abin ya gagara har sai da sa'bani ya gifta a tsakanimu, to kuwa ta yaya za a yi kuwa na manta da mutumin nan tunda ta dalilinsa anti Yagana take furta maganar da ban ta'ba tsammanin fitowarta daga bakinta ba, wai za ta rabu da ni har abada saboda shi yau ga Sahura tana gaggaya mini ba'kaken maganganu. Ban ta'ba nadamar saninsa ba a rayuwata sai a wannan lokacin.
Da daddare muna zaune a babban tsakar gidan gabad'aya har da maigidan Baban Saude an shimfida masa dadduma mu kuma muna zaune a 'katuwar tabarma ana ta hira cikin nisha'di cikin raina ina ta mamakin hakan wato duk wanda zai k'alubalanci Baban Saude akan wani lamari tabbas ba zai zauna dashi ba ne, sannan kuma bai gama karantar hali da d'abi'arsa ba.

Dada da Anti Yagana suka yi sallama a lokaci daya suka shigo gidan. Ganinsu a tare ya sanyayar mini da jiki domin kuwa na tabbatar da cewa anti Yagana ce ta je ta gaya mata abinda yake faruwa.
Suka zauna akan tabarma ana gaisawa Baban Saude yana cewa da Dada ba ta gaya masa za ta zo ba a d'azu da safe da ya je can gidanta domin su gaisa.
Sai ta kuwa ta kada baki ta ce." Ni ma dole ce ta sanya ni zuwa ai domin kuwa abinda ka boye mini shi Yagana ta je ta gaya mini shine na ce bari na zo da k'afafuna gidan naka na ji dalilin da ya sanya ka b'oye matar mutane a gidanka, idan har za ka yi iko da yaranka Haruna wannan dai baka da k'arfi a kanta kuma babu yawuna a cikin yun'kurin da ka ke ko'karin aikatawa."
Cikin nutsuwa ya ce." Wato Yagana ce ta je ta taso ki da daddaran nan kenan, kin kyauta Yagana na ce kin kyauta." Ya fad'a yana kallonta da b'acin rai a tare dashi ita kuma sai ta yi kasa da kanta tana cike da damuwa ta furta." Baban Saude don Allah ka yi hakuri wallahi ba nufi na ba ne na bata maka rai, amma ni nasan Amina bata da wata hujja gabad'aya ma majority lefin nata ne tunda d'azu Babansu Fadila da ya zo ta gaya masa duk abinda ya faru wanda ni ta rufe mini saboda ta san ba zan goyi da bayanta ba."
Ya ce." Shiyasa ki ka je ki ka gayawa Dada kenan saboda ni ban isa na yi hukunci ba, ko kuma ni zan goyi da bayan k'arya ko?"
Ta yi shiru tana girgiza kanta alamun ba haka ba ne.
Ya gyada kansa da takaici ya dubi Dada tare da ce wa." Duk abinda Yagana ta je ta gaya miki akan Amina kada ki amince da cewa ita kadai ce take da laifi domin shi ma mijin nata da akwai tasa matsalar, kuma yana da kyau ace yarinyar nan an dubi matsalarta an kuma d'auki matakin gyara. Ba ni da burin kashe mata aure sai dai idan har hakan ya zama dole, sannan kuma ni babu ruwana da wanda take aure dukiya nasaba ko wata d'aukaka ta mutum. Ni namiji ne amma ba na goyon bayan mazajen da suke zalintar matansu ta kowane 'bangare. Wannan dalilin ne ya sanya da yawa mutane suke yi mini kallon mafad'aci saboda tsage gaskiya. Dada babu yadda za a yi yarinya ta kira ni a waya tana kuka akan wata matsalar da ta dameta na ce babu ruwana a ciki dalili wata hujja dan ban zo a b'angaran mahafinta ba to ban ga dalilin da zai sanya na ja baya akan lamarinta ba, idan na yi hakan kuwa tabbas ban dubi zumunci ba, kuma ban yi wa 'yar uwata kara ba. Ba dalili ba ne a ce wai dangin babanta ne lallai suke da hakkin kare mata mutunci ba, to idan kuma suka gaza fa, ma'ana suka kasa ta'buka wani abu akan lamarinta shikkenan sai ta zauna a hannun wanda bai san daraja da mutuncinta ba......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*68*
Wajan ya yi tsit kowa ya yi shiru yana sauraransa. Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Tun kafin ta zo nan ta gaya mini halin da take ciki a waya da kuma ta zo ta sake jadadda mini duk abinda ya shiga tsakaninta dashi da abinda ta aikata masa da matakin da ya d'auka akanta. Dan Kuskure ta yi kuskure kuma ban goyi da bayan ta sake aikata hakan ba ko bayan raina na gargad'eta domin hakan fasadi ne mai girma. Ta kar'bi lefinta ta yi nadama ta tuba ga Allah kuma ta nemi gafara to me zai sanya ba za a yafe mata ba. Wannan sune kadai matsaltsalun Amina, kuma na ja kunanta kwarai da gaske akan ta gyara ta kiyaye a gaba. Ba wai ina goyon bayanta ba ne a yanzu ta ce ba ta da ra'ayin zama dashi cikinmu babu wanda ya isa ya yi mata dole domin kuwa ita ba yarinya ba ce ta san abinda yake mata ciwo sannan kuma tana da hujja ko a gaban alkali za ta fad'a masa dalilinta na son rabuwa da auransu saboda matsalar rashin daidaituwar jini da za a samar da yara masu ingantaciyar lafiya. Abu ne ya zo a zamanance ba mu ce za mu yi wa Allah wayo ba, amma zahiri lalurar nan akwaita dalilin da ya sanya ma kenan aka fara d'aukar matakin kare kai daga riskar abinda zai faru bayan an yi aure. Amma fa wannan bayanin nawa baya na nufin cewa ina goyuwa da bayan yahudawa ba ne a a ko daya domin kuwa ni kaina a lokacin da na auri iyalina babu gwaji na jini kuma ga yara na nan duka mun haifa lafiyarsu lau babu wani mai lalura daga ciki. Saboda haka Dada ki fahimce ni anan wannan ga'bar kada a tilastawa yarinyar nan a ce dole sai ta cigaba da zama da bawan Allan nan alhalin bai san girma da mutuncin ba."
Dada jikinta ya yi sanyi sosai duk karsashin da ta shigo dashi gidan babu shi a tare da ita a sanyaye ta ce." To yanzu na ji abinda kace Haruna, amma ya za ka yi ka hadu da mijin nata kasan dai shi ba yaro ba ne idan ma ka girme shi ba yawa kuma sannan ba irin mazajen yaranka ba ne da kasa ba yi musu tsawa da gindaya musu sharad'ai."
Dariya ya yi irin ta manya a tsanake ya furta." Ai na girme shi Dada, kuma yana auran 'yata duk kudi da wani abinda yake ji dashi ya zame masa dole ya ajiye a gefe guda kafin ya tunkaro inda nake muddin yana so mu daidaita. Ni wani kudinsa ba zai rud'a ni ba, ke kan ki kin san da wannan Dada."
Wani irin sanyi na ji ya sauka a zuciyata ta yi fes lallai Baban Saude ya shirya kare mini mutuncina.
Ya dubi anti Yagana babu fara'a ya ce." An ce yana kiranki a waya to na gargad'eki duk lokacin da ya sake kiranki akan lamarin ki ce masa ya nemi inda nake kuma ki sanar dashi daf nake da komawa wurin neman abincina domin ina sa ran a satin nan da za mu shiga asabar ko lahadi zan tafi muddin kuwa ya bari na tafi bai neme ni ba to sai na dawo kuma"

Cike da damuwa da kar'bar umarni ta ce." To shikkenan in sha Allahu don d'azu ma mun yi waya da shi har yana sake jadadda mini cewa shi bai saketa ba bayan wanda ya yi mata a baya shi kad'ai ne ya san wànda ya yi har yanzu akwai sauran igiyoyin auransa biyu a kanta."
Gyada kansa ya yi yana gyara zamansa ya ce." wannan kuma abinda ya shafe shi ne, ki yi dai yi kokarin bin umarina idan ya tuntubeki akan matsalarsa ki ce masa ya nemi inda nake domin kuwa matarsa tana hannuna."
Ta ce." To in sha Allahu rabbi."
Kwanan farinciki na yi a ranar saboda irin tsayuwar da Baban Saude ya yi akaina na ji dad'i kwarai da aniya kuma na yi masa addu'ar samun lada a wurin Allah.

***
To kwana uku a tsakani zuwansu Anti Yagana da safe ina bacci Sayyada ta shigo tana tashina wai Baban Saude yana kirana. Da zullumi na tashi na fita na wanke bakina sannan na nufi d'akinsa da yake can gefe da tsakargidan na yi sallama a nutse na shiga yana zaune da tukunyar shayi da mangal a gabansa ya gama dafa shayin yana tsiyayawa a kofi. Na sake gaisheshi duk da cewar d'azu kafin na kwanta mun gaisa. Ya amsa yana d'an motsa shayin da cokali kafin ya dube ni a tsanake ya ce." Jiya Yagana ta kira ni a waya ta gaya mini mijinki ya bu'kaci da a bashi lambata shine take neman izini na ce ta bashi babu komai to shine yanzu nan ya kira ni a waya yake gaya mini cewa yana nan tafe gobe juma'a komai dare zai shigo akan maganarku shin ya kike gani. Ni ba zan yi miki dole ba fa Amina domin kuwa ba kowane yake zaune da mutumin nan ba sai ke, idan har kin ga da 'kwara da cutarwa a ciki to ni don na ce masa ya sawwa'ke miki ba abu ne mai wahala ba a wajena. Idan kuma kin ga kina so ki cigaba da zama dashi sai a ja masa kunne tare da gargadin wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe idan har bai daina ba a gaba sai a d'auki matakin rabuwa ko yana so ko baya so tunda akwai al'kalai, shari'a kuma tana kan kowa da mai kud'i da kuma mai mulki.
Shiru na yi ina nazarin maganarsa. Babu shakka Baban Saude ya cika jarumin namiji domin kuwa abinda ya yi a yanzu ba kowanne zai iya yi ba dalili shi wanda za a titsiye din mutum ne wanda Allah Ya wadatashi da farcen susa ya kuma rataya masa taguwar arziki.

Na ce." Baban Saude idan har na rabu da auran mutumin nan duniya za ta zage ni. Sannan anti Yagana za ta 'kullece ni tunda har yanzu ta kasa fahimta. Ga 'kawata aminiyata Sahura mun samu matsala da ita duk ta dalilin haka. Zan cigaba da hakurin zama dashi muddin an nuna masa cewa abinda ya ke yi mini ba daidai ba ne, idan har ya gyara kuskuransa ni kuma na yi maka al'kawarin in sha Allahu rabbi zan yi kokari wurin ganin mun zauna lafiya, kuma zan kiyaye abinda zai sake kawo sa'bani a tsakaninmu kamar yadda ka yi mini nasiha."

Gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Ya jima yana kallona kafin ya gyada kansa a nutse ya furta." To Allah Ya yi miki albarka, ya kuma kare faruwar hakan anan gaba, sannan kuma ki yi amfani da duk shawarwarin dana d'ora ki akai, kina kallon yadda iyalina suka karanci halina tsaf to sai mu jima wata matsala bata gifta mana ba suna bina a yadda nake so, ni kuma ba na zalintarsu daidai gwargwado ina sauke hakkin kowacce. Ina so ki yi koyi dasu a dan zaman da ki ka yi tare dasu, ki d'auki darasi na zamantakewa tunda kina da abokanan zama to sai ku zama 'yan uwan juna, ku taimaka juna, ku ha'de kan yaranku waje daya, kada ku yarda wata 'baraka ta raba zumuncin yaranku a gaba za ku yi alfahari da haka. Sannan kuma kada ki kara samun ciki ki zubar wannan maganar na nanata miki ki ri'keta da kyau domin ba ke ki ke rayawa ba, haka zalika ba ke kike kashewa ba, tunda har kin yarda za ki cigaba da zama dashi a hakan to Ina yi muku fatan alheri Ubangiji Allah Ya sa har karshen rayuwarku wata matsala ba zata sake faruwa ba."
Hawaye na ji sun ciko idona saboda tsananin mutuwar jiki. Wato ana zaton wuta a ma'kera ashe Baban Saude mutumin kirki ne na gaske ban sani ba, lallai anti Yagana da mutanan da suke masa wani irin kallo sun d'auki alhakinsa domin kuwa mutum ne nagartacce mai mayar da d'an wani nasa, irin wad'annan mutanan masu tsage gaskiya da gudun abin duniya sun yi 'karanci a wannan duniyar.

Ina komawa d'aki anti Yagana ta kira ni a waya na daga tare da jin d'an faduwar gaba domin kuwa ban san dame take tafe ba. Sama sama ta amshi gaisuwa kafin ta fara gaya mini dalilin da ya sanya ta kira ni a waya. Na ce mata ai yanzu ma Baban Saude yake sanar da ni komai. Sai ta ja tsaki da alama har yanzu ciki take da ni don dai na yi mata nisa ne babu yadda za a yi ta zo inda nake ta huce fushinta saboda sanin halin maigidan , shiyasa haushina da take ji ya sake ninkuwa. Shiru na yi Ina sauraran duk maganganun da take yi uffan ban ce mata ba domin Ina iya yin magana ta ce na yi mata rashin kunya domin mu rabu lafiya duk abinda ta ce mini sai na ce to, ta kashe wayarta bayan ta gama gaggaya mini maganganun da ranta yake so da sunan jan kunne da gargadi akan zuwan da zai yi har tana cewa tasan ba ni da mutunci za a iya had'a baki da ni a wulakantashi da tozarci saboda yin hakan a wurin Baban Saude abu ne mai sau'ki dalilin da ya sanya ta kira ni kenan ta gaya mini sun yi waya dashi tun jiya kuma ya tabbatar mata da cewa da zummar sulhu zai zo.

Ajiyewar wayar na yi raina fes cikin zuciyata na ce da ke dashi dukkaninku ba kwa son gaskiya, ko yanzu ai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, na d'auka ai girman kai ba zai bar shi ya tako kafarsa ya zo ba, ai na ji dad'i mutuka da gaske da yadda Baban Saude yake da kafiya da dagiya akan ra'ayinsa. Duk da kwarjini da haibar da yake da ita ina da tabbacin hakan ba zai firgita Baban Saude ba dalili shi ma mutum ne mai ra'ayin rik'au kuma mai tattare da wadatar zucci.

Washe gari da safe bayan mun karya kummalo na koma na kwanta bacci mai nauyi ya d'aukeni ko kadan ba na tare da wata fargaba ko zullumin abinda zai faru idan ya zo garin shiyasa kwata-kwata ma ban sanya abin a raina ba don ni har so nake ma ya zo din naga yadda za ta kaya wannan shi zai nuna mini cewa yana sona da gaske ko kuwa duka karya ce da yaudara.
Sai wajan daya na rana na tashi rana gatse-gatse ina fitowa tsakar gidan da zummar wanke bakina

Please Login or Register in order to submit comment