Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai ba zata iya zama ta lalata kuruciyarta a banza ba. Yana gaya mini baban yaronsa namiji wato Turmuzi yana nan yawo cikin tashar Kano line yana bin 'yan kamasho da samarwa da matafiya mota a sallameshi ya lalace da shaye-shaye tunda wasu lukutan a tashar yake kwana sai yayi sati bai je gida ba.
Kuka sosai na dinga yi ina kiran sunan Allah amma anti Jamila ba ta yi wa kanta adalci ba, ni a tsarina duk wahala ba zan iya watsar da yarana akan jin dadin duniya ba, babu ma yadda za a yi na tafi na bar yarana a wurin da nasan ba zasu samu kulawa ba hankalina ma ba zai ta'ba kwanciya ba. Anti Maimuna ta ba ni tausayi sosai ita kuma tata jarabawar kenan rayuwa kenan. Ba ni da halin da zan iya biyawa Alhaji Muntari bashi har na kusan miliyan talatin gabad'aya ma abinda nake juyawa bai kai hamsin ba ribar da take fita yau da gobe da ita muke buk'ata ni da Hamusu da kuma biyan yaran shago hakkinsu. Alhaji Tajo shi yake da iko koda miliyan dari ne don ya fitar ya bayar ba na tsammanin dukiyarsa zata girgiza amma da nauyi sosai a ce na tunkare shi da wannan maganar har cikin raina nake jin wani iri dangane da ibtila'in rayuwar da ya faru da Alhaji Muntari domin ko banza ya taimaka mini ni ma a can baya a wannan ga'bar ya kamata ace na tagaza wani abu kafin akai ga kar'bar kudin gidan da yake ciki wannan duniyar ta zama abar tsoro.
Haka na kwana na yini da tunanin hanyar da zan bi wurin ganin na nemi taimako daga wajan wannan wannan d'an tahalikin ba tare da ya fassara ni ba.
Na kira anti Yagana na gaya mata domin ta ba ni shawara itama dai abinda Sahura ta ce shi ta fad'a na sauke abinda nake ji kawai na neme shi domin yin hakan babban taimako ne da zai sanya ni dashi mu tsinta a ranar lahira. Na yi na'am da shawararsu domin a raina na ji zan iya jure cin kashi da bakaken maganganunsa muddin zai taimaka ai me nema baya fushi ni ko bashin ne ma ya biya masa su dai zauna a gidan ni kuma zan yi kokarin ganin na d'auki nauyin kaishi babban asibiti domin a duba lafiyarsa sosai.
Na samu lokaci ranar lahadi da la'asar domin a irin wannan lokacin ne yake free sosai na kira shi a waya daf da zata katse ya daga yana sallama.
Na amsa a nutse kafin na gaishe ya amsa can kasa kamar wanda yake cikin mayen bacci.
A sanyaye na ce." Dama na kira ka ne kawai na gaisheka na ji ya kuke ina Yusi."
Ya ce." Ina nan lafiya muna nan Abuja tare dashi gidan babban abokina Alhaji Amadu na taba baki labarinsa ko?"
Na ce." Eh kun dai ta'ba yin waya sau daya a gabana ina yawan jin sunansa a bakinka."
A dan sanyaye ya furta." Yana nan rai a hannun Allah Amina yana jin jiki muna kan shirye shiryen tafiya asibitin jiddah nan da kwana uku"
Jikina a mace na ce."inna lillahi me yake damunsa haka?"
"Kin san yana da ciwon zuciya dama to wannan karon da ciwon ya motsa masa abin ba kyau ni har na fara fitar da raina a kansa Amina."
A sanyaye na ce." In sha Allahu zai tashi zai samu lafiya."
Ya ce." To Allah Ya sa, ina fatan dai lafiya kuke na yi mamakin kiran da ki ka yi mini a wannan lokacin da ban yi tsammani ba, ni da kika kullace ni kina gaba da mijinki ko Amina baki damuwa da halin da nake ciki ba, ai ina kallon yadda ake soyayya a wurin Hajiya Maryam mai d'akin abokina Alhaji Amadu amma ni da nake da mata biyu kun yi watsi da ni ko, ita waccan din idan an yi mata uzuri ke fa? son ranki kike bi, ba ki damu da abinda zai same mu ni da Yusuf ko ba haka ba ne?"
Jiki babu kuzari na ce." Ban kyauta ba ka yi hakuri amma me yasa ka gaza fahimtata ya kamata ku yi mini adalci a wannan lamari sai ka tsiri gaba da ni, ban kullaceka ba kaine ma kake jin haushina dalilin da ya sanya ma kenan na ga rashin dacewar haka na kira ka yanzu domin mu sasanta gabar ta isheni haka.

"To tunda kin nemi sulhu zuwa za ki yi inda nake ai ki lallaba ni domin ni ma ba ni da wata lafiya rashin lafiyar abokina ta dame ni a kwanakin nan Ina buk'atar mai kula da ni ta ba ni magani ta kuma kwantar mini da hankali da kalamai masu dad'i zuciyata ta daina yi mini tunanin kamar ban yi sa'ar iyali ba."
Cike da mamaki na furta." Yallabai duk me ya kawo wannan maganganun don Allah."
Ya nisa kafin ya sake cewa." Kulawar da abokina yake samun wurin iyalinsa shine ya sanya nake jina kamar maraya gashi dai babu abinda Allah ya rage ni na jin dadin duniya amma matata ta na yi mini wulakanci."
Dariya maganarsa ta ba ni wai wulakanci wato shi baya duba abinda yake yi mini a matsayin wulakanci saboda namiji ne duk abinda ya yi daidai ne."
Na yi dariya 'yar kad'an kafin na ce." To shi ba ka ganin bashi da lafiya ai dole a ninka bashi kulawa ko ka manta lokacin da ka yi mura a gidana yadda na dinga lalla'baka ina rarrashinka kamar jariri."
Ya ce." Ni dai na gaya miki zan sanya a kawo miki ticket da za ki same ni anan abuja gobe kafin mu wuce saudiya ki ba ni magani kada na tafi da lalura.
A dukunkune yake maganar amma na gama fahimtar inda ya dosa wannan ya nuna mini cewa a mutukar bukace yake dauriya ce kawai da son dole sai an nuna iko ba zai neme ni ba muddin ba ni na neme shi ba yanzu kuwa dana tsaga billena na kira shi kai tsaye yake neman abu a wurina.
Ni ma saboda tawa biyan buk'atar yasa babu ja'inja na amshi gayyatarsa nasan ta wannan hanyar zan iya samun abinda nake so kai tsaye tunda Allah Ya riga ya ga zuciyata da munufaar da zanyi hakan.

Daya daga cikin masu yi masa jigila
ya turo da mota ya d'auke ni sunan shi Ade wani bayerabe mai gaggausan jiki da rashin fara'a
bayan saukata a garin abuja kai tsaye gidanshi da yake maitama ya nufa da ni kamar yadda ya bada umarni sai dai da yake ya san matsayina duk cud'ewar fuskarsa bai hana shi risina mini ba.
Gidan kwatankwacin na Legos me d'auke da bangarori da dama kuma cike da ma'aikata da masu tsaro da iyayen motacin da na tabbatar da cewa wasu ma sai a yi shekara ba a hau su ba.
Wurin ajiye motoci ya nufa domin gyara parking yayin da nake hangen maigidan da Yusi can daga nesa bakin wata bukka irin ta hutawa.
Yana kashe motar ya fito da sauri ya bude mini kofa har yana dan risinawa na fito a hankali Yusi ya taho a guje ya rukunkume ni yana dariya mamaki mai yawa ya lullubeni ganin yadda yaron ya yi wata iriyar ki'ba kamar wanda aka hura ya zama kato Na dinga binsa da kallo irin na mamaki da al'ajabi wannan wace irin ki'ba ce. Maigidan ya k'araso wurin yana sanye da jallabiya fara mai karamin hannu kansa da fara hula irin ta larabawa as'usul idonsa da farin gilashinsa. Na dube shi na 'yan dakika na fahimci zurmawarsa ya kara tsukewa dama abinka da mai karamin jiki ko dai da gaske yake shima din bashi da lafiya....
'
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*


*56*
Ade ya fito da k'aramar akwatina da na zubo kayana kala uku a ciki ya tsaya suna magana ni da Yusi muna gefa ya rike hannuna gam a cikin nasa yana cike da tsananin farinciki ni kam kallonsa kawai nake yi har na gaza ha'kuri na ce." Kai me ka samu ka ke ci ka zama d'an lukuti kana duba mudubi kuwa?"
Dariya ya kama yi yana cewa." Abinci kawai nake ci ai an yi hutu makaranta Mama amma ina hawa gym na tsinka jina na."
Na dube shi a lokacin da ya zo ya tsaya gabanmu Yana cewa." Ke kuma daga zuwa sai tuhuma."
Yar dariya na yi a hankali na ce." Abin ne ai da mamaki wallahi kibar ta yi yawa." Ya wuce ciki yana cewa." Ke ki ka gada masa ai ba kowa ba.''
Yusi ya kamo hannuna muka bi bayansa yana ta yi mini labari yaran Alhaji Amadu wanda suka zama abokansa jin      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  sa kawai nake yi amma ban ce komai ba sai dai zuciyata cike take da farincikin ganinsa cikin walwala da kyawun yanayi tare da lafiya da suttura irin ta 'ya'yan manya a jikinsa.
Ga gida har gida babu abinda babu a ciki ko 'diyar shugaban kasa za a iya ajiyeta a gidan amma kash babu mace a cikinsa asalima ya tanadi gidan ne kawai domin idan ya zo garin ya sauka a cikinsa tunda karfin zamansa ya fi legos.
Ya d'an ba ni tausayi kad'an domin kamar yadda ya fad'a cewa Allah bai tauyeshi da komai ba na jin dad'in duniya sai ta bangaran iyali, Ina ganin da zamansa anan yake dindindin zan iya ha'kura da can na zauna tare dashi to karfin zamansa ba anan yake ba, ni kuma gabad'aya zaman legos din ne ya fice mini daga raina.
Wajan cin abinci cike yake da cima kala kala da kayan marmarin dogon daning ne mai d'auke da kujeru takwas gaba da baya tsarin gidan gwanin ban sha'awa kuma a gare cikin tsabta kasancewar akwai masu aiki maza da suke yi hidima a gidan koda baya nan.
Sama ya hau nan turarkarsa take Ade ya shigo da akwatina ya ajiye ya fita, Yusi ya tashi da sauri ya bi bayan shi yana kiran sunan shi na bi yaron da kallo da alama akwai sabo a tsakaninsu.
Ajiyar zuciya na sauke a nutse nake bin falon da kallo ya tsaru ainun ya ji kujeru da labuleye na alfarma hotonsa dana iyayensa gasu nan birjik a falo can na hangi na baby Nana kato a wata kusurwa a jingine ba a kafe shi a bango ba.
Na jima tsaye ina duba hoton na share kwallar da ta ciko a idona na d'auka a gidansa na legos kadai ya ajiye hotonta ashe yana dashi a nan d'in ma.
Yana ba ni tausayi sosai a wasu lukutan domin shi din abun tausayi ne....
Sai da na d'an samu nutsuwa tukkuna na tashi na hau saman tunda nan naga ya nufa ai nasan wulakanci da shan kamshi zansha shi nasan sai dai na kai zuciyata nesa.
D'akuna hud'u ne kowanne a rufe sai guda daya da naka key a jikinsa ta waje hakan ya tabbatar mini da cewa yana cike ina ta'ba kofar kuwa ta bude na shiga da sallama a bakina.
Ya fito daga bandaki daidai lokacin da na shiga d'akin wanka ya yi ya ce." Shigo ciki sosai mana."
Na krasa na zauna gefan gado ina dubansa da gaske fa ya rame yanzu na sake gazgatawa da babu riga a jikinsa sa towol da ya dauro.
Ya dube ni yayin da yake ko'karin zama kusa da ni yana fad'in." Ya gajiya?"
Na daure a hankali na ce." Alhamdulillahi ya jiki ashe da gaske dai ba ka da lafiya Baba."
Ya ce." Lafiyata lau me ki ka gani?"
Kai tsaye na ce." Ramewa na ga ka yi?''
"Fargaba ce kawai wallahi na jima ban ga ciwon da ya tayar mini da hankali kamar na Alhaji Amadu ba sam ya'ki jin magani, yana nan fa sai dai a kwantar a tayar na gaya miki yana asibiti a yanzu amma jibi za a yi masa transfer zuwa asibitin makka.
Cike da alhini na ce." In sha Allahu zai samu lafiya kaima ya kamata ka cire damuwa daga ranka kada wani ciwo ya sameka ka rame fa sosai Baba dama kai ba jiki ba."
Yana yi mini wani irin kallo ya ce."Abin har da zolaya Amina."
Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ban isa ba, kawai dai ramar taka ce ta d'an tsorata ni Yusi kuwa kamar wanda ake hurawa."
Ai irin jikinki ne dashi na gaya miki ke ce ki ka gada masa 'kiba.
Ya tashi ya nufi wardrobe yana fito da kayan da zai sanya ya ce." Da daddare idan kin huta za mu je ki duba shi ko?"
Na ce." In sha Allahu rabbi." D'akin ya yi shiru na mintina shi yana ta hidimar shirya jikinsa yayin da ni kuma nake bin d'akin da kallo karaf idona ya sauka kan dirowar dake gefan gadonsa karamin hoton Samira ne irin wanda ya ajiye a gidansa na legos wanda na sanya ya cire shi.
Kishi na ji ya soke ni, ai ta riga ta mutu shekara da shekaru ya kamata ace yanzu ya cire ta a ransa amma ace kowane gidansa da hotonta a ajiye ban san menene amfanin hakan ba.
Ya juyo yana kallona ni kuma na janye idona daga kan hotonta ina ko'karin danne abinda nake ji.
Bai ce mini komai ba ya zauna gefan gadon tare da gyara zaman hoton dukda ba abinda ya yi ganin haka ya sanya na tashi tsaye sai ya yi saurin fad'in." Ki yi wanka sai mu sauka mu ci abinci ko?"
Ban ce komai ba na nufi bandakin zuciyata babu dad'i hotonmu ya fi kamata a ce ya ajiye gefan gadonsa ba na wadda bata raye ba, na fahimci har yanzu akwai sonta a cikin zuciyarsa hirarta ne kawai ba ya yi mini tunda ya fahimci ba na so.
Muna cin abinci yake gaya mini Yusi a gidan abokin nasa yake kwana tare da yaranshi da yake matarsa daya Hajiya Maryam auran saurayi da budurwa suka yi kuma da yake 'yan boko ne sun tsara rayuwarsu haihuwa uku sukayi suka dakata sun fara da mace mai suna Nusaiba wadda suka aurar da ita shekara biyu da ta wuce anan abujan tana auran babban ma'aikaci a central bank. Sai kuma Salim wanda yanzu yake matakin shekara ashirin Adam kuma sha bakwai.
Hajiya Maryam yar boko ce kuma muguwar 'yar gayu ce irin matan nan ne masu kyawun jiki da ado da kwalliya shekarunta sun buya sosai idan ka kalleta sai ka d'auka bata fi talatin ba amma ba haka ba ne shekarunta arba'in da d'aya a yanzu tsabar gyaran jiki ya sanya komai nata yana nan cif mussaman kirjinta sai da basu da wani girma amma dai tana kula da jikinta ainun.
kuma yar kasuwa ce domin manyan shop ne da ita garin abuja da kano da kuma reshenta a jos tunda asali nan ne mahaifarta amma dai harkokinta sun fi yawa a Abuja tana fita kasashen larabawa mussaman dubai da Qatar da India domin sarin kaya dogwayen riguna takalma sari irin na indiya da kayan maza Pakistani da kuma bangaran sarkoki abin hannu agoguna da sauransu. Yar kasuwa ce sosai wadda arzikin mijinta bai sanya ta nemi wuri ta zauna ba. Da yana gaya mini Yusi ya sha'ku da yaranta dalilin gidajensu na ma'kotaka da juna ban yi mamaki ba domin na tabbatar da cewa Yusi zai iya zama da kowa saboda yana da hankali da kuma iya mu'amula shi ma kuma Allah ya sanya masa kwarjini da farinjini a duk inda ya shiga.
Bayan Isha'i ya d'auke ni a mota da kansa ya yi direving din motar muka nufi asibiti a can muka samu Yusi tare da matasan yaran suna zaune kusa da gadon da mahaifin nasu yake kwance ko'ina na jikinsa sa'kale da na'ura yana ta kokawa da numfashi
Gaskiya dan adam ba abakin komai yake ba idan ma kana d'aukar kanka kai wata tsiyane wallahi gwara ka yi karatun ta nutsu domin Allah ne mai sarrafa al'amura gashi dai da kudin wanda da yawa muke ganin kamar sune karshen jin dadi bayan ba haka ba ne mai lafiya shine d'an gata domin kuwa duk wanda Allah ya wadata da lafiya shi ya yi wa arziki..
Ita da yaranta sun ba ni tausayi kwarai da aniya kuma yanzu na sake gazgata maganar da ya yi mini jiya a waya cewa suna mugun tsananin son junansu shiyasa gabad'aya ta susuce! Ta kasance kullum cikin zubar da hawaye...Da kyar ta iya amsa gaisuwata hankalina gabad'aya na kan maigidan nata da ko yatsansa baya motsi shi kansa na lura da kid'imewarsa da likita ya shigo suna magana yake tambayarsa ya ga an sake sanya masa oxygen bayan jiya aka cire ta kuma numfashinsa ya daidaita likitan ya ce masa ciwon ne ya sake tashi d'azu da yamma amma kuma numfashin ya fara daidaita ba kamar d'azu ba. Ya sake duba shi ya fita shi ma da yake likita jikinsa a mace balle ga mu da muke zaune.
Sai wajan goma da wani abin muka bar asibitin cikin damuwa da zullumi domin kukan da Hajiya maryam din take yi ya ta ba mu gabad'aya har dashi gabad'aya yanayinsa ya canza shi bai yi na hawaye ba yana na zucci irin mai mugun cin ran nan.
Na d'auka damuwar da yake cike ba zata bari ya nemi wata buk'ata ba. A daran bai iya bacci ba sai da ya kwanta da ni irin kwanciyar da na ji jiki a hannunsa har abin ya fara ba ni tsoro ganin yadda ya 'kirkiro wani style wanda ba mu ta'ba yin irinsa ba. Ban fahimci komai ba sai wahala saboda bai jima yana yi mini wassanin soyayya ba ya fara gudanar da abinda ya kud'irce a cikin ransa wanda tun ina yi masa kawaici har dai na gaza ha'kuri na gaya masa fa bana gane komai sai zafi da ciwon cinya. Ya ce shi kuwa atafau ta haka yake so ya yi don ya fi jin dadi. Haka nan na ha'kura na kyaleshi ya dingi yi tamkar wani sabon angon da ya jima yana shan sassa'ke. Wallahi kasa juriya na yi don duk fitinata wannan lamarin ya sha kaina kamar da zalinci a ciki. Ashe lumbu lumbu ya yi mini na zo hannu ya yi mini 'keta kuka kariris na dinga domin ya rabu da ni yana fad'in bai gama ba tukkuna. Da ya gama kuwa sai da na yi ruwan d'umi sannan na ji sasaauci na nemi waje can nesa dashi na kwanta cinyoyina suna ta ciwo. Na jima kafin bacci ya kwashe ni ina ta kallonsa yana baccinsa hankalinsa a kwance.
Can gefin asubahi kiran da ya shigo wayarsa ya tashe mu gabad'aya a zabure ya lalubi wayar yana dubawa da sauri yasa a kunnansa yana fad'in." Alhaji Jamil....."Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ce ta fito daga bakinsa bayan ya gama sauraran maganar mai kiran wayar wanda na ji ya kira shi da Alhaji Jamil.

Dama a wasu lukutan mutuwa takan nuna kama kafin wa'adin ya cika. Ni dai dama ganin da na yi wa Alhaji Amadu a wannan dare na sare domin gwiwata a sanyaye muka fito daga asibitin lokaci kawai yake jira amma alamun sallama da duniya ya gama bayyana a tattare dashi. Alhaji Jamil k'anine ga Alhaji Amadu tare suke ta tiriri dashi shi k'aninsa ne uwa daya uba daya shi kuma abokinsa ne tun na 'kuruciya abokin da akayi gwagwarmayar rayuwa.
Mutuwar Alhaji Amadu ta dake shi mutuka gaya domin ni sai na ce tunda na tashi daga kuruciya da girma ban ta'ba ganin kukan babban mutum kariris irin haka ba.
Na fahimci ya yi kokari sosai wurin ganin ya danne kukan amma hakan bai samu ba kuka ya dinga yi sosai amma ba mai gunji ba yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! lamarin ya tsoratani sosai wanda hakan ya sanya ni ni ma fashewa da kukan domin na rasa yadda zanyi na rarrashe shi.......
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=N*

*57*
Shine akan gaba wajan shirya Alhaji Amadu har aka kaishi gidansa na gaskiya, haka ya dinga kai kawo har ya ba ni tausayin da na ji kwalla ta cika kwarmin idona. Tabbas Alhaji Amadu ya wuce aboki a wurinsa sai da d'an uwa, domin tun a daran kafin gari ya waye ya dinga gaya mini irin gwagwarmayar da suka sha duk domin tsayuwa da kafafuwansu. Marigayin ya riga shi auran fari kusan shine ma ya yi masa rakiya ta angonci kuma tare suka dinga jigilar zuwa jos neman auran Maryam din har dai Allah Ya tabbatar da auran. Shekaru kusan goma sha biyu da auransu ne shi kuma ya yi auran fari Samira kenan Allah kuma ya dinga wanzar da ikonsa.

Ni kam da babu sha'kuwa a tsakanina da Hajiya Maryam ban nuna bak'untata ba mijina abokin mijinta ne sannan yarona yana tare da nata yaran ta ri'ke gabad'aya dalilin da ya sanya kenan na shiga cikin 'yan uwanta na zauna tare dasu har dare muna kar'bar gaisuwa a tare. Na sake yin karatun duniya sosai domin mutuwa wa'azi ce ga duk wani mumini na kuma tausaya mata kwarai da aniya ganin yadda ta zabge ta ki'dime a lokaci d'aya babu shakka mutuwar miji wani babban rashi ne da har abada ba za a ta'ba maye gurbinsa ba.
Sai wajan tara da arba'in tukkuna na shiga gida tunda muna kusa da juna amma ban tafi ba tukkuna sai da na tabbatar da cewa ta ci abinci domin yini guda babu abinda yake cikinta babu irin rarrashin da ban bakin da ba a yi mata ba tace ba zata iya cin komai ba. Itace babba a cikin 'yan uwanta shiyasa da suka gaji da rarrashinta suka ha'kura dalili duk ta girmesu iyayensu kuma basa raye itace ke ri'ke da ragamarsu gabad'aya ni ma na tabbata don tana jin kunyata ya sanya ta kar'bi abincin da na hada mata da hannuna ta dinga ci kamar magani tana goge hawayen da suka ki daina fita daga idonta.
Bai shigo ba sai wajan sha biyu saura shi Yusi yana can dama lokacin da ya shigo din har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba din tukkuna ina dakkon shigowarsa.

Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Wanka ya fara yi tukkuna ya same ni a zaune a gefan gado ya zauna kusa da ni. A nutse nake dubansa gabad'aya bashi da kuzari na ce." Sannu baba ya karin ha'kuri?"
Ya amsa da "Alhamdulillahi yana dan duba wayarsa ya ce." Gobe su Hajja suna tafe tare da Hajiya Saratu da sauran 'yan uwan mahaifina."
Na ce." Ubangiji Allah ya kawo su lafiya amma ka ci abinci kuwa?"
A nutse ya ce" Na ci amma ba mai yawa ba."
"Ko kana buk'atar wani abu yanzu wanda sai sanya cikinka ya dan yi nauyi."
"Wannan towon naki nake sha'awar ci irin wanda ki ka yi mini a gidanki amma dare ya yi yanzu za mu bari da safe sai ki yi mini ko?"
Cike da kulawa na ce." Muddin da akwai duk abun bu'kata yanzu ma sai na yi maka har da d'umame ai ba wani abu ba ne."
Ya girgiza kansa yana yi mini wani irin kallo ya furta." Ba ni da imani sai na sanya ki aiki da wannan dare duba lokaci fa sha biyu har ta gota."
A nutse na ce." To ai aikin lada ne?"
Ya d'an jima yana kallona kafin ya girgiza kansa da cewa." Ki huta kawai na gode."
Jikina ya d'an mutu da yawan kallon da yake yi mini wanda na kasa tantance na menene na soyayya ne ko na wani abin ne.
Wayarsa yake latsawa kafin yasa a kunnansa

Please Login or Register in order to submit comment