Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi gyaran murya ya ce." Kin san abinda nake so dake?" Ta ce." A'a. "
Ya ce." Amina ta yi mini bayanin duk abinda yake faruwa, ki yi hakuri ki koma dakin mijinki ki cigaba da kula da yaranki, shi kuma ki kyale shi idan har kina da hakki sannu a hankali Allah zai saka miki. Ni kuma zan yi miki alheri domin ki zauna a wadace cikin walwala zan canza miki gida mai kyau sannan zan baki kudi ki dinga wata sana'ar a gefe sannan ki cigaba da zuwa aikinki kina taimakon yaranki da 'yan uwa, kada don mijinki zai kara aure ki yi fushi ki dasawa kan ki k'unci yaranki su shiga damuwa ki daure na wani lokaci komai zai wuce ."
A sanyaye ta ce." Na gode ranka ya dad'e, Allah Ya saka da alheri, shikkenan in sha Allahu zan koma kamar yadda ka buk'ata."
Cike da jin dadi kuwa ya furta." Ni ma na gode sosai Sahura, zan yi magana da Jamilu sakatare na nan kamfanin naku duk abinda yake da akwai zai yi miki bayani in sha Allahu maganar abinda na ce zan baki kuma za ki gani a daran nan."
Ta dinga godiya har muryarta tana rawa. Ya mik'o mini wayar na kar'ba a d'an sanyaye na ji dad'i sosai da ya shiga lamarin gashi har da alherinsa ko babu komai yana da lada a wurin Ubangiji.
Muka yi sallama da ita tana fad'in." Na kara yi masa godiya. Na dube shi a hankali na ce." Mun gode sosai Ubangiji Allah Ya saka da alheri."
Bai kalle ni ba ya ce." Ba ni details dinta yanzu ."
Ya miko mini wayarsa na kar'ba na sanya masa kamar yadda ya ce.
Ya ce." Ke nawa ki ka bata gudummuwa?"
Na ce." Gudumawa kuma?"
." Dannar kirji kuke cewa ko?"
Dariya na yi na ce." Ban bata komai ba wallahi."
Ya d'an Harare ni yana fad'in." To yaushe kuwa za ta saurari rarrashinki irin wannan ana had'awa da hasafi sai ki ga an shawo kan matsalar."
Na dinga gyada kaina ina dariya lallai ne kudi suna iya sayan komai amma ban da rai da rayuwa.
Miliyar biyar ya tura mata bai gaya mini ba amma yana tura mata da kamar minti goma ta kira ni a ki'dime har da rawar murya "Amina don girman Allah ki kara yi mini godiya yanzu nan na ga sa'ko 5m na gode na gode na gode Allah Ya saka da alheri ga sabon gida an ce za a ba ni."
Dariya ta kama ni na ce." Sahura yanzu don Allah ina rantse-rantsen da ki ka dinga yi, Idiris fa aure zai ka'ra ko kin manta."
Ta ja tsaki tana fad'in." Wallahi tallahi Amina saboda Yallabai ya saka ba ki a maganar nan zan koma zaman aure da Idiris amma wallahi ba don haka ba sai dai ya aiko mini da takardata."
Ta kashe wayar ba tare da ta jira ta ji abinda zan ce ba."
Ya dube ni yana fad'in." Ba ki kyauta ba Amina." Ina dariya sosai na ce." Don ba ka ji rantsuwar da ta dinga yi ba shine abinda ya ba ni dariya da mamaki."
Ya gyad'a kansa Shima da d'an murmushi a saman fuskarsa ya ce." Ai tace saboda na sanya ba ki zata koma. Kuma wallahi na ji dad'i sosai tuntuni na fahimci cewa ai tana da kirki da saukin hali."
A tak'aice na ce." Hakane kam Sahura mutum ce har da rabin mutum mun gode sosai ta ce na sake godiya ina yi akan kaina da ita Ubangiji Allah Ya sa kafi haka."
Ya amsa da Amin suma Amin yana kallona.
Na dan sauke ajiyar zuciya kafin na ce." Sai mu yi maganar Hauwa tunda mun sasanta wannan auran."
Ya bata rai yana fad'in." Za ki bata mini rai kenan ko?"
Na ce." B'acin rai kamar yaya?"
Cikin 'kosawa ya ce." Maganar Hauwa ta ishe ni a gidan nan Amina, ya kamata ke ma ki bar ta kamar yadda na bar ta ba na son abinda zai rikita mini gida dama can itace husumiya yanzu da bata nan ba gashi kuna zaune kalau da Maryam ba."
Haka kawai sai na ji rashin jin dadin maganarsa. A ganina kamar Hauwa bata cancanci haka daga wurinsa ba duk da bai gaya mini abinda ya faru ba a wajan sulhunsu amma na lura haushinta da yake ji ya sake ninkuwa. Zaman da na yi da ita na fahimci macace mai taurin kai da girman kai har shi eanda ya ajiyeta yi masa take kuma a cikin ayyukan da ta dinga yi a gidan nan da gadara da iko take gudanar da komai dalili tana ganin kamar ta fi kowa dangantaka mai karfi bayan ta aure duka na fahimceta. To amma ni wannan baya damuna tunda nasan matsayina a zuciyar mijina ko bai fito ya fad'a ba. Ba na sha'awar a ce sun rabu gabad'aya ga zuria a tsakaninsu mai k'arfi kamata ya yi a ce sun sulhunta junansu sun yi hakuri sun cigaba da zama.
Ganin yadda ya had'e rai da nuna baya buk'atar sake maganar Hauwa sai na shigo da maganar zuwa maiduguri tunda shi ya yi mini alkawari ya ce za mu je a karshen wata amma daga mun dawo za mu tafi legos tunda Alhmdullhi jikin matar tasa ya yi sau'ki.

***
Abinda ya faru kenan kamar yadda ya yi mini al'kawari cikin karamci da kara da kulawa muka je maiduguri tare. Ya bi dangin Mamana da alheri mai yawa. Baban Saude bayan gari a lokacin da muke je garin. Da yawa wad'anda ba su ta'ba ganinsa a zahiri ba suka yi tozali da shi tare da alherinsa. Ni kuma na sayawa Fadila sabuwar freezer 'katuwa da kenan d'inki domin yin sana'ar sayar da ruwa da 'kan'kara.
Kwananmu biyu kacal a maiduguri muka yi sallama da su.

A ranar da muka dawo a gidan Momi ya kwana washe gari ya shigo mini a hargitse yana gaya mini jikinta ne ya sake tashi jiya ba su yi wani baccin kirki ba suma ta yi sai gefan asubahi ta dawo.
Ya ba ni tausayi sosai itama haka domin da gaske ne duk mai zuciyar imani idan ya ga halin da take ciki zuciyarsa sai ta motsa. Dole shiryin tafiyarmu Legos ya rushe yadda hankalinsa ya tashi da ciwon komai nasa tsayawa ya yi

Kwana biyu a tsakani ya sake kwasarta suka sake koma can kasar hindu din asibitin da suka kula da ita a wancan karon domin sake duba lafiyarta.....
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*

https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<Ø2ß<Ø3ß<Ø?ß&þ

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram normal What'sapp group 1k via 0542382124...binta Umar gtbank*
07084653262
Tun bayan tafiyarsu sau biyu muka yi magana dashi kamar dai wancan lokacin da suka tafi muna had'uwa ne ta What'sapp mu yi vidiyo call abinda ya kasance kenan amma wannan karon babu nisha'di da annashuwa a tare da shi muka yi magana. Idan na tambaye shi yanayin jikin nata sai ya ce mini da sauki. A wancan lokacin yi yayi kamar sabon angon da yake watayawa da amaryarsa ya yi fresh dashi don har na dinga tsokanarsa wannan karon kuwa akwai firgici da damuwa a tare da shi ko bai fad'a ba yanayinsa ya gama nunawa.
Na kasance cikin yanayi na tunani da zullumi domin yau tafiyarsu kwana goma sha daya kenan kuma a cikin kwanakin sau biyu kacal ya ta'bo ni, tun daga ranar ma ban sake ganinsa a WhatsApp din ba. Idan na kira waya ta yanke ko na ji busy. Gaskiya na damu sosai hakan ya sanya mini rashin nutsuwa domin sai zuciyata take ta yi mini sa'ke-sa'ken mugun abu bayan mafarkin da nake yi wai gani ina da dariya da ita mara lafiyar muna hira muna ta k'yalkyala dariya. Masana mafarki kuwa suna fad'in yin dariya a mafarki ba alheri ba ne.

Gaza ha'kuri na yi na sanar da Baba Tabawa halin da ake ciki itama ta taya ni zullumi tana ta addu'a Allah Ya sa lafiya ina amsawa da Amin.
Idar da sallar magribata kenan na d'auki wayata dake saman dirowa ba na iya minti ashirin yanzu ban bud'e data na duba ba. Cikin ikon Allah kamar iska sakonshi ya shigo. Hoton Momin ya turo mini cikin mawuyancin hali gabad'aya duk ta 'kare ta yi fiyat da ita tana kwance a tsakure a gado hancinta da abin taimakawa numfashi. Na tsorata ainun da ganinta duk da ba a zahiri ba ne hoto ne sai da na ji wani irin tashin hankali ya rintsa da ni a lokacin zuciyata ta karya na kasa jimirin jure danne hawayen da suke danno mini. Suka fara sauka a kumatuna. Wannan ciwon ya gama cinye matar nan manya cutuka sun zagaye rayuwarta.
Vidiyo call ya kira ni ina goge hawaye na danna da ya ga ina kuka ya fara tambayar menene. Na ce." Ni dai daka sani ba ka turo mini hoton nan nata ba hankalina ya tashi wallahi."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Tana jin jiki sosai Amina ku taya ta da addu'a gabad'aya bata gane wanda yake kanta numfashi kuwa sai da taimako."
Na goge hawayen da yake tsiyaya ina fad'in." Allah Ya saukaka mata. Kai kuma Allah Ya baka lada."
Ya furta da "Amin." A tak'aice kafin ya cigaba da cewa." Kwana biyu mun d'an yi rashin service a garin. Sai jiya da daddare ya daidaita ban kuma samu sukunin ta'bo ki ba sai yanzu ina fatan kuna kafiya."
Na ce." Wallahi lafiya lau, ni ma ina nan hankalina a tashe gabad'aya na kasa nutsuwa ina ta tunanin halin da kuke ciki."
Ya d'an yi murmushi kafin ya kanne mini ido ya ce.'' Ni kuma mafarkin ki na dinga yi kullum na kwanta sai kin zo mini har na yi wanka da asuba."
D'an harararsa na yi na ce." Kai kam ka daina haka don Allah."
A sakarce ya ce." To ya za a yi ne Amina da gaske nake wallahi kin san kuwa ba zan yi miki rantsuwa akan son rai ba. Mafarki nake yi ina tara dake duk dare kuma na yi wanka." Na ce
"Allah Ya kyauta."
Ya amsa da "Amin.'' Kafin ya ce." Bari zan ta'bo ki kafin na kwanta sai mu yi hira ko?"
A sanyaye na ce." To." Ina mamakinsa duk yanayin alhinin da yake ciki halinsa na fitina yana nan.
Na ajiye waya tare da yin kasa'ke gabana sai ya buga da k'arfi idan na tuna halin da naga matar nan a ciki.
Wayar na d'auka na yi saurin goge hoton ba tare da na sake kuskuran sake gani ba.

To har na kwanta ban ga motsinsa ba. Da asuba kuwa ina gama ibada kamar koyaushe na bud'e data sakon shi ya shigo kamar iska.
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! dana fara gani tun kafin na bud'e sakon shine abinda ya assasa mini 'barin jiki da kakkarwar hannu. Na bude gabana na bugawa da karfin gaske...
_"Allah Ya yi wa Maryam rasuwa a daran nan ki sanar da duk wanda ya kamata Amina."_ Abinda yake rubuce kenan
Wani irin tsananin tashin hankali da d'imuwa na shiga ina daga zaune na dinga jin tafin kafata na wani irin yammm! hannuna da ke ri'ke da wayar ya sandare wayar ta fad'i saman cinyata. Ni kaina saukar hawaye na ji a saman dakalin fuskata suna kasa tsare da babban sauti na furta." INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN! Allah Ya jikanki Maryam, Ubangiji Ka yafe wa baiwarka, ashe ciwo ba na tashi ba ne."
Wani mahaukacin kuka mai gunji ya taho mini a guje! Na sanya tafin hannuna na toshe bakina ina fad'in." Mun shiga uku a wannan duniyar da bata da tabbas Ya Allah!!"
Wayar na laluba da saurin gaske tabbas wannan shi zai zama izna ga Hauwa ya nuna mata cewa babu abinda yake cikin wannan duniyar face rikici da firgici tashin hankali da rashin tabbas
Bugu d'aya wayar ta yi ta daga cikin kukan da na kasa jimirin danne shi na ce." Hauwa Momi ta rasu."
Cike da rikicewar murya ta furta." Wac...wace Momin kike nufi Amina?"
Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewar a ki'dime take... Na ce." Momi dai da kika sani matar mijinki Hajiya Maryam."
Dif ta yi sai sautin shuhhh! ne yake tashi a kunnana. Na daga wayar na duba tana ta tafiya. Sunanta na kira ta amsa a sanyaye "Na'am. Na ce." Ki sanar da inna Uwani halin da ake ciki Hauwa kin ga dai duniyar ko ita kenan fa."
Ta yi shiru dai bata tanka ba. Na ja ajiyar zuciya ina jin yadda wani kutittiran abu ya tokare mini a wuya ba komai ba ne face damuwa da tsananin kidima da tashin hankali.
Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai kawai na datse kiran na nemi lambar Hajja domin ba na tsammanin ta san da rasuwar tunda a sa'kon da ya rubuto mini ya ce na gayawa wanda ya dace.
Sosai Hajja ta gigice da ta ji labarin rasuwar dan har sai da na yi dakacen sanar da ita tunda ita kanta ba ta da koshin lafiya. Kasa jimirin sauraran kukanta na yi na datse kiran hannuna na rawa na ajiyeta saman cinyata hawayen suka sake zubo mini a saman fuska. Hannu nasa na sharce na sake saukar waya a karo na uku anti Yagana na kira na sanar da ita domin ta gaya duk wanda ya dace a yi jana'iza da shi. Na kira Babanmu na sanar dashi shi ma ya tabbatar mini da cewar za su kamo hanya gobe da sassafe shi da Baba Sule.
Jiki a sabule na fita falo baba Tabawa tana d'akinta sai na bita can. Na sameta tana ninke kayanta ganin yanayina ya sanya jikinta mutuwa. Rashin kwarin kafafuna ya sanya ni zubewa gabanta na furta." Baba Tabawa Momi ce ta rasu fa?"
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Kalmar da ta fara furtawa kenan kafin ta tallafe ha'barta cikin alhini da tace." Baiwar Allah nan ashe ciwo ba na tashi ba ne." Hanci na ja tare da furta " Baba tunda ranar da muka je dubata farkon ciwon Awallahi hankalina ya kasa kwanciya haka kawai daga ta fad'o mini sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi ciwon nan nata ya tsaya mini a rai na sosai."
Ta girgiza kai cike da kasala ta ce." To a Amina abin ne da ban tsoro ga yanayin yadda hallittunta suka jirkice ba ke kad'ai ba ni kaina da ita nake kwana da ita nake tashi a rana wallahi Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya yafe mata, halinta nagari ya bita don arzikin Annabi."
Da "Amin na amsa tare da cigaba da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un domin samun nutsuwa da k'adaita Allah da kuma tabbatar da cewa gare shi muke kuma gare shi za mu koma.


Wannan littafin na kudi kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Mun jima muna alhini tare da tariyo kyawawan halinta ( mu kula anan kun san dai a al'ada koda mutum ya ninke (boye ) abinda ya shuka na sharri da rashin kyautawa a duniya babu yadda za a yi a ce rud'ani da razani na mutuwa ya bari mutane su iya furtawa. Ku sani ko kafiri ne ya mutu a matsayinka na musulmi kaga gawarsa sai ka shiga hankalinka lokacin ne za ka tuna lallai fa ni ma akwai wannan ranar za ta zo mini ba tare da na yi shiri ba. Zan mutu za kuma a haka rami a binne ni. Amma ita mutuwa ai mai tonan asiri ce idan an shuka kairan za ta nuna idan sharrin ma aka shuka duka zata nuna. Mu bi a sannu a hankali a daina yanke hukunci don Allah kuma a fahimci sa'kon da ake so a isar a wannan littafin ta kowace siga zai fita yadda kuke so)

Sahura na kira a waya na gaya mata. Itama dai kamar yadda yake faruwa a al'ada a kidema take fad'in." Da gaske ta rasu Amina?"
Na ce." An ta'ba wasa da mutuwa dama, wallahi ta rasu da gaske. " Ta dinga nanata kiran sunan Allah tana istigifari da fad'in Allah ka yafe mana.
Na ce." Mutuwar matar nan ta dake ni wallahi
Sahura ba ki ji yadda nake ji ba a raina na tsorata da wannan duniyar gabad'ayanta. Ita kanta Hauwa tana can cike da gigita domin kasa magana ta yi da na kira ta a waya na sanar da ita sai kashe wayata na yi domin bakinta ya mutu murus ta kasa magana."

"Ai Amina mutuwa wa'azi ci ga duk wanda Allah Ya sa zai hankalta, duk d'aukaka da sharafin mutum a duniya ba iya tsallaketa. Mu 'yan adam ai muna da mantuwa shiyasa muke ganin kamar ba za ta zo kanmu ba, a yadda dai kike ba ni labarin irin abinda Hauwa take yi wa matar nan wallahi ita ya fi kamata mutuwar ta dake ta, ta kuma ji tsoron Allah har ta mutu bata nemi afuwarta ba Allah baya yafe hakkin wani akan wani har sai wanda aka zalinta ya ce ya ya yafe, aikin banza ai kishi ba hauka ba ne, ni kaina Hauwa ta ba ni mamaki kuma na raina wayo da iliminta domin jalihi ne kadai ba zai fahimci cewa ba hassada take yi wa baiwar Allah nan ba, misali dani daku duka hasashe muke akanta domin ba mu da tabbas a duniya muke ji ana fad'in mashirika ce amma ai ba mu ta'ba ganinta tana yi ba. Idan ma tana yi din wannan ita da mahallicinta ne, ni yanzu tsoron duniyar nan nake yi wallahi Amina kowa ya kashe wutar gabansa."

Shiru na yi ina ta auna maganganun da take yi. Ni kaina na kan zauna na yi ta nazari akan mai yasa Hauwa ta zafafawa matar nan da yawa. Kishi ne ko hassada mai yasa komai sai ta mayar da shi rigima da sa'insa lefi ni aka yi wa amma ban yi irin abubuwan da take yi ba, tabbas dole a dora ayar tambaya a kanta koda kuwa ba hakan ba ne a zuciyarta ni kaina ba zan fita daga zargi ba tunda yan uwanta da yawa suna ganin cutar da ita muke yi ta hanyar hade mata kai da yi mata tawaye tare da fito da kishi muraran. Idan zan kwana ina rantsuwa da Allah kan cewa ba ni yi mata hassada da b'akinciki babu wanda zai yarda.

Haka dai muka yi sallama cikin yanayi na damuwa da tashin hankali.

Baban Saude ya kira ni yana tabbatar mini da cewa suna kan hanya suna da d'an yawa.
Na kira Babanmu ya ce mini shi ma sun taso su uku har da Ummansu Hadiza.
Wanka na yi na kintsa na fita falo cikin hijabi har kasa na samu Baba Tabawa itama cikin hijabin da carbi ta kammala abin kari da d'an dama. Da asuba na ce ta yi abinci da yawa saboda bakin da suke tafe. Muka gaisa tare da sake yi wa juna gaisuwa. Masa'udu tare da
Sale suka shigo da akwati kafin shigowar Hajjan Kamalu ne ya fara shigowa tukkuna suka shigo Hajja da Gwaggo da Hamusu a biye a bayansu.
Bakin kofar na isa da sauri ina yi musu barka da zuwa. Na kar'bi jakar dake hannun Hajja ina fad'in." Gwaggo sannunku da hanya Hajja kun yi sauri sosai fa kamar a hanya kuka kwana."
Suka zauna a kujera tana fad'in." Kina fad'in rasuwar na ce Kamalu ya sanar da Gwaggo maza ta shiryo mu taho
kuma dai Garba ya k'ure gudu sosai shiyasa Allah Ya kawo mu."
Na nutsu sosai muka gaisa a tsanake Hamusu dake can saman kujera mai cin mutum d'aya ya gaishe ni na amsa tare da tambayar iyalinsa da yaronshi Arif da bai wuce shekara uku ba ya ce mini duk suna lafiya. Baba Tabawa bayan sun gaisa da yi wa juna ta'aziyya na ce ta kawo musu abinci domin bayan karin kummalon da ta yi da yawa har ta kammala na rana
Na dubi Kamalu dake gefe a tsaye jikin labule ya sake girma da fad'i sosai suffa ta mazantaka ta bayyana a tattare dashi har da gemu ya fara ajiyewa. Yatsansa makale da carbi mai lamba yana ta rarraba ido a kanmu yanayinsa gabad'aya kamar mai nazarin wani abu damuwa da tashin hankali sun gama bayyana a tattare dashi. Ganin mun had'a ido dashi ya sanya ni janye nawa idon. Ina jin wani abu na taso mini da tashin hankali. Kawai zuciyata ta fara raya mini cewa ni ma haka zan fadi na mutu yarana su sake kasancewa cikin maraici.
Ya gurfana a gabana cikin kula da ladabi ya furta."Mama ina kwana ya muka ji da hakurin wannan rashi."
Na amsa da "Alhamdulillahi mun gode Allah."
Ya furta." Allah Ya jikan Momi Ya gafarta mata."
Gabad'aya muka amsa a falon.
Na dubi Hajja tare da fad'in." Yusi bai samu zuwa ba ne.......
'þ
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*



https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
<Ø2ß<Ø3ß<Ø?ß&þ

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da

Please Login or Register in order to submit comment