Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabad'aya ya manta da cewar ba ni kadai ba ce matarsa akwai wata wadda son rai da rashin hakuri ya sanya yake take mata hakkinta. Yanzu tun ina jin haushin Hauwa wallahi ta fara ba ni tausayi domin kuwa tun daga ranar da yaron nan Sultan ya suma ta yi bala' 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~in sanyi take neman shiri da ni kuma yanzu takan fito falo ta zauna idan ta ji motsinmu da yara da masu aikin ana wasa da dariya sai ta fito ta zauna tana bin mu da kallo tana d'an murmushi har idan an yi magana ta tsoma baki amma dai duk da hakan yaran nahiyar da take zaune basa kallo balle ma su je wurinta ta dinga jan Usai kenan da wasa ita kuma tana nok'ewa tare da zum'bura baki nata yaran Khalil da Minal bata yi musu magana balle kuma Sultan da baya son ganinta ko zama ta yi idan yana wasa sai ya rarrafa ya nufi wajen uwar rainonsa abin yana yi mata ciwo sosai. Amma babu yadda za ta yi haka gobe ma idan ta ji mu da yaran za ta sake fitowa.
A yau din ne da wa'adin ya cika kwanan turaka ya dawo hannunta duk da na lura duk ranar girkinta bata hawa saman yau kuma tun safe naga tana kai wa da kawo wa a falon ta hau saman har sau biyu. Sai na ji dadin hakan a cikin raina duk dai har yanzu ina jin tsoron kaidinta amma dai zan fi so su shirya su daina zaman gaba da k'ullatar juna tunda tuntuni sun riga sun zama abu daya.
Ban sani ba ko sun sasanta bai nuna mini alamar hakan ba tunda ai namiji ne yau zai ce baya son abu gobe kuma ya canza ya ce yana so kuma itama macace tana da nata dabarun na janyo hankali.
Na so dai a ce a yau din da yake ta gand'okin yin jima'i ya jarraba a kaina domin fita daga kokwanto da samun kwanciyar hankali dan gaskiya damuwarsa ce kawai ta fito fili sai nake ganin na fi shi damuwa kawai ina dannewa ne.
Kwalliya ta yi sosai da yamma nuna tare da yaran a falo da yake Juma'a ce suna hutun makaranta ta fito ta dan zauna cikin mu na kamar minti talatin wajan biyar da arba'in ta haye saman tun daga lokacin ba ta sakko ba har da dare ya shigo na tashi na nufi d'akina domin gabatar da sallar magriba.
Na gama lazimina na dan jingina jikin gado zuciyata na d'an harbawa kad'an sai na tsinci kaina da shiga damuwa. Na sake rintse idona da k'arfi ina kiran sunan Allah ba ni so kishi ya jefa mini son rai a zuciyata idan har da adalci ya kamata a ce na bashi goyon baya wajan ganin ya yi hakuri sun sasanta junansu. kuma daidai gwargwado ta yi hakuri ta jure kuma alamu ya nuna ta zubar da makaman ya'kinta neman shiri take yi ta sigogi da yawa. Amma dai duk da haka na so a ce yau din a yi gwajin a kaina ko don samun nutsuwar zuciya.
Sai da na yi sallar Isha'i tukkuna na ci abinci. Na samu waje na kwanta da wayata a hannu Ina d'an duba What'sapp dina amma dai still can kasan zuciyata sai dokawa yake yi ina mamakin ganin bai kira ni a waya ya nemi abinci ba kamar yadda yake yi idan ya dawo daga sallar isha'i wata zuciyar ta ce mini wata'kila bai shigo ba har yanzu shiyasa. Na girgiza kai ba na tsammanin hakan domin da ya yi sallar Isha'i yake shigowa sai da babban dalili yake sake fita idan ya ci abinci yakan dan duba Loptop din shi har zuwa goma na dare ko sha daya gaskiya ya shigo.
Ko dama murnar da yake yi kenan tunda sun jima ba su had'u ba dole ya yi marmarinta ya nuna gandoki. Idan kuma na tuna irin lugwigwitar da jikina ya sha a hannunsa a tsukin kwanakin da suka kasance na shara'din sai jikina ya yi sanyi na kasa gazgata kowane sashe na zuciya.

"Na gaya miki fa Hauwa na daina kwanciya dake saboda wannan dalilin na ji dad'i dake na dare daya ki dasa mini b'akinciki na shekara goma. Ban had'a shimfida dake ba balle ki d'auki ciki ki haife mu yi fad'a ki dire mini yaro ko yarinya ki tafi gidanku wannan shine hujjata." Ya yi maganar cikin kwanciyar hankali
A raunane ta ce." To yanzu ya kake so na yi na kai geji na rantse da zatin Allah ji nake yi kamar zan yi hauka a tsananin buk'ace nake rayuwata za ta shiga matsala."
A nutse ya furta." Ba ki yarda da hujjata ba kenan. Ba fa zan yi ba na gaya miki ki tashi ki fita kina 'bata mini lokaci zan yi aiki."
"Dan girman Allah ka yi hakuri kada ka jefa rayuwata a wani hali."
Ya dubeta sosai yana fad'in." Kin ga na yi miki kama da wanda zaki karyawa rantsuwa Hauwa?"
Ta girgiza kanta cike da damuwa."
Ya ce." Ba zan yi kaffara akan ki ba, ki tashi ki ba ni waje idan kuma za ki iya yi mini fyade Bismillah."
Tana kuka sosai ta furta." Allah mai ji ne da gani, kana zalintata kana tauye mini hakkina na rayuwar yau da gobe ba zan yi maka fyade ba amma sai Allah Ya saka mini tunda ni ba mazinaciya ba ce balle na je na nemi wani kai kuma kana yi da matarka kuna gamsar da juna hakkina ba zai barku ba wallahi."
Dariya ya kama yi yana kallonta kafin ya ce." Ke ni fa ba wata lafiya na cika ba yanzu idan ma za ki daina shiga 'kunci akan ban kwanta dake ba itama Amina ha'kuri take yi Maryam ta kassara ni da asirinta.
Cikin rashin yarda da maganarsa ta furta." Wallahi ban yarda ba ai dama can haka ka ke yi mini ka jima kana zalintata sai Allah Ya saka mini."
A gajarce ya ce." Ni ma Allah Ya saka mini."
Ta tashi tare da kama hanyar fita ya bi ta da kallo ko daya bai tausaya mata ba domin ji yake yi har yanzu bai gama goge takaicin da ta cusa masa ba a baya.
Da asubahi ban kai ga tashi daga dadduma ba ya shigo da jallabiya da carbi tabbacin daga massalaci ya fito. Muka gaisa ya nemi gefan gadona ya zauna har da cire jallabiyar ya ajiye. Na ninke dadduma na ajiyeta a wajenta na zauna ina kallonsa a nutse na ce." Kwana biyu da suka wuce mun yi waya da anti Yagana tana gaya mini Dada bata da lafiya don har kwanciya ta yi a asibiti."
Da alhini ya ce." Me ya same ta?"
Na ce." Ciwon wuya ta yi amma dai da sauki an sallamota daga asibiti ina son zuwa dubata."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ban 'ki zuwan ba amma legos nake so ki shirya mu tafi cikin satin nan da zamu shiga."
Na ce." Da dai ka d'auke mini zuwa legos din nan tun da kaga a halin da nake ciki ya kamata na zauna waje d'aya na samu nutsuwa ku je da Hauwa kawai."

Ya d'an Harare ni kafin ya ce." Dake zan je Hajiya ba wani dadewa za mu yi ba in sha Allahu mu dawo cikin yaranmu mu je mu huta ni dake na wata d'aya sannan akwai ayyukan da nake so na gabatar a can din."
Shiru na yi ina kallonsa tare da raya abubuwa da yawa na yi masa maganar Hauwa yana hararata kuma bayan tare suka kwana nuna mini yake yi har yanzu ba su daidaita ba.
Ya ri'ke hannuna yana d'an janyo ni jikinsa yana cewa." Jiya me yasa ba ki zo ba?"
Na ce."Me yasa zan zo? Don girman Allah ka daina wasa da tunaninmu yanzu don ka sasanta da Hauwa shine abin yi mini boye-boye na fi kowa farincikin hakan wallahi."
Ya fara ko'karin cire mini hijabin jikina yana fad'in." Ni na gaya miki haka Amina kada ki yi mini rigima a irin wannan lokacin da nake tsananin kewa da bukatarki kada ki yi abinda zai dakusar da farinciki da karsashina my love.."
Ya fara sumbatar sasssan jikina a mutukar dimauce yana yin wani irin numfashi bakina ya mutu murus domin abinda jikina yake marari ne ya samu da na yi yun'kurin yin magana da turjiya sai na ji bakina ya yi nauyi bayan sa'kkonin soyayyar da yake aika mini ta kowace ga'ba. Bakinsa ma amayarwa yake yi tare da wata irin sheshsheka haka muka kasance cikin ru'kun'kumar juna zuciyata na ta tsalle ido a lumshe can kasan zuciyata ina ta kiran sunan Allah da ro'kon Allah wanzar da alheri akan abinda za mu yi Ubangiji maji ro'kon bayinsa wata iriyar rayuwa muka yi wadda ta ki'dimar da mu. Kuzuri da nagarta da mazantaka abin sai godiyar Allah da sake jaddada addu'a ga Malam D'aha da zuri'arsa kamar yadda ya fad'a mun ga zahiri domin kuwa ni zan tabbatar da cewa karfinsa na d'a namiji ya ninka na baya kafin a yi masa d'aurin goro.
Muna gamawa ya dinga godiya ga Allah har sai da ya ba ni tausayi a d'akina ya tsarkake jikinsa yana fad'in." Amina zan iya mallakawa Malam D'aha rabin dukiyata domin wallahi ya taka muhimmiyar rawa ga rayuwata na riga na sare fa ban ta'ba tsammanin mazantaka zata dawo ba sai gani rass da ni ki gaya mini ya ki ka ji don Allah."
Ya fad'a yana kanne idonsa daya.
Ni ma cikin tsokana na ce." A wallahi ras da kai Baba gaskiya ka yi bajinta Allah Ya sakawa da Malam 'Daha da alheri ya cancanci komai daga wajenka
Ya riko ni yana fad'in." A hankali duk zan biya ki bashin da na ci miki ko?"
Cikin nuna ya yi kokari na ce." Haba ai tun jiya ka biya ni Allah Ya taimake ka, a ai sai da na ce alhamdulillahi."
Ya kuwa fashe da dariya yana sake rungume ni a jikinsa.

Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.


To a haka na yi kwana biyu na muna morar juna da nishadi ranar da Hauwa ta kar'bi girki kuwa ya rasa gane inda ba dosa tunda na hau na gaishe da safe ban yadda mun sake had'uwa ba marigaba na yi na shige d'akina na kuma kulle kofata duk da nasan aikin banza na yi yana da mukkulin d'akin amma dai hakan zai fi mini kwanciyar hankali ya kwana shi kadai idan ma ba zai kwanta da ita ba.
Babu kalar rarrashin da bai yi mini ba ta waya na ce ba da ni ba wallahi duk yadda nake jin zafinta a raina ba zan yadda ya had'a kai da ni a zalinceta ba to ballantana ma yanzu da da ta sauko take neman shiri ba na jin haushinta amma fa na ki sakin jikina da ita.
A haka muka cigaba da rayuwar a gidan har ya ha'kura ma duk ranar girkinta baya nema na ban san dai ya suke 'karkewa ba tunda nakan dan ganta jefi jefi ta hau saman a ranakun da take da girkin ta kara ramewa kwarai da gaske ta zama silent ma kamar ba Hauwan da na sani ba mai neman fitina da son kin zaman lafiya. Kuma har yanzu jiya I yau tsakaninta da 'ya'yanta sai dai ido idan ma ta kira su wajenta Minal dai ba ta zuwa Khalil ne koda zai je a cikin fargaba da shakku yake zuwa saboda ta saba dukansa."

"Hauwa Legos za mu tafi ni da matata ban hana ki zama ba tunda kina ganin za ki iya amma wallahi tallahi kada na ji kada na gani akan yarana da wanda ki ka haifa da wanda ma ba ki haifa ba lafiya lau za mu tafi mu bar basu da masu yi musu hidima duk abinda ya faru a gidan nan zan yi kuka dake kuma zan yi miki hukunci mai tsananin gaske."
Ta ce." Hukunci ya wuce wanda kake yi mini a yanzu. Ni ina ruwana da yara kuma abinda ya dame ni daban me zan yi musu ai ni ba azzalima ba ce."
"Na dai gaya miki domin na san halinka ba ki da mutunci babu ruwanki da kowa."
Ta fashe da kuka tana fad'in." To na ji, yanzu sai ka gaya mini menene makomata ai ba maigadi ba ce ni. Wane irin zalinci ne wannan kake yi mini 'kiri-'kiri an raba da ni da yarana suna k'yamatata ai duk tsiya ba za su canza ni ba."
Shiru ya yi mata. Ta cigaba da cewa." Ka gaya mini menene matsayina gaskiya na gaji wallahi, Allah kuma yana ji yana gani."
Ya dube ta sosai tare da cewa." Na yi na yi na ga na ha'kura na yafe miki na kuma sanyawa zuciyata sonki da kaunarki amma kin san Allah babu waje a cikin zuciyata da farfajiyarta Amina ta shimfida mashinfidinta ta zauna daram da can Samira tana da waje amma yanzu Amina ta mayaye ko'ina ita kadai ce a ciki ba kuma na tsammanin har abada wata maccan za ta samu irin wannan sararin."
Ta dinga wani irin kuka mai tsuma zuciya da sosai rai wanda duk wanda ya ji sautinsa sai ya tausaya mata amma a wajensa ma damunsa take yi so yake ta tashi ta fita ta bar masa d'akinsa.
"Ni ba zan ta'ba yi maka irin wannan 'kiyayyar ba domin ko banza mun had'a jini kuma na haihu da kai yara uku duk irin cin fuskar da za ka yi mini da tozarcin da za ka yi mini ba zai dame ni ba, hakkina dai da yake rataye a wuyanka wallahi ba zan yafe maka ba, ka zalince ni kana k'untata mini kuma ba zaka sawwa'ke mini ba idan an yi duniya don manzon rahama ba zan sake nemanka ba."
Ya ce." Hakan ya fi miki Hajiya ai ban hana ki ba idan kina da kwanjin da za ki kwaci hakkin na ki bismillah ai ga ni a zaune."
Ta tashi jiki a sab'ule ta kama hanyar fita kamar zata mutu saboda b'akinciki.
Har ga Allah ba na jin dad'in fuskar gizagon da yake yi wa Hauwa gabad'aya duka kowa ya gane Hauwa bora ce a gidan zaman ha'kuri take yi masu aiki duk sun gane irin zaman da suke yi da ita da maigidan. Abin ya dinga damuna a ganina ai shi ne namiji kuma jagora ce ya ci ace ya tsahirta da wannan tsatstsauran hukuncin da yake yi mata ta dahu lugub ta yi mugun laushi ta kuma tsunduma a cikin nadamar abinda da ta aikata. Shine bai sani ba ko kuma na ce ya sani yana takewa amma mugun zunubi yake nannagawa kansa domin wannan fad'in Annabi Muhammadu S.a.w ne.
Wannan dalilin ya sanya ni ranar da za mu tafi Legos din da daddare na shiga d'akinta na sameta a zaune ita kadai kan gado ta kunna tivi amma gabad'aya hankalinta ma baya kanta kuka take yi tana waya ganin shigowata ta katse wayar tana share hawaye na yi kamar ban lura ba.
Na zauna gefenta muka gaisa na ce." Ya gaya miki Legos za mu tafi gobe ko?''
Ta ce." E, ai jiya mun d'an jima muna magana da shi akan tafiyar taku.".
Na d'an yi shiru Ina nazarin maganarta wadda na tabbatar da cewa 'karya ce kawai wai ita dole sai ta nuna mini suna shiri bayan komai a bayyane yake.
Na ce." Ai da so na yi ku tafi tare idan kun dawo zai sake komawa sai mu je kamar hakan zai fi."
Ta yi ya'ke tana cewa." Duk daya ne Amina ku je tare ni zan kula da yara kamar yadda jiya ya gaya mini cewa ya ba ni amanarsu za ku dawo ku same su lafiya in sha Allahu."
Kamar zararriya haka take magana a tsorace tunda tasan duk abinda zata fad'a ba gaskiya ba ne shiyasa ta kasa had'a ido da ni.''
Na ce." Hakan ya yi Hauwa dama na ce bari na shigo mu yi sallama tunda da wuri za mu tafi wata'kila kina bacci a lokacin."
Kanta a 'kasa ta ce." Hakan ya yi na gode sosai Amina sai kun dawo din.''
Na mike tsaye ina fad'in." To saduwar alheri Hauwa sai mun yi waya." Daga haka ban sake cewa komai ba na kama hanyar fita zuciyata da damuwar halin da take ciki kada fa mutumin nan ya zautata da bak'incikinsa domin duk ta shiririce wallahi........
'
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*
*139*
Ba na tsammanin ya yi sallama da Hauwa da za mu tafi haka na bi shi ba don zuciyata ta so abinda yake aikatawa ba sai don sanin rashin yadda zan yi da shi. Tunda tsakani da Allah daidai gwargwado yana da ilimin addini ya kuma san abinda yake yi din ba daidai ba ne. Na zura masa Ido kawai domin nasan muddin bai gyara ba Hauwa za ta sake tafiya gidansu mahaifiyarsa kuma ta samu labari anan sai ta gane cewa shima ya fi kyarfinta ba Hauwa ba ce kad'ai mara ji shima lamba d'aya ne.
Zuwanmu legos ya sake haifar mana da nutsuwa da kula da juna da kuma bud'e babin soyayya kamar sabbin aure duk da 'karamin cikin da nake d'auke da shi bai hana mun mori juna ba
a duk lokacin da ya zo wajena da buk'ata irin ta d'abia. Daga lokacin na gama gazgata k'aunar da yake mini cewa babu algus ko almundahana domin duk wani nau'in kulawa ina samu da tarairaya har da kyautar kud'i miliyan biyar ya yi mini yana gaya mini na kara akan kasuwancin da nake yi domin yana hankalce da irin nauyi da d'awainiyar da nake yi a b'angarena.
Na yi godiya sosai da addu'ar k'ara samun budi da fatahi ya ce babu godiya a tsakaninmu a duk lokacin da nake da buk'atar kudi domin yin wani abu da zai kawo mini cigaba zai tallafa mini saboda yana girmama duk wani wanda yake tsaye don dogaro da kansa karin abin kuma ina ko'karin ganin na yi alheri da taimakawa wad'anda na fi su wadata.
Na ji dad'i sosai da sosai dama kuma mun yi magana da anti Yagana akan jari da zan bata ta yi sana'a ta ce mini tana so ta bude shagon jikin gidanta ta fara harkar provision da awo na ce mata harka ce mai kyau sosai kuma za ta samu alheri domin yanzu masu sayar da abinci kayan masarufi sune suke da kudi a hannu. Abinda na yanke a raina cewa ita zan turawa kudin gabad'aya ta fara idan Allah ya sanyawa kasuwancin albarka sai ta zama babbar dila ta bud'e manyan shaguna. Sai dai abinda yake dan damuna shine shin kudin da ya ba ni zai bawa Hauwa ko kuwa. Ina sonsa ba kuma zan yi farinciki da cewa ranar lahira ya tashi a cikin sahun mazan da za a yi musu azaba dalilin fifita bangare daya na daga cikin matansu.
Kuma daidai gwargwado Hauwa ta kar'bi kuskuranta yau satin mu uku a Legos idan ba ta kira ni a waya yau ba to gobe za ta kira ni mu gaisa a sati sai mu yi waya biyar ko hud'u mun yi vidiyo call sau d'aya da ita kuma ban hangi nutsuwa da kwanciyar hankali a tare da ita ba. Abinda na fahimta shine kamar tana kamun kafa da ni akan mijin nata wanda ni kuma nasan ban isa na sanya shi ko na hana shi ba tunda ga abinda ya yi wa mahaifiyarsa na yaudara ya nuna mata kamar ya ha'kura ashe akwai abinda ya ajiye a ransa na ramuwar gayya.
Na dinga nanata masa kan cewa yadda ya ba ni kudin nan Hauwa ya bata hakkinta ne. Na farko da na gaya masa shiru ya yi mini bai ce komai ba ya cigaba da sabogoginsa tunda ya ce mini yana shirye-shiryen bud'e sabon kamfanin na suminti ne wanda suka yi tarayya da yaran Alhaji Amadu abokinsa Salim da Adam da Nusaiba. Yana so ya fara sanya Salim din cikin harkokin da yake gudanarwa domin ya tsaya da kafarsa a matsayinsa na namiji babba da ake sanya rai a nan gaba zai zama wani abu. Mahaifinsa Alhaji Amadu harkarsa kenan sayar da siminti da sauran abinda ya danganci gini gidaje to shine yake so ya d'ora yaronsa a kai.
A k'alla dai sai da na yi masa maganar Hauwa ya kai sau shida tukkuna ya tanka mini da tashin hankali ya rintse idonsa yana gaya mini babu ruwa da duk abinda yake yi na dawo masa da kudinsa idan ba na so tunda bai isa ya yi mini kyauta na ce na gode ba sai na yi masa gyara saboda na mayar dashi jahili Wanda ba shi da addini.
Na kuwa bud'e wuta ni ma na ce ai gaskiya ce kuma d'aci ne da ita ban iya munafurci ba kuma zan yi masa shiru ya danne mini baki da kudi mu zalinci wata ba domin ba ni so na mutu da hakkin kowa.
Ya ce idan akan Hauwa nake yi masa rashin kunya sai ya saketa kowa ya huta.
Na ce masa dama hakan ya yi shi zai kara tabbatar mini da cewa babu wanda ya isa.
Magana ce mai harshen damo ya tsargu sosai daga ranar da muka yi haka ya daina kula ni tsayin kwana uku muka yi ba ma magana gashi Muna kwana a d'aki daya a gado daya sai da ya juya baya ni ma na juya nawa.
A ranar na hud'u ne muna bidiyo call da Hauwa na ce mata ta had'a ni da yaran mu gaisa na yi hakane domin na daidaita alakar da take tsakaninsu..
Aikuwa da azama ta tashi ta fita falo alhamis ce babu islamiyya ta yamma ina zaune ina kallonta ta shiga dakinsu tana Kiran sunan Khalil.
Ya zo ya zauna a gefena ban ce masa komai ba shi ma bai ce mini komai ba amma dai tun shekaran jiya na fahimci jikinsa ya d'an yi sanyi ya rasa yadda zai yi ya rarrashe ni ya kuma nuna zai gyara kuskuransa.
Daya bayan d'aya muka dinga gaisawa suna ta tsalle da dariya mussaman Minal sai washe baki take yi. Ya yi gyaran murya yana fad'in." Ni ba bu wanda yake nema ko?"
Jin muryarsa ya sanya suka dinga kiran sunansa." Baba" Baba.'' Ya kar'bi wayar ya haska musu fuskarsa sai dariya suna kiran sunansa yana amsawa cikin nishadi yana cewa ni babu wanda yake nema na ko?"
Usai ta ce." Baba yaushe za ku dawo?"
Ya ce." Mun kusa in sha Allahu ana zuwa makaranta ko?"
Suka ce "Eh.'' Ya gyad'a kansa yana fad'in." Muna nan dawowa in Allah Ya yarda."
Hauwa ta kar'bi wayar daga hannun Khalil tana hasko fuskarta ta ce masa "Ina yini?'' Ya amsa da sakin fuska har yana tambayarta yara."
Cike da jin dadi ta ce." Gasu nan ai suna ta kewa" a Takaice ya ce." Mun kusa dawowa amma ke ba ki yi kewar ba."
'Yar dariya ta yi kamar an yi mata dole ta ce.'' Sosai na yi kewar ku gabad'aya."
Ya yi murmushi a hankali ya ce." Duk ranar da na yanke mana dawowar zan sanar dake."
Da jin dadi ta furta." To shikkenan." Ya mik'o mini wayata na kar'ba muka d'an yi magana da ita akan yaran sannan muka yi sallama tare da bata sakon gaisuwa wajan masu aikin gidan.
Na kashe wayata na ajiye ban dube shi ba na sake hade raina sosai domin har yanzu ina jin haushin bala'in da ya yi mini sai kace 'yar cikinsa daga kawai an ce gaya kayanka.''
Ya riko hannayena duka biyun na dube shi amma ban saki fuskata ba. Sai ya sanya hannunsa d'aya a kumatuna yana ta'be mini fuska da hanci yana d'an murza mini fatar le'be. Tankwa'be hannunsa na yi ya sake mayarwa ya cigaba da ta'bule mini kumatuna da hanci na sake cire hannunsa a karo na biyu.
Ya sauke ajiyar zuciya a 'dan sanyaye ya ce." To ki yi dariya mana tunda na yi magana da ita?''
Juyar da kaina na yi gefe ban ce masa komai ba. Ya matso sosai yana fad'in. Ki yi dariya my love menene haka umm!
Na ce." Wallahi ka ba ni haushi sosai wai me kake ji idan kana gaba da mutum ne babu kyau fa kuma

Please Login or Register in order to submit comment