Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba amma ya fi ni sanin dalilina na yin hakan zan nemi maganin da cikin zai fita tun kafin ya kai matakin da za a busa masa rai a yanzu dai bai wuce kwanaki a arba'in ba na tabbatar da samuwarsa ne had'uwarmu ta farko dashi zuwana Abuja tunda lokacin da na je ban fi sati daya da yin wankan tsarki ba kuma ni ba ban yi amfani da wata kariya domin gujewa faruwar hakan ba. Mun had'u sosai tun kafin ma na tafi maiduguri mun yi kwanciyar aure amma rabon bai rantse ba sai yanzu.
Da kaina na fita da daddare bayan Isha'i cikin hijab har kasa da nikabi har da safar kafa domin yin b'adda kama na nemi maganina na dawo gida.
Zuciyata tana dokawa a daran ina ta shawarwari nasha ko kada nasha domin sai nake ganin kamar Allah zai tuhume ni kuma ba zai kar'bi uzurina ba tunda tun farko ai ba a san da menene silar dake haifar da ciwon ba iyaye da kakanni haka suka yi auransu ba tare da sanin matsayin jini ba. Domin kuwa da yawa As da As suna yin aure ba su san alakar jininsu ba kuma su yi haihuwa fiye da goma ba tare da samun wani mai lalura ba. Da yawa kuma akwai masu S A da S A din da suke aurensu lami lafiya su gama haife haifensu ba su ci karo da komai ba kuma yaransu duk yawansu suna rayuwa. Kamar yadda anti Yagana tasha gaya mini turawa ne suka kawo wannan rikitarwar har aka kafa doka mai k'arfi akanta. Akwai ciwon ba wai babu ba to amma babu hujja mai karfi wadda za a guji auratayya domin raya sunnar Annabi Muhammadu S.A.W.
Cike da cajin kai da zullumi tare da fargaba na sha maganin amma daya nasha sabida yana da k'arfi dayan kuma na yi flushing dinsa.
Wajan karfe uku na tashi da matsanancin ciwon mara da baya, tare da cijewar kafafu. na dinga murkususu ni kadai don sallar asubahi ma sai da safe na yi ta. Abin karin kummalo d'akin Yusura ta kawo mini domin ban Kai ga fita falon ba ina kwance a gado murfin gwiwata sai ciwo yake yi mini da kafafuna kasan marata amma babu d'igon jini a pant dina sai da uban ciwon dai.
Na dinga zurga zurgar zuwa bandaki ina dubawa babu wata alamar zubar wani abu. Jikina ya mutu murus na yi kwance a gado ina istigifari ga Allah lallai duk yadda na kai ga so cikin ya fita idan fa Allah bai kaddara ba sai dai na ci wahalar kuma na haife shi babu yadda zan yi
Idan kuwa aka yi rashin sa'a na shiga hadari gagarimi sakamakon shan maganin da na yi cikin bai fita ba kuma ba ni da tabbacin cewa yana cikin 'koshin lafiya sakamakon yun'kurin zubar dashi da aka yi da ganganci.
Hawaye ya shiga silalowa daga idona tausayin kaina ya kama ni. Na ha'kura kawai na barwa Allah lamarinsa muddin cikin nan bai fita ba kafin yamma to ba zan yi yun'kurin sake zubar dashi ba. Duk abinda Allah Ya yi daidai ne.
Da k'yar na iya kur'bar shayi na ci dankali da 'kwai kad'an na sake kwanciya da wayata a hannuna zuciyata na tashi yayin da nake dan jin sasaauci daga kasan marata na rintse idona a hankali ina tasbihi ga Allah tare da sake jaddada istgifari domin neman afuwata.
Bayan azahar sai ga Sahura da ma mun yi waya da ita ta ce mini za ta zo a cikin satin da muka shiga. Dole ta sanya ni k'arfafa jikina domin kada ta fahimci wani abu amma duk ko'karin da na yi gurin kwarara gwiwata sai da ta gane ba na jin dadi ta fara zolayata wai ko nayi tsaraba daga abuja ne domin wallahi alamun mai yaron ciki ya bayyana a tattare da ni. Bagarar da maganarta na dinga yi na ki ba bata muhimmanci har ta yi ta gama ta fara gaya mini an zo tambayar auran Yusura kuma za a kawo kudin auran ranar juma'a wannan din nan ne dai dan gidan Yayar babanta wanda na tambayeta ta ce mini shi take so kwanakin baya sosai na yi farinciki da jin haka domin duk wani bincike sun yi tana kuma jadadda mini cewa yaron mane mi ne mai zuciyar neman na kansa kuma yana can yana gini a sabuwar unguwar nan ta rimin auzinawa. Yadda ta dinga zolayata ni ma haka na dinga zolayata ina dariya ta tsufa don ana yi wa Yusura aure shekara daya za ta haihu dole ta dau'ki jika. Fad'i take ai tare muka tsufa domin kuwa 'yar ki ce ba tawa ba.
Sai da ta yi sallar magriba tukkuna ta yi shirin tafiya na sanya sabon direban da aka ajiye mini ya dauketa a mota ya kai ta har gida.

To mukan d'an yi waya da maigidan sa'i da lokaci amma mafi akasari shi yake kirana idan ya samu sukuni ba sosai ya fiye amsa waya ba sai mai mutukar muhimmancin gaske Amma fa shi yana kirana a duk lokacin da yake da isheshhen lokaci sai mu fi karfin awa daya muna hira ta waya sosai. Amma fa ko da wasa ban ta'ba kuskuran gaya masa wani abu ba tunda cikin bai fita ba na bar shi kawai duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa.


Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta shi ba tare da kin biya ni hakkina ba.


Bayan wata biyu da dawowo ta ina lissafin watannin cikin dake jikina wata uku da kwanaki kenan wannan karon laulayi nake yi sosai domin kuwa ba komai nake iya ci ba na fi kauri dai a b'angaran manja da yaji wainar fulawa ko d'anwake da manja ko d'anmalele. Sai ko kayan gona wannan kuma Hamusu nake sanyawa ya sayo mini duk bayan kwana uku ya kawo mini hidimar soya waina da danmalele kuwa Yusura ce ke yi mini. Duk cika da kasaitata a ko'ina sai da na rairaye saboda azabar laulayi ban fita na je ko'ina ba balle a gane halin da nake ciki itama Sahura tun zuwan da ta yi bata sake zuwa ba sai dai mu yi waya. Anti Yagana ma waya muke yi kuma ban gaya mata komai ba. Ta ce mini dai karshen shekaran nan za ta zo amma ita kad'ai ba tare da yaran ba saboda makaranta. Muka tsaya akan zuwanta a karshen shekaran nan da muke ciki to sai dai kana taka Allah Ya na tasa domin kuwa rikicin da ya ritsa da Hadiza shine abinda ya tilasta mata zuwa ba tare da shiri ba.
Hadiza garin neman duniya da son lallai sai ta yi kudi bayan tafiye-tafiyen da take yi zuwa dubai sarin kaya ashe ta had'a kai da wata mata da suka hadu a can dubai din itama 'yar kasuwa ce mazauniyar Na'ibawa anan gidanta yake kuma bazawara ce babba da yaranta ta ribaci Hadiza tare da kwaid'ata mata kudin da zata samu idan ta shiga 'kungiyarsu ta shan jini. Ba tare da dogon nazari da tunani ba tunda dama babu wani sanin addini a tare da ita ta fantasma kanta a harkar da babu fita muddin an shigeta kuma sharad'in shine dole sai mutum ya bada jinin dan adam mutum guda.
Suka had'a baki da ita Hajiya Alili suka saci wani almajiri suka mika shi ga kungiyar kamar yadda suka buk'ata da da farko cewa suka yi da ita sai ta bada d'anta na cikinta ta ce musu ai bata taba haihuwa ba shine suka buk'ace ta cikin kwanaki biyu kacal ta kawo musu matashin yaro wanda bai balaga ba.
Matsanancin tashin hankali muka shiga gabad'ayanmu domin lamarin da ya faru sai yake nema ya shafi zuri'armu gabad'aya mutane suna ta ririta maganar tare da 'kir'kiro k'arya da gaskiya har da masu cewa dama sun jima suna zargin alhalinmu ko maita ko karuwanci ashe 'yan mafiya ne, wasu kuma na cewa gidan namu dama ai ya yi 'kaurin suna yara tun suna k'ananu suke sace sace......
'þ

Mun shiga book3 anan har mun yi rabi fa, ina ga ya kamata ku shi mini albarka don ban ta'ba kawo muku wani uzuri ba kullum sau biyu kuke samun update sannu sannu bata hana zuwa=ØÞ=ØMÜ Na gode muku sosai.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*

*60*
Hadiza ta zama kamar zautacciya domin kuwa ita da mahaukaciya marabarsu kalilan ne zafin addu'a da irin saukar karatun al'kur'ani da ake yi akan 'batan yaron ya sanya da bakinta ta fad'i ta yi kisan kai domin kuwa yaron tuntuni an shanye jininsa hakkin rai da rashin sabo ya sanya nutsuwa ta yi kaura daga jikinta.
Yadda bincike ya nuna ita Hajiya Alili tunda ta ji maganar ta fasu a gari ta yi 'batan dabo aka nemata a ka rasa a garin. 'Yan unguwa suka cinnawa gidanta wuta ita kuma Hadiza muna ji muna gani mota guda da 'yansanda suka tafi da ita. Tashin hankalin da ya assasawa Babanmu fad'uwa kenan ranga ranga rai a hannun Allah muka kai shi asibitin nuna koke-koke don wallahi ni tsananin damuwa da fargaba ya sanya na manta halin da nake ciki duk wasu lalure laluran da nake yi a tsaitsaye nemansu na yi na rasa saboda tsananin tashin hankali da fargaba don sai na ce na jima ban ga abinda ya daga mini hankali kamar wannan lamari ba. Da yake tunda ta bar gidana ban sake ganinta ba sai da wannan abin ya faru gabad'aya kammaninta sun canza ta zama kamar wata tsohuwar kilaki hujin hanci biyu kowanne da barima a sak'ale har da sarkar kafa a kafarta ta hagu. Hankalina ya sake tashi a fakaice na dinga share hawayen tausayi da nadamar duniya domin dai Hadiza ta gama tona mana asiri ta 'bata mana nasabar gidanmu, ta ci mutuncin Babanmu yanzu da muna da sauran 'yan uwa mata da wahala su auru da wuri dalilin wannan abin kunyar da ta janyo mana. Anti Yagana tana da juriya sosai ban ga kwalla a idonta ba amma a gigice take mussaman da Babanmu ya fadi. Ita kam Fati dama tana da iskokai domin tun tana yarinya sun taba nunawa zaman bori tayi a tsakiyar tsakargida suka dinga haurowa kanta suna ifece-iface anti sakina ita ce taje ta gurfana a gabanta tana yi mata addu'a.
Muka dinga zurga da kai kawo daga gidanmu zuwa asibiti zuwa ofishin 'yansanda. Ni da anti Yagana mune manya kuma mune masu rufin asiri a ciki. Itama Ummansu Hadiza sun ri'ke dukiya a da can domin mahafinsu tsohon mai kudi to amma yanzu babu domin duk rabinsu sun karye dalilin fafar da suka dinga yi da kudin gadon, kuma dama kaf gidansu babu wani fitacce wanda ya samu ilimin addini sun taso da jin dadi da gata irin na mahaifi wanda shi din aka shede shi mutumin kirki ne, kuma dukiyar da ya tara musu ta halak ce domin ko da can ma baya had'a hanya da riba. To babu
abin yanzu da yawa wasu daga cikin danginta ma sukan rasa abinda za su sarrafa a cikinsu su bawa iyalinau. Ga masifar da take ciki bata fita ba wata ta kara kutsowa Alajiji d'anta na fari da ta haifa a wani gidan ya je ya damfari wani makudan kudi asirinsa ya tuno yana hannun hukuma suna bincike akansa domin dama tsohon mai lefi ne ya jima yana harkar yahoo 419 shine kiran da ta yi Alhaji Tajo a kwanakin baya ta ke gaya masa ya taimaka musu. Son zuciya Sacinta kuma duk wanda ya sayi rariya tabbas ya san sai ta zubda ruwa idan da godiyar Allah iya jarin da Alhaji Tajo ya bata ya isheta ta juya ta kuma ri'ke kanta har ta kula da wasu to amma ta sanya son zuciya da son dole sai ta yi kudi ta kowace hanya ga abinda ya janyo mata nan.
Anti Yagana a gidana ta sauka wannan dalilin ya sanya muke zurga zurgar tare domin ba zan ta'ba bari ta yi ita kadai ba. Hankalinmu bai kwanta ba har sai da muka ga jikin Babanmu ya dawo yadda yake tukkuna muka samu nutsuwar tattauna yadda za a kamo bakin zaran matsalar da Hadiza ta rikitowa kanta. Lamari ne gagarimi wanda duk wanda ya ji abinda ta aikata ya jajanta mata don gaskiya da wahala idan hukuncin kisa bai rataya a wuyanta ba gashi an yi an yi da ita ta fad'i wurin da mutanan da suka sanyata suke ta'ki fad'a duk kuwa da azabar wahalar da take sha a hannun hukuma. Ranar da muka je da dubata alfarma kawai suka yi mana dalilin ina auran Babban mutum amma da babu wani uzuri da zai sanya su bar mu shiga wajenta. Kuka wiwi na dinga yi ganinta a jigace ta dimauce jikinta duk shacin duka abinka da farar fatar da aka had'a mata da man bilitin ta ki'dime sosai tana ta zantuka marasa tushe anti Yagana ce mai dauriya bata koka ba amma idonta kadai ya tabbatar mini da cewa kukan zucci take yi. Fati kam fad'uwa ta yi a wurin aljanu suka bugeta a karon da ba zai lissafu ba domin tunda aka kama Hadiza take iskokai
Hassana da Usaina suka fita da ita can waje domin wurin da muke babu iska. Da muka fito anti Yagana ta gargadi su Hassana akan kada wadda ta kuskura ta gayawa Ummansu halin da muka tsinci Hadiza su nemi hanyar da zasu kwantar mata da hankali koda kuwa ta 'karya ce don za ta iya shiga mummunan yanayi muddin ta ji halin da Hadizan take ciki.
A daran aka sallami Babanmu daga asibiti a waya na kira Ayuba sabon direba na ce dashi ya zo ya d'auke mu a mota gabad'aya domin a galabaice nake kwarai da gaske gajiya da jiri da ciwon mara da kafafu ban kuma kawo komai a raina face wahala da fargaba tare da kai da kawon da na yi.
Muna komawa gida ni da anti Yagana na zube a tsakiyar d'akina domin wani mashahurin ciwon mara ne ya turnike na dinga murkususu ina ri'ke cikina anti Yagana hankalinta ya tashi sosai ta kira Baba Tabawa tana cewa mu je asibiti na girgiza mata cikin halin da nake ciki na fara yun'kurin amai amma bai fito ba kakari na ke yi ban amayar da komai ba sai can na ji kamar an fasa ruwan pure water a zanina jini mai yawa ya fara gudana har ya fara naso a kafet din daidai inda anti Yagana ta ajiye kafarta. Cikin fitar hayyaci na furta." Anti Yagana 'bari zan yi jini ne yake zuba."
A ki'dime ta tsuguna gabana ta daga cinyata jini sharkaf ya jika mini zani sai ta fashe da kuka tana fad'in." Ciki ne dake dama Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ta k'walawa Yusura kira tare da ce mata ta gayawa Ayuba ya fito da mota za mu je asibiti. dishi dishi na fara gani domin kuwa kafin faruwar hakan na yi masifar tsorata da irin mahaukacin jinin da nake zubarwa wannan shine ya assasa d'aukewar ji da ganina na wucin gadi.

To cikin dai ya zube a lokacin da ban yi tsammanin fitarsa ba. Wahala kuma na ci ba 'yar karama ba domin kuwa biyu ne ashe na farkon ya fita ba mu jima da zuwa asibitin ba. Na biyu sai da aka kai ga yin wankin ciki tukkuna aka yo waje dashi. Jini kam na zubar ba kad'an ba aka dibi na anti Yagana aka sanya mini aka nemo leda daya a waje a kara.
Tun a daran anti Yagana suka yi waya da maigidan ta sanar dashi halin da ake ciki. Ina jinshi lokacin da yake gaya mata ai ban ta'ba sanar dashi ina da juna biyu ba har wata uku da sati uku. Ya ce mata in sha Allahu gobe mu tsammaci zuwansa. Da safe Baba Tabawa da Yusura suka tafi gida domin yin abinci. Anti Yagana tana tare da ni a asibitin motsi kad'an sai ta dube ni ta share kwalla. Jikina ya yi sanyi na fara zargin ko likitan da yake tsaye a kaina ya yi mata bayanin wani abu ne. Ni babbar fargabata ma zuwansa asibitin nan domin kuwa gabad'aya na yi sanyi da lamarin dalili na riga na san likitocin asibitin Malam Aminu suna da gogewa ta fannin aikinsu dole zasu yi binciken abinda ya asassa fitar cikin nawa.
Jiki babu wani kuzari na yi wanka da ruwan da ta had'a mini a bandakin dake cikin d'akin da nake kwance da yake waje na mussaman suka ajiye ni a asibitin dalili tun shigowarmu security suka shaida fuskata duk kuwa da yanayin da nake ciki na ciwo.

Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na shirya cikin doguwar riga na kintsa jikina sosai cikin rashin kuzari da k'warin gwiwa gabad'aya rashin walwala da sukuninta ya fi damuna sosai akan fitar cikin daga jikina.
Likitan da yake duba ni ya sake shigowa muka gaisa ya yi mini tambayoyi na ce masa jiri ne ya fi damuna sai rashin jin dadin jikina. Magunguña ya had'a mini tare da ba ni shawarwari da yadda zan yi amfani da maganin ya ce mini sun yi waya da Yallabai din ya ce ya iso garin amma yana dambatta wurin mamanshi zai jira zuwansa asibitin kafin ya tafi gida tunda dama aikin dare yake da shi.
Shiru na yi ban iya ce masa komai ba anti Yagana ta yi masa godiya kafin ya fita. Ina kallonta ta je ta yi wanka ta kimtsa jikinta ta sake zama a gefana ba ta da niyyar cin wani abu bayan gashinan Baba Tabawa ta yi abinci mai kyau Ayuba ya kawo. Na daure na yi mata magana a hankali ta dube ni amma ba ta ce mini komai ba. Na ce." Ba ki ci abinci ba anti Yagana."
Kanta ta girgiza a hankali ta furta." Ba na jin yunwa Amina har yanzu ban daidaita ba wallahi jiyan nan na shiga rud'ani ba kad'an ba sai nake ganin kamar za ki tafi ki barni ne."
Hawaye ya sake silalo mata.
Murmushi na yi cikin raina na ce dama abinda take yi wa kuka kenan. Anti Yagana kenan ai mutuwa kam ta zame mana dole ko na rigata ko ta riga ni babu wanda zai zauna a cikinmu.. Na daure na ce." Ni ma ban ta'ba jin ciwo mai azaba irin na jiya ba wallahi ni kadai nasan halin da nake shiga anti Yagana Allah dai ya takaita mini wahala."
Ta gyada kanta da kulawa ta furta." Gashi ma ashe 'yan biyu ne amma me yasa ba ki taba gaya mini kina da ciki ba Amina, ai ko baki sanar da kowa ba kya gayawa wanda ya yi miki jiya da muka yi waya yana ta fad'a shi bai sani ba."
A dan sanyaye na ce." Anti Yagana shurun da na yi masa shi ya fi alheri domin kuwa nasan halinsa idan ya samu labari zai hana kansa sukuni ne, ni a tawa fahimtar kawai na bari ne duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa.
Ta ce." Wannan ba hujja ba ce ko dan gaba kada ki kara haka ai abin alherine kuma yana da hakki ki gaya masa. Baki san hakan zai yi masa ciwo ba kenan ga yanayin yadda yake magana a wayar ya tabbatar mini da cewa ya ji haushin abinda ki ka yi......
'þ

Akwai pege din da ban baku ba kafin wanda na jiya da daddare ban san yadda zan yi ba wurin tura muku shi. Wad'anda suke comments section zan tura can sai ku karanta mistake na yi wallahi ku yi hakuri.

*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=ØNÜ*
*61*
Na ce." Zan kiyaye in sha Allahu rabbi,
yanzu dai ki ci abinci ba na so na dinga ganin ki cikin damuwa da alhini duk abinda Allah Ya yi daidai ne fa anti Yagana don Allah ki daina daga hankalinki, dama can Allah Ya yi ba rayayyu ba ne."
Ta girgiza kanta da damuwar dai ta furta." Tabbas yadda Ubangiji ya yi shine daidai amma na so a ce kin haife tagwayen nan Amina, amma Ubangiji Allah Ya ba ki wasu, kin gaji Babanmu wurin haihuwar tagwaye ya yi sau biyu Hassana da Usaina da kuma na wurin Ummansu Saminu Hassanan da Usaini.. murmushi na yi tare da
Sunkuyar da kaina kasana furta." Dama ai an ce ana gadonsu bangaran uwa ko uba. Anti Yagana Allah dai ya ba mu masu albarka."
Ta amsa da Amin babu sukuni a tare da ita. Ni kuma na sake yin k'asa da kaina ina jin wani abu a can kasan raina
yanzu idan ba dan'uwanka na jini ba wanene zai gwada maka wannan soyayyar da tausayawa.
Tare muka ci abincin amma ni kadan na iya ci nasha maltina tana ci muna taba hirar lamarin Hadiza. Hamusu ya kira ni a waya ya ce gashi nan asibitin ya shigo dubani domin yanzu daga can gidana yake Yusura ta gaya masa ba ni da lafiya.
Anti Yagana da kanta ta fita ta yi masa jagora muka gaisa sosai dalili tunda na dawo daga abuja ba mu had'u ba sai a waya idan na kira shi ko ya kira ni dangane da harkokinmu ya ce zai tafi amma da yamma za su so tare da Gwaggo anti Yagana ta ce masa sai dai su je can gidana domin kuwa ta ji likitan yana fad'in ya rubuta takardar sallama yana jiran zuwan Yallabai din ne. Ya ce idan ba su zo da yamma ba to gobe da safe za su je can gidan muka yi sallama ya kama hanya ya tafi shago.
To sai bayan sallar azhar tukkuna suka zo asibitin tare da Hajja da Hajiya Saratu. Haka kawai sai na tsinci kaina da kasa had'a ido dasu gabad'aya domin hausawa suka ce mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi. Gabad'aya na kasa nutsuwa domin sai nake ganin kamar za a gane na yi wani yun'kuri a baya.
Hajja sai sannu take yi mini tana fad'in an auna arziki ai tunda cikin ya fita ba tare da wata matsalar ba. Hajiya Saratu ma ta jajanta mini sosai tana cewa idan da rabo a kusa sai a kara samun wani.
Shi kuwa ogan yana tsaye a gefan kaina tunda muka gaisa ya yi mini sannu bai sake magana ba yanayinsa dai ya nuna jimami da damuwar abinda ya faru. Jikina ya kara yin sanyi sai na kasa daga kaina na dube shi a lokacin da likitan ya shigo d'akin yana tambaya ko da matsala na girgiza kaina alamun babu komai. Ogan ya dora hannunsa a saman goshina sai likitan ya dube shi yana cewa." Da zu da muka yi magana da ita ta ce mini jiri ne kadai yake damunta amma in sha Allahu shi ma zai gusa nan da kwanaki uku tunda an dubata sosai babu wata matsala sai ta rashin kwarin jiki, bayan haka kuma ga magunguñan nan masu kyau na hada mata."
Hannu ya ba shi suka yi musabaha da juna yana yi masa godiya yayin da likitan yake jadadda masa cewa babu godiya domin kuwa aikinsa. Tare suka fita sai hakan ya haifar mini da damuwa don sai nake ganin kamar akwai wani bayani da likitan zai yi masa wanda yake b'oyewa. Hira suke yi a d'akin tsakanin Hajja da Anti Yagana dama akwai shak'uwa a tsakaninsu tun zuwan da anti Yagana ta yi wajena a lokacin

Please Login or Register in order to submit comment